Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE

DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register
DOWNLOAD

jikinsu , abunka ga handsome guys ga tsawo ga hadaddiyar sura sai abun ya bada citta 😘

tunanin ta soma yi a ranta "oh ni ko wanene babban yaya acikinsu , koda yake naji azmi tace ba sojan nigeria bane U.S ARMY ne , zanso nagansa daga ji ya hadu yadda hajjaju ke zuzu tashi ,"

takarasa tunanin tana murmushi ita kadai abunta , shigowa azumi tayi tana fadin "maza tukur a shirya abinci a dining before su fito, ai ina ji girkin ya isa ya kammalu ,"

Wasu hadaddun kuloli ta dauko daga kitchen cabinet kamar ranar aka budesu daga kwalinsu tsantsar kyansu kamar ba abinci za'a zuba ciki ba , saboda yadda murfinsu ke glowing har face dinka zaka iya gani aciki just like mirror ,

A wani faffadan tray ta shirya komai ciki , ta mika wa sehrish azuwan taje ta fara shiryasu a dining ,

Gaban ta na faduwa ta karba tsoranta da wa zata fara cin karo a cikinsu , time din da ta isa dining room din , mutun d'aya ta samu zaune shi ya rigasu fitowa jikinsa na sanye da white tshirt da black short , bai lura da ita sai da yaji cool voice dinta ta sauka a kunnan sa " sannu da hutawa " a natse ya dago yana kallonta ,

lokacin da suka hada ido kara ware idonta tayi ganin irin kyawunsa , dan matashi ne ba zai wuce 18years ba , a tunaninsa zai ga mace amma sai ya ga namiji tabbas shi muryar mace ya ji mai dadin gaske a kunnan sa ,

Wani kayataccen murmushi ya sakar mata , wanda yasa ta shiga yanayi , cool voice dinsa ce ta ratsa ta "am nace ko sabon mai aikin da akace za'a kawo mana ne?daga masa kai tayi alamar eh ,
Jinjina kansa yayi tare da d'an tabe small lips dinsa ,
Soma jera abincin tayi , bayan ta gama ta koma ta dauko sauran abubuwan da bata kawo ba ,

Allah Allah take ta kammala jera abincin kafin sauran su karaso , muryarsa ce ta kara katse ta " chicken pepper soup din nan zaka zuba mun ka hadamin da irish cikin plate din ," ta amsa toh kamar wata munafuka haka take sunnar dakai , Ji take kamr asirinta zai to nu ,

Plate ta zaro daga cikin set na filattan da takawo , bude daya daga dana cikin kulolin tayi , nan da nan kamshi ya gauraye wurin , saving spoon ta dauko ta soma zuba kazar a cikin plate din , sai faman hadiye miyau take yi , ga hannun ta dake kakarwa ga wani gumi dake sauka daga gefen sajenta ,

Kammala zuba kazar tayi sannan ta bude kular da ke dauke da irish ta zuba masa k'adan muryarsa ta sake ji "yayi mun k'adan ka take mun plate din "

cika masa plate din tayi dam sannan ta tura masa gabansa , cikin sauri ta kama hanya zata koma ciki "spoon din fa ko so kake na dauka da kaina ne sannan a gidan ku haka ake ba mutun abinci ba tare da drinks ba '? har zuciyarta taji wannan maganar a tunanin zaiyi saukin kai ganin da farko yayi mata murmushi ,

lallai ta jinjina wa izzarsa , ga cokulan kusa da shi ga kuma drinks din da ta jera amma yafi karfin yasa hannu ya dauka sai da ita ta mika masa ,

guntun murmushi tasaki koma tayi ta mika masa cokalin sannan ta zuba masa lemu a cikin glass cup ta mika masa , yamutsa fuska yayi tare da sa hannu ya karba yana cewa " gsky kana bukatar training don da ace babban yaya ko captain kayima haka da ka gane barno gabas take don sai kayi tsallan kwad'i ,"

Ya karasa maganar yana kurban lemun da ta mika masa , a wani irin yanayi sehrish ta juya wannan ne karo na biyu da taji an ambaci BABBAN YAYA , hakan nakara sa mata tsoransa a zuciyarsa ,

Komawa tayi kitchen ta samu azumi tana gyara wuraren da suka bata , jin shigowarta yasa ta dagowa tare da cewa "subhanallah meyasa ka dawo ka kammala saving dinsu ne "?

"A'a naga basu fito bane shiyasa na tafo ," tayi maganar fuska a yamutse sbd rashin natsuwa da take ciki , azumi tace "maza ka koma karka ja mun bala'i , bakasan halin mazan gidannan ba ,"

Ba haka sehrish taso ba , jiki a sanyaye ta kama hanyar komawa dining room din , hannu azumi tasa ta rike habarta alamun mamaki tace "lallai dole na mike tsaye akan yaron nan ! yana abu kamar mace anya wannan ba dan daudu bane ? ta tambayi kanta ,

Tunkan takarasa ta ke hangensu , a lokacin suke karasawa saman dining din kowannen su yaja kujera yazauna , Kasancewar table din dogone mai mazaunin mutum goma sha 12,

Tana jin dayansu na cewa "wai uban wa ake so ya zuba mana abincin ne? cikin sauri sehrish ta karasa tana cewa "ni ce yallabai ,"

Gaba daya suka d'ago suna kallon ta sai ta tsorata tayi wuri wuri da ido.
👮🏻‍♂️ *ABBAN SOJOJI* 👮🏻‍♂️
```The father Of Soldiers```

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•

Page 11-12

'Yan kame-kame ta shiga yi hankali a tashe tana wurwurga ido, " wannan d'an daudun daga ina kuma aka samo shi?" Daya daga cikinsu ya tambaya yana kallon ta , hantar cikinta ce ta ji ta kad'a , su duka sauraren ta suke yi su ji mai zata ce?

Motsi ta soma yi da lips dinta alamar tana so ta ce wani abu "Amm... Amm.." Duk ta bi ta dabarbarce. Jin muryar Azumi yasa Sehrish sauke ajiyar zuciya, karasowa ta yi tana fadin "Afuwan y'an samari ban yi maku bayani game da sabon d'an aikin da aka kawo domin ya rinka taya ni aiki ba."

Kasa kunne suka yi suna sauraron ta , dafa kafadar Sehrish ta yi tare da cewa "Sunan shi tukur daga yau zai rinka taya ni aikace aikacen cikin gidannan ,'

Ta kare maganar tana kallon kowannan su tabe baki yyi ba tare da sunce komai ba dama haka ta yi tsammani , don haka taci gaba da cewa "tukur bari na gabatarka maka da kowannan su saboda ka kiyayi zama dasu ,"ita dai ba ta ce komai ba saboda a rud'e take ,

Azumi ta soma gabatar mata da su daga na farko "Wadannan biyun da ka ke gani sune tagwaye in ka lura komai nasu iri d'aya , suna da son zolaya musamman idan abun mugunta ne sun fi auki a nan na farkon sunansa Jahan shine babba sai twin brother dinsa Ayaan"

Tana gama wa dasu ta matsa na kusa dasu tace "wannan kuma sunan shi Kanal yusif sarkin tsafta , bai cika son surutu ba kuma baya son kallo , na gefensa kuma shine Khaleed bai da matsala shi indai za ayi masa abunda ya ke so ba tare da ya tambaya ba ,

Duk Sehrish na sauraron wannan bayanin na azmi , bayan ta kammala da na hannun damarta ta koma other side din taci gaba da cewa "wannan Junaid kenan sarkin murmushi, duk yadda za'a bata mai rai baya fushi sai in an kuresa , yana da son wasa faran faran da jama'a, burinsa a bashi kulawa a bangaren ci kuwa ba'a magana ," karasa maganar tayi tana y'ar dariya , shima dariyar yake yi haka zalika wasu daga cikinsu sun d'an murmusa ,

Sehrish tagane sa shine wanda ta fara zuba ma abinci mai kyakkyawan murmushin nan

"n6a kusa da shi kuma fawan kusan halinsu daya da Junaid , sai jabir da irfan basu da matsala in dai ba tsokanarsu akayi ba."

Murmushi sehrish tayi taji dadin wannan gabatarwar , sai dai ranta na bata cewa wadannan kananun ne , akwai sauran mutun goma daga cikin sojojin da basa nan , su kuma koya zasu kasance !?

A tare da azmi suka yi saving dinsu abincin har suka kammala kowannnen su ya kama hanyar makwancinsa , tattara plates din da kulolin sukayi a tare suka kakkauda komai izuwa ma'ajiyarsa ,
daga nan sehrish tayi ma azmi sallama ta koma bedroom dinta , tana mai jin dadin fara kasancewarta a wannan awesome family din Babbar damuwarta shine , da tazo a matsayin namiji a maimakon mace batasan ya abun zai kasance ba ranar da asirin ta ya tonu.

Tunda samu gadon nan ta haye ta soma minshari bata kara sanin meke wakana ba sai da tajiyo kwankwasar kopar da azumi take yi mata ,

A firgice ta farka tana neman mayafin da take nad'e kanta da shi , can ta hangosa kasa ashe anan tayi wurgi dashi, daukowa tayi ta hanzarta daure kanta dashi, sannan ta tashi ta nufi kofan ta bude mata, fara'a azmi ta sakar mata " am sorry na Katse maka bacci ko naga ana kiran sallah ne raina ya bani baka yi ba nasan an sha gajiyar tafiya ga aikin da mukayi da dare ,"

Cikin y'ake sehrish tace "a'a wlh naji dadi da ki ka tashe ni saboda banyi sallah ba amma ynx zanje na yi,

Azumi tace "ok in ka kammala karfe 7 ka fito akwai aikin breakfast na jiran mu" reeshi ta amsa da "toh " sa'annan tajuya ciki"

Cikin sauri ta shiga toilet, sai da tafara cire gashin bakin da aka sa mata ta tura sa cikin aljihun wandon ta, sannan taje bakin fanfo ta daura alwala , ta fito tana yarfa hannun ta, hijabi ta dauko ta zura sannan ta shimfid'a kafet, ta soma yin sallar,

Bayan ta kammala sallar wata irin hamma ta rinka ji, ga bacci bai ishe ta ba ga kuma yunwa don jiya da daddare bata nemi abincin ba gashi available

Agogon dake manne jikin bango ta kalla akwai sauran lokaci don haka sai ta baje saman sallayar taci gaba sharar bacci, ba ita ta tashi ba sai wurin karfe 9 na safe hankali a tashi ta wartsake, ganin cewa wannan ce rana ta biyu da fara aikinta gashi zata fara bada matsala, cikin hanzari ta cire hijab dinta ta hada da kafet din sallan ta adana su a saman gadonta, sannan ta zaro gashin bakinta da take likawa ta manna sa a fuskarta, ta gyara nad'in mayafin kanta ta fi ce,

A kitchen ta Sami azmi ta kammala shirya komai na kalacin safen , duk sai taji ba dadi sukuku ta isa gare ta ta ce "barka da safiya nayi laifi dan Allah ayimun uziri,"

Babu alamun bacin rai a fuskar azmi ta ce " karka damu tukur, ba wani abu nan gaba dae aguji yin hakan"

Sehrish ta amsa da toh insha Allah yanzu wani aiki zan yi ?

Ba wani aiki kawai abunda ya rage ynx kabi bedrooms din kowannan su ka Sanar dasu su fito su yi breakfast ya kammalu," azmi ta karashe maganarta ta tana kallon ta,

Cikin zullumi sehrish ta fita ta tunkari jerin dakunan dake a downstairs , na farko ta fara kwankwasa wa shiru ba'a bude ba , kara knocking tayi da karfi , har sai da ya isarwa mai dakin , muryarsa tajiyo ashake yana cewa "who's trying to disturb me? d'aga murya tayi tare da cewa "tukur ne sabon mai aiki,"

"Shigo ciki" ya ba ta izni , turo kofar tayi tare da kutsa kai ciki, har cikin ranta dakin ya yi mata kyau bedroom kamar na mace saboda kyau ga tsafta sabanin wasu mazan da idan ka shiga dakunansu kamar wurin safkar y'an gudun hijra saboda tsaban tarkace da har mutsi,

"Idan ka kammala kalle kallen naka sai ka sanar dani abunda ya kawo ka," muryarsa ce ta dirar mata a kunne sai lokacin ta mayar da idonta akansa , kwance yake a baje saman katafaren gadonsa rabin jikinsa yayi covering dinsa da lallausan blanket , Yusif kenan

Cikin en ina sehrish ta ce "am ..emm dama an kammala breakfast ne shine aunty azmi tace nazo na sanar daku."
ta kammala maganarta ta tana wasa da yatsun hannunta , jin shirun bai ce komai ba ya sa ta dagowa ta saci kallonsa , samun shin tayi yana yamutsa fuska alamar an takura masa cikin lallausar muryarsa ya ce "Idan ina jin yunwa ai ba sai anzo an tayar dani ba ni zanzo da kaina ciki na ne ko cikin wani? ya tambaya yana kallon ta ,

Cikin sauri tace "cikin ka ne" ok fi ce ka ban wuri , ya fada tare da jan bargonsa ya idasa rufe face dinsa ,
Kamar wacce kwai ya fashe mawa a kai haka ta fita salalau salalau , a cikin ranta kuwa tana jinjina ma isa irin tasa " tab aiki y ganni ni sehrish daga abun arziki, wannan shi ake kira da samun wuri tusar asuba, Allah sarki mukam ya'yan talakawa don uban mutun kar Allah yasa ya nemi abinci har rana ta fadi ya ga in za'a a damu dashi kasha iya barcinka yunwa ta taso ka, ka lallaba ka je neman kason ka wani sa'in ma an manta dakai, su kam wadandannan genius din bibiyarsu akeyi suzo suci suna make wa,"

Ta karasa tunanin nata a dai dai lokacin da tazo kofar dakin the next person , knocking tyi bugu d'aya taji ance "Come in"
turo kofan tayi ta bude Samun shi tayi zaune saman sallaya jikinsa sanye da jallabiya ga kur'ani yana karantawa gwanin burge w, da alama wannan zaiyi saukin kai a cewarta

"Barka da safiya yallabai an tashi lafiya" sai da ya kai aya sannan ya juyo ya kalle ta ya ce "da ban tashi lpy ba zaka ganni ina karatun Qur'ani ne? to fah ta ambata acikin zuciyarta , shin mai ya kawo ka ma tukunna ? ya tambaya yana kallon ta a matsayin namiji,
Muryarta na rawa tace "dama an kammala breakfast ne shine ....." Interrupting dinta yayi tare da cewa "shine me ? kai shashashan ina ne da zaka fadowa mutun haka kawai tunda sanyin safiya,kama hanya ka fi ce tunkan nayi football dakai" (Jahan).

Jiki na rawa Sehrish ta fi ce zuciyarta na bugawa saboda tsananin tsoro, dafe kirjinta tayi domin ta samu natsuwar karasawa ga daki na gaba,zullumin ta kar asamu wanda zai kai mata duka don ta lura cewa fusatattu ne, ba mai sauki a cikinsu farawa da iyawa ta fara fuskantar haka nan gaba batasan mezai biyu baya ba.

Next room kwankwasa tayi tana jira taji an bata iznin shiga amma shiru , sake buga kofan tayi da d'an karfi da alama kowanane mamallakin dakin nan ya datse kofar ne,
Jin alamar ana tunkaro kofar yasa ta natsuwa, bude kofar yayi fuskar nan a daure kamar Alkubus "lafiya"? ya ambata rai a bace.
Har ta bud'e baki zata yi magana tajiyo muryar wani daga can cikin ɗakin yana cewa "Wai wane ne"?

"Wannan shashashan sabon mai aikin ne," wanda ke tsaye a gabanta ne ya basa amsa, sai lokacin ta gane cewa dakin twins ne wato kamar yadda suke y'an biyu haka ma wurin kwanansu d'aya ,"

Tuni taji zufa ta ke to mata ganin wancan dake daga ciki ya taso , dukkan su sleeping dress ne riga da wando ajikinsu kala daya milk colour masu kyan gaske,

Jerawa suka yi tsaye a gabanta kowanne na kallonta alamar sun ma rasa wane hukunci zasu yi mata saboda ta katse masu baccinsu,

Gudun kar ta ja ma kanta bugu yasa ta ce "Am...Da ma breakfast ne an kammala shine aunty azmi tace a zo a sanar daku,"

Kallon juna su kayi tare da cizon labba atare, Ayaan ne yasa hannunsa ya kamo kunnanta ya idasa shigo wa da ita ciki , ba karamin zafi sehrish taji ba har sai da tad'an saki y'ar kara "ko da gigin wasa next time ka kara attempting zuwa tashe mu bacci na rantse saika yabawa aya zaki sususu kawai," ya karasa maganar tare da sakin kunnan nata cikin sauri sehrish ta fice tana sharar kwalla don ba karamin zafi taji ba,

Sai da ta samu wuri ta tsugunna ta gama matse yar kwallarta sannan ta tunkari sauran dakunan kowane daki taje da abunda zata tarar na wulakanci, yanzu dai gashi ta tunkari saman bene last room da ya rage ta shiga,

Sai da ta tabbatar ta share dukkan ruwan hawayen da ya zubo mata sannan ta kwankwasa , kusan 3 times tana knocking a na karshen ne taji wata sanyayyiyar murya tace" shigo ciki."

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•

Page 11-12

'Yan kame-kame ta shiga yi hankali a tashe tana wurwurga ido, " wannan d'an daudun daga ina kuma aka samo shi?" Daya daga cikinsu ya tambaya yana kallon ta , hantar cikinta ce ta ji ta kad'a , su duka sauraren ta suke yi su ji mai zata ce?

Motsi ta soma yi da lips dinta alamar tana so ta ce wani abu "Amm... Amm.." Duk ta bi ta dabarbarce. Jin muryar Azumi yasa Sehrish sauke ajiyar zuciya, karasowa ta yi tana fadin "Afuwan y'an samari ban yi maku bayani game da sabon d'an aikin da aka kawo domin ya rinka taya ni aiki ba."

Kasa kunne suka yi suna sauraron ta , dafa kafadar Sehrish ta yi tare da cewa "Sunan shi tukur daga yau zai rinka taya ni aikace aikacen cikin gidannan ,'

Ta kare maganar tana kallon kowannan su tabe baki yyi ba tare da sunce komai ba dama haka ta yi tsammani , don haka taci gaba da cewa "tukur bari na gabatarka maka da kowannan su saboda ka kiyayi zama dasu ,"ita dai ba ta ce komai ba saboda a rud'e take ,

Azumi ta soma gabatar mata da su daga na farko "Wadannan biyun da ka ke gani sune tagwaye in ka lura komai nasu iri d'aya , suna da son zolaya musamman idan abun mugunta ne sun fi auki a nan na farkon sunansa Jahan shine babba sai twin brother dinsa Ayaan"

Tana gama wa dasu ta matsa na kusa dasu tace "wannan kuma sunan shi Kanal yusif sarkin tsafta , bai cika son surutu ba kuma baya son kallo , na gefensa kuma shine Khaleed bai da matsala shi indai za ayi masa abunda ya ke so ba tare da ya tambaya ba ,

Duk Sehrish na sauraron wannan bayanin na azmi , bayan ta kammala da na hannun damarta ta koma other side din taci gaba da cewa "wannan Junaid kenan sarkin murmushi, duk yadda za'a bata mai rai baya fushi sai in an kuresa , yana da son wasa faran faran da jama'a, burinsa a bashi kulawa a bangaren ci kuwa ba'a magana ," karasa maganar tayi tana y'ar dariya , shima dariyar yake yi haka zalika wasu daga cikinsu sun d'an murmusa ,

Sehrish tagane sa shine wanda ta fara zuba ma abinci mai kyakkyawan murmushin nan

"n6a kusa da shi kuma fawan kusan halinsu daya da Junaid , sai jabir da irfan basu da matsala in dai ba tsokanarsu akayi ba."

Murmushi sehrish tayi taji dadin wannan gabatarwar , sai dai ranta na bata cewa wadannan kananun ne , akwai sauran mutun goma daga cikin sojojin da basa nan , su kuma koya zasu kasance !?

A tare da azmi suka yi saving dinsu abincin har suka kammala kowannnen su ya kama hanyar makwancinsa , tattara plates din da kulolin sukayi a tare suka kakkauda komai izuwa ma'ajiyarsa ,
daga nan sehrish tayi ma azmi sallama ta koma bedroom dinta , tana mai jin dadin fara kasancewarta a wannan awesome family din Babbar damuwarta shine , da tazo a matsayin namiji a maimakon mace batasan ya abun zai kasance ba ranar da asirin ta ya tonu.

Tunda samu gadon nan ta haye ta soma minshari bata kara sanin meke wakana ba sai da tajiyo kwankwasar kopar da azumi take yi mata ,

A firgice ta farka tana neman mayafin da take nad'e kanta da shi , can ta hangosa kasa ashe anan tayi wurgi dashi, daukowa tayi ta hanzarta daure kanta dashi, sannan ta tashi ta nufi kofan ta bude mata, fara'a azmi ta sakar mata " am sorry na Katse maka bacci ko naga ana kiran sallah ne raina ya bani baka yi ba nasan an sha gajiyar tafiya ga aikin da mukayi da dare ,"

Cikin y'ake sehrish tace "a'a wlh naji dadi da ki ka tashe ni saboda banyi sallah ba amma ynx zanje na yi,

Azumi tace "ok in ka kammala karfe 7 ka fito akwai aikin breakfast na jiran mu" reeshi ta amsa da "toh " sa'annan tajuya ciki"

Cikin sauri ta shiga toilet, sai da tafara cire gashin bakin da aka sa mata ta tura sa cikin aljihun wandon ta, sannan taje bakin fanfo ta daura alwala , ta fito tana yarfa hannun ta, hijabi ta dauko ta zura sannan ta shimfid'a kafet, ta soma yin sallar,

Bayan ta kammala sallar wata irin hamma ta rinka ji, ga bacci bai ishe ta ba ga kuma yunwa don jiya da daddare bata nemi abincin ba gashi available

Agogon dake manne jikin bango ta kalla akwai sauran lokaci don haka sai ta baje saman sallayar taci gaba sharar bacci, ba ita ta tashi ba sai wurin karfe 9 na safe hankali a tashi ta wartsake, ganin cewa wannan ce rana ta biyu da fara aikinta gashi zata fara bada matsala, cikin hanzari ta cire hijab dinta ta hada da kafet din sallan ta adana su a saman gadonta, sannan ta zaro gashin bakinta da take likawa ta manna sa a fuskarta, ta gyara nad'in mayafin kanta ta fi ce,

A kitchen ta Sami azmi ta kammala shirya komai na kalacin safen , duk sai taji ba dadi sukuku ta isa gare ta ta ce "barka da safiya nayi laifi dan Allah ayimun uziri,"

Babu alamun bacin rai a fuskar azmi ta ce " karka damu tukur, ba wani abu nan gaba dae aguji yin hakan"

Sehrish ta amsa da toh insha Allah yanzu wani aiki zan yi ?

Ba wani aiki kawai abunda ya rage ynx kabi bedrooms din kowannan su ka Sanar dasu su fito su yi breakfast ya kammalu," azmi ta karashe maganarta ta tana kallon ta,

Cikin zullumi sehrish ta fita ta tunkari jerin dakunan dake a downstairs , na farko ta fara kwankwasa wa shiru ba'a bude ba , kara knocking tayi da karfi , har sai da ya isarwa mai dakin , muryarsa tajiyo ashake yana cewa "who's trying to disturb me? d'aga murya tayi tare da cewa "tukur ne sabon mai aiki,"

"Shigo ciki" ya ba ta izni , turo kofar tayi tare da kutsa kai ciki, har cikin ranta dakin ya yi mata kyau bedroom kamar na mace saboda kyau ga tsafta sabanin wasu mazan da idan ka shiga dakunansu kamar wurin safkar y'an gudun hijra saboda tsaban tarkace da har mutsi,

"Idan ka kammala kalle kallen naka sai ka sanar dani abunda ya kawo ka," muryarsa ce ta dirar mata a kunne sai lokacin ta mayar da idonta akansa , kwance yake a baje saman katafaren gadonsa rabin jikinsa yayi covering dinsa da lallausan blanket , Yusif kenan

Cikin en ina sehrish ta ce "am ..emm dama an kammala breakfast ne shine aunty azmi tace nazo na sanar daku."
ta kammala maganarta ta tana wasa da yatsun hannunta , jin shirun bai ce komai ba ya sa ta dagowa ta saci kallonsa , samun shin tayi yana yamutsa fuska alamar an takura masa cikin lallausar muryarsa ya ce "Idan ina jin yunwa ai ba sai anzo an tayar dani ba ni zanzo da kaina ciki na ne ko cikin wani? ya tambaya yana kallon ta ,

Cikin sauri tace "cikin ka ne" ok fi ce ka ban wuri , ya fada tare da jan bargonsa ya idasa rufe face dinsa ,
Kamar wacce kwai ya fashe mawa a kai haka ta fita salalau salalau , a cikin ranta kuwa tana jinjina ma isa irin tasa
DOWNLOAD
DOWNLOAD

6 Comments On ABBAN SOJOJI
avatar
ibrahim-5-3

7 months ago

Reply

Ina son abban sojoji complete

avatar
ibrahim-5-3

7 months ago

Reply

Ina son abban sojoji complete

avatar
muhammad-4-3-8

6 months ago

Reply

I want it

avatar
hauwa-said

6 months ago

Reply

Please Ina so

avatar
hauwa-said

6 months ago

Reply

Please Ina so

avatar
husaini

2 months ago

Reply

I love this novel

Please Login or Register in order to submit comment