Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ce." Farouk ya fada.

Washe baki Khaleel ya yi kamar yana hango Farouk ya ce, "Ma sha Allah maddalla da kai abokin kirki, Thank You So Much,cikin sati ɗaya ko biyu nake so mu kammala komai."


Farouk ya ce, "bana jin ma za akai sati biyun tunda ba gini za a yi ba,ba komai ba ,kawai neman wajen ne,so shikenan kawai."

Da haka suka yi sallama Khaleel na farincikin yadda komai zaizo masa cikin sauki.


Sai da lokacin komawarsa gida ya yi ya koma.
Zahra kuma da kanta taje ta dauko su Anuskha a skul.

Ta ga khaleel ya dawo ya kara fita kuma har cikin dare, Zahra ta ce, "wai me ke faruwa ne lafiya kuwa?"

Khaleel ya yi Murmurshi, "ba komai kawai an bani wani aiki ne kuma akwai bukatar inyi bincike kafin yi."



Cikin cikin kwana goma har aka kammala komai ba tare da ta sani ba,har sai da daliban suka zo da komai kafin Khaleel ya dauki Zahra da su Noor suka je.

Suna shiga suman tsaye Zahra ta yi don mamaki, su Anuskha kuwa ban da tsalle da murna ba abun da suke yi.

Rungumesa ta yi tana kuka ta ma kasa magana sai, "Thank You, Thank You So Much Just wanted to say thank you for your support and guidance and for being one of the best husband in the world."

Rugumeta shi ma ya yi,yana share mata hawaye, "Always Welcome,sanya ki cikin farinciki da walwala duk yana cikin nauyina a yanzu ba zan taba gajiyawa ba wajen faranta miki kamar yadda kema ba kya gajiwa wajen faranta mun in sha Allah."


Daga ranar Zahra ta ci gaba da kula da makarantar girkinta na uk mussaman yadda ya samu karɓuwa tamkar wacce ta dade a wajen tana aiki.
Dalibai ta ko ina fitowa suke.

Karshen wata ya yi zata Indonesia ta shirya komai domin tafiya ita daya domin Khaleel na da aiki a office su Noor kuma suna School.

Har airport Khaleel ya kaita kafin ya wuce office.

INDONESIA

ta isa kan lokaci sai da ta shiga cikin gida ta yi wanka tare da sallah kafin ta nufi restaurant.

Ta yi farinciki sosai riskar abubuwa fiye da zatonta domin Suhana na tafiyar da komai cikin tsari ga ci gaba da aka samu.

Aranta sosai ta jin jina da kokarin yarinyar wajen gudanar da restaurant din yadda ya dace.

Zaune take a office ta gama duba File sai ga Suhana ta shigo ta yi sallama Zahra ta bata damar zama.

"Madam,ina da magana da ke don Allah in ba damuwa ina so in fada miki wani abu."


Zahra ta ce, "Ah ki fada mana ina saurarenki."

Suhana ta ce, " labari na samu kan cewa Babansu Anitha na safarar yara mata mussaman kananun yara kuma na ga hakan ganin idona na tabbatar."

Gaban Zahra ne ya yi mugun faduwa ta furta, "Adams wato abun na sa ci gaba ya yi, Innallillahi wa inna illar raji un.".

Abun da ta iya furtawa kenan kawai ta dafe kai.

Da niyar kwana uku ta je amman sam ta kasa jurewa washegari ta dauki hanyar Uk dauke da damuwa fal a zuciya ,babban tunaninta makomar yaran da yake batawa shin ya zasu taso? Wani irin hali suke yanzu a ciki?"


Tana isa Uk Farouk ta fara kira awaya domin ta sanar masa su tattauna domin tasan ba wanda zai bata mafitar wannan damuwar bayan shi.
*FREYA*


*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ko wata ba, Saƙo ne kawai na ke son ya isa inda ya dace_

PAGE-42

_*Bismillahir-Rahmanir-Rahim*_

_Allahumma munzilal kitabi sari'al hisabi,ihzamil Ahzaba,Allahumma zumhum wazalzilhum🙏🏼_

TALLAH

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!... sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_

★★

_Buy your Mtn Data At Affordable Price_
MTN
500mb = 200
1GB = 300
2GB = 550
3GB = 850
4GB = 1150
5GB = 1450

Cal. Whatsapp 07046767662
Chat on Facebook 👇Maryam-Ashner Isma'l Usman
★★

Farouk ya ce, "ba matsala in sha Allah za dakatar da shi,ya zama dole wannan, amman in Khaleel ya dawo shi ma ki sanar da shi daga nan sai mu zauna muyi meeting duka."

"Alright shikenan komai zai tafi daidai in sha Allah thank you so much."


Dariya ya yi yana, "Welcome Yar Lukuta,Yar Guntuwa."

Bayan sun gama waya kuwa, Khaleel na zuwa ta sanar da shi komai shima,ya jinjina abun tare da nuna rashin jin dadi,hakan yasa nan take ya kira Xavier ya mai bayanin komai domin ta kowanni fanni a fadada bincike.


★★BAYAN WATA BIYU

Da rashin lafiya mai tsanani Zahra ta tashi, cikin sauri Khaleel ya wuce da ita asibiti domin adubata.

Duk ta fice a hayyacinta shima hankalinsa ya tashi,5stars kowa sai kiran waya ta ko ina kawai suke Hankalinsu ya kasa kwanciya.

Sai da likita ya gama dubata ya tabbatar Zahra na dauke da cikin wata ɗaya.

Farinciki Khaleel ya rasa inda zai sa kansa tuni ya kira ya sanar da su Farouk suma kowa murna da farin cikin Zahra na dauke da ciki.


Sai da suka gama komai kafin suka koma gida daga asibitin.

Khaleel sai nan da nan yake Zahra ko motsi ta yi zai ce me takeso ita ko sai dai tayi dariya

Ta tashi zata je kitchen ya janyeta ya zaunar da ita a cinyarsa, "ina zaki je ne wai? Ki fadamun koma miye ni zan miki daga yau kin daina komai a gidannan mu xa muna yi."

Shagwabe fuska Zahra ta yi tana , "Umm ni yanzu ina jina daidai fa zan je in dama custard ne nake son sha."

Khaleel ya ce, "Aa ni zan dama miki ki jirani." Ya kwantar da ita akan kujerar a hankali kamar wata kwai ya ce, "yawwa ki jirani yanzu zan kawo miki."

Binsa kawai ta yi da kallo yayin da wani irin hawaye ke gangaro mata ba abun da idanunta ke nuna mata illa rayuwarta a gidan Adams mussaman cikin Anushka da bata ma san miye cikin ba , ta dai ganta da tulu kawai har ranar da Allah ya kaddara ta haifota a Wulaƙanci sannan kuma na Anitha da shima ya zo siga mafi tozarci wanda bata taba samun tarairayar kasancewarta mai ciki ba ko da na second ɗaya amman yau wai ita ake lallabawa don tana dauke da ciki a duniya,shin daman kowacce mace na Fuskantar gata irin haka? Sai dai wa inda kaddara makamanciyar ta rayuwa a gidan Adams ta afkawa ke fuskantar kalubale.

Muryar Khaleel ta ji cikin rudu yana magana yana share mata hawaye, "Mene ne? Wani waje ne yake yi miki ciwo? Ga custard dinnan na dama fa meya faru ne? Don Allah ki daina,kin san yin kukanki zai iya ja miki matsala ke da babyn cikinki ko? Zahra stop it please."


Rugume Khaleel kawai tayi tana shasshekar kuka.

A hankali ya ci gaba da mata magana yana shafa mata baya, "ya isa ko? Ki yi shiru kinji ,yi shiru dago in baki Custard din ki sha kinji."

Dagowa tayi ta dan zauna yana bata abaki har ta shanye,tana gama shanyewa ya bata maganin da aka basu a asibiti tana sha kuwa agun barci ya kwasheta.

Daukanta ya yi,ya kaita daki ya kwantar da ita,sai da ya gyara mata kwanciya ya lullubeta sannan ya kashe wutar dakin, har zai fita ya dawo ya mata kiss a goshi yana, "Ina Sonki Farinciki na,ina kaunarki, a kullum kara samun farinciki da ci gaba nake a rayuwa sanadin kasancewa da ke, Allah ya saukeki lafiya ya kuma kara inganta miki rayuwa."


Tashi ya yi zai fita kawai yaji ta riko masa hannu.

Ya koma ya zauna bakin gadon, daga kanta ta yi ta daura akan cinyarsa ta kwanta ta ci gaba da barci, murmurshi ne kawai ya bayyana a fuskarsa yana kallonta ,sai da ta yi nisa a barcin kafin ya samu ya saɓule jikinsa ya barta ya fice.


Tun daga Ranar Zahra ke samun tarairaya da kulawa tamkar kwai,indai Khaleel na gidan nan bata isa tayi komai ba shi da su Noor za su yi.


Da safe ma su Anuskha ke hada kayan karyawa kullum kuma su gyara gidan suyi komai kafin su tafi skul su dawo su tafi Islamiya.

Hatta 5stars dukkaninsu kowa sai ya kira waya kullum ana tambayar lafiyan maman Unborn baby.

Gaɓadaya jinta take asabuwar wata duniya da bata taba tsinkar kanta ba, tamkar Sarauniya a babbar masarauta.

Ta kara ƙiba da kyau,kowa ya ganta zai fahimci cewa tana cikin farinciki,da kyar Khaleel ya yarda ta ci gaba da zuwa skul din koyarda girkinta hakanma in taje sai dai tana basu umarnin abun da za suyi ba dai ita ta yi ba,ya kaita kuma ya je ya maidata gida da kansa.



Ranar an samu a kasi bai je daukota kan lokaci ba, ita kuma ganin hakan da dan karfi a jikinta yasa ta shiga kitchen din da kanta tana zuwa kuwa bakin kofar ta subuce ta fadi.
yana zuwa tarar ba yadda take,gabadaya daliban sun taru akanta sunma rasa me zasu mata.

Yana ƙarasawa gabanta tana suma.
*FREYA*


*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ko wata ba, Saƙo ne kawai na ke son ya isa inda ya dace_

PAGE-43 *END*

_*Bismillahir-Rahmanir-Rahim*_

_Allahumma munzilal kitabi sari'al hisabi,ihzamil Ahzaba,Allahumma zumhum wazalzilhum🙏🏼_

TALLAH

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!... sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_

★★

_Buy your Mtn Data At Affordable Price_
MTN
500mb = 200
1GB = 300
2GB = 550
3GB = 850
4GB = 1150
5GB = 1450

Cal. Whatsapp 07046767662
Chat on Facebook 👇Maryam-Ashner Isma'l Usman
★★


Cikin gaggawa ya dauketa suka nufi asibiti.

Ana zuwa kuwa aka shiga da ita likitoci suka hau kanta anata ƙoƙarin ceto rayuwarta ,a ƙarshe suka tabbatar wa da Khaleel cewa ta riga ta razana matuka adaidai lokacin da ta fadi wanda hakan yana daf da lokacin da nakuda ke shirin riskarta , a yanzu abun ya yi tsananin da ba a tsammanin zata iya haihuwa da kanta sai dai a cire kuma a cirewan ma ba a tabbacin cewa ita ko babyn zasu rayu, akwal yiwuwar rasa ɗaya cikinsu.

Gaɓadayan Khaleel ya gigice ya fita a hayyacinsa.

Farouk ya kira ya sanarwa, cikin sauri Farouk ya sanar da sauran, sun umarce shi da yasa hannu in sha Allah Zahra zata kubuta gudun kada ayi biyu babu,daga nan kuma dukanninsu suka hayo jirgi na gaggawa domin zuwa Uk.

Haka Khaleel ya sa hannu ba yadda ya iya domin bai da zabin da ya wuce wannan.

Granny ce ta je ta dauki su Noor ta maida su gidanta, tunda suka ji labari suka duƙufa da sallah suna addu'ar Allah ya ceto masu mahaifiyar su tare da Unborn baby.

Sallah suke suna zubda hawaye tare da kai wa Ubangiji kukansu.

Sun kasa nutsuwa sam bare batun cin abinci ko wani abun.

An gama tanadar komai za a shiga da Zahra dakin aiki.
Khaleel ya rike mata hannu.
Murmurshi ta yi ta dago ta kalleshi tana, "Ka yi mun murmurshi ko da zai zamto na karshe ne,inyi alfahari da cewa na bar duniya a lokacin da mijina ke dauke da Murmushin kaunata a fuskarsa, ka yafe mun in nayi ma laifi, watakila kaddararmu tasa ba za mu yi rayuwa mai dogon zango ba,duk da haka, na yi matukar farinciki Kasancewa da kai na kankanin lokacin nan,ka sauya mun rayuwa ka bani farincikin da ban taba zato ko tunani cikin mafarki ba,kai mutumin kirki ne,kai mutumin kwarai ne, 5stars gabadaya antara mutanen kirki ,kai da Farouk da Haiydar, Zeeyter da Deejerh ban san me zan ce da ku ba sai dai Allah ya saka muku da alkairi, zanyi duk ƙoƙarin da zanyi ganin cewa na ceci rayuwar babyn jikina ta zo duniya da rai,bayan an kammala komai ina so ka je dakina ka duba cikin diarynka da kake rubutu kaina na ajiye wani muhimmin sako a cika mun shi ko bayan raina Don Allah,duk da cewa nasan ba za ka ce aa ba,kuma kada mutuwata ta cire ma tsammani ka ci gaba da rayuwa cikin jin cewa komai zai yi daidai kamar da,rayuwar 'Ya'yana Noor, Anitha, Anuskha na wuyanku duka 5stars na gode,na gode, Alhamdu Lillah,ina sonka,ina sonka har bayan rainaa."

Tana fadan haka suka shige da ita dakin, shi kuwa faduwa ya yi agun kawai yana zubda kwalla.




Awa guda sunata fama, daidai lokacin da 5stars suka isa asibitin daidai lokacin da Khaleel ya jiyo kukan baby daga dakin c.s, mummunan faduwa gabansa ya yi gudun ganin fitowar Doctor fuska babu walwala.

Kasa karasawa garesa ya yi, Farouk da Khaleel ne suka yi saurin ƙarasawa gun doctor din.

Suna zuwa ya ce suje office.

Mutuwar tsaye Khaleel ya yi

Suna zuwa cikin sauri Farouk ya ce, "Mene ne? Don Allah kasanar da ni halin da ake ciki,ka da ka ce mun Zahra ta rasu ka fada mun tana da sauran numfashi a duniya."

Doctor ne ya katse sa da fadin, "koma me zan fada mu kasance masu godewa Allah a kullum kuma a kowanni irin lokaci,domin shine ke rayawa kuma ya kashe, Alhamdu Lillah yau munyi aikin da dukkanin mu muke cikin mamaki da farincikin kasancewar sa domin kuwa cikin kudirar Ubangiji Mahaifiyar Baby da Baby suna Raye da karfin ikon Allah, illa a yanzu muna da bukatar jini da gaggawa wanda za asanyawa ita zahran kasancewar ta zubda jini da yawa."

Cikin sauri Farouk ya fita yana, "Alhamdu Lillah dukanninsu suna raye."

Nan take Khaleel ya yi sujjada agun domin nuna godiya da farincikinsa ga Ubangiji.

Haiydar ne ya fara tsayawa aka gwada jininsa ko zai mata,cikin sa'a kuwa ya yi aka diba

Dukaninsu ban da kukan farincikin ba abun da suke yi.
Mussaman Zeeyter da ta kasa zaune bare tsaye.


Su Noor ma kuwa suna jin labari ban da tsalle da murna ba abun da suke, daganan Granny ta daukesu duka suka nufo asibitin.

Ana fitowa da baby Zeeyter ce ta fara karbanta tana zolayar Khaleel, "Wannan yarinyar dai dani take kama domin kyakkyawa ce ba irin ku."

Sai a lokacin duka suka yi dariya.
Tare da nufowa suna kallon yarinyar kowa na tofa Allah bakinsa.

Shiko Khaleel ko ta babyn baya yi damuwarsa abasa dama ya ga matarsa.

Sai da aka gama gyara ta aka sa mata jinin kafin suka bada damar a ganta.

Da sauri Khaleel ya shiga ya rungumeta yana, "Alhamdu Lillah Allah na gode ma,ban san ya zan kwatanta rayuwata babu ke ba,tabbas addu'a tafi komai a duniyar nan."

Da sauri su Noor suka karasa gunta suna, "Momy ,Momy, Momy."

Khaleel ya kallesu, "ku baku ga bata da Lafiya bane kar ku bugeta."

"Kar ku bige masa mata ya gama kuka zai mana masifa." Farouk ya fada yana dariya.

Dukansu suma dariya suka yi.

Kwanan Zahra a asibiti huɗu ta warware aka sallamesu.


Suna komawa gida kuwa aka fara shirye-shiryen shagalin suna,ranar suna Baby ta ci suna AIZA (respected)

Ana gama suna kowa ya fara shirin komawa ranar da zasu koma duka an fito kawai sai ga Zahra ta dauko AIZA ta mikawa Zeeyter sannan ta ce, "Wannan 'Yar kice Halak malak ,mallakinki ce,kuma abar ikonki ce,duniya da lahira."


Hawaye ne kawai ya fara zubowa daga idanun Zeeyter ta ce, "Mafarki nake ko gaskiya ne? Na kasa gasgatawa ashe da rabon zan raini 'Ya da hannuna tun tana jaririya?"

Haiydar ne ya dafa mata kafada yana kallon AIZA shi ma din hawaye ke kokarin fitowa daga idanunsa ya kalli Khaleel, "bama da bakin godiya gareku sai dai muce Allah ya saka da alkairi."

Murmurshi Khaleel ya yi ya ce, "mene ne amfanin kasancewar mu tare indai ba zamu farantawa juna ba? Zahra ce ta fara wannan tunanin duk da cewa na rigata a zuci amman ta rigani a zuciya kuma nayi Farinciki da hakan matuka, dukkanin mu ɗayane kuma za muyi Farinciki muddin muka kyautatawa junanmu, AIZA yar ku ce, Don Allah ko da wasa kada ataba nuna mata cewa ba Zeeyter ba ce ta haifeta , ina so ta taso da cewa kune asalin iyayenta kuma jigonta."

Farouk ya ce, "Alhamdu Lillah, Gimbiyata na taya ku farinciki matuka na ji dadin abunnan fiye da misali Allah raya mana baby AIZA da imani."

"Ma sha Allah Am Out of words wallah na ma rasa ya zan misalta farinciki na, Alhamdu Lillah." Deejerh ta fada.

Gaba-daya rugume junansu suka yi suna share hawayen farinciki, Zeeyter kuwa ta kara kankame AIZA ta hana kowa har suka shiga jirgi.

*Anan nima nake cewa Alhamdu Lillah, Alhamdu Lillah, Alhamdu Lillah, ya Allah na roƙeka ka yafe mun kura kuren dana aikata cikin wannan littafin,haka kuma ka bani ladan alkairan da na yi,ka sa al'umma su amfana da sakon da ke ciki suyi farinciki kuma su Kasance masu kwatantawa, Alhamdu Lillah ya Allah, YEL DA FREEYA SUN ZAMA COMPLETE ku biyoni a next ci gaban series dinnan mai suna VIXEN in sha Allah na gode sosai*

Shin kin karo da littafin nan?
Da me kika karu da shi?

Me ya fi burgeki?

Me ya fi baki haushi?

Wani waje ne ya fi baki tausayi?

Wani sako littafin yake dauke da shi gabadaya?

Next series na su wa kuke so asa kunsan saura biyu.

Na DEEJERH KO FAROUK?

Domin turo AMSOSHIN ku kai Tsaye zaku turo zuwa wannan number 08103080717

In sha Allah duk wa inda suka amsa indai basu karanta littafaina na kudi ba zan basu su duka free su karanta.


URS XAYYEESHERTHOU

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment