Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

aiki, Babban yaya da kike gani mutun ne mai hatsarin gaske !!!, sai kin kula,"
Cikin sauke ajiyar zuciya sehrish tace "Shikenan aunty azmee, insha Allah zan kula, i won't let that happen zanyi komai yadda ki ke so,"
Murmushi azmee tasaki tare da cewa "yawwa my daughter, ko da yake nafiso nace ƙanwata hakan yafi mun daɗi, yanzu dae ɗauki breakfast ɗin nasa ki kai masa,"
"Tom aunty azmee," sehrish ta faɗi tare da sa hannu ta ɗauki tray ɗin, da ƴar fara a a fuskarta ta fice daga kitchen ɗin,
A natse take tafiya, zuciyarta na bugawa especially in ta tuna abunda Aunty azmee ta sanar da ita nacewa he's a dangerous man, hakan na kara tsoratar da ita,
tana cikin tafiya taji dirar Ball a ƙasan kafarta, ƙiris ya rage ta saki tray ɗin saboda ta tsorata, bin ball ɗin tayi da kallo kafin ta ɗago taga wanene ya jefo mata ita,
Sai faman murmushi yake ta saki, kamar gonar auduga, bawan Allah yasha wahala, kwallo kamar ibada duk zufa ajikinsa sai wanko masa face ɗinsa take,
"Junaid" ta faɗi acikin zuciyarta, a fili kuma sai cewa tayi "Sannu da dawowa"
Sam yaki mata magana, tun da yasa ta a idonsa, notikan kansa suka kwance, zallar ƙaunarta ce ke gudana a cikin zuciyarsa, karasawa yayi tare da duƙawa Yayi yakai hannu ya dauki ball ɗinsa, sannan ya ɗago tare da aza eyes ɗinsa cikin nata yace "Yunwa nake ji, ashirya mun snacks akawo mun a bedroom ɗina tare da coffeee i wll be waiting,, ya ƙare maganar yana kashe mata jiki da wannan smilling ɗin nasa,
Ita ma kanta batasan time ɗin da, ta shiga mayar masa da martani ba, na murmushinsa, tarasa dalilin dayasa take jin wani sanyi a ranta aduk lokacin da idonta suka shiga cikin na junaid (Why?)
daker ta amsa Iya amsa masa da cewa "insha Allah ynx zan kawo,"
"Ok" ya faɗi tare da bi ta gefenta ya wuce upstair duk tana, a tsaye tana kallonsa, ƙiriniyarsa na burgeta sosai,ko tafiya yake yi yana dan tsalle haka, .
Sai da junaid ya 6ace mata, sannan itama ta wuce sashen sgr ,
Time ɗin da ta karasa a bakin kopan sai da ta tsaya ta karanta addu'o'in neman tsari da sharrinsa sannan, ta shiga ciki da sallama,
Ba zato ba tsammani taji wannan sanyayyiyar muryar tasa so sexy ta amsa mata da cewa "Wa'alaikam salama,"
Wurgo ido tayi ta hangosa kishingiɗe saman royal sofa ɗin doguwa, kansa na saman hannun seater ɗinta, yayin da idonsa ke kan Laptop ɗinsa wadda ya aza ta saman stomach ɗinsa, kasancewar yana daga kwance, jikinsa na sanye da jallabiya fara, masha Allah kyau iya kyau, ba'a magana, masu sa kyau tayi kyau ba 😂
Jikinsa sai kamshin turaren imperial majesty ke tashi, wani irin daddaɗan kamshin kasancewar duk wani lotion da soap da yake using dasu bama perfumes ba kaɗae masu kamshi ne na fitar shari'a, kasancewar shi, ma'aboci son ƙamshi ga tsafta,
Lumshe ido sehrish tayi, tana jin wani irin heart beating, kamshin sa na rikitar da ita,
A hankali take tunkararsa, sai da taje dab dashi sannan murya na rawa tace "Gm sir," shiru bai bata amsa ba, hakan yasa ta jin fargaba,
Zuru ta ɗanyi tana tunanin kawai ta ajiye masa ta fice, har time ɗin eyes ɗinsa nakan Laptop ɗinsa yana daddanawa,
har ta ja da baya zata ajiye masa tray ɗin a samar tables ɗinsa muryarsa ta ratsa ta da cewa "Is this the right time daya dace a kawo min breakfast ɗina "?
Shiru sehrish tayi gabanta na faɗuwa, a cikin zuciyarta kuwa tsantsar tashin hankali ne, tabbas akwai matsala, saboda ita azmee ta sanar da ita cewa ba'a tashin shi daga bacci in yana yi, and now kuma yana complain ba'a kawo masa breakfast ɗinsa da wuri ba? to tayaya mutumin da ba'a tashin sa daga bacci zaisan ankawo masa breakfast ɗinsa da wuri !!!?
wannan jinkirtawar da tayi bata bashi amsa ba, ya sashi fusata, aiko tana a tsayan nan ba ta lura ba, ya ƴunƙura yasanya ƙafarsa da karfin gaske dama ga tsayi ya harba tray ɗin dake hannunta, nan take komai ya kife ƙasa, ya tarwatse food warmers ɗin da sauran tarkacen, zaro ido tayi tare da dafe ƙirji gabanta na faɗuwa, tsananin tsoro ne ya bayyana a fuskarta,
Cije lips ɗinsa kawai ya keyi, ganin koma wanene yaƙi moving, wani irin motsi taji bana wasa ba, aiko da gudun gaske ta fi ce daga falonsa, wato da ace sehrish tabari wannan motsin da taji yayi da ba ƙaramin naushi zai kai mata ba,
Kamar daga sama su ka ci karo da azmee wadda ke ƙoƙarin Fitowa daga kitchen ɗin, tana ganin sehrish gabanta ya faɗi, aranta tace "yayi tsiyar,"
Fashewa tayi da matsanancin kuka a lokacin da taganta, agaban azmee jikinta har wani jijjiga yake yi, sai kerma la66anta ke yi,
Hankali tashe azmee tace "menene sehrish me ya faru,? ta faɗi tana jiran bayani daga wurinta,
daker kukan da sehrish take yi ya tsagaita, cikin matsanancin kuka take korawa azmee bayani,
" ...aunty ..azmee...baaa...ke ki ka ce ba'a tashin sa daga bacci ba....ynx fushi ya keyi ba'a kai masa breakfast ɗinsa da wuri ba..ba ki ga yadda yasa ƙafarsa ba ya harba tray ɗin abincin komai ya watse, bansan ya zanyi ba," tana magana tana yarfa hannu, sai faman jan majina take yi, duk ta firgice,
Shiru azmee tayi saboda dama ba wannan ne karo na farko da yake faɗin cewa ba'a kaimasa breakfast ɗinsa da wuri ba, gashi mafi yawancin lokutta bacci yake yi, kuma ba uban da ya isa ya tashe shi yana bacci, saboda kamar ɗan wrestling haka yake, Naushi yake kaiwa, gaba ɗaya kannensa su fawan dasu Irfan ba wanda baije tashe shi daga bacci batare da ya naushe shi ba, shiyasa kowa yayi nesa dashi, ake barinsa sai ya kammala baccinsa ya tashi dakansa, sannan kuma ya hau jarabar ankai masa karin kumallonsa a makare,"
"Aunty azmee ba ki ce komai ba, ya zanyi? gashi can ya 6arar da abincin shima wata matsalar ne, ya za'ae abashi hakuri na samu naje na kwashe wanda ya zubar na zuba masa wani"?
ta ƙare maganar tana kallon azmee wadda tayi zuru cikin rashin sanin mafita,
yarfa hannu azmee tayi tare da cewa "wlh nima bansan menene solution ba, mutun ɗaya ne zai iya shawo kansa, kuma ba kowa bane face Junaid...."


"Naji kamar ana maganata a wurin nan," junaid ne yayi maganar wanda ke saukowa daga saman stair ɗin, jikinsa sanye da jeans da farar t shirt,
Bin su yayi da kallo musamman sehrish wadda ke tsaye, ido luhu luhu tasha kuka, yau taga tashin hankali,
Ajiyar zuciya Azmee tasaki ganinsa cikin sauƙi,
"Junaid matsala aka samu," azmee ta faɗi tana kallonsa,.
"Meya faru"? Ya tamvaya yana kallonsu,"
Nan azmee ta kwashe dukkan abunda ya faru ta sanar mishi, kamar yadda sehrish ta faɗa mata,"
Murmushi yasaki tare da kallon sehrish wadda ta sunnar da kanta kasa, yace "Calm down ur mind, in dai Babban yaya ne, ni ne controller ɗinsa, just wipe ur tears," ya faɗi yana nuna tears ɗin dake zubowa daga eyes ɗinta,.


Hannu tasa tana goge su kamar yadda junaid ya bata umarnin ta share su,"
Sannan yace da aunty azmee "a shirya masa wani breakfast ɗin, ynz zan zo na karba," yana gama faɗan hakan ya juya tare da wuce wa izuwa upstairs part ɗin Sgr,"
"Yanzu sai kiyi murmushi, junaid da ki ke gani shine masarrafin babban yayansu, shi ke juya shi kuma ya juyu," azmee ce tayi maganar tana kallon sehrish,
Ita dae har yanzu bata dawo cikin hayyacinta ba, ta jima tana mamakin abunda sgr yayi, yadda ya hauro da ƙafarsa ya harba tray ɗinta ya kife kasa ba ƙaramin mamakin hakan tayi ba, maimakon taji haushinsa, sai ma taƙara jin ƙaunarsa na ninkuwa azuciyarta 💋
Da sallama junaid ya shiga falonsa yana faɗin " babban yayan mu, gani na iso, nazo na takura maka na hana ka sukuni,"
Jin Voice ɗin junaid yasa, Rafayet tashi zaune daga kishingiɗen dayake, ya mayar da laptop ɗinsa, saman desk ɗinta, a hankali ya ware idonsa akan junaid tare da cewa "sai ynx zaka so wurina? Ina ta fama da yunwa arasa wanda zai tashe ni ko"? yayi maganar yana lumshe sexy blue eyes ɗinsa,.
da murmushi junaid ya karasa yana faɗin "am so sorry babban yayanmu, kaima kasani, na damu da cikin ka sosai, shiyasa ko breakfast banyi ba tun safe, kai kawai nake jira ka farka muci atare" ya karasa maganar tare da russinawa ya rungumosa sannan ya manna masa kiss a gefen face ɗinsa,
Lumshe idonsa yayi, har cikin zuciyarsa, tsananin kaunar yaron ya keyi ba don komai ba, sai don kasancewarsaa mai tsananin biyayya ga iya magana, minti 5 yayi yawa ga junaid ya sace zuciyar mutun especially da wannan murmushin nasa, shiya sanya Hafsat bature ta kamu da tsantsar ƙaunarsa 😥
Juya wa junaid yayi ya kalli, tray ɗin da babban yayan nasu yayi watsi dashi a ƙasa, cike da daɗin baki yace "subhanallahi ya akai kayan abincin nan suka zube ƙasa, ni nasan aikin tukur ne bari na kwashe na canza wani,"
Ya karasa ya zuƙunna yana tattare kayan, duk rafayet nabinsa da ido, sai da ya kammala kwashe komai ya mayar acikin tray ɗin sannan ya ɗauka yana cewa "am coming now yayanmu,"
Sannan ya fice, ajiyar zuciya yasaki lokacin da ya fito daga part ɗin nasa, kitchen ya wuce, azmee kaɗai yasamu aciki ta kammala hada masa wani bf ɗin acikin tray,
Miƙa mata na hannunsa yayi ta karba sannan ya ɗauki wanda ta haɗa masa asaman table, ya dago yana kallonta yace "Ina Sehrish take,"? Murmushi azmee tayi kafin tace "ta tsorata ne sosai, ta koma ɗaki ynz," .
Yace "ok amma aunty azmee yaushe zaki faɗa mata cewa nasan cewa ita maca ce ? Inaso tasani pls !" yayi maganar da shagwa6a,
Ƴar dariya azmee tayi kafin tace "insha Allah yau zuwa anjima, zan faɗa mata,"
Murmushi yasaki ya fice yana faɗin "Can't wait to see," dariya azmee tayi tare da cewa "Romeo kenan,"
Itama fice wa tayi daga kitchen ɗin don tajima yau tana aiki acikinsa since morning kamar enjine,
Yana zaune yana jiran junaid, sai gashi ya shigo, hannu rike da tray, a saman table ɗin dake gabansa daga gefe ya ajiye masa shi, sannan shima yazauna gefensa tare da cewa "Babban yaya zan iya baka a baki," ɗagowa sgr yayi yana kallonsa face ɗinsa tamkar zaiyi murmushi yana kallonsa, wannan fadancin na junaid ba karamin tafiya yake dashi ba,
Plate junaid ya ɗauka, ya shaƙe masa shi da chips har yayi sauro don yasan Babban yayan nasu baya wasa da cikinsa, akwai bama ciki haƙƙinsa 😉
Tura masa plate ɗin yayi agabansa, naɗe hannun jallabiyar jikinsa yayi, junaid ya zuba masa ruwa ya wanke hannunsa acikin bowl, sannan ya soma ya zura hannusa yana ɗibar chips ɗin yana turawa a bakinsa, in kaga yadda yake wawuro wa yana turawa a small mouth ɗinsa sai kayi mamakin tayadda akai abincin ke shiga, saboda ƙankantar bakin nasa,
Robar cool milk ya dauka ya zuba masa acikin glass cup ya tura masa a side plate nasa, ga fresh fruits ya acikin hadadden plate ya ajiye masa ga sauran delicious,"
Junaid ne yazauna yana saving nashi, bayan ya tsagaita ya zuba msihi ido yana murmushi, ɗagowa sgr yyi suka haɗa ido yace "what"
"Kyau nake kallo fuskar babban yayana," junaid ya basa amsa,
"Duk kyau na, nakai ka junaid,"? Ya tambaya yana kallonsa, ɗan sunnar da kai junaid yayi tare da cewa "kai na musamman ne yayana, komai naka na musamman ne, haka kyan ka ma,"
dan ta6e baki sgr yayi yana kallonsa ayayin da yake mika hannu ya dauki cool milk ɗin dake acikin cup ya kurba sosai tare da mayar wa ya jiye,
Sannan cikin natsuwa yace "Ni kam tunda nake aduniyar nan, tun da Allah ya halicce ni a duniyar nan , ban ta6a ganin yaro mai shiga rai mai sace zuciya ba irin ka! junaid u are so special to me i don't know how to explain it but I really really love u so much, just tell me whatever u want am ready to do it for u,"

daɗi kamar zai kashe junaid jin yadda babban yayan nasu ke yabonsa, sam ya gaza rufe bakinsa har sai da sgr ya maimaita cewa "ka faɗamin komai kake so nayi maka insha Allah,"
Cikin sanyin murya junaid yace "babban yaya murmushinka kawai nake so, dan Allah kayimun koda yaushe face ɗinka a daure..." ya ƙare maganar cikin shagwa6a hada ɗan bubbuga ƙafa,
Shiru sgr yayi yana tunanin wai ma ya ake murmushi aduniya, ae shi yama manta when last yayi murmushi aduniyar nan, muryar junaid ce ta ƙara katse shi"smile 4 me plsssssss.."
shiru su kayi gaba ɗayansu, zuba mishi ido junaid yayi yana jiran yaga murmushin babban yayan nasu,
ɗagowa rafayet ya ɗanyi ya kalli junaid wanda ya ƙura masa iso yana jiransa, mayar da idonsa yayi kan plate ɗin dake gabansa mai dauke da farfesun da junaid ya zuba masa,
wa'iyazubillah , A natse a hankali wani irin ƙayataccen murmushi na side face yafara bayyana a kyakkyawar fuskar sgr, Subhanallahi tabarakallahu ahsanul qalikin, wato wasu irin lotsattsun dimples ne suka bayyana a fuskarsa masu shegen kyau, dole babban yaya ya dinga rowar murmushin sa wato wani irin ruwan kyau, madarar kyau yake badawa, irin murmushin kashe zuciyar nan, irin wanda kai tsaye namiji yayiwa Mace shi duk min ji da izzarta sai ta susuce,
A susuce junaid yadinga yarfa hannu yana fadin "wow!!wow !! Oh my God yaya rafayet am just speechless wannan heart killing smile ɗin naka ya tafi dani,"
Lokaci guda kuma ya mayar da face ɗinsa yadda take, kai kace murmushi bai ta6a wanzuwa a fuskarsa ba, sannan yace "Junaid sa hannu muci abinci atare," cikin sauri junaid ya zura hannu suka shiga ci atare abun gawanin burgewa, 💋•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·


*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*


_❤‍🔥Extraordianary Love❤‍🔥_

*Writer*

*©️Hafsat Bature Boss Lady✍️✍️✍️*

End of chapter one

~page 75~

daga inda ku ka ga na sanya part 2, to daganan Labarin ya soma da zafi zafinsa 🔥🔥🔥

...........Sehrish...................
Idonta na facing ceilling a yayin da take kwance tsakiyar bed ɗinta, cike da tsananin shauƙin babban yaya, tabbas ta tsorata da fusatar shi, amma hakan ba ƙaramin burgeta yayi ba, musamman yadda ya hauro da doguwar ƙafarsa yayi wurgi da tray ɗin hannunta, lumshe idonta tayi cikin wani irin yanayi mara misaltuwa, ita dai sgr yayi mata ya kwanta mata aranta (nace ba Allah ya bar ƙauna)
ta jima tana juyi a saman bed ɗin nata, har sai da ta tabbatar cewa sgr ya isa ya fita ynx sannan ta tashi domin zuwa gyara masa bedroom ɗinsa,
A time ɗin junaid ya fita daga part ɗinsa ya koma nasa room ɗin, sai faman zullumi yake, tun da azmee ta sanar dashi cewa zata faɗawa sehrish cewa yasan cewa ita maca ce, zama yayi saman bedmattress ɗinsa ya lankwashe kafarsa, sae faman smilling yake yi, burinsa sehrish ta amince dashi a matsayin ɗan uwanta na jininta suyi shiri sosai, murmushi yasaki tare da yunƙura yakai hannu daga gefe Jikin gadon akwai side drawers ajikinsa, janyo wa yayi wato bakomai yake ajiyewa ciki ba face Chocolates,biscuits, sweet da sauransu, junaid baya rabuwa da shan zaƙi, ajinin sa yake, ledar dairy milk ya ɗauko guda biyu da snickers, ya zauna yana gatsa yana turawa a mouth ɗinsa sai faman lasar baki ya ke yana tunanin Sehrish ɗinsa 😥
Gabanta har faɗuwa yake yi addu'arta Allah yasa sgr ya fita daga part ɗinsa, tafiya take yi cikin sanɗa, ta wuce parlor ɗinsa, adai dai kopan shiga bedroom ɗinsa suka ci karo dashi ƙiris ya rage su gabji juna,
Waro ido tayi tana kallonsa cikin tsananin tsoro, ya shirya tsaf da alama fita zaiyi, ya ɗau wankan jeans da t shirt irin na jikin junaid, ga wannan haɗaɗɗiyar sumar tasa, gyara na musamman tasha, ya daure ta abayansa, yayin da ya saki wata daga ƙasa ta ɗan zubo masa, hakan ba ƙaramin kyau yayi masa ba,
Ƙamshin turarensa sai wankar mata hanci yake yi, kai kace da ruwan turare yake wanka,
gyaran murya yayi alamar abashi hanya ya wuce, da sauri ta ɗan ja gefe, ya bi ta side ɗinta ya wuce da wannan tafiyar tashi mai jan hankali, sam tagaza ɗauke idonta akansa, wani tunanine ya faɗo mata aranta, cikin sauri tace "adawo lpy"
"yawwa" ya amsa mata a time ɗin da yake idasa fita daga falonsa, .
Saboda murna yasa sehrish ta ɗan yi tsallen farin ciki, tare da sakin murmushi koba komai, wannan wani mataki ne, na narasa tunda yana amsa magana in akai masa, 😇
Shiga bedroom ɗinsa tayi har time ɗin tana ayyana muryarsa da yadda ya bata amsa, taci alwashin daga ynx zata dinga yi masa magana, tunda yana amsawa,
Ajiyar zuciya tasaki tare da mayar da hankalinta ga abunda ya kawo ta, bin ɗakin nasa tayi da kallo, Aljannar duniya komai tsaf a gyare, sae ƙamshi ke tashi kamar, koda yaushe tana jinjinawa haɗuwarsa da kuma dollars ɗin da aka kashe masa, nan gaba sehrish zata zayyana mana ya haɗuwarsa yake 😘
A hankali take shafa lallausan blanket ɗinsa, ta janye sa daga saman gadon ta ninke sa, tare da hugging ɗinsa a chest ɗinta tana shaƙar kamshinsa, ta jima tana lalaci a ɗakin nasa kafin ta shiga gyarasa,
.............Hosana .............Jahad ...............
a hankali motocin nan suka shiga dasu a katafaren gidan goggonsu, yadda motocin nan na sojojin nan suka zagaye motar da suke ciki ko shugaban ƙasa albarka,
Sunyi shiru acikin motar,ni'imtaccen sanyin a.c ne kawae ke ratsa, sassan jikinsu, tsantsar farin ciki ne a fuskarsa, ita dai jahad sai godiya take ma Allah daya kawo musu ƙarshen wahalarsu acikin zuciyarta, yayin da hosana ke ta faman zabga murmushi kamar zautacciya,
A tsakiyar gidan suka tsaida motocin, da sauri major ɗin nan dake driving ɗinsu, ya fito tare da buɗe musu kopa, riƙe da hannun juna suka fito, suna bin gidan da kallo ya haɗu masha Allah,
Major ɗinne ya shiga dasu cikin babban falon, saude ce ke ta faman goge goge, tana kakka6e kujeru, ɗagowa tayi jin anyi sallama,
Zuba ma yaran ido tayi tana kallonsu, cikin mamaki ganin tagwaye kyawawan gaske, sam ta gaza magana,
Sai da taji muryar major ɗin yana cewa "Marshal Omar ne yace akawo su nan, shima kuma yana nan shigo wa da anjima,"
yana gama faɗan hakan ya fice, zuru su kayi suna tsoron wata irin tarba za'ayi musu, don sun lura kamar baƙin jini ne dasu kowa baisan su,
ganin matashiyar ta soma sakin murmushi a fuskarta yasa su suma suka ɗan saki fuska,
Cike da zumuɗi takara inda suke kamar tasan su, ta ruƙo hannayen su tana cewa "masha Allah ku shigo ciki ku zauna, ku saki jikin ki ku,"
Haka saude ta ruƙo hannunsu, ta zaunar dasu tare da cewa "bari na kawo muku abunsha ko"?
Cikin sauri hosana tace "ƴunwa muke ji.....," tunkan taƙarasa jahad tasa tafin hannunta ta rufe mata baki, tare da cewa "Hosana banasan wannan abun, daga zuwa gidan mutane kinsan su ne,"
murmushi saude tayi tare da cewa "ba yaya Omar bane yace akawo ku nan ba? Don haka ku saki jikin ku kamar kuna cikin jirgi mai ya ƙare" 😂
"Sannan naji kince batasan mu, ae musulmi ɗan uwan musulmi ne, akwai sanayya da ƴan uwantaka ta addinin musulunci, sannan kuma baƙon ka annabin ki, ku baƙi ne dan haka zan karramaku sosae,
Saude ta karasa maganar tare da sa hannu ta shafa kan hosana tace "kada ki damu ƙanwata, yanzu nan zan kawo miki abinci lafiyayye ki ci,"
"nima zanci," jahad ta faɗi tare da sunnar da kai, murmushi saudat tayi tare da cewa "shikenan bari nazo ga tv nan kuyi kallo," tayi maganar tana nuna musu plasman dakw manna a bango, sannan ta wuce kitchen,
Ajiyar zuciya suka saki atare suna ƙare wa haɗaɗɗen falon kallo,
"Hosana dan Allah ki daina zuba, kina bani kunya sometimes, kin ci ka ɗumi daga zuwa gidan mutane sai ki fara tambayar abinci kamar mayya"?.
Harara hosana ta watsa mata tare da cewa "bani ce mayya ba kaɗai kema mayyar ce, saboda ke ma ae kince zaki ci, " tayi maganar tana murguɗa mata baki, jinjina kai kawai jahad tayi, ba yadda zatayi da ita,
Shigowa saude tayi hannunta ɗauke da tray ta aza katuwar kula aciki, sai plate wit 2 spoon, gefe kuma jug ne mai ɗauke da juice,
Tunkan ta ƙaraso hosana, ta sauko ƙasan carpet ɗin ta zauna tana washe baki,
Ajiye musu tayi tare da cewa "yakamata ku wanke hannayen ku, bari na kawo muku wurin da zaku wanke," ta faɗi kafin ta juya izuwa cikin kitchen ɗin," .
Buɗe kular hosana tayi, zaro ido tayi tare da cewa "Lahh ha ilah Jahad !! Shinkafa kaza ce wlh, hada wasilla masu yawa wayyo daɗi," shiru jahad tayi batace mata komai ba, saboda yunwar da take ji,
Ji su kayi bazasu iya jiran saude ba, takawo musu ruwan da zasu wanke hannu ba, ai kafin saude ta fito daga kitchen ɗin tuni hosana ta ɗauke jug da plate ɗin dake saman tray ɗin ta ajiyesu on carpet ɗin , ta ɗauki kular ta zazzage musu farar shinkafar da miyar duka acikin tray ɗin, gaba ɗaya suka sa hannu suka motse ta suka shiga zubawa cikinsu, hannu baka hannu ƙurya kamar wani yace zai kwace musu abincin,
Tsaye saude tayi akansu tana kallon ikon Allah, gashi har ta ɗauko musu bottle water da bowl ɗin da zasu washing hands ɗinsu aciki, tausayinsu ne yakamata, alamu sun nuna cewa yaran na cikin mawuyacin hali na ƴunwa,
Kamar wasu kuraye haka suka dinga, zuba uwar loma suna ci, Allah sarki anjima ba'a haɗu ba, kitchen saude ta koma cups da dauko musu,
Ta dawo ta zukunna inda suke, tana tsiyaya musu ruwan bottle ɗin hannunta mai sanyi, tunkan ta gama hosana ke miƙa mata hannu tana cewa "ruwa !ruwa!!,' wato taci taci harya shaƙe mata makoshinta,
Miƙa mata saude tayi cikin sauri ta kar6e, ta kai baki tana sha, har wani sauti throat ɗin ta ke badawa "ƙut ƙut kut,
"Hosana nima zan sha in kin gama," jahad ce tayi maganar tana yarfa hannayenta, cikin sauri saude ta zuba mata itama a ɗayan cup ɗin ta miƙa mata, karba tayi tana faɗin "mungode,"
Zama saude tayi kamar ta samu tv tana kallonsu, yadda hosana ta dauki cinyar kaza, ta tura acikin baki kamar kura ta bata tsoro, amma abun mamaki hada ƙashin ta haɗa duka ta taune, zaro ido saude tayi cikin tsoro tana cewa "ki ci a hankali dan Allah,"
"Bazaki gane ba aunty, wlh yunwa muke ji, dan Allah in akwai sauran abincin ma akwaso mana shi duka hada ƙanzoma," 😂
Hosana ce tayi maganar, tana ta fama lashe la66a, mouth ɗinta yayi dama dama da jar miya, kamar mayyar dae," 😆.
Jahad dai ba baka sai kunne, sam bata gane da wane yare suke magana, bata ankare ba hosana ta ɗauke tray ɗin duka tasanya harshenta tana lasa 😅
Ita kanta saude batasan time ɗin da ta, fashe da dariya ba hada dafe ciki, sam tagaza stopping kanta, sae da tayi mai isarta, sannan ta tashi daker tana ci gaba da dariyar ta amshi tray ɗin dake hannun hosana tana cewa "bari na zubo muku alkubus da miya kuna so,"? tayi maganar tana kallonsu, ae har haɗa baki suke yi wurin cewa "eh
DOWNLOAD
DOWNLOAD

6 Comments On ABBAN SOJOJI
avatar
ibrahim-5-3

7 months ago

Reply

Ina son abban sojoji complete

avatar
ibrahim-5-3

7 months ago

Reply

Ina son abban sojoji complete

avatar
muhammad-4-3-8

6 months ago

Reply

I want it

avatar
hauwa-said

6 months ago

Reply

Please Ina so

avatar
hauwa-said

6 months ago

Reply

Please Ina so

avatar
husaini

2 months ago

Reply

I love this novel

Please Login or Register in order to submit comment