Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wasa da hankalinka, koda ace wani ya salwanta cikin yarannan karka d'aga hankalinka, ALLAH n daya baka yafika sanin hikimar k'addara hakan, duk lokacinda kaga Matsaloli sun raunana, buk'atu kan kuma kan yalwata ne, kasa a ranka wannan wata damace tazo gareka, ai duk lokacin da aka rasa kwallo a cikin wasa, ba wasan ake dainawa ba, wata kwallon ake jehowa a cikin fili”.
Duk maganar da takeyi ko motsawa baiyiba, baikuma juyo ya kalleta ba, saidai alamu sun nuna yana saurarenta, ta janye hannunta ta juya zata fita tana hawaye.
Cak ta tsaya saboda rik'o hannunta da yayi, kusan minti 1 suna a haka, ta waigo ta kallesa, har yanzu yana a yanda yake, kallon hannunsa daya ruk'o nata tayi.
Bai kalletan ba kuma bai saki hannunba yace, “Lallai ina shaidama dukkan Wanda ya maida rayuwata data ahalina magijin kallonsa, zan tsiyayar masa da idanun, sannan zan kacaccala rayuwarsa Na binnesa da ransa”. ya mik'e tsaye sosai tareda juyowa ya jawo hannunta ta fad'o jikinsa, saurin dafe Amaturrahman dake bayanta tayi da d'ayan hannun. Ya saka idonsa dasuka firgitata cikin nata, fuskarsa dab da tata yace, “kedai kibama yaranki kariya kawai, dan sune fitilar zuciyar mijinki”.. sakin hannunta yay ya zagayeta yabar wajen.
Tamkar sokuwa haka ta bisa da kallo, yayinda zuciyarta keta kuma maimaita maganar tasa, _yaranta, kuma mijinta?_ mi yake nufi to?, amsar itace bata saniba.
Jitai kawai ya saka mata ledar kayansu Abdurraheem a cikin hannu, baice k'alaba yabar wajen zuwa gaban wardrobe d'insa yafara fiddo had'add'iyar Shadda gizna ash colour, sai maik'o take da d'aukar idonu.
Ganin ya shareta yana cigaba da hidimarsa itama saita juya ta fice.
Tunda Sauban yaji motsin kama handle d'in k'ofar yabar wajen da sauri.

Fitarta babu dad'ewa Saleem ya kawo kayanda Galadima ya umarcesa.


__________________________


Munaya Na komawa Aunty Salamah tahau shiryata, dukda taga a yanayin data dawo bata tambayeta daliliba, saida tagama gyara mata fuska tana gyara mata gashi Munaya tafara fad'a mata iya abinda taga ya dace kawai Aunty Salamahr ta iya Sani, sauran kuma sirrinta ne ita da mijinta.
Murmushi Aunty Salamah tayi, tace, “dukda banida tabbacin faruwar wani Abu dagani har Munubiya dama mun shirya hanyoyin d'aukar matakai saboda tsaro, kowa baisan dalilin Munubiya na dagewa akan ki dawo gida ki haihuba, amma ita tasan dalilinta, ba son zuciya ya sakata yin hakanba, Ubangiji Na kallon kowa kuma zaiyi maganin komai, tun a shekaran jiya Saleem yazo mungama tsara komai dama, kuma ya tabbatar min Muftahu yasan komai dan yaga alamar shima tsaye yake da k'afafunsa, inaga yau dai shine yabama Galadima satar amsa, kuma hakan da yayi shine dai-dai, saboda duk abinda zai faru a yau d'innan shi Galadima zai fara zargi”.
Munaya tace, “hakane Aunty Salamah, shiyyasa wlhy Muftahu yafara bani tausayi, ALLAH ya kawo ranarda zai wankesa ayi walk'iya aga kowa dai”.
Amin ya rabbi gimbiyar Galadima Sameer, ku kwantar da hankalinku, komai kam ya taho gangarar zuwa k'arshe, dan alamomi suna nuna haka”.
“nima inajin haka a jikina Aunty Salamah”.
Da wannan hirar aka gama gyaran kan tahau shiri cikin less d'inta Ash colour irin kamar kayan da Galadima zai saka kenan.
Hummm masha ALLAH, maganar k'yawun da Munaya tayima 6ata lokacine, amma tayi k'yau.
Yaranma tsaf aka gama shiryasu, abin kamar ka sacesu ka gudu, sunyi fes.

Kowa yagama hada-hadar shiri, ana fitowa daga sallar La'asar za'a fara kwasar mutane zuwa hall d'in da aka tanada.

*_4:00pm_*

Dukkan mai ruwa da tsaki akan wannan taro ya hallara a gaban motocin da za'a kwashi jama'a, ana fitowa daga salla kuwa aka fara tafiya.

Munaya dai tana d'aki bata fitoba, hakama Galadima saida ya dawo salla sannan yafara shiri ma shi.
Saida kusan kowa ya tafi sannan iyayen gayya suka fito.
Munaya ce tafara fitowa, kuyangi Uku Na d'auke da yaran a bayanta, yayinda wasu kuma ke take mata baya, a babban falon sashensu suka tsaya jiran fitowar Galadima.
Tunkan ya fito daddad'an k'amshinsa ya fara isowa, saikuma sautin takun takalminsa wanda tarihi yaso maimaita kansa ga munaya, dan takun nasa Na daidaituwa ne da bugun zuciyarta.
Yana gaba Sauban na binsa a baya, Tunda ya fito Kuyangin duk sukai k'asa da Kansu, yayinda ya k'araso sai suka zube k'asa suna kwasar gaisuwa, hannu kawai ya d'aga musu, idonsa akan Munaya wadda itama ta risinar da idonta tana masa kallon k'asan ido.
Ba k'arya yayi matuk'ar k'yau, komai nasa Ash colour ne, kuma kayan sarauta y'an asali, harda rawanin daya kuma fiddi ainahinsa Na jinin sarauta, rawanin ya sakaya sajensa hancinsa zuwa bakinsa kawai ake iya gani, idanunsa na cikin eyeglasses dabaka isa kaga kwayarsu ba, dan ya toshe su 6am.
Juyawa yay ya kalli Sauban dake gefensa, Sauban ya fiddo Alk'yabbar dake cikin bag d'in hannunsa ya mik'a masa, kar6a galadima yayi yana mik'ama Sauban had'ad'd'iyar sandar hannunsa da zaka iya d'auka ta gold ce, ya warware alkyabbar ya matsa gaban Munaya dake tsaye har yanzu, yayinda kuyanginta ke a dur kushe har yanzu suma.
Matsawa yay jikinta tamkar zai rungumeta, k'amshin turarensa ya cika hancinta ta lumshe idanu, ya sako alk'yabbar ta bayanta, Sauban na gefe yanata zuba murmushi da d'aukarsu hoto.
Tamkar sokuwa haka Munaya ta tsaya har Galadima ya gama saka mata alk'yabbar a jiki, ya juya Sauban yakuma bashi turaren dake cikin jakkar, feshi ya shiga yimata da turaren, zuciyarta sai kaikawo take yi na d'umbin mamaki da al'ajabin wannan salo,
Bayan ya gama ya maidawa Sauban turaren yanama Munaya nuni da suje da hannu.
Haka suka fito a jere Kuyangi na take musu baya, yayinda Sauban yake gefe yanata zuba musu hotuna a Camera.
Motar da Sarki ya bada ita aka bud'e musu suka shiga, Sauban ya kar6i yaran d'ai-d'ai ya mik'a musu, sannan ya shiga gaba kusada sarkin mota da Amaturrahman shima.
Motar ta d'auki shiru tamkar babu wani mahaluki mai numfashi, Galadima ya zubama Abdurahman dake hannunsa ido kawai yana kallo, yayinda ya sak'ala hannunsa d'aya cikin Na Munaya yana murzayatsuna a hankali.
Itama dai tayi shiru sassan jikinta Na kar6ar sak'on ninsa.

A haka suka Isa har cikin harabar hotel d'in, Wanda ya cika dank'am da motoci, duk Wanda yagani yasan yau taron Na manyane, kodan tsaro Na musamman da wajen ya samu tundaga farkon Layin da hotel d'in yake.
Sauban da Sarkin mota suka fito, ba'a bud'e su Munaya ba, kalonta Galadima yayi fuskarnan dai babu walwala har yanzu, batareda yayi maganar ba ya kamo kwalliyar zaren gaban alk'yabbarta ya matso da fuskarta kusa da tashi, ta bud'e baki zatai magana ya d'ora nashi.
Saida ya shanye jambakin lips d'inta tas sannan ya saketa yana zuba mata harara.
Idonta harsun tara kwalla, cikin lumshe idanu da k'asaitacciyar muryarnan tasa mai had'e da izza yace, “Sau d'aya nake gargad'i, karki bari nasake miki na uku akan fita da lipstick a baki”. ya k'are maganar da kad'a mata yatsansa.
Wani yawu Munaya ta had'iye kawai tana jinjina masa kai, wannan ikon ikoko yana bata mamaki, shiyyasa fa tace Aunty salamah ta saka mata janbakin kad'an, gashi yamata k'yau amma tsabar mugunta ya shanye, lips d'insa sai zafi yakeyi, ta harari Abdurraheem dake cinyarta, saikace shine yayi laifin🤭😂.

Bud'e musu akayi suka fita, Samha da Ayusher suka kar6i yaran.
Munaya taji matuk'ar dad'i da ganin ashe harda y'ar uwarta a walimar, itama sunsha k'yau cikin Brown d'in kaya itada yaa Marwan, tana cikin less irinna Munaya, kalarce kawai ta banbanta, shikuma Yaa Marwan harda babar riga, maganar k'yawun dasukaima 6ata lokacine, suma Yaa Fadeel da Feena suna d'auke da yaransu.
Sun shiga cikin hall d'in da tawagar rakkiyar Kuyangi da dogarai, masha ALLAH Munaya tafad'a dan ganin d'unbin jama'a da aka Tara a wannan k'aton hall, manyan mutane da iyalansu sun halarci wannan waje, hakama ahalinsu Munaya kwai da kwarkwata sunzo, harda y'an anguwarsu, duk yawan mutanen nan bai hana a saka mata kan tsaro masu tauriba a wajen.
Kowa saida su Galadima suka birgesa, abin akwai tsantsar birgewa da sha'a a cikinsa,
A cikin fans harda masu k'yasa Galadima🙆🏽.
barama namuku gulma, can Na hango muku tawan Miss xoxo fa idonta kamar zai fad'o, hakama zee bawa da Aysha dansabo da kdeey🤥, dukda harar da Maman Khady da takwara billy galadanci ke musu sunk'i rusunar da idanu, lamari ya girmama Slimzy harda k'ok'arin mik'ewa fa wai zata iya barin sadeeq d'inta, da sauri saffiya Huguma ta maidata mazaunin tana hararta, Ummi Ai'sha tace, “kai dan ALLAH Ku nutsu kar'ace 'yan Haske muncika ruwan ido”, Faxy Fation da party zarah da Feedohm sukace ai Galadima d'inne fa yaji gishiri da magi, Hafsat Rano ta toshe baki tana dariya, hajja kam yitai kamar bata wajen, sai loda nama take a baki, Ayusher da khaleesat dake kallonta sukace wai hajja bazaki rage filiba a cikinki?, Mamu gee tace, “kukuma ga sa ido” “kema k'ya fad'a dai” cewar zee yabour, Asmy b Aliyu datun d'an tai shiru itada Ummu Basheer suka yamutsa fuska suna fad'in “please kuja aji mana 'yan haske, kunafa ganin yanda aka karrama mu fiye da kowa, karku jafa a maidamu kujerar baya wlhy”. Ni bilyn Abdull da lamarinsu ya girmeni nace, “kubarsu kudai kawai, sosuke susa a hanamu ganin sarakuna, kokuma mama Fulani ta rainamu, kuna dai ganin innaro ma kanta yanda taja aji ta kwamushe a gefe tana mazurai.
Miss xoxo dake gefena tayi k'asa da murya tana dai-daita kanta, tace, “gaskiya kika fad'a tawan, nidai kinsan dama dai Galadima ya dad'e a k'ok'on raina, ko sau d'ayane kisan yanda kikayi aka mana hoto tare”. Nace, “karki damu tawan, Salfe ma zakuyi, amma fa ki kula, dan Munaya babu sauk'i”. “gulmar mi kukeyi?” cewar Ayusher tana jeho mana handkerchief d'in hannunta. zamanmu muka gyara nuna wani basarwa🥺, kunsan fa muma mun fara koya a wajen Galadima😜.

Lallai, fans sannunkufa, lallai kunma munubiya da Munaya kara, ko Galadima nasan kun gama birgesa aradu, irin wannan anko da kukasha, ko a UK albarka y'ay'an baba buhari😝.


____________________

Isowar Sarki Jalaluddeen da Sarki Abdul-fatah da tawagar wasu amintattun sarakunan abokan Abie ya saka kowa ya mik'e cikin girmamawa, saida suka zauna sannan kowa ya koma ya zauna, an fara bud'e taro da addu'oi ga jarirai da kuma kakansu sannan aka fara gudanar da abinda ya Tara jama'a cikin nutsuwa.
Kusan dai lamari Na manya, mudai Fans d'in raina kama sai zuba salfe muke, karkaje kabada labari ace k'arya ka zula bakajeba😆, shiyyasa muka kafa hujja koya kukace my sweet fans🤷🏻‍♀😂?.

Masu 6oyayyen shiri a zuciyaa fa sunata k'iyasata yanda abubuwan da suka shirya zasu gudana, saidai kuma idan sunsan wata basusan wataba, dan eyeglasses d'in idon Galadima Google ne😏, (wato camera ne) tundaga Inda yake yanayo zooming d'in wad'anda suka k'arshen hall d'in ma, duk Wanda zuciyarsa ta saka masa alamar tambaya akansa yana tantancesu ne d'aya bayan d'aya.

Nidai Galadima ka kula banda fans d'in raina kama😨🙆🏽.

Anyi nisa da taro harma Anfara zubama cikin maik'o da mask'i, ga mai zak'i da sanyi muna korawa, Galadima ya kalli agogon azurfa dake hannunsa sannan ya d'ago ya kalli Muftahu suka had'a ido, lips ya ciza, Muftahu daya fahimci yaren ya gyad'a masa kai, ya kuma kallon Saleem da Nuren da Aunty mimi Mom and Sauban Samha Ayusher, kowannensu Kansa ya gyad'a alamar fahimta.................✍🏻



Turk'ashi, tofa masu karatu, shin mike shirin faruwane haka? Wannan amsa tana page 26 da zaizo ranar Monday insha ALLAH. musha weekend lafiya sisters and brothers.🙋🏻🙋🏻🙋🏻



Barkanku da juma'at😁🤝🏻







*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭👏🏻
*_typing📲_*


💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._*


*_♦RAINA KAMA.....!!♦_*
_(Kaga gayya)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

___________________
_Writer's namu ina mik'o gaisuwa da babbar murya_.🙋🏻
*_(takwara) Bily s Fari, (mamana) Maryam IG, (mamana) Ummu hanan, Hauwa'u A Usman (jidda😘) Rufaida Umor, Qurratul ayn, Ai'sha Alto, Leemat, gwoggo😜 Asykhaleel, miss Xakss, Jameela Janaf, (takwara) Ummie Garkuwa, Khadeeja Candy, Billy Sarki, Sister Naja'atu, Reefat yahya, Sad-Naf, Maryam wasagu, Maman Shaheed, classic Feedo, Mzzdady._*

🙆🏽 _Yawane da kufa. Alkairin ALLAH ya kai gareku aduk inda kuke, bilyn Abdull na nayinku wujiga-wujiga🥰😘😘👍🏻_
___________________

~Book 2~ 👉🏻2⃣6⃣

...................MC yafara shelanta cewa wannan bikin sunafa an had'ashi da bikin birthdays ne, domin ranar haihuwar yaran tai dai-dai da ranar haihuwar iyayensu, dan haka suka had'e wannan biki a yau guri d'aya, dan a waccan ranar murnar haihuwar bata basu damar yanka cake ba😂.
Dariya aka sanya, saboda a yanayin barkwanci mc yayi maganar, Galadima kam ai kod'an murmushin ma baiyiba, garama Yaa marwan ya murmusa.
Galadima ya kalli munaya, cikin maganar nan tasa mai kamada an masa tilas yace, “Kina da sa'a”.
“Sa'a kuma?”. ‘Munaya ta fad'a cikin yanayin mamaki’.
Harya bud'e baki zaiyi magana sai kuma ya basar. ganin haka itama Munaya saita sharesa, dan takula yau y'an mulkin ne a kansa.
Saida ya gama shan k'amshinsa sannan yace, “wannan ne karon farko da Sameer yata6a bikin birthday”.
Baki munaya ta d'an ta6e, tana fad'in “Humm, kodai y'ay'anka suna da sa'a?, domin dai a dalilin haihuwarsu ne kayi”.
“ko kina jealous ne?”. ‘yay maganar cikeda basarwa’.
tura baki tai gaba.
Idonsa akan yaransa yace “idan kika bari na kama wannan bakin a wajennan humm.” ya cije lips d'insa.
Sanin k'aramin aikinsane ya akaita abinda ya fad'a d'in ya sata saurin gyara bakinta , tad'an saci kallonsa, ya wani Fiske tamkar ba shine yay maganar ba ma. ita dai tana mamakin kasaita da izza irinna bawan ALLAH n nan, jinin mulki yana da matuk'ar k'arfi a jikinsa. tunaninta ya katse lokacin da hankalinta ya koma kan abinda ke faruwa a hall d'in

Khaleel da Aiyaan, Aryaan ne suka turo cake mai k'yau da tsari, Wanda yasha kwalliyar White and Golden, an saka sunan Galadima da shekarunsa 31years a sama, a jikinsa kuma daga can k'asa ansa Muhammad Sameer (Dadyn Triples), an d'ora candlestick🕯guda uku, Sai hotonsa da yay k'yau sosai cikin shigar sarauta.
Galadima ya kalli Sauban da Samha, yasan dai wannan aikinsu ne, k'in kallonsa sukayi sukam ballema suyi gamo da tsarabar harara😅.
Ita Munaya ma sai yanzu taga Su Aiyaan, batayi zaton anzo da suba, tunda bataga yaran gidansu k'anana ba a waje, sai manya maza da matan Na ma'auri.
MC ya taso k'eyar su Khaleel har inda su Galadima suke zaune, kowanne aka d'ora masa yaro d'aya, suma mik'ewa sukayi bisa umarnin MC d'in, a tare suke takawa ita da shi, sai k'yastu ake zuba musu, masuyi a waya da masu cameras, sai gidajen TVs d'in da aka gayyata suna nuna live. Sun Isa gaban cake d'in hannunsa rik'e da sandarsa, kaikace sarkine da kansa (gaskiyar Munaya Galadima akwai k'asaita, Kodai sarkin da Kansa ya shafa masa lafiya🤭).
Bayan anmasa wak'ar happy birthday yayma munaya nuni waita hura candles d'in.
Cikin k'asa da murya tace, “yalla6ai bafa haka akeyiba, ka hura abinka da kanka”.
Hannunta ya kama ya matsa yanda zataji zafi, yace, “zakiyi?”.
Ai baima kai k'arshen maganarba ta risina ta hure wutar, hall d'in ya d'auki tafi. cake d'inma dan rigima wai saidai su yanka tare.
“haba yalla6ai, saikace Na wani aure?”.
Cikin ta6e Baku yace, “wama ya sani kona auren ne”.
Shiru tayi bata tanka ba, dan itadai fatanta a rabu lafiya, hannunta ta d'ora kan nasa dake rik'e da wuk'ar suka yanka taren. nanma dai tafin akayi. Ya lakata a d'an yatsa ya duk'o gasu Aiyaan ya daddan gwalama yaransa a hanci da kumatu, sannan ya juyo ga Munaya da haushi ya kamata, ai ita yakamata ma yafara sawa ba yaranba.
Itama akan hanci ya shafa mata yana fad'in “yalla6iya haushi kikajine?”.
Kafin tabashi amsa yakuma lakata ya shafama Aryaan Khaleel da Aiyaan suma.
Dole munaya ta had'iye maganarta. Amma ta kudiri saita rama.

Itama itada Munubiya k'aton cake nasu aka kawo kalar pink and White , Munu da Yaa marwan suka taso a tare.
Munaya da Munubiya suka rungume juna suna maijin dad'in tunawa da ranar haihuwar su, shekaru 20 cif da kwana 7. Sun yanka cake atare suka sakama juna abaki kad'an-kad'an, sannan kowacce cikin son tsokana ta lakatama y'ar uwarta a fuska suka rungume juna suna dariya da k'ananun hawaye, suncika shekaru 20 ranarda yaransu sukazo duniya suma.
Abin ya birge mutane, Munubiya ta matsa ga mijinta ta saka masa a baki kad'an, cikin murmushi yace, “happy birthday my heartbeat ”.
Tace, “Thanks you my luv” k'arasawa tayi ta sakama yaran munaya dasu Aryaan a kumatu, sannan ta sakama nata yaran.
Munaya danta rama abinda Galadima yamata, takai cake bakinsa kamar zata bashi, saida ya bud'e baki saita juya ta shafama yaran Munubiya a kumatu, sannan nata.
Yanda Galadima yay shock akan abinda Munaya tamasa sai mutane suka sanya dariya suna tafa mata, mai martaba da papi ma dai saida suka Murmusa.
Munaya ta dawo ta dangwalama Galadima akan hanci tana masa gwalo.
Shi kansa baisan k'asaitaccen murmushin ya kufce masaba, ya saka handkerchief ya goge yana dawowa mazauninsu ya zauna.


Daga nan aka fara gudanar da wasa, Comedian's sukazo sukad'an saka mutane dariya, saikuma mawak'a da suka bada nasu salon.
Tun da Galadima ya fara yawaita kallon agogon hannunsa su Muftahu duk suka sake shiri, dan lokaci yana gab kenan.
Galadima yay k'asa da murya batareda ya kalli Munaya ba, yace “ki shirya, shirinsu na farko d'aukewar wutar hotel d'in nan gaba d'aya, na gaba kuma shine banida tabbas. Yara dai ALLAH yana tare dasu, gakuma su Aryaan suma”..
Cikeda mamaki Munaya ta kallesa, sannan ta kalli yaran dake gabansu a wani d'an gado mai k'yau.
Jikinta har rawa yake tace, “yalla6ai mi su Aryaan zasu iya? Please k.....”.
Hannu ya d'aga mata alamar karfa ta ishesa yace, “wani ilimin aduhuwar daji kawai ake laluboshi, kinsan kuwa dolene a gamu da had'arurruka Aciki”.
batada za6i sainyin shiru, ta kalli su Khaleel daketa wasa da abinci a teble da suke zaune hankalinsu kwance. Hawayene ya cika mata idanu, yama za'ayi wad'an can sakarkarun yaran ace suna masu bama yaranta kariya? Yaushe suka gama sanin ciwon Kansu ma balle na waninsu? gaskiya wannan gangancine kawai, tasa handkerchief ta share hawayen da ke k'ok'arin zubo mata.
Duk abinda take Galadima yana kallonta. duk tausayinta saiya kamashi, ya tuna da wahalar datasha, amma bashida za6in daya wuce hakan, kuma itace tabashi k'arfin gwiwa ai, yasaka aransa ko salwanta yaransa sukayi zaiyi tawakkali insha ALLAH.
Duk Wanda yake cikin shirinsu Galadima ya gama shirinsa, haka suma mak'iya masu buri a shirye suke.
Gaba d'aya saura mintuna 25 atashi, saboda gabatowar sallar magrib, a kuma time d'inne Sarki Abdul-fatah da Sarki jalalludden dadai duk wani babba Wanda sukazo tare suka mik'e domin tafiya, ganin haka Galadima yama Yaa marwan sigina da ido akan ya fita da Ameen and Ameena suma, yabi tawagar su papi, dan baya buk'atar a cuta musu..
Jikin Yaa marwan a sanyaye ya d'auki yaran ya fita cikin dabara, yana kallon y'an uku, shidai dan kawai Galadima ya dagene, amma bai kamata a saka yarannan a matsayin tarko ba.
Munaya ma dai ta danne zuciyarta tayi shiru, tanason bama Galadima kwarin gwiwa.
Su papi na fita y'an rawar k'oroso suka fara wasa, mintuna goma da aka basu ya k'are, sai wani mawak'i ya fara nashi, nanfa y'an mata da samari aka samu nayi, dama ganin su mai martaba ne ya sakasu nok'ewa, ana tsaka da cashewa hall d'in yay d'iff, wuta ta d'auke agaba d'aya hotel d'in, mutane aka fara hayaniya kowa na k'ok'arin damk'e dukiyarsa a hannu da k'ok'arin kunna fitulun waya.
Gaba d'aya jikin Munaya yahau 6ari, ta fashe da kuka tana laluben gadon da yaran suke, ruk'ota Galadima yay yasaka a jikinsa, muryarsa na rawa yace, “please ki nutsu”.
“bazan iyaba yalla6ai, karsu......”.
Yay saurin rufe mata baki, da tattausan tafin hannunsa..... A dai-dai wannan lokacinne kuma wutar hotel d'in tadawo.
Hall d'in ya kuma kaurewa da hayaniya, zaram Munaya da Munubiya suka nufi gadon da yaran suke ciki, wayam babu komai.
Munaya tayi luuu zata fad'i, saurin ruk'ota Munubiya tayi, Galadima yataso daga inda yake shima zuwa garesu. hall d'in yagama rikicewa da tsantsar hayaniyar rashin ganin yaran, sai kallon kallo akeyi. Securitys d'in da aka baza sun rikice da wannan tashin hankali, dan sune mutane na farko da za'a fara tuhuma.
Rufe hotel d'in akayi aka hana kowa shiga balle fita,
Galadima ya shafama Munaya ruwa ta kawo numfashi, fashewa tayi da sabon kuka ta fad'a jikinsa,

Please Login or Register in order to submit comment