Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

1150
5GB = 1450

Cal. Whatsapp 07046767662
Chat on Facebook 👇Maryam-Ashner Isma'l Usman
★★
Cikin sauri khaleel ya dauketa da Ammuh suka nufi asibiti.

Likitoci gaba-daya sun tattara akanta nan aka sanar da khaleel cewa lung concer ne kuma ya riga ya yi nisa a jikinta ba tare da an farga ba.


Tana kwance akan gado Khaleel ya shigo yake sanar mata.
Girgiza kai tayi tare da rike hannunsa ta ce, "an sanar da ni lung cancer ne ga shi ni ba taba nake sha ba,giyar ma ba wani sha nake ba sai Cikin sauri khaleel ya dauketa da Ammuh suka nufi asibiti.

Likitoci gaba-daya sun tattara akanta
Suka fara bincike, ana yin test da sauran duk wani abu da ya dace.

Bayan sun gama bincike ta dan samu sauki doctorn ya tarar da su duka tare da bayanin lung cancer ne yake damunta sai dai amata Chemotherapy.

Sarah ta kalli Khaleel ta ce, "Aa i can't ba zan iya tsayawa amun ba,ni nasan Alhakin Khaleel ne yake bina Ubangiji ya jarabceni ta wannan barin ko anyi Chemotherapy Ba shi zai hanani mutuwa ba,so ba amfani."

Khaleel ya ce, "Ya zama dole wannan ba shawara nake baki ba umarni ne, za ki zauna acikin asibiti kamar yadda Doctor ya bukata har sai sunyi iya yinsu domin ceto rayuwar ki.".
Ba yadda Sarah ta iya haka ta hakuri da nufin zama a asibitin ana mata treatment.






Bayan sati biyu

Tana kwance akan gado Khaleel ya shigo

jan jikinta tayi tana kokarin mikewa ya yi saurin tallafo ta ta rike hannunsa ta ce " lung cancer ba zai barni in ci gaba da rayuwa ba,na fada maku tun farko, ni ba taba nake sha ba,giyar ma ba wani sha nake ba sai sparkling water, na tabbata talalan da Ubangiji ya mun kenan yanzu yake nuna iko da mu'ujizarSa ta wannan bangaren,na karbi Kaddarata kuma ina neman gafararKa da ta Dad dina,Ka kara mun alfarma guda ka kasance dani har lokacin da zanyi numfashi na karshe a duniya,hanuna ya Kasance cikin naka."

Tana cikin yin maganar sai ga Dad,Noor da Ammuh, da sauri Noor ya karasa wajen yana, "Mamy kar ki tafi ki barmu ni da Daddy muna sonki kin ji, Don Allah kar ki tafi,ina kin fara sonmu ke ma?"

Murmurshi Sarah ta yi ta na yi masa kiss a goshi ta ce, "Daman can ina sonku Noor ka ji, ka mun addu'a kuma ka yafe mun."

Ta ƙarasa maganar tana mika hannu wa Dad dinta.
Mika mata nasa ya yi ya karaso gareta yana, "Za ki bar duniya kina fushi dani kamar yadda mom ɗinki ta tafi? Kar ki mun haka Don Allah sarah,ki yafe mun,ki gafarceni."

Cikin kuka sarah ta ce, "ni ya kamata in baka hakuri,ni ce banyi daidai ba,mai yasa zan alakanceka haka? Me yasa ban girmama ka a matsayin uba ba? Na tabbata na tafka babban kuskure ka yafe mun,ka gafarta mun."

Gaɓadayan su kuka suke,hatta Ammuh dake gefe.

Sarah ta ce, "Ina sonku duka,ku kara yafe mun, sannan kusa aranku cewa Ubangiji ba azzalumin bawanSa bane,wannan ita ce makomata, tun aduniya."

Tana karasa maganar ta yi wani irin nunfashi wanda bata kara ba.

*Innallillahi wa inna illar raji'un* kalmar da khaleel ya shi ga furtawa ke nan.

Noor ma na ganin Khaleel na yi ya kama yi yana shafa fuskar Sarah tare da share mata hawaye.

"Rayuwar Sarah ta kare saura ta mu,a yanzu mune abun tausayi ba ita ba." Ammuh ta fada tana share hawaye tare da daukan Noor.


★★a kwana a tashi sati daya cir da barin sarah a duniya.

Dad ne ya kira khaleel office tare da fadin, "in baka manta ba, sarah na da rabin kaso a Compaynin nan,bayan ita kuma na ba Noor ma nasa, wanda ta haɗa take lura da su duka biyun,tun a lokacin na so baka kasonka ka nuna cewa baka so, a yanzu kam ya zame maka wajibi in mika maka dukiyar matarka da ɗanka domin komai ya koma mallakin Noor, Noor kuma mallakinka ne,ko me kakeso ka je ka yi da shi wannan zabinka ne, ga takardun komai nan na tsara hannu kawai za ka sanya."

A lokacin Khaleel ya sa hannu yana, "Na gode sosai Dad Allah ya saka da alkairi."

Albarka ya sanya masa, nan take daga Office Khaleel ya nufi gidan Ammuh ya sanar da ita komai.

Tayi farinciki Sosai da jin hakan ta ce, "Ibrahim ka yi abubuwa masu kyau dayawa arayuwa, haka kuma ya kara zama dole a yanzu ma ka kara yin abubuwa masu kyau,ta hanya mai kyau,kuma mai bullewa,Kasan me nake magana akai?
Ba zaka taba iya siyan hanyar da zaka kasance ba, kuma ba za ka taba iya siyan soyayyar da zaka kasance ciki ba, har sai kayi taimako."


Khaleel ya ce, "In sha Allah Ammuh ba zan taba mantawa da hakan ba."

★★
A kwana a tashi rayuwa ta sauyawa Khaleel da Noor tamkar an ciro su daga keji.

Dadyn Sarah kuwa ya ce wa Khaleel zai iya ci gaba da aiki in yanada ra ayi ko ya bude nasa companin.

Kullum yana tunanin tsare tsaren da zaiyi tare da gina abun da zai taimake sa kuma ya taimaki al'umma, hakan yasa ya ci gaba da zuwa Officen din kafin ya kammala komai.

Da safe yana shiri zasu fita har sun je kofa Noor ya ce, "Wait Dad, *Hasbiyallah La'ilaha ilallahuwa alaihi takwalna wa huwa rabbul arshil azim* 7× In The Morning Also In The Evening, You forgot it right?"

Murmurshi Khaleel ya yi,ya rike hannun Noor suka zauna yana, "Eheen good boy,Na Gode da tunatarwa yaron kirki."

Sai da suka yi sau bakwai din a tare kafin suka tashi ya fara mika Noor Skul kan in lokacin tashi ya yi za a kaisa gidan Ammuh,sannan ya wuce office.


Yana isa office ya tarar an kafa dandalin gulmarsa ana yi ba tare da sun san ya zo ba banda zagi ba abun da suke.

Dayansu ya ce, "ni fa daman tun farkon zuwan sa Compaynin nanin na fahimci yana da son duniya amman a munafurci yake abunsa yoo ba dole ya jure wulakanci ba tunda daman yasan dole zai samu kudi, na tabbata don kudi ya zauna da ita har ta mutu ga shi yanzu ya kwashi garabasa amman tsabar son duniya ya kasa barin Compaynin nan muma mu sarara kowa ya zo fa sai ya ce ya fi so ya jagoranci zanensa na tsanesa wallahi."


Karaf dayan ya ce, "burinsa ya cika ya kwashi kudin ai yanzu ko da bai bar Office dinnan ba,mu zamu kora shi, haba ace namiji mace na juyasa kamar waina kai ma kasan ai ba a banza ba,kudi ne ke aiki kawai."

Murmurshi Khaleel ya yi ya karaso inda suke yana, "Most people won't ever know your full story
They will know a version of it.
Don't live your life chasing people to understand you.
When you ware made to be different And Anybody who blieves lies about you, before even hearing your side of the story,was Already looking for way to be against you."
Dukan su kasa dogawa su kalleshi suka yi, gaba-daya jikin su ya yi sanyi tamkar an dauke ruwan sama.

Yana karasa maganar ya yi Murmurshi ya wuce.

★★Zahra na sauri Zata mikawa Madam Zuby kayan abincin da tasa ta ta dauko fitowan da za ta yi Sumy ta sa mata kafa,ta kifa da baya ga Anushka na goye.
Wata irin kara Anushka ta.....



08103080717
Xayyeesherthou
[9/3, 5:56 PM] My Number: *FREYA*


*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ko wata ba, Saƙo ne kawai na ke son ya isa inda ya dace_

PAGE-8

_*Bismillahir-Rahmanir-Rahim*_

_Allahumma munzilal kitabi sari'al hisabi,ihzamil Ahzaba,Allahumma zumhum wazalzilhum🙏🏼_

TALLAH

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!... sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_

★★

_Buy your Mtn Data At Affordable Price_
MTN
500mb = 200
1GB = 300
2GB = 550
3GB = 850
4GB = 1150
5GB = 1450

Cal. Whatsapp 07046767662
Chat on Facebook 👇Maryam-Ashner Isma'l Usman
★★

Sake wani gigitaccen kukan

Cikin dimaucewa Zahra ta tashi tana Ciro Anushka a baya, Gaɓadaya ta kwarjane ta ji ciwo, ga hancinta ban da jini ba abun da ke zuba.

Da sauri Madam Zuby ta karaso tana karban Anushka suka yi asibiti.

Gaɓadaya Zahra ta dimauce ta rasa meke yi mata dadi, Sumy kuwa ko ajikinta tafiya ta yi ta ci gaba da aikinta,yayin da sauran ma'aikatan suka tsaya jimami wasu kuma suka bisu asibitin.


Cikin ikon Allah ake yi ma Anushka Treatment jini ya daina zuba,aka mata allura sannan suka dawo.

Madam Zuby ta cewa sumy, " Shin ke bazaki je ki duba yarinyar bane? Ke kika bigeta amman ko kalmar hakuri banji kin furta ba,bare duba ta."


Bata rai tayi ta ce, "Madam zan je ina so ne in gama aikin da nake."

Madame zuby na tafiya, sumy tayi tsaki ta ci gaba da aikinta.
Tana fadin, "A son raina ma da yarinyar mutuwa tayi har ma uwar duk sun zo sun takura mu."


Zaune suke duka suna aiki wata kawar madam Zuby ta zo gunta .

Ta ce, "Daga asibiti nake wallahi, maganar jan da hokorannan nawa suka yi yana damuna,na kasa hakura ko za a dace ,har kunyar shiga cikin mutane nake."

Kafin Madam Zuby ta yi magana karaf Zahra ta ce, "In ba damuwa zan iya taimakonki?"


Murmurshi ta yi,ta ce, "Why Not."

Zahra ta je ta tsinko mata aloevera ta ce, "Wannan ruwan nasa zaki matsa ki sanya akan toothBrush dinki sai ki wanke bakin ,ka da ki damu da batun jini, domin ba zaiyi ba, kuma ko da ma ya yi ba wata matsala,in sha Allah hakorinki zai yi fari tas."

Nan take Anty Asma'u ta ce, "Ah wannan ai ba sai anjima ko gobe ba, anan tun yanzu zan gwada gogewa daman da toothBrush din da na siya a asibiti bara in gwada da shi."

Kamar wasa kuwa ta shiga toilet din wajen abincin, ta wanke bakinta tas da ruwan aloevera, kamar a Mafarki har tun ayi na farko har yanayin bakin ya fara sauyawa ya dan yi kyau.

Tsabar farinciki aguje ta fito tana rungume Zahra, ta kasa rufe bakin tsabar murna ta ce, "ku san shekara biyar ina faman neman mafita amman yau cikin kankanin lokaci kin kawo mun hanyar warware matsalata, , tun a yi daya na ga canji,ina ga inna ci gaba da yi a kullum kuma?Allah ya rayaki ya raya yaranki, ya biya miki dukkanin bukatunki na alkairi,na yi matukar farincikin zuwa wajen nan yau fiye da kullum."


Madame zuby ta yi Murmurshi ta ce, "tabbas Zahra ta ci sunanta ,haske ce ako ina domin zuwanta ban da haske ba abun da ke karuwa a wajenan, yanzu dai in sha Allah case close madam Asmy hankali ya kwanta na tabbata kika daurewa yin hakan sai an sha mamakin yadda haƙoranki za su yi haske,ba ma ke ba,ni kaina zan fara domin kogi bai ƙi dadi ba."

Dariya ta yi ta ce, "Sosai ma wallahi kamar anmun wata babbar kyau,ke sai na miki kyauta ma in sha Allah zuwa gobe,yanzu zan yi sauri in karasa gida saboda yan night School Study Center yau zan fara daukan sabin dalibai kuma nasan tun yanzu za a fara zuwa cika Form,byee oll see you tomorrow."

Har ta tafi ta kara dawowa ta ce wa Zahra, "Thank you so much Daughter."


Bayan ta tafi Zahra ta ce wa Madam zuby, "Madam makaranta ce take da ita?"


"Eh Makaranta ce amman ba norml school jami'a ko secondry ba, makaranta ce ta koyarda wa inda suka girma ba tare da sunyi karatu ba, basu san komai, Madam Asmy bata son ta ga mutum ba karatu Mussamman mata, bata so ta ga ana tozarta su don basu yi karatu ba,hakan yasa ta yanke shawarar bude Makarantar yaƙi da jahilci (Night School Study Center) Amman da dare ake yi from 9 to 12 , ana koyarda maza da mata karatu sosai wanda in mutum ya kammala ma zai iya ci gaba driect saboda government Approved ce,mutane da yawa suna zuwa nan Sumba Island zama don Makarantar kawai."


Zahra ta ce, "Nima zan iya shiga? Ina so nayi karatu ko ba don kaina ba, domin su Anitha da kuma taimakon Al'umma in hakan zai yiwu."

Madame zuby ta ce, "me zai hana? Zaki iya ni da ke ma gobe za mu je sai kiyi registration daman goben zaki fara karban albashi, karfe 9 lokacin ba ki da wani aiki daman sai kije school dinku su Anitha za ana lura da su in sha Allah."

Ba karamin dadi Zahra ta ji ba, domin duk da kasancewar sunan school kawai take ji abaki ba ta san ya take ba,ba karamin so da kaunar kasancewa cikinta take ba.

Washegari kuwa bayan sun gama aiki Madam Zuby ta dauki Zahra suka nufi gidan Anty Asmy wanda anan school din take.

Suna zuwa kuwa suka tarar mutane sosai anata registration.
Anty Asmy taji dadin ganinsu Sosai Mussamman da taji batun cewa Zahra ce ta zo registration.

Ko biyar bata karba nan take aka mata.
Ko da aka zo mata interview ta fannin Turanci ba a sha wuya sosai ba, saboda tana dauka lokuta da dama in Adams nayi, Shiyasa hakan yazo mata da sauki.


Littafan da za'a koyar da su Anty Asmy ta haɗa mata tare da sanar da ita bayan sati biyu za su fara ɗaukar darasi, godiya suka yi suka tafi zuciyar Zahra cike da farin ciki, tana son karatu sosai, don haka ta ƙudirta a zuciyar ta zata jajirce sosai tunda ta samu dama dole zata yi amfani da ita.


★★Khaleel zaune yana aiki a system, Noor kuma yana kallo A tablet dinsa.

Wayarsa ce ta fara kara ya na dubawa ya ga number Xavier .
Murmurshi ya yi a zahiri kafin ya daga yana, "Hello Friend yau wacce sa'a na taka ne?"

Xavier ya ce, "Kai dai ko, ba wani batun sa'a amman afwa ban kira gaisuwar madam ba sai yau aiki ya yi yawa,ya karin hakuri? Allah ya jikanta ya gafarta mata."


"Alhamdu Lillah, mun gode Allah."khaleel ya fada


Xavier ya ce, "Ma sha Allah ana nan ana shan barcin fama ko? ya Yarona kuma?"

Dariya Khaleel ya yi ya ce, "barci ka san ba fashi ai,yanzu ma yaronka ne ya hanani wai muna Lesson."

Noor ya ce, "Dady abani Uncle mana."
Mika masa wayar khaleel ya yi, Noor na karba ya ce, "Uncle na yi kewanka yaushe za ka zo? Ka tawo mun da irin uniform dinka ka ji, da takalmi,da agogo da turare fa."

Dariya Xavier ya yi yana, "Oh Yarona kullum surutu karuwa yake,to shikenan zan kawo ka ji in sha Allah, ka kula da kanka kuma ana karatu sosai da kyau, Gudnyt byeebyee."

Noor ya ce, "Ok Byeebyee unlce kar ka manta da addu'a in zaka kwanta barci dady ya fada mun ba kyau barci ba addu'a kuma ba hali bane mai kyau hakan zai sa mutum ya yi mafarkin Dodo, Byeebyee."

Har cikin ran Xavier yana matukar kaunar Noor, Mussamman dabi'unsa da suka kasance na daban cikin yara.


Khaleel ne ya karbi wayar Xavier ya ce, "Friend yau ba wani guzirin da za abani ne ko da yake kace ka yayeni."

Dariya Khaleel ya yi ya ce, "Eh mana yanzu kam ai sai dai ka koyar dani ba dai in koyar da kai ba,amman kar ka ce nama rowa ,ka wata addu'a da zaka karanta in wani abu ya faru da kai, *Allahumma La Sahla Illa ma ja'altahu sahla,wa anta taj'alul hazna iza shi'ita Sahlan*."

Murmurshi Xavier ya yi ya ce, "Barakallahu fikha Abokina, Maddallah da kai,ina farincikin kasancewa da kai a kullum domin kai din alkairi ne gare ni."

"Umm baka da dama Friend ,na san ba abun da yafi sadaukarwa a duniyar nan cire komai arai,ya yin da duhu yazo yi sauri ka kawar da idanunka tare da hango haske mafi inganci, Allah zaba mana rayuwa mai albarka,ni dai ina fada ma na kusa maka aure kowa ma ya huta,don yanzu ka wuce gauro ka zam tuzuru." Khalil ya fada


Dariya Xavier ya yi yana, "Ey aure ko? Da saura fa,har yanzu ban ga wacce ta dace da tsalelen saurayi kamata ba, sai na zaɓa na dirje eheen amman ka ce za ka mun aure ai za ayi abun kunya don guduwa zan yi in barka da matar."

A tare duka suka yi dariya.

Khaleel ya ce, "ka tsaya wasa ka ga, serious aure zan ma kuma dole ka zauna."

Da haka suka rabu ana wasa da dariya.

_Xavier abokin Khaleel ne, tare suka tashi har suka yi karatu shi ya karanci Law, Khaleel kuma Art suna kammala ya fara aikin MI6 (Military Interligent service) Christian ne Xavier amman kasancewar sa da khaleel ya sanya masa sha'awa da muradin musulunci, khaleel ya yi amfani da wannan damar wajen kara kwadaita masa dadi da inganciin musulunci amman har yanzu Allah baiyi ya musulunta ba, Duk da cewa sanadin Khaleel ya san abubuwa da dama da suka shafi Addinin Musulunci Sosai,Sallah har ma da addu'a, wanda hakan yana masa amfani sosai wajen aikinsa, lokuta da dama ba a iya bambamce cewa shi musulmi ne ko akasin hakan domin ya kan yi amfani da kowacce siffa so,a kullum buri da fatan Khaleel ya ga ya musulunta, Mussamman yadda ya kasance da kyawawan dabi'u_

★★Ruwa ake sosai tamkar da bakin kwarya, Noor ya ce, "Gud.......
Kafin ya karasa aka yi wata tsawa mai hargitsa kwakwala.

Ya ce, " *Subhana Man Yusabbihu Ra'adu Bihamdihi,wal mala'ikatu min khifatihi*."

(Wannan ita ce addu'ar da ake yi ya yin da aka yi tsawa cikin ruwan sama)

Khaleel ya kalli Noor Ya ce, "Ma sha Allah daz my boy,Gudnyt ayi addu'a kar amanta ama Mom addu'a Allah ya haskaka kabarinta ko?"


Noor ya ce, "In sha Allah Dad,Ina sonka ka ji,u are d best papa in the world." Ya karasa gaban Khaleel ya masa yana yi masa kiss
Kan ya tafi yana, "Byeebyee,Gudnyt."


*Lemme See Ko akwai masu zafafan sharhi yau😤*


08103080717
Urs Xayyeesherthou
[9/3, 5:56 PM] My Number: *FREYA*


*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*LABARI DA RUBUTAWA*
_Aisha Sani Abdullahi_
_*(Xayyeesherthul-humaerath)*_

_*TSOKACI:* Labarina Kirkirarrene ban yi shi don cin zarafin wani ko wata ba, Saƙo ne kawai na ke son ya isa inda ya dace_

PAGE-9/10

_*Bismillahir-Rahmanir-Rahim*_

_Allahumma munzilal kitabi sari'al hisabi,ihzamil Ahzaba,Allahumma zumhum wazalzilhum🙏🏼_

TALLAH

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!... sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_

★★

_Buy your Mtn Data At Affordable Price_
MTN
500mb = 200
1GB = 300
2GB = 550
3GB = 850
4GB = 1150
5GB = 1450

Cal. Whatsapp 07046767662
Chat on Facebook 👇Maryam-Ashner Isma'l Usman
★★
★★a kwana a tashi yau sati biyu cir tayi ,adaren ranar Zahra za ta fara attempting class.

Da safe bayan ta gama aikinta ta yi ma su Anitha wanka, ta shirya su tsaf da kayan da madam Zuby ta basu.

Sumy ce ta fito daga kitchen jiki ba laka ta karaso gaban Madam ta ce, "Ma...

Sai kuma ta kasa karasa maganar ga alamun tsoro fal fuskarta.

Madam Zuby ta ce, "Ya dai? Lafiya kuwa? Kiyi magana mana Sumayyah."


Cikin in ina Sumy ta ce, "Maaa...dam wallahi Allah ba da sani na bane Allah ku..wa..."

"Ki fada mun mai ya faru mana mene ne wai?" Madame Zuby ta fada


Sumy ta ce, "Ruwan Shinkafar da nasa ya yi yawa ta fara caɓewa, kuma,kumaa Soup din ma gishiri ya zarce mun."

Hanu aka Madame zuby tasa tana furta, "Innallillahi wa inna illar raji'un, yanzu kina nufin Shikennan na yi asarar abincin yau? Shikennan sai dai a kara komai sabo? Allahumma ajirni fi musibatiy."

Zarah ta ce, "Aa Madam muje in gani watakila za a iya gyarawa ba tare da anyi asara ba."

Kitchen din suka je duka, Zahra ta duba Shinkafar ta ga ta fara caɓewa.
Biredi ta dauko irin mai yanka yanka dinnan ta jera guda hudu a saman tukunyar da ke abincin da yawa kan ta rufe.

Ta duba miyar ta dandana gishiri sosai ya fito,ta dauko dankali ta fare guda biyu ta jefa cikin miyar ta barsa ya ci gaba da tafasa.

Gun Shinkafar ta dawo cikin minti biyar har ruwan ya kafe duk ya koma jikin biredin ta ware kamar ba ita ba.

Miyar ma aka cire dankalin tana dandanawa duk babu gishirin ya koma ya tattare cikin dankalin.

Rungumeta

Please Login or Register in order to submit comment