Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tamkar suna tare suna ganin juna tun da.

★★Khaleel na zaune a office ba aiki ya kunna data ya bincike, kamar wasa ya ga wani comment na ALIYU HAIYDAR
"The Beautiful realization that every living being has a life as complex as your own,they experience,pain, suffering, happiness
And life just as vivid as you do."

Liking comments din ya yi, azahiri ya ce, "Yes wannan ya yi ." Nan take ya yi following dinsa , tare da nuna bayanai akansa.


*AFWAN DA GUNTUN PEJIN YAU NAYI ALKAWARI GA KUMA CIWON CIKI YA RIKENI🙏🏼*


*FREYA*


*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ko wata ba, Saƙo ne kawai na ke son ya isa inda ya dace_

PAGE-16

_*Bismillahir-Rahmanir-Rahim*_

_Allahumma munzilal kitabi sari'al hisabi,ihzamil Ahzaba,Allahumma zumhum wazalzilhum🙏🏼_

TALLAH

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!... sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_

★★

_Buy your Mtn Data At Affordable Price_
MTN
500mb = 200
1GB = 300
2GB = 550
3GB = 850
4GB = 1150
5GB = 1450

Cal. Whatsapp 07046767662
Chat on Facebook 👇Maryam-Ashner Isma'l Usman
★★

Bayanan Haiydar khaleel ya duba tas kafin ya fara yi masa magana har suka fara fahimtar juna.


★★Yau ne ranar da su Zahra zasu koma kotu domin a yanke Shari'a

Brss Danish ya zo domin tafiya da su tare, lokacin kuma Mr Imam har ya daukesu ya kai su kotun
Sam bai ji dadin hakan aransa ba,ya cije yatsa kawai ya shiga mota ya mai jin takaici.

Suna zuwa kotu kafin su shiga Zahra ta ce,"Husnah, domin mu rayu dole sai mun taka siratsi, domin mu yi nasara dole sai mun sha wuya, haka kuma domin fadan gaskiya dole sai mun cire tsoro, ki kwantar da hankalinki, ki furta dukkanin abubuwan da ke yawo a cikin ranki, ki sa aranki cewa ba rayuwarki za ki ceto ba,rayuwar yan uwanki mata ne,na yanzu dama wasu masu zuwa nan gaba,ya yin da kike furta duk wani abu da ya fito aranki ki maida idonki tamkar cikin duhu kike, babu mai ganinki kuma babu wanda kike gani,har sai kin kai ga matsaya, a lokacin da kika samu matsaya tabbas za ki fuskanci wani haske wanda bakya zaton cewa fitowar ki cikin duhu za ki iya arba da shi, haka kuma kar ki manta babu bawan da ya isa yi miki abun da Allah bai miki ba,kin jure rayuwa cikin wannan kuncin a baya yanzu da kike kokarin fitowa ne ba za ki jure ƙalubalen da ke bakin kofa ba,ki sa a zuciyarki za ki iya kin ji? Duk abun da kika sa arai za ki iya ka da ki karaya za ki iya kina tare da ni?"


Husnah ta girgiza kai, "In sha Allah zan iya, na sa araina Mah kuma zan iya indai ina tare da ke ba zan gagara komai ba da ikon Allah."


"Alright, Allah zaba mana mafi Alkairi." Zahra ta fada tana rike hanun Husnah suka shiga ciki.


Ko da aka fara shari'a babban buri da kudirin Mr Alhassan shi ne a kama Zahra da Husnah a kulle gidan yari,kamar yadda ya saba ada duk wanda ya nemi tona masa asiri sai yasa a kamasa da laifin cewa ya yi masa kazafi.

Husnah za ta fara jawabi kenan ta haɗa ido da shi, ji ta yi gabanta ya fadi nan take a zuciyarta ta furta , " *La'ilaha illa anta subhannakha inni kuntu minal zalimin* Tsintar ta yi da yi masa murmurshi ya yin da jawaban Zahra ke yawo a kunnenta.

Cikin kwarin gwiwa ta furta dukkanin abubuwan da ke faruwa har ma wanda bata fadawa Zahra ba kan cewa akwai abokanensa da suke zuwa yana sa su kwanta da su.

Nan take shi da lawyern sa suka musanta kan cewa sharri ne da kahe kawai suna son samu kudine agunsa kawai suka ga ba hanya shiyasa za su bata masa suna.

Nan take Brrst. Danish ya gabatar da hujjar sakamakon asibitin da aka bayar da Husnah da kuma dan sandan da ya sa hannu kafin adubata.

Sannan kuma ya gabatar da sauran yan matan da Mr Alhassan ya boye har ma da iyayensu.

(Xavier ya sa abokinsa na Indonesia ys yi zurfaffen bincike har sai da ya gano inda aka boye yaran ya fiddo da su ba tare da sanin Mr Alhassan )

Gaɓadaya Mr Alhassan da lawyernsa har ma da mutanensa sun shiga cikin rudu domin tunda suke ba a taba sanin sirrinsu kamar haka har a fitar ba.

Nan take Alkali ya yanke masa hukuncin zaman gidan yari tsawon shekara ashirin bisa cutar da rayuwar yara kanana mata ya yi da zambo cikin Aminci.

Kamar xaiyi karamar hauka Gaɓadaya ya fita a haiyacinsa ya birkice, su ko yara suna ganin iyayensu suka je suna rungumesu ,dukansu kuka suka fara ba ga iyayenba, ba ga yaran ba.

Don farinciki Zahra ma sai da tayi kwalla.
Karasowa gareta suka yi, suka durkusa suna godiya tare da fatan alkairi.

Murmurshi ta yi ta share hawayen da ke idanunta ta ce, "ni dai kumun alkawari kawai za ku lura da yaranku wannan shi ne babban burina,kuma ku sanya suyi karatu,ku inganta masu rayuwa yadda za ku yi Alfahari da juna nan gaba duka."

Wata babbar cikinsu ce ta ce, "In sha Allah Yar nan mun yi miki wannan alƙawarin ,ina ma ace su kasance kamarki ai da munii dadi."

Murmurshi Zahra ta kara yi, "bana so su zam kamar ni,sai dai su zama maifiyina,ko ninkina wanda kasa Gaɓadaya za su Alfahari da su, na Gode sosai,sannan na san za a iya samun matsala Mussamman stage din da suke a yanzu yaki ce masu dabi'ar da ya fara daurasu za ta iya masu wahala ko ta zam barazana a gare su,In sha Allah zan forming mana group da zanna zuwa duk karshen wata muna tattaunawa yadda komai zai tafi daidai,amman da taimakon ku iyayensu,kuna nuna masu cewa hakan baya nufin rayuwar farincikin su ta kare ko babu abun da za su iya,aa an rufe babin waccer rayuwar yanzu sabuwa za abude a ginata su rayu kamar kowa, zan kasance da ku in sha Allah aduk lokacin da ake bukata ina tare da ku ."

Albarka suka dunga sa mata kafin suka tafi, har Husnah ta tafi ta dawo ta ce."Na gode sosai Mah Allah kara haskaka rayuwarki, zan yi kewarki sosai ina sonki."

Rungumeta Zahra ta yi ta ce, "Nima ina sonki Husna ba mu rabu ba in sha Allah ana tare ai,babban alkawarin da nake so ki mun shine ku kula da kanki kuma ka da ki kara tunanin cewa rayuwarki ta lalace ki karfi kaddararki a hska kuma kiyi farinciki da ita komai zai yi dai-dai da ikon Allah."

Husnah ta ce, "nayi alkawari Mah In sha Allah na gode sosai."

Da haka suka rabu cikin kewar juna.

Brrst. Danish na zuwa ya ce, "Congratulations Mss Zahra ina fatan ba dai daga yau an bar gaisawa za a manta damu ba ko?"

Zahra ta ce, "Ah haba dai Aboki ai an fara zumunci kenan in sha Allah, words can't express how Happy am I wallah, ka taimakeni fiye da zatona ban da abun fada gareka sai fatan alkairi Allah biya ma dukkanin bukatunka na alkairi duniya da lahira."

"Ana tare In sha Allah,Amin nima na gode sosai,za mu yi waya akwai maganar da nake so mu yi." Brss Danish ya fada yana Murmurshi,suna hada ido da Mr Imam kuma ya bata rai tare da kawarma ya tafi cikin sauri.

Murmurshi Mr Imam ya bisa da shi kawai.

Yana tafiya Mr Imam ya budewa Zahra mota ta shiga tana, "Thank Sir."

Suna cikin tafiya ya ce, "Ma Sha Allah nima yanzu let me say congratulations Allah kara dimbin nasarori arayuwa , kin taimake su kuma kin ceci rayuwar wasu yaran masu tasowa nan gaba, na san kina da kokari wajen azkar amman ya kamata ki kara da abu guda,wato sadaka,komin kankantar abu ki ba da,,in yau nasara ce gobe ba mu san mene ne ba, ki kasance mai ba da sadaka,in kina da hali ki dunga sadakar dabino ki sai kamar mudu ko rabin mudu,ko kulla guda uku uku a leda kije wajen da akwai yara sosai ki ajiye kowa cikinsu yazo ya dauka da kansa,in sha Allah za ki ci gaba da ganin haske rayuwarki ta fanninkan da bakya zato bare tunani."


Zahra ta ce, "In sha Allah zan kokarta hakan na gode sosai Allah saka da alkairi kuma in sha Allah zan yi ."

Har sai da ya kaita restaurant ya ajeta kafin ya wuce.

Tana shiga Anushka da Anitha suka rungumeta Anushka na ,"welcome Momy."

Tsayawa kallonta Zahra tayi tana mamaki domin tunda take bata taba fita ta dawo Anushka ta zo ta rungumeta da gudu haka ba

Murmurshi ta yi ta ce, "Thank You, How Are you doing all?"

Cikin fara'a Anushka ta ce, "We Are Fine Momy."

"That's Good,Oya Mu je agaida Madam ko?" Zahra ta fada tana daukan Anitha tare da rike hannun Anushka.


★★Washegari
Noor na zuwa skul yanata Tsokanar Anjali amman sam ko juyowa ba ta yi ba

Har lokacin break ya yi, kowa ya fice ita bata fita ba.

Dask dinta ya karasa ya dago fuskarta yaga tana kuka

Goge mata hawayen ya fara yana, "What's Wrong Anjali? Stop crying please."

Cikin sheshshekar kuka ta ce, "I Forgot my chocolate,cake, biscuits with my drinks at home, i don't have anything for break,and am feeling hungry." Ta karasa maganar tana kara fashewa da kuka.

Share mata hawayen ya yi harda runguma yana shafa mata baya.

"Sorry Anjali, i will give you my own ,stop crying, alright?" Ya karasa maganar yana dauko jakarsa.

Gaɓadaya kayan break dinsa ya dire mata agaba,ya fara bata abaki tana dariya yana dariya.

Mika masa ita ta yi zata ba shi abaki.

Ya girgiza kai, "Aa ki ci kinji."

Ita ma ta girgiza kai.
Har sai da ya bude baki ta sa mai kafin ita ma ta ci gaba da ci.

Suka yi wasan su Sosai suna dariya.

Yana komawa gida bayan ya yi sallah ya kira Anushka.

Ta ce, "Assalamualaikum."

"Wassalam alaikum good Evening Anushka." Cewar Noor.

"Good Evening,How i are you?"

"Alhamdu Lillah And You?"

Anuska ta ce, "Nima Alhamdu Lillah."

"Yau wani wasa za mu yi kafin mu yi karatu?" Noor ya fada.

Anuska "Umm i have no idea."

Noor ya ce, "Oyaa close our eyes."

Nan suka yi wasan su Sosai tukun Noor ya ce yess na tuna yau addu'ar hawa abun hawa za mu karanta bari kiji yadda Dad ya koya mun.
" *Bismillahi Mujraha wamursaha inni Rabbi lagafurun rahim*, Kullum in zamu fita kan mu hau mota sai mun karanta ni da Dad ko ma dawowa za mu yi, ranar ma na kara koyawa Ammah (Granny) And you know what Anuskha?"

Ta girgiza kai.

Noor ya ce, "Ina son granny sosai, Dadyn Mom suna sona suma suna goyani suna mun wasa da yawa inna girma dukansu nima zan na goyasu, in basu abinci a baki kuma ina masu addu'a kullum inna yi sallah,ke da Anitha ma zan ce su soku ina kuma kuna sonsu."

"Eh mana sosai ma,muma muna sonsu,ina so ana goyani, kuma ni ban da Dad momy kadai ce dani, za ka bani aron dadyn ka?"Anuska ta fada cikin yanayin tausayi kamar za ta yi kuka.

Cikin sauri Noor ya ce, "Aa kar kiyi kuka,e ai dad dinmune harda ku.". Ya kara sa wajen Khaleel yana, "Dad ka cewa Anuska kai Dadyn su ne kaima ko?"

Murmurshi khaleel ya yi ya ce, "daman waya ce ni ba dad dinku ne ba? Am all urs oh oh, ina sonku yaran kirki."

Zahra na zaune tana jin Anushka ta ce bata da dady ta tsunduma duniyar tunani.


_(Aiki ya birkice mata ta kowanni ɓangare ga Anitha nata kuka,Adams ya shigo a fusace yana daukan Anushka tare da fadin, "ki dauko ta ita ma yanzu muje hospital akwai abun da zan yi, haka ta saba Anitha a baya suka nufi asibiti,suna zuwa aka ce abada yara, ba yadda ta iya dukanninsu suna kuka haka aka shiga dasu wani daki a asibitin, can kusan awanni uku sai ga shi an dawo da su likita na yiwa Adams da abokinsa Anash bayani, tsarin jini da kwayoyin halittar sa sam basu yi daidai dana su Anushka ba, atakaice komai na su na Adams ne,don haka ba za a iya amfani da komai nasu ba wajen cutar da ke domin Anash wato LUEKEMIA,Saboda bincike ya tabbatar da cewa yaran ba na Anash bane,na Adams ne, ba karamin takaici Adams ya yi ba, domin yasan bayan shi a wa inda suka fi kwanciya da Zahra Anash ne na biyu amman kuma yaran sun zama duka nasa,ason ransa ya so ace komai ya yi daidai abada yaran ko da zasu rasa Rayuwar su ne, shi dai ya samu kudi"_

Hawayen da Zahra taji Anitha na goge mata ne yasa ta dawo daga duniyar tunanin da ta fada.

Aranta ta ce, "Kuna da uba,tabbas kuna da uba,kuma ubanku na raye amman baya da zuciyar rikeku bare ya ja ku ajiki har ya kai ga ya goyaku,mahaifinku azzalumi ne mai zuciyar dalma, baya da tausayi kuma baya da adalci ban san yadda za ku ji aranar da zaku kasance gabansa..


*KWANA BIYU BA A COMMENT'S FA😢KO DAI YA GUNDURE KU NE ADAINA KAWAI?*

08103080717
*FREYA*


*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ko wata ba, Saƙo ne kawai na ke son ya isa inda ya dace_

PAGE-17

_*Bismillahir-Rahmanir-Rahim*_

_Allahumma munzilal kitabi sari'al hisabi,ihzamil Ahzaba,Allahumm zumhum wazalzilhum🙏🏼_

TALLAH

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!... sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_

★★

_Buy your Mtn Data At Affordable Price_
MTN
500mb = 200
1GB = 300
2GB = 550
3GB = 850
4GB = 1150
5GB = 1450

Cal. Whatsapp 07046767662
Chat on Facebook 👇Maryam-Ashner Isma'l Usman
★★

Anushka ta ce, "What Wrong Mom?"

Murmurshi Zahra ta yi azahiri ta ce, "Nothing Oh oh kun gama hira da Dad da Noor dinne?"

Anuska ta ce, "Yes Mom Dad ya ce zai zo ya daukemu,muyi wasa, ina son shi sosai Mom."

"Eheen good girl hakan ya mun,yanzu ki je ki aje tab din a huta ko?" Zahra ta fada.

Tashi Anuska ta yi tana, "Okay Mom."

Ci gaba da danna wayarta ta yi tana dube dube wannan posting ne ya ja mata hankali sosai.

KHADIJA (DEEJERH)

Rayuwa ta kan yi tsanani, Mussamman in ka ce za ka dauki komai a lokaci ɗaya,bi komai a sannu tare da sanyawa arai zan kai ga cin Nasara shine kawai haka kuma
A women can be in the worst position possible,And Only words you will hear from her is "I'll figure it out." and i promise you she wil find a way,she might have a trillion breakdown,but she will get through it,To All the women's your hard work does not go unnoticed keep striving.
Watarana mune masu ba da labarin da za aji har ma ayi mamakin ya muka kasance ? Ya muka jure duk wannan ƙalubalen har muka kai ga haka? I just love my self they way i am, am strong and i will be strong at anywhere i found my self in these world.

Zahra na gama karantawa ta yi Murmushi a azahiri kuma ta ce, "ba shakka tana daya daga cikin irin mutanen da Khaleel ke nema."
Reply ta mata kamar haka

"Women need the seat at the table,they need an invitation to seated there, and in some cases where, isn't available,well then you know what?the need to create their own table, because it isn't not enough simply talk about equality,One, must believe in it,and it isn't enough to simple believe in it,One, must work at it,let us work At it together, starting now."

A lokacin ta yi tagging din Khaleel, Haiydar da Farouk.

Suna zuwa suka fahimci inda Zahra ta dosa.
Following din deejerh suka yi duka, daga nan suka fara tattaunawa.

(Daga ranar 5stars ta hadu kuma ta fara aiki wanda ya bayyana acikin littafin Yel, kun san aikin kowa da fashion din kowa no need of more explanation)

Sun fara shirye-shirye da yadda duk tsare tsarensu zai kasance kuma sun samu fahimtar juna.

Kamar wasa Zahra har ta kammala Culinary school dinta har ta tafi Enternship, kasancewar tana da kwazo da kokari yasa mutumin ya riketa har ya fara biyanta, yana biyanta tana tara kudin har ta siya wani karamin gida dan daidai suka koma ita da Anushka da Anitha.

Daga nan ta ci gaba da tattalin kudinta, madam Zuby ta bata shawarar ita ma ta bude karamin restaurant gaban gidanta, tunda yanayin gunsu ba restaurant kuma ana da bukata sosai, hakan yasa ta dage ta ci gaba da tattala kudin, ta biyawa Anuska da Anitha school fees kuma ta ajiye na restaurant da kayan abinci, da kadan ta ci gaba da yin Donut ana yin over har ta fadada wajen.

★★Karshen wata za ta je ƙauye karo na kusan biyar ke nan tana zuwa su tattauna da su Husnah.

Bayan taje sun gaisa dukkanin yaran da iyayen suka zauna tamkar makaranta ta fara masu jawabin bada shawarwari.

"Ka da ku taɓa sawa aranku ba za ku iya rayuwa ba,in babu wani abu da ba ku zo da shi duniya ba, xuwan kowanni abu da dalili haka kuma tafiyarsa da dalili, gobenmu za mu kalla ba wai jiya da ta wuce ba,ta shiga sahun kaddararmu Amman mancewa da ita da fuskantar yau da gobe shi ne mafi cancanta a gare mu,mu so kanmu fiye da komai kada mu fifita son wani bayan kanmu,mu inganta kanmu kafin hango kowa,yayinda muka gyara rayuwar mu tai kyau daga lokacin muna da iko da karfin gyara rayuwar duk wanda muka ga bata kan daidai...
Zahra na cikin magana ta hango Aleesha ɗaya daga cikin yaran da Mr Alhassan ya ɓata, yanayinta ya sauya ta kasa zama mai kyau sam.

Katse maganar Zahra ta yi ta kira, tana zuwa ta lura tun daga yanayin tafiyarta ma ya canja da ka ganta za ka fuskanci akwai wata matsala.

Sallamar sauran Zahra tayi ta ce tana so su tattauna da Aleesha ne.

Haka kuwa a ka yi suka basu waje.

Suna tafiya Zahra ta karasa tana rike mata hannu.
"Kina da damuwa ko? Mene ne yake damunki? Me kike bukata?"

Kuka Aleesha ta fara ta kasa cewa komai.

Zahra na shafa mata baya ta ce, "ki daina kuka,ki fadamun na miki alkawari da ikon Allah zan yi kokarin magance matsalarki."

Cikin kuka Aleesha ta ce, "Mah na kasa jurewa,na kasa ba zan iya ba." Ta kara fashewa da kuka.

Tana fadan hakan Zahra ta fahimta cikin yanayin damuwa ta ce, "kin kasa ? Subhannallahi me kike yi kenan Aleesha? Yanzu na gama magana ka da ka taba sawa aranka akwai abun da za ba za ki iya ba,za ki iya da yardar Allah."

Wani tsumma ta dauko ta warware abun da ke ciki, ta ciro cocumber tana kuka ta ce, "Da shi nake amfani, Mah ya riga ya sabar mun,inna ji yanayin bukata in ba wai nasa wannan ba,bana taɓa jin dadi, na gagara hana kaina, wani lokacin na kanji tamkar in kashe kaina in huta,ba zan iya ci gaba da rayuwa haka ba."

Share mata hawaye Zahra ta yi,ta ce, "za ki iya, na san dole da wuya kauracewa hakan duk da cewar ni ban ba kaina damar fuskantar kalubale irin hakan ba,amman za ki iya Aleesha xa ki ci gaba da rayuwa a sake kamar kowa rike abunnan a hannunki ina so da kanki ki yanka tare da sawa aranki ba komai bane shi face abun vegetable kuma ba zai taba iya miki maganin kishinki ba."

Kamar yadda Zahra ta fada haka Aleesha ta yi tana kuka ta yanka.

"Yawwa saura abu na gaba, ka da ki dunga zama ba alwala a kowani lokaci ki kasance cikin tsarki, sannan ki kusanci karanta Alqur'ani, ki kauracewa duk wani abu dake nuna tsaraici, aduk lokacin da kika ji kina da bukata yi sauri ki kori shedan sannan ki kama ambaton Allah,ka da ki manta hakan ba zai taba samuwa ba har sai kinsa aranki cewa za kiyi yaƙi da wannan badakalar tun kafin ki yi nisa cikinta,duk da hakan zan nemo wato mafita amman ki fara amfani da wannan shawarwarin da na baki, in sha Allah xa a dace,ki kasance mai gwarin gwiwa da dauriya kan duk

Please Login or Register in order to submit comment