Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

550
3GB = 850
4GB = 1150
5GB = 1450

Cal. Whatsapp 07046767662
Chat on Facebook 👇Maryam-Ashner Isma'l Usman
★★
*MALAYSIA*

2:00pm
Gaɓadaya Iyalan 5stars sun hadu a gidan Farouk da ke birnin Malaysia.

Zeeyter ce kwance a cinyar Haiydar tana danna waya.
Farouk ya ce, "Gimbiyata wai Don Allah ke kin fi kowa son mijine? Anan dinma ba za ki bar shi ba ko dan ganin idonmu?"

Kallon Haiydar ta yi tana jan sajensa.
Kafin ta gyara zama tana, "eheen kana so in barshi ana masa kallo daidai da yarda ake maku? Ana tunanin gauro ne? Aa fa tom gwanda ina bayyanar da bambancin kasan akan kishi na kan manta wace ce ni ma bare shi."

Bige hannunta Haiydar ya yi yana, "ki barni fa tun kafin inyi tamola dake,wai hakan da kike shi zai sani fasa kara auren ko ya?"

Gallara masa harara ZEEYTER ta yi ta ce, "mu mola juna dai,kasan ba amun in kyale ehee, And maganar kara aure kuma ka yi mana ni na hana ka ne? Ai akujera zata zauna ba dai akaina ba ko?"

"In ta kama ai zata zauna akan kin ma." Haiydar ya fada.

Tsaki Zeeyter ta yi tana kasa da murya, "Sunshine."
Haiydar ya ce, "yes."

"Umm abar maganar nan haka, kasan dai ina sonka ko?"

Dariya Haiydar ya yi ya ce, "love you too YEL."

Dukansu dariya suka yi Zahra na fadin. "wato ku dai duk wanda ya ce zai shiga Tsakaninku ma sai ya ji kunya , kuna kara girma amma halinku sam yaƙi canjuwa yadda kuke tunda din dai haka kuke."


Khaleel ya ce, "Ba wai dan ganin idonsu ba amman kam tsarin rayuwarsu na birgeni zan so ace nima na samu hakan ko kwatankwacin hakan."


"Allah ya zaɓa mana mafi Alkairi da zuciyar hakuri tare da dangana kamar yadda suka kasance." Deejerh ta fada.

Tashi Farouk ya yi yana, "kun fi kowa sanin bana juram zaman nan haka barin je toilet in dawo asamu abun yi tunda sai gobe za mu fita."

Ya tafi yana, "Gimbiyata aduba su Noor fa kar suyi wani wajen."

Zeeyter ta amsa da okey kafin ta fita dubasu Noor da suketa wasa.

Suna ganinta suka yi tsalle Noor ya rugumeta yana , "Yes Anty ki zo muyi basketball dinnan please,tun tuni yaƙi yin dadi saboda babu ke."

Zeeyter ta ce , "alright amman in na cinye sai kun goyani kun yarda?"

Dukansu da karfi suka amsa, "Yesss."


Farouk kuwa yana shiga toilet ya fito zai wuce kenan ya ga littafi ya fado a jakar Khaleel.

Komawa ya yi ya dauka zai mayar mai ya ga an rubuta "FREYA" a bangon littafin cikin sauri ya bude yana budewa ya fara bi yana karantawa.
Murmurshi ya yi kawai azahiri ya ce, "zargina ya tabbata zama gaskiya."
Mai da masa ya yi cikin jakar ya rufe kafin ya fice.

Yana komawa ya same su a falo ya ce, "yanayin gidan fa ya yi ba wani armashi salam tunda dai an koshi muje mu ga abun da yarancen ke yi inda hali muyi joining."

Tashi suka yi duka suka fita ganin suna basketball yasa Khaleel cewa, "Yes daman anjima ba a gamu ba ina kewar basketball ball."

Fara yi suka yi duka cikin nishadi da Tsokanar juna ana yi khaleel na satan kallon Zahra , Farouk na kallo yana Dariya ba tare da sun sani ba.

Suna cikin yi Zahra da Zeeyter suka tafi suka daura abincin dare .

Suna cikin aiki Zahra sai tsaki take Zeeyter ta ce, "Mene ne wai sai tsaki kike tun dazu?"

Zahra ta ce, "takaici ne yake damuna wallahi tumbi yaƙi barina nayi na yi amman abu ba sauki ni kamar ma kara fitomun yake."

Zeeyter ta yi Murmurshi ta ce, "wannan ai ba abun damuwa bane ki samu ganyen mangoro (mango) guda ashirin da biyar ki wanke ki tafasa shi kina shan ruwan karamin kofi sau biyu arana safe da dare in sha Allah za ki ga canji cikin sati biyu."
Zahra ta ce, "na gode sosai in sha Allah kuwa zan gwada."

Suka ci gaba da aikinsu cikin nutsuwa.

suma ana kiran sallah suka daina dukan su suka yi sallah suka ci abinci.

FAROUK ya ce, "Gimbiyata tasa hannu a girkin yar guntuwa shiyasa ya kara armashi ina ga yau sai na fi kowa cin food dinan,yanzu na gano dalilin da yasa Haiydar yaki kyale Gimbiyata yana kwasar abinci kamar ba gobe."

Dariya suka yi duka deejerh tana, "ba dai santi ba aci a hankali Friend."

Bayan sun gama sai da suka yi sallar isha kafin suka kada su Noor daki suyi barci.

Bayan dukaninsu sunsa kayan barci sunyi addua xasu kwanta Anitha ta ce, "ku tsaya mu yi wannan addu'ar, duk wanda ya yi Allah yana kankare masa zunubansa haka Mom ta ce mun ranar *Astagfirulla-hal Azeem Al-lazi la ilaha il-la huwal hay-yul-Qayyum wa atubu ilaih*."

Tare suka yi dukaninsu suka nemawa iyayensu gafarar ubangiji sannan suka nemawa kan su kafin suka kwanta.


Farouk da Khaleel suna kokarin kwanciya dake Haiydar suna tare da Zeeyter, deejerh kuma da Zahra, Farouk ya ce, "nikam fa akwai maganar da nake so muyi."

Khaleel ya ce, "eheen ina ji."

"A cikinmu ba za asamu wanda zai auri Zahra ba kawai? In muka bari wani ya yi yunkuri tamkar munws kanmu asara ne gwanda ya kasance ayi abu cikinmu zai fi inganci."

Khaleel ya yi shiru.

Farouk ya ce, "in fa baka sonta ni ina sonta kuma a shirye nake da in aureta."

*FREYA*


*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ko wata ba, Saƙo ne kawai na ke son ya isa inda ya dace_

PAGE-37

_*Bismillahir-Rahmanir-Rahim*_

_Allahumma munzilal kitabi sari'al hisabi,ihzamil Ahzaba,Allahumm zumhum wazalzilhum🙏🏼_

TALLAH

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!... sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_

★★

_Buy your Mtn Data At Affordable Price_
MTN
500mb = 200
1GB = 300
2GB = 550
3GB = 850
4GB = 1150
5GB = 1450

Cal. Whatsapp 07046767662
Chat on Facebook 👇Maryam-Ashner Isma'l Usman
★★

Dafa kai khaleel ya yi da hannu saboda yadda yaji kan na sara masa.

Muryarsa ta fara rawa yama rasa me zai ce.

Farouk ya yi gyaran murya da gyara zama yana," Alright ga dukkan alamu ba ka da ra ayin tarayya da ita,ni kuma ba zan tursasa maka ba don haka ni kawai zan gwada sa ata in Allah yasa an dace in aureta, gudnyt na san barci ka ke ji, barin je falo in amsa video call din Mifyaz ga dukkan alamu yana so mu tattauna kan wani batune,byee."

Ya karasa maganar yana ficewa.

Dogon numfashi kawai Khaleel ya ja kafin ya ja bargo ya kwanta idonsa bude sam ya kasa barci,duk sonsa da barci amman ya gagara ban da tunani ba abun da yake.

Farouk na fita ya amsa kiran Mifyaz yana, "yane zaka addabeni cikin daren nan ne wai?"

Mifyaz ya ce , "Oh Sorry Abokina na san da baki agidan ne yasa banzo munyi magana ba, Shiyasa na ki.....

Sai ya dakata da maganar.

Ganin gilmawar Zahra ta shige kitchen tana, "dogon mutum ba a kwanta ba kenan."

Farouk ya ce, "eh guntuwa gadinku nake kin san mu nan sace guntayen mutane ake ana ƙonawa."

Da dariya Zahra ta fito ta nufi daki.

Farouk ya kalli Mifyaz yana, "lafiya kai kam? Daga ganin mace ka yi karamar suma?"

"Kai bar batun suma Ince dai ba matar aure ba ce,wallahi ta mun Don Allah ka hadani da ita." Mifyaz ya fada.

Dariya Farouk ya yi ya ce, "shikenan amman da sharadi nima ina sonta za mu yi game duk wanda ta aminta da shi, shikenan ka yarda? Duk da cewa dai ni ba wani son guntayen mata nake ba kawai tausaya mata zanyi."

Mifyaz ma ya yi dariya, "hakan ya mun gobe zan zo in ganta don Allah yanzu ma da ,da hali zuwa zanyi."

FAROUK ya ce, "kai dalla har wani zaƙewa kake akan guntuwar nan,ka kiyayeni fa,And ka san miye game dinnan zaiyi sosai zan sanar da ita komai kamar yadda kai ma zan ma bayani yanzu, a cikinmu akwai mai sonta ya kasa fitowa ya fada mata duk da cewa bata sani ba ita har yanzu,amman saboda ta aminta da kai zan sanar da ita cewa game zamuyi tsakanin ni da kai mu ga wanda zai ci, ina so mu tunzira shi yana kishi har ya kai ga ya fito ya bayyanar da abun da ke ransa."


Mifyaz ya ce, "but ni da da Gaske fa nake sonta Allah ta mun,amman tunda hakane ba matsala duk dayane in sha Allah zan yi duk abin da ya dace domin tabbatar da abun ya tafi kan tsari."

Farouk ya ce, "Yes abokin kirki na san ni da kai bama da matsala ai , na tabbata zamu samu lada tunda alkairi muke son haɗawa, ita kanta ba za ta san don shi muke ba,amman zata san cewa game ne tsakanin ni da kai kawai yadda zata sake jiki ayi komai yadda ya dace."

Daga nan suka tattauna sosai kafin suka yi sallama

Farouk na komawa ɗaki ya hau online cikin sa'a kuwa ya tarar da Zahra online.

Ya ce, "ke guntuwa damsn ko nemanki nake zamuyi magana."

"To dogo gani ai ko kaci Sa'a kuwa yanzu nake shirin kwanciya."

Nan Farouk ya fada mata komai kan game din da zasu da mifyaz.

Zahra ta ce, "to amman menene asalin dalilin yin game din?"

"Indai kin yarda da cewa ba zan taba abun da zai cutar da ke ba,ina tunanin ya ci ace kin yarda kawai kuma kin bada goyon baya dari bisa dari shine abun da nafi bukata kawai." Farouk ya fada

Zahra ta ce, "shikenan ba komai in sha Allah zan kokarta yadda kukeso mu kwana lafiya."

Dariya Farouk ya yi, "yawwa yar guntuwata shiyasa fa nake sonki,kinsan guntayen mutane kwai ladabi,in ma daga game mun sasanta kin sace zuciyata na daina ganin guntancinki ai sai kiyi wuff dani kawai ko ?"


Tsabar dariya Zahra ta ma kasa magana kwanciya kawai ta yi.

Washegari kuwa da sassafe sai ga mifyaz ko karyawa ba suyi ba.

Zahra da ZEEYTER na kitchen suna haɗa masu abinci.

Gaisuwa ya fara yi da su Haiydar da,da Khaleel bayan sun gama gaisawa Farouk ya ce, "wannan abokin takarata ne fa gun guntuwar cen tun da ya ganta ya birkice ya susuce ina ji kamar inyi Hakuri in bar masa amman da kyar zan iya fa."

Dariya Mifyaz ya yi yana, "in zaka hakura ma tun yanzu ka hakura."
Daidai da fitowar Zahra.
Ya kalleta yana, "ko ba haka ba Madam ni da ke ai mun fi dacewa."

Murmurshi Zahra ta yi ta ce, "ai kuwa kan don ni bana son dogon mutun kamar falwaya."



"Bright Eye wai kina inane? Am hungry oh oh please ki zo ki samun abincin nan na lura su fa ba jin yunwarnan suke ba."

Dariya suka sa dukan su Zeeyter ta tawo tana, "Sorry Sunshine gani nan."

Zuwa ta yi ta fara zuba masa abinci tana, "wai sai ku tsaya hira kun manta da food Master na kusa ba zai jurewa ganin abinci ba tare da ya ci ba."

Shi kam dai Haiydar tana sa masa ya fara ci ko kulasu bai yi ba.

Farouk ya ce, "tun da kin gama sallamar mijin naki to ga abokina mifyaz bazawarin guntuwar cen ku gaisa."

Zeeyter ta ce, "Ah ma sha Allah ka ce sabon angonmune barka da zuwa daga Sunshine sai kai kadai da yarana zan sawa abinci Sauran kowa ya yi ta kansa."

Zahra ta ce, 'ba matsala ni na sallami sauran mutanena ai."

Zahra ta zubawa Khaleel da Farouk suma sannan ta sa masu ita da Deejerh.

Tana gama zubawa Mifyaz ya dawo kusa da ita,sunata hira wasa da dariya kokarin sa mata abinci abaki ya yi

Khaleel na gani ya sunkuyar da kai yans dafa kirjin da ke yi masa zafi.

Ganin da gaske zai batan dai
Ya dago cikin zafin rai ya ce, "Wait.......


08103080717
*FREYA*


*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ko wata ba, Saƙo ne kawai na ke son ya isa inda ya dace_

PAGE-38

_*Bismillahir-Rahmanir-Rahim*_

_Allahumma munzilal kitabi sari'al hisabi,ihzamil Ahzaba,Allahumm zumhum wazalzilhum🙏🏼_

TALLAH

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!... sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_

★★

_Buy your Mtn Data At Affordable Price_
MTN
500mb = 200
1GB = 300
2GB = 550
3GB = 850
4GB = 1150
5GB = 1450

Cal. Whatsapp 07046767662
Chat on Facebook 👇Maryam-Ashner Isma'l Usman
★★

Sai ya wayance ya kalli su Noor.

"Noor ku bar irin wannan wasan ku ci abinci kunji."
Ya fada yana kawar da kai tare da ci gaba da cin nasa abincin.

Mifyaz da FAROUK suka hada ido tare da sakin murmurshi.
Kafin ya kawar da hanunsa ya fasa bawa zahra abincin.

Suna gama karyawa Farouk ya ce, "ina ga zamu dan fita mu duba wurare ko?"

Zeeyter ta ce, "Yes ni na zaƙu ma wallahi in ga yadda kauyen nan naku yake."

Farouk ya bude baki , "What? Akwai kauyen da ya kai niger ne? Habawa Gimbiyata kar ki sa in fara miki kallo irin na guntuwarcen."

Dariya Zahra ta yi," gaba dai gaba dai za aji kanku ai muna tare."

Tashi suka yi dukansu suka fita waje suna shirin hawa mota.

Mifyaz ya ce, "Madam kin san dai a mota zaki tafi ko? Ba zan iya bari ki hau wata motar ba gaskiya sai dai mu tafi tare."

Yana gama fada Zahra na dagowa suka hada ido da Khaleel.
Cikin sauri ya kawar da kansa kamar bai gani ba.

Mifyaz ya bude mata gaban mota yana, "Madam Bismillah."

Shiga ta yi kawai tana sakin Murmurshi , "As You wish Yallabai."

Ya rufe tare da zagayawa zai shiga gaban, da sauri Farouk ya tawo yana, "ka san dai nima ba zan iya rabuwa da yar Guntuwata ba,gwanda in shiga ko me za ace a fada gaba na kar in barku zuciyata ta buga,ko ba haka ba my baby guntuwa?"
Ya ƙarasa maganar yana kallon Zahra.

Murmurshi kawai ta yi tana,"kwarai nima gwanda ina ganinka a gefe ko ba komai kallonka na sani nishaɗi."

Shiga cikin motar Farouk ya yi suna kokarin tashi

Haiydar, da Zeeyter sun dauki yara suma.
Deejerh kuma tana jiran Khaleel ya zo su tafi,ganin kowacce mota na kokarin tashi ban da tasu deejerh ta kwallarawa Khaleel kira
Sai a lokacin hankalinsa ya dawo jikinsa domin ya ma manta shaf cewa tsayawa ya yi yana kare masu kallo.

Jikinsa a mace ya shiga motar suka tafi.

Sun yi yawo sosai cikin Malaysia da kewayenta duk wani waje babba na shakatawa da ya amsa sunansa sun je.
Bayan sun gama Haiydar ya fara complain yana jin yunwa.

Zeeyter ta ce, "eheen komai za ayi yanzu fa dole a dakata Sunshine na jin yunwa a cici mala'ikun tauna."

Haiydar ya kalleta, "nine acici mala'ikun tauna?"

"Eh mana to ko ni ce?"

Tashi ya yi yana kokarin damkota.

Da gudu ita ma ta tashi ta gudu tana dariya, "wasa fa nake na ce wasa nake."

Yana binta tana kara gudu har sai da ta fara gajiya.

Tsayuwa tayi tana rike kirji alamun yana masa ciwo tana kokarin kuka.

Da sauri Haiydar ya karasa yana, "mene ne ya faru? Kirjinki ko? Sannu bari muje asibiti sorry da baki gudu ba,ba zan biki ba ai sorry kinji kar kiyi kuka Please ."
Ya fada yana rungumeta.

Da sauri su khaleel suka karaso ganin Haiydar ya birkice suna tambayar me ya faru.

Haiydar ya ce, "kirjinta ne ke ciwo , Farouk Don Allah wani asibiti ne ya fi kusa anan muje ne?"

ZEEYTER ganin da gaske Haiydar ya tsaru dariya ta yi ta zare jikinta daga jikinsa tana gwalo tai gudu ts koma ta zauna .


Dukansu suka yi dariya,shi ko Haiydar tsaki ya yi,yana, "zan kamaki ne kuma sai nayi abun da nayi niya ko ba yanzu ba."

"Ba mutuwa zanyi in barka ba dai Sunshine, Smile tare zamu mutu fa."
Zeeyter ta fada.

Gefe yaje ya zauna yana, "karki kara kulani,ni kuzo muje inci abinci yunwa nake ji."

Rungumesa ta yi cikin Shagwaba tana fadin, "I'm Sorry Sunshine ba zan kara ba ka ji."

"Na ji shikenan."Haiydar ya fada.

Kara Shagwabe fuska ta yi, "Uhum tom ba ka yi Murmurshi ba."

Kara kawar ds kai ya yi

Cakulkulu ta shiga yi masa bai san lokacin da ya tinsire da dariya ba.

Farouk ya ce, "Gimbiyata kwa iya tashi muje a ci abincin ko sai kun gama soyayyar."

Da dariya suka tashi duka suka tafi.

Mifyaz yana naniƙe da Zahra shi ko ya damke mata hannu.

Khaleel na kallonsu sai ya saki tsaki ya kau d kai.

Suna zuwa cikin rawar jiki Zahra ta fara karfowa mifyaz abincin kasa jurewa Khaleel ya yi.
Ya ce, "wato yanzu ba a ma tamu ko? "


Zahra ta ce, "aa fa nina isa Friend? Barin karbo ma nakan yanzu in sha Allah."

Sun zauna duka suna ci Zeeyter ta ce gaskiya ina bukatar fashin baki akan wannan abincin NASI LEMAK."

Farouk ya ce, "My Yar Guntuwata ki mata bayani don na san kin san kin iya ."

Zahra ta ce,"
National dish of Malaysia,nasi means rice, and Lemak can be translated as rich or tasty,Rice is boiled in water with coconut milk,pandan leaves,and other spices,nasi Lemak is traditional served with sambal (chili sauce with shrimp paste,),fried dried anchovies and roasted peanuts."

"Ma sha Allah,Thank You So Much."

Suna gama cin abincin suka wuce
BATU CAVES, SELANGAR.

Batu Caves,Selangar yana da matattakala (steps) guda dari biyu da saba'in da biyu (272),yana dauke da mutum,mutumi daban daban tare da gumakai masu kimanin Shekara dari wanda suka kasance sadaukarwa ga kabilar hindu,a lokacin shagalin bikin al'adar ƙabilar mutane sama da dubu daya sukan ziyarci gurin domin shagalin

sai da suka gama zagayesa tas tare da duba duk wasu abubuwa na tarihi da ke wajen sannan suka zauna.

Zahra ta ce, "Dogon mutum ni kam wajen nan ya mun kyau Sosai gwanin sha'awa duk zuwanmu baka taɓa kawo mu ba wato sai da Zeeyter ta zo kana son ka birgeta,kar ka manta dai da mijinta ehee duk wannan rawar karfan."

Dariya Farouk ya yi, "Yoo kin san dai babu mai rabani da Gimbiyata, Haiydar haka ya ganmu kuma zai barmu,ina son ganin farincikinta sosai."

Dariya kawai Haiydar da Zeeyter suka yi ba su ce komai ba.

Zahra ta ce, "Umm to yanzu sai ka bawa gimbiyar taka takaitaccen tarihin Malaysia don ni kullum in kana badawa sai na tsinci wani abu da ban sani ba na karu da shi, abubuwan suna da yawa Dangane da kasar nan gaskiya."


Farouk ya ce, "an gama yar guntuwata ta ga kasa ba irin nasu ba daji, Gimbiyata ki saurara da kyau don guntuwar cen tasan abubuwa da dama kece yake farkon zuwa agunki
Maleziya kasa ce, da ke a yankin Kudu maso Gabashin Asiya. Tarayya ce wacce ke da jihohi guda 13. An raba ta zuwa gida biyu ta Tekun Kudancin China. Mainungiyar ta tana kan Tekun Malay. Tana fuskantar mashigar Malacca a gabar yamma da Tekun Kudancin Sin a gabar gabashinta. Daya bangaren kasar nan, wani lokaci ana kiransa da gabashin Maleziya, yana yankin arewacin tsibirin Borneo a Tekun Kudancin China. Kuala Lumpur babban birni ne a tsibirin Malay. Ba da daɗewa ba an maida da babban birnin tarayya zuwa Putrajaya, wani sabon birni da aka ƙera don keɓewa.

Kasar tana da kabilu da al'adu daban-daban, tare da yawancin mutane ƴan ƙabilar Malay ne, amma kuma akwai Sinawa da Indiyawa. Harshen hukuma shine Malay da aka rubuta a cikin haruffan Latin. Ingilishi yare ne sananne sannan kuma harshen hukuma a cikin jihar Sarawak tare da Malay. Ana amfani da Tamil da Sinanci sau da yawa. Akwai fiye da wasu harsuna 130 da ake magana da su a cikin Malaysia, tare da 94 a cikin harshen Borneo na Malaysia da kuma 40 a yankin teku. Addinin Islama shine addini na hukuma, amma waɗanda ba harshen Malay ba suna da ƴancin yin wasu addinai kin ji takaitaccen tarihin Malaysia."

"Ma sha Allah gaskiya na yarda da maganar Zahra akwai abubuwa na ban mamaki da sha'awa dangane da kasar nan." Zeeyter ta fada.

Zahra ta ce, "aikuwa

Please Login or Register in order to submit comment