Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na k'asa ce masa komai, dan yabani kunya gaskiya, nakula kuma yanada yawan tsokana, aunty Mimi kam dariya tayi, yayinda Samha tarufe baki tanayin tata.
Momma tamasa dak'uwa, “o kai Sauban ALLAH ya shiryeka, kowama bazaka d'agama k'afaba?”.
Dariya ya kumayi yana satar kallon Galadima dayay tamkar baya wajen, yace “to ai gaskiya nafad'a Momma. dan ALLAH aunty ba haka bane?”.
“gaskiyarka fa Sauban”. Aunty Mimi ta fad'a tana dariya.
Momma tace “barsu kinji my daughter, ci abincinki”.
Kai na jinjina mata cikeda kunya.
Galadima dai har yanzu baice k'alaba, baima d'ago ya kallemu ba.
Haka muka ci abincin nidai duk a takure nake, kamar yanda yafara cin abinci haka yarigamu kammalawa, tashi yay yabar wajen, yakoma can saman wasu kujeru guda biyu ya zauna, laptop d'in dake saman table d'in wajen ya d'auka ya kunna, da alama shiya ajiye kayansa.

Bayan mun gama duk muka mik'e, kowa ya hau shirin zuwa asibiti duba Abie, time d'in barcin sane shiyyasa ma Momma tasamu tataho, jakadiya kawai aka bari a wajen, itama a waje, da yake in time d'in barcinsa yayi kowa fitowa yake daga d'akin a barsa shi kad'ai.

Galadima saboda aikin da yakeyi yace muyi gaba shima zai taho.
Momma tace “to matarka ta zauna ta jiraka, mudai mun tafi”.
Kamar zaiyi magana saikuma yayi shiru, cigaba yayi da aikinsa harsuka fice, jinai kamar nace nidai zan bisu kawai. Amma na makaro, dan harma sun fice abinsu.
Ganinai tsayuwa ta isheni, shikuma d'an latsin baice na zauna ba, sai kawai naje na zauna d'ayar kujerar dake kallon tasa, nima na d'ora k'afa d'aya kan d'aya tamkar yanda yayi. nayi gefe da kaina cikin basarwa.
Daina danna System d'in yayi, ya d'ago idanu yana kallona, yayinda yake Murza hannunsa na haggu daya d'ora guywar a hannun kujera hannun yana sama, yinai tamkarma bansan yana kallona ba kwata-kwata.
cije lips d'insa yayi kad'an, ya janye idonsa ya maida ga system d'in, aransa yana mamakin izzar yarinyarnan, tabbas data fito gidan sarauta da anga mulkin tsiya.
Falon shiru babu kowa, tunda kuyangin suka gama hidimarsu duk suka koma 6angarensu dake can baya.
Kusan mintuna 40 yagama abinda yakeyi, laptop d'in ya kashe sannan ya mik'e, batare da ya kalleni ba yace “muje”.
Saida na d'an ja wasu seconds sannan na mik'e, saidama ya juyo ya kalleni, dan har yakai k'ofar fita.
Gyalena na maida saman kai nabiyo bayansa, a k'ofa na iskeshi tsaye, na fito shikuma ya daddana wasu madannai agefen k'ofar, Ashe wai security yasaka.
Ranar farko danaga yayi tuk'i da kansa, dogarin dasuke gate suka bud'e mana muka fice.
Tunda muka tafi ba Wanda yayma wani magana, shi yanata deriving d'insa nikam ina kalle-kalle abuna, mun Isa katafaren asibiti mai k'yawun gaske, inma badan sunanba da saika d'auka wani wajen shak'atawa ne, asibitin ya had'u gaskiya, har ciki muka shiga bayan security sun mana 'yan tambayoyi dakuma gaisawa da sukayi, naga alamar sun sanshi sosai, amma duk da haka saida akai searching d'inmu.
Abin ya birgeni gaskiya, inda aka tanada domin parking ya tsaya, ya kashe motar sannan muka fito kusan a atare, bai tafiba saida na zagayo, muka jera zuwa ciki, yanata gaisuwa da jama'a, ina mamakin yanda ya iya yarurrukansu, nikam dai saidai da turanci nake gaishesu, kuma ba kowaba.
Mun fara zuwa office d'in wani doctor, suka d'an tattauna akan cigaban da aka samu na jikin Abie, mun gaisa dashi yaymana murnar aure, murmushi kawai nayi, sai Galadima ne ya amsa masa.
Daga nan muka shiga d'akin da Abie yake jiyya, iyalansa su aunty Mimi duk suna zagaye dashi, nidai a raina danaga d'akin nace oni kamar ba Asibitiba?.
Tunda muka shigo fuskar dattijon dake kwance a gadon ta fad'ad'a da murmushi, kallo d'aya namasa naga kamanninsa dana hoton d'akin Galadima na Nigeria.
Gabansa muka k'arasa, Galadima ya durk'usa yarik'o hannunsa, nima saina durk'usa ina gaidashi da Hausa.
Momma ce tazo ta kamani na tashi, cikin wani yanayi tace, “d'iyata ai Abban naku baya iya magana kinji”.
Da sauri na kallesa, ya sakarmin murmushi, sai kawai na mayar masa hawaye nabin kumatuna domin tausayi, duk kallona sukeyi sukam, harda Galadima.
Kuma zamewa nayi na durk'usa a gaban gadon, cikin rawar murya nafara jera masa addu'ar samun sauk'i wajen ubangiji. duk suna amsamin da amin.
Murmushi yakasa barin face d'in dattijon, Wanda k'aunata take shigarsa har zuciyarsa, Momma takuma d'agoni a karo na biyu ta rungume tana lallashina.
Galadima ya had'iye hawayen dake Neman zubo masa shima, yafara gaida Abie dake murmushi, da ido ya nuna masani wai ya lallasheni mana.
Sai Galadima yayi murmushin jin kunya yana susar k'eya.
Murmushi Abie yayi sosai, har hakwaransa na bayyana.

Ban ta6a jin tausayin Galadima ba sai yau, dama haka suke cikin tashin hankali? Lallai dan ba'aga dariya a fuskarsa ba ba laifi baneba, nama yabama k'ok'arinsa yanda yake zirga-zirga tsakanin Nigeria da nan d'in.
Ahaka akaita firar dani bana fahimta, danshi Abie da idanu yake maganar.
Bamu baro asibitinba sai dare sosai, a can mukayi salloli dacin abinci.
Mun taho muka baro Momma a can, jakadiya ma ta biyomu, dama Momma kad'ai ke kwana a wajensa, shima ba kullumba, dan wasu ranakun basa bari a kwana dashi, a sati sau uku take kwana a wajensa.


**********

Tunda muka baro asibitin tsohonnan ketamin yawo a zuciya da ruhi, sai cud'awa nake da kwancewa, inason jin labarin masarautar su Galadima gaskiya.

Yanzun ma iza k'eyarmu aunty Mimi tayi muka wuce d'akinsa, muna zuwa bathroom yashiga, kusan mintina 25 saigashi yafito, da Alama wanka yayi, harya sauyo kayan barci aciki, dama da abinsa yashiga.
Nima tashi nayi nashiga da nawa masu kauri a hannu. Wankan nayi da shirin barci, sannan nasako hijjab na fito.
Saman gado na iskeshi yawani barbaje a tsakiya, alamar baya buk'atar wani ya hau.
Na ta6e bakina, a raina nace koma bakayi hakaba ai bazan ta6a had'a makwanci da kaiba, aikin banza kawai, naja tsaki a zuciyata.
Saman sofar d'akin na hau na kwanta, inata tunanin Abie da ma tsalarsa.

Kasa daurewa nayi, na kallesa nace, “ wai miye matsalar Abie (kamar yanda naji suna fad'a)”.
Shiru yamin, harma na zata yayi barci, sai can yacemin “ciwone dai kawai”. daga haka yaja bakinsa yay shiru.
Nima shirin nayi, dan bakuma nida abin fad'a, musamman yanda yabani amsar.
Nidai zan iya cewa barcina na daren ranar rabi da rabine, kewar 'yan uwana da bak'unta, gakuma matsalar babansu Galadima data k'asa Barin zuciyata.
Da asuba narigashi tashima, na fito toilet bayan gama d'aura alwala na iskeshi zaune bakin gado dafe da kai, k'ala bance masaba nad'au abin salla na shinfid'a, tashi yayi ya shiga bayin yana Jan tsaki a zuciyarsa, Shifa wlhy dukya takura, yasaba zamansa shikad'ai a d'akinsa, yanzu duk anzo an cika masa🙄.
Haryaje k'ofar toilet d'in yadawo baya, doguwar riga ya d'auka ya shige, saida yay wanka da brush sannan yayo alwala yafito sanye cikin jallabiya blue.
Turare yad'an fesa sannan ya d'au key d'in mota yafita, Ashe inda yake zuwa sallan can gaban gidanne, kuma daga sallar asuba yake wucewa asibiti ya kar6i Momma tataho gida itakuma, duk ranar weekend haka yakeyi, yanzu kuwa yana cikin hutune.
Da yake ina sallah yafita, banyi zaton yafita kenanba, bayan na idar saina d'an kwanta, maganar d'akin sirrinsa ce taita cin zuciyata, namik'e nafita, saida na lek'a falon k'asa naga babu kowa sannan nadawo, cikin tantama na murd'a k'ofar d'akin, sai naga ta bud'e, banyi zaton hakaba gaskiya, musamman danaji an kira d'akin dana sirri. (bakisan ya manta bane bai rufeba Munaya😆 dan harda security a d'akin).
'Dakin k'aramine bashida wani girma, gaba d'aya bangon d'akin zagaye yake da hotuna, sai Computers guda hud'u da kuje d'aya gabanta akwai deck's babba, wanda duk Computers d'in akansa suke, sai pens da yawa cikin wani d'an Abu, gefe kuma k'aramar loka Ce ta glass cikeda takardu, gakuma tarin wasu takardun kashi-kashi da akayi kamar files a seman decks d'in, matsawa nayi jikin bangon nafara kallon picture's d'in, hotunan mutanene daban-daban, harda wasu manya dana Sani a TV, mafi yawa yayi rubutu a k'asan kowanne photo, bana fahimtar rubutun gaskiya, danhaka nacigaba da kallon picture's d'in kawai, harda na mama Fulani,😂
😱
Kutu melesi hotona fa jama'a a d'akin sirri, naga idi, nakaranta rubuntun k'asan yafi sau goma ban fahimci komaiba, saiwasu lissafi-lissafi kamar mai rubutun Mathematics😫.
Na Muftahu nagani a k'arshe, abinfa ya d'aure minkai, mu kuma ni da amininsa Muftahu miya kawomu d'akin sirri🙆🏻?.
Agogon d'akin na kalla naga 7am tayi, da sauri nafita gudun karya zo ya sameni.
Na rufe k'ofar a hankali nakoma bedroom d'insa, ajiyar zuciyata na sauke ganin bai dawoba.
Zama nayi na zabga tagumi ina tunanin ma'anar wad'ancan pictures d'in dana gani, danma a tsorace nake, ban nutsu tsaf naganiba🤦🏻‍♀.

Ban sauka k'asaba saida 9am tayi agogon k'asar, na iske su Samha suna breakfast, harda Momma, na durk'usa har k'asa na gaidasu itada aunty Mimi, cikeda fara'a suka amsa.
Momma tace “ai nayi zaton barci kike, shiyyasa na hana a tadoki”.
Cikeda kunya nace “a'a na tashi tun d'azun”.
Aunty Mimi ta zaunar dani kusada ita, Sauban ya had'omin komai na breakfast d'in.
Yanzun ma a kunyace naci abincin, kunyata na burge Momma sosai.

Bayan mun kammalane Momma ta kama hannuna muka shiga d'akin ta, a bakin gado ta zaunar dani itama ta zauna, anutse ta kira sunana.
Hakan yasani maida hankalina a kanta nima dan nakula magana mai muhimmanci zamuyi da ita............✍🏼




*_tofa, mi Momma zata fad'ama Munaya kuma?._*🤔








*_Ya ALLAH ka gafartama Iyayenmu😭🙏🏻_*
*_Typing📲_*



*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
_(Home of expert and perfect writer's)_




*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_




*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*



👉🏻2⃣9⃣


...........“Munaya taimakona nakeson kiyi akan mijinki”.
'Dagowa nayi na kalleta cikin tsantsar mamaki, saina sinne kaina alamar jin kunyar ta, nace “Umarni zaki bami Momma, domin ke mahaifiyatace”.
Murmushin jin dad'i tayi kamfin takamo hannuna cikin nata, “Alhmdllh Munaya, nagode da wannan karamci naki, yanzu nakuma aminta Muh'd yasamu irin macen danake musu addu'a shida d'an uwansa, ALLAH yayi miki albarka. nasan dukkanin yanda aurenku ya gudana”.
Gabana yafad'i, a raina nace badai Na yarjejeniyar ba?.......maganarta ta katsemin tunanin.
“Mahaifina Sarki Abdul'fatah shine yasakashi aurenki saboda abinda yafaru daku, Wanda nasan k'addarar Muh'd ce kawai tashigo dake cikin lamarin. Kafin nafara neman alfarmar zan fara baki tarihin masarautar su Muh'd, da dalilin zamanmu wannan k'asar daba tamuba tsawon shekara 24 kenan”.
Kaina na jin jina mata, nace “to Momma”.
Zamanta ta gyara sosai yanda zataji dad'in fad'ar abinda ke a bakinta.


*_MASARAUTAR GAGARA BADAU A WASU SHEKARU DASUKA SHU'DE🤔_*

Masarautar gagara badau masarautace mai d'unbin tarihi, da mulkinta ya gudana hannun sarakuna masu yawa, a hasashen masana masarautar sarakuna a k'ala 51 ne suka mulketa harda Sarki na yanzu, wato *Sarki jalaludden Abubakar*.
Sunan masarautar awani shud'ad'd'en lokaci ba *gagara badau* ake kirantaba.
Tasamo sunan gagara badaune dalilin wani Sarki daya mulki masarautar a zamani mai shud'ewa.
Abaya mulkin masarautar basai ka mutuba yake barin hannunka, a'a, da zarar anyi yak'i kayi sakakin da aka ci masarautar tom dolenefa kayi murabus a nad'a wani kuma. kuma bawai cikin 'ya'yankaba, saidai asamo wani hazik'i a masarautar a nad'ashi sarautar.
Tom alokacin Sarki Hameesu Alasan sai aka kawowa masarautar wani gagarumin hari dayaso girgizata. Sarki Hameesu yanada wani d'a da ake kira da suna *Barde* amma asalin sunansa shine Salisu. lokacin da aka kawo musu harinnan ba'a cikin shiri sukeba, amma haka Salisu barde yay saurin had'a mayak'a suka tunkari wannan runduna, bak'aramin gumurzu akashaba, sojojin masarautar Sarki Hameesu duk sun salwanta, amma hakan bai tsorata Salisu ba, yacigaba da bata kashi shida wasu 'yan tsirarun mayak'a, ALLAH mai iko saigasu sunci wannan runduna data kawo musu hari.
Wannan nasara da Salisu yasamuce tasaka babansa Sarki hameesu sauka a kujerarsa aka nad'a salisu. tundaga ranar takoma *_MASARAUTAR GAGARA BADAU_* abin nufi annan salisu barde yazama gagara badau.
Bayan Sarki Salisu gagara badau sarakuna kusan goma sunyi mulki kafin Sarki *_ABUBAKAR_* kakansu Muh'd kenan, mahaifin su takawa.
Shima ya gaji sarautarne a hannun mahaifinsa Yusufa.
Rana d'aya aka nad'a Abubakar Sarki shida amininsa d'an sarkin kan karofi yarima Abdul'fatah, mahaifin Abubakar Yusufu abokine ga Sarki idres na ll, dan haka rana d'aya suka yanke shawarar yin murabus suka nad'a 'ya'yansu.
Sannan aka d'aura musu aure kuma a ranar da matan da su Sarki Yusufu & Idres suka za6a musu.

Gimbiya Marawuyya (mama Fulani) d'iyace ga waziri Sama'ila k'anin Sarki idris, a masarautar Idrees kenan, Sarki idres bashida d'iya mace, dan haka ya d'auki mama Fulani d'iyar k'aninsa yabama Abubakar d'an Sarki Yusufu a masarautar gagara badau, shikuma Sarki Yusufu ya d'auki Khadeeja (inno) yabama Abdul'fatah d'an Sarki idres.
To Ashe ita gimbiya Marayuyya (mama fulani) tana masifar son yarima Abdul'fatah ne, kuma yasani, amma ya nuna mata shi dama gimbiya Khadija (inno) k'anwar abokinsa Abubakar yakeso.
Tun daga lokacin gimbiya Marayuyya (mama Fulani) ta tsani Khadija (inno), ko wani Abu yahad'a masarautunsu bata mata magana, sai zagi da habaici.
Sukuma iyaye basusan gimbiya Marayuyya nason yarima Abdul'fatah ba, sukayi wannan had'in aure. (Iyayen mama Fulani ma sunso ta Auri yarima Abdul'fatah d'in domin sarauta ta dawo tasu)
Gidan sarauta idan an shata layi babu mai k'etarashi, dan haka gimbiya Marayuyya da iyayen ta dolen suka hak'ura da auren yarima Abubakar (tunda acanma suna saka ran gadar sarautar) haka aka kawota gagara badau. ita kuma Khadija (inno) aka kaita masarautar su Mama fulani.
Kusan atare duk suka haihu, saidai Khadija (inno) namiji ta Haifa, yayinda Marayuyya (mama Fulani) ta Haifa mace.
Duk da ba masarauta d'aya sukeba hakan yasaka mama Fulani bak'in ciki, dan aganinta inno taje zata gaje musu masarauta, ita kuma bata samu damar gaje tasuba. A haihuwa ta biyu kuma sai inno ta Haifa mace, mama Fulani kuma ta Haifa namiji. Alokacin kuma duk mazajen nasu suka k'ara aure, daga Sarki Abubakar har Sarki Abdul'fatah. kamar atsare haka sukaita kuma aure har suka cika mata hurhud'u.

A masarautar gagara badau Mama Fulani na zuba mulkinta a masarautar, yanda kasan itace sarkin, dayake shi Sarki Abubakar yanada hak'uri da sauk'in kai.
Humm matan Sarki Abubakar duk basu haihuba, sai mama Fulani keta zubo 'ya'ya. Saikuma amaryar Sarki ta uku ta Haifa d'anta namiji, kusan tare da mama Fulani a haihuwa ta hud'u, duk da mama Fulani itace da manyan 'ya'ya mace 1 maza 2 hakan bai hanata shiga tashin hankaliba, saita shiga tsangwamar gimbiya bagobura da aibanta d'anta *Saifudden*, wani lokacin har shegantashi tayi, saida Sarki Abdul'fatah yazo har masarautar ya taka mata birki sannan.
Mama Fulani tasaka sauran matan Sarki Abubakar sun juyama gimbiya bagobura baya gaba d'aya, batada sakewa ko kad'an acikin gidan. Sarki Abubakar yasan komai dake faruwa a gidansa, amma saiyayi tamkar bai ganiba, bakuma Dan mama Fulani tafi k'arfinsa baneba, yadai zuba mata idanu kawai yaga iya gudun ruwanta.
Ahaka yaran suka taso, gimbiya bagobura ma bata sake haihuwa ba, sai mama Fulani ce takuma biyu, mace 1 da autanta namiji Hayatudden.
Saifudden da jalaludden sun tashine tamkar tagwaye, dukda Saifudden ya girmi jalaludden d'in dakusan 1½ kuwa. danma mama Fulani na hana jalaludden sakewa da Saifudden ne. Kokuma Kamaludden da Shamsudeen suyita dukan Saifudden idan sun gansa tareda jalaludden d'in.
Ahaka Saifudden yatashi cikinsu a tsangwame har suka girma suka zama manya.
Saikuma wani Abu tashin hankali ya samu, a time d'in da mama Fulani ke ganin sarauta zata dawo wajen 'ya'yanta sai ubangiji ya nuna mata ikonsa.
Dan kuwa Shamsudeen da kamaludden sai sukayi had'arin jirgi zasuje umara duk suka rasu.
A time d'in a marine kawai ba a saka mama Fulani ba, amma hauka tuburan tafara a masarautar gagara badau. Saida aka had'a da addu'a sannan talafa, saita kullaci gimbiya bagobura, wai ita tama 'ya'yanta asiri suka mutu domin d'anta Saifudden yagaji sarauta.
Gimbiya bagobura zata tada hankalinta Sarki Abubakar yace tama kwantar da hankalinta.
Bayan mutuwar su Kamaludden babu dad'ewa aka had'a auren gimbiya Zakiyya d'iyar Sarki Abdul'fatah da Saifudden aure, shikuma lokacin Jalaludden da Rafi'atu d'iyar wani Sarki.
Aikam sai mama Fulani ta hau bala'i wai munafunci aka shirya. Babu Wanda yabi takanta akasha biki.

Gimbiya Zakiyya da gimbiya Rafi'atu kusan atare suka haihu a time d'in, gimbiya Zakkiya ta Haifa d'iyarta mace, saidai tana haihuwarta ko ganinta batayiba takoma ga ALLAH😭.
Wannan shine silar aurena dana Saifudden.
Dan bayan rasuwar yayata gimbiya Zakiyya da kwana 7 aka d'aura min aure da yarima Saifudden, domin nacigaba da rainon abinda tabari.
Banason Yarima Saifudden, domin ina masa kallon *Mijin yayata* amma banida yanda zanyi, dole na aminta da auren domin yima iyayena biyyaya.
Nasha wahalar zama dashi, saboda shi hankalinsa yana kan yayata ne marigayiya, silar soyayyar danake nunama Habeefa (aunty Mimi) d'iyar da gimbiya Zakiyya tabarine ya siyamin soyayyar yarima Saifudden, a hankali har shak'uwa tafara shiga tsakanina dashi. Soyayar dayakema 'Yar uwata saita dawo kaina.
Sai daifa inashan wahalar mama Fulani, duk da kuwa itad'in (Gwaggona ce) tana amsa sunan k'anwar mahaifina, amma k'iyayyar datakema mahaifiyarmu gimbiya Khadija (inno) saita shafemu, duk da abaya tana ik'irarin son mahaifinmu Sarki Abdul'fatah kuwa. Kamar yanda yayata gimbiya Zakiyya tasha wahalarta a gidan nima hakane, saima tawa taso fin ta 'Yar uwata, bansan dalilintaba, wai Ashe dan ina tsananin kama da inno ne😆.

“Ina fata dai kina fahimtata Munaya” ‘Momma tayi maganar tana kallona dana rabga tagumi inajin cakwakiyar masarauta.
Kaina na jinjina mata cikin damuwa.
Saitayi murmushi tacigaba da fad'in.

Mama Fulani taso d'iayarta ta farko gimbiya Mansura ta auri yayanmu yarima Abubakar, Wanda babanmu Sarki Abdul'fatah yayma amininsa takwara.
To saikuma hakan bata faruba, dan ita tata dabarar itada iyayenta, idan Yayana Yarima Abubakar ya auri gimbiya Mansura sarauta takoma hannunsu kenan, tunda yarima Abubakar shine magajin masarautar mu, kinga ai d'ansa ne zai gajesa kenan, idan tahad'a auren kuwa yazama jikanatane da masarautar nan gaba.
To saikuma tsarin nata bai yuwuba, saima nida yayata mukazo masarautar gagara badau tushen mahaifiyarmu mukayi kane-kane, gashi kowa yana Saran Saifudden shine zai gaji masarautar gagara badau alokacin, tunda manyan 'ya'yan Sarki Abubakar sun rasu, Saifudden kuma shine babba namiji a lokacin.
Shiyyasa takuma d'aukar karantsana ta d'aura mana muda gimbiya bagobura.
Bayan haihuwar Haneefa babu dad'ewa gimbiya bagobura ta rasu, rasuwar data gigita yarima Saifudden kenan da Sarki Abubakar har ma da jama'ar masarautar gagara badau, amma banda mama Fulani da sauran matan Sarki, dansu hakanma dad'i yamusu.
Sanadin rasuwar gimbiya bagobura Sarki Abubakar ya kwanta ciwo, sai yayi murabus yace a d'aura d'ansa Saifudden a madadinsa.
Wannan Abu yama kowa dad'i a masarautar, amma banda mama Fulani dakejin tamkar tamutu dan bak'in ciki.
Saidai batada yanda ta iya, tanaji tana gani yarima Saifudden yazama Sarkin masarautar gagara badau.
Alokacinne kuma akace dole ya k'ara aure, dan Sarki baya zama da mace d'aya, gashi kuma ni ban haihuba har lokacin.
A rana d'aya aka d'aurama Sarki Saifudden aure da mata biyu. Nanfa mama Fulani tashiga jansu ajiki wai dan a kuntatamin, tana kuma koya musu yanda zasu kuntatama shi Kansa Saifudden d'in.
Sarki Saifudden nada shekara 9 a karagar mulki ALLAH yayma Sarki Abubakar rasuwa, mutuwarnan ta girgiza mahaifinmu Sarki Abdul'fatah sosai, dan saida aka had'a masa a addu'a.
Tun daga wannan lokacin masarautar gagara badau takoma hannun mama Fulani, dan sai yanda tace tanaso Sarki Saifudden zaiyi, dayake shi mutumne mai sanyin hali, baya ta6a sa6a mata.
Duk da haka wannan bai ishetaba, hattada yanda za'a gudanar da mulki saita tsara.
Har lokacin amaren Sarki Saifudden babu wacce ta haihu.
Cikin ikon ALLAH sai gani da ciki, babu kitumurmurar daba aima cikinnan nawaba d'anya zube amma ALLAH ya k'addara mijinki *Muhammad Sameer* saiyazo duniya.
Lokacin Dana haihu shekarar haneef 10 cif a duniya.
Muhammad shine jika namiji na farko da aka fara haihuwa a masarautar gagara badau, dan kuwa matar Jalaludden ma mata taketa haihuwa.
Daga nan nima ban sakeba saida Muhammad yacika shekara hud'u, yanda Saifudden yasha tsangwamar mama Fulani haka Muhammad ma yashata tun yana yaro.
Shima Sameer hak'urin mahaifinsa Saifudden ya gado sosai, dan ko abu aka masa saidai yayi kukansa ya goge hawaye, koni bazai sanarmawa ba, saidai in wata baiwa tagani ko Haneefa (aunty Mimi) su sanarnin.


Please Login or Register in order to submit comment