Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nan take wandon ya tafi suuuuuuuuuu zai sabule jiki na rawa ta cafko shi tayi saurin maidashi ta ɗaure abunta a yayin da zufa ke wanko mata,
◻ Dariya haroon yayi kafin ya tsagaita yace "Ke !!! nifa tun jiya dana ganki nasan cewa Ke maca ce ba namiji ba !!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!
◻ ɗagowa da ido sehrish tayi a firgice tana kallonsa tamkar a mafarki take jin kalaman haroon .
◻ Ƙara jaddada mata yayi da cewa "Ke maca ce ba namiji ba !! ki faɗamin uban miyasa kikayi shigar namiji kika zo gidannan? Da kwai wata manufa aranki ko !!?
◻ Muryar na rawa sehrish tace "innalallahi wa'inna ilaihirraji'una!! taya akai ka gane cewa Ni maca ce farat ɗaya!?
◻ Dariya haroon yayi tare da cewa "saboda ni Shu'umi ne ! Kuma cikakken ɗan duniya wanda idonsa ya buɗe a harkar barikanci ! ba wani abu da mutun zai 6oye mun batare dana gano sa ba,"
◻ "Shikenan nashiga ukuna !! dan Allah ka rufemun asiri karka ce zaka tona cewa ni maca ce pls!!
◻ Ajiye ayabar dake hannunsa yayi cikin tray ɗin sannan yace "Okey, i won't expose ur secret but under one condition!!?.
◻ Ya faɗi yana kallonta a raunane sehrish tace "koma meye zanyi nidai karka tona mun asiri," tuni idonta ya ciko tab da kwalla,
◻ Har wani lumshe ido haroon yake yi yana kallonta " share hawayenki baby, bani da matsala muddin za'a biyamun buƙatata,'
◻ shiru sehrish tayi tana sauraron shi
◻ "Zamuyi magana anjima yanzu zaki iya tafiya naga kuna cikin aiki ne,"
◻ tunkan ya idasa mgnr sehrish ta fuce tana shasshekar kuka ,
◻ sai da ta dakata bayan ta fita ta tsaya ta share hawayenta tare da dai dai ta natsuwarta sannan ta sauka ƙasa, anan ta samu ma Aunty azmeen tana jera musu breakfast ɗin a dining,
◻ Karasawa tayi suka ji gaba da jerawa atare,
◻ Kallonta azmee tayi tare da cewa "Naga kin jima ! Lapiya dae ko?
◻ "Eh," ta bata amsa atakaice, ita kaɗae tasan yadda take ji aranta, brain ɗinta ta gama shiga ruɗu tashiga tashin hankali mamakinta taya akai farat ɗaya haroon ya gane cewa ita maca ce !? how many days ta share a gidan amma ba wanda ya ta6a lura in aka cire junaid sai shi wanda jiya jiyan nan yazo da daddare, tabbas abun ya ɗaure mata kai, kuma tasa mishi alamar tambaya, (?) Anya ba Aljani bane

◻ gaba ɗaya ta tafi duniyar tunani har batasan cewa masu gidan duk sun fito ba, domin yin breakfast, yawancinsu duk jallabiya ce ajikinsu,
◻ Fawan da twins ne suka fara hallara suka zauna a kusa da juna, sai Irfan da jabeer bayansu sai khaleed da kanal yusif, duk suka gaishe da Azmee ta amsa musu kafin ta ci gaba da saving ɗinsu,
◻ Har time ɗin sehrish bata cikin hayyacinta tana tsaye kamar gunki tana tunane tunane iri iri aranta, sam azmee bata lura da halin da take ciki ba,
◻ A tare Abbansu ya fito da baby junaid hannunsu cikin na juna, fuskar nan tasa a washe tun da idonsa su kayi Arba da sehrish ɗinsa, tunkan ya ƙaraso ya lura da cewa ta tafi duniyar tunani,
◻ Ganin Abbansu yasa suka haɗa baki wurin gaishe shi "Barka da safiya Abba, kun tashi lafiya,"
◻ "Alhamdulillah My Sons ina fata kuma kuna lafiya,"
◻ da fara' a fuskan kowannansu suka amsa mishi,
◻ Bayan sun zauna cike da tsokana junaid yace
◻ "Ni bazaku gaishe ni ba"? ya faɗi yana kallonsu,
◻ Tsoki fawan yaja tare da cewa "kabari sai ka fara ajiye gemu da ƴa'ƴa tukunna,
◻ "Wai junaid da gemu ba rana ba wata, don gsky ban ga alamar junaid zai yi gemu ba ko nan gaba,'
◻ Acewar Jahan,
◻ Abbansu yace "Talle zatai wa audu gori, ka fara duba fuskarka tukunna, muddin junaid bazaiyi gashin baki ba ko na gemu to kaima haka baza ta6a yi ba,"
◻ dariya su kayi gaba ɗayansu kanal yousuf yace "Wai ina Haroon ne ? Shi bazai fito bane?
◻ Abba yace "taya zai fito bayan abunda ku kayi masa jiya, sam banji daɗi ba, tun da ya dawo ya kamata ku tarbi ɗan uwanku hannu bibbiyu, in baku ja shi ajiki ba taya zai shiryu ? Yayi maganar cike da nuna 6acin rai akan abunda su kayi jiya,
◻ "Abba amma ba ka ga irin yadda yake mana magana ba har agabanka batare da jin komai ba? Acewar Irfan,
◻ Ajiye cokalin dake hannunsa yayi tare da cewa " in da sabo ae ya isa ace kun saba da halinsa, addu'a kawai zaku bishi da ita Allah ya shirye shi," yana kai karshen maganar ya ɗauki spoon ɗin yaci gaba da cin abincin dake gabansa,
◻ Jinjina kai su kayi kawai shikam fawan ta6e baki yayi tare da cewa "Ashe dagaske yazo, ae ni nayi tunanin duk mafarki ne zuwan nasa jiya,"
◻ Harararsa khaleed yayi "dole kace haka dama bakwa good time dashi ae,"
◻ tun da suka ambaci sunan HAROON hankalin sehrish ya dawo jikinta, sai faman sauke ajiyar zuciya take yi ga zufa na wanko mata,
aza idonta tayi akan junaid wanda ke ta faman satar kallonta yana mata murmushi
◻ Murmushi itama tasakar mishi,
◻ So yake yayi mata magana amma ba hali sai dae daga inda yake ya rinƙa yi mata alama da bakinsa batare da sauti ya fita ba yace "Sehrish kin tashi lafiya,"
◻ tagane me yake cewa don haka itama tayi kamar yadda yayi tace "lafiya lou junaid ina fata kaima haka,"
◻ ɗaga mata kai yayi alamar eh, duk abunda junaid keyi akan idon Abbansu mamaki yake menene tsakanin junaid da mai aikin nan tukur, kodae sun ƙulla abota ne, ɗan murmushi ya saki domin yaji daɗin hakan, sbd duk wani abu da zai sanya shalelensa farin ciki son shi yake,
◻ "Ga babban yaya nan fa kowa ya shiga taitayinsa" fawan ne yayi maganar a yayin da yake cunkusa kebab abakinsa,
◻ Yadda fawan yayi maganar yasanya abbansu yin dariya, wai ga babban yayanan kowa yashiga taitayinsa, Kanal yusif yace "wato kaine annoucer duk in big bro zai fito sai kace kowa ya shiga taitayinsa, nawa ake biyanka salary ne ?
◻ Dariya sukayi gaba ɗayansu cikin nishaɗi in ka cire Twins dake ta faman jin bugun zuciya,

◻ A tare suka fito su biyu shi yana saukowa daga saman stairs yayin da shi kuma Haroon ke fitowa daga part ɗinsu dake a nan down,
◻ Jikinsa na sanye da tank top riga ce kamar singlet haka take fara, sai wando jeans, sumar nan tasha gyara,
◻ Shi kuma Haroon shirt ce da gajeran wando ajikinsa, ga uban gashin jiki da Allah yayi masa don ma Allah yasa kwantacce ne amma duk da haka ba kyan gani,
◻ Ganin Sgr yasa shi fara yi mashi kirari "Barka da Fitowa Babban yayanmu Namijin Zaki Uban dawa, mai mulkar ƙananun ƴan iska kai ɗaya tak kake tada runduna, gabanka Bullet bayanka Bomb ka ga Ingarmar Namiji ƙasaitacce takawarka lafiya Namijin duniya,'
◻ wannan kirarin na haroon yasa su Yousouf dariya, shi kuwa Sgr ko kallo haroon bai ishe shi ba,
◻ A tare suka ƙarasa ya zauna a empty chair ɗin dake kusa da Junaid, haroon ma yasamu wuri ya zauna,
◻ "Barka da safiya Abbana abun alfaharina,"
◻ Murmushi Abba yayi tare da cewa "Yawwa barka dae Haroon ya gajiyar tafiya ?
◻ "Abba ae ta washe tun jiya, yanzu garass nake jina,"
◻ Jinjina kai Abba yayi tare da cewa "Naji kace ka ƙaro wulaƙanci dagaske ne?
◻ Cikin sauri haroon ya saci kallon Babban yayan nasu yace "Bana cikin hayyacina ne, shiyasanya nayi maganar,"
◻ Murmushi su kayi gaba ɗayansu,bayan nan suka shiga gaishe da babban yayan nasu, bai amsa ba sai dai ya rinƙa yi musu alamar yaji da kansa, gyaran murya abbansu yayi hakan yasa Sgr ɗagowa ya kallesa cikin sanyin murya yace "Gm Dad,"
ta6e baki Abba yayi tare da cewa "sai ynx ka ganni? Ni fa narasa ganewa, nan gaba ina ga sai na rinƙa gaishe ka dakaina da alama,
"Insha Allah hakan bazata ta6a faruwa," sgr yayi maganar ayayin da yaɗauke idonsa daga nakan Abban, Murmushi Abban yayi, yarasa dalilin dayasanya yake jinshi sosae aransa ko dan yana kama da Momynsa alexandra,

Sehrish kuwa
◻ Wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarta time ɗin da tayi arba da kyakkyawar fuskar Sgr duk da a firgice take ganin yadda haroon ke satar kallonta,

◻ tunkan azmee tayi yunkurin zuba mishi breakfast ɗinsa sehrish ta riga ta, plate ta ɗauka ta zuba mishi Chips ta shake mashi shi, sannan ta tura mishi agabansa ta kuma haɗa masa da hot coffee a acikin cup,
◻ "Mlm tukur ni baza'a zuba min bane"? Haroon ne yayi mata maganar yana binta da wani irin shu'umin kallo,
◻ Jiki na rawa sehrish ta ɗauki plate hannunta har kerma yake yi, tama rasa me zata zuba mishi,
◻ Muryarshi ce ta katse ta da cewa "Snacks nake so",

Cikin sauri sauri ta zuba mishi snacks ɗin sannan ta haɗa masa da lemu a cup ta tura mishi,

◻ "Yawwa Good Job," ya faɗi yana kai hannunsa cikin plate ɗin ya ɗauki donuts yakai bakinsa,'

◻ matsawa tayi daga bayan sgr ta tsaya saboda ta
◻ samu damar da zata rinƙa kallon sumar kanshi da kyau, tana shakar turaren shi,
◻ Ji take tamkar takai hannunta ta shafi sumar nan tashi, tun da ta tsaya abayan sgr bata motsa ba, duk wanda ya faɗi yana buƙatar wani abu sai dae azmee ta zuba mishi, ita kawai Babban yaya take saving abunda yake so,
◻ ɗagowa junaid yayi da idonsa ya ɗan kalle ta dayake tana tsaye daga bayansu, mamaki ne ya kamashi ganin yadda sehrish ke ta faman kallon Babban yayan nasu ko kyaftawa batayi, sam bai kawo wa ransa komai ba game da kallon nata kawai yasanwa ransa cewa wata'ƙil respecting ne yasanya sehrish tsayawa abayan, kallonsa kuma da take yi may be burgeta yayi ne, amma yaso ace shi sehrish take ma wannan kallon dayaji daɗi, mayar da kansa yayi jikinsa a sanyaye yaci gaba da shan farfesun naman dake gabansa cikin plate,
◻ Sun jima suna ɗawainiyar zuba musu breakfast ɗinsu kafin daga bisani kowa ya fuce, banda junaid da haroon suna acikin gidan, Sgr sun fita tare da abbansu headquater


_______________________________________________


A 6angaren su Hosana kuwa Tun da asuba da saude ta tashe su su kayi salla, suka koma tare da shimfiɗa wani sabon baccin kamar matattu haka suka dingi sharar bacci, dole kuyi bacci Allah, zaman cell ba daɗi anjima ana cikin tashin hankali, ga sauƙi yazo daga Lillahi,
Koma wa kitchen saude tayi ta shiga harhaɗa kayan breakfast da zatayi amfani dashi, shaf shaf ta fere dankali turawa bayan ta kammala ta yanka shi slide sannan ta shiga soya shi a saman frying fan,
Muryar goggo ce ta katse ta da cewa "umm agogo sarkin aiki nace ya akai banga yaran nan ba? Kodai mafarki nayi jiya?
Fuska ɗauke da dariya saude tace "Su wa kike nufi kenan"?
Watsa hannu tayi tare da cewa "Ƴa'ƴan Abusufyan mana? waɗannan tagwayen ?
ta tambaya tana neman jin ƙarin bayani,
Bin ta da kallo saude tayi jikinta na sanye da kayan baccin nan ƴan gado, sun yamutse sun tsufa riga da wando kwalar rigar ta sukurkuce, gasu Over size sun mata yawa kamar agwagwa haka ta koma acikinsu, taƙi ta janza wasu koda yaushe akayi mata magana akan ta sauya wasu kayan baccin sai tace tafi son waɗannan saboda ƴan ƙasar turƙiya ne irin wanda Zehra ke sanya abarmata abunta, wato ta cikin tarkon kauna, Abusufyan ne yayi mata tsarabar su tun last year dayazo nageria,
Gashi ta ƙife ɗan kwalin atamfa akanta abundae ba'ace wa komai,
"Saude kinyi shiru baki ce mun komai,"
daker saude ta iya cewa "Suna nan mana, ba mafarki kikayi ba goggo, suna can suna sharar bacci ɗakina,
Washe baki goggon katsina tayi tare da cewa "Yawwa madalla har hankali na ya kwanta," ta faɗi tana shafa saitin zuciyarta, hakan ba ƙaramin sa saude dariya yyi ba,
goggo taci gaba da cewa "Saude so nake ki shirya musu karin kumallonsu mai daɗin gaske, a shaƙe musu tray, sannan a hada musu farfesun kaji dan Allah naga ƙasusuwan wuyansu kamar an jera ƙarafuna suna fama da yunwa, so nake kafin Abusufyan yadawo daga ƙasar turƙiya ko ina na jikinsu ya cicciko suyi kyau ƴan dumur-mur,' tayi maganar tana kwatanta yadda take so su koma da hannunta,
Dariya kawai saude ke saki jin abunda goggon tace wato ƙashin wuyansu kamar an jera ƙarafuna, har dafe ciki take yi,
"Bansan iya shege wa kike wa dariya? Saude kin raina ni ko ina magana kina mun dariya, idan kika fusata ni, yau yau ɗinnan zakiyi fiffige ki koma rugarku acigaba da kiwon shanu,"
Tsuke fuska saude tayi jin abunda goggo tace rai abace tace"shikenan tun da haka kke so bari naje na shirya kayana yau dai na tafi na huta da gori," tayi maganar tare da kama hanya zata bar kitchen ɗin, .
Da sauri goggo ta ruƙo hannunta fuska dauke da murmushi cikin lallami tace "haba ƴar saude ta ke ko bakisan wasa ba, in kika tafi wa zai haɗawa ƴa'ƴan abusufyan ɗina breakfast ɗinsu,"
Murmushi saude tasaki ganin yadda goggo ke lallashinta yau, ita tasan saboda twins ɗincan tasamu wannan kulawar,
Koma cikin kitchen ɗin tayi tana cewa " shikenan na fasa, amma goggo gsky ki barni nayi aikina mana, kinzo sai katse ni kike yi,"
Juyawa goggo tayi ta fi ce tana cewa "To natafi Allah baki haƙuri, ayi aiki lafiya,
Sai da goggon katsina ta wuce ɗakin saude ta tura kopan ɗakin ta hangi su Hosana da Jahad suna bacci sannan hankalinta ya kwanta hada jinjina kai da cewa "Masha Allah, ƴa'ƴan abusufyan ɗina kusha baccin ku ku more ƴan gatana abinci na nan yana jiran ku," ta kammala sambatun nata sannan ta koma falo ta kunna kallo ta samu wuri ta zauna saman 3 seater tana cewa "Oh ko yaushe suke maimaicin shirin Omaru da zahra, aiko bari waɗancan yaran su tashi daga bacci in nuna musu ƙasar da mahaifinsu ke zaune, ni nasan ma ba'a rasa ganin shi acikin film ɗin wata'kil ko yazo giftawa aciki Camera man ya hasko dashi,"
Haka ta runka sambatu ita kadae abunta, sam bakinta bai zama hakannan batare da tace wani abu,
Bayan saude ta kammala breakfast ɗin, acikin katon tray ta jera warmers ɗin da sauran food stuffs ɗin ta shigo falon dasu,
Tunkan ta karaso goggo tace "Yawwa saude na maza ajiye shi anan gabana, sannan kije ki tasomun ƴa'ƴan Abusufyan ɗina, bayin Allah suna can suna fama da yunwa, bacci bai da imani baisan in kana jin yunwa ba ya ƙyale ka ba,"
Fashewa da dariya saude tayi aranta tana cewa wato da ace goggo ƴar comedy ce ba ƙaramin nishaɗantarwa zatayi ba,
Ajiye tray ɗin tayi asaman carpet ɗin geben ƙafar goggon kamar yadda tae commanding ɗinta, sannan ta wuce room.ɗin ta don ta tayar dasu Hosana da Jahad,
Duk wannan abun dake faruwa Goggo da saude basusan cewa Omar da Babban likita suna cikin gidan ba, saboda dama jiya bayan sunyi bacci suka dawo, Su hosana ne kawai suka sani saboda sunyi magana dashi,
duk in taga yaran wani farin ciki take ji aranta, sai faman sharar baccinsu suke, addu'arta Allah yasa Yaya Omar yabar musu twins ɗin su zauna agidan koba komai zata samu abokan fira,
Ƙarasawa tayi gaban gadon ta sanya hannunta ta ɗan bubbugi ƙafafunsu a hankali kamar wadda zata tasar da Jarirai,
Farkawa su kayi kowa na faman yin hamma, atare suka tashi zaune suna kallonta, lokacin da jahad ta shaida ta cikin sauri tace "ina kwana Aunty," murmushi saude tasaki tare da cewa "Lpy lou my sisters fatan kun tashi cikin ƙoshin lpy,"
Jahad tace "Alhamdulillah aunty, munji daɗi sosai da kulawarnan,
"Aunty nidai Yunwa nake ji, da yunwa natashi kamar na cinye ƴan hanjin ciki na," hosana ce tayi maganar, fashewa da dariya saude tayi hada jahad ɗin, murya a ƙule Jahad tace "waike baki da kawaici ne? Ko gaishe ta bakiyi ba sai magana akan yunwa yunwa,"
Murmushi saude tayi tare da cewa"kwantar da hankalin ki, special breakfast na nan nayi maku reserving ɗinshi a palor, kuma goggonku na nan tana jiran ku, sai tambaya take ina ƴa'ƴan abusufyan ɗinta,"
Jin hakan yasa su yin murmushi tare da kallon juna, kafin jahad tace"Aunty saude dama ina so na faɗamiki jiya yaya Omar yazo munyi magana dashi har yace mana, mu shirya yau zai wuce damu kaduna gidan yayan shi, gsky mun fi so muzauna anan," ta ƙarasa magar tana kallon sauden,
dafe ƙirji saude tayi tare da cewa "Wai dagaske abunda ya faɗamaku kenan ! Hakan na nufin bazai bar mana ku nan ba, mu zauna atare ya Allah,' sam bataji daɗin hakan ba, har cikin ranta, babban tashin hankalin ma da taji Jahad tace zai kaisu kd gidan Yaya ishaq,
Aranta tace "tabɗijan gidan wannan shu'wa arab ɗin jarababbiya, sam bana fata akai yaran nan can saboda bazata ƙyalesu ba, sai ta azabtar dasu waiyo Allah na, ya zanyi yaya omar yabar mana su anan su zauna, wlh aunty babba bata da mutunci ga Hafsat kuma yadda yarinyar nan ta tsani talaka aikom yaya omar zaiyi gangancin jefa rayuwarku cikin hadari,'
"Aunty baki ce komai ba? dan Allah kice masa yabarmu anan muzauna daku munfi jin daɗi," jahad ce ta katse mata tunanin da take yi,
Jiki a mace saude tace "i dont know wat to do, yaya omar in yayi niyar yin abu no body can stops him, kuyi addu'a kawai Allah yasa goggo ta hana shi tafiya daku, amma muddin aka kaiku gidan yaya Ishaq kun shiga uku,"
Hankalinsu ba ƙaramin tashi yayi ba jin abunda saude tace, murya na rawa jahad tace "aunty meyasa kika ce haka"?
Saude tace "hmmm abar zancen kawai, ku tashi ynx ga breakfast can na jiranku, ga goggo kuma nasan ganinku, ni ynx kitchen zan koma na shiryawa su yaya Omar nasu, pls kusan yadda zakuyi kar yaya Omar yabar gidan nan daku," tana gama faɗan hakan ta fice izuwa kitchen zuciyarta nayi mata ba daɗi saboda tausayin yaran duk da batasa su wanene su ba amma tasan basu da gata, yaya Omar kuma dama shi mutun ne mai son taimakai wata'kil wani wuri yagansu a wahalce yake son taimakon rayuwarsu, da wannan tunanin Saude ta shige kitchen,
Kallon juna su kayi cikin tsananin tsoran inda za'a kaisu, atare suka tashi haryanzu doguwar rigar material ɗinnan ce ajikinsu, mayafi kawai suka ɗaura akansu sannan suka fito,
Goggo naganinsu ta soma washe baki tana cewa "masha Allah ƴa'ƴan abusufyan ɗina maza ku matso ku kwashi albarka wurin gaggonku, ga kuma abincinku na jiranku,"
Da fara'a suka karasa atare suka zauna suna gaishe ta "barka da safiya goggonmu fatan kun tashi lafiya,"
"Lafiya lou Alhamdulillah, har mafarkin ku saida nayi jira, tsorona kar na farka na taras da bakwanan agidan bansan ya zanyi ba, in banga ƴa'ƴan abusufyan ɗina ba,"
fuskarsu cike da tsantsar farin ciki ga kaunar goggon katsina data shiga ransu daga jiya izuwa yau,"
"Yawwa maza ga shinan kuci ku ƙoshi, in ma bai isa ba aƙaro maku,"
Cike da zumuɗi hosana ta ɗauki plate ta bude warmer ɗin dake ɗauke da soyayyan dankalin turawa ta shake plate ɗin dashi, sannan ta bude ƙaramar kular jar miya ta lafta asama, ta motse ta shiga da turama cikinta,
Jahad kuwa Wainar kwai ta rinƙa haɗawa da slide bread tana cunkusawa abakinta, hannu goggo tasanya ta ɗauki flask ɗin dake ɗauke da ruwan liptop, ta tsaiyaya musu a cup kowa da nasa sannan tace "ga madara nan leda kowa ya zuba yadda zata ishe shi,"
Zame hannu hosana tayi daga irishi ɗin da take ji don haɗama, ta ɗauki milk ɗin ta zazzafa acikin ruwn tea ɗin mai uban yawa, tana jin jahad na cewa "banza kaɗan zaki zuba,"
Harara ta watsa mata tare da cewa "ina ruwanki ! ki ci abunda ke gabanki," sai da taga ruwan tea ɗin yayi kauri yaji uwar madara sannan ta tsagaita ta sanya sugar," ta hada tana sipping ɗinshi,
girgiza kai kawai jahad tayi tare da haɗa nata tea ɗin tashiga kurbarshi tana ci da bread ɗin,"
Kamar kura haka ta lamushe abunda ta zuma sannan ta bude warmer ɗin dake dauke da chicken pper soup, ganin lafiyayyiyar kaza yasa hosana gyara zama, anjima ba'a haɗuwa hannunta har kerma yake yi wurin daukar cinyar kazar tana turawa abakinta, gwanin daɗi kunnanta har rawa sukeyi,
Goggo sai murmushi takeyi tana kallonsu tsananin ƙaunar yaran take ji har cikin ranta,
Jahad kam kunyar abunda hosana keyi take ji kamar ta shaƙo ta take ji, sai faman licking hands ɗinta take kamar mayya,
Ƙasa ƙasa da murya tayi cike da jan faɗa tace "su hosana basaban ba, gida babu makwabta babu gidan miji ba tabbas, banza tasamu sai wankarta ake ba baka sai kunne,"
Fashewa da dariya su kayi gaba ɗayansu, ashe goggo na jinsu sai cewa tayi "Inji wa ya faɗi maki cewa gida babu, tab Ke ko kinsan katafaren gidan da abusufyan yake rayuwa acikinsa acan ƙasar Turƙiya? Kinsan irin daukar dayake ciki ? ae wannan bakomai bane, hmmm lokacin da naje turƙiya nakai masa ziyara, in zan ci abinci saiya sa an jera mun kayan maƙwalashe cike da dining tabur ae masu aiki gare shi sun iya girki sosai in sukayi abinci kamar abincin Aljanna don daɗi," ta ƙare maganar tana jaddada musu mgnrta
Tsagaitawa da cin abincin su kayi suna sauraronta baki asake, sukam wai wanene wannan abusufyan ɗin da Goggon katsina ke ta faman labarta musu zancen shi?
Kallon juna su kayi alamar neman karin bayani, goggo tace "ae ku kwantar da hankalinku, ni da kaina zansa abusufyan yazo nigeria ƙafarsa ƙafarku baxan ƙara bari ya tafi yabar yaransa cikin wahala ba,"
Sunnar dakansu su kayi ga dariya na cinsu, jin yadda goggo ke ƙaƙaba musu mutumin da basu san da Existing ɗinsa ba a duniya,
Atare Omar ya fito shi da babban likita sun shirya tsaf,
Goggon na ganinsu tace "Kai dirar yaushe ? ta ina kuka shigo cikin gidan,"
Murmushi Omar yasaki tare da cewa "goggona ke nan, ae jiya muka dawo tare da mutumina, mun same ku kuna bacci,"
Babban likita yace "Barkanka da safiya Mommyna fatan kun tashi lpy' yayi maganar ayayin da yake zama saman 2 seater, shi kuma marshal Omar ya samu wuri gefen gaggo yazauna saboda ya samu damar gaisawa dasu Hosana dakyau,
Atare suka haɗa baki wurin cewa "Barka da safiya yaya Omar dafatan ka tashi lpy," .
"Lafiya Alhamdulillah," ya amsa musu yana mai ƙara azan idonshi akansu," ba ƙaramin daɗi yaji ba ganinsu suna cin abinci,"
Duk kunya ta kama jahad har takasa idasa cin abincin, ita kuwa hosana bakin nan nata dama

6 Comments On ABBAN SOJOJI
avatar
ibrahim-5-3

1 year ago

Reply

Ina son abban sojoji complete

avatar
ibrahim-5-3

1 year ago

Reply

Ina son abban sojoji complete

avatar
muhammad-4-3-8

1 year ago

Reply

I want it

avatar
hauwa-said

1 year ago

Reply

Please Ina so

avatar
hauwa-said

1 year ago

Reply

Please Ina so

avatar
husaini

9 months ago

Reply

I love this novel

Please Login or Register in order to submit comment