Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na gama video wishes din Khaleel kwatsam ciwon da bamu san da shi ba ya zo gadan gadan har yanzu muna asibiti anata fama."


Cikin damuwa Zahra ta ce, "Subhannallahi me yake damunta? Meya sameta?"


"Cancer." FAROUK ya fada jiki a sanyaye.

Zahra ta ce, "fatan amman bai yi nisa a jikinta ba ko?"

Farouk ya ce, "Eh to haka likitocin suka ce bai yi nisa ba."

Dogon numfashi zahra ta ja kafin ta ce, "Alhamdu Lillah in sha Allah yanzu za a taresa da wuri yadda ba zai mata illa ba,Steep in 2 cups of hot water,1 teaspoon of turmeric power +Tables spoon of chopped ginger

Kullum tana sha sau uku, safe rana dare na wata guda in sha Allah za asamu Nasara.

Yana matukar tallafawa masu cancer da fibroids."


Farouk ya ce, "In sha Allah kuwa yanzu za a jika thank you so much yar guntur kawata."

Murmurshi kawai Zahra ta yi tana, "Uncle Dogo."

Suna gama wayar zahra ta shige restaurant.

Zaune take a office dinta sai ga Suhana ta shigo tana fadin, "Anty Anzo nemanki."

Da mamaki Zahra ta ce, "Ni kuma?"

"Eh wasu matane su biyu sai namiji." Suhana ta fada.

Zahra ta ce, "Ok su shigo."

Suna shigowa ta ga manya mata da namji babba guda daya hakan yasa ta kara jin mamaki aranta amman a azahiri ta ce, "Bismillah ga waje ku zauna."

Zama suka yi sannan suka gaisa

Annaya, Elsa da Arif suka gabatar da kansu ga Zahra sannan Annaya fara fada mata Dalilin zuwansu.

"Kamar yadda muka gabatar miki da kanmu mu jagorori ne karkashin wata karamar kungiya da aka ginata domin tallafawa marayu da marasa karfi, munji labarinki muna da zaton cewa zamu iya kawo kukanmu gareki kai tsaye." Annaya ta fada.

Arif ne ya numfasa kafin ya ci gaba daga inda ta tsaya, "Batu na gaskiya muna da bukatar ki acikin wannan tafiya bangare biyu,na daya kudi na biyu kuma ki bamu shawarwarin yadda zamu kara inganta tafiyar mu da kuma tsarin da za mu bi, domin kuwa muna daf da amsar bakoncin Wani dan siyasa wannan mataki da muke son kaiwa yasa muka zubarar da kanmu zuwa gareki."


"Muna da tabbacin zamu samu hadin kai gareki kasancewar ki mai karamci da damuwa da damuwar al'umma jin labarinki ya matukar kara mana kwarin gwiwa da jin cewa muma zamu iya kuma sanadinmu al'umma za su yi farinciki." Cewar Elsa

Zahra ta numfasa kafin ta ce, "Alhamdu Lillah na ji dadi matuka fiye da zatonku ko ince zato na ma rayuwa xata tafi daidai cikin aminci indai xamuna tausayawa na kasa damu, shawara ta farko da zan baku shine ka da kuyi aikin Alkairi kuyi tunanin dawowar wani abu baya gareku,ku sanya aranku cewa kawai za ku yi don Allah ne,kuma domin Allah kuke, sannan kada ku karaya don an samu a kasi ta wani bangare watakila wannan akasin ma haske ne gareku ku jajirce haka kuma kuyi kokari kuyi komai da zuciya ɗaya sannan duk wani babba a kasan nan da zai zo gare ku kada ku taɓa boye masa komai ku bayyanar da iya gaskiyar ku wannan ke nan a yanzu hakan kadai nasan in kuka rike za asamu Nasara da ikon Allah batun tallafin kudi kuma ina zuwa minti biyu Don Allah."


Fita tayi a restaurant din taje gida, dakinta ta shiga ta dauko wani kudi a Envelope zuciyarta nata mata sake sake kawai ta yi Murmurshi ta fito da kudin ta koma cikin office dinta ta mikawa Arif.

"Abun da ke gareni ke nan kuma nasan in sha Allah zai muku abun da kuke so kafin aje gaba kuyi hakuri, sannan duk lokacin da kuke bukatar taimakona ina free in sha Allah haka kuma inna samu lokaci zanzo tunda ga address kum bani daga nan sai mu kara tattaunawa, Fatan nasara."


Godiya sukai mata sosai dukan su domin sunji dadi mussaman yadda ta karbesu fiye da tunaninsu.

Bata bari sun tafi bama har sai da suka ci abinci suka koshi.


★★★Theraa ce taje ta dauko Noor askul kasancewar Khaleel ya fita.


Suna cikin mota Theraa ta ce, "Noor."

Ya amsa

"Kana so na? Kana so in zama momynka?"

Noor ya ce, "Yes Anty indai zakina sa Dad farinciki kuma ba za kina masa magana da tsawa ba."

"Zaka yi farinciki inna kasance hakan?"
Ta fada.

Noor ya gyara zama yana, "Sosai da yawa Anty,kin san mene ne? Ina son dad dina fiye da kowa ,bana so in ga baya Farinciki ,na fi so kullum yana dariya yana jin dadi nima sai inji."


Theraa ta ce, "Alright nama alkawari Dad dinka zaita farinciki ba zan bari ransa yana baci ba,kuma ba zan na masa masifa ba ,sannan kaima zanna kula da kai."

Dariya Noor ya yi, "Thank You Anty,Thank You So Much."

Bayan sun koma gida noor yayi sallah ya ci abinci ya kira su Anitha yana basu labarin ya kusa samun sabuwar Mom.

Sunata hira har lokacin sallar la'asar ya yi a Indonesia.

Noor naji ana kiran sallar har an idar da kira su Anuska ba su yi addu'ar Bayan kiran sallah ba ya ce, "Aniy , Anushka ba kuyi addu'ar da ake bayan kiran sallah ba kun manta ne?"

Girgiza kai Anitha ta yi.
Anuska ta ce, "Ba mu iya ba."

Noor ya ce, 'Tom zan yi kuna maimaitawa, *Allahummah Rabba haxihid da'awatit timmat,wassalatil ka'ima ati Muhammadan alwasilata wal farilata waddarahatar-rafi"ata wab'ashul maƙamal Mahmudan allazi wa 'attahu innaka la tukhliful mi'ad.*"


Yana yi suna maimatawa har suka kammala.

Noor ya ce, "Wannan ita ce Addu'ar da ake aduk bayan kiran kowacce sallah."

Hada baki suka yi suna, "Thank You Noor."


DARE
★★5Stars haduwa suka yi duka suna yiwa FAROUK ya mai jiki.

Bayan sun gama gaisawa kamar kullum suka fara sanar da junansu duk abun da ya faru da au aranar.

Khaleel ya ce, "Ni dai kam yai ziyara nai zuwa tsohon companynmu na ji dadi sosai kuma ganinsu mussaman yadda suke nuna kewata hakan yasa ni jin cewa ba abun da ya kai mutum ya zauna lafiya da mutane dadi da yanzu ba ayi zaman lafiya dani ba,ban isa inje ba,kuma ko da naje babu mai murna da zuwana bare jin dadi Alhamdulillah."


Deejerh ta ce, "Ma sha Allah,ni kuma yau ina office naga abun mamaki wata yarinya aka kawo mun wai tana da shaawar designing kaya bata wuce shekara biyar ba, na bata takadda da biro baka ga rigar da tai mun designing da ace kowasu iyaye zasuna girmama baiwar yaransu da anji dadi kuma an samu ci gaba sosai a rayuwa."


Dukanninsu kowa ya bada na shi jawabin illa Zahra da tayi shiru Farouk ya ce, "Yar guntuwa muna sauraren ki."

Dariya ta yi kafin ta ce, "ni kam dai yau naji mamaki da akazo neman alfarma guna har office kuma manyan mutane ba kananu ba, na basu shawara yadda suka bukata sai dai kuma kudin da suka nema ban da shi hakan yasa na dauki kudin makarantar su Anitha da Farouk ya Turo mun na basu kawai."

Deejerh ta ce, "What? Kudin makarantarsu? Wannan sam bai kamata ba ko adddinance gida bai koshi ba,ba a taba bawa na waje,sam ban yarda da cewa ban da shi ba in bayar wannan ai ganganci ne, yanzu ya zakiyi da biyan kudin makarantar nasu, kin san dai in har basu tsallake wannan karshen shekarar ba, babu batun canja aji.....


*Fans gareku shin zaku iya wannan kasadar da Zahra tayi? Bata da shi an bata ta biya kudin makarantar Yaranta ta bada ga wasu mabukatan bayan cewa ita ma tana da bukata?* Ina sauraran ku cikin comments


*Amman indai tani ce yadda deejerh ta fada ina bayanta ba zan bada abun da nake da bukata ga wasu mabukatan ba sai har gida ya koshi kafin a mikawa waje*

*Shin mene ne ra ayinku dangane da hakan? Ina sauraro kowacce ta fada in zaki iya yadda zahra ta yi mene ne dalilin? In ba za ki iya ba shi me mene ne dalilin? Mu je zuwa Xayyeesherthou fans club*

08103080717
Urs Xayyeesherthou
[9/30, 4:22 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *FREYA*


*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ko wata ba, Saƙo ne kawai na ke son ya isa inda ya dace_

PAGE-25

_*Bismillahir-Rahmanir-Rahim*_

_Allahumma munzilal kitabi sari'al hisabi,ihzamil Ahzaba, Allahumma zumhum wazalzilhum🙏🏼_

TALLAH

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!... sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_

★★

_Buy your Mtn Data At Affordable Price_
MTN
500mb = 200
1GB = 300
2GB = 550
3GB = 850
4GB = 1150
5GB = 1450

Cal. Whatsapp 07046767662
Chat on Facebook 👇Maryam-Ashner Isma'l Usman
★★

Khaleel ne ya katse deejerh da fadin, "Aa fa, Yadda ta bada da niyar alkairi Allah zai kara bata ta wata hanyar da bata tsammani, abun da ta yi daidai ne babu kuskure tunda har ta yi imanin da cewa Allahn da ya bata ta bayar ba zai taɓa bata kunya ko kasa biya mata bukatun ta ba, wannan ita ce rayuwa, tunda har bata rasa abun da zata ci ba,kuma bata rasa wajen zama ba, sannan numfashi bai gareta ba Alhamdu Lillah hakan ba karamar ni'ima daga Ubangiji bane, ku tausayawa na kasa da ku Allah zai tausaya maku,ku taimaki yan uwanku, Allah zai taimaka maku ba sai mukusantamun ko wa inda muka sani ba, aa muddin mutum na da bukata kuma kuna da hanyar biya masa ko da ba duka bane daidai gwargwado kokarta yin hakan, dukanninmu muna rayuwa ne kawai ba tare da sanin cewa ina gobe zata kaimu ba,ya zamu kasance kuma wani yanayi? Watakila cikin wa inda muka taimaka sune zasu ji kanmu Allah yasa mu dace."


"Tabbas wannan haka yake Friend ina bayanka 💯 rayuwar duniyar nan ba komai bace,mu taimaka muma Allah zai taimakemu da ikon sa." Cewar Haiydar.


Farouk ya ce, "Kwarai kuwa Yar Guntuwa anyi abun kirki , wannan shine asalin dabi'ar 5stars."


"Na fahimta ni kaina kuma na karu tare da daukan wani darasin tabbas abun da Zahra tayi shine daidai." Deejerh ta fada.

suna cikin chat dinnan kuwa kwatsam Zahra ta fara ganin kudi na shigo mata, farko khaleel na biyu Farouk na uku Haiydar sai ga na deejerh daga karshe.

Mamaki da farincinki fal ya mamayeta domin ninkin ba ninkin abun da ta bada ta samu tun kafin aje ko ina.

Cikin farinciki ta shiga group dinsu tana.

"I am so lucky to have a friends like you,
I am so blessed to have you,
Friends like you are too rare,
Friends like you a really few,
You are the real gem that shines,
With you things are so good and fine,
Thanks my friends for being there, words can't express how Happy am I,Thank You all
Love ya so much."

Khaleel ya ce, "Alright yanzu da maganar da nake so muyi duka daman,akwai bukatar kasancewar mu tare duka domin bikin fara aikinmu da yin rigisternmu zamu yi haduwar gani da ido na farko kuma dukan ku yana da matukar muhimmanci hallartarku."


Farouk ya ce, "Yes ka rigani azahiri amman na rigaka azuci ina matukar bukatar ganin waccer guntuwar ko ta rage rainani."

Dariya suka yi duka

"Aikuwa ni damuwata inci chicken breast kun san bana wasa da food." Haiydar ya fada.

Deejerh ta ce, "eheen aiko ba mai ma girki bare ka ci sai dai kana girka kayanka ehee."

Zahra dai bata ce komai ba illa dariyar da take.

Farouk ya ce, "Yar Guntuwata baki ce komai ba ko dai bakya farinciki da haduwa da mune? Kina tsoron ganin kyakkyawan saurayi ko?"

Murmurshi Zahra ta yi ta ce, "Nop kawai ina jin kewar cewa ni ba zan kasance cikinku bane abune mai wahala gareni tunda ban taba fita a kasata ba,ga kuma Anushka da Anitha ba zai.....
Sai kuma ta yi shiru.

Khaleel ya ce, "Mene ne hakan yake nufi? Dole fa ki Kasance domin baza mu ji dadin hakan babu ke ba sam zan clearing maganar passport,Visa dinku da jirgin da zaku shiga just ki kasance cikin shiri."

Farinciki zahra tayi sosai tare da kara yiwa khaleel godiya.

Kafin Haiydar ya ce, "Case close Weldone Friend, yanzu ya kuke ganin ya kamata Musa date?"

Farouk ya ce, "Ina ganin ai ba zancen wani jan lokaci zamu iya yin komai cikin wata ɗaya tunda Khaleel zai tura da latter of invitation ga Zahra."

"Tabbas hakan zai yi, karshen watan nan kawai Can't wait." Deejerh ta fada tare da emojin rawa da murna.


Daga nan suka ci gaba da hirar su suna tsokanar juna har suka watse.


Washegari Mr Imam yazo Zahra take bashi labarin zasu tafi Uk In sha Allah.

Ko kadan hakan bai masa dadi arai ba,har ma sai da yanayin fuskarsa ya canja.

Ta ce, "Mene ne ? Baka Farinciki da jin hakan?"

Murmurshi kawai ya yi Azahiri ya ce , "Aa na maku murna mana sosai Allah sa aje lafiya a dawo lafiya."

Murmurshi kawai ita ma ta yi tare da fadin Ameen domin ta san hakan sam bai masa ba.

Ana saura kwana biyu su tafi komai ya kammala Zahra da su Anitha sunje sunyi passport da visan su har sun karbo.

Daren ranar Gaɓadaya daga ita har su sun kasa barci sai farinciki,mamaki take wai da gaske ita ce yau zata fita wata ƙasa ta bar Indonesia

Noor ma kasa barci ya yi sunata video call da su Anitha yana murna tare da basu labarin abubuwan da zai nuna masu in suka zo.

Washegari bayan Zahra ta kai su Anitha school ji tai Danginta sun fado mata arai,hakan yasa kawai ta kudurci zuwa.

Kamar wasa ta kama hanyar gidansu ,tana tuno rayuwarta ta baya harta isa, abun da ta tarar ne ya matuƙar gigita riskar rasuwar kakarta da tayi shi kuwa Uncle dinta da matashi cikin mamaki suke kallonta domin sam basu ma ganeta ba.

Zahra ta masu bayani Gaɓadaya sake baki suka yi tare da hada baki wajen furta, "Zahra ke ce? Kina raye daman? Baki mutu ba? ."

Murmurshi ta yi ta ce, "Ina raye."

"Amman Adams ya sanar da mu cewa kin rasa ranki lokacin haihuwa." Cewar Uncle dinta.

"Ehto gani nan dai kam da raina Allah bai kaddara hakan ba."

Tsabar mamaki sun kasa sakewa suyi wata kwakwarar magana da ita , ita kuwa Zahra kudi ta basu kawai tayi ficewarta tana jin kunar rashin ganin kakarta domin da kudirin tafiya da ita ta je gidan domin lura da ita.

Komawa gida tayi ta ci gaba da shirin tafiyansu.

5stars sun shirya tsaf kowa ya hau jirgin.
UK.England/Manchester

Farouk, Haiydar da Deejerh duk sun isa , Zahra da iyalanta kawai ake dako, Noor ya kasa sakat hakan yasa aka tafi da shi airport tararsu.

Anitha ce ta fara fitowa kuwa ta rungume Noor,sannan Anuskha ma ya fito suka rungume juna,ban da ihu ba abun da suke yi.


Zahra da su Farouk ma Gaɓadaya sun kasa rufe baki sai dariya kawai ana farinciki tare da rungumar juna.


FAROUK ne ya mika mata hannu yana, "Welcome to Manchester Yar Guntuwa ya ki ka ga santalalen saurayi? Ince dai zuciyarki bata kusan bugawa ba da kika ganni?"


Dariya Zahra ta yi, "Yoo ni ai duk tunanina inna ganka suma zanyi tsabar kyau tsayi kuwa na zata sai na daga idona sama kafin in iya ganoka,amman yanzu ji tsayin fa da kadan ka darani." Tsaya ta fada tana kara tsayawa daf da shi.

Cikin dariya Haiydar ya ce, "Yau kam ai kuma Shikenan awaya ma ya aka kare bare a fili, guntuwa da dogo an hadu."

"Yanzu dai zan nemowa Friend ataimaki wada tana sawa kawai." Deejerh ta fada.

Dariya suka yi duka sai alokacin Khaleel ya ce, "Yanzu Shikenan dai ga motoci nan sunzo ya kamata mu tafi gida sai ku karasa guntayen da dogayen."

Da dariya dukkanin su suka shiga mota

Na su Noor daban.

Khaleel , Farouk da Zahra a tare

Sannan Haiydar da Deejerh.

Suna zuwa gidan Theraa ta gama shirya masu komai na abinci ta tsara.

Bayan sun gaisa duka tayi sallama da Haiydar kan cewa ta tafi.

Noor kuwa nunawa su Anitha ita ya yi ya ce momynsa ce.

Tana tafiya Haiydar ce, "Hungry."

Dariya suka yi Deejerh na, "Tun tuni nake jira ka fada ai Food Master."

Bai kulasu ba yana shafa ciki kawai ya nufi daining tare da fara cin abinci sai daga baya suka biyo shi.


Noor kuwa kin cin abinci ya yi ya ce shi popcorn zai ci kuma na shi ya kare.

"Za ka zauna ka ci abinci ko ya ya? Noor ka kiyayeni fa." Khalil ya fada.

"Why not muje yanzu mu siyo dare baiyi sosai ba ai." Farouk ya fada.

Zahra ta ce, "Aa akwai masara agiddanan "

Noor ya ce, "No Mom."

Ta ce, "Bread fa?"

"Yess akwai." Noor ya fada.

Tashi ta yi tana, "Owk barin maka bread popcorn zaka ci ina?"

"Yes." Noor ya fada
Anitha ma ta ce, "Mom nima ina so zan ci."

Khaleel ya ce, "Oh oh ba za ki huta ba, daga zuwa zasu saki aiki?"

Zahra ta ce, "Ba wani aiki barin masu na san ku kanku ma za ku so ci."

"Aiko ba za su ci ba nikam dai zan ci." Haiydar ya fada.

Dariya suka kara yi.
Deejerh ta tashi tana, "Yakamata in koya nima don banma san ana popcorn da Bread."

Kitchen suka nufa tare.

Zahra ta dauko bread ta rabasa ya yi dogaye da wuka tukun ta dauki almakashi ta rabasa kanana-kanana


Sannan ta daura tukunya kan gasa.

sugar ta fara zubawa sannan ta sa ruwa kadan, sai da ya fara tafasowa tukun tasa butter da madara ta hada su duka tana juyawa har sai da suka gama jikinsu kuma suka dan canja kala kafin ta zuba bread din ta ci gaba da juyawa sai da ko ina ya ji ya samu kuma ya soyu kamshi ya fara tashi kafin ta sauke ta juye a bowl babba.


Deejerh ta ce, "Wooo daga kamshin ma kadai ya isa ya bada dadin da zaiyi abu cikin sauki yan mintuna kalilan kuma ba wani cin kudi gaskiya na ji dadin koyon wannan tsarin ." Ta karasa maganar tana kaiwa baki tare da rufe ido.

"Gaskiya ya yi dadi fiye da tunanin mai tunani ba dan kar ace santi bane kodayake gaskiyata kawai zan fada ni har yafi mun normal popcorn ma dadi."

Dariya Zahra ta yi ta ce, "Su Anuskha suna so sosai don su sam ma basa yarda da cin popcorn yanzu in ba na bread ba sun riga sun saba."


Tana kai masu kuwa aka fara warwaso Mussamman Farouk da Haiydar .

Su Noor kuwa tunda ta basu nasu suka shiga daki ba wanda ya kara jin motsinsu sai da suka cinye kafin Noor ya leko yana, "Mom."

Dukansu suka juyo suna kallonshi.

Ya ce, "Gobe za a kara mana bread popcorn?" Ya karasa cikin sigar shagwaba.

Dukansu basu san sanda suka tinsire da dariya ba.

Zahra ta ce, "In sha Allah Son."


Washegari zahra na tashi sallar asuba ta ga deejerh na murkususu.

Zahra ta ce, "Mene ne ya faru lafiya?"

"Cikina,marata ciwo zan yi period ne." Deejerh ta fada da kyar.

Zahra ta ce, "Sannu Ki jirani bari inyi sallah in sha Allah yanzu zan miki wani magani ki sha."

Zahra na idar da sallah ta nufi kitchen.

Ginger ta fara yayyankawa kanana sannan ta zuba ruwa kofi biyu a tukunya tasa jinjina din ya tafasa na minti biyar tukun ta juyesa akofe tasa cokali daya da rabi na cinnamon powder Ta juya.

Tana zuwa ta bata ta sha aikuwa cikin mintuna kadan deejerh ta watsasake ta ce, "Thank You So Much Friend, da yanzu sai in wuni yau cikin ciwon nan don ba abun da zan iya ko abinci ba zan iya ci ba,amman daga shan wannan har na samu relief , Alhamdu Lillah in sha Allah daga yanzu nima zanna yi da kaina ina sha na gode sosai."

Zahra ta ce, "ba komai, Allah kara sauki ba ma sai wannan kadai ba zaki iya tafasa bay leaves shi ma ki sha ruwan yana magani sosai in sha Allah."


Ƙarar su Noor da ya zagaye gidan nan ya katse masu magana.

Daga mazan har matan a tare suka fito da gudu suka nufi dakin.
Suna zuwa.......



Urs Xayyeesherthou
*FREYA*


*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ko wata ba, Saƙo ne kawai na ke son ya isa inda ya dace_

PAGE-26

_*Bismillahir-Rahmanir-Rahim*_

_Allahumma munzilal kitabi sari'al hisabi,ihzamil Ahzaba,Allahumma zumhum wazalzilhum🙏🏼_

TALLAH

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!... sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_

★★

_Buy your Mtn Data At Affordable Price_
MTN
500mb = 200
1GB = 300
2GB = 550
3GB = 850
4GB = 1150
5GB

Please Login or Register in order to submit comment