Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya gwada imaninsu , kiyi kokari ki cinye wannan jarabawar , ki rungumi kaddara a duk yadda tazo miki dama can rutacce ne daga Allah dukkan tsanani yana tare da sauki ! Allah yana sane daku kuma shine gatanku ,"

Hannu tasa tana clearing face dinta saboda bata so hajjaju tagani , tunanin y'an uwanta shine yafi komai tayar mata da hankali , bata san wani gidan mahaukata bane zasu juri daukar nauyin haukan ta ba idan akace yau husanna tarasa ranta , haka abubuwa suka dinga zuwa mata aranta har suka isa garin abuja, wuraren karfe 2:30 na rana ,

Wannan ne karo na farko da ta fara yin tafiya mai nisa irin wannan ,

tunda suka shiga take kallon manya manyen gine gine , har suka iso gidan da zasu wato gidan Abban sojoji , sehrish ta razana da ganin katafaren ginin mai matukar girman gaske da daukar hankali , irin gidan da ta saba gani a cikin mafarki,

Lokaci da idonta suka sauka kan Narka narkan sojojin dake tsare da babban gate din gidan sai da taji gabanta ya fadi rass , bakake ne wulik dasu sanye cikin uniform dinsu , ga bindigu rike a hannunsu , ga wasu guns din soke a west dinsu ,

Wani irin miyau ta hadiye ganin an tsaida motarsu , nan take taji zufa na gangaro mata ta cikin sumar kanta , guda biyu ne suka karaso inda motar tasu take , d'aya ne yasa hannu yayi knocking , hajjaju ta zuge glass din , ita kanta a tsorace take cikin en ena tace "barka dai sannu ku da aiki ," amsa yayi da "yawwa muna bukatar sanin daga ina kke kuma wurin wa kka zo "?

Da sauri hajjau ta dauko wayarta cikin yar purse dinta ta shiga neman number abban, yatsun hannunta sai kakarwa suke , kira d'aya tayi masa ya daga , bayan sun gaisa ta sanar masa da abunda ke faruwa, ya umarce ta da ta basu wayar , mika musu tayi daya daga cikinsu yasa hannu ya karba tare da karawa a kunnansa , juyawa hajjaju tayi tana kallon sehrish wadda tuni ta ta gama tsuma , ta nannade wuri d'aya ta matse jikinta , idon nan sunyi furi furi kamar wadda tayima sarki karya , muryar sojan taji yana cewa "take your phone , u got permission to go in , but firstly we must check the car ," kallon sehrish tayi tare da cewa " mu fita zasu bincika motar ," bude mota sehrish tayi ta fita , itama hajjajun ta fito , suka tsaya suna jiran su gama binciken nasu ,

Matsawa Sehrish tayi kusa da hajiyar tayi kasa kasa da murya tace "hajiya amma nan barrack din sojoji ne ko "? cikin rashin natsuwa hajjaju tace " A'a gida ne na sojoji dae not a barrack ni bana cikin kwanciyar hankalin wadannan sojojin sun firgitani , sai kace wasu masu safarar miyagun kwayoyi za'a tsare mu ! that's why ban cika son zuwa gidannan ba ! ," takarasa maganar tana yatsina fuska ,

Jikin sehrish ya gama yin sanyi , bin jikinta tayi da kallo tasha kayan maza , ga uban burgujejan wandon da tasa kamar zata tashi sama, kara kankame jakar dake hannunta tayi wacce ke kumshe da y'an kayan da hajjaju ta bata kyauta ,

Hatta purse din hajjaju sai da suka bincika , zuciyar sehrish sai bugawa takeyi tunanin ta masu gadi sun kasance haka da ban tsoro ina ga y'ay'an gidan da taji ance they're all soldiers 😒

Muryar sojancce ta ratsa kunnanta "lemme see your bag "! cikin sauri ta mika mar jakan , zazzago kayan ciki yayi kasa yana duddubawa , trousers ne da riguna na maza , da hijabai da ta kudundunesu saboda sallah , bayan ya gama checking dinsu ya dago ya zuba mata ido yana kallonta , nan take taji fitsari ya cika mata mararta , sunnar da kanta tayi kasa , jikinta na rawa , Ji tayi yasa hannunsa ya dankwashi kanta yana cewa "mara kunya kana namiji baka iyasa Cap akan ka , kai ga d'an daudu ko ? sai dai kasa abu na mata ka nannade kai kamar wani limamin masallaci ",
Karasa maganar yyi tare da wurga mata jakar , sannan ya juya ya tafi , hannu tasa ta dafe wurin don taji zafin rankwashinta da yayi mata wannan gabjejan hannun nasa , dole ita ta zukunna ta kwashe kayanta daya zubar a kasa ,

A karshe dai Sun sami shiga ciki , a jiyar zuciya Sehrish tasaki , time dinda motar tasu ta wuce babban gate din ta shantalelen titin da zai kai ka can cikin gidan ,

A hankali take bin ko ina da kallo ta cikin glass din motan , tana kara jaddada haduwar ginin , taga wurare daban daban masu ban sha'awa , sai ta dinga tunanin cewa kodai tabar nigeria ne domin daga inda kasa kafarka cikin gidan kamar ka fita daga 9ja ne 😔

ihu da sowar da taji ne yasa takai idonta wurin , y'an matasan samari ne kyawawan gaske suke wasan football , acikin playing field n gdn , gwanin burgewa tabisu da kallo har sai da suka wuce su ,

A wurin da aka ware na parking space , hajjaju ta tsaida motarsu , wurin cike yake da motocinsu Na gayu ga kuma jibjibgan motocin irin na sojojin man

Waigawa hajjau tayi ta kalle ta tace "sehrish ki natsu dan Allah in mun shiga kada ki jamun , kuma kada ki manta sunan ki tukur daga ynx ," cike da gamsuwa ta masa mata da "Toh"

Fitowa sukayi daga motan suka miki hanyar data zata sada ka da babban falon gidan , tuni sehrish ta raina kanta , tamkar karta taka kasan tiles din take ji saboda wani irin design ne mai daukar ido , duk yadda ka taka saiya bada sauti kwas kwas ,

Komai na cikin living room din mai tsadar gske ne , kana gani kasan bana nan bane , an kawata shi da expensive furnitures , wasu hamshan royal sofa ne aciki , set shida ne a jere , ko da ido ka kallesu kasan zasuyi laushi da dadin zama , duk yawansu basu cike falon ba saboda girmansa ya isa a gina madai madaici gida acikinsa,

Komai da ake bukata acikin falo akwaisa sai da ba tarkacen nan na hauka komai a natse ,

Bin ceiling din tayi da kallo ba irin rufin da tasaba gani bane , wannan na glass , acikinsa akwai light bulbs masu haske wurin ,

Hankalin hajjaju ba karamin kwanciya yayi ba ganin falon tsit ba kowai sai sanyin a.c dake ratsa sassan jikin mutun, dama zullumin ta ace wadannan sojojin na nan ,

Ruko hannun sehrish tayi wadda hankalinta ke kan twin stairs din da tagani wato tagwayen bene guda biyu wadanda zasu kai ka upstairs, tsantsararrun gaske ,

Sehrish tace "hajiya naji tsit ko ba kowa ne ? hajjaju tace "ina ga duk suna wurin aiki , mu samu wuri mu zauna mu jira wata'kil mai aikinsu na nan ,"

Suna kokarin zama suka ji takon takalmi daga left dinsu , karfaffar maca ce irin giantess dinnan , tana da hasken fata , jikinta na sanye da doguwar riga ta atampa har kasa ta kashe daurin d'an kwalinta , tana ganin hajjaju ce ta saki fara'a tana fadin "me nake gani kamar hajjaju makkatin "? murmushi hajjaju tasaki tare da cewa "kwarai kuwa nice AZUMI ashe kina ciki , nayi tunanin ba kowa ciki ne ,"

Karaso wa tayi inda hajjaju take tayi hugging dinta tana cewa " I really missed u alot hajjaju kin boye mana nayi expecting din bakya kasar ne ," sakin juna sukayi hajjaju tana dariya tace "Ina nan mana ina zani an gaya miki ynx barin kasar nan sauki ne yadda komai ke kara farashi , yar dubai dinnan danake zuwa kamar hauka ynx nadaina saboda rashin kudi ,"

Murmushi azmi tasaki , tare da nuna masu wurin zama tace "bismillah ku zauna bari na shiga na kawo muku abin sha , firar zata fi dadi idan kuka jika makoshinku ,
tana gama fadan hakan tajuya ta nufi hanyar da zata kai ka kitchen dinsu , zama sukayi a tare saman 3 seater , har lokacin sehrish na makale da yar jakarta a kirjinta , sai karewa falon kallo takeyi tana jinjina kyansa , wai itace zata rayu a cikin katafaren gidannan , wayyo dadi boye farin cikinta kawai take yi , ta wani bangaren kuwa hankalinta a tashe yake , saboda batasan ya rayuwarta zata kasance ba a matsayinta na yar basaja , matsayin namiji a gidan sojoji ,

Dawowa azumi tayi hannunta dauke da tray , plate ne mai dauke da snacks , sai 2 cups da jug , a jiye su tayi a sman table sannan ta janyo shi izuwa gabansu ta ajiye ,

Koma tayi tazauna tana murmushi , Sehrish kuwa sai kallon matar take yi har taji ta burgeta saboda tana son mutum mai fara'a ,

Lemu ne a cikin jug din zuba musu hajjaju tayi ta mika ma sehrish , cikin sauri ta karba dama kishi take ji , kurbarsa tayi wani irin sanyi ya ratsa ta ga dadin gaske ,

Azumi ta bi ta da kallo cikin mamaki tace "in ce ko wannan ne d'an aikin da akace za'a kawo mana"? hajjaju ta danyi guntun murmushi tace "eh shine sunan shi tukur kwararre ne wurin iya sarrafa abinci ," saboda jin karyar da hajjaju ta shirgo akanta yasa ta kusa fetsar da lemun da takurba a bakinta , abunda ya kusa sata ta shake shine da ta ce kwararrene wurin iya sarrafa abincin shin yaushe ta son da wannan ?

Sauraron hajjaju ta ci gaba dayi jin tana introducing dinta a wurin azumi " yaro ne mai matukar basira ga wayau , zakiji dadin yin aiki dashi ," takarsa maganar tare da ajiye cup din dake a hannunta saman table din gabanta , sannan ta kalli sehrish tace "tukur wannan itace azumi , itama y'ar aiki ce a gidannan amma taji ssae tana kula da yaran gidan hakan yasa ta zama tamkar uwa agaresu , ina fata zakuji dadin yin aiki da juna ,"

Dakyar sehrish ta kakaro murmushin dole tace "Insha Allah hajiya ,"

Ita kadai tasan halin da ta shiga , wannan zaman da tayi ji ta , kamar ta dosa na ass dinta a saman wuta , saboda tsabagen tsoro , A ranta sai maimaita kalmar 'yaya goma sha takwas kuma duk sojoji take yi ,

Azumi ta janye idonta daga kan sehrish (tukur) ta mayar da idonta kan hajjaju tare da cewa "am inaso na tambaye ki tundazu maganar ke shigemin meyasa kika daina leko mu bayan ina da tabbacin cewa kina zuwa abuja zuwane kawae ke baki yi ,"

Murmushi hajjaju tayi tare da yin yar dariya tace "ai dole zuwa gidannan ko jaraba ! oh kin manta Abunda ya faru last time dana zo ko ? Ina wannan BABBAN YAYAN nan nasu wani mai shegen kyau tubarkalla kamar d'an sarkin aljanu mai kirar zakunan nan ," dariya azumi tayi tare da cewa "wai wa kike nufi cikinsu , kinsan suna dayawa , akwai major , akwai Captain ga janar , akwai Marshall ga kuma Canal da sauransu , kowa da sunan da ake kiransa " takarasa maganar tana kallonta

Sarai tasan wa take nufi amma tafiso taci gaba da zuzutashi don hajjaju ta iya bada labari ,

taci gaba da cewa "oho nidai nasan shi kadai suke ce ma babban yaya , ina gaya miki last dana zo , lokacin nazo dubiyar wannan younger bro dinnasu mai asthma wanda aka fidda kasar waje akayi masa aikin a kirjinsa , " azmi tace "oh nagane junaid kike nufi ae suna waje suna buga ball ynx yaji sauki Alhmdllh ,"

Hajjajun ta ci gaba da cewa "ina fadamiki daga zuwa abun arziki , wlh ina shigowa falon nan ni bansan meya faru ba , nasame shi da y'an uwannan nasa sae faman rirrike shi sukeyi sai huci yake yi just like a hungry lion from the bush gaba daya yayi watsi dasu kasa , ya daga dining table yayi wurgi dashi , gabana ya fadi rass banyi aune ba naji yace "don ubanki kama hanya ki fice, ashe ya ganni "

Wallahi a tsorace a fujajen nabar gidan don tsabagen rudi , da kafa nakama hanyar fita babban gate din saida wani soja cikin security din gidan nan yace mun hajiya kin manta motarki , sannan fa natuna jiki na rawa nakoma nadauko,"

Tun kafin ta idasa labarin azumi da sehrish suke ta faman tikar dariya , kamar cikinsu zai kulle , ita kanta hajjajun dariyar take yi ,
dakyar azumi ta tsaida dariyarta tace

"Hmmm sai ynx nagane wa kike nufi , ai da kinsani ba ki daina kawo mana ziyara ba domin shi ba sojan nigeria bane , US ARMY ne ba a kasar nan yake ba yna dai zuwa sometimes in yasamu hutun aiki ,"

Hajjaju tace "bazaki gane ba ne , yadda na tsorata , ai ko ba don shi ba , wadannan tantiran na gidannan marasa jin magana..." Azumi ta katse mata maganarta ta da cewa "twins kike nufi , tom & jerry suna nan haryanzu basu canza ba sai ma abunda yayi gaba ",

Hajjaju tace "ehen su nake nufi",

Ci gaba da fira sukayi , yayin da hankalin sehrish ke atashe , tunda taji sun ambaci babban yaya sai taji tsoransa har ya shiga ranta , sam ta nemi natsuwarta ta rasa ,

Sun jima suna fira har time din ba wanda yashigo daga cikin soldiers din , har hajjaju tayi shirin tafiya , bayan ta yiwa azumi bayanin akan nemawa tukur wato sehrish alfarmar in tayi one month da fara aiki ta taimaka a ansar mata kudin wata uku a dunkule ,

A tare suka fita har bakin motar ta , sannan suka tsaya suna idasa takarkare zancen
"meyasa bazaki jira abban ba yazo? koya yi miki sallamarki ne "? hajjaju tace "ae indai abba ne bani da matsala dashi nasan zanji alert kinsan hannunsa a bude yake , kuma Abunda yasa nake sauri zan shiga gwarinpa ne gidan wata goggo na "
Murmushi azumi tayi tana kallonta,

Ita ma murmushin tayi mata , harta bude mota zata shiga tasake juyo wa ta kalli azmi tace "pls game da tukur na baki amanarsa , ki kula da duk wani motsi nasa pls ,"

Azmi tace "in dai nice u don't ave to worry about it I will look after him insha Allah ," sallama sukayi hajjaju ta shige cikin motarta ta ja ta ,

Bayan fitarsu sehrish ta zabga uban tagumi tana jin kewar kasancewarta ita kadai a wannan hamshakin gidan da batasan kowa a cikinsa ba , gashi tazo a matsayin namiji , duk in ta tuna wannan hankalinta tashi yake , abu dayane ke kara mata karfin guiwa , y'an uwanta in ta tuna su sai taji ba irin kasadar da bazata iya shiga ba ,

Dawowa ciki azumi tayi fuskarta a sake tace da sehrish " tashi mu shiga ciki na nuna mka bedroom din ka , in ka huta zuwa anjima before magrib zamu shiga kitchen",

Sehrish ta amsa da toh tare da mike wa tabi bayan azmi , suka shiga ciki tayi mamakin bedroom din da azmi ta nuna mata a matsayin nata na yar aiki , wannan koda amayarce tasamu wannan falillahil hamdu , ba tarkace a ciki , single bed ne , ga beside drawer mai dauke da bedside lamp a samanta ga wardrobe madai-daiciya ta manne jikin bango , ga wadatattun curtains a kowane window , komai na cikin bedroom din brown color be banda labulayen da suka kasance milk colour , da zanen gadon ,

Ba abunda ya kara burgeta sai dressing mirriow din da tagani , duk da ba cosmetics a samansa , madubin yayi mata da yar chair din dake gabansa ,

Murmushi azumi tayi ganin yadda yaron yake ta farin ciki don haka tace "komai yayi ko "? da sauri ta amsa da "eh hajiya harma yayi yawa "

Dariya azumi tayi jin yace harma yayi yawa ,
"Ynx dai ni zan shiga ciki , ka zauna ka huta , sannan akwai bedsheets a cikin wardrobe din nan , in zaka canza saika dauka ," tana gama fadan hakan ta fice ,

Kamar jira takeyi azumi ta fita tahau ihu tana tsalle , kafin ta tsagaita da haukan nata ta shiga bathroom din dake ciki ,

Nan fa ta soma wani sabon kallon , ko a mafarki bata taba tunanin zata mallaki irin wannan tsantsararren bathroom dinba mai kama da bedroom saboda haduwarsa ,

Dakyar ta samu natsuwa , ta dauro alwala tafito , a cikin wardrobe din ta samu prayer mat (sallaya) ta dauko ta shimfida , ta kabbara sallah , duka ta hada tayi zuhr da isha saboda batasamu damar yi ba a kan hanya , gashi ynx ankira isha'e shiyasa ta hadesu duka tayi ,

Bayan ta idasa sallar , ta daga hannayenta sama tana addu'ei at the end ta fashe da kuka , Sbd tuna wa da halin da y'an uwanta ke ciki , magana ta soma yi cikin kuka " har ynx na gaza yarda cewa nice zan yi rayuwa a cikin wannan daular ba tare da y'an uwana ba , taya zanji ddin rayuwata batare dasu ba , ni ina nan sukuma suna asibiti cikin wani hali , Allah sarki rayuwa ! bazan taba yafe ma wanda yayi silar shigarmu cikin wannan tashin hankalin ba , Ya Allah ka hana sa jin dadin duniyar nan gaba daya , Ya Allah ka kaskantar da rayuwarsa kamar yarda yayima ta mu....." kuka ne yaci karfinta har ta kifa kanta saman sallayar tana cewa "I will never forgive u in my life and I will neva forgt u ! i must take revenge koda ace nikadai ce na rageda zan yafe maka ka shiga aljanna to tabbas bazaka taba shigar ta ba.
*_Hafsat Bature_*
~(Boss Lady)~


Page 9-10

Bata tashi daga saman sallayar ba har aka kira Magriba tana tunanin abu daya, sai da ta kammala sallar sannan ta nad'e carpet din ta turasa cikin wardrobe , tare da hijab din duka.

tsayawa tayi gaban dressing mirror tana kallon kanta a cikinsa , sak namiji ba wanda zai gane mace ce sai yanayinta ya koma kamar d'an daudu , hannu tasa tare da shafa gashin bakin da ma'reeya ta sanya mata , murmushi ta d'an saki a ranta ta ce "Sehrish ke nan dramatic girl."

Kara kimtsa kanta tayi saboda azmi tace mata akwai aiki a kitchen da zasuyi, sai da ta fara rufe kofar dakin gudun kada Azumi ta same ta tana canza kaya , ta gane cewa maca ce ita ,

Cire kayan jikinta ta yi , ta maida su cikin bag dinta , sannan ta dauko wasu riga da wandon , ta rige a hands sinta gaban mirror din ta koma ta tsaya tana kallon jikinta , ziririn pant ne a ajikinta , takai hannu tasha fa flat tommy dinta , wanda yake a dam'e kaman bata cin abinci saboda shafewarsa ,

Mayar da hannun tayi saman boobs dinta wadanda ta matse su gam , da abun matse belly , har cikin ranta ba taso hakan ba tana son abunta ssae , amma ba yadda zatayi duk cikin aiki ne ,

ga hairs dinta da aka maida mata shi guntu , amma hakan bai dame ta saboda a iya sanin ta in aka aske mata gashi irin hakan cikin one month zai koma yadda ya ke tsayinsa ma harya karu ,

Jin alamar tafiyar mutun kamar bedroom ta ake nufowa shine ysa ta yin saurin , zura dogon wandon tare da rigar sa , tayi gaggawa gyara daurin da m'reeya ta yi mata , mai kamar rawani ,

Kwan ! kwan !kwan taji an knocking , cikin sauri ta karasa ta bude kopan azmi ce tsaye fuskanta da murmushi tace "tukur ina fata ka shirya sbd ynx zamuje na nuna maka yarda abun aikin yake ,"

Cikin girmamawa sehrish tace "toh hajiya ,"

Azmi tayi mata wani irin kallo har gaban sehrish ya tashi a tunaninta ta gano lagwanta , amma sai taji tace "stop calling me hajiya , my name is azmi call me by my name , cos we re d same , am a house maid just like u ,"

taka rasa mgnr tare da fice wa tana cewa "follow me" rishi ta bi bayanta tana d'an murmushi ,

Kitchen suka shiga amma sehrish ta gaza gane a ina suke , haduwar wurin ce ta rikitar da ita , an kawata komai na kitchen din da dukkannin abubuwan da akeso,

Sam ta manta aiki ya kawosu sai faman kalle-kalle take yi , sai da taji muryar azmi a kunnanta sannan ta dawo dai dai

"tukur ynx bamu da enough time , we'll make a dinner now in yaso zuwa tomorrow i will explain everything to u , Especially zama da samarin gidan nan darasi ne me zaman kansa duk zan koya maka ,"

sehrish sai take ganin maganar azmi kamar shiriri tace , ynx har akwai mutumin da za ace sai an koyi darasin zama dashi ?

haka suka fara aiki , azmi ce ke yin girkin , yayin da tabarma sehrish ferar dankalin turawa , ga yankan albasa , acewarta tafara da karamin aiki ,

Suna cikin aiki sehrish tafara jiyo karar shigowar motoci , rass taji gabanta ya fadi , da jiniya motocin ke shigowa ,

"Hmmmm wannan alama ce mai nuna cewa masu gidan sun dawo " a cewar azmi ,

Zuciyar sehrish sai harbawa take yi saboda tsananin firgicin da wa zata fara cin karo ,

"Ka'ida ne daga sun shigo babban falo zasu fara kwalamin kIra ka saurara kaji ," azumi ta fada tana murmushi ,

Hannun sehrish sai kakarwa suke yi ,

ita dai baza ta iya tantance muryar mutun nawa bace amma taji sauti iri iri

"Azumi ! Azmi !! Azam zam !!!" da karfi suke kwala mata kiran without any respect , cikin sauri azmi ta fice tana ce ma sehrish "pls ka kula da girkin am coming back now ,"

Sehrish ta amsa da toh , daga inda take tana iya hangosu saboda kitchen din irin model design dinnan ne wanda ba kopar shiga gare sa a bude yake bata iya identifying faces dinsu ,

Hankali a tashe azmi takarasa wurunsu tana fadin "welcome back Sirs ," ko arziki amsa bata samu ba sai complaining da suka soma yi mata, "Ina fata angyara min bedroom dina don bansan kazan ta ! in ma kinsan baki gyara ba let me know ," daya daga cikinsu ne yayi wannan maganar ,

matsawa tayi kusa dana gefensa don taji shi mai zaice , hannu ysa yana shafa ciknsa yace "Ni matsala ta abunda zansa ma cikina pls kafin na shiga ciki nayi bath na tarar da abinci jere saman dining table if not kinsan sauran ,"

matsawa azmi ta sake yi kusa dana gefensa dayake duk suna a jere kusansu takwas,

" Na fadamiki Injin wanki na ya samu matsala dazu da safe ga shi na tara kayan dauda , gajerun wanduna na ma duk sunyi dirty dafatan kin wanke mun su ,"

Haka ta dinga sauraransu ba wanda baiyi magana ba acikinsu , bayan ta gama sauraransu one by one tace " Komai da kuka lissafamin na kammala sa , abinci ne kawai shima ynx zan idasa ,"

Kama hanya suka yi kowa ya wuce bedroom dinsa , wasu na upstairs wasu na a downstairs,

Babu abunda ya burge sehrish sai kakin sojojin dake

6 Comments On ABBAN SOJOJI
avatar
ibrahim-5-3

1 year ago

Reply

Ina son abban sojoji complete

avatar
ibrahim-5-3

1 year ago

Reply

Ina son abban sojoji complete

avatar
muhammad-4-3-8

1 year ago

Reply

I want it

avatar
hauwa-said

1 year ago

Reply

Please Ina so

avatar
hauwa-said

1 year ago

Reply

Please Ina so

avatar
husaini

9 months ago

Reply

I love this novel

Please Login or Register in order to submit comment