Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kota gamajin komai, amma sainaji sa6anin haka, da y'ar raharta ma tace, “Muh'd duk hidimar sunance haka?”.
“Uhm Momma bashi bane nice”.
“a'a d'iyata kece?”.
“eh Momma, kuna lafiya? ya jikin Abie?”.
“Alhmdllh d'iyata, ya k'arfin jikinki kema? ina yaran?”.
Gabana ya fad'i, Na had'iye wani yawu da k'yar, cikin in ina nace, “lafiyar kowa k'alau Momma, shima y... yana barcine”.
Dagacan Momma ta murmusa tana gyara zama a harabar asibitin, dan batason Abie yaji wayar da zatayi, tace, “humm d'iyata kema 6oyemin zakiyi kenan? yanzu koda mutuwa yaran sukayi dashi kansa kowama saiya shiga fargabar gayamin?”.
Na had'iye yawu dak'yar, “kiyi hak'uri Momma, ki gafarcemu” https://2gnblog.blogspot.com/.
“Bakumin laifin komaiba ni, hakan da Muh'd yay shine dai-dai, dan lokaci yayi dazai daina zama jiran sak'on mak'iya ko zuwansu, shine yakamata ya fita farautarsu domin kawo k'arshen komai, na yarda dake 100% Munaya, nakumayi imani insha ALLAH kece zaki sauyamin yaro daga k'uncin dayake ciki zuwa farin ciki, tamkar yanda Na fad'a miki tun farko karki ta6ama Muh'd sanya ko nuna tsoronsa, lokacin dazaki kwantar masa dakai kizama kowacce irin mace a agidan mijinta har yanzu baiyiba, kada ciwonsa yasakaki fargabar fad'a masa gaskiya, rayuwa da mutuwa duk Na ALLAH ne, ko ayanzu Muh'd yabar duniya bazanyi bak'in cikiba, domin ya nuna musu shi jarumine, kuma ya haifi wad'anda zasu iya zama magadansa su sauya komai koda ba'aso, nanda kwanaki biyu komai ya gama lafawa ki tabbatar kin masa maganar tafiya wanka gida, wannan shine target d'inmu Na k'arshe akan rayuwar zaman aure na dindin, kowacce irin birkicewa zai miki akan bazaki jeba, kema ki birkice masa, dan nasan abinda yafaru zaisashi dagewa akan yaran bazasuyi nesa dashiba, idan kuma har aka cigaba da tafiya a haka, kowane irin dana Sani zai iya biyo baya”. Momma ta share hawaye dake kwarara a idanunta, taci gaba da fad'in “ALLAH yayi miki albarka Munaya, dake da abinda kika haifa, yanda kikamin biyya wajen k'autata kar6ar Abu mai wahala (duk da bani na haifekiba) kema ALLAH yasa y'ay'anki sumiki biyyaya fiye da wannan, ALLAH yasaka hannu adukkan lamarinki keda mijinki da sauran y'an uwansa, nusar dashi abinda duk baki gamsu dashiba shine zai rage ma zuciyarsa baraza, dan tarawar yagani a lokaci d'aya shine mafi had'ari Munaya, zuciyarsa zata iya bugawa a lokacin, kiyi hak'uri nasan bak'yajin dad'in zama da Muh'd ko kad'an, domin ni kaina mahaifiyarsa wataran gaza gane kansa nakeyi, amma inaji a jikina akwai sauyi maiban mamaki dazai zo ya rusa komai, ki sameshi fiyema da yanda kikeso, ALLAH yayi muku albarka, idan ya tashi ki kirani naji ya jikin nasa”.
Bata jira nayi magana ba ta yanke wayar, da alama kukane yaci k'arfinta. nima saina fashe da kukan ina kallon Galadima, insha ALLAH zan cikama baiwar ALLAHr nan burinta, koda ace mun rabu dashine, dan maganar gaskiya bazan iya rayuwa da mutum murd'ad'd'e mara yarda irin Galadima ba, labarinsa kawai kukeji, amma halinsa saika zuna dashi, Mara hak'uri zai iya gundurarsa ne cikin awanni biyu kawai, dan zaka dinga kallonsa a matsayin mai wulak'anci ko dizgi, girmankai da sauransu. Na sauke ajiyar zuciyarsa ina maida kallona ga Abdurrahman dake motsin tashi, nasan dukansu saisun tashi inhar d'aya ya tashi, saina lalla6a na kwanta kusa dashi na saka masa nono a baki.


********************

Har akayi la'asar Galadima bai farkaba, Nuren yazo shida Sauban, da Saleem har sau biyu suka iske yana barci, hakama Mom da inno da mama Fulani. Gashi su inno 4:30pm zasu wuce ma, laraba tazo tama yaran wanka, dan tuni sun farka, Nima nakumayi sannan naci abinci, kaina ciwo yakemin sosai, dan haka Sauban yafita ya samomin Magani nasha na kwanta, munyi sallama dasu Mom, zasu dawone kawai idan Galadima ya farka kafin su tafi. yaran kam duk d'insu suna can an kaima papi su tun d'azun.
Nidai barci yay awon gaba dani, daga nankuma bansan wainar da aka cigaba da toyawa ba a gidan.


*******************

Bayan la'asar kad'an Galadima ya farka, ganin shi kad'aine a d'akin ya tashi zaune bakinsa d'auke da addu'ar tashi barci, jin k'irjinsa yayi sakayau yasaki babu nauyin kamar d'azun, saidai abinda ba'a rasaba, yatashi zuwa bathroom yay wanka da alwala.
Sallan zuhur da la'asar ya rama, tareda addu'ar neman sauk'i akan wannan lamari da samun k'arfin zuciya, dolene saiyayi yak'i da dukkan abinda zai zama makamin barazana a agaresa inhar da gaske aikin zaiyi, falo ya fito bayan ya kimtsa, zamansa da mintuna baifi 2 ba saigasu inno.
Basu jira isoba suka shigo, a zatonsu yana bedroom yana barci, sunsan Munaya kuma tana d'akinta tana barci tunda daga can suke. ganinsa a zaune ya saka fuskar kowannensu fad'ad'a da murmushi. Shidai kallonsu kawai yake d'ai-d'ai.
Inno ta mangari kansa tana fad'in “ja'iri baka sanmu bane halan?”.
Hannunta ya rik'e yana kallonta, cikin maganarnan tasa ta k'asaita yace, “Inno wai ina zakuje ne?”.
“inda muka fito mana”. Inno tafad'a tana zama kujerar kusa dashi.
“saikace wad'anda ake kora?”.
“A'a wazai koremu nida gidanmu, komawar dai ne yafi cancanta, dan takawa ma yace a gaisheka basai ya shigoba, zakuyi waya, idan ka murmure kaje yana nemanka”.
“To shikenan ALLAH ya tsare hanya, mun gode sosai da sosai”.
“Amin” inno tafad'a tana shafa kansa ta ciga da kwararo masa addu'oi shida matarsa da yaransu, falon kowa tana amsawa da amin, itama mom tayi nata.
Yace, “mom hada ke wai?”.
“eh mana Sameer, zaman mi zanyi to? tunda ALLAH ya iyakance komai cikin sauk'i, nanda y'an kwanaki kuma basai na zagayo naga masu jego ba da jikin naka, a dai dunga kulawa sosai, gasu laraba nan da bayi 2 anbar muku, dukdai wata kulawa insha ALLAH zasu taimaka wajen badata akan yaran, dan yakamata dukkan bayi da kuyangin sashen nan naka ka sallamesu kawai”.
Kansa ya jinjina mata alamar amsawa.
A gurguje sukad'an kuma tattaunawa da kwantar masa da hankali suka fito, dukda yaso musu rakkiya suka dakatar dashi. Abincin da mom ta zuba masa takumace yamata alk'awarin zaici ya dage yaci sosai, sannan Sauban daya dawo rakkiyarsu d'auke da y'an uku shida bayinnan biyu yabashi magani yasha, kar6ar Amaturrahman yayi, Sauban kuma na zaune dasu Abdurraheem yana musu wasa wai dole sai sunyi dariya, (nace, “aiki jaa kenan, inba dariyar k'udaba ta jarirai idan suna barci keyi aiko ka dad'e baka ganiba Uncle triplets😂).

Galadima ma madai yatsansa d'aya ya saka cikin hannun Amaturrahman yana wasa dashi, dukda idonsa a lumshe yake ya jingina kansa da kujera, maganganun Munaya na d'azun kawai yake nazari dalla-dalla.
Ana cikin haka Samha tayi Knocking, Sauban yace ta shigo, saida ta gaida Galadima damasa ya jiki.
Ya amsa mata batareda ya kalleta ba, tareda tambayarta Khaleel fa?. Tace, “yana 6angaren Ummu hasheem”.
Baice komaiba, itama ta k'araso ta d'auki Ammaurrahman data rik'e yatsansa gam tak'i saki..
d'agowa Galadima yay yana kallon yarinyar, Samha dai dariya takeyi, har Sauban shima ya farga da abinda ke faruwa ya shiga tayata. Galadima ya zare yatsansa yana murmuahin gefen baki da lakatar hancin Amaturrahman.

Har Magriba suna nan sun shashance akan yaran, yayinda Galadima ke zaune yanata cud'awa da tantancewa, lokaci-lokaci yakan kallesu dagasu har yaran. Tunda ya tambayesu Munaya sukace tasha Magani tana barci bai sake tambaya ba.


********

Ban tashiba saida suka fara kuka, a time d'in har magrib tama wuce, nagama shayar dasu na lek'a Galadima, na iske doctor jalal tareda Dr Yaseen da Akash Wanda yake shirin komawa gobe, sai Muftahu da Nuren.
Muka gaisa dasu suka kuma tambayata jikinsa? na Amsa musu da Alhmdllh. fitowa nayi na barsu, da aka kawo mana abinci ma can nace akai musu, Sauban yazo ya kwashi yaran bisa Umarnin Galadima, doctors zasu kuma duba lafiyarsu.


★★★★★★

Tunda Harun ya fita saiya kira wata Number lokacin daya k'arasa d'akinsa, dukkan abinda ya faru ya labarta mata, daga can tace k'aryane bahaka akaiba, ita an sanar mata lallai da Galadima aka kar6o yaran, babu wasu police, amma itafa kamar tafara saka alamar tambaya akan wannan ficikar matar tasa.
Harun yace, “haba dai, wannan y'ar yarinyar mizata iya, akwai dai abinda bamu saniba, yanzu dai kibari zamuyi maganar daga baya, zand'an bincika yarannan danni na lurama kamar ba wad'anda muka saka bane sukayi aikinnan?”.
“sunefa gaskiya, abinda dai na lura dashi sun had'a aikin da wasune, shiyyasa suke 6oye mana Kansu, tunda kaga mudai baiwarnan bamu muka sakata ba, amma shi namijin yana cikinsu, nasan sunyi luff ne sai k'ura ta natsa su fito”.
“ok shikenan to, zandai sake bincikawa, dan Sameer yanada wayo, shiyyasa naso bugar cikinsa akan batun, amma wannan shegen k'asaitar tasa ta rainin hankali ya hanashi tankamin, sai matarce ke bani amsa”..
“karka damu zamu sauke masa shine ai”...............✍🏻





🤣abin dariya, ku a naku zaton yaranku sun 6oye Kansu be?, to suna hannun Galadima, lafiya kawai muke jira ya samu ya yagalgalasu kuma ya cafkoku munafukai🙄😏.







*_ALLAH ka gafartama iyayenmu._*😭🙏🏼
*_typing📲_*


💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._*


*_♦RAINA KAMA.....!!♦_*
_(Kaga gayya)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*



~Book 2~ 👉🏻2⃣9⃣


..............Harmun kwanta zuciyata ta kasa samun nutsuwa, inason naje naga halin da yake ciki, Dan koda su Nuren suka wuce ban komaba, sakkowa nai daga kan gadon, laraba dake a tsakar d'akin kan katifa tace, “ranki ya dad'e lafiya kuwa?”.
Banason ta kalli abun da wata manufa, dan haka nad'an murmusa, “uhmm iya inason duba Abbansu ne, ban saniba koyasha maganinsa kafin ya kwanta”.
“eh lallai hakan yanada k'yau, badan ma jego ba ai bai kamata ya kwana shi d'ayaba”.
“aiba shi kad'ai baneba iya, Sauban ne zai tare dashi ”.
A to hakan yayi.

Bance komaiba Na kar6i gyale wajen Samha Na saka na fita.
Masarautar tayi tsit, da alama kowa yasamu nutsuwa a sashensa, ban tsaya knocking ba na shige kawai, a falo na iske Sauban zaune yana kallon ball, cikin tsokanar da ya iya yace, aunty gimbiya kin kasa barcine?”.
Nayi murmushi, “yaa Sauban matarka taga ta kanta wlhy”.
Dariya yayi kawai, nikuma na wuce abina.
Saida nayi sallama kusan uku banji an amsaba, saina shige kawai. Zaune na iskeshi a bakin gado ya jingina da fuskar gado, hannunsa d'auke da Qur'an yana karatu a hankali, idonsa cikin medical glasses, gakuma system a gefe itama a kunne. naji dad'in yanda na sameshi, Addu'a da karatun Qur'an babban jigone dake wanke zuciya da damuwar d'an Adam (duk lokacin da ranki ya 6aci d'auki Qur'an ki karanta koki saurara, wlhy zakuji sassauci mai yawa).
Har zan juya na fita sai naji yay gyaran murya, juyowa nayi na kallesa, har yanzu dai karatunsa ya keyi. na dawo na zauna a bakin gadon ta d'ayan gefen, shikuma ya cigaba da karatunsa, kusan mintuna 6 kafin ya rufe Qur'an d'in ya ajiye, ya cire medical glasses d'insa shima ya ajiye yana kallona, ko kad'an fuskarnan babu walwala, nuni yamin da inzo.
Ban musaba na tashi nadawo 6angaren inda yake, zama nai d'an nesa dashi kad'an.
Ya lashe le6ensa da cizarsa kad'an yana hard'e hannayensa a k'irji.
Muryata can k'asan mak'oshi nace, “yaya jikin?”.
Kansa kawai ya jinjina min cikin lumshe ido, sannan ya motsa baki kamar zaiyi magana saikuma yay shiru, saida yaja wasu seconds sannan yace, “Munaya!?”.
“Na'am”. Na amsa ina kallonsa da janye idon lokaci d'aya saboda ya tsareni da nasa.
Huci yad'an furzar, ya cire hannayensa daga k'irji yana gyara zama, “Nayi nazaci sosai akan maganganun ki na d'azun, nakuma fassarasu aji-aji, na fahimcesu a yanda tawa fahimtar take, so a wannan karon rok'o nake miki na k'arshe akan ki fad'amin abinda kika sani, ni d'an Adam ne, ban isa cewa komai na sanshi a rayuwaba ko na iyashi, sai abinda Ubangiji yaso in sani kawai, Munaya ada ba haka rayuwata takeba, mutumne ni mai yawan raha dason nishad'i, amma daga lokacinda nafara sanin kaina da matsalar mahaifina sai komaina ya canja, nazama mutum mai yawan rashinson magana, nafison kullum na kasance ni kad'ai a kuma ke6antaccen waje” yay murmushin takaici sannan ya cigaba da fad'in “Bawai hakan Na birgeni baneba ko a San raina, saboda Ina shiga k'uncine, amma banida za6in daya wuce hakan. nasha wahalhalu Na rayuwa kala-kala kafin na tsaya da k'afafuna, zuciyata ta bushe namance daga wane tsatso na fito, domin idan kinganni a lokacin da nake karatu da koyan sana'oi bazaki ta6a kawo ni jinin sarauta baneba, ko d'an wani, nayi gwagwarmaya sosai irin wadda d'a Mara gata yakeyi, badan mahaifiyata bata sona bane ta tsaya tsayin daka wajen ganin na horu kona nemi na kaina, hikimarta itace nazama jarumi mai yawan juriya, nakuma kwato mana y'ancinmu a lokacinda ya dace, duk wannan fad'i tashin da kikaga inayi wlhy badan nayi mulki baneba kamar yanda su suke tunani, Burina kawai nasan miyasa aka durk'usarmin da mahaifi? Tabbas ni jinin sarautane gaba da baya, kuma yana yawo a cikin jinina, amma rashin kwanciyar hankalin dake cikin sarauta baya birgeni, kallon kitse kawai akema rogo, ayau inason Kituna kema kin haifi yaranda sun rigada sun shigo cikin wannan harmutsi, tunda tazama jininsu, ki fad'amin kodan mu gyaramusu gobensu su rayu cikin salama koda bama numfashine, nasan hakanan bazakima Harun abinda kikai masa d'azunba saboda son zuciya kawai, please miyasa kika hanashi d'aukar Abdurraheem ne? Miyasa kikak'i barina na fad'a masa gaskiyar abinda ya faru?”.

Shiru nayi nakasa cewa komai, sai faman had'iye abinda ya tsayamin a mak'oshi nakeyi, Dan bansan yanda zai kalli abunba koya fahimceshi, babu Abu mafi saka rud'u irin cin amanar makusanci, gashi dai a Ransa shifa ba k'aunarka yakeba, amma kulum yafi kowa kusanci da kai, da Nuna girmama alak'ar tsakaninku. (ALLAH ka Shiga tsakaninmu da duk wani Wanda yake tare damu a matsayin fuka biyu, Dan yanzu abinda yafi komai yawaita kenan a rayuwar d'an adam☹😭).
Cikin katsemun tunani Yace, “please my friend say Something mana”.
Kaina na jinjina masa, cikin nutsuwa nafara masa bayani, Dan yau nayi alk'awarin sanar masa komai, koda zai samu wani haske akan lamarin, shima yasamu nutsuwa a rayuwarsa.

“Tabbas kamar yanda kake zargi aiki nakema wani, saidai fahimtar wanene d'in shine mai wahala, na fad'a maka tun farko a dalilin bak'on Abbanmu naji wani yankin matsalasa da bai ta6a sanarma waniba a ahalinsa, a lokacin da wancan abin yafaru Abba yak'i fad'ama kowa dalilin fishinsa a kanmu, dakuma abinda muka masa, hakanne yasaka innarmu zuwa tasamu baba mai kanwa abokin kakanmu na k'ut da k'ut ta sanar masa fushin da mahaifinmu keyi damu, ankuma bashi hak'uri yak'i sauraren kowa, gashi ba dad'in zama takejiba cikin matan gidanmu, wannan Abu daya faru sai sukejin dad'i damata arashi da habaici, harma damu kanmu. baba mai kanwa yace taje zai masa magana, bayannan bamusan misuka tattaunaba. Sai da bayan komai ya lafa harma mun fara karatu sai sanata halluru ya buk'aci abbanmu yabama y'ay'ansa biyu auren yara cikin yaransa, sunzo gidanmu har suka nuna mune za6insu, a lokacin tabbas naji a raina Sa'eed yamin sosai a rai.....”
Galadima ya tsuk'e fuska yana taune lips dajan k'aramin tsaki.
'Dagowa nayi nad'an kallesa, amma saiya basar tamkar bashine yayiba, nima sharewa nayi na cigaba, “bamusan miya faruba sukace Zarah da siyama sukeso, wannan Abu ya 6atama Abbanmu rai, dan aganinsa anyi wani abune domin k'untatama mahaifiyarmu, hakkane yasashi zuwa ya sanarma Baba mai kanwa, dama duk dai wani Abu dazai taso gidanmu shine ake sanarmawa, yayi sasanci koya tsawatar, koda kuwa innro ce. bayan Abbanmu yaje da kwana d'aya, sai innarmu ta aikemu wajensa muka kaimasa goro da y'ar sayayyar da takan masa lokaci-lokaci, saboda yamusu hallaci a rayuwa a yanda take bamu labari, shiyyasa a kullum take d'aukarsa uba”.
Mun iske baba mai kanwa a d'akinsa na zaure kamar ko yaushe, muka gaidashi cikin girmamawa da tsokanarsa a matsayinsa na kaka, shima ya tsokanemu tareda sakamana albarka kamar yanda ya saba, saiya murmusa tareda gyaran murya, hakanne yasaka muka nutsu dan fahimtar magana mai muhimmanci zaiyi, ya nisa cikin dattako na tsufa ya fara fad'in___”.

_“yarana kuyi hak'uri da damuwar da kuka tsinci kanku a ciki, wadda tunkafin Ku mahaifiyarku a ciki take, amma nasan watan watarana kuda ita duksai kunci ribar wannan hak'urin, karkuyi bak'inciki akan hanaku wannan auren da akayi na y'ay'an halluru, dama can sud'in ba mazajenku baneba, hasalima aurensu ba alkairi baneba”._.
“A razane duk muka kallesa baki bud'e”.
Yayi murmushinsu na manya, _“abin ya baku mamaki ko? Humm ba abin mamaki baneba, yau zan fad'a muku wani sirrin dabaku saniba, domin ina hango wani tarin alkairi tattare da rayuwarku, inakuma ji ajikina kune wad'anda zaku fidda mahaifinku daga wata sark'ak'iya daya Shiga a dalilin taimako tun kafin a haifeku. Alhaji halluru da wata manufa ya nema ma y'ay'ansa auren d'iyan mahaifinku, amma Shifa na fuskanci bai fahimci hakanba, sabo da ya aminta da amintar dake tsakaninsu ta tsawon shekaru. Alhaji halluru yanason shiga jikin mahaifinku ne sosai danya kar6ama iyayen gidansa wani sirri dake hannun Auwalu, ina k'yautata zaton shine kukaji wani Abu a ciki, shi kansa Auwalu baisan minene a ciki ba, domin kuwa bashi akai amana ya Isar dashi ga Wanda yadace, kuma baita6a yunk'urin ya duba ba ya barsa a yanda aka bashi. Kuyi hak'uri akwai wasu k'alubale dake tunkaro rayuwarku, kuma yanada tsananin sark'ak'iya, saidai insha ALLAH zan baku dikkan gudunmawa inhar ALLAH yabani tsawon ran kaiwa wannan lokacin, Ku dage da yawan sadaka kudai da mik'a lamuranku ga ALLAH mai kowa da da sirrin komai, ALLAH kuma ya cigaba da tsareku.”_
“duk cikin tsantsar damuwa muka amsa masa da amin, haka muka baro gidan jikinmu duk a sanyaye, dan har innarmu tata bincikarmu a lokacin, sai muka fake da ciwon mara. sati biyu da faruwar wannan lamari sai Munubiya tafara min k'orafin yawaita mafarkin wani bawan ALLAH, kullum takan gansa ne a cikin dokar daji zagaye da wasu irin halittu masu ban tsoro suna kaimasa hari zasu halakashi, yakanyi k'ok'arin kare kansa amma saiya gaza, idan yanemi taimakonta kuma bata zuwa, saboda tsoro suke bata. Duk sanda tafad'amin wannan mafarki sainace bata addu'a ne, shaid'anune kawai. haka taita jera wannan mafarki kullum dare, kuma da gari ya waye bazata fasa fad'aminba, tundai abin na damunmu har muka watsar muka cigaba da harkokinmu. Ranar kuma sai nima nayi mafarkin makamancin na Munubiya, saidai nikuma na shige ina taya wannan mutumin kare kansa ga wad'annan halittun kamar yanda ya buk'ata, na jigata sosai dan harnatashi jikina duk yayi week, nima ban 6oyema Munubiya komaiba na sanar mata, abin yabata mamaki, kuma tundaga sannan nima na cigaba da mafarkin, kullum kuma ina taimakon wannan mutumin dako fuskarsa ban ta6a ganiba, itako Munubiya takan cemin saidai ta tsaya kallonsa daga nesa yana bata tausayi, kuma yana shan nuna mata tazo ta taimakesa, amma saitak'i ta nok'e kafad'a. nikam a nawa mafarkin duk lokacin da ya nuna na taimakesa nakanje nashiga muyita fama da wad'annan halittu, ita Munubiya tana ganin fuskarsa, amma da zaran ta tashi, saita manta, niko ban ta6a ganin fuskarsa ba ko sau d'aya. Muna cikin halin wannan mafarki ne aka shiga bikin salla, tabbas randa muka had'u dakai a asibiti sainaita jin haushinka akan dalilin da ni kaina nasan bai isa daliliba, (dan kawai ina maka kallon mai girman kai bai kamata naji haushinka ba, tunda bawai hud'ace ta had'amuba, banikuma da tabbacin akanka abbanmu ke a had'ari), saidai had'uwarmu ta filin idi tasha banban data asibiti, dan a filin idi tsoro-tsoro mai gauraye da mamakinka ne suka zaunemin a zuciya, bayan kabani wayarka kabar wajen inata mamaki da juyata da tambayar kaina kaid'in wanene? Sai wata murya ta bani amsa da cewar *Galadima!* saidai koda na waigo banga kowaba sai alamar gittawar mutum mai jajayen kaya, na dad'e soaai wannan al'amiri bai bar rainaba, a haka muka shiga shagalin bikin y'an gidanmu, harda kuma su siyama, anan ne muka had'u da Fu'ad, harga ALLAH bansan wanene Fu'ad ba, bankuma San daga wace tawagar ango ya fitoba, amma amamakin kaina lokaci d'aya na aminta dashi, dukda kasancewata mutum mai masifar tsarta, cikin kwana d'aya kacal na saki jiki dashi, dukda ban amsa masa Cewar na kar6i soyayyarsa ba, daga ni harsu Ayusher bansan miya shiga kanmu ba muka yarda ya kaimu birnin gayu plaza ba, dukda kowannenmu ransa akwai fargaba, musamman ni danakeji kamar akwai wani gagarumin Abu dake tunkaro rayuwata. hardai muka shiga muka fito abinda ya faru ya faru a tsorace nake. fitowar wannan jarida a washegari yasaka dukkan wani ahalinmu a rud'ani, Wanda bansan yazan musalta makashi ka fahimtaba, lokaci d'aya da akazo bincikar wacece a cikinmu na amsa, dan jinai bazan iya bari Munubiya ta amsa laifinba, saboda tanada hak'uri, amma tanada tsauri Wanda nikad'ai da mahaifiyarmu muka San wannan tsaurin nata, dan sometimes takanyi mugunta amma tayi tamkar ba ita baceba, kai tsayema sai'a zargeni ita ba'ayi tunanin zata iyaba....”
Galadima ya katseta da fad'in, “kina nufin bakece kika kusa fad'iwaba a plaza?”.
Nad'an murmusa ina gyaran mayafina dake zamowa saboda kayan sunada santsi, “tabbas bani baceba yalla6ai, Munubiya ce, tausayi. Y'ar uwata yasani kar6ar laifin. Bayan wannan Abu ya faru nanma kowa yata fushi damu musamman Abbanmu, haryace saina nemo miji cikin 2weeks kacal, wannan ya d'agamin hankali, dan nikam kaf samarina babu Wanda yamin, amma sainaga kamar zan iya auren Fu'ad, wannan dalilin yasani kiransa bisa shawarar su feena, amma saiya toshe sukkan hanyar dazamu iya yin magana. bansan yazan misalta maka halin dana tsinci kaina a tsakaninba, naji natsani Fu'ad matuk'a, a wannan time d'inma na cigaba da wancan mafarkin, amma yazomin dawani sabon salo, sannan ita kuma Munubiya ta daina, mafarkin ya canjane zuwa salon da mutumin kanyi yunk'urin ta6ani, amma nakan hanashi damar hakan ta hanyar ja baya da masa gargad'i, shikuma saiya ringa rok'ona da cemin karna masa haka, ni fitilarsa ce. Har sannan kuma still bana ganin fuskarsa, abubuwa da yawa sun had'u sun dagulemin, dukna fige na fice hayyacina. A lokacin da baba mai kanwa yaje dubani asibiti bayan maganar aurenmu da haidar ta rushe saiyake magana cikin murmushi, k'asa-k'asa kuma ta

Please Login or Register in order to submit comment