Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

ni nace !!! meyasa kowa bai son mune !! Laifin me muka aikata, babu mai ƙaunar mu wlh Jahad ba zan koma cell ba sai dae a shigar da gawa ta, amma bani ba,' tana gama fadar hakan ta koma wurin mutumin nan dae dake a tsaye, ta zura hannunta cikin lallausan tafin hannunsa ta rike gam, ta marairaice masa da kyawawan idanuwanta tace "Dan Allah ka tafi dani,ka da kabarni anan, bana son ganin waɗannan masu fararen kayan (wato likitocin dake tsaye da nurses ɗin dake wurin) kuma bana son waɗannan masu bakaken kayan," ta faɗi tana nuna ƴan sandan dake tsaye baki asake suna kallonta,
kwantar da kanta tayi a damtsen hannunsa, sannan tasanya dukkan hannayenta ta rungumo nashi, (mutu ka raba kenan)
Lumshe idonsa yayi a hankali, sai lokacin kallon police men ɗin dake tsaye a wurin yace "wane irin shashanci ne yasa ku kabar yarinya harta kwaci bindiga daga wurinki!!"? Ya tambaya yana kallonsa,
Rai a6ace wani inspector yace "kaga malam ka iya bakinka, mu jami'an ƴan sanda ne munsan me muke..." tunkan ya ƙarasa major ɗin dake bayansa wanda ya fusata rai a6ace yace "Ka iya bakin ka !! Kasan wanene shi!!!"?
"maganar wanene shi bata shafe mu ba, mu dae a bakin aikin mu mu ke," wani inspector ne ya bashi amsa a yayn da ya fiddo da ankwa alamar zai sanya masu hosana,
Itakam ƙara kanƙameshi take yi, gaba ɗaya ta gama kashe mishi jikinsa, daurewa kawai yakeyi,
"Laifin me suka aikata"? Ya tambaya yana kallon ƴan sandar,
Wannan copral ɗin ne yayi saurin cewa "ana suspecting ɗinsu da kisan wata tsohuwa wadda take riƙonsu,"
Shiru ya ɗanyi tare da jinjina kai, kafin yace "Cancel the case (akashe case ɗin)"
ɗagowa su kayi jami'an ƴan sandan suna kallonsa cikin mamakin jin abunda yace, a fusace wannan inspector ɗin yace "malam wai wanene kai !! dame kake taƙama ne !! kaga ka kama gabanka kawai cikin salama, in ba haka ba, zamu haɗa dakai mu tafi police station.....'
Jikin major ɗin dake bayansa har tsuma ya ke yi wurin cewa," Shut Up Stupid !!! ka iya bakin ka ƙaramin ƙwaro ko kuma nayi ƙasa ƙasa daku a wurin nan....' cikin hanzari ya dakatar dashi tare da cewa "i did not allow u to talk again, last warn,'
Shuru major ɗin yayi sai faman huci yake yi tamkar zaki, rai a6ace ya wurgawa ƴan sandar bindigarsu ƙasa,
Matsawa Inspector ɗin yayi da nufin yasanya wa hosana ankwar dake hannunsa, amma sai mutumin ya dakatar dashi da cewa "karka kuskura !!! domin ban bada izini atafi da yarinyar nan cell ba, kamar yadda ta roƙe ni cewa bataso ta koma, daga nan ba inda zata je,"
Mamaki ne ya rufe ƴan sandan, inspector ɗin yace "idan ka cika shisshigi zamu sa bindiga mu kashe ka !! A wurin nna,"
Jinjina kai mutumin yayi tare da cewa "idan kuka kashe ni, ba hukumarku kaɗai bace zata shiga haɗari ba, gaba ɗaya sai an tada nigeria saboda raina kawai,"
Kansu fa ya gama ɗaukar zafi kowa mamakin wannan mutumin ya keyi, ganin ya toge yaki bari su ta6a yarinyar dake kwance ajikinsa yasa inspector ɗin cewa "wai dan Allah wanene kai!!"?
"Yanzu naji bayani" acewar mutumin bayan ya faɗi hakan ya zura hannunsa cikin aljihunsa ya zaro ƴar waya nokia, ya yi dialing wasu numbers da basu fi 5 digits ba ya miƙa wa, inspector ɗin wayar yace "Ka kira numbers ɗin dana sanya ka tambaye su*WANENE MARSHAL OMAR* za ka samu amsar da kake so,"
Jikin kowa yayi sanyi jin ance marshal, shi kansa inspector ɗin yana ɗan sauko, hannu yasanya ya kar6i wayar, ya danna call tare da karawa a kunnansa, one bugu on ɗauka, cike da kwarin guiwa ɗan sandar yace "WANENE MARSHAL OMAR, cikin harshen turanci yayi tambayar yana jiran amsa daga cikin wayar,
tunkan ya cire wayar a kunnansa, wasu irin jibga jibgan motoci ne suka soma antayo wa cikin asibitin aguje masu ɗauke da fusatattun sojoji zafafan gaske, runduna guda kamar a filin yaƙi, zaro ido su kayi gaba ɗayansu cikin tsananin mamaki, kowa dake kallon wannan al'amar tsantsar mamaki ne a fuskarsa,
Da gudun gaske sojojin nan suka shiga dirowa daga saman motocinsu kowanne riƙe da manyan bindigogii, da gudun gaske suka tunkaro inda Marshal omar yake sukayi masa ƙawanya, tare da buga ƙafa suka sara mashi sannan suka haɗa baki wurin cewa "We're waiting for your command Sir !" (Umarninka mu ke jira yalla6ai) 😳
Gaba ɗaya hankalin kowa yayi mugun tashi, sun tsorata ainin ganin sojojin ma ba na nan qasar bane, Black americans ne masu wata irin ƙira ta zakuna, kai kana ganinsu ba ɗigon Imani a fuskarsu, umarninsa kawai suke jira, koda hospital ɗinne su tada gaba ɗayansa 😳
Cikin rawar murya ɗan sandar nan wanda yaci ka zaƙe wa yace "Yalla6ai, dan Allah wanene kai"?
"dan Allah ka miƙa masa wayarsa, salin alin mu tafi," acewar wannan copral ɗin daya gama tsorata,
Hosana ta firgita sosai, amma maimakon ta cire hannunta daga nasa, sai ma ta ƙara ƙanƙamesa sosai, duk yana jin motsin hannun yarinyar acikin nasa, ita kuwa jahad ƙiris yarage tasaki fitsari don tsabagen tsoro, gashi tayi tayi da hosana ta janye hannunta daga nashi amma taƙiyi,
Hankali fa ya tashi, kowa da ke wurin so yake yaga fuskar marshal Omar, sun jinjinawa ƙarfin ikonsa, .
"Yalla6ai! dan Allah ka karbi wayarka, wlh zamuyi biyayya akan abunda kace," acewar wannan copral ɗin,'
sai lokacin Marshal Omar yasanya hannu cikin natsuwa, a hankali tare da zame face mask ɗinsa, Wow zo ka ga ido
Cikin wannan Cool voice ɗin tasa yace "Sunana Marshal Omar, U.s Army ni ɗane ga Chief of Army staff wato Abban sojoji,'
tunkan ya idasa maganar tasa gaba ɗaya police ɗin dake wurin suka sara masa, hatta sauran mutanen dake tsaitsaye a wurin duk suka sara mashi jin sunan daya ambata,
"Nayi muku uziri ne, saboda na lura bakusan koni wanene ba, duk da nayi mamakin hakan,"
Sauke hannayensu su kayi, Tabbas sai yanzu suka shaida shi, abunda yasa suka rikice sun san cewa Marshal Omar ɗin da su ka sani suke yawan gani tare da SGR ba anan suke zaune ba, kuma basu ta6a tunanin zasu ganshi ido da ido ba, sun saba ganinsa a kafafen sada zumunta, shiyasa su kayi tsammanin ko raina musu hankali zaiyi, gashi kuma yayi hiden face ɗinsa da mask sannan, babu uniform ajikinsa shiyasa komai ya shige musu,
"Ynz yalla6ai ya zamuyi kenan? Domim Case ɗin yaran ya kai har wurin commissioner of police, cikin week ɗin nan ma muke shirin miƙa su court don gudanar da shari'a, rashin lpyr yarinyar ne ma ya dakatar da komai," inspector ɗinne ya kora masa bayani,
"Ku bar komai a hannu na, zan yi magana da commissioner ɗin, zaku iya tafiya," ya basu umarni
Yayi magana tare da amsar wayarsa daga hannunsa, ba musu ƴan sandar suka kama hanya tare da barin asibitin suna masu tsananin mamakin ƙarfin ikon Marshal Omar lallai shi ba ƙaramin jan wuya bane 💪💪💪
(Yanzu shikenan an kashe case ɗin su Hosana da jahad kurmus ya mutu) 😁😬
Mutanen wurin gaba ɗaya murmushi kawai suke saki, kamar a shirin film haka suke kallon lamarin, haƙiƙa marshal Omar ya gama tafiya dasu,
Ajiyar zuciya kawai Jahad ke saki tarasa me zatayi don farin ciki, sam bakinta taƙi rufuwa (shin bana faɗa muku ba? Cewa dukkan tsanani yana tare da sauƙi? Sannan bawani yanayi na arayuwa da yake kasance wa na dundundun ba? this is an example) 💞😊
Murmushi kawai hosana ke saki, sam taƙi barin jikinsa har sai da yace "My hand" sannan ta janye jikinta, daga nasa tana zazzare masa waɗannan kyawawan idanuwan nata, sai faman murmushi take zabga mashi, shi kam binta kawai yake yi da kallo,
"Kowa ya koma bakin aikinsa!!" Marshal Omar ya faɗi yana kallon jama'ar dake wurin, cikin sauri doctors ɗin dake wurin da nurses ɗin da other peoples ɗin suka watse,
Ajiyar zuciya yasaki tare da mayar da eyes ɗinsa akan major ɗin dake bayansa yace "A tafi da twins ɗin nan, akai munsu gidan goggona, asanar da ita cewa zandawo later,"
Ya ƙare maganar da cewa "asan irin driving ɗin da za'ayi dasu," murmushi kawai major ɗin ke saki, aransa yace "Oga fa yayi kamu da alama, Allah yasa ayi da ran mu" 😇
A fili kuma yace "Consider it done Sir!!"
Haka suka tasa ƙeyarsu hosana, waɗannan hot soldiers ɗin suka sasu agaba, har aka fice dasu marshal Omar bai dauke idonsa daga kan yarinyar ba, sai da yaji tashin motocinsu sannan,
Haka motocin nan suka fice dasu, daga asibitin, 😊
Police ɗin nan yajima yana mamaki, daga cewa wanene marshal omar sai kawai yaga rundunar sojoji, sojojin ma bana nan ba tab, lallai ba ƙaramin Jan wuya bane, 💪
Murmushi kawai babban likita ke saki wanda ya rage a wurin tsaye, sai lokacin marshal omar ya lura dashi, cikin sauri ya ƙarasa tare da hugging ɗinsa yana cewa "Am sorry ban lura dakai ba wlh,"
Babban likita yajanye jikinsa tare da cewa "Shege Omar ! Mutanen U.S wlh yau ka bani mamaki, kayi matuƙar burgeni sai naga abun kamar ashirin film, shin wai ma ni dirar yaushe ? dama ka shigo garin kenan ?
Ɗan ƙayataccen murmushi marshal omar yasaki tare da cewa "3 weeks kenan da zuwan mu, tare da Captain mu ka taho daga kd shi ya wuce zariya wurinsu ammi ni kuma na wuto nan kai tsaye, tomorrow insha Allah zan juya nima,"
Ruƙo hannunsa babban likita yayi suka tunkari office ɗinsa, domin samun damar tattaunawa dakyau, sai faman murmushi yake saki, Allah sarki ɗan uwa mai daɗi, yama rasa ina zai sa Marshal Omar saboda tsabar farin ciki,
Yana lura da nurses ɗin dake ta faman leƙensa, wato sun ƙyasa koda yake dole ne abunda ya faru ya burge kowa,
A office ɗinsa suka zauna, ga sanyin A.c komai tsaf tsaf, suka zauna suna facing juna,
"Bari nasa akawo maka abunsha," acewar Babban likita, cikin sauri umar yace "A'a no need"
"Wai ni kam ina SGR? wato shi bazai ajiye makaman yaƙin nan ba , yazo ya kawo mana ziyara ba ko"?
ɗan murmushi omar yayi tare da cewa "rikicinsa da Ammi ne, kasan tace ita ƴa'ƴan fatima, ba jinin ta bane don haka bata buƙatar, waninsu ya sada zumunci da family ɗinta," .
tsoki doctor yaja rai a6ace yace "wannan guyababban jarababbiyar tsohuwar bansan meke damunta ba, ƙiri~ƙiri ki tsani yara grand child ɗinki kuma? inace faɗanta da Aunty fatima ne ba da su ba, haba !!" ya ƙare mgnr cikin ƙunci
Omar yace "Abun yana damuna nima, especially yadda take nunawa su junaid tsana batasan su ƙiri-ƙiri, yanzu ni ba wannan ba game da Twins ɗin can,' ya ɗan dakata da maganar,
Murmushi big doctor yayi tare da cewa "me kake son sani game dasu"?.
"Me ke faruwa dasu ne, kuma wacece bata lafiya acikinsu, sannan ina iyayensu ne "? Omar ya tambaya cike da son jin taƙaitaccen bayani,
Gyara zama dr ɗin yayi tare da cewa" ita wadda ta faɗa maka ajikin ka, itace bata da lpy, she has a mental illness har aiki ma an ta6ayi mata, ina ji anan asibitin ne, sannan tana da asthma, bansan dae taƙamaiman labarinsu ba, amma ita ɗayar mai hankalin munyi magana da ita, ta gayamun cewa, basu da kowa a hannun wata tsohuwa suke, so tsohuwarce ta rasu kuma bincike ya nuna cewa poison aka bata, tace mun basu ne suka kashe ta ba, iya abunda nasani kenan,"
Shiru Omar yayi na ɗan wani lokaci kafin yace "zanyi binci ke akansu amma ba ynx ba, suna buƙatar kulawa ssae, ynx ita mara lafiyar, me take bukata," .
"drugs ne kawai dama ake bata, ynx ma already na rubutamusu waɗanda zata yi amfani dashi, sannan suna buƙatar abinci mai gina jiki sosai tabbas, akwai yunwa atattare dasu,' babban likita ya kare jawabin yana kallonsa,
Shiru yayi baice komai ba, yana wani tunani,
" ynx ya zakayi da twins ɗin naji kace akaisu wurin goggonku," babban likita ya tambaye sa, .
Ajiyar zuciya Omar yasaki tare da cewa "as frm now dukkan wani responsibilities ɗinsu ya dawo underneath ɗina ! ban damu da sanin su wanene parent ɗinsu ba ko family ɗinsu, saboda banga kowa atare dasu ba, that means anyi watsi dasu, don haka na mallakawa kaina su !!!!!
Wani irin Murnushi babban likita yake saki yana kallonsa, wannan ƙarfin halin da ƙwarin guiwar Omar ba ƙaramin burgeshi su ke yi ba, .
Sam bakinsa ya gaza rufuwa don murna cikin tsananin farin ciki yace"haƙiƙa Omar kai na dabanne ko acikin mutane, halin ka na musamman ne, ka cancanci fiye da komai ma, Allah yasa ka maka da mafificin alkhairi, ya ci gaba da ɗaukaka ka, sakamakon wannan ceton da kayi Allah yasa ka maka da gidan Aljanna first step,"
Murmushi kawai Omar ke saki, shikam babban likita ya gaza rufe baki addu'o'i kawai yake masa, a ƙarshe yashe "Allah yasa su zama Alkhairi agare ka,"
"Ameen" ya amsa mar,


....................SEHRISH......................
Tsaye take tana leƙen su junaid dake buga ball a cikin filin kwallon dake a gidan ,
ta cikin window take leƙensu, tana murmushi, tashin ta kenan bayan ta koma baccin da suka kammala breakfast,
Jersey ɗin dake jikinsa ba ƙaramin kyau su kayi masa ba, abunka ga farar fata, yellow ne kayan kwallon sai faman tsalle tsalle ya keyi, dama shi indai wurin wasa ne da ci a nan yafi auki,
Tare da wasu daga cikin sojojin dake tsaron gidan suke buga ball ɗin,
dariya kawai take yi masa, ganin sai zura wa da gudu yake yana taro ball ɗin su kuma suna kwace ta,
tunano wa tayi da farkon zuwanta gidan, lokacin da motar Hajajju ta shigo da ita cikin gidan, tabbas tagansu a time ɗin suna buga wasan kwallo,
kamar yadda dae take kallonsu a yanzu, amma awancan lokacin, shi dasu twins ne da fawan suke kwallon, sa6anin ynx da masu gadin gidan suke buga wasan,
"Allah sarki junaid, ji bi yadda yake ta faman shan wahala wurin taro ball suna kwace mashi, maimakon yaji haushi amma sai faman murmushi ma yake yi, shi dae baya gaji da murmushi a face ɗinsa,"
Tayi maganar nan a lokacin da take ƙoƙarin zuge glass ɗin windon, ta janyo labulen ta rufe, tana sauke ajiyar zuciya,
tunanin ta ya koma kan Babban yaya wanda tun da safe take jiran saukowarsa, amma bai fito ba, ko breakfast bai sauko ya ci ba, hakan yasa ta cikin damuwa sosai,
"Bari dae na fita naje na tambayi aunty azmee, ko naje na tashe shi in bacci ya ke yi "?
tayi maganar a fili, cikin sauri ta ƙarasa saman bed ɗinta, ta ɗauki dogon wandonta ta zura, dama daga ita sai riga dai-dai guiwa,
Gashin bakinta kawai ta ɗauko a saman mirror, ta maƙala shi kafin ta fice daga ɗakin,
A hankali take tafiya, a main parlor ɗin ta hangi su Abbansu tare da wani Amininsa Alhajin gaske daya kawo masa ziyara,
Su biyu suna tattaunawa,
saɗaɗawa tayi ta wuce kitchen, anan ta sami aunty aunty azmee tana shirya musu drinks a tray, cikin wasu kofuna masu kyau,
"Yauwa rishi dama yanzu nake ƙoƙarin zuwa na tashe ki, kin barni da aiki ko," ? ta tambaya tana kallonta,
Cikin jin kunya Sehrish tace"Am sorry aunty azmee wlh, ina shiga bedroom ɗina naje na watsa ruwa, kawai sai bacci 6arawo ya ɗauke ni,"
Dariya azmee tayi azmee tayi tare da cewa "Bacci 6arawo ko? mutun yaje ya saki baki yana bacci, kuma yazo yace wa mutane wai baisan ya akai bacci ya ɗauke sa ba,'
Murmushi sehrish tayi tare da miƙa hannu ta kar6i tray ɗin da azmee ke miƙa mata,
Amsa tayi tana cewa "Aunty azmee wanene baƙon da yazo "?
"Ki je ki tambaye sa mana, ki ce wanene kai zai baki amsa,"
Dariya sehrish tayi jin amsar da azmee ta bata, ɗan zaro ido tayi tare da cewa "tab dana sha mari wlh,"
Azmee tace " ba wani mari wlh, amsa kawai zai baki da yaren da zaki gane,"
"Ae wannan bugu kenan," ta faɗi tana kokarin fita, har ta sa kai zata fice ta kuma juyo wa tare da cewa " Aunty azmee babban yaya fa, bai fito daga bedroom ɗinsa ba ko lpy,"?
"Ki je part ɗinsa mana ki tambaye sa," ta faɗi cikin zolaya, ɗan ta6e baki sehrish tayi tana jinjina kai tace "wai Allah ! ni asuwa? ɗan wake a hotel,"?
dariya azmee tayi tare da cewa "ynx dae kije ki kai musu, kin tsara surutu kamar ƴan jarida, "
Cikin sauri sehrish ta fice izuwa cikin main parlor ɗin, cikin natsuwa take tafiya tunkan ta isa, tajiyo muryar abokin abban dayazo yana cewa "Ae ni ba ƙaramin daɗin zuwan nan nasu Rafayet da Omar naji ba, koba komai kafin su koma U.s zasu gyara wa wasu zama A Qasar nan,"
Abba yace "Oh damuwarka kenan, baka damu da bala'en da zai jawo mun ba, kwarama Omar shi da sauƙi, amma rafayet kana ganin last da yazo ya rinƙasa ana kawo masa ƴa'ƴan mutane har cikin gidan nan yana hukunta su, babu yadda zanyi dashi, sai dae nabishi da ido kawai, saboda yafi ƙarfi na,'
Dariyar Alhajin yayi tare da cewa "Ae samun ƴa'ƴa kamar Omar da rafayet wlh abun alfari ne, kowane Uba zai so ya mallaki ƴa'ƴa irinsu, gashi ynx asanadinsu darajarka da ta family ɗinku ta ɗaukaka sosai a faɗin duniyar nan, Kowa yabonsu ya ke yi, yakamata karinka alfahari dasu, mu gana mu nan ƴa'ƴan shaggu kamar mata, basa iya ta6akawa ƙasa komai, ga Jabeer nan har asibiti na gina masa in yadawo daga Uk ya ci gaba da kula dashi, amma yaron nan ya watsa mun ƙasa a ido, wai shi yafin karfin ya yi aiki a nigeria, Naji haushi lokacin duk mun lalacewar kasarka ae ƙasarka ce," Cikin nuna takaici Alhajin yakewa Abban wannan bayanin
da sallama Sehrish taƙarsa cikin girmamawa ta gaishe su, suka amsa mata sannan ta miƙa musu drinks din suka ɗauka suna sa mata albarka,
bayan sun gama ta kama hanyar komawa cikin kitchen, wani irin son Babban yayan ne ya kara shiga ranta, jin yadda Abokin abban nasu ke yabonsa, murmushi kawae take saki, ynx ta kara jin ya kwanta mata luf acikin ranta,
Shiga kitchen ɗin tayi tare da ajiye tray ɗin, azmee tace "yanzu sai ki je, ki gyara masa part ɗinsa ko? tayi maganar tana kallonta,
Sehrish tace "Yana fa ciki, kuma kince baisan atashe shi yana bacci, kuma baisan ƙara, in nayi kwaratsi fa zai ji harya farka,"

Murmushi azmee tayi tare da cewa " to ina ruwanki da bedroom ɗinsa? Falonsa zaki fara gyara wa, kafin ya tashi sai ki gyara can ɗin ko ?
Sehrish tace "To bari nace"
tafice tana fargaba, tana jiyo muryar Aunty azmee tana cewa "Anaso ana kaiwa kasuwa,"
Ƴar dariya tayi tare da fi ce wa, kai tsaye part ɗinsa ta wuce zuciyarta na ɗar ɗar,
Kamar kullum a buɗe door ɗin parta ɗinsa take, a hankali tashiga tana sanɗa kamar 6arauniya,
Sai da tayi tsakiyar falonsa nasa tasoma tunanin wai me ma tazo yi? Saboda ko'ina agyare yake tsaf ba datti ko kaɗan, sai walwali wurin yake har yau tana jinjinawa haɗuwarsa,
Murmushi tasaki tana wani tunani aranta, wanda bazai yiyu ba, 😔
Sai da tagama zagaye falon nasa tana tunani iri iri aranta, sannan ta soma gyara sa, babu wani aiki awurin, kawai ta ɗan yi goge goge ne,
tsayawa tari riƙe da waist ɗinta, so take ta sashi a idonta, zuciyarta ce ta bata shawara da cewa "ki ɗan leƙa sa, mana,"

"Anya? idan kuma idonsa biyu fa? In ya kama ni karairaya ni zae yi Allah,' ta bata zuciyarta amsa,

"Ke sai ki bari ya ganki? Ae lalla6awa zakiyi a hankali sai ki dan leƙa,'

Murmushi tasaki tare da tafiya cikin sanɗa, ta tsaya a bakin ƙopan ɗakin nasa, taci sa'a kopan a bude take, curtains ɗin ta ɗan janye tana leƙensa, 👀👁️

Kwance ya ke yana sharar baccinsa, cikin natsuwa a saman Royal bed ɗinsa, kai ka ce da zallar gold aka ƙera gadon, yadda ya ke wani kyalli ajikinsa,

Half body ɗinsa yayi covering ɗinsa da lallausan blanket, hannunsa na dama, ya zagayo dashi har izuwa saitin left ear ɗinsa, yayin da hannunsa na hagu kuma ya ke a saman wide chest ɗinsa,

Bin shi take da kallo kamar kura taga nama, wannan haɗaɗɗiyar sumar tasa, ta rufe masa half face ɗinsa, dogon hancinsa kawai take hange,
Lumshe ido kawai take, ita kaɗae tasan yanayin da ta shiga,
Tana cikin wannan leƙen nasa ko ƙeftawa babu, taji an shaqi wuyanta da ƙarfin gaske, Shaqa ba ta wasa ba,
Wani irin tsoro ne ya ziyarce ta, hankali atashe ta zazzare idanunta,
Muryarsa ce ta ratsa kunnanta da cewa "meyasa ki ke leƙe na !!"?
wata irin zufa ce ta wankowa sehrish, tsananin tashin hankali ne ya bayyana a idonta, lokacin da ta lura cewa babu shi asaman gadon nasa, yaushe har ya sauko yakuma wuce ta, ya zagayo ta bayanta,harya shaƙi wuyanta,
Wani irin fitsari ne mai zafin gaske ya kufce mata, ji kake zirrrrrrrr yana zubo mata,
Muryarsa ce ta sake karaɗe kunnanta, " baza'a bani amsa ba" 😳😳😳😳😳😳😳

*Hafsat Bature Moh'd Boss Lady* 💋✨👏
*I Need your prayers urgently* 😔💕💞💕💞💕💞💕💞💕💞💕💞

*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*

_💞Extraodinary Love💞_


*Writer✍️✍️✍️✍️*

*💋HAFSAT BATURE BATURE BOSS LADY💋*

Full episode


~Page 73 -74

End of Chapter 1

*✨✨LAFAZI WRITERS ASSOCIATION* ✨✨

Not edited 😎

Jin shiru ba ta da niyar bashi amsar yasa shi harya fusata, a wani irin zuciye ya buga kanta jikin kopan da ƙarfin gaske, nan take sehrish ta fasa wata irin azababbiyar ƙara mai sauti tare da faɗuwa yaraf a sume,
Wannan sounds ɗin da sehrish ta fidda ne ya farkar dashi daga dogon baccin da ya ke yi, a hankali yake buɗe eyes ɗinsa yana yamutsa fuska agajiye blue eyes ɗinsa na facing Ceilling,


Hankali tashe sehrish ta farka daga nap ɗin daya dauke ta, sai uwar zufa ke zubowa daga cikin sumar kanta, ashe bayan ta kammala gyara masa parlor insa bacci ne ya ɗauke ta a nan kasan lallusana carpet ɗin dake shimfiɗe, sai faman zazzare kyawawan idanuwanta take, tana shasshafa jikinta don ta tabbatarwa da kanta cewa mafarki ne take ba gaskiya ba,

Ajiyar zuciya ta saki tare da faɗin "Alhamdulillah Allah na gode maka," cikin hanzari sehrish ta miƙe tare da fice wa daga part ɗin nasa ta koma kitchen ,
Shiru tayi tana ƴan kame kame ashe tun ɗazu azmee na zaune tana jiran.dawowarta,
Tana zaune saman daya daga cikin dining chairs dake a kitchen ɗin, ga tray da ta kammala shiryawa babban yayan breakfast ɗinsa ajiye a saman table ɗin gabanta, ta zabga tagumi tana jiran Sehrish,
Bin ta tayi da kallo ganin yadda ta shigo a hargitse tana wurwurga ido,
"Sannu ko'? Shanyar da ki kayi harta bushe," ta faɗi tana kallon ta,
Sunnar da kai sehrish tayi tana wasa da fingers ɗinta tace "Am sorry aunty azmee wlh bacci ne ya kwashe ni a falonsa without my knowing...'
tunkan ta ƙarasa azmee ta katse ta da cewa "bacci !!! A part ɗinsa!? Kin sha giyar wake ne?anya ko kinsan wanene SGR kuwa? You ave to be very careful sehrish, don't let that happen again if not u will Explain it !!,"
Azmee ta faɗi cikin faɗa faɗa, hakan ba ƙaramin tayarwa Sehrish da hankali yayi ba, ta tsorata sosai tuni eyes ɗinta sun cicciko da kwalla," .
"Aunty azmee tsotsai ne, ba da sani na ba nima, wlh sharrin shaiɗan ne,"
Sototo tayi da baki tana kallonta cikin takaici tace "na gane Ki sehrish whenever u did something wrong sai ki ce sharrin shaiɗan ko? ga iya bada hakuri kamar matar aure tagari,'
duƙar da kai sehrish tayi, jikinta ya gama mutuwa jin aunty azmeenta nayi mata faɗa,
ganin halin da sehrish ta shiga yasa azmee sassautawa da murya cikin lallashi tace "Sehrish ba faɗa nake miki ba, i just wanna u to be very careful in this home, bana so asamu matsalar da zata sanya a kore ki daga
DOWNLOAD
DOWNLOAD

6 Comments On ABBAN SOJOJI
avatar
ibrahim-5-3

7 months ago

Reply

Ina son abban sojoji complete

avatar
ibrahim-5-3

7 months ago

Reply

Ina son abban sojoji complete

avatar
muhammad-4-3-8

6 months ago

Reply

I want it

avatar
hauwa-said

6 months ago

Reply

Please Ina so

avatar
hauwa-said

6 months ago

Reply

Please Ina so

avatar
husaini

2 months ago

Reply

I love this novel

Please Login or Register in order to submit comment