Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

inda muke kuma a duk inda za mu Kasance, Allah na tare da bayinsa kowacce jarabawa akwai dalilinta kamar yadda take da karshe, babban buri da fatan shine Allah ya ba mu ikon karfan jarabawar rayuwarmu aduk yadda ta zo mana.
Haka kuma kada mu Kasance masuyiwa jarabawar wani dariya ko rainata komin kankantar ta, Allahn da ya hallici bawansa yana sane da shi kuma shi yasan dalilin wannan jarabawar.
Girmama jarabawar duk wanda zaka tara, hakan zai sa kai ma a girmama jarabawarka.
Rayuwar duniya cike take fal da ƙalubale.


Kamar daga sama ya jiyo sautin Sarah da kawayenta sun shigo.
Bata kwana agidan ba,kuma babu damar ya yi mata magana.

Fisge remote din hannunsa tayi.
Suna yi masa wani irin kallon banza daga ita har kawayen nata.
Ta ce, "Za ka iya ba mu waje ko? Ina bukatar hutu Ni da kawayena."


Tashi ya yi ba tare da ya ce komai ba,ya dauki Noor dake barci a jikinsa suka shige bedroom.

Daya daga cikin kawayen ta mai suna Sofiya ce ta ce, "haba Sarah why are treat him like that? This is not good oh Oh ,he is kind ba ruwansa sam bai son hayaniya da ace ni ce zan samu miji irin wannan ai ba a magana."


Tsaki Sarah ta yi , "To ko za ki aure shi ne? I know what i am doing, kar ki ce za ki koya mun yadda zan yi rayuwa, haka nake so,kuma haka za mu Kasance zai fi kyau mu yi abun da ya dace."

Dariya Dayar ta yi ta ce, "Oh Sorry bea kinsan Sofiya ita adole gwanar tausayi, and ni ban ga wani abu da ki ke mai ba daidai ba, haka ya kamata ana Treating maza especially irin wa innan, in ba haka ba mutum shi zai zo ya yi nadama daga baya."


Sofiya ta ce, "Allah dai ya kyauta ya kuma ganar da ku amman wannan ba abu bane mai kyau."

Tsaki Sarah ta kara yi.
"Bara inyi wanka ni inzo gaɓadaya jikina ya mun nauyi."


Khaleel kuwa na daki suna ta wasa shi da Noor.

Wayarsa na kara kenan sai ga shigowar Sarah.
Kallon ta ya tsaya yi
Hakan yasata saurin zuwa tana duba wayar tasa.

Sunan mace ta gani tana kira.
A harzuƙe ta dago tana kallonsa.

"Wace ce wannan? Me za ta ma? Miye hadinka da ita?"

Khaleel ya ce, "Abokiyar aikina na ce ta office,akwai bukatar in tafi lokaci ya yi,zan kai Noor gidan Ammuh in wuce."

Ta shi ya yi tana kokarin daukan Noor, ta hankadasa gefe sai da ya fadi kansa ya fashe.

"Na ce ka fada mun wace ce me kiranka, wato za ka tafi Office ku je can ku haɗu ko? Har ta gaji da jiranka ta fara kiran waya, shin baka da hankali ne ko kuwa hauka kake?"

Taɓa goshinsa ya yi yaji jini,a harsule yake maganar, 'na fada miki bana da wata alaka da ita illa na aiki, muna da aiki sosai,tun tuni jiran dawowarki gidannan nake in fita,haba sarah ya kamata kina tunani kafin aiwatar da wasu abubuwan."

A fusace ta karaso garesa tana fara dukansa.

Dukansa take tana masifa tamkar tana kwaba fulawa.
Da kyar ya subuce gefe.
Ya tashi ya shiga toilet wanka ya yi,ya zauna tare da dafa kansa yana jin radadin da ke fita.

A lokacin gabadaya jikinta ya yi sanyi.
Karasowa gaban sa tayi ta durkusa tana, "ka yi hakuri, nima ba da son raina nake komai ba,zan chanja,don Allah ka yi Hakuri,nama alƙawali."


Kawar da kai Khaleel ya yi yana, "ba za ki canja ba Sarah,indai kece ba za ki taba canjawa ba,da ko zaki canja da tun tuni kin jima da canjawa."

Sarah ta ƙaraso tana kokarin rugumesa,kaucewa ya yi ya tashi.
Ya dauki Noor yasa shi a hanger goyo ya fice.

Yana fita ya nufi gidan Ammuh.
Bayan ya gaisheta ya mika mata Noor yana ta kokarin kawar da kai gudun karta gane.

Kallon fuskar shi ta yi ta ce, "Khaleel miye haka? Da farko yau yanayin ka a sauye sannan ga goshinka da ciwo miye faru?"


Wani irin murmushi ya kakalo ya ce, "Ba komai Ammuh bana jin dadi ne,dazu kuma na bige akai shine ya kara mun zazzabi da ciwon kai."

Ita ma Murmurshin ta yi , "Ma sha Allah nasan Khaleel dina kullum cikin fara a yake,kada ka manta in zaka fita kayi addu'ar fita daga gida _*Bismillahi Tawakkaltu Alallah wala haula wala ƙuwwata illa billah.*_ adawo lafiya, Allah ya kare mun kai ya tsare ka aduk inda zaka Kasance."

Murmurshi khaleel ya yi azahiri tare da fadin, "In sha Allah ,Thank Ammu."

Ya fice fuskarsa fal walwala kamar kullum ba za ka taba zata ko yi masa kallon mai damuwa a zuciya ba ko da wasa.

*Sharhinku wani Sirri ne😍a ci gaba da yi yadda ya kamata*
08103080717

Urs Xayyeesherthou
[9/3, 5:56 PM] My Number: *FREYA*


*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ko wata ba, Saƙo ne kawai na ke son ya isa inda ya dace_

PAGE-4

_*Bismillahir-Rahmanir-Rahim*_

_Allahumma munzilal kitabi sari'al hisabi,ihzamil Ahzaba,Allahumma zumhum wazalzilhum🙏🏼_

TALLAH

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!... sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_

★★

_Buy your Mtn Data At Affordable Price_
MTN
500mb = 200
1GB = 300
2GB = 550
3GB = 850
4GB = 1150
5GB = 1450

Cal. Whatsapp 07046767662
Chat on Facebook 👇Maryam-Ashner Isma'l Usman
★★★★★★

*INDONESIA*
_(Jakarta)_

11:00pm

Dare ya yi Sosai, cikin duhu suke, kasancewar wutar gidan ta samu Matsala.
Daga Anitha har Anushka ban da kuka ba abun da suke yi.
Harda shidewa.
Adams baya nan tun da ya bi bakinsa da rana har yanzu bai dawo ba.

A gigice Zahra ta goya Anushka sannan ta dauki Anitha suka fita wajen gidan suka zauna.

Kowa rayuwar shi yake ba mai damuwa da damuwar wani.

Binsu take da kallo gwanin sha'awa domin kusan kowa na gun walwala ce fal a fuskarsa.
Jin hakan take kamar wani sabon al'amari, domin wani Lokacin aranta ta kan ji cewa ko dai kowa ma haka yake rayuwar nan ne? Wacce ta zama dole in yita haka.

Kamar daga sama ta ji ana kokarin taɓa mata jiki.
A razane ta dago tana kallonsa.
Murmurshi ya mata yana, "Hi nawa ne farashin ki?"

Kallon kanta da yaran da ke tattare da ita tayi tana mamakin son zuciya irin na wasu mazan masu dabi'un Adams.

Ganin bata ce masa komai bane yasa shi saurin damkota ya rungemeta yana kissing dinta.
Gaɓadaya ya birkice taɓa jikinta yake ta kowanne bangare da hannu,da baki kuma yana lashe mata fata.

Duk kokarinta na ganin ta matsar da shi gefe sam ya citura domin ta gagara.

Duk da mutane na gani amman ba wanda ya nufo da niyar taimakonta.
Kowa harkarsa ya ci gaba da yi,ko da sun hada ido sai dai su kawar da kai.

Kokarin fara janye mata wandon da ke jikinta ya yi.
Karaf sai ga Adams.
Cikin Muryar sa yake fadin, "Au daman in bana nan fitowa kike neman kudi?"
Ya karasa maganar yana Dalla mata mari.

"Kin manta cewa nina siye ki? Ni nake da mallakin yin duk wani kasuwanci da ke? Wato har idonki ya yi budewan da za ki fara fitowa nema da kanki."

Sauri ya yi zai gudu Adams ya tsayar da shi.
"Kai Malam Dalla tsaya Ni ban da damuwa da kai,ko ma menene dai a biyani, in kuma ka bata ne ta bani."

Ganin hakan yasa shi sakin jiki tare da fadin, "Aa sam ban ma aiwatar da abun da nake so ba,amman tunda na lura baka da matsala,mu yi ciniki nawa ne farashinta? Sai ka dauki yaran nan muje da ita mu kwana."


Wani irin kallo Adams ya mai ya ce, "kenan za ka biya harda kudin rainon yaran? Sannan zaka dawo da ita da kanka zuwa safe?"

"Eheen ."
ya amsa

Washe baki Adams ya yi,ya yinda ya miko masa wasu maƙuden kudade ya sanya a aljihu yana karban Anushka da Anitha.

Tsabar takaici Zahra ta kasa kukan zahiri sai na zuci da ke dawainiya da ita.
Inda sabo ta saba domin wani zubin Adams da kan shi ya ke siyo mata kaya ya bata tasa sannan yaje ya ajeta inda karuwai suke zama har asamu mai tayinta.

Suna tafiya ya je ya aje Anitha da Anushka ya basu maganin barci Dukansu yadda ba za su taba farkawa ba sai safe.
Kafin shi ma ya kama gabansa.


Gabadaya Zahra hankalinta baya jikinta,idanuwanta ba wansa suke nuno mata illa 'Ya'yanta shin wani hali suke ciki yanzu? Ya suke? Me faru da su?
A iya saninta dai Adams ko kusa da shi Anitha taje hantararra yake bare kuma yanzu da aka barsu tare.
Zuciyarta na ƙuna tana jin zafi matuka sosai har cikin ranta.
Kasancewar ba yadda ta iya yasa kawai ta addu'ar Allah ya tsare mata 'Ya'yanta arai.

Da safe misalin karfe 10am kuwa ya daukota ya dawo da ita, sannan ya bata wani kudi a hannunta ta boye,tana shiga ba Adams gidan shiru,ga dukkan alamu babu kowa aciki.

Cikin tsoro ta shige ciki tana neman su Anitha.
Tana shiga kuwa ta tarar da su yashe akan kafet suna wani irin barci, ko motsi basa yi ban da numfashi da ke fita ajikinsu.

Gyara masu kwanciya tayi tana mamakin yadda aka yi suke barci har yanzu basu farka ba.

Aikin gidan ta shiga yi har wajen 12 basu farka ba,sai a lokacin Adams ya shigo.
A sanyaye take fadin, "Lafiya kuwa su Anitha basu farka ba har yanzu."

Galla mata harara ya yi yana, "daman kina tunanin zan zauna gadin yaranki ne? Lallai kin samu sake,maganin barci na masu domin bazan iya bata sabgata ba da sunan zaman yi miki renon yara tunda ba ajiye ni kikai ba."

Tafiya ya yi,ya barta tana suman tsaye kallon yaran da za ta yi kawai ta ji wani zazzafan hawaye na sauko mata daga Idanunta

Sharewa tayi,ta karasa gabansu duka ta sanya su a jikinta ta rungume.

Ta san anayin sallah amman sam bata san abubuwan da ake fadi cikin sallar ba,hakan yasa tana jin an kira sallah ta tashi tayi yadda ta ga mutane nayi amman bata fadin komai illa.
Ya Allah na rokeka ka dubeni.
Ka kawowa rayuwata da ta yarana mafita, ka ba wa rayuwarmu ma'ana ko za mu san jin dadin rayuwa.

Tana idarwa kuwa cikin ikon Allah Anitha ta farka tana kuka, can ma sai ga Anushka ta farka.

Share hawayen da ke fuskarta ta yi tana fadin, "Allah na gode ma, Allah na gode ma."

Nono ta shiga bawa Anushka, Anitha kuma ta dubo sauran abincin da Adams ya rage a kitchen ta bata.

★★UK
Friday 12/08/22

Zaune Khaleel yake acikin massallacin ana hudubar juma'a.

Malamin ya ce, "Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam yana fadin aduk lokacin da zaka kwanta kasance mai fadin (Subhannallah sau talatin da uku, Alhamdu Lillah sau talatin da uku,Allahu Akbar sau talatin da hudu) duk wanda laxumci hakan Allah zai gafarta masa, haka kuma za ka iya mika kokon baranka ga Ubangiji bayan ka kammala, Allah zai biya ma bukatun da ikon sa, sannan duk abun da ka Kasance kana yi kullum wannan shine asalin kai.

Ku kyautata kowa zato kuma sai a kyautata maku.
Ina so inyi wata magana dangane da masu kallon cewa mata kadai ake cutarwa a tarayyar aure ban da maza.
Shin kuna Sane da cewa cikin kashi dari za asamu kashi arba'in na mazan da ake cutarwa?
Meyasa ba za mu yarda ba?
Meyasa ba za mu fahimci hakan ba?
Meyasa a kullum muke kallon cewa mata kadai ake zalinta aduniya ban da maza?.
Watakila duk baku da amsoshin nan.
Amman ni ina da su.
Na farko maza sun rasa Muryar furta hakan ne saboda kowa na ganin ba mai yuhuwa bane.
A takaice ma duk wani namiji da ya fito ya ce matarsa na cutar da shi kallon sakarai za amasa ko mara wayo, a karshe ma ya xam abun dariya.
Meyasa?
Na ce Meyasa?
Ba abun dariya bane don namiji kaddararsa ta zo da cutarwa wajen mata, abun tausayawa ne kuma abun jajantawa.
Zan yi misali da nan Uk.
Yanzu in namiji ya fito ya daga murya ya ce matarsa ta dakesa ya kai kara police station maimakon a hukunta matar shi za a hukunta.
Me hakan ke nufi?
Kowa na yiwa namiji kallon isasshen da iya da gidansa sai dai ya azabtar ba dai a azabtar da shi ba.
Ba haka bane.
Sam na ce ba haka bane.
Ya kamata ace mun ba kowanni bangare dama.
Ni na yarda kuma na aminci akwai mazan da zuciyarsu ta mamaye da kunci wanda suka kasa bayyanarwa dalilin tsoro da kuma kunya.
A shawarce in dai za ka ga dariyar karamin yaro ta sanyaka jin dadi to kada ka karaya,kullum zauna cikin karfin gwiwa tare da tuna babu yanayin da zai dauwama arayuwa,kowanni yanayi ya kan zo kuma ya kan shuɗe.
Indai kamshin karamar fulawa zai iya sanyaka murmurshi to kada ka karaya da cewa watarana kamshin babba ma zai sanyaka murmurshi.

Kada ka taɓa karaya,ya yin da zuciyarka ta so shiga cikin duhu,tirsasa mata ta shiga cikin haske, duk wanda ya ji dadi a farko tabbas zai iya shan wuya a karshe,don rashin jin dadi in yazo a farko tabbas ba a fida tsammanin dadi a karshe,ka da acire tsammani kuma kada a karaya, bana da cikakken lokacin magana amman ina kara shawarta maku da ku jajirce sannan kuyi kokari kowacce rayuwa bata taba tafiya sai da kalubale,ku rike addu'o'i a komai kuma a ko ina Allah na tare da bayinsa.
Lokacin Sallah ya yi
Allah yasa mu dace."

Gaɓadaya Khaleel kara jin jawaban yake acikin zuciyarsa tamkar don shi aka yi wannan hudubar yake ji.


Ana idar da sallah ya koma office.
Aikin zanen wani Company aka basu suna tsarawa shi da abokiyar aikinsa Rumy.
Ta rike hannunsa tana nuna masa abu a computer .
Dai-dai lokacin Sarah ta shigo.

Kallon takaici ta masu duka tare da bige hannun ta akan na Khaleel ta dalla mata mari tana, "Get Out,I said Get Out." Ta ƙarasa maganar tana nuna mata kofa.

A firgice Rumy ta fice.
Sarah ta karasa daf da Khaleel.
"Ita ce ko? Wato dai ita ce ko? Owk mu je ma ina zuwa." Ta janyo hannunsa suka fice a office din.

Wani babban office ta shiga da shi tana fadin, ",Dad sau nawa zan ce kar in dunga ganin Khaleel na hulda da matan offishin nan? Daga yau , Daga yanzu na fada na kuma fada ka da in kara ganin an hada shi aiki da wata yarinya,in ba haka ba kuma, humm." Tayi kwafa kafin ta ci gaba da cewa, "kun fi kowa sannin irin abun da zan iya aikatawa, as per as na kara ganinka da wata 'Ya mace,labarin zai canja, wanda ba zai taba sauraruwa ba."

Sake masa hannu tayi tare da yin tsaki ta fice a Compaynin.

Tana fita Dad ya kallesa tare da fadin, "Na san kana hakuri, ka kara ba don ni ba,kuma ba don ita ba,Don Allah kawai,na sani ba don kudina ba kuma ba don na isa ba kake zaune da ita,kai din na Mussamman ne,mutumin kirki mai farar zuciya,kana da hakuri da kawaici matuka domin sarah ban da son kanta ba abun da ta sani, bata damu da Farincikin kowa,bata damu da rayuwar kowa ba,ina mamakin yadda ta kasance haka domin mom dinta ba......


Sai kuma ya yi shiru ya kasa ƙarasawa.

Murmurshi khaleel ya yi azahiri ya ce, "Komai ya yi farko zai yi karshe muddin an sanya tsammani."

SHIN ME KUKA FAHIMTA DANGANE DA FEJIN NAN?.

*IN GA RUWAN COMMENTS ARADUN ALLAH KO A CASU*


08103080717
Urs Xayyeesherthou
[9/3, 5:56 PM] My Number: *FREYA*


*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ko wata ba, Saƙo ne kawai na ke son ya isa inda ya dace_

PAGE-5

_*Bismillahir-Rahmanir-Rahim*_

_Allahumma munzilal kitabi sari'al hisabi,ihzamil Ahzaba,Allahumm zumhum wazalzilhum🙏🏼_

TALLAH

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar gPAGE number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!... sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_

★★

_Buy your Mtn Data At Affordable Price_
MTN
500mb = 200
1GB = 300
2GB = 550
3GB = 850
4GB = 1150
5GB = 1450

Cal. Whatsapp 07046767662
Chat on Facebook 👇Maryam-Ashner Isma'l Usman
★★

Komawa office Khaleel ya yi,ya ci gaba da aikinsa.

Sarah kuwa wajen shagalinta ta wuce kai tsaye inda kawayenta suke.

Dukkaninsu sai dare suka koma gida.
Khaleel na tashi daga Office yabi gidan Ammuh ya dauki Noor.
Kafin ya wuce gida.
Dariya Noor yake tunda ya ga Khaleel amman suna shiga gida ya ga Sarah sai ya bata rai.

Sarah ta ce masu, "Welcome."
Khaleel ya amsa da, "Thank You."

Kallon Noor tayi ta daga masa hannu tana, "Hi Baby."

Ya sunkuyar da kai ba tare da ya ce komai ba.
Ko a jikinta tai kitchen ta dauko masu abinci ta jera kan daining.

Shiga tayi tai wanka, shi ma Khaleel ya yi yama Noor kafin suka zo cin abinci.


Sarah ta ce, "Ba zan gaji da fada ma,indai kana son zaman lafiya dani ka da ka shiga sabgar wata 'Ya mace kuma kada ta shiga sabgar ka,bana so kafi kowa sannin hakan ko?"

Dagowa Khaleel ya yi ya ce, "Eheen haka kuma ke ma kin fi kowa sanin cewa bana ra ayin rayuwa irin wacce kike tsammani ko? Yadda ki ken nan kyanta ma na kasance haka,amman ina na gagara, ba ki san cewa kina cutar dani bane?"

Cikin tsawa ta fara yi masa magana, "da me nake cutar da kai? Haka ya kamata in kasance domin hakan shi zai bani damar yin rayuwa cikin 'Yanci, ba zan taba bari wata rayuwar ta maimaitu akaina ba, haka zaka zauna dani kuma ka rayu dani ."

Khaleel ya ce, "Haka zan zauna dake Amman ina ji ajikina cewa akwai ranar da zan ji karfin gwiwa,akwai ranar da zan aikatawa kaina daidai."

Cikin fushi ta tashi tana yarda kofin glass kasa ta cukumo shi tana, "wannan karya ne, ba zai taɓa yuhuwa ba,na fada ma."

Magana take tana bugun kirjinsa.
Kokarin tsadata da ya yi, karaf ta fadi kasa wannan glass din ya caketa a ciki.

Birkicewa Khaleel ya yi,yana kokarin taimaka mata.
Har ta samu.
Kamar daga sama sai ga yan sanda a gidan,ganinta a sume ga jini da Khaleel gabanta yasa suka damkesa tare da mikata zuwa asibiti, shi kuma aka kullesa da zargin cewa yana cin zarafin matarshi ta hanyar duka.


Farkawa ta yi ta ga Noor gefenta ga ta kuma a asibiti.
Da mamaki ta tambayi Doctor ina Khaleel.
Ya sanar da ita yana police station.

Noor ta dauka kawai ta fice.

Tana fita ta shiga taxi.
Ko da taje office din ta samu anata fama da Khaleel kan cewa me ta masa yake dukanta ya kasa bada amsa kuma ya kasa karyata hakan.
Aransa ya san cewa karyatawan ba ta da amfani domin in zai bude baki ya ce Sarah ce ke dukansa ba shi ya duketa ba,kallon makaryaci za amai,wasu ma su mai kallon mahaukaci.
Ya zaɓa yin shiru saboda rashin karfin gwiwar bayyanar da gaskiya,duk da cewa yana jin zafi aransa.

Tana shiga ta nemi belinsa sannan ta sanar da su cewa ba laifinsa bane,laifinta ne, duk da cewa basu yarda da hakan ba kawai sun bata shi, domin gani suke kawai tana son kwatar mijinta ne.

Mika masa Noor tayi suka shige mota.
Ta ce, "Meyasa ba ka fada masu gaskiya kan cewa ni ce da laifi ba?"

Tsaki Khaleel ya yi ya ce, "wa zai yarda? Wa zai aminta da abun da zan ce,karki yi tunanin Cewa sun yarda da abun da kika fada masu, sun aminta da hakan ne kawai don abu biyu,na farko kudi na biyu kuma kan cewa ni mijinki ne."

Matsowa tai daf da shi tana kokarin rungumarsa ta ce, "na ma alkawari zan canja,ka yi hakuri ka ji, ka san dai ina son ka ko?"

Janye jikinsa ya yi,ya ce, "hakan ba sabon abu bane da kunnuwa na suka fara ji, canjawarki sai dai awata rayuwar amman ba a wannan rayuwar ba Sarah."

Tsaki ta yi tana, "eh ba zan canja ba,ba zan canja ba,ka yi abun da ka ga dama in za ka iya." Ta fada tana daga murya.

Murmurshi Khaleel ya yi, a zuciyarsa yana fadin, "ni na sani, ko da kowa na duniyar nan zai canja ban da ke, na san kina sona, canjinki na lokaci kalilan ya canja mana rayuwa dagani har kai,ban san wacce irin kaddara ce ke bibiyar rayuwata haka ba, amman ba komai ,mahakurci mawadaci komai zai daidaita da ikon Allah."


Suna isa gida tunda Khaleel ya ga sarah ta karbi Noor kan cewa shi yaje ya yi wanka,ita ma ta yi ta ma Noor ya fahimci inda ta dosa.

Domin Sarah

Please Login or Register in order to submit comment