Join Our WhatsApp Group

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register

lokacin hutune yawanci kowanni skul ana hutu yasa Zahra yin tunanin amfani da wannan damar wajen hada kananun yara maza da mata kamar su Anitha da Anuskha ta masu Training din girki.

Bayan ta gama tunani sai kawai ta shiga group din take sanar da su.

Khaleel ya ce, "hakan kuma ya yi fa sosai wannan shawara ce babba mai zaman kanta zanso ace hakan ya kasance matuka."

"Inda hali ma kawai ina ganin abude karamar makarantar catring acikin gida na yara abun xai bada ma'ana sosai." Farouk ya fada

Haiydar ya ce, "Anya ba xan dawo Indonesia ayi class dinnan dani ba?"

Dariya suka yi duka deejerh ta ce, "ni dai komai aka yi ana samuna Videon ko kuma ana yin live muna gani."

Sun bata goyon baya sosai tare da kwarin gwiwar yin hakan wanda yasa ta jin dadi sosai aranta,nan take taje ta duba bangaren da zata iya amfani da shi sannan ta kira wa inda zasu tsara mata wajen.

Saukan sakonnin kudi taji ya fara bayyana a account dinta daga 5stars dukkaninsu kowa ya bata contribution.

Farinciki ya kara lullube Zahra matuka ta ma rasa ina zata kanta yadda ta samu 💯 support daga Friends dinta.

Cikin sati guda ta gama tsara komai, Farouk ya tsara mata Form online wanda kowa zai cike kyauta sai charges din da za a cire ta online din da shi za tai maintaining in case ko da wata bukata ta tashi.

Yara 20 ne adadin yadda ta bukata suka cike.

Nan take a ka fara class gwanin sha'awa domin dukkaninsu yaran deejerh ta masu designing rigar girki da tambarin 5stars sannan kowa da sunan shi a baya.

Wata guda suka yi ana yi har aka kammala tare da ba kowanni yaro certificate din kammalarsa, Noor sai murna ya iya girki inya koma shi zaina yiwa dad dinsa.

Aranar da suka kammala sai da gidajen rediyo d tv suka zo aka dauka tare da baxawa duniya domin abun ya tsaru bisa tsari da inganci.

Bayan sun gama lokacin taron su Zahra ya yi a Australia gidan Deejerh kowa zai tafi da danginsa ne agana na farko domin karawa juna sani.

Khaleel ya tafi da Mahaifiyarsa, haka ma Farouk ya tafi da mahaifiyarsa Haiydar ne shi daya sai Zahra da su Noor.

Noor da su Anitha suna ganin Khaleel da gudu suka je suka rugumesa suna murna.

Ya ce, "eheen ba kun manta dani ba? Mom ta baku abun manta mutane ko?"

Dukansu dariya suka yi kawai.

Bayan dukkaninsu sun huta Ammien FAROUK ta ke ma Zahra godiya.

"Na gode sosai 'Yata magani ya yi aiki matuka fiye da zatonmu , don da yanzu wannan taron ba za ayi dani ba amman taimakonki da taimakon Allah ga shi nan kamar bani ba."

Murmurshi zahra ta yi kawai ta ce, "ba komai Ammiey tunda kin ji sauki ai Alhamdu Lillah."

Noor da su Anitha sam sunki barin kankanni biyun nan su huta ban da tsalle-tsalle a jikinsu ba abun da suke.

Za ayi girkin dare Anuskha ta ce su zasu yi.

Zahra ta ce, "alright let's see, sannan ba wanda zai tamakeku da komai."

A tare Dukansu suka amsa da, "Yess."

Da gudu suka shiga kitchen din har suna rige rigen sanya rigunan girkinsu

Suna sawa Anuskha ta ce, "me kuke tunanin za mu yi ne ma? Kar ku manta babu taimakon Mom ba na kowa ina so muyi abun da xa su so kuma ya basu mamaki."

"Spinsh tortilla patatas."Anitha ta fada.

Noor ya ce, "Yess gud idea na san zasu so yanzu mu dibo dankali a mu fare mu biyu da Anitha ,ke kuma sai ki yanka albasa."

"Alright." Anuskha ta fada.

Suna gama fere dankalin suka yanka shi fale-fale sannan suka daura mangyada a huta ya soyu sama sama irin na dahuwa sannan suka kwashe.

Anuska ma ta soya albasarta da ta yanka fale fale sama sama sannan suka fasa kwai suka dagargaza dankalin suka zuba, suka sa albasar nan tare da kayan dandano ,da fasli duka waje guda suka juya sannan suka kara daura mangyada a huta.

Suna zuba mangyada suna soyawa har sai kowanni bangare ya yi brown kafin su kwashe.

Gidan ya baɗe da kamshi ta ko ina, haiydar na zaune sai rike ciki yake yana sambatu.

"Ni fa na gaji da jiran yaran nan kamshin nan xai sumar da ni janjin cikina sunata rawa suna kiran Food."

Zahra ta ce, "aiko ka ce da su yi sorry har su jira yau kam."

Haka ya yi hakuri yana shafa ciki ban da hadiyar yawu ba abun da yake suna gamawa kuwa fitowarsu shi ya fara tararsu da testing.

Rufe ido ya yi yana, "Can't believe this, da gaske yaran nan sukai wannan abun? Friend gaskiya ke ta Mussamman ce." Ya ƙarasa maganar yana kallon Zahra.

Dukansu ba wanda bai yabi abincinnan ba hatta su granny a karshe ma sai da Farouk ya masu kyauta dukkaninsu na kudi, haiydar kuwa mota ya yi alƙawarin yi masu ta mussaman, deejerh kuma kayayyaki za ta designing masu.

Sunji dadi sosai sai tsalle da murna kawai.

Washegari kuwa dukkaninsu bazama cikin Austaralia sukai yawo wajejen shakatawa.

Sunje Opera house Sydney, great barrier reef marine park-QueenSland,kata tjuta national park-Uluru,harbour bridge-sydney, da kuma Whitsunday island-queenisland.

Sun zaga kasar Sosai duk wani waje na ban sha'awa sunje sun huta kuma sun ji dadi mussaman iyayensu da suka jima basu je wata ƙasa ba, sunyi hutu sosai anyi wasa anyi dariya har kowa ya watse Khaleel ya tafi da Noor Zahra ma ta dawo da yaranta.

Washegarin dawowarsu da sassafe taji ana mata nocking din kofa cike da mamaki ta je budewa ganin waye.

Cikin mamaki tsaya cak ta ma rasa abun furtawa bakinta na rawa ta ce, "....
*FREYA*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ko wata ba, Saƙo ne kawai na ke son ya isa inda ya dace_

PAGE-32

_*Bismillahir-Rahmanir-Rahim*_

_Allahumma munzilal kitabi sari'al hisabi,ihzamil Ahzaba,Allahumma zumhum wazalzilhum🙏🏼_

TALLAH

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!... sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_

★★

_Buy your Mtn Data At Affordable Price_
MTN
500mb = 200
1GB = 300
2GB = 550
3GB = 850
4GB = 1150
5GB = 1450

Cal. Whatsapp 07046767662
Chat on Facebook 👇Maryam-Ashner Isma'l Usman
★★

"mene ne yake faruwa Suhana?."

Ganin Suhana tsaye da yan sanda.

Murya na rawa ta ce, "Mah An samu matsalar abinci ne a restaurant da bakya nan,ansa guba cikin abincin duka wanda ya yi sanadiyar sumar da wasu, wasu kuma suka dunga amai da gudawa."

Cikin tsawa Dan sandan ya katse Suhana yana, "Ki yi mana shiru,dukanku muje can kwa yi bayani."

Suka sanyawa Zahra ankwa suka tafi da ita.

Gaɓadaya Zahra ta rude ta fara fita hayyacinta ban da Innallillahi wa inna illar raji'un ba abun da take iyawa furtawa.

Suna zuwa station aka fara yiwa Zahra bayani.

"An kama gidan abinciki hannu biyu da sanyawa mutane guba a abinci wacce da yawansu da kyar aka ceci rayuwarsu, shin daman kuna jan al'umma ne don ku cutar da su ?"

Hawaye ne kawai ya fara zubowa Zahra ba tare da ta ankare ba cikin kuka ta ce, "wallahi sam a zuciyata bana da niyar cutar da kowa bana da niyar ha'intar kowa atakaice ma ban san yadda akai hakan ya faru ba dawowata daga Australia kenan jiya."

"Za ma kiyi bayani ,yayin da hukunci ya tabbata akanki,kina da damar kiran lawyern ki a yanzu domin an mika ki kara kotu,duk da cewa da zan baki shawara ma da mika kafa kikai ba sai kin wahalar da kanki da kudinki ba, domin rufe wannan gidan abincin ya zam dole tare hukunci mai tsanani."

Zahra ba ta ce da shi komai ba a lokacin.
Sai da suka kulleta cikin cell ta dunga addu'a har zuciyarta ta fara sanyi kafin ta ari waya agunsu.

Khaleel ta fara kira ta sanarwa sannan ta kira Brss Danish shi ma ta masa bayanin komai.

Tuni Hankalun 5stars ya tashi ban da waya tsakanin juna suna tattaunawa ba abun da suke har sai da suka kira Brss Danish da kansu suka kara yin magana ,duk da hakan ma kowa ta bangarensa yanata faman kokarin yadda za a bullowa abun duk da cewa ba kasa daya suke ba.

Zahra ko na zaune a cell ta tuna da wata addu'ar da Khaleel ya taba bata wacce mutum ke yi in yana cikin tsananin bukata kuma Allah ya biya masa bukatarsa cikin ikonsa.
Suratul Yasin ta fara karantawa duk inda taje MUBIN sai ta tsaya ta karanta AYATUL KURSIYU ta roki Allah ya fitar da ita cikin wannan kangin kafin ta ci gaba, har ta kammala karanta surar tana yi tana kuka.

Haka Zahra da Suhana suka kwana awajen nan cikin kunci.
Zahra kam ko rintsawa ba tai ba har garin Allah ya waye sallah kawai take tana kaiwa ubangijinta kukanta.

Da sassafe aka kawo mata waya kan Khaleel zai yi magana da ita.

Tana karfa sai ta ji Farouk ne.

Sai da suka gaisa kafin ya ce, "ga dukkan alamu yanayi ya nuna kin shiga damuwa sosai dangane da lamarin nan,nasan cewa dole hakan amman kasancewar ki musulma ya zam dole a gareki da ki karbi wannan jarabawar hannu biyu har ki cinyeta, dukkanninmu mun damu matuka amman babbar damuwarmu bata zarce ki kwantar da hankali ba ki ci gaba da addu'a, kuma ki tuna cewa Ubangiji ya kan gwada bayinsa ne ta hanyoyi da dama domin bayyanar da imaninsu a gare shi, yau in munyi dariya watakila gobe kuka za muyi rayuwar kenan ,kuma cikar mu'mini ke sanya Ubangiji jarabtarshi komai zai yi daidai kuma zai wuce muddin muna numfashi da ikon Allah kina karanta wannan adduar in sha Allah komai zai zo da sauki *Allahumma inna na uxubikha min jahadil bala'i wa darakil shaka'i wa su'il kada'i wa shamatatil a'ada'i.* Addu'a ce mai karfi duk musibar da ke fuskantar mutum inya luzumci yi Allah ya kan saukaka masa ko ya kawar ma cikin sauki da ikon sa"

Zahra ta ce, "In sha Allah na gode sosai Friend."

"Ahas My Yar Guntuwata kar kiji komai da kin fito zan nema miki guntu irinki in aura miki." Cewar FAROUK.

Zahra bata san sanda dariya ta subuce mata ba tana, "Allahumma Yahadikha Friend."

Suna gamawa sai ga shi an kara dawowa Khaleel na kira.

Shima suna gaisawa ya fara cewa.
"Jin ki nake wata iri kamar ba zahran da na sani ba,kar ki manta wannan ba shine kalubale na farko rayuwar ki ba,kuma bama tsammanin shi ne ƙarshe ina so ki tuna what ever you go through,what ever you face,how ever you feel, just remember, your Destined for increase, why ? god is with,more then that God is in you and god is for you, addu'o'i kar kiyi wasa da su kuma muma muna yi, komai zaiyi daidai."

Ya mata nasiha sosai kafin suka yi sallama ya katse kiran.

Madam zuby ce taje ta dauko su Anitha ta dawo da su gidanta.

Su Zahra kuwa an shiga kotu abun da aka fara na farko shine bada takardar dakatar da girki a restaurant dinta tare tarar da biyan makuden kudade wajen nemawa wa inda abincinsu ya illata lafiya.

Sannan aka ce a maidata ofishin yan sanda domin za a cigaba da bincike kafin a koma zama na gaba wanda ake tunanin akwai yuhuwar yanke mata hukunci mai tsanani muddin ba asamu kwakkwarar hujjar da zata wanketa ba.

Ba abun da ya dagawa Zahra hankali irin kudaden da aka ambata domin bata ma hanyar da zata samo rabinsu ba.

Nan take awajen ta fadi sumammiya.

*COMMENTS DINKU YA YI LOW INFACT MA BAKWA YI🌝🌝HAKA ZA MU YI DA KU🤔*
*FREYA*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ko wata ba, Saƙo ne kawai na ke son ya isa inda ya dace_

PAGE-33/34

_*Bismillahir-Rahmanir-Rahim*_

_Allahumma munzilal kitabi sari'al hisabi,ihzamil Ahzaba,Allahumm zumhum wazalzilhum🙏🏼_

TALLAH

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!... sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_

★★

_Buy your Mtn Data At Affordable Price_
MTN
500mb = 200
1GB = 300
2GB = 550
3GB = 850
4GB = 1150
5GB = 1450

Cal. Whatsapp 07046767662
Chat on Facebook 👇Maryam-Ashner Isma'l Usman
★★

Haka aka dauketa suka nufi asibiti da ta farfaɗo kuwa kai tsaye suka koma ofishin yan sanda.

Brss Danish kuwa ya sanar da su khaleel duk yadda lamarin kotu ya kaya, hakan yasa nan take suka tura masa kudin da aka ci Zahra taran domin ya biya ba tare da ta sani ba.

An ci gaba da fafutukar neman mafitar da za a kare Zahra a zama na gaba.

Ita kuwa ta kasa jure yanayin da take ciki kallo daya za amata tabbatar da cewa tana cikin tashin hankali magana ta fara yi mata wuya sai dai bin mutane da ido kawai, addu'a kuwa duk wacce tazo bakinta yi take ba dare ba rana duk ta susuce.

Rana ta yi,kuma Lokaci ya yi an koma kotu.

Lawyern gwamnati ne ya tabbatar da wani babban laifin ga zahra tun kafin a yi nisa.

Sheda ya nuna na miyagun kwayoyi wanda ya tabbatar da cewa a restaurant dinta aka samu tare da zargin cewa tana safarar miyagun kwayoyin.

Kanta taji yana sarawa ,idanunta na rufewa, kafafunta na kokarin kasa rike ta.

Dafa kan tayi tare da fadin, "Innallillahi wa inna illar raji'un, Allahumma ajirni minal musibati wa akrijni khairan minha."

Kasancewar harda yan sandan da suka tabbatar da hakan tsakanin Zahra da brss Danish ba mai iya jayayya da lamarin.

Hawayene kawai yake zuba daga idanunta ba tare da ta iya motsawa ko furta wani abu ba.
Azuciya take tambayar kanta , "shin wa na aikata wa laifi mai girman da yake son ramawa ta hanyar ruguza mun rayuwa? Shin me na aikata? Me na tarewa wani? Allah na tuba ka yafe ni,ka fitar da ni cikin wannan tsananin , Rabbie ka dubeni ka yafe mun."

Haka aka tashi a kotun ba nasara bare alamarta murna ta koma ciki,ana zaton sassauci sai ya kara tsananta hankulan 5stars ya tashi sosai matuka sun kasa zaune sun kasa tsaye communication suke kawai ta kowacce hanya don neman yadda zasu bullowa lamarin.

An kwashe wata guda ana bincike tare da kilace Zahra.
Gaɓadaya ta canja yanayinta ya yi muni ta shiga cikin tashin hankali da kyar Khaleel ya samu Magana da minister domn neman belinta ta koma gidanta sai a cigaba da binciken mudin aka tabbatar da ta aikata duk abun da ake zargi sai ayanke mata hukunci daidai nata.

An aminta kuma an sa hannu ta koma gida amman zata ci gaba da zuwa kotu kuma babu batun bude wajen abincinta.

Haka ta koma gida,su Anitha suna ganinta ban da kuka ba abun da suke, danne damuwarta tayi domin karfafa masu har sai da suka sake suka daina kukan.

Dawowarta da kwana uku sai ga Adams yazo.
Anitha ce ta bude masa kofa.
Tana kallonsa cike da mamaki.
Ya yi wani munafukin murmurshi yana, "Aniy ba za ki gaida Dadynki ba?"

Durkusawa ta yi kawai ta ce, " good Morning."

Ya amsa yana dagata tare da shafa kanta, "ina mom dinku?"

"Tana ciki." Cewar Anitha.

Adams ya ce, "thats good to ki karasa dani gunta ko ?

Anitha ce ta rakasa har falon,cikin mamaki Zahra ta kallesa, ya sake mata murmurshi tare da neman wajen zama.

Anuskha na gaishesa suka fita da Anitha kamar yadda Zahra ta sabar masu da bayan gaida baki suna basu waje su tafi wasa ko dakinsu.

Yana ganin fitarsu ya tashi tare da matsawa daf da Zahra, kokarin sanya hanunsa ajikinta zaiyi tai saurin kawarwa tana, "kar ka kuskura."

Dariya ya yi, ya ce, "kin ga yadda kika zama kuwa? Abar tausayi gabadaya kin rame kin kara muni gaskiya kin sha wuya, ashe abun da ya faru kenan? Na ce ya kamata inzo jaje kuma in ga yarana, da ace tun farko baki biyewa wa incen gardawan kina karuwanci ba da tuni mun koma aurenmu na gyara miki rayuwa cikin jin dadi,amman yanzu ai kin ga sakayya ko?."

Dariya ya sheƙe kafin ya ci gaba, "banji dadi ba ta wani bangaren amman wani ɓangaren kam na ji dadi fa."

Murmurshi Zahra ta yi ta ce, "Ma sha Allah maddalla na gode da jaje And in ka manta ni bari in tuna ma,cikar bawa ne Ubangiji ya jarabceshi ta inda yaso kuma a lokacin da ya so sannan ya tseratar da shi, jarabawa na kan kowa ba,bata tsaya iya kaina ba har kai da ma duk wani bawa da ke cikin Duniya,duk da cewa har yanzu ina cikin tawa jarabtar amman zan iya cewa tayi kyau ka jira taka watakila sai ka rasa gane kai wane ne,na karbi jarabawata hannu biyu kuma ban fasa godewa Ubangijina ba yanzu,dazu,anjima har ma gobe in Allah ya nufeni da numfashi Alhamdu Lillah, zaka iya tafiya tunda ka mun jaje kuma ka ga yaranka Allah saka da alkairi."

Tana gama fada ta shige ciki ta bar shi Tsaye.

Mamakine ya lullube Adams jin furuncin Zahra,cije yatsa ya yi Azahiri ya furta, "Ah lallai wannan da sauranta,tabbas zan yi maganinta sai na rufe bakin nan ya kasa furta komai."

Rai abace ya bar gidan.

Zahra na gidanta an ci gaba da bincike kuma ana zuwa kotu.
Sunje kotu ranar da Alkali ya ce muddin ba asamu mafita ba za a yanke hukunci.
Abun mamaki sai ga Brss Danish da Xavier sunzo da wani matashi yazo yana kuka yana bayanin cewa shi aka sanya ya bata abinci da guba.
Kuma miyagun kwayoyin ma shi ne yaje ya zuba amman babbar Matsalar ita ce shi kansa bai taba ganin fuskar wanda ke bashi aikin ba ta waya suke komai ya biyasa shi kuma ya yi aikin.

Aranar aka wanke Zahra tsaf shi ko aka kama wannan saurayin kan cewa har sai an binciko wanda ya sanya shi.

Kasancewar lamari ya yi tsamari ne Khaleel ya bukaci da Xavier ya je Indonesia domin tsananta bincike kuma anyi sa a ya an wanke Zahra illa wanda ya sanya abun da za a cigaba da bincika.

A Take lokacin aka bata damar ci gaba da aiki a restaurant dinta tare da yin duk wani abu da ta saba.

2YEARS LETTER
Malaysia
*FREYA*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ko wata ba, Saƙo ne kawai na ke son ya isa inda ya dace_

PAGE-35/36

_*Bismillahir-Rahmanir-Rahim*_

_Allahumma munzilal kitabi sari'al hisabi,ihzamil Ahzaba,Allahumma zumhum wazalzilhum🙏🏼_

TALLAH

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!... sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_

★★

_Buy your Mtn Data At Affordable Price_
MTN
500mb = 200
1GB = 300
2GB =

Please Login or Register in order to submit comment