Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kotu, Wanda dama shi tuni yana ganin duk abinda sukeyi, sunedai basa ganinsa.
Galadima dake zaune a falon gidan da yake tsare dasu harun ya mik'e tsaye domin girmamawa ga alk'ali, sannan ya gabatar da sunansa kamar haka, “ya mai shari'a sunana Muhammad Sameer Saifuddin Abubakar, ma'aikaci a hukumar bincike ta DSS”.
Wani sabon kallon kallon aka koma, Wanda yaja hankalin mutane fiyema dana d'azun, hattada y'an masarautar gagara badau basusan da wannan aiki Na Galadima ba.

Alk'ali ya kuma tsawatarwa, sannan ya maida hankalinsa ga Galadima yana fad'in “To Muhammad Sameer minene alak'arka da iyayen yaran dakake rik'e dasu, danmu ka rikita mana tunani, da farko kallon Criminal muke maka, saikuma gashi sunanka yafito a d'aya daga cikin manyan hukumominmu Na tsaro masu muhimmanci?”.
Murmushi Galadima yayi yana gyara tsayuwa, ya hard'e hannayensa a k'irji yana sauke numfashi da cije lips, yace, “ya mai shari'a wannan labarine mai tsawo, amma tabbas abinda lauyana ya fad'a shine gaskiyar zance, Camera dake hannun Alhaji Auwal Fharuk itace babbar alak'ar dake tsakanina dasu, wadda nad'au tsawon shekaru akan nemanta, sai a shekararnan ne cikin watanni shida nasamu labarin inda take dukda banida tabbacin ita d'ince, bansan mike cikin camera d'inba, amma su Alhaji Balala duk sun Sani, tunda har suka iya salwantar da rayuka da yawa akanta, shi kansa Wanda suka hara a yanzu ALLAH ne kawai yasaka yanada tsawon rai, amma da tuni sun kasheshin, ni kaina rayuwata tasha hare-hare iri-iri harda jariran yarana da aka sace kwanaki 7 kacal da zuwansu duniya”.
Alk'ali da yay shiru yana sauraren Galadima yaja dogon numfashi yana ta faman jinjina kai tamkar k'adangare yaga abinci mai manja😱🤭.
Yace, “lallai wannan Court tana buk'atar jin cikakken bayani daga Muhammad Sameer Saifuddin, dan haka ta d'aga wannan k'ara zuwa nan da kwanaki uku masu zuwa, kotu tana bama y'an sanda Umarnin subar Muhammad Sameer Saifuddin ya fito daga wannan gida a ranar da Court zatayi zama Na gaba batare da koda masa hararaba, sannan kuma kotu ta bada Umarnin a cigaba da tsare su wad'annan mutane guda 11, likitoci kuma su cigaba da bama Alhaji Auwal Fharuk kulawa ta musamman dan shima kotu Na buk'atar ganinsa a zama Na gaba saboda son sanin mike cikin camera d'in”. Alk'ali ya buga gudumarsa yana mik'ewa.
Gaba d'aya kowa ya mik'e har alk'ali ya shige.

Galadima yay wani k'asaitaccen murmushi yana zaunawa cikin kujera bayan shigewar alk'ali.
Muftahu, Nuren, dasu Harun dake zaune gefe suma suna kallon komai tun farkon Shari'ar duk sunyi mutuwar zaune tun lokacin da Galadima yafad'i kasancewarsa cikin hukumar C.I.D.
Ameer ne kawai yay murmushi yana k'amewa da salute d'in Galadima.
Shima baki sake su Nuren suka bishi da kallo suna nunashi alamar dama yasani shi?.
Murmushi yay musu har hak'oransa Na bayyana ya had'e hannayensa waje d'aya alamar tuba a garesu.


★.....................................★


Yau kam Galadima wani farin ciki Na musamman ya tsinci kansa a ciki, ya shige d'akin da yake matsayin nasa a yanzu ya fad'a gadon yana rungume filo idonsa Na zirar da hawaye, ko a haka aka tsaya lallai yaci nasara, dan ya nunama su Alhaji Abdul-Naseer d'an zaki ya girma.
Wayarsa dake saman gadon a can gefe yasa hannu ya janyo, ya kunnata, massages ne sukaita shigowa a jere-jere kamar jira, bai bud'e ko wanneba ya shiga binciko number Munaya, ya dad'e yana kallon Number amma ya kasa dialing, yaja wasu seconds kafin yatsansa ya sauka akan number ya danna kawai.

Munaya Na zaune a falo tare da su Ayusher da kullum sai sunzo, d'an kunne ne ya shige cikin jikin Amaturrahman yanata cin jikinta basu saniba, sai yau da an ta6a fuskarta koyaya saita fashe da kuka, Munaya tarasa mike damun yarinya, dukta rikice ita kanta, saida laraba tace ta bata nono, tana kwantar da ita ta wajen kunnen sai takuma d'ad'ewa da kukan da Munaya ke jinsa har cikin jini, d'agota tayi tana duba wajen, Laraba tace, “Anya ba kunenta ke ciwoba?”.
Munubiya dake kusada Munaya ta amshi Amaturrahman ta kifata a cinyarta tana dubawa, sai taga d'an kunne ne ya shige Ashe duk bayan kunnen yayi ruwa, tsoro ya kama Munubiya, cikin zaro ido waje tace, “innalillahi, d'an kunne natacin kunen yarinya bamu saniba”. Da an fara k'ok'arin ciremata saita kuma fashewa da kuka tana mimmik'ewa, gwaggo safiya data shigo yanzu saboda jiya ta iso akan abinda ya faru da Abba, ta k'araso cikin falon tana fad'in “mike faruwane?”.
Bayani feena tai mata, gwaggo safiyya ta kar6i Amaturrahman tana cewar asamo mata ruwan d'umi da k'aramin handkerchief.
Ana cikin hakane Galadima yayi kiran Munaya, tashitai tabar wajen tana had'iye kukan dake shirin taho mata saboda tausayin yarinyar.
'Dakinsu ta shiga, ta fad'a saman gadonsu ta kwanta tana amsa wayar.
A hankali Galadima ya sauke ajiyar zuciya yana gyara kwanciya. Murya can k'asan mak'oshi yace, “babu fad'a miya kawo gaba yalla6iya?”.
Murmushi Munaya tayi tana share hawayenta. Tace, “Kodai Kaine za'aima wannan tambayar?”.
Jimm yayi saboda jin muryarta ba ayanda yasaniba. yace, “mike faruwa kike kuka?”.
Mamaki ya kama Munaya, ta Yayama ya gane kukan take, cikin k'ok'arin kare kai tace, “ba kuka nakeba yalla6ai, ina yini”.
bai amsa gaisuwarta ba yace, “kina wasa da sanin danai miki ko?”. Yay maganar cikin d'an kausasa murya.
Munaya sai bataji dad'iba, tace “kayi hak'uri, dama Amaturrahman ce d'an kunne ya shigema a jiki taketa kuka, amma gashi can suna cire mata d'an kunnen”.
Babu shiri Galadima ya tashi zaune yana fad'in “k ya akayi har d'an kunne ya ringa cin jikinta baki saniba? Anya kuwa kinason yarannan Munaya?”.
Wani haushine ya kamata, tama rasa mizata Ce masa.
Shima bai jira amsartaba yace, “maza ki tashi kuje asibiti a dubamin yarinya, karkuce zakuyi gangancin cire mata a gida wata matsalar ta biyo baya”.
“Uhumm”. Kawai Munaya tace ta yanke wayar.
Ta jefar da wayar gefe tana hawaye, shi kawai yaransane damuwarsa, harma zaice yafita sonsune dazai dinga jifanta da bata sonsu kulum-kullum, itafa wannan Abu yafara kaita bango wlhy.

A can kuwa shima Galadima duk sai yaji ya damu, jiyake tamkar yay tsuntsuwa yafita yakai yarinyarsa asibiti da kansa, amma babu damar hakan.
Ya dad'e jikin window tsaye yana kallon mutane daketa zirga-zirga a anguwa da police d'in dake zagaye da gidan har yanzu.

Fita munaya tayi dan ganin ko ancire?, ta iske an cire ana gasa kunnen, Amaturrahman taci kuka harta koma ajiyar zuciya, Gwaggo Safiyya tace, “zoki zauna kibata tasha sai'a k'arasa gasawar”.
Zuwa Munaya tayi ta zauna tana kar6ar Amaturrahman.
K'in k'ar6ar nono tayi, sai ajiyar zuciya taketayi, Laraba tace, “yaranan zuciya irinta Magajin gari suke da ita, yanzu inba sa'a ba bazatashaba”.
Dariya su Ayusher sukayi.
Dak'yar dai Munaya ta turama Amaturrahman nono abaki ta kar6a. Akad'an kuma gasa kunnen dayay uwar huda naman wajen yafita sosai, k'ofar tazama babba.
Munaya dake kallonta tasaka hannu tana goge mata zufar data taru mata a goshi, saikace wata babba.

Galadima yanata kiran Munaya yaji kosun tafi asibitin amma bata d'agaba, dayake ta bar wayar a d'akinsu.
Saida Ayusher taje d'akin ta gano, ta d'akko da sauri ta kawo mata tana saka mata a kunne.
Maganarsa kawai munaya taji yana fad'an ina ta ajiye wayar.
Ajiyar zuciya ta sauke tabashi hak'uri kawai, dan bata buk'atar jan maganar.
Yace, “kunje asibitin?”.
Munaya tace, “An cire mata ai, babu wata matsala tunda bai ta6a cikiba”.
Ca yay ta d'auka hoton wajen ta turo masa yagani, kamar tace bazatayiba sai kawai ta cire wayar ta katse kiran, hoton wajen ta d'auka ta tura masa”.

Tausayin yarinya ya kamashi ganin yanda wajen yay cinye sosai, Yakuma kiran Munaya yana jaddada mata karta sake akuma sakamata wani d'an kunne.
To kawai ta amsa masa dashi dan a zauna lafiya.



..............................★


Tun daga ranar Munaya bata sake jin Galadima ba, saboda yayi busy da yawa akan shirye-shiryen shari'ar dake gabansu, dan fatanshi wannan zaman yazama zama Na k'arshe insha ALLAH.


Alhmdllh jikin Abba anata samun haske sosai, dan sauk'i yana samuwa iya gwargwadon iko.

RANAR DA ZA'A KOMA KOTU................✍🏻




Hummm😬

ALLAH ya gafartama iyayenmu😭👏🏻

BOOK 3 👉🏻1⃣8⃣


.................Yauma dai kotun ba'a cewa komai, wad'anda ma basuzo zaman farkoba yau sunzo, Dan su sir Isa duk suna wajen da muk'arabansa, hakama tawagarsu Tanderu, Dan suma lauyansu a cewarsa yau yazo da sabon shiri, ranarma an mamesa ne kawai.

Galadima yagama shirinsa tsaf cikin wani lallausan yadi sky blue dayasha d'inkin boda, Dan rigar iyakarta Rabin cinyarsa, kayan sunmasa k'yau matuk'a, danya fito ainahinsa Na jinin Hausa Fulani, ya Mirza hularsa sky blue itama, fuskarnan tayi fayau Dan hardasu gyaran fuska yayi abinsa, danma ya tabbatarma mak'iya yana cikin farinciki fiye da zatonsu, yana cikin saka sock's Nuren ya lek'o yana fad'in “Brother ka hanzartafa mun makara”.
“umhum” kawai yace masa yacigaba da saka kayansa a tsanake kamar yanda yafara, danshi komai saurin dazaiyi akan Abu to anutse zaiyi abinnan, ganin haka sai kawai Nuren ya ida shigowa, ya durk'usa gabansa yana kama k'afar daya sakama sock's d'in ya saka masa takalmi.
Baki Galadima ya tsa6e yana cewa, “kaifa shegen gaggawane dakai wlhy, ni bansan INA kuka kwaso halinnanba, haka Momma da Aunty Mimi suke, komai kunfison mutum yanayi kamar wani mazari”.
Nuren ya sanya dariya yana saka masa d'aya takalmin, yace, “to sokake muke Abu kamar marasa laka a jiki? Munaya dai kam tana fama...”
Hararsa yayi, hakanne ya hana Nuren k'arasawa, Galadima daya wani tsaresa da ido yace, “Tana fama da k'aniyarka”.
Nuren ya mik'e yana fad'in “oho maka dai, mu ka fito su sarkin mota tuni sukazo”.
Mik'ewa yay ya d'auki turarensa Na kullum a bag d'in daya had'o kaya ya fesa, k'amshin ya gauraye ko ina, waya d'aya ya zura a aljihu ya fito.
Su Ahakam duk shagala sukayi da kallonsa, a ransu suna matuk'ar yaba tsarinsa, komai nasa abin birgewane, kamar yanda ya saba haka yabasu hannu da kansa sukayi musabaha dukda suna nok'ewa alamar jin kunya da girmamawa a gareshi, shikam babu ruwansa, inhar bakasan halinsa bane dolene tashin farko ka jefeshi da kalmar girman kai.
Su Farhat ma suka gaisheshi cikin risinawa, wani miskilin murmushi yamusu yana d'aga musu hannu kawai, ya kalli Saleem tare da masa nuni yabama kowa kayansa.
Saleem ya amsa da cewar “ok boss”.
Bag d'in da wayoyinsu ke ciki ya d'akko, amma sai sukace sukam ya barsu, Dan inhar ba'a yanke hukunci ba zasu dawo su cigaba da zama dasu, Dan zama da Galadima akwai dad'i, kuma ko an yanke hukuncima masarauta zasu bishi.
Shi dariyama abin ya bashi, hakanne yasakashi bubbuga kafad'ar Yassar dake kusa dashi yana sakin murmushin da har hakwaransa ke bayyana, ya wucesu yana sauka daga benen cikin takunsa Na birgewa.
Suma duk binsa sukayi a baya, komai nasa Saleem ya tattaroshi, dan bazai sake dawowa gidanba koda ba'a yanke hukunci ba kuwa.
Harun dai anyi laushi matuk'a, dan maganarma yanzu ba iyayin mai k'arfi yakeba, saboda saiya gadama yakecin abinci, babu kuma mai sakashi dole yaci.
Cikar k'ofar gidan tabama Galadima mamaki matuk'a, yakuma d'aure fuska tamkar bai ta6a dariya ba, musamman yanda duk aka zubo masa ido, a Bayama an kallesa balle yanzu da yayi abun kallon, y'an sanda da dogaransa da suka zo d'aukarsa tun d'azun sai k'ok'arin hana y'an jarida dakeson zuwa ga Galadima sukeyi, amma suna k'ok'arin kutsowa.
Tsaye Galadima yayi ya zuba dukkan hannayensa a aljihu, saida yaga shigarsu Rahma mota dasu alhaji darma sannan yanufi inda sarkin mota ya bud'e masa, y'an jaridar daketa masa tambaya ko kallo basu isheshiba ya shige mota abinsa, yayinda Muftahu ya zauna gefensa, Nuren Na a gaba.
Mortar y'an sanda Na a gabansu da Bayansu, a haka akayi tafiyar.
Sauran y'an sandan da aka bari suka shiga gidan domin d'akko gawar Ahmad, amma sun bincika lungu da sak'o babuma alamar an cutar da wani, sai harbi guda d'aya daya shiga jikin bango, (shima Wanda Galadima yayine sanda ya tsoratasu da cewar ya kashe Ahmad), basu samu komaiba dazai nuna Galadima d'an ta'addane, sai suka fito suna kulle gidan, amma basu tafiba harsai kotu tabada damar hakan.


............................★

Sun Isa Court d'in, inda Galadima da Nuren da Muftahu ne kawai suka Shiga, yaran dasu Alhaji Darma an kaisu wani d'akine kusada wajen.

Takun takalman Galadima dake tafiya cikin tsantsar izza da nuna jinin mulki ya saka dukkan jama'ar kotun zuba masa idanu, shikam ya had'e fuska tamkar hadarin gabas Na tsakkiyar ogusta dabaya d'aga k'afar zubar ruwa, kallon kowa bayayi, gashi ya toshe idanu da Google eyeglasses d'insa da babu mai kallon kwayar idonsa.
A kujerar farko irin wadda su Alhaji Mamman ke zaune shima aka nuna masa shida Nuren da Muftahu.
Wani zama yayi dake tabbatarma da mak'iya shid'infa sarakine, gaba da baya kuma.
Hakan ya k'ona zuciyar su Alhaji balala matuk'a, amma babu yanda zasuyi.

Zaman Galadima babu jimawa saiga alk'ali ya fito, kowa ya mik'e domin girmamawa, saida ya zauna sannan duk aka zauna.
Kotun tayi shiru kowa ya zubama alk'ali idanu, yagama dube-duben ta kardun gabansa sannan ya d'ago ido yana kallon jama'a, yace, “Yau shari'ar zata tafine kai tsaye batare da shigar lauyoyi Na kowanne 6angare a tsakiyaba, Dan haka muna buk'atar Wanda yay k'ara, da wad'anda ake k'ara a gaban kotu”.
A hargitse su alhaji Sageer suke kallon kallo, hakama lauyansu dukya shiga rud'ani, saboda mugun shirin dayayo yau akumace ba haka za'ayiba.
Shikam Galadima wani mugun murmushi yayi yana kallonsu Alhaji mansur d'in damusu wata inkiya da yatsu biyu alamar a kafta, sannan ya mik'e.
Dole suma duk suka mik'e inda aka buk'aci ganinsu, dukda wajen yamusu kad'anma.

Alk'ali ya kalli galadima. Yace, “kaine Wanda kai k'ara, Dan haka munason jin shin minene mafarin wannan takun sak'a kai tsaye?”.
Murmushi galadima yayi, ya cire eyeglasses d'in idonsa ya saka cikin aljihu, tareda zaro handkerchief ya goge fuskarsa, yasa hannayensa biyu ya dafe katakon gabansa yana jifan waziri mahaifin Harun dawani mugun kallon daya hargitsa y'an cikinsa da tunaninsa, hakanne yasaka mutane kallon waziri suma, duk sai yaji ya muzanta.
Galadima ya ta6e baki yana janye idonsa dad'an cije lips, cikin k'asaitacciyar muryarsa yace, “ya mai shari'a labarina mai tsawone kwarai da gaske, sannan cike yake da abubuwan ban mamaki da takaici masu tarin hargitsi, duk da nasan kowa yasan sunana amma zan sake maimaitawa, sunana Muhammad Sameer Saifuddin Abubakar, gidan sarauta Na fito, mahaifina shine tsohon Sarki da k'addarar ciwo ta kwantar tsawon wasu shekaru, amma lallai da sanadi, wannan kuma sanadin shine Na d'auki tsawon shekaru tundaga tasowata har zuwa yau ina nema. tun daga lokacin dana mallaki hankalin kaina nasan minene matsalar mahaifina natashi da burin d'aukar fansa, sai dai kuma tayaya? Wannan shine yayta wahalar da Muhammad Sameer a tsawon shekaru”. Galadima ya k'are maganar idonsa Na ciko da hawaye, yay murmushin takaici yana jinjina kansa da had'iye hawayen.
Hakanne yasaka jikin wasu fara yin sanyi, musamman wad'anda suka k'ullaceshi da farko.
Galadima ya cigaba da fad'in, “Ban taso maraya ba, amma nayi rayuwa irinta marayun, ALLAH shine gatana saikuma mahaifiyata da kakana da suka tsaya tsayin daka wajen tsayamin nazama jarumi wajen sanin wahalhalun rayuwa Na yau da kullum, duk Sana'a mai wahala kad'ance banyitaba a k'asar daba tawaba, gakuma gefe ana gwagwarmayar Neman ilimi, ga burin son sanin suwaye suka durk'usarmin da mahaifi?, ban cutar da kaina wajen nutsuwa Na fahimci rayuwa ba, hakama nabama karatuna muhimmanci saboda k'aunarsa da nakeyi, duk da banida burin yin aiki a k'ark'ashin kowa, Alhamdllh yanzu haka inada Company Na had'aka da duk shekarar duniya yake fidda wayoyin Hannu da computers dakan zagaya cikin duniya, ina alfahar da samun cikar burina sosai, Na dad'e ina bulayin Neman hanyar bincike akan abinda yafaru da Abie na, alokacin mutum d'ayane zuwa biyu ke bani gudun mawa, wato lauyan mahaifina, baffina Barrister Usman Audu, sai kakana Sarki Abdul-fatah. Ganin inata wahala sanan babu wani haske a cikin lamarin sai suka bani shawarar mizai hana a nemamin aiki k'ark'ashin wata hukumar tsaro, da farko ban aminceba, Dan irin wad'annan ayyukan basa wani birgeni, hasalima haushin masu yinsa nakeyi, Dan sun gaza binciko Wanda ya cutarmin da Abie na. A tashin farko dana nuna banaso Papi da Baffi sun k'yaleni, basu sake min magana ba, sai wata rana kwatsam wani Abu yafaru anan Nigeria, wasu y'an ta'adda sukayi mummunar 6arna a sirrin gwamnati, k'ark'ashin hukumar DSS. wannan 6arna ta rikita Nigeria sosai a lokacin, shekaru 10 kenan inhar ban mantaba, a lokacin nagama bautar k'asata anan Nigeria ina shirin komawa india, bansan ya akayi sukasan nasan Computer ba, har masarauta akazo aka rok'i mai martaba akan Na taimakesu. Da farko kam naso bijirewa amma babu abinda iyayena zasuce nayishi banyiba inhar bai sa6a shari'a ba, nasanma bazasu sakani wannanba, bisa umarnin mai martaba Na amince da gwadawa idan zan iya, haka akaje dani headquarters d'insu, tun hawan Computers d'in danai a tashin farko Na gane da had'in kan waaunsu aka kwashi bayanan, sannan masu kula da Computers d'in sunada buk'atar k'arin ilimi ma gaba d'aya. Cikin sauk'i Na d'akko bayanan da aka d'auka Na dawo musu dashi, sannan nasaka musu securitys masu tsaurin gaske daba wani mahaluki dazai kuma musu irin wannan kutsen. Ni ban d'auki abinda nayi matsayin komaiba, amma agaresu sun girmamashi, sunkuma biyoni har gida da rok'on kasancewa a cikinsu amma nak'i Sam, nama tattara Na koma India, Ashe sunata bibiyata ta wajen kakana, to shima dama yana burin nayi aikin, Dan haka yabasu goyon baya, sannan yaje har India ya sameni da batun, ya nunamin ta wannan hanyarne kawai zan iya binciko abinda ya faru da mahaifina cikin sauk'i, hakama Baffi ya fad'amin a lokacin, Na zauna nayi nazari dakuma samun kwarin gwiwa daga Mahaifiyata. Rana d'aya sai nima naji yakamata Na amince, Dan haka Na amince, tundaga lokacin nashiga cikin hukumar CID nima, saidai ina musu aikine cikin sirri, a hukumarma ba kowa yasan daniba, tunda ni komai ta computer nake gudanar dashi. Sir Isa Maharazu shine ya taimaka min wajen binciko file Na binciken case d'in mahaifina, Wanda tun kusan shekaru 8 mai kula da case d'in ya rasu, Wanda kuma suke ta fannin y'an sanda suma sukayi shiru, daganan aka ajiye case d'in gefe kawai. Tun a file d'in nafara cin karo da sunayen wasu daga cikinsu Alhaji Lawan tanderu. Nasha mamaki kwarai da gaske amma sai banyi wani yunk'uriba, ina wata shida da aiki wani yaso min kutse a cikin Computer, ta silarsa nagano uban gidansa, har zuwa Kansu Marigayi Alhaji Labaran kachia. Tundagafa wannan lokacin saina tsananta bincike da kwakwalwa dakuma tannin aiki, bisa taimakon sir Isa, mun baza yara cikinsu Tanderu batare da sunsaniba, kullum kuma cikin bin diddigin motsinsu suke. Kwatsam sai Tanderu ya rasu sanadin had'in mota, babu jimawa shima Alhaji Labaran khacia ALLAH yamasa rasuwa sanadin rashin lafiya. daga nan saina d'an dakatama gaba d'aya da wani bincike Na koma gefa Na zuba musu ido kawai.
Saida Na d'auki kusan shekaru biyu ban sake wani yunk'uriba sai kwatsam muka wayi gari mijin Yayata Haneefa yayi had'arin Mota, saidai kuma a ranar ne aka turomin massage daya nuna accident d'in nashi akwai saka hannu a ciki, dayake bai rasuba a lokacin sai a asibiti bayan awanni uku da kaisa, Alhaji shehu Darma abokinsa ne Na kut da k'ut sannan d'an uwansa, Dan haka yana tare damu a wajen, saina matsanta akan tambayarsa kozai fad'amin akan miya faru dashi kafin had'arin? Bai iya cemin komaiba sai murmushin k'arfin hali da yayi yana kallon Alhaji shehu har numfashinsa ya k'are, wannan kallo ya tsayamin a rai sosai, Dan nagaza mantawa dashi, abinda Yakuma k'arfafa min zargin Alhaji shehu shine Aunty Mimi Na fita daga takaba sai Yace yanason aurenta, nine Na hana, nama tattarata gaba d'aya itada y'ay'anta Na maidasu india, dukda dangin mahaifin yaran sunso d'aukarsu suma. Dama can lokaci-lokaci Alhaji shehu yakanbi mijin Aunty Mimi suje duba Abie, dan haka ko bayan rasuwarsa bai daina zuwaba, abinda na fara fahimta shine Samha d'iyar marigayi tana tsoron Alhaji shehu, amma shi yana tsananin nuna mata kulawa dayin kaffa-kaffa da ita a gaban mutane. Wannan ma yasa na kuma saka ido a kansa, abinda Na fara karo dashi shine Alhaji shehu yana tursasa Samha ta hanyar mata barazana akan ta d'akko masa wasu sirrikana”. Galadima ya murmusa cikin takaici yana gyara tsayuwa da goge fuskarsa da handkerchief. Yaciga da fad'in,
“Tunda Na fahimci hakan saina jata a jikina, nakuma dinga ajiye mata dukkan abinda yasaka ta d'akko, itako data gani saita tura masa saboda tsoron barazanar da yake mata. Suma sauran Na cigaba da bibiyarsu suda ayyukansu, so banida matsala da sauran mugayen halayyarsu, nidai kawai wadda ta had'amu nakeson Sani, Dan Na gano sun gana da mahaifina ana gobe abinda ya sameshi zai sameshi, kuma yafito daga d'akin tattaunawar ransa a 6ace. Batanci da akaimin a shekara d'aya data wuce cikin jaridar manuniya shine mafarin yalwatur haske a matsalolina, dukda Na fahimci ankai tsawon shekaru ana bibiyar dukkan al'amurana, kuma inhar Nazo k'asarnan kullum cikin bibiyata ake, domin rufe bakin mak'iyana Na auri wadda sukaso sakawa a matsalar dabatajiba bata ganiba, wadda a yanzu Alhmdllh itace uwar y'ay'ana, nasan hakan ya girgizasu a lokacin kwarai da gaske, adalilin zama da ita nama fahimci abinda ban fahimtaba da farko, Dan da Duk zargina ko da itane aka had'a kai wajen Neman 6atamin suna, amma sainaga dukba haka baneba, ya mai shari'a Alhaji Auwal Fharuk sai shine surikina mahaifin matata, kuma anyi yink'urin kasheshi watanni kusan 7 da suka shige, saidai ALLAH ya k'addara yanada sauran kwanaki a gaba, bisa dalilin yun k'urin kisansa ne kuma Na fara karo da alak'ar case d'in mahaifina dashi, hakan

Please Login or Register in order to submit comment