Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

~Boss Lady~


*page* *39 to 40* 😁


jiki na rawa ta ƙarasa gabanta cike da tsoro tace" husanna ina waya ?
Shiru tayi tana mazurai, hannu jahad tasa ta shaƙo wuyan rigar dake jikinta cikin matsanancin tashin hankali ta sake cewa "tell me where did you kept it ?
muryar na rawa husanna tace" wani kyankyaso ne ya hau mun saman kaine shineee...sai wayr ta faɗa cikin....'
"Cikin Uban me !? jahad ta tambaya cikin daka mata tsawa,
duk tabi ta gama firgita tata cikin takura tace "cikin ramin"
Aikuwa rai a tsananin bace jahad ta shiga kai mata bugu ta ko'ina, nan suka shiga dambe, faɗa ya katse me a tsakaninsu kai kace basu son junansu,
A ƙarshe jahad tasake ta cikin tsananin ƙunar rai tace"shikenan kinyi farin ciki ko? kada kiyi tunanin ina bakin ciki ne don kin jefa waya, ina bakin ciki ne saboda kinyi mana babbar asara, taimakon da zamu samu na kuɗi a siya miki magani mun rasa, sannan ƴar uwarmu ma mun rasa ta ! saboda daga ni har ke ba wanda ya riƙe numbar da take kira, sannan ita inta kira zata ji waya a kashe kinga shikenan tamu ta ƙare.....'
Zuƙunnawa tayi tare da fashe wa da matsanancin kuka, itama husannar koma tayi ta tsaya jikin bango tana shesshekar kuka jin jahad tace sun rasa ƴar uwarsu SEHRISH
A cikin wannan yanayin mara daɗi tsohuwa ta same su, shigowa tayi hannunta ɗauke da bakar leda wadda fura ce aciki ta samo musu don su sha tun safe rabonsu da abinci har izuwa yanzu da ake ta faman kiran sallar isha'e
hankali a tashe ta ƙarasa inda jahad take tana faɗin"lafiya meya faru ƴa'ƴan ne me kke wa kuka? Nasan yunwa ce ku kwantar da hankalinku gashi nan na samo mana ƴar fura musha,'
Jin wannan maganartata yasa jahad ƙara sautin kukan nata, tana kuka tana magana "ba wannan zararriyar bace nasamu sehrish tace mu tura mata acct number, nashiga gidan makwabtan mu wurin mamee nace taban nata acct number ɗin, sai da na anso ina shigo wa nasamu husanna wai ta jefa wayar cikin masai,"
Jin wannan maganar yasa tsohuwa sakin ledar furar dake hannunta, tashiga tafa hannu tana faɗin "Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un shikenan ae kun gama dani shekara 10 kenan wayarnan da ita nake lallabawa ashe kune ajalinta, kun kyauta,'
tana faɗin hakanan ta shige cikin ƙuƙuƙun ɗakin nata ta rufo kopa, tunda suka ga hakan yatabbatar masu da cewa ran tsohuwa ya bace, saboda bata taba yi musu haka ba,
Gashi ɗaki ɗayane a gidan ɗayan ɗakin ya rushe sakamakon ruwan sama da akayi,
ga wani irin sanyi a wajen nan da nan jikin husanna ya soma kakarwa, hankali a tashe jahad ta tashi daga zukunnawar da tayi ta tunkare ta,
"zo muje mu lallashe ta tabuɗe mana ɗakin mu kwanta waje sanyi,"
Haka suka je bakin kopan ɗakin sukai ta kwankwasa wa amma tsohuwa tayi shiru babu alamar zata buɗe,
A ƙarshe sai dai suka rungume junansu suka ƙanƙame juna saboda sanyin dake akwai, wannan abun ya tuna musu da wani lokaci daya shuɗe a rayuwarsu mara daɗin ji 😭
Rashin gata baiyi ba a duniya

Story by (Hafsat Bature)

Rashin kwanciyar hankali yasa ko kwakkwaran bacci bata samu ba a daren jiya, tunaninta meyasa samu wayar tsohuwa ba'a samu tayi tarying amma swich off, hakan na matuƙar tayar mata da hankali tsoronta kar ace wani abu ya same su su duka,
Jiki a sanyaye ta kammala shiryawa ta wuce kitchen wurin azmi,
"Good morning aunty azmi"
ta faɗa tana kallonta, azmi dake faman gyare gyare a kitchen ɗin tace "morning baturiya hope u slept well"
yar dariya sehrish tayi ta shiga daga ciki tana faɗin "dame zamu fara ne?
Azmi tace "yau fa akwai manyan baki da zasu zo,"
dafe ƙirji sehrish tayi kamar wadda taji mugun abu tace"suwa!"?
dariya axmi tayi ganin yadda ta ɗan raxana,
"suna da yawa wasu yau zasu zo wasu sai gobe, daga ciki akwai chief of army staff wato Abban su junaid wanda zai dawo daga ƙasar chaina, amma shi gobe ne zai zo yau dai wasu daga cikin manyan ƴa'ƴansa dake other states ɗin zasu zo domin tarbarsa,
Da buɗan bakin sehrish sai cewa tayi "Babban yaya fa shi bazai zo ba,"?
girgiza kai azmi tayi tace"oh shirt! ni wannan babban yayan da kike ta faman zumuɗin gani bansan dalili ba,'
"Aunty azmi it's just a question ba wani abu ba, naji kince manyan ƴa'ƴansa shiyasa na tambaya,' ta ƙara maganar tana wasa da yatsun hannunta,
Kafin azmi tace wani abu junaid ya shigo da sallama, nan fa sehrish ta hau satar kallonsa yayi fes abunsa yayi dressing cikin suit black colour
A cikin zuciyarta tace "wai madarar kyau"
"Morning azmi how was everthing" ya faɗa shima yana ɗan satar kallon sehrish,
Azmi tace "barka dai komai lafiya kana buƙatar wani abu ne"_?
sam baiji me tace ba domin idonsa nakan sehrish wadda ita ma shi take kallo,
Sai da ta maimaita da cewa"junaid ina magana"?
a ɗan firgice ya mayar da kwayar idonsa kan azmi da ɗan murmushi yace" am dama nazo na sanar miki da cewa sai gobe jirginsu abba zai sauka, sannan jibi babban yaya tare da marshall Omar da Captain suma zasu taso, "
Saboda tsananin zumuɗi sehrish tasa hannu a baki irin mamakin nan ga wani farin ciki daya baibayeta kai kace tasan shi ne,
Junaid ya ci gaba da cewa "kada kusha wahalar yin aiki, akwai ma'aikata da zasu zo daga company zasu tsara komai ku hutu kawai,'
yagama faɗan hakan tare da juyawa ya fice,
Ita kanta azmi murmushi kawai take yi ba don komai ba sai don ta ƙosa sehrish taga wanene wannan babban yayan da take ta zumuɗi a kansa, tayi tunanin ganinsa abune mai sauƙi , mutumin da saboda tsabagen zafin rai ko magana bayayi saboda abu kaɗan ke 6ata masa rai,
"Yanzu hankalin ki zai kwanta tunda kinji cewa babban yaya zai dawo ko "?
murmushi sehrish tayi ita kanta tana mamakin wannan zumuɗin nasan ganinsa

tunda aka sanar da su cewa Babban yayansu zai dawo next tomorrow saboda kiɗima ranar ko breakfast basu ci ba, ba inda suka je kowa zullumi yake yi ba don komai ba sai don tsoransa,
a bangaren su twins kuwa suna a bedroom ɗinsu sai faman safa da marya suke yi yau ba harka, duk hankalisu ya tashi su sunsan mezai faru a zuwan Babban yayansu,
cike da damuwa Ayaan yace"gsky jahan am gonna cut my hairs today if not babban yaya will accuse something about us am afraid of him seriously,"
Ya faɗi hakan tare da zama a side bed ɗin yana kallon Jahan wanda ke faman zarya frm well to well yana haɗe hands ɗinsa yana naushin su atare,
"just feels like to cry wlh, Ayaan i dont wanna see him, am really scared of his eyes, mutumin da ko haɗa ido kukayi dashi sai gaban ka ya faɗi, we must find the solution,
cikin damuwa ayaan yace "what is the solution now ? do u ave any plan?
wuri jahan ya samu ya zauna gefensa tare da cewa "yanke gashi da kace zaka yi is not the solution, sbd shima yana tara doguwar suma ,ayaan kasan bama iya rayuwa even one hour without having sex , and if he finds out about it we are already doomed,"
Zugum su kayi kowa na tunanin yadda zasu 6ullowa lamarin,
Can Jahan yace "me zai hana mu kama room a hotel ? when ever we are horny we can go there hakan yayi ?
Jinjina kai Ayaan yayi ganin jahan ya kawo shawara ruƙo hannunsa yayi tare da cewa "thats why i love u so much cos you're very smart hakan yayi,'
murmushi jahan yayi yana kallon cikin idonsa ya ce "since i found the solution ynx sai muje mu ci abinci ko? ko ba kajin yunwa?
Ayaan ya ce "Am starving too let's go nd ave something to eat"
A tare suka fito
Tabbas jin zuwan baban yayan nasu ba ƙaramin kashe musu jiki yayi ba domin duk wanda yasan yana aikata ba dai dai ba neman takansa yake yi,
cleaners ɗin da aka ɗauko daga company sun hallara kuma sun fara gudanar da aikinsu, wasu parts aka buɗe wanda ita kanta sehrish batasan da zaman su a katafaren gidan gidan ba ,
ta dai san akwai wuraren dake a rufe bata taba ganinsa a buɗe ba, kamar other parlours ɗin dake a gidan amma yau ko'ina buɗe sa ake yi muraren saboda gyara,
Bayan sun kammala aiki ta shiga neman junaid saboda ta damu da rashin su husanna tana damuwa sosai,
ganin sai faman zarya take yi daga upstair zuwa down ga ma'aikata sai fama aikace aikace suke,
"Zonan sehrish" azmi ta kira ta alokacin itama ta shigo babban parlourn ita kuma sehrish tana saukowa down ƙarasawa tayi gaban ta tana faɗin "gani aunty azmi"
Azmi tace"lafiya kike ta faman yawa ce yawace baki ganin ma'aikata na aiki ne"? ta tambaya tana kallonta,
"Junaid nake nema ne" ta bata amsa, azmi tace i don't think yana kusa ki koma ɗakin ki idan ya dawo i will inform you,'
Amsawa tayi da toh sannan ta wuce izuwa room ɗinta, kasa zama tayi sai faman safa da marwa take burinta taji wani hali su husanna suke ta damu da son jin hakan,
tana cikin wannan zagayen ta dinga jin jiniyar shigowar motoci kamar hauka, har sai da gabanta ya faɗi rass, cikin sauri ta ƙarasa gaban window ɗinta ta janye curtain ɗin jiki ta zuge glass ɗin tana leƙen abunda ke wakana a waje,
motoci ne na sojoji ke ta faman antayowa ciki, sanye cikin uniform ɗinsu, kowanne hannunsa sanƙame da jibga jibgan bindigu, wani irin miyau ta shiga haɗiye wa saboda tsananin tsoro, kamar mara gasky kamar ita suka zo kamawa,
Sakin labulen tayi ta koma ciki ta ci gaba da zagayen tana zare ido, abubuwa dayawa suna zuwa mata aranta damuwarta shine yaya zatayi idan suka gane cewa ita mace ce? tana tsoran waɗanda zasu zo musamman abbansu chief of army staffs da kuma surgeon general rafayet ga marshall Omer tare da Captain Adams da zasu zo daga outside country , gashi taji hada sauran ƴa'ƴansa waɗan da batasani ba, wasu ma anan garin suke wasu kuma na other states,
Yinin ranar cikin fargaba tayi shi, ga tunanin wani hali su husanna ke ciki ga kuma tunanin zuwansu Abban sojoji,
A bangaren junaid kuwa ya jira yaga ko zasu turo masa account number yaji shiru ba text message a time ɗin yayi niyar ya tura masu 300k duk da baisan ko su wanene ba, amma yana ji aransa cewa siblings ɗin Sehrish ne,
Jahad & Husanna
Abunda ya faru daren jiya A waje suka kwana, cikin dare jikin husanna yayi tsanani sosai saboda weather din akwai sanyi and she's athmatic, haka ta rinƙa tari jikinta har jijjiga ya ke yi, hankalin Jahad ba ƙaramin tashi yayi ba, tana rungume a jikinta, wani irin ajiyar zuciya taji husanna na saki wanda bata ta6a jin irin hakan ba, a hankali ta kira sunanta "Husanna!"_.
Cikin wata irin galabaitacciyar murya tace"mutuwa zanyi baki ji yadda ni ke ji ba, dan Allah idan kin haɗu da sehrish ki ce mata ta yafe min ke ma ki yafe min nasan najima ina 6ata maku rai.......'

tana gama faɗin hakan rai yayi halinsa 😖
*🔥ABBAN SOJOJI🔥*

_the father of soldiers_


_Story by_ _Hafsat Bature_💓

*Boss Lady*


*page* *41 to 42*

Theres some typing errors like spelling mistakes🥱its not edited just manage 🤨



_ Sulalewa tayi daga jikin jahad ta yi ƙasa luuuuuu....wani irin ihu jahad ta saki cikin tsananin tashin hankali tabi ta ƙasan inda take kwance a baje rai hannun Allah,
"Kada kiyi mun haka ƴar'wa pls stay alive me kike so na faɗa ma sehrish? In ki ka tafi ni kuma ya kke so nayi da rayuwata? narasa sehrish ynx ke ma zan rasaki...' cikin ƙunar rai tayi maganar tana kallon face ɗin Husanna wadda ke fidda numfashi sama~sama idonta na ƙoƙarin rufe wa gaba ɗaya,
Fashewa tayi da kuka saboda tsoran karta rasa husanna, hannu husanna ta miƙa tare da riƙo nata dakyar ta iya buɗe baki tace "Idan kika rasa ni ba akwai Allah ba,'
Wannan maganar tasa jahad bin husanna da kallo bakomai ne ya faɗo mata arai ba face mahaifiyarsu haka kullum ta kece musu aduk lokacin da suke tunanin zasu rasa ta sai tace,
"Idan kuka rasani ba akwai Allah ba, shine gatan kowane bawansa, shi zai tsare ku ya kare mun ku ba wanda ya isa ya taba ku batare da izninsa ba, yana sane daku,
tuna wannan yasa jahad jin komai ya dawo mata sabo fal azuciyarta
Jiki a mace ta kwanta itama a ƙasan cikin ƙasa a side ɗin husanna ta ɗan ruƙo hannunta a haka suka kwana, ga sauro ga sanyi ga tsoro saboda gidan ba ƙopa,
tun da safe da jahad ta farka cike da tsoran kar ace husanna ta mutu, amma tana buɗe ido taga akasin hakan , samun ta tayi zaune hannunta ɗauke da kofi ta dama furar da tsohuwa ta kawo masu jiya wnda ta yarda a ƙasa, sai sha take yi hankalin ta kwance,
Cike da tsananin farin ciki tace "shashasha ashe kina nan ! I thought u ave already gone, "
murmushi husanna tasaki tare da cewa "Ba kin ce kar na tafi na barki ba that's why i stayed alive,'

yar dariya jahad tayi kafin tace"nima yunwa nake ji dan Allah ki rage mun furan wai yaushe ma har ki ka tashi ki ka dama ta? bayan jiya ki ka ce mun mutuwa zaki yi?
"Lokaci na ne baiyi ba in yayi zan tafi,' husanna ta bata hamsa tana idasa sipping porridge ɗin da takai a bakinta,
dakyar jahad tasamu ta rage mata furar, itama ta sha sai da cikinsu ya ɗanyi nauyi sannan suka tuna basu yi sallar asuba ba, ga tsohuwa har time ɗin she didn't open the door,
Haka suka tashi su kaje su ka dauro alwala suka tsaya a kofan ɗakin da tsohuwa take suna cewa "dan Allah ki buɗe mana ko sallaya mu ɗauka muyi sallah, kuma tun jiya muke baki haƙuri amma kin ƙi buɗe mana kopan,
Jin shiru bata alamun motsi balle tayi masu magana yasa suka wuce gidan makwabtansu don su gudanar da sallar acen,
haka suka ruƙe hannu cikin na juna suka fice gidansu mamee, bayan sun kammala gudanar da sallarsu, mamansu mamee ta kawo musu kosai da kunu a plate saboda ta lura da yunwa a cikinsu, nan suka samu wuri suka zauna saman ledar ɗakinsu suka hau ci, ita mameen ba bata gidan ta tafi school,
After each 30 mins sai sun leƙa sun ga ko tsohuwa ta buɗe masu ƙofa but still a datse ta ke,
Abun ya wuce na hankali har ƙarfe 2 na rana tayi time ɗin mamee ta dawo daga school nan ta same su jugun, sai da tayi wanka taci abinci sannan ta zauna kusa dasu saman tabarma wadda mamansu ta shimfiɗa musu saboda ciki akwai zafi,
kallonsu tayi tace"meya faru ne ? laifi ku ka mata ko har tayi fushi haka? Jahad ta nuna husanna da hannunta tare da cewa "gata nan ita ce ta jefa mata waya a cikin toilet tun daga lkcn ta shike ɗaki ta datse tun daren jiya zuwa ynx"
murguɗa baki husanna tayi tace"ae ni ma ba laifina bane kyankyaso ne mai fiffike ya hau mun kaina shine na firgita har wayar ta sulale cikin masan,'' ta ƙare maganan tana hura hanci,
Jinjina kai mamee tayi kafin tace"gsky bana tunanin cewa tsohuwa zata iya yin wannan fushin saboda ƙaramar waya nokia harta rufe ɗaki tun yesterday night up to now bata buɗe ba, tabbas there's something behind we've to find it but firstly ya kamata mu fara trying na buɗe kopan,
tana cikin wannan bayanin mamansu ta fito daga kitchen tana cewa "nima ina tsammanin hakan, saboda baiwar Allan nan duk yadda zaka 6ata mata rai bata nunawa, maca ce mai haƙuri gsky tsohuwa fa akwai na annabawa sai dai wani abun na daban,'
Jikinsu ne yayi sanyi sosai jin wannan maganar daga bakin mamansu mamee, hankalin jahad ba ƙaramin tashi yayi ba, cikin sauri ta miƙe tana cewa"dan Allah ku tashi mu je musa ƙarfi mu buɗe kopan, nidai Allah yasa lafiya...' ta ƙare maganar tana zura silifa ɗin ta a ƙafarta,
Suma suka tashi kowa ya zura takalmansu suka fice mamansu mamee kawai suka bari a gidan tana idasa sanwar rana da ta aza,
Shiga cikin gidan su kayi cikin hanzari, jahad da mamee suka shiga kaiwa kopar bugu da hannunsu da ƙafafunsu, amma gam bata buɗe ba,
ganin zata basu wahala yasa jahad dakatawa ta shiga kitchen ɗinsu ta ɗauko tabarya,
"Matsa mamee kar na buge ki" ta faɗi hakan tana ƙoƙarin kaiwa kofan naushi, cikin sauri mamee taja da baya ta koma gefen husanna ta tsaya,
Da iya ƙarfinta na ƙarshe ta shiga kaiwa kopan bugu da tabaryar nan, amma gam taƙi buɗuwa ko motsi, a wahalarce ta miƙa wa mamee tabarwar "ke ma ki gwada" hannu tasa ta karba ta shiga bugun kopan amma garam taƙi ko motsi,
Sai da husanna ta bari suka sha wahala sun haɗa uban gumi sai nishi suke sannan tace" ku matsa na jaraba nima"
ja da baya su kayi suka bata hanya, baya husanna tayi dama shegen ƙarfi gare ta, da gudun gaske ta tunkari kopan naushi ɗaya tayi mata kofar ta balle gaba ɗaya,
gaba ɗayansu suka sauke ajiyar zuciya suna murmushin jin daɗi sai dai me !?
husanna ce ta fara kutsa kai cikin ɗakin kafin jahad da mamee suka shiga su ma, gabansu ne yayi mugun faɗuwa cikin tsananin firgici jahad ta dafe ƙirji tare da cewa "Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un! Mun shiga uku!!!!
Tana faɗin hakan ta yanke jiki ta faɗi sumammiya, fashewa da wani irin matsanancin kuka na tashin hankali husanna tayi tana faɗin "shikenan komai yazo ƙarshe" zube wa tayi saman guiwowinta tana kuka cikin ƙunar rai,
Mamee kuwa fita tayi da gudun gaske sai gida ta sanarwa mamansu da abinda ke faruwa, ko hijabi bata tsaya dauka ba, zani ta lullu6a a kanta ta biyo ta suka shigo gidan,
Hankalin ta ya tashi ganin tsohuwa baje a ƙasa bakin ta na fidda ruwan kumfa, tama ji ma da mutuwa bakomai bane yafi tayar ma mamansu mamee da hankali ba face ruwan kumfar dake malale a bakinta wannan alama ce dake nuni da cewa poison ne!!! hakan na nufin cewa bata akai tasha, meke shirin faruwa ne? menene ke faruwa? Meye zai biyo baya !?
Wannan koke koken da suke yi ne yasa sauran makwabta ji, nan fa mutane suka yo buya guda sai cikin gidan, lokaci guda gidan ya cika da mutane kai hada cincirundon samarin unguwar wasu harta saman katangar gidan suna leƙe,
Babban tashin hankalin ma wata mata nan da suke kira da maman baffa tayi tsalle ta dire da cewa "Dama ni banyarda da waɗannan yaran ba! Mayu ne sune suka bata guba taci! dama bamu san asalin su ba haka rana tsaka muka gansu a gidan munafukan Allah asirin ku ya tonu," wata da ga cikinsu ma ta ƙara da cewa"maganarki gaskiya ce maman baffa yara sai shegen kyau ga rashin son shiga mutane ashe su suka son me suke ƙullawa, dama ance tsintacciyar mage bata mage wlh dole mu ɗaukar mata fansa tunda ku bakusan halacci ba, ta janyo ku inuwa kun kaita rana har kunyi silar mutuwarta,'
Nan fa wuri ya ɗau cece kuce hayani ta cika wurin, mamansu mamee na ƙoƙarin ta kare su amma abun yaci tura,
Ga matasan dake waje jira suke kawai a basu dama su halakar da yaran dama haushinsu suke ji saboda rashin basu haɗin kai, basa kula kowa yau ga dama ta samu,
Hankalin husanna ba ƙaramin tashi yayi ba ita dake zaune ido biyu tana jin abunda mutane ke cewa ita kuwa jahad har yanzu bata farfaɗo daga suman da tayi ba,
Mamee ce ta taimaka ta ɗebo ruwa a cup suka yayyafa mata, da wani irin matsanancin ciwon kai ta tashi idonta sunyi jawur, bala'i biyu ga raɗaɗin da take ji a zuciyarta ga kuma abunda tafarka taji mutane na cewa,
ganin cewa dagaske hukunta yaran zasuyi su kashe su suma, yasa mamee gudu izuwa gidansu cikin hanzari ta laluba school bag ɗinta, wayarta ta ɗauko ta dannawa ƴan sanda kira, taci sa'a an ɗaga nan tayi reporting akan abunda ke faru tare da basu address na anguwar,
Abunda yasa tayi hakan kwara hukuncin da ƴan sanda zasu ɗauka akan wanda ƴan unguwa zasu ɗauka, kisan wulaƙanci zasu yi masu ba bincike,

Lokacin da ta koma gidan dakyar ta samu hanyar shiga mutane sun cunkushe ko'ina,
Ta raza na da ganin wasu matasa guda biyu hannunsu ɗauke da galons na fetur ga ashana a hannunsu kira suke abasu hanya su ƙone mayun, saboda rashin imani matan dake cikin gidan suka shiga basu hanya, haka aka janyo su waje daga cikin ɗakin sai kuka suke yi gwanin bantausayi,
Zazzaga musu fetur ɗin suka soma yi ajikinsu nan take numfashin husanna ya soma hau hawa, jahad kuwa ta ƙanƙameta tarungume ta ajikinta sun rungume juna suna jiran ta Allah ta kasance,
A dai-dai wannan lokacin jiniyar motar ƴan sanda ta karaɗe ko'ina, mota guda suka yo sai a kopan gidan dandazon mutanene da suka gani ne ya tabbatar masu da cewa nan ne address ɗin da yarinyar ta basu,

Tabbas a ranar sunga bakar rana, dakyar ƴan sanda suka kwace su, suka sanya su a bayan kanta suka tafi dasu,
Mamee da mamansu sun sha kuka saboda tausayin ya rayuwar yaran zata kasance ?
Case ya koma hannun police sai yadda hali ya bada, a police station suka kwana ana investigation akan mutuwar tsohuwar, ga baƙar yunwa ga tashin hankali, duk yaran su firgita matuka ga kwanan cell sai uban sauro dake cizonsu,_ 😭•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•
*ABBAN SOJOJI*

_mallakin_

*HAFSAT BATURE*

_wannan ƙirƙirarran labari ne wasu abubuwa ma daga cikinsa ƙirƙirarsu akayi domin ilmantarwa faɗakarwa da kuma nishaɗantarwa_


_gargaɗi ko da gigin wasa ban yarda wani yayi amfani da wani sashe na littafin nan ba batare da iznina ba, wahala tace ban shiga harkar kowa ba kuma nima bana so a shiga tawa kowa ya tsaya iya matsayinsa_


*page* *43* to *44*


_The Father Of soldiers

Kamar yadda su husanna suka kwana a cell ba bacci itama haka ta kwana ido buɗe, banbancin shine su suna cikin matsanancin hali, ga sauro ga yunwa ga ba wanka komai ya hargitse musu bayin Allah,

Zuciyarta ce ke matsanancin buga mata wanda hakan ya tabbatar mata da cewa, ƴan uwanta na cikin mawuyacin hali, saboda aduk lokacin da wani abu mummuna ya faru dasu sai taji a jikinta,

zuciyarta ce ke matsanancin buga mata, zufa ce ke ta faman sintiri a jikinta, kai kace akwai zafi ne Alhalin yanayin garin sanyi ne,

dukkan ilahirin jikinta sai makekketa yake yi, sam zama saman gadon ya gagare ta, tadawo ƙasa jikinsa ta jingina bayanta, tausayin rayuwarsu ce ta kamasu,
tun suna cikin ciki ƙaddarar su ta soma, sun sha baƙar wahalar rayuwa, ba irin tashin hankalin da basu gani ba, wani lokacin har tambayar kansu suke wai Allah baya sonsu ne? astagfirullah 😥

Amma hakan baisa sehrish tadaina nafilfilin da take yi ba, yau ma rashin tsarkin da bata dashi ne ya hanata yin sallolin, addu'o i kawai take faman maimaitawa duk wacce ta zo mata a bakinta,
Amma fa a daren nan tasha kuka, kamar ba gobe, dole mane sehrish tayi kuka domin kuwa halin rayuwar da suke ciki duk juriyar mutun yaji sai ya matse kwalla,

fargabarta wane hali su husanna ke ciki tana tsoran ta rasa jininta, na biyu wane hali mahaifiyarsu take ciki shin tana raye ko

6 Comments On ABBAN SOJOJI
avatar
ibrahim-5-3

1 year ago

Reply

Ina son abban sojoji complete

avatar
ibrahim-5-3

1 year ago

Reply

Ina son abban sojoji complete

avatar
muhammad-4-3-8

1 year ago

Reply

I want it

avatar
hauwa-said

1 year ago

Reply

Please Ina so

avatar
hauwa-said

1 year ago

Reply

Please Ina so

avatar
husaini

9 months ago

Reply

I love this novel

Please Login or Register in order to submit comment