Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daki kunnuwana Halimatu ne suka amsa masa domin lokaci d'aya na nimi nutsuwata na rasa "Barka da warhaka Sir" Hanisa tace mishi tana satar Kallon Jiddah "Barka kun daga l'na kuke da Yammacin Nan?" Hanisa tace "munje Dubiyar 'yar islamiyar mu" yace. "shigo na karasa daku" da sauri nace. "Mungode Mallam" Hannun Hanisa na rik'e sosai taku d'aya nayi yace "Haba de ku dai shigo na sauke ku" Hanisa tayi kasa da murya "Mu shiga in-law" hararanta nayi , motar ta nufa Su Sahiba tuni aka shige Hanisa na shiga ya kulle kofarsu zan bud'e naga ya turo kofar d'ayan b'angaren Tsaki naja, a hankali nayi bisimillah na shiga juyar da kaina nayi waje ,


Tafiyar kurame mukeyi chan ya jefomin tambaya. "wani layi muka nufa?" Ban Juyoba bare na bashi amsa kad'a kai yayi tare da cewa. "Halimatu lna muka nufa?" Nan ta fad'a mishi bayan mun karaso suka fita inna shirin fita ya kulle motar , gefenshi ya bud'e yacewa Hanisa "Aron Yar uwarki zaki bani dan Allah" Sunkuyar da kanta tayi domin wani i'rin nauyinsa takeji da girmansa ya rok'eta "Amma Sir karta dad'e domin Ummi bata bamu wannan damar ba"


"insha Allahu nagode" Suna barin gurin ya shigo motar meda glass din yayi sama "Baki iya gaisuwa bane ko a gidanku babu manya ne" ya fad'i Haka Yana me juyowa Gareta wani i'rin kunya ne ya rufeta. A gajarce tace "ban i'ya ba" Murmushi me sauti yai "Jiddatuh" ban tab'a jin Mutumin da ya iya Kiran sunana kaman Sir Nabil ba. Wani i'rin juyowa nayi a Hankali nan idanunmu ya sarke cikin na juna narkeken kallo yake binta dashi yana sakar mata Murmushi Sunkuyar da kai tayi kasa "Bazan iya abinda kake so ba dan Allah ka fita rayuwata da zaran na kalli mutum nake gane manufar shigowarshi rayuwata na rok'eka ka barni ka zauna da matar Haka!" Na karasa maganar inna sakin kuk'an da bansan dalilinsa ba "Kiyi hakuri da abinda ta Miki"


"Ban rik'e abinda tamin ba ko nice zanyi fiyye da hak'an"


Bud'e motar nayi zan fita. "Ki tsaya ki saurareni"


"Banida lokacin shirmenka Sir Nabil Dan Allah ka kyaleni , kamar yadda nace maka!" Na fad'i Haka tare da had'a hannuwana biyu alamar rok'o ,


Hannunta ya kama kamar wacce aka watsa ma Wuta Haka taji tana shirin kwacewa ya manna hannunta da Saitin Zuciyarshi dake bugawa. "Tun randa kaddara ta had'amu Allah ya d'oramin jarabtan abinda bata Sona hasalima kallon tsana da kiyayya nake hangowa tsagwaron daga cikin kwayar idanunta, ki bani dama Jiddah Bazan samu sukuni ba har se kin amince da..." Janye hannuna nayi Zan tashi ya jawoni da karfi tare da rugumarta Ajiyan zuciya ya sauke "Ka fito fili kawai kace inna bukatar jikin ki, in kace min Haka zanfi fahimtar ka" Cikin Gida na shige na barshi da rik'e hab'a domin be tab'a tunanin zata mishi wannan fassaran ba,


Koda suka shiga cikin Gida, Sega Kiran Ummi dafe qirji Hanisa tayi "Nashiga uku ummi.." da sauri Halimatu ta karb'i wayar "Da fatan kuna cikin k'oshin lafiya?" Abinda Ummi tace kenan Tana sauke Ajiyan zuciya Halima tace. "Alhamdulillah ummi ya jikin iyanmu?" Ummi tace "Alhamdulillah lna Jiddah da Hanisa suke?"
Mikawa Hanisa wayar Halima tayi "Ummina Barka da warhaka yame jiki" Ummi tace "Lafiya Lau lna Jiddah" jin tayi kafin tace. "Ta zaga.."
"Dai-dai wannan lokacin Hauwa bata shiga band'aki zuciyata babu dad'i meke faruwa daku ne?"
Shigowa Jiddah tayi tana cire Himar d'inta tsaban dad'i har da lumshe ido Hanisa tayi, "muna lafiya Ummi ga Jiddah" Mika Mata wayar tayi narke mata nayi "Ummina kina lafiya?"


"Lafiya lau shalele Nah da fatan Kuma haka domin zuciyata babu dad'i kaman an bud'e wani shafi na rayuwar d'ayarku" kasancewar duk sunajin maganar yasa suka ware i'do "Babu komai ummi".


Ummi tace. "Allah ya jishemu Alkhairi ku kula sosai insha Allahu na kusa dawowa" daga Haka sukayi Sallama bayan ta musu addu'a.


Hanisa tace "Wallahi ganin Kiran Ummi seda zuciyata ya buga"


Halimatu tace "Wallahi kuwa"


Zaune nayi tare da rafka tagumi "Me ya ce Miki?" Murmushin takaici nayi "abinda kuke zato ne"


"Toh ke Kuma kin amince masa?" Girgiza Kai nayi Halima tace "me yasa?"


Qura musu ido nayi jin yanda suka maida hankalinsu kan maganar yasa ni Jan tsaki "Kun manta kashedin Ummi garemu? Yanzun har wani murna kuke da bukatar Sir Nabil?"


Tsaki halima tayi. "Kefa banzace Dan maganar Ummi ze hanaki kula zab'in ranki wallahi bari kuji, da zaran na samu muradi na babu ruwana da wani karatu Na kai, matsayin da Zan tsayar da gwani i'ta Ummi banda samarin Banza take nufi, bawai kar mu kula kowa ba".


"Amma sahiba kin shayar dani mamaki se yanzun na kara tabbatar da sauran Hankalinki, Bari kiji ko banda maganar Ummi Sir Nabil baya cikin tsarin Mazan da nake so"


Hanisa da tunda aka fara maganar bata ce komai ba, se yanzun "Amma Sir Nabil bashi da wani nakasu Wallahi kunyi bala'in dacewa yan kwanakin da yayi cikin makarantar bakiga yanda ake bibiyarshi ba, Amma bawa kulawa hasalima abinda ya kawoshi yake..."


"in-law ban katseki ba, Amma kina tabbacin haka, ba'a shedar Namiji domin Wallahi ze kunyatar dake"


Girgiza Kai tayi. "inna kyautata mishi zato in-law ki amshi tayin sa"


"Toh Allah ya taromun ku, na lura Aure kuke bukata yanzun, Amma ni kan, bawai ban bukatar hak'an bane, koda l'na ra'ayi banda Sir Nabil , Domin be cika sharud'an da zanyi tarayya dashi ba"


Kama hab'a Halimatu tayi. "Toh sahiba fad'amin ya kike so Mijin Auren ki ya kasance?" Mikewa nayi domin magariba ya gabato "Yanzun lokacin ganawa da ubangiji ne" D'aki muka nufa Hanisa ce ta fara shiga band'aki kasa kasa Halima ta fara magana. "Meyasa sahiba? ya chanchanci hak'an ya k'ask'antar da kanshi" kallon kofar band'akin nayi "Halima bai da nagartan haka!"


"Kin amshi bukatarshi ne da zaki fahimci hak'an? Haba sahiba ki daina yanke hukunci da Sauri haka.." tsit tayi sakamako fitowar da Hanisa tayi,


Shiga nayi na watsa ruwa tare da alwala in na Fitowa Halima ta shiga sallah na tayar,


Washe gari.
Tunda mukayi sallar subayi bamu zauna ba, muka hau Gyare gyaren Gida, inna shirya Mana abinci Nace. "sahiba jekiyi wanka zamu ci gaba da in-law, in kika fito se d'ayar mu ta shiga"


Tafiya tayi, tana barin Gurin nace. "Hanisa inna jinki" murmushi tayi,


"Hmm 'Yar uwarshi ce zata iya yi komai a kanshi"


"Bata isa ba!.." nace Mata inna fiskantar ta, "karki zage da yawa"


Nace. "Ba zancen zagewa Gaskiya ce Domin bata isa ta Hana abinda ubangiji ya nufa ba"


Hanisa tace. "Zaki sha wiya zefi kyau ki kama wani ki bar mata shi"


"Banjin sonshi Amma Zan i'ya hakurin zaman , kodan na nuna mata iya matsayinta zanyi amfani da karfin son, na daki zuciyarta"


Wani i'rin murmushi Hanisa tayi. "Nuwairah ta wuce tsammaninki , domin tasan yanda zata Tafiyar da komai musammam akan abinda take ma Haukar SO! Kawai ki kyale"


Shuru nayi kaman bazanyi magana ba Chan nace, "Wallahi bazan Kyale ba"


Juyawa tayi zata fita na jawo ta da sauri shammatarta nayi na zare karamin Bluetooth d'in dake kunninta "Basirar ki da jajir ce warki Suna birgeni ki sake taku sannan ki d'ora d'amara yanzun aka fara"


Murmushin takaici nayi "Wallahi bazaku tab'a samun abinda kuke so a kaina ba"


fita tayi ta barni da sauran aikin a gurguje na karasa aikin nima naje nayi wanka muna Fitowa muka nufi makaranta ban shiga harkan kowa ba, har aka tashi inna lura da yanda yake bina da kallo kaman maye Zama mukayi nida Hanisa muna jiran Halimatu tana Fitowa muka nufi bakin titi don tare abin hawa motarshi ne ya tsaya gabanmu. "Ku Shigo na sauke ku" kallon juna mukayi nida Hanisa "ai shidin kaman jela nane duk inda nayi seya bini" nace mata tare da bud'e Gidan baya na shiga, Suma suka shigo "au wato na zama drive d'inku" kunshe dariyata nayi Hanisa tace "Yi hakuri Sir" Jan motar yayi har muka karaso Gabdy muka fita "ah jimana 'Yan mata"


Dawowa nayi suka nufi cikin Gida. "Sir Nabil inna ganin mutumcinka nace baka ka Kyale ni se kace Dole? Haba!"


Sosa kanshi yayi da makullinshi "Kiyi hakuri dole ce Domin zuciyata taki ta barki, Duk bugun numfashi na K'aunarki dad'e karuwa take Jiddatuh ki bani d'an dama"


Tafiyata nayi na barshi cikin sati uku ya mayar da gidanmu Gurin zuwa gashi be iya zuwa haka ba,seya tawo Mana da tsaraba nide ban d'aukar komai haka Halima zasu raba da Hanisa Alhamdulillah na amshi kwangilar girkin, kuma na kammala komai da temakon su Hanisa Wanda bak'in ciki kamar ya kashe ta Amma bata Bari sun fahimci hak'an ba, na samu Alkhairi sosai , Na sanar da Ummi Kuma ta tayani murna.


Cikin k'ankanin lokaci Hanisa ta fara jawo min jama'a domin i'ta ke amfani da waya, nan ta ringa Post abincin gargajiya har da na, nasara kala kala, mutane da yawa sunce Suna so,


Nabil ya takurawa rayuwata ya hanani sakat tun ban kulashi har de na fara sake mishi duk da bana jinshi lna jin Zan iya maneji ,


Wani ranar Asabar ranar dana tabbar da gaske Nabil Kaunata yake Amma ni har yau ko kad'an ban jinshi a Raina,


Da yamma yace na Shirya Yana zuwa ta wayar Hanisa ya Kira domin naki karb'an waya ba so D'aya ba ba, so biyu ba, yasha bani waya naki Karb'a inna tsoron Allah inna tsoron Ummi.


Ban tab'a Sanya gyale ba tunda nake duk shigar da zanyi Babban Himar nake sakawa Kuma ban tab'a fente fiskata da Sunan kwalliya ba, kyau dede gwargwado Rabbi ya bani inna da suran d'aukan hankalin shiyasa nake suturta jikina,
Waje na fito na sameshi Yana jin gine da motarshi, Ban mishi magana ba, Haka shima be mun ba inna shiga motar shima ya shiga fita yayi ranar munyi yawo gurin shakatawa har magariba ta gabato ..


Karshe wani kayataccen Gurin hutawa muka yada zango duk yawon da mukayi ba kalmar data shiga tsakaninmu sede in ya kalleni ya sakar mu murmushi , nima Haka nake mayar masa da martani tunda muka shigo gurin nake jin bugun zuciyata na karuwa ganin duhun magariba ya fara hankalina duk ya karkata Gida, duk da inna fashin sallah hak'an be sa najini a takure ba, gurin da ba hayaniya jama'a muka nufa, tsarin gurin yamin yanda d'add'eku jama'ar gurin suke sha'anin gabansu "Jiddatu Nah me kike bukata" tab'e baki nayi "Ruwa ma ya wadatar" Mikewa yayi minti kad'an se gashi da Ruwa me sanyi da cofuna..


Zuba Mana Ruwa yayi jin Abu nabin kafata ne yasa na mike da sauri cikin razana har bansan lokacin dana ture ruwan daya ganin d'an tsaka nabin kafa ta, "Yah Allahu" da sauri ya mike "Lafiya?" D'if haske gurin ya d'auke buga kafata nake a kasa , lalub'en inda nake yake har ya kamoni "ki nutsu" Kuka ta saka mishi rumgume ta yayi sosai Yana jin yanda kuk'anta yake tab'a zuciyarshi a hankali kananun haske ki tashi naga Haka so biyu Amma ban d'auki hak'an da wata manufa ba,


Lokaci d'aya haske ya gauraye gurin barin jikinshi nayi tare da zama ganin tsakan baya Nan,


Kallonta yayi "Jiddah Zan tafi chadi zanyi sati biyu Dan Allah ki kularmin da kanki zanje ma abba na da maganar ki"


"Allah ya tsare" abinda nace mishi kenan inna mikewa


Shima mikewa yayi na lura Yana so muyi magana naki bashi damar Haka, Haka har muka dawo Gida bakar leda ya Mika min lokacin da nake shirin fita,
"Kiyi min wannan alfarman Baki tab'a karb'an kyauta na ba, dan Allah ki karb'i wannan koda bazakiyi amfani dashi ba"


Ya fad'i Haka Yana me kama hannunta a hankali ya fara murzasu ji yake kaman karya tafi, ya barta kasa hakuri yayi ya matso jikinta Girgiza mishi kai tayi tana kokarin danne hawayenta kwantar da kanshi yayi saman wiyarta "Kina Raina ki daure ki furta min kalma me dad'i Hauwa'u Jiddah" kwantar da kanta tayi jikin motar a hankali take d'auke qwallanta, ta kasa mishi magana Haka suka rabu,




Watan Ummi uku da kwana goma wanda yayi dai-dai da kammalawar namu karatun domin Hanisa kan, ta rigamu zatayi bautar kasarta Nan kaduna , mune de bamu San l'na za'a cillamu ba,


Munyi murna kaman me domin dirar Bazata ta mana i'ta da Arab wanda rabon da in ganshi na manta Nan muka shiga hidima dasu Sallar a zahar ne ya d'aga mu,


"Ummin Halimatu.." yace tare da Sunkuyar da kanshi kasa ,


Ajiye takardan dake hannunta tayi tana duba tsarin Girke girken Jiddah "ka kirani Kuma kayi shuru?"


"Daman nace dan Allah na shirya zama da matata Dan har yanzun matsayinta na Nan ban saketa ba,.."


Wani i'rin murmushi tayi "Alhamdulillah ranar da nake jira yau gashi tazo Muazzan Ko ka manta abinda kace ne?"


"Wallahi Sawdat har yanzun Jiddah matatace"


"Karka mayar dani jahila man ta lna Aure shekara nawa ba abinda ya shiga tsakaninku zakace matar ka, ka fara Hauka ne!"


"Wallahi Allah matatace.."


Marerece mata yayi sosai da kyar ya shawo kanta bayan tace zai bata kudi, na siyayyar da zatayi ,


Da yamma Nabil yazo Ummi na d'akinta na fita, tun kafin in karaso nake jefa mishi murmushi Ashe duk na bankwana nake mishi ban sani ba,


"Barka da warhaka"


"Barka Jiddatu Nah nazo Miki Sallama insha Allahu gobe zamu wuce"


Sunkuyar dakai nayi kasa "Ubangiji ya sada mu da Alkhairin sa Allah ya tsrae hanya"


Daga Haka na wuce ko waiwayenshi banyi ba shuru yayi, har yanzun taki karb'anshi har yanzun ya kasa samun matsunguni a zuciyarta , Haka yaja motarshi jiki a sanyaye.


inna Sanya kaina a falon Ummi tace "Bansan nayi sake ba, sai yau, Hauwa har kinyi wayon da zaki fita bada izini na ba, ashe ban isa nasa doka abi ba?"


"Dan Allah kiyi hakuri Ummi"


"Kul karna Kara jin Suna na a bakinki Kin mata matsa Yinki ne kin Mata Har Gobe, kina matsa yin matar Arab da Auren ki kike kula wani..."


Wani i'rin zubewa nayi a kasa tare da fashewa da kuka ,Aure? Aure? lna tunani na yaje Ne? wai daman har yanzun Matar Aure ce Ni ,
innalillahi wa'innailaihi rajiun..
~Saura kar naga Comments da Vote~
Maman Faruq
12/26/23, 9:03 AM - UMMI JB: *♡SIRRIN ƊAUKAKA♡*
_Wattpad@ayshajb_


®️🌁


*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION..📚📚*
[Kungiya Domin wayar da kan mata, Farin jini writer's domin ci gaban Mata.]


_♡F.J.W.A♡_


https://www.facebook.com/FARIN-JINI-Writers-Association-109861227874440/


AsmeebashBashir💗💋,


Free Book
Page 12
“Nashiga uku Ummi Aure wani Auren da, dashi da babu duk d'aya? taya ummi, Gaskiya Baze Yuwu ba.." a guje nayi D'aki tare da banko musu kofa duk sunyi tsaye kuka nake kaman Raina ze fita , lna da ilimi. da nasan da wannan Auren yaushe Zan Riga kula Sir Nabil? Wayyo Allah, komawa nayi kaman karaman yarinya dabas na zauna, inna kirga yatsuna ,yau shekarata ashirin da hud'u, tun innada sha hud'u aka K'ak'abamin Wannan jangwan d'in, inda nake ajiyar kud'i naje na cire dubu tamanin na nufi falo kamar mahaukaciya har yanzun Suna tsaye, har dashi daya shigo watsa mishi kud'i nayi. "Wallahi baze Yuwu ba! Ban manta jahilcin da suka nunamin ba, ga inda ake Sona ake karramani me ze kaini cikin , uƙuba, Ga kud'in ka, harda Kari na maka ka barni na rok'e ka dan girman Allah.. nakasani zakuyi zaku kassaramin Rayuwa!"


Zubewa nayi saman gwiwowina "Ka dubi girman Allah da Darajan Fiyayyen Halitta Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi a wasallam, ka rabani da Nauyin ka, Wallahi ban tsara Tafiya da kalar ka ba, ban tsara Zama Karkashin inuwarka Ba! Ban shiryawa Matanka Nafisa Zaina da Fure ba, Haukatani zasuyi kaima basu Barka ba bare ni , Loma d'aya Kayiwa girman Allah ka sauwake min..."


Rik'e kafad'unta Arab yayi Yana murmushi "Kai Wallahi sai na kara jin son kasancewa Dake , Ga jarumta inna hangowa qwayar Idonki, wannan ragwantan ba Na jarumar mace i'rin Hauwa'u Jiddah bace daure Amariyata , daure ki razana min su, daure ki kwace musu ni" cike da murmushi ya karasa maganar , kwacewa nayi "A'a ban isa na karb'i Muazzan ba.." kuka wiwi harda majina (kazama baranyi k'awance dake ba, Gwara Nuwaih Nah)


Kwanciya nayi cik'e da Tausayi Halima tace "Toh uncle tace bata yinka ni ka daina sata kuka" kaman zata fasa ihu ta karasa maganan. Takuwa Ummi ta mata "kubar Nan!" Ta daka musu tsawa "Amma ummi"


"Bar Nan Hanisa".
Suna barin gurin Ummi tace "Rufe min baki shashasha kawai kwashe kud'in ki bar Nan kafin na shiga jikinki" mikewa Nayi a zuciye Nayi hanyar d'aki "Dawo ki kwashe" Wallahi ko juyowa banyi ba, Haka nabarta Nan ta shiga fad'a inda take shiga ba Nan take fita ba, domin ranta yayi bala'in b'aci "Tashi ka tafi"


Sanin ranta na b'ace ne ya hanashi mata magana Haka ya tafi bayan ya tura mata kud'in data bukata ,


Koda naje d'akin Suna tsaye ganin shigowata yasa suka Nufo ni "Ku barni!" Abinda nace Kenan tare da kwanciya a kasan carpet wani i'rin kuka nake inna tuna rayuwar da nayi da Sir Nabil cikin k'ankanin lokaci da sauri na kawar da tunanin tare da yin lstigfari tuna matsayi na da nayi, Ranan Haka mukayi kwanan bak'in ciki, domin ko abinci na kasa sakawa cikina Suma ganin banci ba, ya hanasu Cin abincin ko hirar da muke na gajeren lokaci bamuyi ba , juyi kawai nake can barci ya d'auke ni.


Mafarki.
Zaune nake ni kad'ai a wani fili me shegen duhuwa , baka jin motsi komai sai kukan Ababen halitta sunkuyar da kaina nayi kasa wani i'rin kuka nake inna lalube can na hangi mahaifiyata da sauri nace "Ummana dan Allah ki tawo gareni zasu kassara Rayuwata" kokarin mikewa nake Amma na kasa tashi batace komai ba, Amma daga inda nake inna hango hawaye a idanunta Sallaya ta shimfid'a ta hau sallah.
Kuka nake sosai..


Kamar kiftawar bakin Abu ta fiskata yasa ni farkawa Nan na kunna wutar d'akin shuru na zauna rik'e da kaina dake wani i'rin juyawa chan na tuna mafarkin da nayi da mahaifiyata wanda rabon da nayi mafarki da i'ta na manta, jiki a mace na nufi Band'aki tsarki nayi tare da d'auro alwala Agogon d'akin na kalla naga karfe biyu, da minti shida, Sallaya na shimfid'a na tada sallah nafila nayi raka'a hud'u cikin sujjadar Karshe na fashe da kuka inna rokon Allah. "Ya Allah ni baiwarkace Allah kafi kowa sanin sirrin dake b'oye Allah nayi tawassali da sunayenka tsarkaka Allah ka jibb'aci lamarina Allah ka kawo agaji cikin rayuwata Allah idan Akwai Alkhairi cikin tarayyata da Arab Allah ka tabbatar in kuma babu Alkhairi ubangiji ka nisanta ni dashi Kamar yanda ka nisanta sama da kasa, Allah babu wani abin bautawa sai kai, Allah ban had'aka da kowa ba, Allah dakai kad'ai na dogara Allah ka saukaka min.." Haka ta ringa kuka tana gayawa Allah damuwarta har karfe Hud'u da arba'in kafin ta idar da sallarta tana Zaune akayi Kiran sallar farko , lokacin na karatowa ta make kafar Hanisa da Halimatu. Komawa tayi, ta gabatar da raka'a tainin fajir, kafin tayi sallar subayi,


Koda ta idar bata koma ta kwanta ba, Fitowa tayi ta hau Gyara falon Hanisa da Halima suka hau , shara tana kammalawa ta Nufi kichin ta d'ora musu abin kari kunnun tsamiya da alale tayi sannan ta soya musu dankali tana gamawa ta Gyara abinda ta b'ata wanka taje tayi karfe bakwai taji motsi ummi d'akinta ta nufa ta sameta Zaune tana duba littafin addini "lna kwana ummi" ta fad'a tana Sunkuyar da kanta kasa,


Batare data d'ago ba ta amsa mata jikinta ne ya mutu cikin sanyi murya tace "Dan Allah Ummi kiyi hakuri insha Allahu hak'an baze Kara faruwa ba" murmushi tayi "Babu komai!"


Kuka na saka ganin taki ta kalleni na rik'e hannunta "Ummina fushinki masiface a gareni Zan Miki komai bazan sake sab'awa umurninki ba dan Allah ki yafe min" kad'an ya rage hawaye be zubo Mata ba, ganin yanda Jiddah take rok'onta "Na yafe miki Allah ya yafe mana"


"Nagode Ummina insha Allahu zanci gaba da faranta miki Kamar yanda kika d'aukaki lamarina zan rik'e kaninki Zan mishi biyayya kodan na samu lahirata"


Murmushin jin dad'i Ummi tayi. "Ubangiji yayi Miki Albarka"


Da ameen na amsa kafin na fita inna share qwallar dake zubomin na amsa Mata ne Dan na faranta mata domin matar tamin komai tamkar Halimatu haka ta rik'e ni.


Bayan kwana Goma.
Duk wannan kwanakin haka Nan nayi su, domin jina nake wani i'rin ga Halimatu da suka taso ni gaba matar uncle ko kofar Gida ban lekawa karatun islamiyar ma wata malama ummi ta d'auko min inna ji inna gani Haka zasu fita Amma banda ni, in Kuma nace Zan bisu Hanisa sai tace "Bari na Kira Miki uncle Arab ki tambayeshi ldan ya Baki izini toh" tsaki nayi "Kuyi Tafiyar ku"


Zama Halimatu tayi tare da fashewa da dariya "kai Allah ya nuna min ranar da uncle Arab ze yi shagali inga yanda zakiyi" ayarin da nake taje kaina na jefeta dashi. "Toh Allah ya shiryaki sahiba"


Hanisa tace. "Uhm in-law Wallahi kina da aiki wannan Gidan zamanshi se kin shirya" D'aure gashina nayi "Nadogara da Allah zai kawo mafita"


"Amma an cuce ki in-law uncle ya tsofe shekarar data Wuce ya Aurar da yaransa biyu MashKhura da mansura 'Yan d'akin zainaba , d'akin zaina Wanda uku ne duk Mata, i'tace matar uncle Arab ta biyu , yanzun saura mata Marzkhura , Fure'atu nada Biyar Sadiq Sagir Sabilah sai'rah Sajidah , Uwar Gida Hajiya kwatakwata Nafi tanada yara biyu rak Jamil da Jumaina Allah be bata tun daga su bata Kuma ba, a duk matar shi Fure i'tace me 'ya'ya a tak'aice yaran Uncle goma maza uku Mata bakwai , Gidan uncle ana wani Abu wai shi K'azamin kishi , domin Wallahi mata ukun Nan Gobara ne har gwara Nafi kishinta da sauki akan na fure Zaina kuwa tace in bakayi bani guri, Da har chasu sunayi ban sani ba ko har yanzun Suna yi, in-law inna tausaya miki Sabida ke yarinya ce , zaki shiga cikin jigajigan Boko Nafi Dr ce, Zaina ma'aikaciyace Fure kuwa Yar kasuwace domin dukk'ansu Nan Basu cika zaman gida ba sai Juma'a da sabar da Lahadi"


Ta karsa maganarta tana zauke Numfashi "Toh amma.." taya kuke ganin zan billowa rayuwar Gidanshi nifa banson tashin hankali da hayaniya yamin nawa gurin daban, Halima tace. "Me wiyar kenan Domin ya gwammace ya had'asu Sabida gwara zamansu Guri d'aya.."




Maman Faruq
12/26/23, 9:03 AM - UMMI JB: *♡SIRRIN ƊAUKAKA♡*

_Wattpad@ayshajb_


®️🌁


*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION..📚📚*
[Kungiya Domin wayar da kan mata, Farin jini writer's domin ci gaban Mata.]




https://chat.whatsapp.com/HsMb0FG2FMMFCBLoDfHoyQ




Page 13
Sahiba gwara ki zauna tare dasu d'in ta hakan ne zaki gane halin ko waccen su Ki daure kawai Halima tace haka Hanisa tace. "Banji Nafisa domin nata seya motsa take Haukar duk da Haka ba, i'rin tasu bane idan ka fahimci Halinta ka fahimci abinda take so Wallahi zakuyi zaman lafiya , Amma Kinga Yar Banza ba kaman Zaina wannan matar Allah kad'ai yasan me Take Nufi a Gidan Uncle kodan taga 'Yaranta sunfi nasu ne oho Fure ma Zumace seda Wuta , basa Zaman Gida amma in suka zauna Ranan Gidan ya zama Filin daga , kawai kici gaba da addu'a kaman yanda kika Saba Allah d'oraki k'ansu"
Shuru nayi domin jikina yai bala'in sanyi banjin Zan i'ya zama tare dasu.
Mikewa Nayi na nufi 'Dakin Ummi samunta nayi da tarkacen itatuwa zama nayi tare da d'aura kaina saman kafad'arta a hankali hawaye na yake sauka a jikinta "Kiyi hakuri Nanda Mako guda Zaki amshi ragamar rayuwar shi ki kulamin dashi domin duk a cikin kannina nafi jinshi yafi Kaunata fiyye da sauran yafi Kulawa dani fiye dasu , Yana bala'in son mata musammam 'Yan Gayu shiyasa ya tarasu a gidanshi gasu de Basu da wata makusa Abu d'aya suka rasa , gamsassiyar ilimin addini dalilin da rayuwarshi take walagigi kenan sun bawa aikinsu mahimmanci Basu cika Girkawa ba, 'Ya'yansu mata ma Basu koyar dasu Girkawa ba, wani lokaci Nafisa ke daurewa ta kulashi Sabida tafisu sauki ta wani fannin,
"Hauwa Bazan Baki maganin mata ba, Amma zan

Please Login or Register in order to submit comment