Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanda wani bazai jimu ba”.
_“Ki kwantar da hankalinki Hussaina, har yanzu dai mijinki bai kai ga zuwaba, kuma bayan wannan ko 10 zasu k'ara zuwa saisun barki, dan akwai k'alubale a gabanki kafin kisamu nutsatstsiyar rayuwa._”
“Da mamaki na kallesa, amma saiyak'i bani damar neman k'arin bayanin komai a wajemsa. Bayan na warke nadawo gida kuka saka aka saceni kaida Muftahu, na koma gida mangariba ta rufa a ranar, ashe wai baba mai kanwa yaga sanda na shiga gida a firgice, sai'a washe gari ya aiko a kirani, innarmu da Munubiya sunyi mamakin kiran, dan cayay Hussaina taje, (shi dama baya kiranmu Munubiya da Munaya, sai Hassana da Hussaina). Haka na saka hijjab naje, a yau baiyi wasan daya sabayi da niba, kai tsaye yafara maganarsa”.
_“Hussaina jiya daga ina kika dawo a firgice?”._
“A tsorace na kallesa, dan lallai tsohonnan yafara bani tsoro, dama tun muna yara mukanji ana cewa tsoronsa akeji, saidai bamusan manufar tsoronba, murmushi yayi yana gyara zama da cigaba da gyaran wasu takarsu Dana tarar yanayi, yace___”.
_“karkiji tsoro, nimai taimakonki ne gwargwadon abinda ALLAH yabani ikon sani, dan haka ki fad'amin gaskiya_”.
“dak'yar na iya had'iye yawu, sannan na fad'a masa abinda yafaru tsakanina daku. Murmuahi yay mai matuk'ar sauti, wanda ya bayyana fararen hak'oransa da basu wuce goma sha ba da suka rage, wad'anda a kullum zaka sameshi da ashuwaki yana d'abbak'a sunna, yace___”.
_“Hussaina ni bazance ki amince ko karki aminceba, saidai nabaki dama kije ki duk'ufa rok'on ALLAH, a cikin kwana ki biyu rak ALLAH zai nuna miki mafita da abinda zai zama alkairi a gareki, sannan karki sanarma Hasaanar ki, danna kula bazata amince ba tacikin sauk'i, tashi kije”._
“A wannan ranarma haka baba mai kanwa ya sakani cikin rud'ani, nazo dukna hana kaina nutsuwa da kwanciyar hankali, saidai nabi shawararsa ta mik'a kukana ga Ubangijin al'arshi, dan shine gatana kuma fitilata, a kwana na biyu kuwa saiga dalilin dayasani amincewa da buk'atarka ya faru, na amince maka badan hankali na ya kwantaba. tunda kuma lokacin baba mai kanwa bai kuma min maganar data shafi auren ba, harma na d'auka duk mafarki nayi, har maganar da mukayi d'in dakai. Saida ana gobe d'aurin aurenmu da safe na fita yin wani Abu na gamu da baba mai kanwa, shine yace na biyoshi gida. Mun Isa gida a d'akin zaurensa, yabani wasu abubuwa dabansan mineneba na sha, sannan yabani turare kashi biyu, yace ni 1 Munubiya 1, yace____”
_“Hussaina kimin wata alfarma mana?”._
“A sanyaye nace kabani Umarni akwai baba. Yay murmushi da fad'in___”.
_“ALLAH ya yimiki Albarka Hussaina, ina tausayinki ta wani fannin, ta wani fannin kuma murna nake tayaki, duk abinda nake hasashe a kanki nasan zaki iya, dan kinfi y'ar uwarki wayo, ni dake zamu had'a kaine wajen fidda mahaifinku a sark'ak'iya, su a gangancinsu sun tozarta kune domin tunzura mahaifinku da karyar masa da zuciya, amma basusan Ubangiji mai hikima baneba, yafisu sanin akan abinda su bai basu damar saniba, kiyi hak'uri inata miki magana a cirkud'e, zaki fahimci komai anan gaba kema, alfarmar da zakimin shine dukkan abinda kikaci karo dashi a rayuwar aurenki ki sanar min shi, insha ALLAH Zan miki fashin bak'i gwargwadon abinda na fahimtar nikuma, maganar zaman aurenku da yanda kuka ginashi kuma ya rage naku bayan warwarewar komai, wannan ba hurumina baneba, tashi kije, daga nan dai zamu dinga tayaku da du'ai”._
“Dukda banida tabbacin mijin dazan aura wannan magana tashi tamin nauyi da wahalar fasaara, da y'an gidanku suka kai lefena kuma saina kuma tsintar kaina a rud'ani da firgici, ban kuma fita daga wannan firgicinba har aka kawoni wannan masarautar. Saka pills da Muftahu yayi mana shine k'alubale na farko dana fara cin karo dashi Wanda nake k'yautata zaton baba mai kanwa ya hangomin, hakanne kuma ya sakani tada hankali nace nafasa auren, dan a zatona kun had'a bakine da Muftahu, amma sai maganar tafiya India ta datse dukkan hanzarina, ko kad'an banyi yunk'urin sanarma baba mai kanwa wannan batunba, dan aganina baya cikin abinda shima zaiso Sani. Idan baka mantaba a lokacin da ka kaini sallama gida da kuma gidansu Munubiya ka barni a can?”.
Kansa ya jinjina mata idonsa a lumahe ya jingina da gado, kai kace ba saurarenna yakeba barci yakeyi.
Ajiyar zuciya na sauke, na cigaba da fad'in “Aunty Salamah tazo gidan ta sameni ai, saboda Munubiya ta sanar mata zaka tafi dani, wannan itace damar farko dana samu na rok'onta yimin bincike akan Muftahu da Saleem yaronka na plaza, (abinda yasa Saleem yashiga Layin zargina saboda randa abinnan ya faru bayan fitowarmu shikuma naga ya fito daga tsakanin wasu motoci a firgice, dayake a time d'in bamusan mizai faruba ban kawo komai a rainaba sai washe gari, danayi bincike a kansa saina gane yaronkane na shago kuma amintacce) daga ita har Munubiya a lokacin basusan dalilina nason amin bincikenba, saidaga baya Munubiya ta fiskanci komai, dayake tanada kaifin basira, amma batasan tsakanina da baba mai kanwa ba. mun tafi India nabar Aunty salamah da wannan aikin”.
Knocking k'ofa da akayine ya saka Munaya yin shiru bata cigaba ba, na kalli Galadima da har yanzu idonsa a lumshe, batareda ya bud'eba yabada izinin shigowa, yasan dai bazai wuce Sauban ba.
Samha ce ta shigo, ta risina tana gaidashi, sannan tace, “Aunty Amaturrahman ta tashi itada Abduraheem”.
Yunk'urawa nayi zan mik'e galadima ya katseni ta hanyar fad'in “jeki kawosu”.
Na kallesa da mamaki, yayinda Samha ta fice abinta, “amma yalla6ai darefa yayi, mubari mu k'arasa zuwa gobe mana?”.
“uhm-uhm”. Kawai ya fad'a.
Shiru nayi nakasa cewa uffan, har Samha da Sauban suka shigo d'auke da yaran duka uku, kar6ar Abdurraheem nayi, dan yaron tausayi yake bani saboda rashin kuzarinsa (karku manta har Yanzu Munaya batasan yaron yanada irin ciwon mahaifinsa ba), su kuma Sauran ya kar6esu. Sauban da Samha suka fice sudai suna tunanin wannan zaman nasu, komi suke tattaunawa oho.
Bayan fitarsu a cikin gyale na fara shayar da yaron, Galadima dai baice dani uffanba, sai kallon yaransa kawai yakeyi, na cigaba da fad'in “Abu na biyu dana fara cin karo dashi shine ganin Abie a halin daya tsinci kansa, wannan lamari ya d'aga hankali na, amma a lokacin banida wayar kiran baba mai kanwa na sanar masa, ina tsoron na saka a wayarka kuma ka gano wataran, sai kuma tarihin masarautar nan da Momma ta bani.......”
Cikeda mamaki Galadima ya kalleta, dak'yar ya bud'e baki cikin yamutse fuska yace, “Momma!?”.
Nace, “eh lallai Momma da kanta, dukkan rayuwar dakasha ta gwagwarmaya ta sanar min, tundaga yarinta zuwa girmanka, ta sanarmin hakanne danna lura da abinda ban saniba a masarautar, kar wani yayi amfani dani wajen cutar dakai. Bayan nan babu dad'ewa kabani waya, daga nan nasamu damar sanarma baba mai kanwa sirrinan guda biyu, ciwon Abie da tarinku. shine yabani dukkan addu'oin da maganin daza'a nema arink'ama Abie, kuma Alhmdllh munakan ganin haske. daga nan kuma na cigaba da samun haske game da dukkan Motsin Muftahu, amma kuma babu wani abinda bai daceba ko cin amana tattare dashi, damukaga mun shiga kokwanto saimuka saka Sarkin Mota da Saleem suka sace manashi a randa kaje d'akkomu a airport ni da Sauban lokacin da Abba yay accident ”.
“ya salam! Kina nufin kece?”.
Murmushi na masa, nace, “kwarai nice, hakan shine kawai mafita agareka damu kanmu, dan satar nashi ya zame mana haske, aunty salamah taje masa a amatsayin d'aya daga cikin matan Abie, ta hakanne kuma muka ji sunan Harun a bakinsa. daga nan muka sakama Harun ayar tambaya, su Ameer suka cigaba da bibiyar Harun d'in, kayi hak'uri ka gafarceni da abinda zan fad'a yalla6ai”. ‘nai maganar ina kwantar da Abdurraheem na d'auki Amaturrahman dake cinyarsa, itama na fara shayar da ita.
“ki fad'i komi ke bakinki, na shirya kar6arsa da makamin HAK'URI”.
Murmushi nayi cikin nisawa, “yalla6ai akwai sirrin dabaka saniba Wanda ya banbanta Muftahu da Harun, Muftahu shine masoyinka na gaskiya, Harun kuwa akwai manufar ra6arka tattare dashi, yasan kuma komai game da satar yarannan, akwai dalililai masu yawan gaske dazan iya kare kaina dasu, amma nabaka dama kayi wannan binciken da kanka. Sannan k'arin bayanin dazan maka shine, mak'iyane zagaye dakai, sannan kowanne akwai manufar sa a kanka, abinda yasa suka taru maka da yawa akwai k'iyayyar mahaifanka data dawo kanka a yanzu, wasu saboda tsoron ta6argazar dasuka aikatane basason kayi mulki ka yak'esu, wasu y'ay'ansu sukemawa, wasu iyayensu ne, wasu kuwa kansune, dukkuma akan inhar kahau mulki zaka iya canja komai da hukunta kowane ya sakasu wannan k'iyayyar a gareka, a yanzu dai kanada Avedance guda hud'u zuwa biyar a hannu, na farko sune wad'anda ka kama da yaran nan, yakamata kasan wanene ya saka su kafin kasan dalilin sasun, na biyu Harun, yakamata kasan miyasa yake tad'eka bayan ka yarda dashi Yakuma San airrinka, na Uku shine Saleem, dolene a wannan karon kasan wanene ya sakashi aikin tsaida CCTV cameras a waccan ranar, na hud'u shine SD minene had'insa da mahaifina, na biyar shine Fu'ad wanene ya sakashi kaimu birnin gayu a waccan ranar, sai Malam saminu driver Alhaji balala dan akwai abinda ya Sani tabbas, hakama farhat ku sake bata tsaro sosai, dan mahaifinta zai kawo kansa gareka cikin sauk'i saboda k'aunar dasuke mata, Sauran kuma zuwa nan gaba zan baka haske a kansu, wad'annan dai ka gaggauta sanin abinda suka Sani a cikin kwanaki biyunnan kacal, dan mak'iya bazasu zauna kallonka ba suma, sunacan suna had'a kayan yak'i. zanje na kwanta, saboda yakamata zuwa gobe mu fara shirye-shiryen komawa gida bisa al'adar haihuwar Fari, yau Munubiya tana can ma ita”.
Ido kawai ya tsura min yakasa koda motsi, na d'auki Amaturrahman Na Goya, sannan Abdurrahman da Abdurraheem kuma a hannu nayi ficewata. Sauran bayani na k'ok'arin mahaifiyarsa Momma kuwa bazan fad'a masa yanzuba, sai komai ya lafa, saboda suna tattarene da sirrikan dasuka shafeni wad'anda bazan ta6a yarda ya sansuba................✍🏻



*Kudai k'ara hak'uri dani, nasan a zak'e kuke da sonjin Galadima ya fara caskale, komai a sannu-sannu ne, dama ba tufk'ar keda wahala ba warwarar, babu abinda yakai k'arshen Novel da saka ciwonkai irin k'arshe, musamman ma mai sark'ak'iya, idan kuka cigaba da hak'urin bina kamar yaune komai zai k'are, shiyyasa nakebi daki-daki yanda kuma zaku gamsu cikin sauk'i.*


_lallai Comments naku nasakani nishad'i, musamman addu'oin Ku gareni ni da mahaifina😭, harma nakan Gaza sanin yanda zan nuna muku jin dad'ina, amma ina kallon kowa wlhy, saidai idan bana cikin group d'in kuwa, ALLAH yabar zuminci, ina yinku irin Trillion's d'innan, I love you all wujiga-wujiga wlhy🥰🥰🥰🥰😍😍😍😍😘😘😘😚😅🤝🏻🤝🏻👍🏻🤸🏻‍♀_.






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏼
*_typing📲_*


💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._*


*_♦RAINA KAMA.....!!♦_*
_(Kaga gayya)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*



~Book 2~ 👉🏻3⃣0⃣


................Galadima daskarewa yay a zaune, gaba d'aya magudanar jininsa tana neman Gaza aiki, saboda jininsa a daskare yake, dai-dai da bugun zuciyarsa salon datake bugunta da banne a yanzu, lallai masu kiran mata masu k'arancin *TUNANI* a zahiri sune masu k'arancin tunanin, lallai mata suna suka Tara, akwai mata akwai mata maza, juye-juye yay tayi a gadon ya kasa ta6ukama kansa komai, barci ya k'auracema idonsa, d'aya bayan d'aya Brain nasa ke markad'a maganganun Munaya dalla-dalla, wani murmushi yasaki yayinda yakai hannunsa yana shafo kwantaccen sajensa zuwa gemu, dukkanin bincikensa akan dai-dai yake, saidai rashin tsoron Munaya da kaifin basirarta ya matuk'ar k'ayatar dashi, ya tashi zaune yana jawo laptop ya kunna, saiga su Munaya sun bayyana a itada yara da Samha a kan gado, saidai yanda ya lura ba barci takeba itama, Dan tana d'an girgiza k'afarta daga kwancen. tsayin wasu mintuna ya kashe tareda mik'ewa ya d'auro alwala, abin salla ya shimfid'a ya fara gabatar da nafila kamar yanda ya saba inhar yanada lafiya.


********************

Yau likitocin Abie dasu Momma suna cikin farin ciki, saboda k'afarsa ta dama sun wayi gari tana motsawa, bayan gwaje-gwaje suna tabbatar da canjin da aka kuma samu a dukkan halittun ga66ansa, yau daga shi har Momma harda kuka, tako rungumeshi cikin tsantsar farin ciki da godiyar ALLAH, jakadiya sai fita tayi jiki na rawa.....

Galadima na tsaka da salla kira ya shigo wayarsa, koda ya idar saiya share, har yana masifa a ransa wane ke kiransa a wannan time d'in bayan yasan shi mai iyaline (🤣 kaga mai iyali😜👍🏻).
Ganin dai baza'a barsa yaji da abinda ya damesa ba saiya d'auka a masife da nufin kashewa, kad'an ya rage ya aikata hakan sai yaga Ashe Momma ce, mugun zaro idanu yayi, jikinsa na rawa
yay picking video call d'in, Momma ce ta bayyana tana sharar kwalla, har taune harshe yake wajen fad'in “Momma mike faruwa ne?”.
Ganin ya rikice saita hau dariya da share kwalla tana masa bayani, ta matsa kusada Abie ta had'asu, yaukam dai Galadima harda k'ananun hawaye yayi Dan dad'i, gashi yau yaji muryar Abie d'insa tafito sosai ba laifi. Sunja lokaci suna waya, har kud'in wayar Momma ya k'are sannam suka hak'ura, baibi kiranba yacigaba da mik'a godiyarsa ga ALLAH. ranar dai zumbur akan abin sallah yayisa, sallar asubahi ma a d'aki yayi sannan ya samu ya kwanta, barci mai nauyi kuwa ya kwashesa.


Da shirye-shirye Munaya ta tashi, dukkan abinda zasu buk'ata tagama tanadar musu itada yara, Samha dai tayi tagumi tamkar zatayi kuka.
Bayan anma yara wanka Munaya ma tayi sai ta zauna yin break fast, suna d'an hira jefi-jefi da laraba dake ma y'an uku shiri cikin wasu kayan sanyi masu laushi.
A kullum Munaya kan tsarkake sunan Ubangiji idan ta kalli yaranta, takanyi mamakin anya kuwa daga jikinta suka fito? idan ta tuna a yanda mahaifinsu ya Samar dasu takanyi murmushi da cizar lips (copy copy😜😂).
Duk abinda takeyi laraba na lura da ita, Munaya na birgeta sosai, Dan idan tana wani abun takanyi tunani kodai Munaya jinin sarautace? Dan salonta da takunta tana kamada na mashahuran y'ay'an sarakuna masu aji da Jan aji, cikin hikima irin tasu ta manya tace, “Ranki ya dad'e ko Baban y'an uku yatashi? Naga bakije dubashiba, gashi tun d'azun naga ankawo Karin kumallo, kuma since shima sunkai NASA amma baya falo.
Munaya tad'an Sosa k'eya tana murmushi, tace, “eh iya, ban saniba koya tashi, amma bara na lek'a na ganni”.
“yauwa ko kefa ranki ya dad'e”.
d'aukar k'aramin mayafi tai ta fita, sanye take cikin sket da riga na wani yadi mai kama da boyal Orange color, an masa kwalliyar surfani kad'an da stones da milk . Sai mayafinta siriri ya kasance milk shima, tayi k'yau sosai gashi tasha d'aurin zarah buhari😜.

Tunda ta fito daga bedroom d'inta idon Galadima a kanta, fitowarsa kenan daga wanka sanye da bathrobe da k'aramin towel a hannu yana tsane ruwan kansa zuwa fuska da wuya, daina tsane ruwan yayi yatsaya kallonta ta cikin Computer d'in, harta shigo falonsa, tad'anyi kalle-kalle da lakatar center table d'in falon da d'an yatsa, da alama tana duba ko da dattine, idonsa yad'an lumshe yana lasar lips, yabar gaban Computer d'in zuwa ga mirror, zamansa babu dad'ewa tayi knocking k'ofar tare da sallama, kamar bayaso ya amsa mata, ko kad'an bata wani jisaba, Dan haka ta harari k'ofar sannan ta bud'e ta shigo.
Ko motsi baiyiba daga inda yake, saima cigaba da shafa mansa dayayi, itama batareda ta kallesa ba ta wuce zuwa ga bed d'insa tana fad'in “yalla6ai barka da asuba”.
Yanda tayi wani masifar basar dashi saiya d'an waigo ya kalleta, sa6anin da da yake kallonta ta cikin mirror. Zanin gadon ta cire hankalinta kwance, ta wuce ga wardrobe nashi ta d'akko wani tazo tana k'ok'arin shinfid'awa.
Mik'ewa yay ya tako gareta.
Jinsa akwai nayi a kaina, amma ban lura da sanda yabaro gaban mirror d'inba, k'amshin sabulun dayay wanka dashi da man days shafa duksun addabi hancina, na d'ago gaba d'aya na ina gyara mayafina domin ya rufemin k'irji da k'yau, saboda kayan babu laifi sun kamani, wajen yakuma cika sakamakon shayarwa. Dab dani yake a she, koda na mik'e sainayi kamar zan fad'a masa a jiki, nadai samu nad'an jaa baya ina tunzura baki, taku d'aya yayi yakuma matsoni, na matsa nima, shima ya matso, hardai muka kai k'arshen bango, kad'an ya rage na yandda Prime dake saman drowan gefen gadon, Wanda hoton Y'an uku ne yasa akayi ya ajiyeshi a wajen, na kalla ina gyara masa zama cikin d'an rankwafawa kad'an, hakkane yabama gyalen damar kuma zamewa, batareda na luraba na tsaya sosai, nad'an 6ata fusaka ina fad'in “yalla6ai lafiya kuwa?”.
Luuu yay da idanu saikuma ya bud'e a kaina yana cizar lips, ganin ya tsurama waje d'aya ido a jikina saina kalli wajen, baki na bud'e nakama gyalen zan rufe k'irjina da sauri ina tura baki.
Caraf ya rik'e hannun, zan saka d'ayanma shima ya rik'esa, sosai na had'e fuska idona na tara kwalla, kuma matsoni yayi sosai, ya rankwafo da kansa saitin k'irjina, rufe idona nayi ina k'ank'amesu sosai saboda tsoron mizaiyine haka?.........
Bankai k'arshen tunanina ba naji saukar iska a wajen, a hankali na bud'e idona, sainaga Ashe gyalen yake hurawa da iskar bakinsa danya bud'e sosai, kunya ta kamani, dan rabin k'irjin duk abid'e yake, wuyan rigar ya cika girma.
Wata muguwar girgiza nayi, had'eda shock a lokaci d'aya, saboda saukar nutsatstsiyar Sumbata danaji a wajen, babu shiri na maida idona na lumshe ina sauke ajiyar zuciya cikin shashsheka da nima bansan nayiba.
Hakan ba k'aramin yamutsa jinin Galadima yayiba, ya d'ago yana matsoni jikinsa sosai da maida hannuna duka baya ya rik'e da hannu d'aya, na manne da jikinsa sosai. K'asa nayi da kaina saboda wata matsananciyar kunya data ratsani da mamakinsa, murmushi ya saki, Wanda tundaga zuciyarsa ya taho, Dan naji alamar hakan ta k'irjinsa, ya wani kuma maida muryarsa very slowly cikeda k'asaita yace, “yalla6iya dama kinada lafiya haka?”.
Bansan na d'ago kai da idoba na kallesa, baki bud'e nace, “kamarya? Dama nace maka banida lafiya ne? ni kabarni nayi aikina inada abunyi”. ta k'are maganar da kauda kai gefe tana tura baki.
Gira d'aya ya d'age sama, cikin ta6e baki yasa yatsu biyu ya maido fuskata Inda take, yace, “kin tabbatar kinada lafiya?”. Yay maganar yana d'aura yatsansa kan la66ana da zagayasu a hankali.
Yanzunma tilas na lumshe ido, jikina harya fara tauma, zuciyata kam sai fat-fat take tamkar zata faso k'irji ta fito.
Gangaro da yatsansa yafarayi daga saman bakina zuwa wuyana har yazo k'irijina.
Bansan nafara kamo addu'a inayiba azuciyata, gashi na kasa bud'e idanu, muryata na rawa nace, “please yalla6ai k...ka...kabari”.. Uffan bai ceba, idonsa akan fuskarta yana murmushi da taunar lips, kuma bai bar abinda yakeba har saida ya dire saitin da zuciyata take, yace “ita wannan miyasata fargaba?”.
Bud'e ido nayi a hankali dan naga miyake nufi? Na kallesa, ya nunamin k'irjina da ido, a d'arare na kalla inda yatsan nasa yake, na had'iye wani yawu dak'yar ina fad'in “babu komaifa, kaga yara zasu iya kuka ina nan fa”.
“Uhmyim” yafad'a yana d'auke yatsansa daga saman k'irjina yana maidawa kan k'uguna, ya tura hannunsa cikin rigata cikeda wani salo, hannuna nafara yunk'urin kwacewa, saiya tsaya kawai yana kallona, saida nayi harna jigata kafin yayi wani munafikin murmushi, ya matso da k'uguna da k'arfi ya had'e da jikinsa, saida naji zafi na yamutsa fuska da cewa “Uhchhh! Yalla6ai ciwo”.
“Da gaske?”. ‘yay maganar cikin matso da fuskarsa dab da tawa tamkar zai had'e bakinmu, idonsa cikin nawa yace, “kinsan mizan baki?”.
Kaina Na girgiza masa kamar wata sokuwa.
Hannunsa Yakuma turawa cikin rigata har zuwa gadon bayana, a hankali yace, “k'yauta”.
“K'yauta kuma? Tami to?”.
K'ala baice daniba ya juyani ta hanyar murza k'uguna ya maidani saitin gadon yana lankwasani a hankali, yayinda shikuma yake biyoni idonsa kan lips d'ina danake motsawa amma maganar ta gaza fita.
Muna gab da kaiwa gadon ya saki hannayena ya tallafe bayana da hannunsa, d'ayan kuma yana rik'e da k'uguna har yanzun, ahaka muka fad'a saman gadon, saidai bai sakemin nauyinsaba sosai, koda ya fad'o jikina banji zafi mai tsananiba, yay min runfa da faffad'an k'irjinsa yana matso da face nashi daf da tawa. cikin wata iriyar murya mai sanyi da k'asaita yace, “bud'e ido ki gani”.
Ban musaba na bud'esu, sai cikin mayun nasa da har yau launinsu yakeda sirkin jaa, duk yanda naso fiddawa na kasa, dan ya hanani wannan damar, saima wasu abubuwa danaga tamkar yana zubawa cikin idona, batareda na fargaba na shagala nima nabar yunk'urin janye nawa. Munkai tsawon mintuna a haka, saida ya tabbatar nagama zuwa hannunsa sannan ya d'ora tattausan lips d'insa akan nawa ya fara sarrafasu cikin tsantsar nuna yana tare da kewa da bege.
Ni munaya naga ta kaina, bansan ya akayi galadima yaci galabar samun kainaba, lallai shid'in yanada wani baiwar iya sarrafa mace a yanda yaso, ya mantar dake wacece ke balle daga ina kika fito, yakan basar tamkarma baisan micece wata soyayya ba, duk kuma randa kikazo hannunsa zaki tabbatar yacika namiji, Dan asalin jinin Malam bahaushen Na yawo ajikinsa, dukda kasancewar wayayye kuma bai girma cikin k'abilarsa ba, yakan maida hankali a harkokinsa, randa kuma soyayyar ta motso yabata muhimmanci Na ban mamaki (Matan hausawa konayi k'ayya ba hakan mazan hausawa sukeba😂?) (Shiyyasa Muke cewa basu iya soyayya ba🤭🤣⛹🏻‍♀).
Sosai na shiga bashi dukkan goyon baya harda saka hannayena na zagaye bayansa dasu...........


😨yaukuma su Oga Galadima an tina da sadaki😌🤭😂.

Tafiya tafara nisan da naji yana neman sakin layi, a kasalance na rik'e hannunsa dake yawo a jikina, sannan na fara k'ok'arin janye fuskata daya koma bama kisses tako ina, sai gwama numfaahi yake yana sakin tagwayen ajiyar zuciya. ganin bazai bariba nasakar masa siririn kuka, ina fad'in, “yalla6ai jegofa m....mu...mukeyi”.
Sai a lokacinne ya tsaya cak,

Please Login or Register in order to submit comment