Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

= 1450

Cal. Whatsapp 07046767662
Chat on Facebook 👇Maryam-Ashner Isma'l Usman
★★

Noor ne tsaye ya baɗe fuska da farar hoda suna wasa yana Tsokanar su Anitha adole shi dodo.

Dukanninsu kallon juna suka yi can kuma suka sa dariya Zahra ta ce, "Allahummah Yahadikhu."

Da Ameen suka amsa sannan suma suka yi dariya a lokacin tare da gaishe da iyayen nasu.

Zahra ce ta koma kitchen domin hada masu breakfast Haiydar ya bita, Khaleel kuwa komawa ya yi barci.
Farouk kuma da Deejerh suka zauna suna hira.

Suna shiga Zahra ta kalli Haiydar kafin ta ce, "Friend yanzu me kake ganin zamuyi ba tare da bata lokaci ba kuma yara basu fara jin yunwa ba."

Murmurshi Haiydar ya yi ya ce, "eheen ina da shawara me zai hana ayi bread roll, kin san ni ds bread ba wasa mussaman ma yadda ake sarrafasa ta hanyoyi da dama abun da matukar birgeni."

Dariya Zahra ta yi kafin ta ce, " alright ka kawo shawara muyi kawai yanzu ka taimaka mun ka yanka naman cen kanana kanana ni kuma bara in gyara greenbeans da red pepper din cen."

Tare suka fara aikin bayan sun soya naman suka ajiyesa waje guda su greenbeans din.

Bread mai yanka ta dauko kowanni daya sai su xuba nama Greenbeans da green pepper sannan suyi rolling da stick ta yadda ba zai fito ba sai da suka gama duka sannan suka kwaba madara da kwai

Suka daura mangyada a wuta in suka sa bread din acikin ruwan kwai da madaran sai su ciro su sa a mangyada ya soyu sai ya canja kala a kwashe har suka gama.

Sauran bread din suka dauko suka sa chocolate a tsakiya sannan suka dauko wani suka rufe daidai inda suka sa chocolate din sukai cutting dinsa rawun da plastic cup suka sa acikin ruwan kai sannan sukai toasting dinsa, sauran gefe gefen biredin kuma suka sa shi a toster suka yanka sousage kananu da sauran greenbeans da red pepper suka zuba a tsakiyan da ba komai da gudan kwai wanda ba a kada ba suka rufe toster din har ya yi.

Sai da suka gama hada abubuwa ukun nan cir da Bread.

Haiydar ya hada masu tea ita kuma Zahra ta hada juice duk mai son tea ya sha mai son juice yasha.


Suna gamawa tare suka jera komai kan daining kafin Zahra taje ta kira kowa don shi Haiydar tuni ya zauna ya fara break.

Khaleel na zuwa ya ce,"Mutumin ba wasa ko jiranmu ba za ayi ba?"

"Kasan dai bana wasa da food ahto kai kana cen kanata barci ina zan tsaya cikina ya fara kuka ƙuƙu ." Ya fada yana kai bread roll baki.

Dariya suka yi duka deejerh na ,"wa ya ga ƙuƙu."

Ci suke suna santi dukanninsu.

Noor ya ce, "ina sonki Mom kin iya girki sosai zaki zauna anan ke da su Aniy ko?"

Murmurshi Zahra ta yi kawai.

Anitha ta ce, "Yes Mom muna muna son nan mu zauna kin ji."

Zahra ba ta ce komai sai Khaleel ne ya katse maganar da "alright yanzu dai kowa ya ci abincinsa."

Bayan sun gama karin kummalo an gyara gidan dukkanin kowa yasa kaya Farouk ya ce, "ni dai kun san da lafiyata ba zan zauna waje ɗaya ba basar ya kamani in zama guntu kamar wa'e mun san komai fa basir ne ya ke sa wasu xama guntaye."


Dariya zahra ta yi tana, "kai dai fada abun da ke damunka mu nema ma magani kawai ba wani kame kame ehee."

"Ai kuwa dai na lura baya zama da kyau fa." Deejerh ta fada.

Khaleel da Haiydar me zasu yi kuwa ban da dariya.
Farouk shima dariyar ya yi yana, "ina ga kaf cikinku ba mai lafiyata eher nidai yanzu a shirya yarancen mu fita mu ga gari gari ya ganmu abun da nake bukata kenan."

Khalil ya ce, "Nice Idea nima abun da nake ta tunani kenan ya kamata muje da ku ku ga gari kam su Madam yan kauyen Indonesia anzo birni."


"Ah ah ni fa ban gane ba kundi kuna so ku takurawa friend dina to ahir dinku." Haiydar ya fada.

Zahra ta ce, "kar ka damu dasu duk zan rama ne ai."

Zuwa Zahra tai ta shirya Su Noor kafin duka suka fito .

Zasu fita kenan Noor ya tsaya ,"Wait.. sai ya yi shiru duka suka tsaya suna kallonshi kafin ya ce, " Adduar fita daga gida."

Murmurshi duka suka yi suna haɗa baki tare da fadin.
*Bismillahi tawakkaltu alallah wala haula wala kuwwata illa billah*
Suna kammala fada Noor ya kara cewa, "Allah ya kai mu lafiya mu dawo lafiya."

Nan take suka dau hanya sun zagaya England da kewayenta
Sunje LEICESTER SQAURE sannan suka je MUSEUM daga nan suka wuce TOWER OF LONDON sun yi yawo sosai sun zagaya sun ci sun koshi Mussamman Haiydar komai ya gani sai ya ci, sun ga abun ban al'ajabi da mamaki sunyi nishadi sunyi wasa da dariya sai da suka kwana uku suna yawo.
Sai arana na ukun suka koma gida.


Tsabar gajiya suna komawa su Noor suka nufi dakinsu suna yin sallah suka kwanta.

Su kuwa suna zaune a falo kamar wasa suka ji but anyi tusa Haiydar ya dago yana rarraba idanu dukansu suka fiske.

Can da ya kara wata bu bu but mai shegen kara da wari basu san sanda duka suka watse a falon ba suna dariya.

Shi ko cikinsa muradawa ya yi aguje ya nufi toilet ranar kusan kwana Haiydar ya yi yana shiga toilet ban da dariya mai Farouk da Deejerh za su yi.

Gaɓadaya jikin Haiydar ya sake ya gama jigata.

Khalil ya ce, "Gaba ka kuma yo ba dole ba kwana uku duk inda muka je sai kaci abinci over komai ka gani sai kaci ai dole cikinka ya rikice."


Zahra ta ce, "dame zai ji haba ku barsa mana,ko da baici abincin nan haka ba Allah ya ƙaddara dole sai ya yi ciwo."

Farouk ya ce, "to su guntaye an fara jawabi bari inje in kwanta nikam ku ci gaba da jinya inya mutu kuma kwa tadani."
Ya karasa maganar da salon tsokana.

Dariya suka yi kawai.
Khaleel ya kira Doctor aka zo aka duba Haiydar tare da bashi magani da yan allurai kafin ya samu ya yi barci.

Da safe kuwa suna tashi ya sha tsokana .

Ranar shiryawa suka yi suka nufi gidan su khaleel domin gaida mominsa da kuma ajiye su Noor saboda xasu na fita wajen kammala abubuwan da ya kawo su.

Suna zuwa Noor ya rugumeta yana, "Granny kin ga Aniy da Anuskha munzo kuma anan zamu zauna."

Murmurshi ta yi tana, "barkanku da zuwa." Ta karasa maganar tare da rungumarsu.

Su khaleel ne suka shigo suna gaidata tare da yi mata bayanin kowa.

Taji dadin ganin su sosai ban da albarka ba abun da take shi masu.
Zahra da kanta ta shiga kitchen ta masu girki tamkar sun saba ko ince yara sunje gun mahaifiyarsu haka suka kasance.
Sai can dare suka bar gidan .

Noor da su Anuskha harda yi masu byeebyee su zasu zauna gun grandma.

Wasa suka dunga yi suna dariya suka rufe wa grany ido da kyalle suna xagaya gidan.
Anuska da Anitha sai dariya kawai da Farinciki na musamman.


Sukuwa suna komawa gida Khaleel ya ce, "Gudnyt oll don nasan gobe ba samu zan inyi barci yadda raina ke so ba Gwanda inyi amfani da wannan damar."

Deejerh ma ta ce, "Niko ina da sauran aiki a system ma inaso in karasa in tura masu byee."

Saura Haiydar Farouk da Zahra ne kawai zaune a falon.

Farouk ya lura Zahra yau sam bata da walwala hakan ya shi tabata yana cewa, "Reminder....
You are strong like FREYA. You Being Going through alot ,
And you still standing strong, What Ever You Thinking you have surpass that because you are phenominal Woman, you are enough to stand as an army to face what ever difficulties in your life so stay strong."

Yana gama fada ya tashi ya tafi.

Binsa da kallo tayi kawai tare da sakin Murmurshi ita ma ta nufi daki.
*FREYA*


*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ko wata ba, Saƙo ne kawai na ke son ya isa inda ya dace_

PAGE-27

_*Bismillahir-Rahmanir-Rahim*_

_Allahumma munzilal kitabi sari'al hisabi,ihzamil Ahzaba,Allahumma zumhum wazalzilhum🙏🏼_

TALLAH

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!... sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_

★★

_Buy your Mtn Data At Affordable Price_
MTN
500mb = 200
1GB = 300
2GB = 550
3GB = 850
4GB = 1150
5GB = 1450

Cal. Whatsapp 07046767662
Chat on Facebook 👇Maryam-Ashner Isma'l Usman
★★



Su Noor suna zaune adakin granny suna wasa, kallon su ta yi ta ce, "Dare ya yi maza aje akwanta kar amanta ayi addu'a ko?"

Dukansu suka amsa da Yes granny.

Har sun tafi ta kira su ta ce, "kau zauna bari in baku wannan adduar kuna yi Manzo Allah SAW ya ce, "duk wanda ya karanta wannan adduar kafin kwanciya barci Allah zai yafe masa zunubansa gabadaya *La ila ha illah wahdahu la sharikalahu lahul mulƙu wa lahul hamdu wa huwa ala kullu sha'in kaddir, la haula wala kuwwata illa billahil aliyul azim, Subhannallah wal hamdullilah wala ila ha illah wal lahu Akbar*"


Sai da tayi suka maimaita ta kuma tabbaatar ya zauna abakinsu kafin suka tafi.

Washegari

Da asuba suna tashi suka ki komawa barci.

Dakin Granny suka shiga a laɓe tana barci suka fente mata fuska da jan fenti da baki Gaɓadaya kaminta ya buya ban da dariya ba abun da suke a hankali suka tafi falo suka ci gaba da wasa.

Can kuwa tana fitowa suna zaune bata lura da fuskata ba dukansu suka yi raxanar gulma harda gudu suna , "Granny fuskarki fuskarki."

Juyawa tai ta kalli kanta cikin glass da ta ganta nan take ta shiga cikin wani firgice bata san lokacin da ta sake wata kara da fitsari nan take ba

Da gudu mai aikinta ta tawo su Noor kuwa dawowa sukai suna dariya harda rike ciki.

Anitha ta ce, "Fenti ne fa kawai muka miki."

Gaɓadaya jikinta ya sake kallonsu kawai ta tsaya yi sai mai aikinta ne ta tallafa mata suka je toilet ta wanke mata jiki da fuskar.

Tun da suka je gidan nan basu barta ta huta ba daga wannan sai wancen.


Bangaren su Khaleel kuwa.
Shiga aikin su suka yi kai tsaye nan take babu wani batu kowa cikinsu ya bada contributing dinsa an hada an fiddawa kowa office dinsa hakan yasa suka kudirci cewa a lokacin zasu fidda form din employment .
Nan take Farouk ya tsara komai dake wannan ma na sahun bangaransa.


Suna fitarwa kuwa aka samu masu cikewa sosai fiye da zato.

A list din suka samo wani karamin Company mai suna CREATIVE TILE COMPANY da suka turo bayanan su kuma a England suke abun da ya fara jan hankalinsu ga companin abu biyune na ɗaya yadda suke kokarin magance matsalar Air pollution na biyu kuma TILES din su na da kyau da arha hakan yasa suka yanke hukunci fara tallafin su na farko ga Companin.

Tura masu sakon neman suka yi tare da basu lokacin zuwa.

Sun shirya komai illa zuwansu da suke jira
Su uku kuwa suka zo.

Zack,Raj da Jesmin.

Abun mamakin shi ne dukkaninsu matasa ne babu wani mai shekaru mussaman macen cikin su Jesmin.

Gabatar da kan su suka fara wa juna sannan Deejerh ta basu damar bada bayani dangane da company.

Zack ne ya ce, "CREATIVE TILE COMPANY ,We harvest air pollution as a resource to buil tiles for design and architecture


We build tiles out of air pollution, we are team of architecture engineers and designers.

We're working at the intersection of architecture, craft and technology.

We are all trying to see how we can solve this massive issue of air pollution through an architectural intervention.


We started to think
Whay is the most basic elements that we can bulid?

And that is why we then came into building a tile.

It took us three years to develop the right formula for carbon tiles.

The the ingredients we use to make carbon tiles are:

★Marbie chips
★Carbon Emissions
★And marble Powder

Carbon is taken from the air through a propietary device by AIR-INK,it is made into a slurry and then compressed into a tile.

So,we are using this 200 year old traditional crafting technique, Which was use by the local quarry masons
To upcycle the broken marble chips and produce higher garde surface finishes.

With this technology,we want to make various building element or an entire building made out to this.
We want people from divers background like Researchers, architects, designers to come together and solve this problem of air pollution creatively."

Yana tsayawa anan Jesmin ta ce, "Dukkanin hakan ba za su samu yadda muke so ba har sai muna da ishasshen kudin da zamu fadada harkar da kuma wadataccen albashi ga duk ma aikatan da za mu dauka."


"Muna da burin habaka lamarin kamar yadda dan uwana ya fada ta kowanni fanni domin amfanuwar al'umma da dama." Cewar Raj.


Khaleel ne ya numfasa kafin ya ce, "Ma sha Allah ,mun same ku yadda muke zato zamu tallafa maku in har kun aminta da dokokinmu tare da tsare tsarenmu wanda yanzu Za a sanar da ku."


Haiydar ya ce, "dokikinmu gasu nan kamar haka atakaice duk da cewa kun gansu a rubuce amman zan kara maimaita maku abaki kamar yadda aka buƙata, na Farko zakuna cire mana kasonmu aduk ribar da kuka samu cikin kashi biyar za ku cire mana kashi daya, shi wannan kashi dayan da zaku cire ba mu za abawa ba kuma ba mu zamu karba ba ga mabukata za ku mika ,walau gidan marayu ko kuma wasu wanda suke matukar bukatar taimako, na biyu zaku dau marasa karfi ku koya masu aikinku ya kasance rayuwarsu ta inganta sanadinku, kasancewar ku masu taimakon al'umma na da matukar muhimmanci ku taimaka sannan inda hali ku sanar da wa inda kuka taimaka suma su taimaki na kasa da su hakan shi ne burinmu a kullum sanya Murmushi a fuskar kuka, tallafawa wanda ya kasa tsayuwa ya tsaya haka kuma gyara abun da yake ba daidai ba, zamu kasance masu bibiyarku a wasu lokutan domin duba lamaranku in kuna aiki yadda ya dace kuma ana samun ci gaba za mu iya ci gaba da tallafa maku har ku kai ga inda bakwa zato wannan ke nan,ina fatan kun fahimta."


Jesmin ta ce, "In sha Allah mun yarda mun amince zamu aikata dukkanin sharudanku da ikon Allah."

Raj da zack ne suka sanya hannu akomai nan take Zahra ta mika masu tallafin su.

Sunyi farinciki matuka sosai musamman 5stars aranar basu yi barci ba da suka koma gida farinciki suke ji ta ko ina yau ya kasance rana ta farko da suka fara aikata aikin alkairin da suka kudurta.

Karamin party suka hada suka dunga tikar rawa Haiydar kuwa ban da Video da hotuna ba abun da yake yi masu .



Cikin sati biyu komai da suke so ya daidaita.

Sai da suka tabbatar sun kammala komai kafin su Noor suka dawo gidan.

Suna dawowa kuwa kwana ɗaya suka kara kowa ya kama hanyar kasarsa.

Noor da su Anitha da kyar suka rabu cikin kuka da ihu.

Su kansu 5stars ji suke tamkar su ci gaba da rayuwa a tare kar su rabu.

Gaɓadayan su an rabu cikin kewar juna da soyayya.

Su Zahra na sauka a Indonesia sai ga Mr Imam daidai lokacin da Khaleel kuma ya kirata awaya.



08103080717
Urs Xayyeesherthou
*FREYA*


*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ko wata ba, Saƙo ne kawai na ke son ya isa inda ya dace_

PAGE-28

_*Bismillahir-Rahmanir-Rahim*_

_Allahumma munzilal kitabi sari'al hisabi,ihzamil Ahzaba,Allahumma zumhum wazalzilhum🙏🏼_

TALLAH

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!... sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_

★★

_Buy your Mtn Data At Affordable Price_
MTN
500mb = 200
1GB = 300
2GB = 550
3GB = 850
4GB = 1150
5GB = 1450

Cal. Whatsapp 07046767662
Chat on Facebook 👇Maryam-Ashner Isma'l Usman
★★

"Welcome Mah kin san yadda nai kewarki nayi kewarki kuwa? I did not know what you mean to me

I did not know what you mean to me,
Until you are gone so far,
Now, I know what your real worth is,
What you really are,
I Miss You So Much.
U really mean a lot to me,
You are in my every thought, ba zan kara bari ki mun nisa ba."

Karaf a kunnen Khaleel lokacin ta amsa kiran, Murmurshi tayi kawai sannan ta ce wa Khaleel , "Barka Friend Mun sauka lafiya,ya Noor?"



"Ga shi nan ya kasa nutsuwa ya bata rai shi fa sai ya zo Indonesia gun su Aniy." Cewar Khaleel.

Zahra ta ce, "Sorry Noor ka bari ku gama exams a askul sai ka tawo ko bayan speech and prize giving day dinku saura kwana kadan ai sorry na san yarona na jin maganata."

"Alright Mom Allah ya kaimu." Noor ya fada yana kokarin kiran su Anuskha a tab dinsa.

Khalil ya ce, "barin barki ki huta ko, bye-bye a huta gajiya."

"Thank you byebye."

Tana dagowa ta ga Mr Imam ya kura mata ido.

Dago hannunta tayi wajen idonshi tana, "Why are you stirring at me?"

Murmurshi ya yi yana, "kallo nake da tunanin yadda zaki kasance mallakina nan gaba kadan, lokacin zan kalleki son raina ba tare da kinyi kokarin hure mun idanuna ba."

Dariya Zahra ta yi, "kai kam baka da Matsala sam yanzu dai bara inje inyi wanka in duba su Anuskha,kana nan ko zaka tafi ne?"

Mr Imam ya ce, "ina naga ta tafiya ai yau ko awa nawa zaki yi ina jiranki a parloun nan idona ya yi kewar ganin murmurshinki mai ratsa zuciya,haka kuma kunnena ya rasa sauraron zazzagar Muryar nan."

Dariya Zahra ta kara yi ta girgiza kai kawai ta shige ciki yana binta da kallo.


Tana shiga wanka kawai ta kalli jikinta duk gashi ya fito da ke zahra ba mai son barin barin gashi ajiki bane take ta fito a toilet din ta nufi kitchen.

Madara ta daura a huta sai da ya tafasa tukun ta sauko ta zuba a bowl zuma ta dauko ta xuba ta juya sosai sannan ta zuba cumin powder da gelatin ta juyasu suka hade jiki sannan koma toilet tasa aduk inda gashi ya fito mata sai da ya danyi mintuna,tana cirewa gashin na fita kuma babu zafi sam sai da ta gama kafin tai wanka.
Jikinta ya kara kyau Sai sheki.

Mai ta shafa kawai tasa kaya da turare ta shiga kitchen ta hada masu bread popcorn da tea ta kira su Anuskha suka dau nasu kafin ta nufi falon da Mr Imam yake.

Tana zuwa ya wani ja dogon numfashi, "Ma sha Allah, Barakallahu fikhi, tsira da aminci su kara tabbata ga Ubangijin talikai wanda gyangyadi bai taba riskarsa ba bare barci maddallah da ke maddallah da kasancewarki haka."


Karasowa tai tana ajiye plate din Bread popcorn and tea tana, "Yau kam sam na rasa gane dalilin wa'innan sambatun da kaketa surfo mun anya lafiya kuwa?"

Murmurshi ya yi, "Lafiyar ce ta kawo hakan amman babban muradina a yau bai zarce inji kin amince dani ba."

Gyara zama zahra tai kafin ta ce, "Ehen ka san ba zan taba kinka ba amman ina so kana tuna cewa har yanzu da auren wani akaina,ka fini sanin cewa babu damar yin aure kan aure har yanzu jirar hanyar da xan samu wannan damar nake cikin sauki daga nan kuwa kana da damar cika muradinka."


Numfasawa ya yi kafin ya ce, "Tabbas hakan amman in kika so a koyaushe xa a iya dikile komai domin kina da iko da yancin yin hakan ban san Dalilin ki na dakatarwan ba amman karki manta komin tsanani daren dade ina nan da muradina agefe tare da kokon baran neman cikawa."


"In sha Allah." Zahra ta furta tana zuba masa tea din.

Tare suka ci abinci kafin ya bar gidan.

1Month Latter.

Ranar speech and prize giving day din su Anushka da Anitha.

Murna suketa yi hakan yasa da wuri suka shirya ranar suka nufi skul su da Zahra.

Suna zuwa ganin kowanni table na Mom And Dad ne ya fara sa jikin Zahra sanyi.
Anitha da Anuskha suna gani kowa ya zauna biyu ita kuma daya suna hada ido dukananinsu yanayinsu ya canja

Gaɓadaya jikin Zahra ya mutu kokari tai ta kakulo murmurshi tayi

Please Login or Register in order to submit comment