Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi," sannan yasa hannu ya ɗauka, ta ajiye musu tray ɗin a saman table,
kamar karta fuce haka take ji, wani irin sanyi take ji in tana kallonsa, yayi wani fresh abunsa cikin singlet da shorts,
"Ji mana," adams ne yayi mata magana cikin sauri ta juya ta kallesa tare da cewa "Na'am"
"Amma kai sabon mai aiki ne ko? Ina aunty azmee ne?
ya tambaya yana neman jin ƙarin bayani
Sehrish tace "Eh sabone, aunty azmee tana nan,"
Jinjina kansa yayi kafin ya kuma cewa "Suna fa"?
Rishi tace"Tukur,"

Abun mamaki sai taga yana mata dariya gashi kuma yana bin ƙafafunta da kallo abun ya ɗan bata tsoro,
Tsagaitawa da dariyar yayi tare da cewa "Wow good wasan kwaikwayon fa yayi kyau sosai," sam Bata gane me yake nufi ba duk ta dabarbace, duk wannan maganganun nasu a kunnan sgr,
"u can go mr Tukur," adams ya umarce ta yana mai ci gaba da ɗan murmusawa,
Jiki asanyaye sehrish ta fuce tana mai mamakin wannan abokin na Sgr, komai yake nufi da dariyarsa Oho, ta faɗi tana yarfa hannayenta,

Kurbar coffee ɗin yayi yana cewa "Sgr ina kuka samu ɗan aiki ne?
"Don't know," ya bashi amsa,
Adams yace "Wannan fa maca ce tayi shigar maza wlh, amma fa ta iya shiririta,"
ɗan kallonsa sgr yayi tare da cewa "Wa kenan?
"House boy ɗin nan mana, daya kawo mana drinks yanzun nan,"

Sgr yace "Are u serious ?

Adams yace "Of course baka ta6a lura bane?
Sgr yace "taya zan lura, bayan ko face ɗin mai aikin bansani ba,'
Adams yace "No wonder that's y baka lura da hakan ba, amma fa maca ce wannan hada sa gashin baki, ' ya ƙare maganar yana dariya don kam ba ƙaramin nishaɗi abun ya bashi ba, shigar yarinyar amatsayin namiji kamar ɗan chali chali,
"Amma ko meyasa tayi hakan"? Adams ya tambaya yana kallonshi,"
Ajiye cup ɗin dake hannunsa yayi tare da cewa "Zan bincika, koma wa ya turo ta, zan sani ne, zasuyi bayani," Acewar sgr,
"Gsky kam, u ave to investigate about it, kasan mugun mutun bakasan da wata siga zai shigo rayuwarka ba, especially yadda kke da suna haka ba'a rasa enemies masu son kawo muku hari ta bayan fage, ya kamata ka miƙe tsaye akan lamarin wannan mai aikin tukur, kasan da wata manufa yazo domin kuwa wlh maca ce ba namiji ba,"
Adams ne yake kora masa bayani yana ƙara jaddada masa akan mai aikin Don ayi saurin dakatar da shi daga abunda yake ƙoƙarin aikatawa, 😳

Sehrish fa batasan wainar da ake toyawa ba, Ashe watan cin uban wata yayi acikin gidan nan 😂
bedroom ɗinta ta koma tana safa da marwa, cike da tunanin dariyar da taga abokin sgr nayi mata aranta tace wata'ƙil shigar mazan da nayice ta bashi dariya Allah saki,


__________________________________

A hankali motocin marshal Omar suke shiga cikin katafaren gidan General Ishaq wanda ke a Unguwar rimi,

Hamshaƙin gidan wanda sojoji ke tsare dashi ta ko'ina, jahad sai faman bin gidan take da kallo ganin haɗuwarsa ta cikin glass ɗin motar, jinjina kanta tayi aranta tace "Aljannar duniya,"
Juyawa tayi ta kalli hosana wadda ta kwantar da kanta a kafaɗar Jahad ɗin sai faman bacci take shararawa murmushi jahad tasaki tare da cewa "Nasan hosana in taga wannan haɗaɗɗen gidan dole ta susuce,'
Mayar da idonta tayi kan glass ɗin tana ƙarewa gidan kallo aranta tace "Allah yasa kamar yadda gidan nan yake da kyau mutanen gidan ma zuciyarsu ta kasance mai kyau ce kamar haka, Ya Allah kasa kasancewar mu acikin gidan nan yasa ƙarshen wahalar mu kenan, Allah yasa mutanen gidan suyi marhaban da zuwan mu kuma su tarbemu hannu bibbiyu kamar yadda goggon katsina tayi mana," ta ƙare maganar tana mai jin wani sabon yanayi atattare da ita,

A jere motocin suka tsaya, sajan ɗin dake driving ɗinsu ya fito ya buɗe musu mota,
fitow jahad tayi tana faɗin "Hosana ki tashi mun iso fa,"
daker hosana ta buɗe idonta da sukayi luhu luhu tana bin jahad dake mata magana da ido, daker ta iya sa ƙafa ta futo daga motar tana murje idanunta don taƙara tabbatarwa kanta cewa dagaske ne hamshaƙin gidan da take ganinsu aciki ba mafarki ba, aiko ta shaida hakan,
Fitowa Marshal Omar yayi daga tashi motar, yana sauke ajiyar zuciya kafin ya juya ya kalli su hosana yace " ku biyo ni,"
Bin bayansa su kayi atare suka shiga hadaɗɗen jigunannan babban falon Aunty babba, wani irin daddaɗan ƙamshi ne ke fitowa ta cikinsa abunka ga ƴan maiduguri dama an shaidasu akan hakan,

Wasu irin haɗaɗɗun Sofas ne masu Numfashi sets guda, launinsu Maroon colour, ga sofa tables ɗinsu launinsu,
Falon yasha ado da decorative object ga vase ajiye (tukunyar flower) ga wata irin faskekiyar plasma manne a wall ɗin kai komai fa yaji ya haɗu,
Babu kowa a falon sai sanyin A.c dake ratsa sassan jikin mutun,
"Have a seat," umar ya umarce su sai faman bin ko'ina suke da kallo , a tare suka zauna saman 2 seater suka takure junansu tsoransu dawa zasu fara cin karo,
Shima yasamu wuri saman 3 seater ya zauna yana facing ɗinsu idon shi nakan hosana wadda ke ta faman lumshe ido saboda baccin da takeji ga yunwa,
Phone ɗinsa ya zaro daga trouser pocket ɗinshi ya danna numbar aunty Babba ya buga mata Calling,
Da ƙarfi wayarta ƙirar Iphone 13 pro max ta soma ringing tana ajiye saman bedside drawer gefen lamp,
Hajiyar na hakimce tana sharar bacci Saman haɗadɗen gadon nata, jikinta na sanye da riga da wando masu kyan gaske ga laushi kamar sleeping dress haka suke,

takurar da ringing ɗin yayi mata ne yasa ta buga uban tsoki a ƙule cikin bacci take cewa "Mtsww Wai wanene ne yake son takuramin ina tsaka da jin daɗin baccina," ta ƙarasa maganar tana buga Uban tsoki rai a bace ta tashi zaune fuskarnan kamar Alkubus a kumbure take don ma Allah yasa akwai kyau da haske ssae da ba ƙaramin muni zatayi ba,
Hannu tasa ta fisgi wayar ta duba ta ga wanene, sunan (Marshal Omar ) ne ya bayyana akan screen ɗin wayar, ae tuni ta wartsake daga baccin da take yi, jiki na rawa ta ɗaga tare da karawa a kunnanta tace "salamun Alaikum," bai amsa mata ba sai cewa yayi "Muna a palor muna jira,"
Cikin sauri tace "oh to gani nan zuwa,"
Ta ajiye wayar tare da miƙewa tasa hannu ta ɗauki mayafin kayan jikinta dake ajiye saman gadon, ɗaure shi tayi akanta maimakon tayafa shi a jikinta, sumar kannan nata tasha ƙananun kitson kalaba,

A hankali take tattaka steps ɗin benen tana saukowa down, tun da suka ji takon takalmi suka ɗago suna kallonta haƙiƙa sun tsorata da kyawun matar ga yanayinta na marasa son mutane da hayaniya haka,
Jinjina kai su kayi tare da kallon juna lokaci guda suka mayar dakansu ƙasa,
A second to the last steps na stairs ɗin ta tsaya Curus ! tana kallon tagwayen matan da tagani zaune saman kujerunta sai taga abun kamar a mafarki gadai marshal omar zaune to su waɗannan isassun da suka zauna matan saman kujerunta su wanene ta tambayi kanta, har hannu take sawa tana murza idanunta don ta tabbatar cewa ba mafarki take yi ba,
Idasa saukowa tayi har time ɗin bata sauke idonta ba daga nasu Hosana wani irin kallo take binsu dashi kallon neman ƙarin bayani,
Muryar Omar ce ta katse ta da cewa "barka da fitowa aunty, fatan na same ku lafiya,"
Lokaci guda ta saki fuskarta ta ƙarasa ta zauna saman 1 seater tana cewa " Yawwa Omar saukar yaushe? wlh bacci ne ya kwashe ni nasan dae ka ce mun zaka zo nan bfr ka wuce abuja,"
Omar yace "Eh hakane, ina yaya ishaq ne?
"Ae bayan kabar nan, shima yayi tafiya,"
Ta faɗi tana kallonsu hosana da jahad, wadanda suka sha jinin jikinsu tuntuni musamman da suka gaisheta sai tayi kamar batagansu ba,
Miƙewa tayi tare da cewa "bari na kawo muku abun ta6awa,"
tayi mgnr tare da wuce wa kitchen, tana shiga ta tsaya riƙe da qugu tana sake sake iri iri aranta.
"Su wanene waɗancan twins ɗin da Omar ya kawomin a gida? hankali na fa bazai kwantaba har Sai nasan su wanene da kuma matsayinsu a wurinsa,"
ta ƙarasa tunanin nata tare da shigewa ciki tana shirya musu Abunsha dana ci,"

Su hosana da jahad kam sunfa shiga taitayinsu tundaga irin kallon da Aunty Babba tayi musu,
"Bacci kike ji ne har yanzu"?
Jahad ce tayiwa hosana tambayar, a kasalance hosana tace "sosai ma ga yunwa ina ji,"
"Wacece ke jin bacci"? Marshal Omar ya tambaya don yaji firar tasu,
Hosama tace "Ni ce, kuma hada yunwa nake ji ma," tayi maganar tana ɗan turo baki,
Murmushi gefen fuska yasaki yana ɗan kallonta yanayin yadda tayi maganar ba ƙaramin tafiya tayi dashi ba,
" ok ki bari ki fara cin abincin sai ki yi wanka inyaso daga baya sai kiyi baccin ko? ya faɗi yana kallonta, hosana tace "to shikenan,"
Ya jinjina kansa

Shigowa Aunty Babba tayi hannunta ɗauke da tray tinkis tinkis take tafiya, har ta ƙaraso ta ajiye musu shi a saman table ɗin dake kusa da Marshal Omar,
"ki miƙa musu, ni bana buƙatar komai ynx," ya faɗi yana kallon wayar dake hannunsa dayake dannawa,
daurewa kawai aunty babba takeyi, matsar musu da table ɗin tayi gabansu tace "gashi nan ƴan mata,"
Har haɗa baki sukeyi wurin cewa "mungode,"
Jiki na rawa hosana ta ɗauki coke mai sanyi ta buɗe tashiga ɗaɗɗakar lemun har ta kusa shanyewa duka, jahad kuwa jiki asanyaye ta ɗauki robar swan tana sha,
Jinjina kai aunty Babba tayi ganin yadda yarinyar take ta faman kerma jikinta na rawa taga abunci aranta tace "To fa !
Bayan ta koma ta zauna ta kalli marshal Omar tare da cewa "har yanzu bakayimun bayanin waɗannan twins ɗin ba dana ganku atare,"?
gyara zama Omar yayi cikin natsuwa yasoma magana "Babu buƙatar dogon bayani, na kawosu ne zasu zauna nan atare daku na wani lokaci.......'
Yadda aunty babba ta zabura tsaye yasa shi dakatawa da bayanin yana kallonta yace "lafiya"?
A susuce ta koma tazauna tana cewa "babu komai ci gaba da bayani,"
Ajiyar zuciya yasaku tare da cewa " zasu zauna anan, kamar yadda nace bana buƙatar kowa ya kashe ko sisin shi akansu, komai suke buƙata lissafi kawai za'a yimun na turo,'
Murmushin yaƙe aunty babba tayi tare da cewa "wannan ae mai sauƙi ne Omar, zasu samu kulawa sosai amma abunda nakeso nasani shin su wanene su?
"Ba buƙatar sani Aunty Laila, kawai a kulamun dasu yadda ya dace," ya faɗi yana kallonta,
Jinjina kai aunty babba tayi tare da cewa "shikenan za'ayi kamar yadda kace insha Allah,"
Ya amsa da "Okey ynx zan wuce masallaci kafin nadawo pls abasu bedroom ɗin da zasu zauna su huta,"
Ya faɗi tare da miƙewa yasa kai ya fice,

Maida idonta tayi kansu Hosana da jahad fuskarnan a murtuke,
Hosana sai faman cin fried rice ɗin da ta shaƙe a plate takeyi tana korawa da lemu a cup, ko lura da kallon da Aunty babba keyi musu batayi ba,
Sai jahad ce ta ankara da hakan har tayi saurin ajiye spoon ɗin dake hannunta cikin plate gabanta na faɗuwa,
Muryarta ce ta katse su da cewa "kai !! Su wanene ku? ƴa'ƴan waye ku a dangin Su Omar?
dakatawa da cin abincin hosana tayi tana kallonta, murya na rawa jahad tace " Mu bamusan kowa a dangin shi ba, taimakon mu yayi saboda ya tsince mu cikin wani hali,'
Fashewa da dariya aunty babba tayi har saida suka razana, hannu tashiga tafawa tare da cewa "Wlh kun shiga uku !! meyasa baku bashi shawarar yakai ku Orphanage Home ba? Sai gidana za'a kawomin tsintattu, to bari kuji in faɗa muku Omar yayi gangancin jefa rayuwarku cikin haɗari domin ni bani da Imani wlh,' ta faɗi a faɗace tana kallonsu
Gabansu ne yayi mugun faɗuwa just now suka zo gidan amma gashi matar gidan ta bayyana musu halinta tabbas akwai matsala,
Shewa tayi "Ahayyye !!! wai ni za'a kawo wa tsintattu na riƙe ae wlh kun shiga uku kuna cikin masifa domin Laila bata da mutunci ,
Sam sun gaza ci gaba da cin abincin jikinsu sai kerma yake yi saboda tsoran wannan matar da ta kira kanta da Mara imani, mara mutunci,
jinkirtawa tayi tana kallonsu tana yatsina fuska kafin tace "me kuka tsaya kuna kallone? Kuci gaba da cin abincin ku domin daga inda Omar yasa ƙafa yabar gidan nan kuda ganin Abinci sai dae kuji ƙamshin sa Wlh," ta faɗi tare da miƙewa ta wuce room ɗinta dake asaman upstairs,
Tuni hawaye sun soma zubo ma jahad masu zafin gaske har taji ta tsani abincin da take ci ma, ita kuwa hosana jikinta yagama mutuwa jin abunda matar tace wato su da ganin abinci sai dae su ji ƙamshinsa, tuna wannan yasa ta fashe wa da kuka,
Haƙiƙa suna cikin tashin hankali kuwa,

Cikin kuka hosana tace "jahad Mun shiga uku,dama yaya Omar yabarmu gidan goggon mu da aunty saude,' tayi maganar tana lashe hannunta ga hawaye sha6a sha6a,
Cikin shesshekar kuka jahad tace "hosana duk yadda za'ae karmu bari yaya Omar ya tafi yabarmu agidan nan, wlh kashe mu zatayi tace bata da Imani, kuma xata mana Horon yunwa innalallahi mun yi gudun gara mun faɗa gidan Zago 😭

Jikinsu duk ya gama mutuwa ga gajiyar tafiya gashi suna son suyi sallah su ɗan kishin giɗa amma ba halin hakan,

Murya na rawa jahad tace "Hosana ki ci gaba da cin abincin, kwara muci ko na yau ne tunda tace daga yaya Omar yabar gidan sai dae muji ƙamshinsa,
Hannu suka sa Hannu suka ci gaba da cin abincin ba ƙaƙƙautawa, hannu baka hannu ƙurya suna ci suna matsar kwalla,
Sai da suka kammala da komai sannan suka jinkirta suka zauna jiki a mace,

Jin ƙarar shigowar motocin Omar yasanya Aunty babban yin saurin fitowa daga room ɗinta ta sauko down jiki na rawa ta kallesu tare da cewa "Maza ku share hawayen nan dake a fuskarku, wlh muddin ku ga ja Omar ya gane cewa wani abu ya faru saina Murƙusaku a wurin nan, Dallah ni ku taso ku biyoni,
Jiki na kerma suka bi bayanta cikin hanzari takai su wani room ya hadu sosai ba hayani komai simple,
Shiga ciki su kayi rai a6ace tace "ku shiga toilet ku gyara jikin ku, ko da gigin wasa kar na kuskura naga wata ta leƙo d daga ɗakin nan balle ma ta fito!"
Tana gama faɗin hakan ta fuce tana sakin murmushi mugunta,
Falon ta koma ta tattare kayan abincin da sukayi Amfani dashi ta wuce dasu kitchen, tana a cikin kitchen ɗin tajiyo shigowarsa,
Fitowa tayi tana faman sakin murmushi taƙarasa tana faɗin "harka dawo kenan,"
Ya amsa mata da cewa "Eh ina yaran suke," ya faɗi a yayin da yake zama saman seater,
itama ta zauna tana faɗin "Ae tunda kasa kai ka fuce, bayan sun kammala cin abinci na nuna musu ɗaki ynx haka sun kammala wanka sunyi sallah ynx bacci ma suke yi,"
lumshe ido Omar yayi alamar jin daɗi aransa sannan yace "naso ace na nasake gaisawa dasu don yanzu zan wuce abuja,"
cikin sauri tace "gsky kam, amma fa sunyi nisa a baccin nasu, bai kamata atashe su ba,
Omar yace "hakane kuma, Ni yanzu zan wuce," ya faɗi tare da miƙewa

Aunty babba tace "Toh Omar agaishe mana da mutanen gidan Allah ya tsare hanya,"

Su hosana dake cikin ɗaki suna faman safa da marwa duk maganar da Omar yake yi da aunty babba a kunnansu yake yi, bayin Allah suna so su fito suce mashi karya tafi yabarsu a hannun wannan matar amma ba hali don ta tsawatar musu akan karsu Kuskura Su fito, hawaye kawai ke zuba daga idanuwansu domin suna leƙen Omar ta Window ɗin ɗakin, a yayin da yajuya baya ya soma tafiya shi kanshi hakanan ya dinga jin babu daɗi jikinshi atlease yaso ya sanyasu acikin idonshi kafin ya tafi tunda baisan ranar dawowarshi ba,
Har yakai bakin kopan fita daga falon ya juyo ya kalli aunty babba dake tsaye yace "AMANATA ki kulamin pls,"
Murmushi tasaki tare da cewa "Baka da matsala dani ƙanin Miji na, insha Allah zan kula maka dasu sosai,'
Jinjina kansa yayi tare da juyawa yasa kai ya fice,"
Su Hosana najin tashin Motocin shi, nan take suka fashe da wani irin matsananin kuka mai cin rai suka rungune junansu😭


*BossLady*

Keep sharing my Novel everwhere
,*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*

*🔥the father of soldiers🔥*

Story by *Hafsat Bature*

~BossLady~

ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭ ﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ
ﺭﺍﻓﻴﺖ💓💞


*Episode 90-91* 💘

*🔔🔔🔔daga ynx ranakun da zaku samu posting na abban sojoji 3 days ne a week sbd ina busy ssae, amma zan ƙara muku yawan pages, days ɗin danayi Choosing sune Monday Tuesday da kuma wednesday daga zarar wadannan kwanakin sun zo daraina da lafiyata zaku samu posting da sassafe* 👏🙏



~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~SEHRISH


Jin knocking yasa ta tayin saurin miƙewa daga zaunan da take saman gadonta , ƙarasawa tayi jikin ƙopan tare da cewa "Wanene"?

"Aunty azmee ce" ta bata amsa daga waje,

Ajiyar zuciya sehrish tasaki tare da buɗe mata ƙopan, shigowa azmee tayi jikinta na sanye da Doguwar riga sai babban mayafin da ta yafa,

"Ƙanwata me kke yi yanzu ne? halan kina nan zaune cikin damuwa ko? ko irin kiyi tunanin kin gaji da zaman kaɗaici ki kawomin Ziyara a bedroom ɗina bakya yi ko?

tayi maganar tana kallonta, cikin jin kunya sehrish tace "Aunty azmee bana so na taƙura maki ne, shiyasa bana zuwa ɗakin ki,"

Murmushi Azmee tasaki tare da cewa " babu wani batun takura anan, kawai bakya son zuwane, nima kaina gajiye nake da zama wani sa'in duk atukure mutun kamar maye shikaɗai a ɗaki haba,"

azmee tayi maganar tare da shigewa cikin ɗakin sehrish tasamu wuri ta zauna gefen gadon, itama sehrish ɗin wuri tasamu gefen azmee tana fuskantarta,

Kallon juna su kayi lokaci guda suka sakarwa kansu murmushi, Azmee tace "Naji shiru baki tambaye ni game da sabuwar wayar da nace an baki ba"?

Sehrish tace "jira kawai nake, in kin bani in kar6a,"

Jinjina kai azmee tayi tare da cewa " kiyi hkr sai zuwa gobe wayar zata iso,"

"Babu komai aunty azmee zanjira ni da za'a taimaka mawa abani kyauta, amma aunty azmee wanene ya siyamun wayar"?
ta tambaya tana kallonta,
"Ba abani iznin in faɗa ba, sai nan gaba zaki ji koma wanene,'
Murmushu sehrish tayi tare da cewa "Allah yakaimu time ɗin da rai da lpy

"Ameen" azmee ta amsa mata sun ɗan yi shiru na ɗan wani lokaci, kafin sehrish ta ce "Aunty azmee wai su Babban yaya Ina mahaifiyarsu take ko ta rasu ne? ta tambaya tana kallonta ,

"tana nan mana, tana zaune a sydney ƙasar Australlia,'

Jinjina kai sehrish tayi kafin ta kuma cewa "Amma mommynsu ita ba ƴar nigeria bace ko?

"Kin ga hotanta ne"? Azmee ta tambaya

Murmushi sehrish tayi tare da cewa "ban shaida ba, amma naga hoton wata mata Mai kyau baturiya mai sanye da kakin Soja a bedroom ɗin Babban yaya saman bedside drawer aka ajiye hoton,

Azmeee tace "dawa tayi miki kama acikin su"?

Sehrish tace "Babban yaya sunyi kama ssae hada blue eyes ɗinsu ma, sai kuma su twins da fawan, amma dae aunty Azmee dukansu ba uwarsu ɗaya ba ko? Ta ƙarasa maganar tata da tambaya,
Azmee tace "eh su Twins da fawan da Babban yayansu da junaid uwarsu ɗaya, suma su Kanal Yusif mahaifiyarsu daban'

Jinjina kai Sehrish tayi tare da cewa "Su mommynsu ƴar wata ƙasa ce aunty azmeee?

Cikin zolaya Azmee tace "Kice yau kin shirya son sanin wacece surikarki da alama naga kina ta jefamun tambayoyi akanta ko ba haka ba"?

Sunnar da kai sehrish tayi tana kallon yatsun hannunta cikin jin kunya

Azmee taci gaba da cewa "Sunan ta *Fatima ita ƴar America ce amma tana zaune a Australlia,"

ɗan shiru tayi na wani lokaci kafin ta sake cewa "Aunty azmee Yaushe zata zo nigeria ne? ita bazata zauna nan ba ko Abba ya sake ta ne?

Dariya azmee tayi tare da cewa "Wasa wasa sehrish kema fa kin iya surutu na lura wurine baki samu ba shiyasa kike noƙewa kamar bakyason magana," tayi magana tana ɗan kallonta,

"In har aka tashi aurenki da babban yayansu ae dole tazo asha biki da ita,"

Jin wannan maganar ta aunty azmee yasa Sehrish ɗan zaro ido hada dafe ƙirji aranta tana cewa "tab ! Wannan matar ta cikin hoto anya xata barni in zama surukarta daga gani zatayi zafi Allah,

Murmushi kawai azmee takeyi tana kallon Sehrish dake faman sake sake aranta,

Ita kanta Azmeen zolaya take mata amma tasan cewa sarai Alexandra bazata ta6a bari Sgr ya auri bakar fata ba,

Sun jima suna fira har wurin sallar la'asar sannan azmee tayi mata sallama ta fuce izuwa nata ɗakin,

tashi tayi itama ta shiga ta ɗauro alwala tayi sallah, bayan tagama ta shirya zuwa kitchen don tasan da wuri zasu fara preparing dinner,"

time ɗin da tafito babu kowa wayam falon kai tsaye kitchen ta wuce, azmee bata iso ba don haka tafara fiddo abubuwan da zasu yi amfani dashi, tafara aikin kafin ita tazo, Aiki take amma hankalinta natashe tarasa dalilin dayasa take jin wani irin ɗaci aranta, wanda hakan alama ce dake nuna cewa waninsu nacikin matsala, Ita ko suna hosana
Har azmee ta shiga sam sehrish bata ankara ba har sai da tace "Good girl haka nakeso kina aiki da azama," murmushi sehrish tasaki tare da kallonta tace "Aunty azmee ae dama baki fito ba ni namiki aikin duka,'
ɗan harararta Azmee tayi tare da cewa "Ki zubamin detergent aciki a matsayin gishiri?
Dariya sehrish tayi jin abunda tace "No aunty azmee bazan sake wannan mistakes ɗim ba,'
Azmee tace "Hmmmm zamu gani ae,'

Shiga ciki tayi suka kama aiki cikin ƙanƙanin lokaci suka kammala, basu jera abincin a dining ba sun bari sai after magriba prayer,"

Cike da zumuɗi ta shiga tayo wanka, ta kimtsa kamar kullum, hada alwalarta jira kawai take Yi a kira sallar magrib taje su haɗu da junaid cos she's so eager to see him,'
_________________________________
Fitowa daga wanka junaid yayi fuskarnan a washe zai haɗu da sehrish ɗinsa, daga shi sai shorts ajikinsa, shaf shaf ya shirya cikin shirt ash colour mai dogon hannu sai dogon wando black colour, wow baƙaramin kyau kayan su kayi mashi ba, ya feshe jikin shi da turaren spice bomb sannan ya zura shoes a ƙafansa launin wandonsa,

6 Comments On ABBAN SOJOJI
avatar
ibrahim-5-3

1 year ago

Reply

Ina son abban sojoji complete

avatar
ibrahim-5-3

1 year ago

Reply

Ina son abban sojoji complete

avatar
muhammad-4-3-8

1 year ago

Reply

I want it

avatar
hauwa-said

1 year ago

Reply

Please Ina so

avatar
hauwa-said

1 year ago

Reply

Please Ina so

avatar
husaini

9 months ago

Reply

I love this novel

Please Login or Register in order to submit comment