Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nan ƙafafuwan naki masu kama dana Zabbi,'
Tsananin bakin ciki ne ya cika sehrish ganin mutumin da ta tsana,
A faɗace tasanya hannunta tare da Buge nasa, da gudun gaske ta wuce shi ta faɗa bedroom ɗinta tana shessheƙar kuka, datse ƙopan tayi gudun kada haroon yasamu damar faɗo mata,
Jingina jikinta tayi jikin ƙopan bayan ta rufe, tana kuka mai cin rai, ta ƙara jin tsanar haroon a ranta hada shine yaja mata barin junaid yayi ta faman jiran ta a garden gashi hakan yayi masa Illah ssae, duk inta tuna ɗigon jinin junaid da tagani daga hancinsa, sai taji wani irin ba daɗi aranta,
Ta jima jikin kopan kafin daga bisani ta wuce toilet ta tu6e wandon daya jiƙe sharkaf da futsari tasa shi a bucket ta wanke sa, sannan ta shanya shi a siririyar rigiyar dake a toilet ɗin, wadda akayi ta domin shanya panties, da hanging ɗin kaya, bayan ta kammala tayo wanka sannan ta fito ta canza wasu kayan riga da wando
daga bisani ta haye saman gadonta tana sauke ajiyar zuciya, shigewa tayi cikin bargo tana dariya lokaci guda da ta tuna abunda junaid yaso yayi mata a yau da ta shiga uku kuwa, daker bacci 6arawo yayi awon gaba da ita,

A hankali Babban yaya ya kwantar da junaid saman shimfiɗeɗan gadonsa, har lokacin junaid fa bai dae na sambatu ba akan abunda sehrish tayi masa, sai da yaji yatsun sgr a bakinsa, sannan ya ware idonsa da kyau yana kallonsa, yayi tsit daga maganar da yake yi,
Tashi yayi ya kashe a.c ɗin ɗakin gaba ɗaya, sannan ya kunna masa Room heater (na'urar dake ɗumama ɗaki ta zafi) nan take bedroom ɗin ya ɗumama da wani irin ɗumi mai daɗin gaske, hakan yasanya junaid fara dawowa cikin hayyacinsa, sanyin jikinsa ya soma ragewa ssae,
Bayan ya kunna masa, ya fice daga ɗakin izuwa medication room ɗinsu, inda suke ajiyar magunguna,
Abunka ga professional surgeon doctor within minutes sai ga junaid yadawo cikin sense ɗinshi, bayan babban yayan nasu ya bashi medicine ɗinshi yasha,

Sannan yace "Bazan ƙyale ka Ba junaid, u must explain to me where did u go in this night, ka tanadi amsar da zaka bani before tomorrow, Kana mun wasa da lafiyarka ko?" sgr ya faɗi yana kallonsa A yayin da suke daga zaune saman gadon,'
narai narai junaid yayi da ido yana kallonsa, aiko hakan ya fusata sgr rai a6ace yace "zaka kwanta kayi bacci ko saina murƙusaka a wurin nan"? Koma wa junaid yayi tare da jan bargo ya lullu6e hada fuskarshi duka, bawan Allah yana so yace ma Babban yayan nasu Yunwa yake ji, amma ya gaza saboda ganin yadda ya fusata dashi,
Kwanciya shima sgr ɗin yayi yaja bargon ya lulu6e jikinsa har wurin neck ɗinsa sannan bacci ya kwashe su, su duka,
(Bacci da Yunwa😥)

________________________________________________________________

A 6angaren su hosana kuwa, tun da suka shiga cikin wannan tsohon store ɗin da Aunty babba ta turasu, Sam sun gaza samun sukuni, daker numfashin su ke fita saboda ƙura ga ko ina a tsohe ba windows,
Sun jima a tsaye cikin tashin hankali ga wani yin bacci da suke ji,
Jiki a mace hosana tace "nidae bacci nake ji, zan kwanta ko,a ƙasan ne," ta faɗi tare da tattarewa zata kwanta ƙasa, ruƙo hannunta jahad tayi tare da cewa "A'a hosana in ki ka kwanta ƙasan nan wlh ƙwarin nan shigar miki cikin kunne zasuyi suyi miki illah,' ta faɗi tana kallonta cikin karayar zuciya,
Muryar tamkar zatayi kuka hosana tace "to ya kike so nayi jahad ! A tsaye zamuyi baccin ne !!,
Jahad tace "a'a bari ki ga dabaran da zanyi mana mu kwanta," tayi maganar tare da sakin hannun hosana ta wuce inda jarkokin nan suke burjiki, tasa hannu tashiga ɗauko su tana kwantar dasu ƙasa a jere, kusan jarka Goma sha biyu ne, ta rabasu shida shida biyu na jikin biyu su ka ɗanyi faɗi, sannan ta ta ɗauki tsumman dake a ƙasan ledar ɗakin tashiga kakka6esu saboda sunyi ƙura ssae ga matattun girgizo asaman su, daker tasamu suka ɗanyi haske sannan ta wurgar da tsumman, ta cire mayafin jikinta wanda saude tabata, ta shimfiɗa musu asaman jarkokin,
murmushi hosana tayi na jin daɗi ganin irin dabarar jahad, gashi ta mayar da Jarkoki sun zama kamar single bed,
Itama jahad ɗin murmushi tasaki tare da juyawa ta kalli hosana tace "To ya kika gani yanzu?
"Yayi kyau ssae jahad ," ta bata amsa da murna a fuskarta,
"Zoki kwanta to," jahad ta faɗi tana Yi mata alamar tazo ta kwanta,
Wuce wa hosana tayi tare da hayewa saman jarkokin ta kwanta, sannan itama jahad ta hau a hankali ta kwanta suna fuskantar junan su,
tace "mu kuma haka rayuwarmu zata ƙare Ko jahad? ko munyi addu'a Allah baya kar6a......
Cikin sauri jahad tace "Waya faɗa miki? Karna sake jin kince haka, Allah shi ya halicce mu, kuma yana sane damu, yana jarabtarmu ne ba don baya sonmu, face donya jaraba ƙarfin imanin mu, in har muka cinye jarabawar nan, zamu kasance masu nasara arayuwa,'
Hosana tace "Yaushe jarabawar zata ƙare jahad? Ae anyi mana dayawa yakamata suma wasu a ɗandana musu jarabawar mukuma mu huta,'
Murmushin takaici jahad tayi kafin tace "Allah shine mafi sani hosana, mu ci gaba da addu'a kawai kada mu daina, domin Allah yana fushi da duk wanda baya rokonsa,'
Cikin sanyin murya hosana tace "Insha Allah bazamu fasa Yin addu'a ba, muna kai kukan mu wurin Allah ba, har sai ranar da muka koma gare sa,
Murmushi jahad tayi tare da cewa "Hakane hosana,"
A haka har wani wahalallan bacci ya kwashe su, tsakar dare wani uban zafi ya fargar dasu, wata irin zufa ce ke zazzafowa daga jikinsu,
Hosana duk ta razana sai kuka take ta faman yi saboda bata da juriya duba da halin da take ciki ga ciwo ga ta6in hankali,
Daker jahad ta shawo kanta, da cewa ta kwanta ita zatayi mata fifita, cikin kuka tace "dame zakiyimun fifitar,"?
Jahad tace "Hijab ɗin jikin ki, zaki bani," hannu hosana tasanya ta cire guntun hijab ɗin dake ajikinta wanda saude tabata, ta miƙawa jahad, Sannan ta kwanta saman jarkokin,
A haka Jahad ta shiga yi ma hosana fifita tana kore mata saurayen dake shawagi asama, nan take bacci ya ɗauki Hosana mai nauyin gaske,
Baiwar Allah Jahad idonta sunyi jawur saboda jin bacci, amma sam tagaza runtsawa saboda fifitar da take yima Hosana, tana tsananin tausayinta ssae, tana jin son ƴar uwarta bazata so wani abu ya kuma cutar da ita ba,
Tana Hamma tana yi mata fifita idonta na rurrufewa saboda bacci Amma haka ta jure ta tsayar da kanta don hosana tasamu isasshen bacci 😥 wani sa'in in tana gyangyaɗi har kusan faɗama Hosana take ta galabaita ssae,

Rayuwa kenan wasu mutanen basu da ɗigon imani aransu, basa tuna dame aka haliccesu, basa tuna ta yadda suka zo duniya, Son zuciya kawai, Ynx duk girman gidan general ishaq a ƙalla ba'a rasa bedrooms sama da shida, ga palor Amma a rasa inda za'a ba rai ya kwanta don baƙar mugunta da zalunci sai Store ɗin ajiye tarkacen buhunhuna da jarkoki? Wasu mutanen dae ba tausayi aransu,😿
Masu gidan na can suna shan ra6ar a.c a haɗaɗɗun bedrooms ɗinsu yayin da sukuma suke nan suna fama da Uban zafi, haƙiƙa su hosana sunyi dana sanin zuwansu gidan nan , sai suka ji dama Yaya Omar ya barsu gidan Goggon katsina da aunty saude, Allah sarki ƙaddara ta riga fata 😖

_ku gyara zama domin kuwa yanzu hot pages suka fara, da zafi zafinsu hada hayaƙi ma🔥😅 Sannan kada maganar payment ta sagar muku da guiwa zanyi muku sauƙi ssae, kuma ku shaidane akan littafin nan in yayi daɗi ma kunsani ba asara zakuyi ba_ 🤝💋










An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


6 Comments On ABBAN SOJOJI
avatar
ibrahim-5-3

1 year ago

Reply

Ina son abban sojoji complete

avatar
ibrahim-5-3

1 year ago

Reply

Ina son abban sojoji complete

avatar
muhammad-4-3-8

1 year ago

Reply

I want it

avatar
hauwa-said

1 year ago

Reply

Please Ina so

avatar
hauwa-said

1 year ago

Reply

Please Ina so

avatar
husaini

9 months ago

Reply

I love this novel

Please Login or Register in order to submit comment