Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bata da hakuri sam aduk sanda ta so kasancewa da shi, amman shi in bukatar shi ta tashi a lokacin da bata ra ayi dolensa ya yi hakuri domin ba za ta taba amincewa ba ko zai mutu.

Shi kuwa ya zaɓi hakuri tare da mikawa Ubangiji kukansa a kullum hakan kuma baya hanasa biya mata bukata aduk lokacin da ta so.
Aransa yake fadin, "ba zan rayu da hakkinki ba Sarah, zan biya miki duk wata bukata ta duniya indai ina da hali ko da ni ba za ki dubeni ba."


Da kanta ta sanya Noor cikin abin wasa sannan nufi Khaleel tare da fara janye masa kayan jikinsa.

Addu'ar da ya saba yi ya yin kasancewar hakan ya fara *Allahumma Jannibnash-shaiɗana Wajannibshi Shaiɗana Ma Raxaƙtana*

Sai da ya tabbatar ta gamsu da biyan buƙatar ta kafin ya barta.
Ta shi tayi abunta tamkar wacce ta je shago siyan abu,an bata ta tafi.

tashi ya yi shi ma,ya je ya kara yin wanka ya yi sallah raka'a biyu bayan ya idar ya yi addu'ar Neman Tsari Da Kasala da kuma mummunan tsufa
اللهم إني أعوذ بك من العجز والكسل والجبن والحرم والبخل, وأعوءبك من عذاب القبر ,وأعوذ من فتنة المحيا والممات

Sai da ya shafa kafin ya je ya yi shirin office.
Sarah har ta kammala breakfast ya ci ya ba Noor ma.
Zai fita ya ce,"Byee."

Kallon shi tayi ta sake Murmurshi , "Byee."

Ya fice.



★★★★zaune Adams yake da Sofiya suna hira.
Zahra ta kammala abinci ta kawo masu.

Da sauri Sofiya ta dauki abincin tana fadin, "Bo Yarinyar nan ta iya girki sosai,tun daga kamshin abincin ta zaka ji bambanci ina so inxo nan gidan inci abincinta, wannan dama gidan abinci ka bude mata."


Tsaki Adams ya yi yana, "Tir wannan me ta iya,ki ma daina wannan batun."

"Amman ina fada ma da Gaske za a samu kudi da girkin yarinyar nan ,ta iya fiye da zatonka,na tabbaata ko da bani ba,duk wanda zai shigo ya ci abincinta dole ya yaba."

Adams ya numfasa,"ki bar batun nan Please bana so zai fi kyau ki ci abincin nan muyi mu gama mu fice."

Dariys sofy tayi tana kai masa kiss.



Zahra na jinsu ta koma kitchen din ta zauna abunta.
Har aranta ta san cewa ta iya girki amman bata daukan hakan wani abun jin dadi domin baya da wani cikakken amfani gareta, sai dai ta girka wa wasu su ci su sammata, wani zubin ma sai dai hange.


Jiyo Kukan Anitha tayi tana wani irin numfashi zazzaɓi ya kamata.

A razane ta karasa ta dauketa.
Gaɓadaya numfashinta ma na shirin daukewa.

Kuka Zahra ta fara cikin firgice tana yi wa Adams magana.
"Don Allah ka taimakeni Anitha ba lafiya zata mutu,ta kasa Numfashi, Don Allah."

Gaɓadaya daga shi har sofy sun shiga duniyar baɗalarsu , suna ganinta Amman ko ta ita basa yi bare su fahimci me take fada.

Jikin Anitha sai ya kara zafi yake tana gurnani.

Tunawa tayi da wannan kudin da mutumin ya bata, ta dauko su ta kara daurewa a jikinta.
Kallon waje tayi,ruwa ake kamar da bakin kwarya ga shi ba bu lemar da zata sa ta fita.

Tunani tayi cikin sauri ta goya Anushka a baya, ita kuma Anitha ta riketa a hannu tare da lullubeta da bargo.

Haka ta shiga cikin ruwan nan ba takalmi tana gudu, tana kuka tare da tambayar Mutane chemist ko wani a asibiti da ke kusa ta kaita.

Da kyar ta samu wani asibiti da ke cikin jakartan ta kaita.
Tana kaita aka karbeta taimakon gaggawa.

Da kyar likitocin suka yi nasarar ceto rayuwar Anitha.

Zahra kuwa Gaɓadaya ta fice a hayyacinta...

★★Uk
Dare ne sosai Noor da Khaleel suna karatu kamar yadda ya saba duk dare sai koya masa karat mussamman addu'o'i

Khaleel ya ce, "Oya karanta mun Addu'ar tashi daga barci."

Noor ya fara, " *Alhamdu Lillahil lazi Ahyana ba'adama amatana wa'illaihin nushur*."
Cikin muryar yara gwanin sha awa yake karatun.

Khaleel ya ce, "Ma sha Allah Barakallahu fikha,yanzu yi mun adduar cire kaya."

*"Alhamdu Lillahil lazi kasani ma asturu bihi aurati wa'atahammalu bihi."* Ya fada.

Murmurshi Khaleel ya yi ya ce , "Ma sha Allah bara mu yi ta yau to Addu'ar juyawa cikin barci, "La'ilaha ilallahu wahidul kahhar Rabbis Samati wal ardi wama bainahuml azizul gaffar." Sai da ya masa yana maimaitawa sau uku kafin ya ce ya yi shu daya.

Noor ya ce, " *La'ilaha ilallahu wahidul kahhar Rabbis Samati wal ardi wama bainahuml azizul gaffar."*

Khaleel ya shafa kansa yana, "Maddalla Allah ya yi albarka ka da ka manta kullum da safe da yamma me ake yi?"

Noor ya ce, " *Hasbiyallah La'ilaha ilallah,alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azim*, sau bakwai da safe kuma sau bakwai da dare,Allah zai dauke mana dukkanin gajiyarmu kuma ya gafarta mana."

"Good boy yanzu sai barci ko?" Khaleel ya fada.

Cikin tsamin bakin Noor ne ya ce, "Dad."

Khaleel ya amsa da, "Yes."

"Me yasa Mom bata sona? Bata kula dani? Amman grandma da kai kuna sona,kuma kuna kula dani,Ni bana sonta,kuma bana son ganinta,na tsaneta."

Cikin sauri khaleel ya rufewa Noor baki, domin yasan Noor zai iya fadin mafiyin hakan yarone karami amman sai shegen Suratu da wayo, shekara hudu kacal amman yana lure da kowa.

Khaleel ya ce, "Kar in kara jin haka ka ji,Mom dinka ce,kuma tana sonka SOSAI, kai ma na san kana sonta ko."

Girgiza kai ya yi, alamar Aa.

Khaleel ya rike masa hannu, "kana sonta Noor, ba a kin uwa ko ya take ka ji,ita ce tai sanadin zuwanka duniya,kuma tun kana ciki take dawainiya da kai."

Noor ya ce, "Dad amman meyasa take mana haka ni da kai?"

"Me take mana? Bata mana komai ai, kowa da yanayinsa ka dauka cewa wannan shi ne yanayinta ita ai." Cewar Khaleel.

Noor ya fara girgiza kai yana, "Aa aa Dad kai ne,kai ne za ka gyara."

Daga nan Noor bai kara cewa komai ba,har ya yi barci.
Khaleel kuwa tunanin maganganun Noor yake gabadaya ya kasa runtsawa mussamman in da ya ce, "Kai ne za ka gyara."



*TSAKANI DA ALLAH TYPING BA YA DADI IN BA ABUN TAƁAWA😭A FITO AYI KARO-KARO A SIYA MUN PURE BLISS DIN TYPING INDAI ANA SO INA YIN MAI INGANCI DA YAWA*


08103080717
URS XAYYEESHARTHUO
[9/3, 5:56 PM] My Number: *FREYA*


*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ko wata ba, Saƙo ne kawai na ke son ya isa inda ya dace_

PAGE-6

_*Bismillahir-Rahmanir-Rahim*_

_Allahumma munzilal kitabi sari'al hisabi,ihzamil Ahzaba,Allahumm zumhum wazalzilhum🙏🏼_

_Ina ga ya zam dole in fahimtar da wa inda suka kasa fahimta,Na fada tun farko amman har yanzu ba kowa ya fahimta,*FREEYA* bangare ne na *YEL* Duk ma su karanta Freya in basu karanta Yel ba su karanta haka duk wa inda suka karanta yel in basu karanta Freya ba su fara,littafina Seris ne dukkaninsu suna da alaka da juna_

*TALLAH*

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!... sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_

★★

_Buy your Mtn Data At Affordable Price_
MTN
500mb = 200
1GB = 300
2GB = 550
3GB = 850
4GB = 1150
5GB = 1450

Cal. Whatsapp 07046767662
Chat on Facebook 👇Maryam-Ashner Isma'l Usman
★★

Ganin cewa ya kasa barci yasa shi tashi ya dauro alwala da niyar yin Salatul-Tasbihi.

*Salatul-Tasbihi*
Raka Hudu ake kamar la'asar, Azahar ko Isha.

In kaso za ka yi karatu a sirrin ko a bayyane.
Ko ka raba biyu a sirince biyu a bayyane.

Ita ana karanta mata fatiha da sura ne acikin kowacce raka'a bambamcin kenan.
In ka gama karatun fatiha da sura ba ruku'u za ka yi ba sai ka yi tasbihi.
*Subhannallahi Wal-hamdulillahi wa la ilaha illallahu wal lahu akbar* sau goma a tsaye.
Bayan ka yi ruku'u ma ka yi zikirorin da ake a ruku'u sai ka kara
Yi *Subhannallahi Wal-hamdulillahi wa la ilaha illallahu wal lahu akbar* sau goma.

In ka taso ma ka kara sau goma kafin kayi sujuda, in kayi sujuda ma kayi zikirorin da ake cikin sujuda ka kara tasbihi goma.
*Subhannallahi Wal-hamdulillahi wa la ilaha illallahu wal lahu akbar*

Sanda ka dago daga sujuda ta biyu kar ka mike tsaye sai ka kara tasbihin sau goma.
Sannan mutum ya tashi ya ci gaba har ya idar.

Manzon Allah S.a.w ya ce , "za ka iya yi da rana kuma za ka iya yi da dare, in da hali kayi duk sati, in bai samu ba duk wata,in hakan ma duka bai samu ba ko sau dayane kayi kafin Allah ya dauki ranka, tana da falala mai dama da inganci.

Wannan ita ce Salatul-Tasbihi sallah mai daraja, wanda Annabi S.A.W ya bawa kawunsa.
Tare da albashirin Allah zai yafe masa kurakurensa kananu da manya, sannan ya biya masa bukatunsa da ikonSa.

Haka Khaleel ya yi,yana idarwa tun daga lokacin ya fara jin sanyi aransa tare da jin tsammanin da ya rasa ya dawo.
Barcinsa ya yi cikin kwanciyar hankali nan take.


★★Indonesia
Zahra kuwa tana zaune dauke da Anushka a hannunta tana feeding dinta.
Kallonta take ita kanta ta san cewa babu maraba tsakanin kammaninta da na su Anushka, tamkar anyi kofin ta ne.
Duk cikin kunci da take shiga indai ta kalli Anitha da Anushka ta kan ji dadi aranta zuciyarta tai sanyi.
Ta lula duniyar tunanin hanyar da za ta bi ta koma gidan Adams kamar daga sama ta jiyo sauti a Tv,daga idonta tai cikin sauri ta ga wani matashin saurayi na jawabi.

"Daga karshe, kuma a karshe
A wani yanayi na rayuwar mutum ya kamata ya yankewa kansa cewa ya isa haka, wannan ba rayuwar da zan ci gaba da yi ba ce, na hango rayuwa ta daban wa kaina, a yanzu kuma zai zamto yanayi mara dadi, kuma zai zamto yanayi mai ban tsoro, sannan yanayi na daban,kuma yanzu ne ya kamata na fuskanci abubuwan da zan canza game da kaina da rayuwata, kuma dole na girma, dole kuma na shiryawa wa kaina kuma na tsarawa kaina, na nemi taimako, amman wannan abar da ake kira rayuwa, lallai ya zo karshe yanzu, dole na canzata zuwa wani abu daban, Kuma dukan dan Adam din da ya ke jina ko sauraron muryata a yanzu, yanada karfi da damar da zai iya canza rayuwarsa.
Ba a fidda tsammani,ka da mu fidda ko na second dayane sanya tsammanin wani ci gaba na rayuwarka."

Maganar Doctor ne ya katseta yana mika mata Anitha tare da bata Bill din kudin da ta biya harda sauran canji.

Dare ya yi sosai ga shi tana jin yunwa karban canjin tayi tana kallo, tare da goya Anushka kafin ta rike Anitha suka fice.

Tana cikin tafiya ta ga wajen sai da abinci, karasawa tayi ta bada kudi aka zubo mata da mamaki kudin nata kadan ne amman an zubo mata abinci da yawa,aranta ta ke rayawa lallai nan gurin suna da arhan abinci.

Tana cikin ci jawabin mutumin tvn nan na yawo aranta nan take ta ji cewa ba za ta koma gidan Adams ba, ta yarda da cewa ta fuskanci rayuwarta da duk wani ƙalubale har ta kai ga cin Nasara da kuma samun ma'ana fiye da ta koma rayuwa irinta baya.

Ta ci abinci ta koshi sannan ta bawa Anitha ma ta ci.
Duka sunyi barci
Har kowa ya watse agun sai ita kadai da mai gun abincin.

Karasowa matar ta yi gareta tana, "Madam ya dai? Dare ya yi gashi har yaranki sunyi barci,ya kamata ki koma gida kar mijinki ya nemeki."

Dagowa Zahra tayi cikin sanyayar muryarta ta furta, "Don Allah ko za ki iya taimaka mun da aiki da gurin kwana anan? Ko me ki ke so zan miki."

Tsayawa matar tayi tana kallonta kafin ta ce, "ina da wadatattun ma'aikata anan, amman kuma in zaki iya aikin wanke-wanke da Shara sai abaki,gaki kuma da yara anya zaki iya?"

Zahra ta ce, "xan iya,na miki alƙawari zan iya indai xaki daukeni."

tausayin zahra ne ya kama matar duk da cewa bata san asalin dalilin zuwanta ba,amman Mussamman domin yaran taji cewa lallai zata taimaka mata.


Hakan yasa ta karbi Anitha suka shiga ciki tare da nuna mata wani dan gefe ta dunga kwana da yaran.
Ta dauko mata wani dan bargo mai kauri da za su kwanta akai.
Ba karamin dadi Zahra ta ji ba hakan yasa ta fara gode mata.


Washegari
Safiya na yi kuwa Zahra ce ta fara tashi ta share wajen tas ta yi moping tayi wanke-wanke .

Madam Zuby na zuwa da mamaki ta tarar har Zahra ta gama komai, gun ya yi kyau fiye da zatonta tamkar mutane goma sunyi kwalimarsa.

Ba karamin farinciki ta ji ba da ta tarar da wajen haka.
Hakan ya kara sawa taji zahra ta shiga ranta Sosai.

Su kansu sauran ma'aikatan da suka zo cikin mamaki suka kasance,sai da Madam Zuby ta gabatar masu da Zahra tare da nuna cewa ita tayi dukkanin wannan aikin.
Faran faran sun amsheta hannu bibbiyu sai mutum daya Sumy da kallon banza ne kawai ya haɗata da Zahra,tana gaisheta ma ko Amsawa ba ta yi ba.

Nan da nan suka shiga girki, ganin cewa Zahra bata aikin komai taje ta fara kama masu tana taya su.

Da sun hada ido da Sumy sai ta harareta.
Ita ko sunkuyar da kanta take kawai.
Anitha na gun Madame zuby har sun fara sabawa da ke tana son yara.
Anushka kuwa na bayan Zahra.

★★★Uk
Khaleel na Tashi da safe kawai zuciyarsa ta yara masa cewa komai ya zo karshe.
Bayan sun shirya shi da Noor ko Sarah ba su jira ta fito ba ya fice.

Driect kotu ya nufa tare da karbo takardar saki.

Ya nufi gidan Ammuh.
Bayan yaje ya kira sarah kan cewa ta zo ta same shi acen.

Sarah ta ce, "Mene ne ya faru da ba zaka zo gida ba,ko kuma ka bari sai ka dawo?"

"Aa wannan lokacin shi ya dace kuma anan gidan, ba zan bari tsammanin da nake da shi ya kau ba,ya zam dole a yau in canja rayuwata, taki,har ma da ta Noor.".

Bai ce ma Ammuh komai ba har sai da sarah ta zo ya ciro takardan saki ya karasa gareta yana, "komai ya zo karshe komai ya zo karshe daga yanzu bazan kara lamunta ba,ba zan kara barin komai ba,ci gaba za a samu ba ci baya ba, dole in gyara ya zam dole in gyara."

Ammuh ce ta karaso tana fadin, "meya faru? Wai mene ne kake haka ne Ibrahim Khalil? Me ka ke nufi."

Khaleel ya ce, "Ammuh cutarwar da nake fuskanta a rayuwar aure bana da muryar furta, tsoro,gudun magana da kawa zuci sun hanani aikata komai uwa uba jawabanki da na rike araina sukan kara karya mun zuciya a kullum ki kan ce (mace Abar tausayi ce,abar a girmama ce kumq abar a tarairaya, ka da in musgunawa kowacce 'Ya mace domin mata taurari ne,a tafiyar dasu tamkar sarakai) a kullum wannan batutuwan suna yawo acikin zuciyata ,suna kara sanya mun cewa mace ba zata iya cutar da kowa ba, na kan manta cewa ni ana cutar dani, rayuwar shekara ɗaya na yi kacal na jin dadin rayuwar aure daga nan Sarah ta fara fidda mun Dabi'un da suke kokarin nukusar dani na tsawon shekaru hudu,ban taba furtawa ba,kuma ban taba nunawa ba,a yau yazo karshe komai ya zo karshe."

Ammuh ta ce, "duk da haka ka bata dama,na tabbaata zata gyara da ikon Allah ."

Khaleel ya ce, "Aa na tabbaatar ba zata gyara ba Ammuh ba zata taba sauya wa ba wannan jta ce rayuwarta ,na gaji zan matsa ga wata rayuwar haka.".
Ammuh zata kara magana sarah ta dakatar da ita cikin kuka tana fadin.
"Aa Ammuh zan sanya hannu komai da ya fada gaskiya ne,babu karya aciki ko da wasa na aikata mafiyin zato ma Amma kafin nan zan tabbatar maka da cewa hakan ba son raina bane,a tunani hakan ne kawai mafitar da zan bi don kubutar da rayuwa daga kuncin rayuwar da Mahaifiyata ta fuskanta,na dauki hakanne tamkar daukan fansa,munyi auren soyayya kamar yadda mahaifina suka yi da mamana, amman abun mamakin shine daga shekara biyu bayan auren su ya fara juya mata baya,na taso da kiyayya, tsana da rashin son mahaifina sam. Mahaifiyata ta zam tamkar baiwa ga ubana,ta zam shara mara amfani, baya darajarata bare darajara ra ayinta,bata da karfin furta damuwarta, tunda na taso aduniya ban taba ganin mahaifina yana yiwa mahaifiyata magana cikin lumana da nuna kauna ba, kullum hawaye ne dak ke mamaye fuskar mahaifiyata maimakon dariya, inko zata yi murmushi sai dai ni takewa wasa gudun kada in sanya damuwa araina, hatta kai ta kawo duka ne yake mahaifina da Mahaifiyata, kullum cikin duka da zagi ga, cin fuska ba wanda bata fuskanta, agaban idanunmu zai shigo da 'Ya'Ya mata,yaje ya kwanta da su, Mahaifiyata bata isa ta ce komai ba,to ina ma take da karfin maganar? Ya yi amfani da rauninta ya tozartata har ta mutu sanadin bakin cikinsa, na taso da zuciyar daukan fansa, da kallon cewa dukkanin maxa haka suke mugaye da alhakin cutar da mata, na sa araina ba zan taba lamuntar hakan ba, kuma ba zan jure ba, sai na fito na gwada mace ma za ta iya,amman haduwata Khaleel ya sauya mun tunani tun farkon kasancewar mu , shekara guda da muka yi na yarda cewa ba duka aka tura aka zama daya ba,abu dayane sanadin komawa ga wannan mummunan kudirin nawa."
Cikin kuka Ta numfasa ka fin ta ci gaba da fadin.

_"ba zan taba mantawa ba akwai ranar da naje office na bi Khaleel domin ba shi wasu takaddu da ya manta da su, office din dad na fara bi, kamar a kunnena na ji yana sanar da wani abokin huldarsa kan cewa shi ne yasa Khaleel ya nemeni har ya aure ni, ba tare da na jira jin mai zai ce agaba ba kawai na tafi tare da wata fasarar araina, na dauka cewa kawai ya aura mun Khaleel ne don nima inyi rayuwa tamkar yadda Mahaifiyata ta yi,hakan kuma yasa na canja akalar rayuwarmu tare da niyar daukan fansa tunkan a aikata mun ni na aikata._

Gabadaya jikinsu ya yi sanyi karfan takardar tayi da bairo tayi signing.

Ammuh na kuka ita ma na kuka.

Ta ce, "Na sa hannu, amman ina buƙatar alfarma daya,ba don ni ba ko Don Noor mu ci gaba da rayuwa tare ba tare da kowa ya sani ba, sannan na je asibiti bayan wannan abun ya faru likita ya kirani ya sanar da ni cewa ina dauke da Leukemia ma ana blood concer,ya riga ya yi karfi tun kafin in sani ba abun da za a iya a yanzu, na san sauran rayuwata aduniya kalilan ne ya rage,ka yafe mun kuma ka gafarta mun."

Rungumeta Khaleel ya yi yana share mata hawaye tare da fadin, "In sha Allah ba zan taba fidda miki sirrinki ba, ina sonki ba wai hadani da ke dad ya yi ba,har cikin raina ina kaunarki."
A lokacin Khaleel ya tafi tunanin farkon haduwar su da sarah.

_ranata ta farko da kasancewa a company, ke ce wacce na fara toxali da ita in ban manta ba,kina sauri kin fito na bige ki takardun hannunki suka fadi kasa,na baki hakuri sannan ya kwashe miki,baki ce dani komai ba,inata kallonki ko ince muna kallon juna, a lokacin dad dinki na lure da mu ba tare da mun sani ba,bai mun magana awannan ranar ba har sai da ya gama aminta da ni kuma ya lura da cewa a kullum in kikaxo company bana da muradi sai kallonki.ya bani amarnki tare da fadin indai ina sonki inje mu daidai ,na kuma amshi hakan ne da son raina domin cika muradi na har muka fara soyayya,sannan abun da yake fadawa mutumin nan ba komai bane illa nuna cewa yarda da kuma yana neman hanyar da zaki yafe mai ne yasa shi jin sha'awar hadani da ke ba komai ba."_

A lokacin sarah ta fara wani irin tari Da aman jini......



*Pure Bliss😩 comments duk ina SO*😶

Domin kasancewa cikin group dina.
Kai tsaye tuntubeni ta wannan number
08103080717

Xayyeesherthou
[9/3, 5:56 PM] My Number: *FREYA*


*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ko wata ba, Saƙo ne kawai na ke son ya isa inda ya dace_

PAGE-7

_*Bismillahir-Rahmanir-Rahim*_

_Allahumma munzilal kitabi sari'al hisabi,ihzamil Ahzaba,Allahumm zumhum wazalzilhum🙏🏼_

*Ba Pure Bliss Ana Typing Kai Na Ciwo🥹Wai Bakwa Sona Ne?*

TALLAH

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!... sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_

★★

_Buy your Mtn Data At Affordable Price_
MTN
500mb = 200
1GB = 300
2GB = 550
3GB = 850
4GB =

Please Login or Register in order to submit comment