Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[12:17PM, 02/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: [1/6, 9:06 AM] A A Dboy: *YAR TALLAH NEW EPISODE*


*CHAPTER 1*

Tafe tAke tana rusa kuka wiwi,,,,,wiwi
Duk ta hada miyau majina da hawaye ta dame fuska gaba
daya
Rungume take da tiren tallan tata wanda ba komai a cikinsa
sai ihu take kwararawa tana kiran wayyo kudina wayyo ni
kudina
Mutane sai kallonta sukeyi masu tausayi daga cikinsu su
kirata suji abinda ya faru su lallasheta ta tafi
A haka taita saqawa ta lunguna harta iso layin gidansu
Tunda ta iso layin rabi,u wanda bai wuce dan kimanin
shekara goma sha huduba kejiyo sautin kukanta yana duqe
yana faman wanke wanke
Yai niyyar miqewa karaf sukai ido hudu da inna laure
Ta watsa masa wani irin kallo simi simi ya koma yaci gaba
da wanke wanken
Tace munafuki dan iska wlh ka sake tashi baka gama
wanke wankennaN ba saina karya maka qafafu
Ta qara jan tsaki ta hankade labule ta shige Daki
Rabi,u yai saurin tsame hannunsa daga wanke wanken ya
kwasa yai waje da gudu
A bakin kofar zauren sukai kicibus yace waya tabakine
saude?
Ta qara fashewa da wani kukan wanda yafi nada sauti
Rabiu ya qara janta jikinsa kiyi haquri saude fadamin meke
faruwa?
Tadan sassauta da kukan tace kudina yaya kudin tallah na
wani ya kwaceminsu
Rabiu ya dafe kirji ido waje yace garin yaya saude?
Kinsan halin inna laure kuma dukanki zatayi
Ta qara fashewa da kuka wayyo yaya dan allah ka roqeta
karta dakeni
Ya danyi jimm kiyi haquri saude babu yaddah zan iya kixo
muje kawai ta dakekin
Ta qanqameshi wayyo yaya wlh yankani zatayi
Idanunsa suka kawo kwallah ya cije yace zo muje saude
insha allahu bazata dokekiba kinji?
Kai kawai ta daga masa tana share hawaye yaja hannunta
suka shiga ciki
Tsaye take a kofar daki da alamun ta cika ta tumbatsa jira
kawai take a tabata ta bashe
Saude ta qara fashewa da kuka wayyo allah na wlh yaya
dukana zatayi
Inna laure ta zaburo tayo kansu
In dokeki don ubanki laifin me kikayi?
Hala kin dawomin da sauran raguwar alalen ne ko?ta fada
lokacin data shaqo wuyanta
Ina kudun suke in gani?
Ta qara fashewa da kuka tace wani ya kwace kutumar
ubannan wani ya kwace? Aiko yarinya yau zaki daku a
gidannan don wlh saina lahira ya fikijin dadi. Ta jata
kiyyyyyyyy..... A qasa har zuwa bakin rijiya ta janyo igiyar
guga zaki fadamin ina kudina suke ko saina miki dukan
mutuwa da igiyar gugannan?
Cikin kuka tace wlh wani ne ya kwace ya ruga tace lallai
yarinya aiko jikinki zai gaya miki ni zaki kawowa zancen
banza zancen wofi
Tasa qafarta ta tureta ta fadi ta dinga lafta mata igiyar
gugar kamar badan mutum take duka ba
Hankalin rabiu ya tashi yaddah yaga qanuwar tashi keyi
gashi tasa qafa ta take mata ruwan ciki. Wani irin kuka ya
kwace masa ya duqa a wurin yana bata haquri
Inna laure tace au har kanada bakin magana munafiki
xonan daman ai jiranka nakeyi ta shaqoshi ta hadesu guri
guda taci gaba da jibga tamkar zautacciya
Hankali tashe inna mai dan wake ta zagayo gidan ko lullubi
babu a tare da ita
Kai jama,a lafiya maike faruwane a gidannan?
Inna laure ta tsaya da dukan tana huci. Barni da yan iskan
yarannan mai danwake nema suke su samin hawan jini.
Niqi niqi ina fama dasu inkai gwauro inkai mari wai dondai
a samu a rufama kai asiri amman yan iskan yaran basu
gani kawai an mutu an barni da jaraba yanxu ace kamar
saude wai har tasan taje tallah ta boye kudin wai tace wani
ya kwace sbd mugun hali irinna wannan munafukin
annamimin dake koya mata
Inna mai danwake tace eh kam gaskia baku kyautawa
kankuba. Yanxu ku harkunfi son aita jibgarku irin haka idan
kun boye kudin kuci me dasu fisabilillahi
Tadan numfasa tana kallonsu kafin ta qara zaro ido a,a
laure yaya nake ganin yarcan kamar bata motsine""
Ta qara matsawa tana tattabata ta dago da sauri hankali
tashe tace wlh laure bata motsi. Tace kai haba mai dan
wake da gaske kike?
Inna mai danwake ta daga hannun nata ta saki taga ya tafi
ragwaf alamar ba rai
Inna laure ta kwasa da gudu tana gyara daurin zani fadi
take iya karfinta na shiga uku ni laure

Dis is just d begining
[1/6, 9:06 AM] A A Dboy: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚
[1/7, 5:48 PM] A A Dboy: *YAR TALLA*

*CHAPTER TWO 2*

Inna laure ta kwasa a juge tana fadin na shiga uku ta isa
bakin randa ta ciko tasa da ruwa taxo ta sheqa mata gaba
gaba daya yarinyar ta firgita ta tashi tana fadar wayyo inna
kiyi haquri mai dan wake ta riqeta ke yi shiru da allah aita
kyaleki
Inna laure ta sauke wani nannauyen numfashi ta shiga zare
na mujiya
Mai dan wake ta miqe tana fadin ni na tafi amman dan allah
laure ki dinga kula kisan irin dukan da zaki dinga musu don
karkije ki daure kanki da kanki
Inna laure ta sake jan kwaron numfashi kafin tace insha
allahu zan kiyaye mai dan wake ta fice abinta
Laure ta juya ta shige dakinta ta barsu a nan
Saude ta rarrafa ta nufi dan uwan nata
Wanda ke zaune ya hada kai da gwiwa yanata faman kuka
Saude ta raba jikinsa ta kwanta ya qara janta a jikinsa
sosai
Bata jima da kwanciyaba barci ya dauketa sai faman jan
ajiyar zuciya take
Akai akai
Malam bala yayi sallama ya shigo gidan nasa hannunsa
saqale dana iklima yarinyar da bazata wuce yar shekara
goma sha daya ba
Qanwar saude ce don ita yanxu tana shekara sha biyu ne a
duniya
Malam bala ya shigo tsakar gidan tare da miqama iklima
baqar ledar dake hannunsa ta karba ta shige dakin
mahaifiyarta tana tsallen murna
Malam bala ya kalli rabiu fuskarsa ba yabo ba fallasa yace
bakin munafiki kallon uwar me kakemin? Me mugun halin
tsiya hala wani abun kukai aka dakeku ko?
Inna laure ta hankado labule ta fito kamar an bankadota ai
daman jiranka nake malam wallahi yau saika biyani kudina
in dorama yarinyarnan tallah ta boye kudin wai tace an
kwace
Na rantse da allah ban daukar asara
Malam bala yace ai daman tunda na gansu zazzaune anan
nasan wata ta'asar sukayi
Yan iskan yara masu tsinannan hali wanda sukai gadon
Halin tsiya niko yarannan dada inda zan kai
Su wallahi dana kaisu na huta da bala,in su
Tace ahto nidai kudinane sai an biyani
Babu mai doramin asara alalata ta murtala biyuce da goma
Malam bala yace toya zanyi ai dole na biyaki tunda allah ya
hadani da jarababbun yaya
Kiyi haquri idan na dawo daga kasuwa gobe saina biyaki
miqomin buta nayi alwala
Laure taja kwafa ta juya ta koma dakinta ta dauko masa
butan ya nufi bayan gida
Ta watsama rabiu harara sannan ta wuce dakinta ta samu
iklima ta zazzage baqar ledar sai diban kilishinta takeyi
Ta miqa hannu zata dauka yar tasa kuka tana tirje tirjen
qafafuwa inna laure tayi saurin ajiyewa
Ga abinkinan sarkin rigima. Ai nasandai duk cinki baki iya
cinye wannan kilishin
Yarinyar ta turo baki irin na shaqwababbun yaya taci gaba
tacin abinta
Duhun magaribane ya fara ketowa sauro suka fara duduma
a jikin rabiu ya lallaba ya kwantar da saude saman siminti
Ya lallaba ya nufi dan akurkin dakinsu ya shinfida musu yar
yagalgalallan tabarman kaba irin mai cin jikinnan
Sannan ya dawo ya lallaba ya dauketa da qar
Ya kaita dakin ya kwantar da ita ita kadai ta mamaye
tabarman don haka shi saman simintin dakin ya kwanta
babu ko filo balle abun rufa
Ga duhun dakin. Ya runtse idanunsa dukda yanada yakinin
yunwace ke kwankwasarsa bazata barshi yayi barci ba
Tunanin mahaifiyarsu ya fado masa kamar yaddah kullun
yakeyi kafin ya kwanta
Wasu hawaye suka cika masa idanu masu zafi tabbas
yasan wahalar da sukesha somon tabice
Akan wanda mahaifiyarsu tasha a gurin mahaifinsu
Nasiharta gareshi itace ta dawo masa tamkar yanxu take
masa su tace
Rabiu don allah don annabi ko bayan raina. Ka kula da
rayuwar qanwarka karkabar rayuwarta ta gurbata a duk
halin da kuka tsinci kanku a ciki kaga ita mace ce dole tana
buqatar taimakon wani wanda zai jibanci lamarinta
Nasan kaima kana buqatar taimako amman a duk yanda
rayuwa taxo rabiu yinta ake
Nasan kodani ko bani dole ku rayu bakuda mataimaki sai
allah.
Rabiu kuyitayimin addu,a in rayu kodan saboda ku. Nima
inason in rayu sbd ku
Baisan sanda kuka ya kwace masa ba saida yaji saude
jikinsa tana jijjigashi.
Tace yaya kuka kake?
Yayi saurin hadiye kukan tare da goge hawayensa
Ya lalubo hannunta ya riqe kafin yace ba kuka nakeba
dariyace nake na tadaki ko?
Tace a,a yaya yinwa nakeji cikina sai cixona yakeyi tun safe
banci komaiba na tafi tallah har yanxu
Ya salam ya fada a fili sbd rashin sanin abinyi
Saude ta kwantar da kanta a kan cinyarshi tace kaji cikina
sai kuka yake ko yaya?
Bai tanka mataba ta qara girgizashi cikin muryar kuka tace
yaya abinci zanci
Rabiu ya kwantar da murya yace dakinyi haquri kin kwanta
kinga da safe ba saiki karya ba
Tace wlh bazan iya barciba yace to lallaba ki kwanta ina
xuwa
Ta zame daga jikin nasa sai shi kuma ya miqe ya fita
Duk suna kwakkwance a tsakar gida cikin gidan sauro sbd
lokacin zafine
Sai radio ce keta faman babatunta a banza
Rabiu ya lallaba sadab sadab ya isa har inda suke ya dauko
langar fura ya lallabo ya shigo
Dakin ya zauna yana fadin tashi saude ga fura na samo
miki kisha
Ta tashi da hanzarinta ya lalubo bakinta ya kafa mata
langar furar tasha iya shanta sannan shima yasha kadan ya
rage sauran ya lallaba ya tafi don mayarwa
Yana qoqarin ajewa kenan iklima ta farka tana fadin laure
zansha fura
Rabiu yai saurin durkusawa a wurin jikinsa nata faman bari
Inna laure ta tashi tana haska fitila da niyyar dauko langar
furar
Taga mutum a durkushe wuri guda
Ta fasa wani uban ihu wayyo allah malam baraw barawo
Malam ya tashi a firgice ya rarimo adda yana ina yana ina ?
Kafin ya fito daga ciikin gidan sauron rabiu ya kwasa a guje
yayi dakinsu yana famar rawar jiki
Malam ya fito yana ina barawon yake laure?
Tana rawar murya tace nan nan na ganshi duqe wlh
Malam bala yaja tsaki to idan nan kika ganshi yana ina ?
A,a ka. Haska mana ya dauko touc light ya tafi yana
haskawa har zuwa zaure ya dawo yana fadin kedinnan
Wallahi kinada matsala. Yanxu haka inuwa wani tsuntsun
kika gani kinxo kin rikita mutane da wani barawo
Laure tace malam nifa mutun na gani anan duqe
Yace to idan da mutum kika gani da ban ganshiba ko laya
yayi ya bata? Don allah ki koma ki kwanta kinji
Laure tace niko malam wlh bazan iya rintsawa ba don da
idona naga mutum nan tsugunne
Malam bala ya shige gidan sauransa yana fadin ai saikiyita
zama ke kadai
Sai a lokacin hankalin rabiu ya kwanta ya saki wata ajiyar
zuciya ya lallaba ya kwanta abinsa
Bai jima da kwanciya ba bacci barawo ya sacesa
Qarshe shida na safe laure ta hankado kofar dakin nasu ta
gansu sai sharar barcinsu kawai sukeyi wani takaici ya
kamata ta juya ta debo ruwa cikin kwanon sha ta daga
labulen ta sheqa musu a firgice duk suka tashi sukai wuqi
wuqi kamar ya,yan zakaru
Inna laure ta taba baki cikin masifa tace
Hmmmmm
Ya labarin
[1/7, 5:49 PM] A A Dboy: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚
[12:17PM, 02/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: [1/8, 4:40 PM] I love my mum: *YAR TALLA*

*CHAPTER 3*

Inna laure ta tabe baki cikin masifa tace nan har lokacin barcin safe gareku?
Sannunku yayan hutu to saiku tashi
Kai kaje ka jido mana ruwa ke kuma kije ki share mana gida ki tafi kai markadan waina
Ta saki labulan ta juya tai gaba
Babu wanda yace komai cikinsu rabiu yadau jarka ita kuma tadau robar markaden ta fice babu alwala bare wanke ido
Rabiu ya jido ruwa yafi jarka goma
Saida ya ciccika komai na gidan sannan ya fara gyaran gidan
Saude ta dawo daga markaden tana hada wuta iklima ta fito riqe da kofin shayi da qaton biredi a hannunta
Saude tai saurin tashi daga hura wutar
Da take ta kalli iklima tana miqa mata hannu sanmin zo indan gutsira kadan kinji?
Rabiu yai saurin kwAbarta ke da,ala kyale mata abinta
Saude ta bata fuska nidai don allah zanci
Yace toki bari idan na samu kudi zan siyo miki
Ta qara bata fuska nidai zanci
Kullum saikace zaka samu kudi kuma ba samu kakeba
Rabiu yadan kura mata ido kafin yace insha allahu yanxu zan samu kinji?
Kai kawai ta daga masa yana juyawa ta miqama yarinyar hannu iklima tace ban badawa
Ta juya ta shige dakin nasu tana fadin laure wai kinji wai in san mata biredin ni kuma nace ban badawa
Laure ta hankado daki tana fadin au biredin yar tawa kike sama ido
Wato ta kawo miki keme cikin ci ki cinye ita kuma ta fadi ta mutu kenan ko?
Ta shaqo wuyan rigarta tana fadin dan ubanki kin sabacin irin wannan ne ?
Ko sAlon kici kiyita zawo yar banza kawai wuce ki bama mutane wuri ta hankadeta saidata fadi
Ta zuya ta kalli rabiu kai kuma zakaci gaba da aikin gabankane ko kuwa?ko zaka rama matane?
Bai tanka mataba ya duqar da kansa yaci gaba da sharar da yake
Ita kuma taja kujera ta zauna taci gaba da hada kullun wainarta
Malam ya kwalama rabiu kira. Ya ajiye tsintsiyar ya tafi
Ya watsa masa kallon banza kafin yace. Ungo ka bata munafuki wanda yai gadon mugun hali
Rabiu ya amsa jiki na rawa ya fice
Dan guntun biredi ne wanda bazai wuce gutsira biyu ba. Sai dan ruwan shayinda ba ko madara
Rabiu ya miqa mata ta karba cikin rawar jiki
Ta tura biredin duk a baki tana tauna da kyar sbd yaddah ya cika mata baki
Rabiu ya kalleta yace kisha a hankali kar kiyi amai bata kulashiba ta
Ta kafa kai ta shanye ruwan shayin tas tana lashe kofin
Inna laure ta kafa mata dundu wanda yasata amayo duk abinda taci yayo waje cikin takaici tace shegiyar yarinya mai kama da mayyah maqerin kofin zaki tando duk wanda kikasha bai isheki ba? Munafuka tashi kibar wurin kona haureki
Ta saka kafa ta tunkudeta
Saude ta kwasa da gudu ta nufi dakinsu tana kuka mai sauti
Rabiu ya rakata da kallo inna laure ta daka masa tsawa zakaci gabane kokuwa binta zakayi
Dan iska mai kama da igiyar shanya
Rabiu ya durkusa. Ya soma kwashe aman sautin kukan nata na tsinkulansa a kirji
Laure ta gama tuyar wainar ta kukkulla a farar leda naira. Biyar biyar ta zuba mata a cikin bokiti ta dauki ta goma ta miqama rabiu sannan ta kwalawa saude kira
Ta fito tana matsar hawaye laure taja tsaki au kukan kike har yanxu kenan? Baki bugu bane shiyasa tashi ki dauka gatanan ta murtala huduce kiyi maza ki dawo kinsan alala nanan tana jiranki
Saude ta durkusa ta dauki bokitin tana fadin ina tawa?
Inna laure tace eh lallai ai dadin sai yayi miki yawa kisha shayi kici waina ai dadin sai yayi miki yawa yar gidan uban waye ke a garinnan?
Batace komaiba ta lallaba ta wuce rabiu dake kusa da ita ya kamo hannunta ya damqa mata nashi wainar ta fice tana murna
Inna laure taja tsaki tace matsalarkace nidai ko suma zakadingayi sbd yinwa wlh tallah saika gamamin duk ayyukana dondai na rigada na fita haqqinka
Zakara kawai mai neman suna ka bada kwaya kaci tsakuwa
Bai tanka mataba yaci gaba da aikin nasa
Yana gamawa inna laure ta tattaro kayan iklima masu himilin yawa ta watsomasa ta wurgo masa kullin omo maza ka sabe mata kayannan
Rabiu ya durkusa yana tattare kayan bayansa na faman cijewa ya nufi bakin rijiya ya soma wankin
Malam bala ya fito daga dakin hannunsa riqe da wani dan takurerren buhu na zuwa kasuwa harya wuCe yadan dawo kadan yace kai rabiu idan ka gama wankin ka shiga daki ka tattaro nawa ya wurgo masa naira hamsin ga wannan nan kasai omo
Kuma banason wankin banza don wallahi na dawo naga basu fitaba komin dare saika sake wankesu kanajina ko?
Ya karba da hannu biyu gamida daga kai alamar eh
Saidaya kammala na iklimar gaba daya sannan yaje ya siyo omon talatin garin goma sugar goma
Yaxo ya jiqa saidaya kumbura sannan yasa suga ya fara sha
Baiyi cokali biyuba ya tsaya gamida kafama kofin garin idonsa ya cikoda hawaye
Wata rayuwa can ya tuno lokacin da mahaifiyarsu ke jiqa musu gari ta tasasu gaba shi da saude susha. Ita kuma ta zauna a gefe tana kallonsu
Ko cokali daya ba zatayiba duk kuwa da yinwar da zata tashi da ita ta wuni da ita
Tausayin mahaifiyar tasu ya dirsar masa ya tuno yar uwarsa saude yanxu haka yasan da yinwar a cikinta
Yaja numfashi sannan yaci gaba dashan garin
Laure ta giftashi kamar zata wuce don taka me yakeyi ganin garin rogone yasa ta wuceshi kawai ba tare data tankashiba
Shima kuma bai tankataba yasha garinsa ya rage sannan ya tashi ya tattaro kayan mahaifin nasa yaci gaba
Karfe daya na rana saude ta dawo daga tallar wainar tana aje bokitin laure ta miqa mata tiren alale idon yar ya ciko da hawaye wahala ya isheta
Ga wahalar yawo ga azababbiyar rana ga uwa uba yunwa ita kenan tallah ba dare ba rana
Har yaran unguwa sun nada mata suna da YAR TALLA ina kika fito tallah ina zaki tallah ina kika dawo tallah
Saude ta daura tiren saman kai wasu hawaye suka gangaro kuncinta laure ta tafa hannuwa na shiga uku
Muhammadu dan Abdullahi mezan gani ni laure ? Tallar ce bakyason zuwa to dawo ki ajiye ki zauna ki huta yar hutu zoki ajiyemin tunda baki zuwa
Saude ta wuce tana faman sharbar hawaye laure tace uhm hum yarinya kenan ai dama kin adana hawayenki don tallah yanxu kika fara alalata ta murtala hudu ce da goma ki dauki ta gomar kuma wallahi ragin sule idan kikayi a jikinki zan fanshe sannan ko kanxo bance ki dawomin dashiba
[1/8, 4:41 PM] I love my mum: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚
[1/8, 4:42 PM] I love my mum: *YAR TALLA*

*CHAPTER 4*

Tace kuma wlh ragin sule kikayi a jikinki zan fanshe sannan ban yarda da ki dawomin da ko kanxo ba anan muka tasaya
Saude dai bata kulataba ta wuce tana sharbar kwallah
Rabiu dake wanki ya tsame hannunsa daga cikin ruwan wankin ya dauko kofin garin ya bita da gudu
Ya jawo hannunta ya kaita kan dakalin wani kofar gida ya zaunar da ita gamida sauke tiren tallar a gefe ya zuba mata idanuwansa
Kukan me kike? Tallar ce bakyason zuwa?
Saude ta girgiza kai alamar a,a tana share hawaye da bayan hannunta
Rabiu yace idan ba tallar bace bakyason zuwaba to menene?
Taja majina tanata faman sheshsheqa kafin tace na gaji yaya kafata ciwo take gashi banida takalmi ga zafin rana fasona sai jini yake famanyi
Wani irin abu ya tsikari zuciyar. Rabiu ya tsirama kafar ido
Wasu hawaye suka cika a idanuwansa gashi bashi da ikon iya taimaka mata
Don shi kansa kafar tashi babu takalmi. Tabbas da tausayawa qaramar yarinya kamar saude tayi tafiya babu takalmi
Yaddah ake tsala rana yau ga uwa uba kafar duk ta tsatstsage da faso
Rabiu yasa yatsa ya goge kwallar data tarar masa muryarsa a sanyaye yace
Kiyi haquri kije insha allahu zan samar miki takalmin da zaki dinga sakawa dakin dawo kinji?
Ta daga masa kai ya miqa mata kofin garin ta karba ta shanye ta miqa masa kofin
Ya amsa ya karbi tiren ya dora mata ta tafi
Yana tsaye yana kallonta harta bace
Sannan ya juya ya koma gida
Laure ta watsa masa harara tace ni naci uwar zariyama ballentana bita zaizai
Bai tanka mataba ya duqa yaci gaba da wankinsa harya gama
Ya shanya wankin sannan ya nufi kofar dakinta ya durkusa daga waje
Inna na gama ina alalata
Inna laure ta dago daga kwancen da take saman katifa ita da yarta
Ta watsa masa wani kallo tace abincima wato har kaso biyu zaka dinga ci kenan
Koba dazun na giftaka naga naga kanacin garin kwaki ba? Dallah ni tashi ka bani wuri ta doka masa tsawa
Rabiu ya miqe tamkar almajiri ya nufi bakin rigiya ya janyo ruwa guga guda yayi alwala ya nufi dakinsu yayi sallar asuba da azahar a hade
Sannan ya kwanta nanfa gajiyar daya kwaso ta rufeshi
Saude tasha yawon tallarta harta godema allah amman alalar ko rabi bata samu ta saida ba nanfa idonta ya ciko da hawaye ta soma bin jama,a tana hadasu da Allah su siya
Danladi ya tabo abokinsa ilu kai baba yarinyar canfa tana cikin matsi ina yawan ganinta a cikin tasharnan anya ba zamu far matAba kuwa?
Ilu yace nimafa na dade ina wannan tunanin to amman abinda ke tsoratani yarinyar karamace sosai karkaje ka balloma kanka ruwa
Danladi yace kaiko da mugun baki kake idan zakaxo muje mu fasa kawai kaxo muje malam
Mu jata kangon alhaji sani
Ilu yace kuma hakanefa to taro mana ita ni bari naje na duba mana wurin na tabbatar da tsaro
Ya dire daga kan teburin da yake ya nufi gurinda saude take duqe gaban wani direban j.5 tana zazzage masa alala a kwano ilu ya iso waje yace ke yarinya idan kin gama sayar masa kikaima wancan gashi can zai siya tace to ta miqama direban alalan ya karba ya somaci ita kuma ta rabe gefe tana jiransa ya gama ya bata kudin da kwanon ta qara gaba
Direban ya soma ci gaya dago sai yaga ta kura masa ido ji take dama bakinta yakekai alalar sbd tsabar yunwar dake cinta
Direban yadan daga murya yan mata ya kike kallona ko na miki ne ?
Saude tayi saurin dauke kanta yayi daria yaci gaba da cin alalarsa
Karen matar dake can gefe yace sai oga baka tambayeta ko tana ciki bane
Yace kai share wannan bata inda ke mata dadiba
Karen motar ya sake bushewa da daria yace sai oga allah yabar mana kai
Baice masa komaiba ya qarasa cinye alalar ya wurga mata robar ta zabura ta miqe gamida saka kwanon cikin tiren ta qarasa inda yake domin karban kudin ya kura mata ido yaya akayine?
Tace kudin zaka bani
Ta nawace?
Saude ta numfasa kafin tace ta murtala daya da gomace
Yasa hannu a aljihu ya ciro kudi masu yawa ya dubeta
Yace yanxu idan na baki wadannan kudin zaki barni nayi lalata dake
Saude ta zaro ido tana kallonsa
Ya sake maimaita mata a karo na biyu
Idonta ya ciko da kwalla alamar zatayi kuka
Yace a,a meye abin kuka yanmata karbi kudinki kisan inda kikai kuma karna sake ganin kafarki ta tako inda nake
Idankuwa ba hakaba saina turmusheki
A wurinnan ya miqa mata kudin karbi
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment