Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Madame Zuby ta yi tana fadin, "Thank you, thank you so much, da yanzu ban san yadda zanyi ba, da na tafka babban asara wanda kafin in dawo daidai sai anji jiki na gode sosai Zahra,kina da baiwa matuka, Allah ya kara haskaka rayuwarki da hasken sa, Allah ya biya miki dukkan bukatunki na alkairi duniya da lahira, baki ya yi kadan wajen nuna farin ciki na,mamaki nake wai biredi ne ya gyara mun Shinkafar da ta fara jiƙewa ko kyan gani babu, dankali kuma ya dauke mun gishirin miyar da ko mahaukaci aka ba ada ba zai iya sha ba, Alhamdu Lillah na gode sosai."

Murmurshi Zahra ta yi ta ce, "ba komai dabarun gyara na da yawa in an samu kuskure irin wannan akan yi amfani da su domin kaucewa asara,kin ga yanzu shi dankali ya dauke gishirin,biredi kuma ya dauke ruwan, Allah ne abun Godiya domin shi ke bamu hanyoyin da za su taimake mu arayuwa."


"Hakane kam Alhamdulillah na gode ma Allah kuma kema na gode miki, amman kin ga sumy? Ba abun da ta iya sai ci da bata abinci wannan shine kusan karo na uku da take janyo mun matsala ba dan kina nan ba da yau kam tayi rana ta karshe a wajennan." Ta karasa tana nuna Sumy da hannu.

Zahra ta ce, "Aa Madam ba wanda ya isa kaucewa kaddara da yin kuskure a yi hakuri."

Suna hada ido Sumy ta harareta
Ita kuwa sunkuyar da kanta ta yi.


Dare na yi kuwa ta fara shirin tafiya School.
Gaɓadaya Anitha da Anushka sunyi barci, hakan ya bata damar ta yi cikin kwanciyar hankali.

Tana zuwa kuwa lokaci daidai Ya yi.
Za a fara yi masu darasi.

Wani Malami ne Namiji, da ka gan shi kasan Yana da kudi ba sai an fada ba,daga jiki,har ma da yanayin mu'amularsa,wanda kasancewar sa night School Study Center ra ayine da kuma jin zuciyar cewa shi ma zai iya bada gudunmawa har a taimaki wasu, sunan Imam Abdallah yana koyarwa a babbar jami'ar da ke Indonesia, kuma babba ne acen sosai.

Da kasancewar sa cikin class din tun a karon farko idanunsa ba wanda suka fara cin karo da shi sai zarah.
A tare suka kalli juna.
Tayi saurin kawar da kanta ya yin da taji gabanta ya yi mummunan faduwa, a zuciyarta ji take tamkar da Adams ta hada ido, domin a tunaninta yawancin maza dabi'unsu dayane, tunda kawunta ya Kasance haka, Adams ma haka sai ya zam mata zuciyarta da idanunta na kallon kowanni Ɗa Namiji da wannan tabon.

Gyaran Muryar da ya yi ne yasata sauri kaucewa daga dogon tunanin da ta fara.

Gabatar da kansa ya yi,sannan yasa kowa ya gafarta da kansa.
Duk wanda ke da Matsalar English wahen gabatarwa ya gyara masu,duka class din amman ban da Zahra da ta yi komai nata daidai kuma cikin nutsuwa.

Karatu ya shiga yi masu, cikin salon hikima dukkaninsu suna fahimta saboda kwarewar sa a hakan.

Yana karatun amman Kallon Zahra yake,da ta dago ido kuma sai ya kautar da na shi tamkar bai ma san da zamanta awajen ba.

Har ya gama karatu ya masu tambayoyi duk aka basa amsa
Ya jin dadin kasancewa cikin ajin Sosaii, Mussamman da ya fahimci cewa suna gane karatun nasa.

Suna kammala ɓangaren turanci ya ce, "To yanzu za mu dan taɓo Islamic Religion, akwai bukatar yin sharar fage aranar mu ta farko a yau dangane Ibada wato sallah wacce ta kasance babban ginshiƙi acikin musulunci, ta yiwu kowa yasan ya ake yinta ta yiwu kuma ƙalilan ne suka sani,hakan yasa zanyi sharar fage domin warware duk wani dauri in ma akwai su cikin zukanku, a kan yi Sallah sau biyar a kowacce rana, Asba raka'a biyu,Azahar raka hudu,la'asar hudu,magrib uku sannan isha hudu, kowacce sallah ana karanta mata fatiha domin babu sallah ga wanda bai karanta suratul fatiha ba ma'ana Ummul kitab, bayan an karanta sai a karanta wata sura cikin Alkur'ani, raka biyun farko ne ake karanta fatiha da surah, in Azahar,la'asar ko isha ne,sauran biyun zallan fatiha ake karantawa,in kuma magrib da subhi ne duka za a karanta fatiha da surah ne,sannan kowanni ruku'u da zikirorin da ake masa,nan da sati ma in da wanda bai sansu ba zaku sani kuma har ku iya in sha Allah acikin littafanku akwai zaku iya fara koya agida ko awajen aiki ya yin da kuke free,kar amanta bara in danyi baya da jawabi na, kafin ayi sallah sai anyi alwala kuma alwala tana fa farrilanta da sunnoninsa wanda yana da matukar muhimmanci ga dukkanin Musulmin kwarai ya san da su, farrilan alwala guda bakwai ne sunnoninta kuwa guda shida ne,haka ma sallah tana farrilai guda goma sha biyar da sunnoninta guda bakwai, ka da ku manta sharar fagene nake mana, Tunatarwa ga wa inda suka manta da kuma nusarwa ga wa inda basu sani ba, za mu zo har practical za mu yi na sallah a aikace nayi ku gani kowa yayi na gani inda kuskure a gyara, sannan a yau zan koyarda mu addu'ar da manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam yake yi a kullum ya yin da ya idar da sallah, zan karanta kowa kuma ya bude acikin littafinsa shafi na farko asama, Bismillahir-Rahmanir-Rahim, *Allahumma Antas-salam wa minkas-salam Tabarakhta Ya Zaljalalu Wal-Ikram.*

Bai tsaya ba har sai da ya tabbatar kowa acikin ajin ya iya kuma ya fahimci fahimmacin addu'ar.

Suna gama karatu zarah ta shiga wajen Madam Asmy.

Da farinciki ta karbeta tana, "Yarinyar kirki." Ta karasa maganar tana bude hakoranta.

"Har yanzu na kasa yarda ki ga yadda hakorana suka dawo cikin 2weeks? Sunyi fari,sun yi kyau sai sheƙi da haske,ba datti sai tambayata ake wani irin toothpaste nake amfani da shi kowa na ce aloevera ne kawai sai suyi mamaki, ni kam ai daga yanzu da shi zan ci gaba da yi a kullum in nayi da shi tukun sak insa toothpaste a karshe in kara wankewa."


Zahra ta ce, "gaskiya na ji dadi kuma na miki murna Anty Asmy, In sha Allah Shikenan yanzu hakorinki ya dawo daidai ba wata matsala."

Asmy ta ce, "Sosai ma na gode miki ke kam."

Zahra ta ce, "zan tafi Anty sai da safe."

Nan suka yi sallama zarah ta tafi.

Washegari da asuba Zahra na tashi taga fuskarta duk ta baci da kuraje.
Sallar asuba ta fara yi da ta idar ta karanta addu'ar da aka koya masu jiya da daddare, da mamakinta taji tayi ta tsaf daidai har karshe.
Hamdala tayi tana yi wa Allah godiya aranta.

Sai da ta bari ta gama aiki kafin ta dauko madubi da lemu ta zauna tana duba fuskar.

Lemun ta yanka gida biyu tana ta fara shafa ɗayan bangaren a fuskarta.

Tana cikin gogawa sai ga ɗaya cikin masu aiki agun, Suhana ta zo wucewa ta tsaya kallonta ta ce, "Oum Anitha lafiya? Lemu ne fa kike gogawa afuskarki."

Zahra ta ce, "Eh Wallahi Kuraje ne suka fitomun in ba haka ba bazai bar mun fuska ba Har sai ya gama bata mun."

Suhana ta kara tsayuwa ta ce, "Ikon Allah magani ne kenan yanzu kike sawa?"


"Kwarai ma kuwa,yanzu inna ci gaba da goge fuska da shi akan lokaci kurajen zasu mutu,fuskata tayi kyau in ma da wani boyayyen dati duk zai goge mun shi ya gyara mun fuska sosai." Zahra ta fada.

Suhana ta taba fuskarta ta ce, "da wahalar kashe kudin da nake kan neman maganani ashe ga magani mai sauki ma, gaskiya nima daga yau zan fara ga sauki ga aiki,baxa abarni a baya ba in sha Allah na gode sosai."

Zahra ta yi Murmurshi, "ai kuwa da kin huta da kurajen fuskarki ."

Suhana ta tafi tana dariya, "bari kawai ai naki wasa ne."

★★Noor na tashi a barci ya ga bai ga khaleel kasancewar sun tashi sunyi sallar asuba tare suka koma, Sunday ba aiki kuma ba skul zasu zauna a gida.

Bincika gidan ya yi duka bai ga khaleel ba sai can ya ji motsi a toilet.

Nocking din toilet din ya fara yana "Dad are you there?"

Khaleel ya ce, "Yes Baby."

"What Are you doing?"
Noor ya fada.

Khaleel ya ce, "abu na ke am coming ka jira ni mana Just few minutes."

Noor ya ce, "Dad like you are doing pupu ,na ji warin humm."

Khalil ya yi gyaran murya, "Noor ana toilet ana magana hakan abune mai kyau? Ka je ka jirani na ce ko."

Da gudu ya tafi yana, "Humm Sorry Dad amman i swear pupunka da wari."

Murmurshi khaleel ya yi yana kwafa a zuciyarsa kan in ya fito zai yi maganin Noor.


_*Maddallah da ku fasihan makaranta na,kuma masoyana masu karatu ba don su ji dadi a azuciyar su ba,masu hakuri domin jiran na kai inda na dosa, masu karfafa mun gwiwa ko da ban faranta masu ba🤗 ku din na musamman ne,in sha Allah watarana za kuyi dariya har cikinku ya koshi albarkacin hakurin da kuka yi na fuskantar littafinnan a haka ba tare da nuna gajiwarku ba,da sannu danwaken da ke kasa zai ji mai har yaji ya fito🥰ina sonku aduk inda kuke kuma ina kaunarku wani jinkirin alkairi ne....*_


08103080717

Urs Xayyeesherthou
[9/3, 5:56 PM] My Number: *FREYA*


*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ko wata ba, Saƙo ne kawai na ke son ya isa inda ya dace_

PAGE-11

_*Bismillahir-Rahmanir-Rahim*_

_Allahumma munzilal kitabi sari'al hisabi,ihzamil Ahzaba,Allahumma zumhum wazalzilhum🙏🏼_

*Mah Group Members ina jin dadin comment's dinku over irin sosai dinnan mussaman Mhix Abdullahi sistorna,My Walida,Feena, Fadimatulzahra,Ummu hafsat,Fatima Zahra, Kawas Oum Ayrah, Maman Adnan,Hajara Umar,Maman Ummi,Ummu Ammar,Serdeeyerh,Mmn Mhmd Jiddah, dama sauran kowa da kowa😘ku din na musamman ne ba zan iya maku so kadan ba😍ina yinku 💯*
_*JIKI YA WARE IN SHA ALLAH MASU KIRA, MASU TEXT DA MA MASU MAGANA A GROUP NA GODE SOSAI DA NUNA KAUNA*_

TALLAH

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!... sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_

★★

_Buy your Mtn Data At Affordable Price_
MTN
500mb = 200
1GB = 300
2GB = 550
3GB = 850
4GB = 1150
5GB = 1450

Cal. Whatsapp 07046767662
Chat on Facebook 👇Maryam-Ashner Isma'l Usman
★★

Yana fitowa Noor ya kara zurawa a guje.
Khaleel ya bisa ya kamosa yana, "Ni kake zolaya ko? Kana so in ma duka ashe za ka sani."

Cikin dariya Noor ya ce, "Dad ai pupunka ne ya dameni da wari amman yanzu kamshi ina ji Sosai, ina ba za ka kara ba? Manya basa pupu sai yara."


Dariya Khaleel ya yi ya ce, "Kwarai ma kuwa yau ma ai kai nayima,amman manya basa yi."

Noor ya tallafo fuskar Khaleel ya ce, "Dad."

Khaleel na girgiza kai ya amsa , "Yes My Boss."

", Ina ba za ka tafi ka barni ba,kamar yadda mom ta tafi?" Noor ya fada.

Murmurshi Khaleel ya yi, ya ce, "In sha Allah ko da zan Barka a duniya sai na tabbaatar da na ginaka da kasar alkairi."

Dariya Noor ya yi, duk da cewa bai san nufin maganar babansa ba,amman ya ji dadin amsa cewa ba zai barsa ba da ya yi,ya ce, "I love you Dad,I Really Really Love You."

Khaleel ya rike masa kumatu kafin ya ce, "Love You Too My Boss, Yanzu ni ka barni in yi barci ci gaba da wasanka ko."

Tafiya ya yi yana fadin, "Owk Dad."

★★

Tunda Zahra suka tashi yau suke aiki kasancewar an basu kwangilar Snacks da drinks din wani taro.

Gaɓadaya Madam Zuby ta rikice damuwarta kar ta ji kunya ayu abun da baiyi ba.

Zahra ta ce, "Madam kar ki damu,zan yi iya yina indai kin bani dama."

"Me zai hana? Ni da nake neman taimako a cireni ga fadawa kunya Bismillah Zahra."

Nan zahra ta karbi aikin agun su Sumy tana jagorantar su.

Donut suka fara yi.

Madara,kwai,yest, ta hada tayi mixing dinsu , tukun ta sa sugar,da gishri, sai flour.
Sannan tasa Mixer dinta ya kwaba komai duka sai da ya hade jikinsa ta ciro.

Tana cirowa ya gama hada jikinsa ta sa cikin wata roba babba kafin ta dauko farar leda da ake rapping abu tayi rapping.
Sai da ya yi kusan awa daya da rabi kafin ta bude,ya ninka yadda ta bari,ya kunburo ya yi kyau Sosai.

Zuba flour ta yi akan table sannan ta dauko kwabin donut dinta ta sa agun sai da tayi flat da shi kafin ta dauko abun cire shef dinta ta fara cirewa.

Sai da ta cire duka kafin ta fara suya.

Bar wa sumy da Suhana suyan ta yi ta je ta kara dibo kawai da madara.

Koduwar ta cire kawai ta zuba cikin madarar ruwa tayi mixing sai da ya hadu kafin ta tace shi tas.

Ta dibo sugar ta sa ruwa kadan tukun ta daura akan gas har sai da ya fara canja kala ya yu brown kafin ta sauke,tana saukewa ta dauko wannan ruwan madaran da kwaiduwan ta juye akan sugan.
Rapping dinsa tayi da rapping shid, sannan ta dibo ruwan dumi tasa akasan, sai da ya yi kusan minti biyar kafin ta cire tasa a obun, sai da ya kara wani minti biyar din kafin ta ciro, ya kama jikinsa ya yi kyau, ta juye a wani faranti, kasan gun sugan ya yi brown shi kuma gun madarar ya yi milk color.

Shef din circle ta dauko ta ciccire daidai yadda zai iya zama a tsakiyan donut din.

Suna gama suyan aka jera kowanne sannan aka dauki wannan abun akasa a tsakiyan kowanne.

Ban da kamshi ba abun da ke tashi,daga ido ma ya yi kyau bare kuma ankai baki.

Juice din kuma kayan fruit ta hada waje ɗaya,karrot, Apple,cocumber wanke su tayi duka kafin ta yayyanka su kanana sannan tasa tayi blanding dinsa har ya zama ruwa.

Cikin awa ɗaya Zahra ta kammala hada komai daidai lokacin da aka zo dauka.

Madam Zuby ce ta bi masu dauka har wajen taron domin tabbatar da cewa komai ya yi, ba tare da an samu matsala ba.

Da mamakinta kuwa tunda aka fara raba drinks da donut dinnan wajen taron ban da yabo da santi ba abun da mutane ke yi,a ƙarshe ma har sai da aka nemeta wasu suka mata kyauta tare da sanar da ita cewa indai wani abu nasu ya tashi ba wanda zasu nema sai ita, ita kuwa uwar bikin ninka mata kudin tayi tsabar farincikin yadda bakin ya tafi cikin tsari sanadin aikinta.

Farinciki Madam Zuby ta rasa inda zata sa kanta,tsabar xumudin ta rasa me za ta ma Zahra don ta faranta mata, kasuwa ta wuce kai tsaye ta siyo ma su Anushka kayan wasa, Zahra kuma ta siyo mata rantsatstsiyar waya.
Tana zuwa ta ba Zahra bakin ciki kamar zai kashe Sumy, tsabar takaici wajen ta bari.

Suhana kuwa murna ta taya Zahra sosai har tana nuna mata yadda za ta yi amfani da shi.

Madam Zuby ta ce, "Gaskiya kinyi matukar kokari ko da gasar yin donut za asa ba zan ji tsoron kasancewa ciki ba indai kina nan, gabadaya manyan mutana ne masu kudi na azo a gani amman sai yabo suke harda wacce tace za ana mata duk wata kawai akai mata gida,kai yau nayi farincikin da ban taɓa ba akan wannan sana'ar na gode miki Sosai Allah ya kara haskaka miki rayuwarki da yaranki,in sha Allah duk wani abu da za ki yi indai na ci gaban rayuwarki ne zan shige gaba gwagwadon iyawata har sai kin cimma nasara."

Zahra ta ce, "Na gode sosai komai na yi a yanzu kam sanadin taimakon da kika mun ne na gode sosai Allah ya saka da alkairi."

Madam Zuby ta rugumeta tana, "Daga yau kin daina aikin moping da shara, kitchen zakina shiga kawai kuma zan kara miki ninkin albashi In sha Allah."

Ba karamin dadi Zahra ta ji ba hakan yasata Hamdala ga Allah.
Aranta ta ce, "Yau Leches flan donut ya daga mun kima da darajar rayuwata."

Sunan Donut din da ta yi kenan (Leches flan donut)

Sai da wayar tayi chaji Lokacin ba aiki Zahra da Suhana suka zauna tana ta nuna mata abubuwa yadda suke, mussaman da ya kasance yanzu ta fara iya karatu da rubutu.


Taimaka mata tayi ta bude shafukan yanar gizo, WhatsApp, Facebook, twitter,da Instagram.

Tana bude mata Instagram Wajen Description Zahra ta shiga, daga zuciyar ta take jin maganar na fito mata ta rubuta kamar haka, "Ban fidda tsammanin cewa zan yi rayuwa kamar kowa ba,kuma ban fidda tsammanin cewa zan yi dariya kamar kowa ba,duk wuya duk rintsi da zan fuskanta nan gaba ko yanzu ba za su taɓa sanyawa na karaya ba,na tabbatar ko a yanzu inada labarin bayarwa bare kuma akai ga zuwa gaba."

Gurin abun da mutum yafi so kuwa haka ta rubuta, "Abinci shi ne zaɓina na kan ji dadi araina aduk sanda nake sarrafa wani abu da hannuna,ina son girki matukar gaske domin yana da mahimmanci a rayuwata dama al'umma gabadaya."


★★Da sassafe Khaleel da Noor suka shirya ya nufi hanyar kaisa Skul,domin khaleel baya son Noor yana hawa skul boss,shiyasa a kullum ya zaɓi da ya kaisa da kansa in lokacin tashi ya yi kuma Ammuh ta dauko shi.

Suna zuwa daidai bakin get din skul din Noor na hango wata yarinya ya fara kyafta mata ido yana Murmurshi.

Kuka ta fara tana nunawa mamanta shi, "Mom You see? Bana so yana ta kallona yana mun wani abu."

Mamanta na juyowa ya durkusar da kai.
Ganin bata ga komai ba yasa ta shareta suna kokarin shiga ana checking dasu su sai su Noor.

Taɓo mata baya ya yi,tana jiyowa ya yi mata sigina.

Fashewa tayi da kuka nan take tana nuna Noor.

Khalil ya ce, "Bo me ka ke ne haka? Bana son neman rigima fa."

Noor ya ce, "Dad me yasa take ta kallona ni kawai hararta na yi and ban mata komai ba,ni bana son kallo kawai."

Khaleel ya ce, "What Ever ka bata hakuri oya say sorry to her."

Kama kunne Noor ya yi ya ce, "I'm Sorry."

Yana karasa fada suka kara hada ido da ita ya mata sigina harda gwalo yana dare suka shige.

Hararsa tai kawai ta kau da kanta tana tsaki.


Suna shiga aji ita ce gabansa shi yana baya.

Ana cikin karatu sai ya caka mata pencil tana juyowa sai ya koma kallon wani wajen daban.

Ba abun da ke yiwa Noor dadi arai irin ya takurawa wannan yarinyar Anjali, hakan na matukar faranta mai a kullum in dai zasu je Skul to sai ya tsokaneta, kuma su biyune kanana kaf acikin ajin sauran sun fi su girma,amman Noor ya fi kowa rigima,duk wanda ya taba Anjali kuwa ko kuma ya ga da gaske tana kuka hankalinsa ya tashi kenan,sai ya rama mata ko kuma ya yi abun da dole zai sata dariya,amman daga nan kuma zai ci gaba da addabarta.



★Lokacin Tafiya Skul din Zahra ya yi,sun gama aiki,shiga tayi,tai wanka tukun ta duba kaya cikin wanda Madam Zuby ta siyo mata,guntuwar riga ce iya cinya sai dogon wando da belt din rolling.

Ba karamin kyau ta yi ba, kasancewar ba mai haske sosai ba,kuma ba mai duhu ba,sannan Zahra gajera ce a tsaye wanda duk da hakan baya boye diri da kyawun surarta,tana da gashi daidai gwargwado hakan yasa ko sha'awar karawa ba ta yi.
Dagon takalminta da Madame ta siyo mata da kayan tasa, wanda ya dan kara mata tsayi kadan, ta yi kyau Sosai wanda ita kanta ta ji hakan ajikinta domin tunda tazo duniya bata taɓa shiga kwantankwacin hakan ba sai dai ta ga ana yi.

Wani irin sanyi take ji na ratsa sassan jikinta da zuciyarta ga farinciki mara misaltuwa, kallon kanta ta tsaya yi.
Anushka ma tsayawa tayi kawai tana kallonta shin Mominta ce ko kuwa wata mai kama da ita

Kallonta ta yi,ta dauketa tana, "Anshuka baby,yau kin ga momynki tayi daban ko? Ni kaina na san na yi daban ba kamar kullum ba,kuma ba kamar da ba na yi kyau?"

Anushka ta girgiza kai tana dariya.
Bakinta ya bude ta iya magana amman bata cika yi ba sam sai dai murmurshi ko dariya har yanzu bata gama watsakewa da rayuwar gidan Adam ba.

Kissing dinta Zahra ta yi kafin ta ce, "gud gurl byeebyee zan tafi skul yanzu Anty Suhana za ta zo ku kwanta, ki lura da Anitha in ta tashi kinji ko byeebyee."

Tana dariya ta daga mata hannu ita ma tana mata byeebyee din.


Zahra na isa night School Study Center har an fara masu karatu, Imam yana masu karatu amman sai duba kofa yake ya ga inda Zahra zata fito.

Sai ko gata suna haɗa ido kamar kullum ta yi kasa da kanta amman sai sam shi ya kasa daga idonshi akanta daga karshe ma cewa ya yi, "Ma Sha Allah."

Sai ya kalli sauran daliban ya ce, "Ina fatan kuna sane da cewa in Mutum ya ga abun da ya masa kyau maimakon ihu ko wani abu *MA SHA ALLAH* ya kamata ya ce."


Dukan su dariya suka yi kawai domin sun lura da kallon Zahra yake.

Ita kuwa wucewa tayi kawai ta zauna. Tana kokarin ciro littafanta.

Karatu ya ci gaba da yi masu,sannan ya koya masu sallah a aikace ba karamin dadi Zahra ta ji ba,nan ta fahimci cewa ashe da kawai wasa take ba ibada ba,yanzu ne zata fara asalin ibada.

Lokacin tashi na yi kamar kullum ya ce, "Yau addu'ar da zan baku ta neman Soyayyar Allah ce, Addu'ar na da matukar kyau da kuma inganci ku Kasance masu yinta Aduk Lokacin da kuka samu dama, Bismillahir-Rahmanir-Rahim *Allahumma Inni As aluka hubbak,Wa Hubba man yuhibbuk, Wal-Amal al-ladhi Yuballighuni hubbak*."

Sai da masu Sosai ya tabbatar za su iya koda da gyara ma kadanne kafin aka tashi.

Da farinciki Zahra ta bar cikin makarantar fiye da kowacce rana,amman tana cikin tafiya tayi karo da abun da ya mugun daga mata hankali.

Yarinyace bata zarce 'Yar kimanin shekara tara ba yashe a gefen titi jini na kwaranya daga gabanta, cikin dimuwa Zahra ta karasa gareta ban da hawaye ba bu abun da ke ambaliya a fuskar wannan yarinyar domin ko sautin kukan bata iya fiddawa.

Kokarin daukanta ta fara yi amman sam ta kasa, taran masu tazi ta fara tana kuka su taimaka amman da kyar wani ya yarda ta shigar da yarinyar suka tafi asibiti....



08103080717
[9/3, 5:56 PM] My Number: *FREYA*


*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ko wata ba, Saƙo ne kawai na ke son ya isa inda ya dace_

PAGE-12

_*Bismillahir-Rahmanir-Rahim*_

_Allahumma munzilal kitabi sari'al hisabi,ihzamil Ahzaba,Allahumma zumhum wazalzilhum🙏🏼_

TALLAH

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na

Please Login or Register in order to submit comment