Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kallon shi sai dai in ummi na Gurin ne take sakewa Suyi magana in Kuma Bata Nan sai dai ya d'auki 'Danshi in ya gama kallonshi ya tashi ya tafi Ta samu arziki sosai a haihuwar domin ta ko'ina samu take costumes d'inta sun mata alheri da makota shima yayi rawan Gani sai da ta samu wata Biyar Ummi ta koma Bayan ta mata nasihohi sosai domin tafahimci Yadda suke Zaune ba me shiga harkan wani, a hankali take Renon Yaronta tare bashi kulawan daya dace Shekaran shi d'aya ya bar nono batare data yaye shi ba, bata fita tunda ta dawo,


A hankali take fuskanta yadda matan ubanshi suka tsane shi shiyasa bata barin shi ya fita sajida na shigo Mata jefi jefi, domin saita faki idon uwarta take zuwa, Ranan daya cika shekara biyu da wata Uku inna kichin inna girki na fara jin kukan shi domin na barshi kwance Yana barci D'aki na shigo Naga baya Nan da sauri na fita inna Kiran sunanshi “Aakif Aakif.." dakatawa nayi Ganin Zaina da bulala Yaron na ganin uwarshi da sauri yazo Yana makalewa bayanta “Yanzun me wannan yaron ya Miki da zaki mishi wannan dukan?" Ta fad'a hawaye na zubo Mata ganin i'rin dukan data mishi sai Ajiyan zuciya yake tsaki Zaina tayi sannan tace "ba duka ba wata rana saina kashe shi" tana fad'in Haka tabar Gurin jikina na rawa na d'auke shi inna kuka nayi d'akina dashi Wayata na d'auka tare da Kiran Abbanshi ba b'ata lokaci yazo,


Ya sameta Zaune ta tasa yaro gaba tana kuka Zama yayi tare da cewa "Meya Faru?" Tura mishi yaron nayi "Tsakani da Allah na gaji Yanzun wannan karamin Yaron ya chanchanchi Haka! Mena tsarewa Zaina meyasa ta tsaneni haka" tana kuka tana fad'a mishi yadda Zaina ta Zane mata yaro Gashi har yanzun yaki daina kuka, d'aukar shi yai ya kaishi d'akin Nafisa tana wanka ya zauna jiranta , k'aurin Girki yasani mikewa da sauri domin na ma manta da inna girki saukewa nayi, na kashe gas din sannan na biyoshi d'akin. Na samesu tana dubashi Magani ta rubuta mishi “Ki ringa lura da lafiyan d'anki" Gyad'a Mata Kai nayi, sannan na d'auke shi na fita.


inna Zaune shuru shuru bai dawo ba na Miki na dawo falo Bayan na Goya Aakif dake kuka inna jijjigashi kiranshi nayi a waya, Yana d'auka yace “Kinga banson damuwa gani zuwa" kafin tayi magana ya kashe wayar sai Tara ya shigo Mata da maganin zuwa lokaci yaron yayi barci , Karb'a tayi batare da tace mishi komai ba ta nufi d'akinta ajiye magungunan tayi tare da shimfid'e yaron ta kwanta biyota yayi Bata hanashi abinda yake so ba, Yana Gamawa ya mike Yana Jan tsaki, fita yayi i'tama taje tayi wanka halinshi sai shi,


Washe gari tana Zaune da safe Aakif na cinyarta har yanzun zazzab'i yaki barinsa Tana jin hayaniya na tashin cikin Gidan Amma taki Fitowa tana Zaune suka shigo shida Gimbiyar shi hotuna ya watsa mata “Shegiya karuwan banza" Zaina tace tana jifanta da Mugun kallo fiska k'unshe da murmushi kallon Hoton tayi taga i'tace da Sir Nabil, lokacin da suka fita da Ummi tayi tuntub'e ya tare ta sai d'ayar lokacin da suka fita da Yamma dashi maganarshi ne ya katseta “Nagode da abinda kika min Jiddah da Aurena kike cin amanata nagode kije nagaji Allah ya had'a kowa da rabonsa..." 'Dagowa nayi inna murmushi "Toh sai me inka sake ni? Ance maka zanji haushi ne ko Zan kurma ihu ne! Alhamdulillah Allah Nagode maka daka rabani da wannan Qangin Yah Allah sharrin Zina da ake bina dashi Ubangiji Allah ka yafe min Allah kasa su gane"


"Wake Miki sharri Bayan ga zahiri kece fa kwance jikin wani Kato da Aurena Amma kin cuce ni Allah ya i'sa!"


"Na sake ki saki uku ki fito ki barmin Gidana!"


Murmushi ta sake yi "insha Allahu Yanzun kuwa Mena tsinta a gidana banda bak'in ciki da masifu Allah Yana kallo zaluncin da kamin kaida matanka Allah baya barci seya saka min Wallahi bazan tab'a Yafewa Rayunkan 'Ya'yana biyu da nake jin K'aunarsu ba" Fita yayi a d'akin Takowa Zaina tayi Gabanta "Ya kika ga wasan? Nayi Cari up, abin wani sarkin Kuma gwara ki sake hawayen ki daina matsewa.."


Kallon sama da K'asa na mata “insha Allahu bazaki tab'a ganin Kukana ba, Duniyace Zainab ta i'shi kowa Riga da wando bare mu da muke cikinta Na barki da Allah na barki Kuma da fitowar Rana da fad'uwarsa Hakk'i na bazai tab'a barin ki ba" Kayanta ta had'a na sawa tare Dana Aakif dake Zaune Yana Kallon maman shi na kwashe kaya Tana Gamawa ta kashe duk wani kayan wutan d'akin tare da Goyashi, Fitowa tayi tana jan jaka zata fita ya kwance Goyan tare da karb'an Jakan kayanshi “d'a nawane bashi kika Zo ba, Zaki iya tafiya"


"Wannan ne Kuma baka i'sa ba Wallahi..! Ka bani d'ana" ta fad'a tare da Kai hannu zata karb'i yaron Mari ya kifa mata tare da Bawa Zaina yaron "Tashi ki barmin Gida 'Yar iska kawai.." janta yayi da jakar Kayanta har waje tare da Kullo kofar Falon wani i'rin kuka ta sake tare da buga kofar “Ka bani ‘DANA lbrahim..!" Kuka take sosai Ganin yaki bud'ewa yasa ta shiga motar ta a guje tabar Gidan ikon Allah ne kawai ya kaita Kaduna Da karfi take danna horn ba shiri me Gadi ya bud'e mata tun kafin ya gama bud'ewa ta danno hancin motarta da gudu ya matsa ko gama dai-daita tsayuwar motar batayi ba ta fito a guje tayi cikin Gidan, ummi na Zaune taga mutum ya fad'o tana shirin magana taga Jiddah ce “Ke Lafiyar ki kuwa?!" Zubewa tayi a kasa tare da Rik'e Ƙirjinta tana Jan numfashi da sauri Ummi tayi Kanta..




Maman Faruq
12/26/23, 9:03 AM - UMMI JB: ♡SIRRIN ƊAUKAKA..!♡*


Farin Jini Writer's Association


Page22.


"Dan Allah kice ya bani Yarona Wallahi bazan iya barin shi cikin wannan Gidan ba, Ummi Yarona.."
Gyatsa mai had'e da Aman jini tayi cikin tashin hankali ummi ta qwalawa Yahgana Kira da sauri ta fito "Maza temaka mu kaita asibiti" Girgiza kai Jiddah tayi cikin fitar Hayyaci tace. "Aakif Ummi dan girman Allah.." zubewa tayi jikin ummi Numfashinta na shirin barin gangan jikinta, da sauri suka fita da i'ta motarta dake bud'e suka sakata A guje ummi ta figi motar Suna i'sa Emergency aka shiga da i'ta, sai lokaci ummi ta fara niman waya, Dole sai gurin nurse ta ara ta kira wayar iyanmu tana d'auka tace "Sawdat ce lyata, Ga Jiddah tazo cikin mawiyacin Hali ki binciki Nafisat Meyafaru kar Yar mutane ta Mutu domin Aman jini take, Sunan 'Danta kawai take ambata Bansan Me Arab ya mata ba.."


"inna zuwa" kashewar tayi tare da Bawa Nurse sannan tayi Godiya.


Da kyar suka mata alluran barci domin surutai take musu tare da fisgewa tana son fita. "Kubarni ni lafiyata Lau, ku barni na d'auko Yarona!" Abinda take fad'a kenan idanunta na rufewa "wayyo Aakif d'ina bashi da lafiya Zane min yaro tayi Allah ya i'sa min wayyo Akif.." ruf idanunta ya Rufe tana sauke numfashi alamun alluran da suka mata yayi nasaran sata barci.


Likita na Fitowa ummi ta tare ta, ofishinta suka nufa tsaban tashin hankali ummi ta kasa zama duk da tace ta zauna. "Doctor bazan iya zama ba, fad'a min wani hali 'Yata take ciki? Meke faruwa da i'ta?" Rubutu likitan tayi sannan tace. "Ummin Halima zuciyarta ya kunbura sosai Jininta ya sake hawa fiye dana baya, tana b'oye Abu a zuciyarta dalilin dayasa yayi Haka kenan.." Hoton da'aka d'auki zuciyarta Doctor ta tura mata zubewa ummi tayi saman Kujera tana kallon yadda zuciyarta ya Kunbura "Allahuma ajirni fih musibati waa'akhlifni Khairan minhaa innalillahi wa'ilaihir rajioun! Yah Allah" Wani i'rin hawaye ne ya zubo mata "Dalilin tashin hankali yasa karamin cikin jikinta na wata biyu ya b'are.." runtsa ido Ummi tayi tare da fad'in "Hasbunallahu waa ni'imar wakeel"


Takardan da tayi Rubutu ta tura Mata.
"muna bukatar wa'yannan abubuwan Yanzun!" Mikewa ummi tayi ta fita da sauri Kuma ta dawo "Zuwa wani lokaci zata farka?"


"insha Allahu zuwa dare."


Gida Ummi ta koma tare da Yahgana wayarta ta d'auka ta kira Halimatu da Hanisa ta sanar musu Abubuwan da zata bukata ta d'auka tare da kud'i ta koma asibiti.


Washe gari
Sai biyun Rana alluran ya saketa mikewa tayi a zabure da karfe take son sauka daga Gadon Ummi dake sallah ba shiri ta yanke sallar tare da Rik'eta Yadda ta mike ne yasa jinin zubowa sosai Girgiza kai tayi tana cije leb'e jin yadda Maranta ke ƙullewa Halimatu ce ta shigo da kulan abinci Ganin Halin da jidda ke cikine yasa ta ajire Kulan da sauri ta karasa Hanisa dake Bayanta ne ta juya domin Kiran likita.


"Dan Allah ki nutsu Jiddah." Ummi tace tana sake riketa sosai Girgiza mata kai tayi "Taya zan nutsu Yarona na cikin mawiyacin Hali? Ki fad'a min Ummi taya zan samu kwanciyar Hankali yarona na gurin matar da tayi ikirarin saita kashe shi! wayasan me ta masa Yanzun, yaron da magana ma bai iya ba, Wallahi gwara da cikin Ya fita, wannan ai masifa ce Wallahi ki fad'awa lbrahim ya bani Yarona in ba Haka ba, Kotuce zata rabumu, Ya dawo min da Yarona, Har mari na yayi dan zan d'auki Aakif. ki kalli yadda ya shimfid'amin hannunshi jikina, Wallahi Bazan bar musu d'ana ba ki fad'a mishi Ya bani Yarona kafin Hukuma ta shigo ciki.." magana take tana jijjiga kai tare da cije baki tana son ƙwacewa.


"Naji kiyi shuru Zai baki d'anki Meya had'aku?"


"Saki uku yamin"


Zaman dirshan ummi tayi a K'asa "innalillahi saki d'add'ai har uku?" Hannu Halimatu ta d'ora akai tare da buga salati Hanisa dake baya tace. "Amma Uncle yayi asara!"


Halimatu tace. "Babbama kuwa" daƙuwa ummi ta musu "Zanci Gidanku" shuru sukayi Ganin doctor ta shigo dubata tayi sannan tace "Ki daina motsi me karfi jikin ki, ba ƙwari fa"


Kallon baki San mai nakeji bane Jiddah ta mata sannan ta d'auke k'anta "Zansha ruwa" nace inna sakin numfashi me d'auke da Hawaye ni kad'ai nasan Abinda nake ji, a zuciyata Doctor tace. "Ruwan d'umi zaku bata" Hanisa ta d'iba a cofin fulask ta bani, Karb'a nayi nasha kad'an Ajiye nayi sannan na sauka a hankali na nufi Band'aki.


Sai Yamma Nafisa ta dawo Gidan nan ta Ga Aakif shi d'aya a falo hawaye ya bushe mishi a fiska "a a Aakif mamma fa" kuka yaro yasa daga Zaune Yana Mika mata hannu domin Yunwa ta cishi sosai babu wadda ya bashi abinci d'aukar shi tayi zata nufi d'akin Jiddah taga fitowar Sa'irah Kofar ta gani Kulle cikin mamaki tace "Ke inna Maman Aakif?" Nan yarinyar ta fad'a mata yadda Akayi i'do ta zaro tana kallon Yarinyar kafin tayi magana wayarta yayi Kara, "Iyah" tace sannan ta d'auki Kiran "Assalamu alaikum Nafisa" cikin Girmama Nafisa ta amsa Mata Iyanmu tace. "Meke faruwa Ummi ta kirani wai Hauwa'u ta nufi Kaduna!" Cikin sanyi jiki Nafisa ta sanar mata komai salati Iyanmu tayi sannan tace. "Yayi kyau zai Gamu dani i'ta Kuma Zainab zata ga karshenta Sakamakon Yanzun tun anan Duniya Allah ke nunawa insha Allahu sai rabbi ya saka mata."


'Dakinta ta nufa da yaron shayi ta had'a mishi me Kauri ta d'aurashi saman cinyata kafin ta bashi ya fara Kokarin Karb'a, tana sanya mishi Kofi a baki da sauri Ya Karb'a Yana Sha yana sauke Ajiyan zuciya, wani i'rin kuka tasa ganin yadda yaron yake karb'an tia din a Yinwace. "Allah saiya saka maka" wani i'rin kuka ta fashe dashi kallon yadda yaron yake rik'e da Kofin tayi "Wannan wani i'rin son zuciyane yaro karamin za'a rabashi da uwarshi!" Aakif na gama sha ya sake kofin tare da qwala ihu Yana Kiran "Mamma.." mikewa tayi dashi tana jijjigashi Jumana ce ta shigo "Momy lafiya naganki da Aakif Aunti Amariya fa kofarta ƙulle?" Kallon yarinyar tayi sannan tace. "Kisa ruwan zafi ki masa wanka" ajiyeshi tayi domin ya fara barci ta nufi Band'aki tayi wanka.


Zaina ce ta fito bataga Yaron ba rik'e Qugu tayi tare da K'unduma ashar. "wani d'an shege da shegiyace ya d'aga yaro anan? Akan mutum yake da za'a d'auka?"


Nafisa ce ta fito daga d'akinta hannuwanta hard'e a baya, ta rik'e igiyan caji. "Nina d'aukeshi ko zaki dakeni ne, kaman yadda kika sa ya daki Yar mutane.." Hannun Zaina ta d'aga da niyar marinta da sauri Nafisat ta rik'e Hannun. "Ki nada tsaurin i'do ga shegen saurin Hannun Yanzun ke ki kalli tsaban idona Kice zaki mareni? Sa'arkice ni Zainaba?.." Zaina tace. "Ked'in Banza ked'in wofi wacece ke da baran dake ki, ba..." Kafa tasa mata ta fad'i K'asa "Kina cikamin ciki Zainaba Yau zanci ubanki harda uwarki zanga uban da ya d'aure miki tsuliya kike zuba mulk'an Gidana dan inna Miki shuru inna K'yale ki.." zuba mata wayar ta shigayi sosai Zaina ke ihu tana Kare K'anta, Mikewa tayi da sauri tana rik'e zaninta Fure dake tsaye tasa dariya. "Yar Banza Wallahi Nafisa baki burgeni ba, dakin fasa jikin shegiya.."


Zaburowa tayi tare da Rik'e wiyar rigan Fure "Ni ni kike fad'awa haka zaki gani zan miki abinda harki bar duniya bazaki manta ba, na barki na Yau!" Tureta tayi ta fad'i kallon Nafisat tayi. "Kin burge tunda har kika iya dukana Amma zakiga ladar dukan domin zan miki Babban Kyauta..." Wani i'rin dariya tasa harda hawaye tana mata kallon Tsana "Kaman yadda kika Zane jikina sena addabi rayuwarki, kaman yadda kika sani kuka, saina saki, zan Kashe ki da ranki, zan miki abinda kina jin kukan Amma zaki kasa Yinsa! Nice fa! Zainabu-Abu HahhhHahhh!!" Ta karasa maganar tana dariya kaman zautacciya.


"Bakince ke shed'aniya ba, insha Allahu babu abinda zan gani Wallahi Kaman yadda kike tak'ama da shed'an, Haka nake tak'ama da Allah Yanzun aka fara!" Kad'a kai Zaina tayi tare da shigewa d'akinta.


Yana dawowa ya shigo d'akinta. Yana kallonta ta saka kwalli a idanunta "Muazzan ni Nafisa ta duka dan nace ta bani Aakif harda zagin iyayena ni ta Zane har tana ikirarin saita Kashe ni akan ka saki Hauwa'u-Jiddah, Taci min mutumci ni Wallahi ka sake ta, daman nace zan Bata ladar abinda tamin ko ka, saketa Kona bar maka Gidanka..." Jikina rawa yace. "Dan Allah Zaina kiyi hakuri wallahi zanyi yadda kike so" takarda ta wurga mishi "Zana mata d'aya Kuma ka karb'o Aakif ka kawo min!" Dauka yayi da sauri zama tayi tana murmushi Yana Gamawa ta Sashi gaba, Zaune tayi akan Kujeran falo shi Kuma Yana K'asa Fure ya fara Kira, a waya sannan ya Kira Nafisat.


Suna karasowa ya Mika mata takarda "Meye wannan?" Cikin masifa yace "ki Karb'a in kin bud'e Kya gani! Sannan Aakif ba d'anki bane da zaki d'ukesa nasan dake na zab'eta dan haka ki ajiye min d'ana!!" Ya kasara maganas kicin tsawa.


Murmushi Nafisat tayi. "Qwarai ba d'ana bane, naka ne Amma ka sani Allah yana sane Yana ji Yana Kuma Gani, Zakaga sakamako"


Bud'e takardan tayi a razane ta kalleshi tare da kallon Zaina.


"Kyautace! Na baki sannu a hankali zan baki ladar dukana da kikayi Ba'a tab'a ni a tashi Babu kyauta me tsoka, Na, baki wannan".


Mikewa Nafisat tayi tare da sauke yaron kasa jiki. "inkin manta zan tuna Miki Ayi a Kare yafi abari gobe a karasa". a sanyaye ta nufi d'akinta Fure ma jikinta yayi bala'in sanyi "Kinsa ya sake ni ko? insha Allahu zai mike fiye da abinda kika min namiji ne fa? Ance miki namiji D'an Amana ne wallahi ko kad'an ba'a bawa namiji Amana , ba'a d'aukan yarda abawa namiji , Namiji bad'an goyo da zani bane, insha Allahu Zaina Zaki ga sakamako karki manta aci a sha a rage don gobe, Amma Kuma aci yau aci Gobe , shine Ci! Gida kuwa inna Zaune daram domin zuwa kikayi kika same ni" shigewa tayi d'akinta


Kallon Banza ta watsawa Fure "Malama tashi ki bar Nan!"


"Abinda Dama ta jure, hagu. Bazata Jure ba, ko Nima sawa zakiyi ya sake ni?"


Girgiza kai Zaina tayi. "Ai abun fad'a namai Baki ne." Tace tana murmushi


Kallon shi Fure tayi, "Kayi shuru ai baka ga komai ba, bade ka zauna Gindin Zaina ba, se kayi kuka Mara iyaka shashasha kawai.."


d'akinta ta shige mikewa Zaina tayi zata shiga d'akinta yace. "Kinbar yaron Kuma?"


"Kai a banzar tunaninka zan rik'e d'an kishiya ne, Allah sauwake, ai ya Zama na tsakar Gida, Kuma Wallahi naji ka d'auki yaron Nan ka kai, mata saika gamu dani" ta karasa maganar da jan,tsaki sannan ta shige abinda.


Kallon Yaron da ya zauna shuru yayi wadda da tukan alamu ya fara maraicin uwarsa "Aakif" yace Yana mikawa Yaron hannun "Affa.." yaron yace Yana Mika mishi hannu d'aukar shi yayi tare da Rumgumeshi hawayen da baisan na menene ba ya sauko mishi. d'akin sa ya nufa da yaron,


Kwana na Goma aka sallamoni Gida. Koda muka dawo kurma nazame musu bana magana damuwa tamin yawa Yarona nake son gani kusa dani inna kewar d'ana sosai Yau da abin ya isheni Fitowa nayi na tsaya mata bakin Kofa. "Wallahi kewa K'anin ki ya dawo min da d'ana.. Ummi" Murmushi tayi sannan tace "Yi hakuri shalele" kuka na saka mata tare da zama a kasa Hanisa dake Zaune tace. "lah ji shashasha Yanzun kuka kike Ai wiya Bata kisa, Babu abinda zai samu d'anki Kinga Anwar na Miki dariya Zamu lalub'o Sir Nabil, yayi Wuf dake Kinga saiya Baki wasu 'Ya'yan ba d'aya ba Biyu ba.."


Hannu bibbiyu na auna mata zagi. "Ba uwar da zanyi dashi ki barni Kinga tashi ki bar Gidan Nan Wallahi kafin na b'ata ranki!" Na fad'a inna niman abinda zan bigeta dashi kallon Hanisa ummi tayi sannan tace. "Tashi! ki tashi Nagode tunda kinzo ki b'ata mata rai ne, a dai-dai wannan lokacin da take cikin damuwa Bai kamata kizo da wannan batun ba" Cikin sanyi jiki Hanisa tace. "Kiyi Hakuri in-law" Cikin zafin maganganunta Jiddah tace. "Bakisan zafin da nake ji, bane Shiyasa kika Fad'i Haka Amma ba komai, ki tafi kawai banson Ganinki" fita Hanisa tayi.


"Kiyi hakuri na kirashi Yana zuwa" da sauri nace. "D'ana nake bukatar gani ba shi ba uwar me zan mishi"


Murmushi ummi tayi domin tana mata uziri sosai tunda abin nan ya faru ta zama mai zafi Rai, bata da hakuri kana fad'a mata zata baka amsa , can tace. "Ummina dan Allah kiyi hakuri inna miki rashin Kunya, ba laifi na bane, na kasa Jurewane. na kasa Yin hakuri, ni nasan rad'ad'in da nake ji na rashin Aakif"


Sati biyu tsakani ummi na Zaune falo.
Sallama yayi tare da shigowa Kujeran dake fuskantar ta ya zauna. "inna yaron?" Ummi tace mishi " 'Da nawane inna da iko dashi na Riga na sallameta tayi rayuwarta Nima nayi tawa rayuwar, bazai Yuwu na barmata d'ana ta b'ata min tarbiyanshi ba Kamilar mace ake barwa Yara ba watsattsiya ba.."


Dai-dai fitowarta. Nuna kanta tayi tana dariya tare da Zama "Me acikin ido banda tarin ruwa, ka sake ni shine zai hanani rayuwa, Ance maka sonka nake dazai dameni! So uku kana jifana da K'azamar kalma nice Karuwa mazinaciya Ko? Yau Kuma kace min watsattsiya! Bazan maka Gorin abinda na maka a baya ba, Amma kaje nabarka da fitowar rana da fad'uwarsa insha Allahu Kalman da kake jifana dashi zai tsaya a kanka.." mikewa tayi tana hawaye tabar Gurin


Kuka ummi ta fashe dashi tana kallonshi "A gabana kake wannan maganar zarginta kake daman Arab yaushe ka zama Haka! Yaushe ka zama Mara adalci da son zuciya Naji Nagode tashi ka tafi...!"


Azuciye ya mike "Akan yar iska kike Korata shi kenan na tafi.."


Fita yayi mikewa Ummi tayi da sauri ta nufin d'akin da Jiddah take tab'a kofar tayi taji a kulle. "Zoki bud'e min Kofa" murya cike da kuka tace "Me zan miki Ummi kina ji ai Kinji abinda ya fad'a, Yace bazai bani Yarona ba, kin kasa yin komai, ya rabani da d'ana ya baiwa Muguwar matar Sa ba matsala yaje Allah na Nan"


"Ki bud'e min Kofa Hauwa!" K'ememe taki bud'e Mata kofar Haka har ummi ta gaji ta koma falon ta zauna.


Wayarta ta d'auka tare da Kiran Nafisat tana d'auka tasa mata kuka. "Lafiya?" Nafisat tace mata


"Maman Jamil wani nauyi zan d'aura miki Ga amanar Aakif dan girman Allah banida wadda zai masa Kyakkyawan rik'o sai ke, Ki kula min da Yaro na dan Allah" kashe wayar tayi tare da fashewa da sabon kuka. "Allah kana gani Allah in wani laifi na maka wadda kake Hukuntani Ubangiji na tuba, Allah ka yafe min.."


Maman Faruq
12/26/23, 9:03 AM - UMMI JB: ♡SIRRIN ƊAUKAKA..!♡*


Farin Jini Writer's Association


Page23.



Haka ta wuni a d'aki tana kuka ko lek'owa waje batayi ba, rayuwar daki tacigaba dayi, Bata jin dad'in komai ko abinci ummi ta kawo mata sai tayi da gaske take cin kad'an , kukan d'anta take yawanji yana cika kunnuwanta Ga zaurawa ta ko'ina zuwa sukeyi , bata san ya'akayi jama'a suka san bazaurace i'ta ba, Yau da abin ya i'sheta ne ta fito d'akin ummi ta shiga tana sallan walaha , zama tayi kusa da i'ta tana sallamewa ta kwanta jikinta tare da sakin kuka, addu'a ummi tayi ta tofa a ruwa d'agota tayi tare da Sanya kofin a bakinta Bisimillah tayi tare Da shanyen ruwan tana sauke ajiyan numfashi. “Ummi.." kasa karasawa tayi sakamakon hawayen dake zariya saman fiskanta share mata fuska ummi tayi “Allah ya sanya Dangana a zuciyarki Ubangiji ya sassauta wannan zafin ran da kike fama dashi kiyi hakuri kiyi hakuri, ki fauwala Allah lamuranki ki cire damuwar Aakif wiya bata kisa..." Hannuwan ummi ta rik'e


“Wallahi bazan i'ya ba, 'Dana na cikin wani hali Yana bukatar kulawata Dan Allah ki rok'eshi ummi ya bani Yarona! 'Dan uwanki ne ,Bakiji yadda kunnuwa suke jiyo kukansa ba, Kullun mafarki nake dashi yana kuka Yana mik'omin hannu ummi.."


“A Gabanki so nawa inna kiransa ba ya d'aukan kirana so nawa inna tura masa saƙo baya bani amsa laifi na kike ganin ko? Zakice nafiya son Kaina da ƙanina ko Hauwa'u?.." zataci gaba da magana Jiddah tace. “Kiyi hakuri ummi" daga Haka ta mike ta fita, d'akinta ta koma.


Bayan sati biyu.


Fitowarta kenan daga wanka taji yaro yayi Sallama Himar ta saka tare da Fitowa “wa kake Nima?" Yaron yace. “wai ana Sallama da Jiddah.."


"Koma kace bata Nan" har zai fita ummi dake Fitowa tace “Je kace tana zuwa"


"Amma ummi.." katseta tayi “Kimanin wata takwas kenan duk wadda yazo sai ki Kore shi me yayi zafi Jiddah?" Sunkuyar da kai tayi K'asa .


“Babu Aure cikin tsarina a Yanzun d'ana kawai nake bukata, ummi duk wadda ya aureni Yanzun gangan jikina ya Aura zuciyata da tunani na yana ga Yarona, ki barni ummi bana bukatar wani Namiji cikin Rayuwata!" Ummi tace. “Laifi wani baya shafan wani shalele Nah, in har na i'sa jeki shirya ki fito.." ‘Daki ta koma tare da saka doguwar rigan atamfa shigowa ummi tayi tare da kallonta sama da K'asa “wani i'rin shigace wannan? Haka zaki fita Baki shafa mai bare Hoda, Yanzun wannan katon Himar d'in zaki saka? Haba Jiddah ban hanaki suturta Jikinki ba, amma ki cire wannan Himar d'in ki saka mayafi yaushen rabon da kiyi kwalliya ya kamata ki sanyawa zuciyar ki nutsuwa"


“kwalliyar me Ummi? A Yanzun ban bukatar wani Namiji yaga kyawuna bare har na rud'ashi, zamana a Haka yafi min wallahi in har kika ce na sake shiga na fasa fitan!" Murmushi ummi tayi “Allah ya sauke wannan shed'anin dake kanki"
"Ameen" tace sannan ta fita.


Batayi Sallama ba ta bud'e gaban motar da yake “Kaine wadda ke niman iso dani ko ? da alama an fara bud'e babinka na Karshe To bara na fad'a maka ban shirya Aure ba, Bak'in aljani gareni abinda yasa Mijina ya sake ni kenan Wallahi kana Aurena Zaka mutu in kashirya ma yaranka su zama marayu to.." da sauri Mutumin yace “a a Wallahi" murmushin jin dad'i tayi sannan tace “Shi kenan zaka i'ya tafiya"


Tana tsaye Gurin ya tada motarshi sai da taga fitarshi sannan ta shigo Gida, Haka ta ringa Koran duk wadda yazo Gurinta da Sunan Baƙin Aljani gareta. Wasa wasa aka shafe shekara da watanni Abin na Bata mamaki ganin yadda take Wahal dasu Amma har yanzun Banzaye wawaiyu basa ganewa Matsorata ne, ta kanyi dariya in ta tuna yadda suke rikicewa da zaran tace Bak'in Aljani gareta. i'do

Please Login or Register in order to submit comment