Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tare da fashewa da kuka “Ciki de na Haihuwa? Kina da ciki? No! Ƙariya ne!!” dawowa tayi da gudu takai mata wani mummunan naushi a ciki, ƙara me ƙarfi Aaliyah ta saka tare da zubewa a ƙasa ɗif Numfashinta ya ɗauke na wasu daƙiƙu, ruwa me sanyi Jiddah ta zuba mata a Fuska tare da ɗagota “Karki yarda ki sake raɓan mijina ke ko Sunan mijina kikaji Ina so ki toshe kunnuwanki dan wallahi naji Mijina yana tare dake kashe ki zanyi!!” Kaman mahaukaciya haka Jiddah ta shiga dukanta ba ji ba gani, kafin ta shiga janta har ƙofan gida ta watsar da ita dawowa tayi cikin Gidan tare da Zuba fetur ta cinnawa gidan wuta tana fitowa ta tarar da Nabil yana shirin ɗaga Aaliyah dake ƙwance cikin jini Cikin wani irin mawuyacin halin Aaliyah ta Riƙe hannunshi tana faɗin “Yau nake shirin sanar da kai amma matarka ta ɓata komai Nabil Baby Na ciki gareni shine tazo ta kashe ni da Abinda ke ciki na” A zabure ya sa ke ta tare da nufo Jiddah nan ya shiga zuba mata mari cikin ɓacin rai “Akan me? Me yasa kika zubar min da ciki...”
“Nabilllll” da gudu ya nufi gurin Aaliyah tare da ɗaukanta yasata a Mota suka nufi asibiti.
Gida ta nufo gbɗy bata cikin nutsuwarta “Jiddah Ina kika je?” Ina Jiddah bata ma san da ita ake magana ba, riƙe ta Nuwairah tayi tana faɗin “Jiddah menene haka? Ya naga fuskan ki a kunbure waya dake ki?” wani irin kuka ta fashe dashi tare da faɗin “Nuwairah Yarinyar da Nabil ya ajiye har ciki gareka wannan Karuwar tasa nake faɗa miki ciki gareta saboda naje na dake ta shine Nabil ya mayar min da fuska haka Akan karuwa Ya min haka!” Cikin tashin hankali Inna ta ƙaraso gurin har zaninta na shirin faɗuwa kasa “Me nake ji haka? Ke! Jiddah me kike faɗa ne?”
Girgiza kai Jiddah ta shigayi tana faɗin “Babu komai..” Rufe mata baki Nuwairah tayi itama cikin kuka tana faɗin “Ƙwarai Abinda kunnuwanki suka jiye miki haka ne, Nabil ne ya ajiye Karuwa a waje duk wannan rigingimun da muke duk akan maganar ne..." Rufe mata baki Jiddah tayi tana girgiza mata kai alamar karta faɗa “ƙyale ni Jiddah Halin Nabil ya isheni gwara na fayyace komai” tiriyan-tiriyan ta dinga faɗa musu komai Wani wawan burki Nabil yaja yana kallon Nuwairah dake bayani Juyowa mahaifiyarshi tayi nan ta shiga zuba mishi mari tana faɗin “Wannan ba tarbiyan dana baka bane, wannan ba Renon Asma'u bace, Nabil kaine da ajiye mace a waje har da ciki?” sunkuyar da kanshi yayi ƙasa yana sake jin wani ɓacin rai, duk abinda suke Mahaifinshi na kallonsu jinjina kai yayi yana mamakin Halayyar da Nabil ya ɗauko “Da Girman ka, da ilimin ka, kana da iyali kasan Hukuncin zina kuwa? Anya Nabil baka fara shaye-shaye ba kuwa? To wallahi ka buɗe kunninka kaji da kyau bazan ɗauki wannan ƙazantar a cikin gidana ba, ban taɓa Zina ba, dan haka...” da sauri Jiddah tace “Dan Allah Abba karka masa baki, dan girman Allah kuyi masa addu'a shine kawai abunda yake buƙata” gyaɗa kai Mahaifinshi yayi tare da nuna shi da yatsa ransa a ɓace ya bar gurin haka ma mahaifiyarsa Nuwairah kuwa hannun Jiddah ta kama suka dawo part ɗinsu.
yanke shawaran barin Gidan Jiddah tayi, nan da Nan ta shiga haɗa kayanta tare da buɗe wani ƙaramin jaka ta ɗauko hoton Mahaifiyarta, rumgume hoton tayi tana hawaye sosai cikin kuka take faɗin “Umma lna cikin Ahalinki yau nice matsayin matar ɗan da kikafi ƙauna yau gashi zan barshi bazan iya cigaba da zama dashi a irin wannan rayuwar ba, bazan iya zama baƙin ciki da damuwa su kashe ni ba, gwara na koma inda na fito gwara na tafi kuma tafiyar da bana jin zan sake dawowa”
Zoben Azurfa da awarwaronsa ta ɗora kan hoton tare da ɗan shot note ta ajiye, ATM ta ɗauka tare da Nufar part ɗin Mama-Sadin ganin tana barci ne yasa ta juyawa da niyar fita ɗan gyaran murya taji mama tayi a hankali ta juyo tana kallon yanda Mama ke motsawa da sauri ta fita a gidan kuɗi masu yawa ta cire kafin ta bar ƙasar direct Gidan Fadilah ta nufa dan bata so kowa yasan tazo Nigeria daga dangin Ummi bata samu Fadilah a gida ba, me musu gadi ne yake sanar da ita tafiyan da tayi tare da mijinta key ɗin cikin gidan ta karɓa daga gurinshi kasancewar ya santa da Fadilah shiyasa bai wani damu ba, Ɗakin Fadilah ta shiga nan ta adana kayanta tare da shiga bayi tayi wanka a gurguje tazo ta biya sallolin dake kanta kasancewan dare yayi sosai bazata iya yin girki bane yasa ta haɗa tea kawai tasha ta kwanta.


Chadi....


Bana ganin Comment


Maman Faruq
12/26/23, 9:03 AM - UMMI JB: ♡SIRRIN ƊAUKAKA..!♡*


® AYSHA JB


FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION

Alhamdulilah jiki ya yi sauƙi sosai ina matuƙar godiya da addu'o'inku🥰🤝


35 Riƙe hannuwanshi tayi da ɗan ƙarfi tana kiran sunan shi, a hankali ya buɗe idanunsa tare da faɗin. “Sannu Aaliyah ya kike jin jikin naki yanzun?” ya ƙarasa maganar tare da shafa fuskan ta. “Da sauƙi Lover ai na ɗauka ka tafi..” Girgiza mata kai yayi sannan ya taimaka ma ta ta zauna, shafa cikinta tayi tana kallon shi da murmushi. “Kana murna kuwa?” zama ya yi kusa da ita tare da kwantar da kan shi bisa kafaɗarta shima ya ɗora hannunshi saman nata tare da sa kin kyakkyawan murmushi yana lumshe ido, sun jima a haka na tsawon lokaci kafin ya janye jikinshi daga gareta tare da nufan ofishin likita tattaunawa sukayi akan yanayin jikin na ta kafin ya dawo ya samu har ta koma barci gyara tsayuwar sa ya yi yana ƙare ma ta kallo tare da ƙurawa cikin jikinta ido, sosai yake jin farinciki mara misaltuwa a ran shi kallon agogon da ke ɗakin ya yi yana tunanin zuwa gida gashi dare ya yi sosai banɗaki ya shiga ya kama ruwa tare da alwala ya dawo ya shimfiɗa sallaya ya fara nafila a saman sallayan ya kwana washe gari aka basu sallama ya dawo da ita gida bayan ya sa an gyara komai na gidan da ƙyar ta ƙyaleshi ya nufo gida.
Nuwairah ce kaɗai zaune a falon domin tun jiya suke niman Jiddah amma babu ita babu labarin ta hankalin su ya yi matuƙar tashi sosai dalilin haka yasa mahaifin Nabil ɗaukan zafi kasancewar ba irin kiran wayan da ba'ayi masa ba amma ya ƙi ɗagawa Mama-sadin ma da taji labari hankalin ta ya tashi sosai inda ta shiga faɗa tana faɗin basu kyauta mata ba me yasa basu faɗa mata tunda wuri tayiwa abun tufkar hanci ba, shiyasa kwanaki take ganin Jiddah cikin yanayin damuwa ashe da walakin goro a miya domin Jiddah yarinyace me sakewa da mutane duk da ita ba mace bace me yawan surutu da son hayaniya amma akwai ta da daɗi hira ga iya tausasa lafuza duk maganar da zai fito daga bakinta me kyau ne da kuma ma'ana. tana da haƙuri da kawaici, sau da dama tana tambayar ta yanayin zaman nasu ba ta taɓa gaya ma ta wani abu da ake mata mara daɗi ba yawancin lokuta ma idan ta tambaye ta sai dai tayi murmushi kawai daga haka zata shashantar da zancen ta wani siga yarinyar ta shiga ran ta sosai tana jin ta kamar yadda take jin sauran jikokinta sai dai ƙaunar da take mata daban ne dalilin da yasa ta ɗaga hankalinta kenan akan ɓatan nata.
“Lafiya kuwa Nuwaih naganki cikin wananan yanayin?” kallon shi tayi tana jin takaici da baƙin cikin kasancewar shi ɗan'uwan ta wanda kuma yake matsayin miji a gareta ɗakin Jiddah ta nuna mishi tare da ɗauke hawayen dake zubo mata kallon ta yayi zuciyar shi na dukan uku uku a tunanin shi wani mugum abune ya samu Jiddan hankali a tashe ya nufi ɗakin cikin hanzari nan yaga gabaɗaya ɗakin a hargitse ga dukkan alamu babu wanda ya kwana cikin ta kallon inda akwatunanta suke yay nan yaga babu wasu daga cikin akwatunan zama yay gefen gadon tare da dafe kanshi da hannuwanshi duka biyu yana jin wani irin tashin hankali tare da tunanin Ina taje? Ina ta kwana? a wani hali ta ke? duk ba shi da me bashi wannan amsar kallon gaban madubin ya yi nan yaga gabaɗaya babu kayan kwalliya da mayukan shafe shafenta miƙewa yay yana zagaye ɗakin zuciyarshi na bashi lallai tana Nigeria yanzun haka, naushin iska ya yi yana jin babu daɗi a ran shi, ta gefen gadonta yaga awarwaro da sarƙa ɗauka yay tare da bude hoton dake gurin da wasiƙar da ta rubuta. “a lokacin da zaku iske wannan saƙon nasan nayi nisa Ina so abar wata maganar dangantaka kayi gaggawan aikomin da takarda ta, domin bazan iya cigaba da zama da mutum mara adalci irin ka ba, a yanzun na haƙura da aure da duk wani abu daya shafi ɗa namiji nafi sha'awar zama ni kaɗai domin babu komai cikin rayuwar Aure daya wuce baƙin ciki da damuwa. duka halin maza haka yake, duk yadda ka kai ga son gane halin maza bazaka taɓa fahimta ba, domin kullum cikin canzawa suke baka gane gaban su balle bayan su, Ina sake jaddada maka ka sauke min wannan ƙadararren Auren nake damin bazan iya cigaba da zama da kai ba, karka ɓata lokaci gurin niman inda nake” wani irin gumi ne yake tsattsafo masa tun daga tsakiyar kan sa zuwa wiyansa kalman Innalillahi wainna ilaihi rajiun kawai yake maimaitawa kallon hoton yake hawaye na tarige rigen saukowa akan fuskansa, Kenan Jiddah ɗiyar Ammah Asma'u ce? ita ɗin ƴar'uwa tace ta jini tasan da haka tsawon wannan lokacin shine bata bani fuskan da zan fahimci hakan ba? Ya Salam me kenan na aikata ban kyauta mata ba, juyowa yay da niyar zuwa shashin Mama-sadin nan yayi arba da Nuwairah tsaye “Ashe akwai ran da zakayi kuka? tabbas nasan wacece ita shiyasa tun farko na watsar da makaman yaƙina muke zaman lafiya nasan Jiddah ƴar'uwa tace Ƙanwa tace shiyasa nayi haƙuri muke zaman lafiya..” dakatar da ita yay ta hanyar faɗin “Kinsan da waɗannan abubuwan shine baki faɗa min ita ɗin Jinin mu ɗaya ba? maiyasa kika rufe ni? taya kika gano hakan? ni kaina nayi mamakin yanda lokaci ɗaya kika watsar da wannan kishin naki kuke zaune lafiya taya haka ta kasance?”
“Hanisa ita ta sanar min da komai ita ta sanar min da Jiddah ƴar'uwar mu ce, amma sai na musanta daga ƙarshe se nasa aka bincika min har can Benue ɗin a nan ne na samu labarin komai shiyasa na watsar da komai amman nace bazan faɗa ba, har sai ita da kanta ta fallasa komai. Nabil baka kyauta ba, bai kamata ka taɓa Jiddah akan wata karuwa mara daraja ba, bai kamata ka ɗagawa matarka ta Sunnah murya akan wata banza mara ƙima ba, Jiddah tana da haƙuri ni shaida ce.
Jiddah macece me sauƙin kai da kwantar da kai dan a zauna lafiya macece da abin duniya bai rufe ma ta ido ba, duk da tana kasuwanci amma haka tayi haƙuri tabar komai duk saboda tana son zaman Aure amma sai kaƙi fahimtar haka, duk wani ƙoƙarin da muke maka da ƙoƙarin sauke duk wasu haƙƙin ka dake rataye akan mu amma duk bamu ishe ka ba, meye a jikin wancan yarinyar?” shuru yay yana sauraronta daga ƙarshe suka nufi part ɗin iyayensu nan suka suka mishi faɗa sosai tare da nuna ɓacin rai akan abinda ya aikata mata shuru sukayi suna sauraron bayanin da Nuwairah take koro musu game da Jiddah “Innalillahi kika ce Asma'u ta rasu? Lahaula walakuwwata illabillah Allah sarki ashe babu rabon mu sake ganawa da Auta ta! Allah ya gafarta muku Husnah Allah yaji ƙanku da rahama ashe Hauwa'u jikanya tace shiyasa wani lokaci nake mata kallo kamar Asma'u ashe jininta ce to ka buɗe kunnuwanka da kyau ka jini maza-maza ka tashi ka nimo min jikanya kai harda ɗanta dan baza'a bar shi can ba, bazai yuwu mu danginta muna raye ita tana can wata uwa duniya ɗanta na tsakiyar kishiyoyi marasa adalci ba. Karka yarda ka dawo batare da ka samo su ba” Mama saddika ta ƙarasa maganar tare da fashewa da matsanancin kukan rashin ƴarta, nan suka fara lallashinta tare da kwantar mata da hankali.
Miƙewa ya yi yana duba wayarshi da niyar kiran ummi nan ya tuna ya bar wayan a gidan Aaliyah dole ya fito ya nufo gidan, sai dai ganin wata mota yasa shi shiga cikin mamaki fitowa yay yana kallon motan tare da nufar ƙofan ɗakin ya kai hannu da niyar tura kofan Bedroom ɗin nan yaji maganan daya kusan sumar dashi “Shi fa duk a tunaninsa cikin nan nashi ne bai san ƙariya nake masa ba, wallahi ina baka labari susucewa yay yana faɗa min in kula mishi da Cikin saboda yana tsananin son Haihuwa be san bayan shi Ina tare da kai ba...” da ƙafa ya taka ƙofan a zabure ta ja zanin gadon tana rufe jikinta, wayarshi yaje ya ɗauka tare da tattara duk wasu abubuwan da yasan nashi ne sannan ya nufi ƙofan fita yana faɗin “ki tattara duk wasu tarkacen ki nan da minti talatin ki bar min gida idan kuma ba haka ba se nayi miki dukan da yafi wanda Jiddah tayi miki shashasha wallahi nayi dana sanin haɗa jikina dake ƙazama! kariya!! kiyi gaggawan barin Gidan nan!”
“Nabil! dan Allah ka tsaya nayi maka bayani Nabil wallahi ina matuƙar ƙaunarka wallahi bazan sake ba, dama ɗaya kawai..” wani mugun tsawan daya daka mata ne yasa ta kasa ƙarasa sauran zancen nata fita yayi yana jin zuciyarshi na zafi, lallai ya aikata kuskure a tunaninshi cikin nashi ne ashe ba haka bane bayan shi tana tarayya da wanin sa, yana dawowa gida ya fara shirin tafiya washe gari kuwa sammako ya buga sai Nigeria ummi tayi mamakin ganinsa da kuma abinda ya kawo shi ranta ba ƙaramin ɓaci yayi ba lokacin daya ce mata ya biyo sawun Jiddah ne “To ai rabo na da Jiddah tun ranan da mukayi magana ta wayan ka bayan nan ban sake jinta ba, daman ina tunanin kiran ka ganin kwana biyu shuru ba labari” miƙewa ya yi da sauri yana faɗin “Innalillahi wainna ilaihi rajiun Allahuma ajirni fi musibati..”
“Amma bari na tuntuɓi Iyanmu in ji ko taje zaria” kiran Iyanmu tayi nan ma babu labari hankalinta ya tashi matuƙa nan ta shiga kiransu Halimatu da Hanisa suma cikin tashin hankali suke sanar ma ta lallai bata zo ba, babu ɓata lokaci suka iso gidan duk hankalinsu a tashi.
Ummi tace “To wai nikan meya haɗa ku da har tabar Chadi? anya Nabil ba wani mugun abu ka aikata ba kuwa? domin nasan halin Jiddah nasan irin tarbiyan dana bata faɗa min abinda ya haɗa ku”
Sunkuyar da kai ya yi yana jin girman maganan a ranshi “Bari na kira Fadilah ko Gurinta taje” cewan Halimatu kiran Fadilah tayi tare da sanar mata halin da ake ciki , nan ita ma take sanar mata cewan sunyi tafiya amma yanzun haka suna kan hanyar komawa gida in ta huta zata zo, daga haka ta ajiye wayan jiki a sanyaye fita yayi a gidan yana tunanin Ina zaije nimanta yanzun.
Kiran Arab Ummi tayi tana tare da sanar dashi halin da ake ciki sannan ta buƙaci ya kawo mata Aakif shuru kawai yayi yana kallon wayar domin bata jira taji abinda zai faɗa ba ta kashe wayar Kallon Nafisa ya yi kasancewar a ɗakinta yake nan ya sanar mata Halin da ake ciki “Masha Allah kaga yanzun babu wata damuwa inaga ka basu yaron kawai Ita kuma duk inda take Allah yasa tana hannu na gari” Jinjina kai kawai ya yi tare da miƙewa ya fita a ɗakin a falo ya samu Aakif ɗin Yana karatu “Aakif dare fa yayi sosai kaje ka kwanta haka mana” ɗagowa yayi tare da faɗin “To Abba” yana cikin tattara takardunshi hoton Jiddah ya faɗo kallon yaron yayi tare da ɗaukan hoton kana yace mishi “Kana son ganin Jiddah?” da wani irin mugum sauri Zaina dake fitowa daga ɗakinta ta ƙaraso gurin “Ji nayi kamar kace zaka kaishi gurin Jiddah Hahahaha! Nace maka Jiddah bazata taɓa zama da wannan yaron ba, nice tayi asiri na rabaku nice nasa aka tunzura zuciyarka har ka koreta sannan nice na hanaka Bata ɗanta duk wasu abubuwan da suke faruwa nice na aikata Hahahaha! Nice silar mutuwar Mazkhura nice nayi karan tsaye a rayuwar Jumana nice! Nice!!” miƙewa yayi ya shiga kifa mata mari ba gaggautawa da sauri Aakif ya riƙe shi yana faɗin “Abba kayi hakuri ka dena dukanta bata cikin hayyacinta mu kaita asibiti..” Nafisa dake fitowa tace “Babu wani asibiti Ishara ce Allah ya nuna mata, ai dama duk wanda ya ɗebo da zafi bakinsa” dariya kawai Zaina take ba ƙaƙƙautawa duk tayi wani iri nan ta shiga fisge kayan jikinta tare da watsar dasu, gashin kanta ta shiga fisgewa tana ihu da surutai da wani irin gudu tayi waje wani irin sanyi jikinsu yayi nan take tsoron Allah ya sake ɗarsuwa a zukatan su Fure'atu dake tsaye wani irin kakkarwa jikinta yake hankalin ta tashe, hakama Nafisa da Arab jikinsu yayi matuƙar sanyi fita yayi domin duba yanayin da take ciki sai dai duk yadda ya kai ga hanata fita Ina tafi ƙarfin sa Tafi take tana faɗin “Huhuhuuuu zan je gani nan zuwa Jiddah zan zo bazaki taɓa ganin daidai ba tunda kika ɗauke hankalin mijina Ihuhhuuuu ja muje ina tafe” a zabure tayi waje shi da mai gadi tare da me musu wanki suka mara mata baya, gudu take akan titi tana ihu da surutai wani Babban gwangwaro ne yazo a guje tare da take ta, gabaɗaya yanayin babu kyan gani baka iya ganin komai banda Ƙwaƙwaluwan kanta tare da kayan cikinta wadda suke waje duk tayi daga daga, motan na wucewa suka nimi gawar suka rasa zaman dirsham yayi yana faɗin “Innalillahi wainna ilaihi rajiun” kalman da yake ta nanatawa kenan gabaɗaya ya tsorata ya firgice ya fita cikin hayyacinsa haka aka rirriƙoshi zuwa gida wani irin mugun zazzaɓi ne ya rufe shi gabaɗaya jama'ar dake anguwar jikinsu ya mutu tabbas mutuwa babban wa'azice Nan kowa ya dinga faɗan halayyar ta da irin abubuwan da take aikatawa duk yadda Nafisa taso dubashi a gida kasawa tayi domin ita kanta tana buƙatar me dubata haka duka ɗunguma asibiti har Fure'atu Jumana ce kawai aka bari a gida tare da sauran yaran wadda suka rikita gida da koke koke.
** ** **
Buɗe ido nayi ina kallon Fadilah data zuba min marin a cinyata “Kai Amma Jiddah ke ba ƙaraman ƴar iska bace daman nan kika zo kika maƙale gabaɗaya kin ɗagawa mutane hankali kinga yanda ummi dasu Hanisa suka ɗaga hankali kuwa? yanzun fa daga can nake nace bari nazo na ɗanyi gyare-gyare se na koma kawai ina shigowa me gadi yace nayi baƙuwa wallahi take zuciyata ya bani kece Haba komai yayi zafi fa maganinsa Allah komai na duniya fa sai da haƙuri domin itace jagaba kuma jagoran dake tafiyar da komai, wallahi yadda naga Nabil ya bani tausayi sosai koma menene yayi miki tunda ɗan'uwan ki ne ya kamata ki ƙara Haƙuri akan na baya wallahi baki kyauta min ba domin lokacin da Ummi ta take magana hawaye take..” da sauri na tashi zaune ina faɗin “Ummin tawa ce ke hawaye wayyo Allah sarki Sorry ummi...”
“Allah ya shirye ki wallahi nayi tunanin zakice mu tafi ne yanda kika wani zaburo kika tashi zaune” yatsina fuska nayi tare da nufan Toilet da niyar wanka kiran Ummi Fadilah tayi tare da sanar mata Jiddah na gidanta jin haka yasa Nabil nufo gidan cikin gaggawa fitowa nayi ɗaure da zani yayinda nake goge gashi na da towel kasancewar na wanke shi ganin mutum kawai nayi a gabana take nasa ihu ina shirin zubewa saboda tsananin tsoron daya kamani da sauri ya taryo ta cikin jikinsa yana shafa fuskanta domin da gaske de sumewa tayi ruwa ya shafa mata a fuska tare da zubama kyakkyawan fuskanta ido yana kallon yadda take buɗe idanunta a Hankali tureshi nayi ina niman zani na wani irin Kyakkyawan Murmushi yayi tare da danneta yana faɗin “Im so sorry Jiddah nasan na aikata abubuwa da yawa Amma dan Allah kiyi Haƙuri komai ya wuce wallahi nayi nadama kaina bisa wuyana ina mai bada haƙuri kodan albarkacin Ammah da Ummi ayi haƙuri a yafe mini Please Sweetheart” ya faɗa cikin kashe murya tare da zuba mata narkakkun idanunsa shuru kawai nayi domin bana jin zan sauko lokaci ɗaya a bazata naji bakinshi cikin nawa da wani irin masifan na fara ƙoƙarin tureshi ina faɗin “Kawai kace min kazo kaji daɗi dani ne, kazo na Buɗe maka ƙafa bayan irin cin mutuncin da kamin akan wata karuwa..” haɗe bakinsu yayi tare da girgiza mata kai.
Wani irin lafiyayyen kissing ɗinta yake tare da shafo na shanunta laƙwas tayi tana jinshi domin gabaɗaya yayi nasaran kashe mata gaɓoɓin jikinta kifa kanshi yayi yana wasa ƙirjinta sosai tare da faɗa mata wasu irin kalamai masu wiyar ɗauka kuka ta saka tare da ƙanƙameshi tana faɗin “Me yasa ka kasa fahimtar irin soyayyar da nake maka Sir Nabil! mai yasa! Wallahi ina ƙaunar ka sosai, Yayana ina sonka soyayya mara iyaka amma ka kasa fahimtata duk wani kawaici da kunyata na ajiyesu gefe na fito fili na fayyace maka Sirrin zuciyata kaine muradina tun lokacin dana fara arba da kai, sai dai nayi ƙoƙarin nesanta kaina da kai ne saboda sanin matsayi da kuma son kare mutunci da martaban Aure na..” shafa fuskanta yayi yana faɗin “Na sani nasan kina sona nasan kuma kinyi haƙuri da halin ƙuncin rayuwa kinyi haƙuri akan komai lallai ke macece da kowa zaiso ki zamo mallakinsa Ina miki nikin ba nikin ƙaunar da kike min. Ina so kiyi Haƙuri kizo mu ƙarasa rayuwarmu kina da farinciki da jinin daɗi domin Ahalinki suna can suna tsumayin zuwanki Kowa nason sake ganinki kowa na murna dajin cewa ke ɗin ɗiyar Asma'ulhusnah ce ke ɗin fa Autar Ummanta ce shalelen Ummi Ƙanwar Nuwairah da Nabil matar Nabil farinciki a gidana..” (tsakani da Allah wanga soyayyar ta tsumani..)
rufe mishi baki tayi da nata daga haka suka lula duniyar ma'aurata can ƙololuwan sararin samaniya Cike shauƙin So da Ƙauna suke faranta ran junansu.
Bayan komai ya lafa ne ya kalleta tare da jan karan hancinta yana faɗin “Ki shirya sai mu wuce gidan ummi tare ko?” Ajiyan zuciya ta sauke tare da gyaɗa mishi kai, tare sukayi wanka sannan ya tayata shiryawa wanda gabaɗaya cikin shiririta aka gama shirin fita yayi yana jiranta a waje, shigowa Fadilah tayi tana kallon Jiddah ta fashe da dariya “Taɓ lallai har an kammala soyewan Allah yasa de ba'a ƙone ba..” da ɗankwalin hannunta ta jefi Fadilah tana dariya “Kinga bana son sa ido fa” Fadilah tace “Babu wanin nan munafuka ana so ana kaiwa kasuwa, sai a cigaba da haƙuri kisan lamarin rijalu sai ana haɗawa da batun haƙurin nan” rumgumeta Jiddah tayi tana faɗin “Na gode sosai Bestie sai kin shigo kenan” daga haka sukayi sallama gidan Ummi ya kawota sannan ya nufi hotel ɗin daya sauka domin yaƙi zama cikin gidan nan ummi ta shiga faɗa kaman zata ari baki domin ranta yayi matuƙar ɓaci, “Kiyi haƙuri Ummin mu tunda tana cikin ƙoshin lafiya ai Alhamdulilah koma dai menene ya wuce kema Jiddah baki kyauta ba domin kin ɗaga mana hankali sosai” cewan Hanisa “I'm so sorry nasan ban kyauta ba amma in sha Allahu hakan bazai sake faruwa ba ayi haƙuri Ummi na Please kiyi mun ɗan Murmushi mana haba uwata kin san de bani da tamkar ki a yanzun dan Allah kiyi Haƙuri kinji haba ummi Shalelen ki ce fa..” rumgumeta Ummi tayi tana jin hawaye na cika mata ido “I'm so happy too you Shalele naji daɗi ƙwarai kasancewar

Please Login or Register in order to submit comment