Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kusan awa d'aya sannan duk suka fito suka barsu dan sud'anci abinci.
Suna fita Sa'eed ya kalli Sulaiman a yatsine, “my man nida yaran nan nakula sunada rawar kai, garama mai farin kayannan naga kamar tafisu nutsuwa (Fauziyya)”.
“wlhy gskyarka bro... Amma Kasan dolenefa mucika umarnin dad, tunda yayi rantsuwa akan dolene muza6a acikinsu, kai wlhy mun jama kanmu, ni dama tun maganar farko da dad yamana Na maida hankali naza6o da duk hakan bata faruba gareni”.
Cikin ta6e baki Sa'eed yace, “wannan kuma kaika Sani malam. amma basuma 8 akace manaba?”.
“eh hakane, amma kamanta ance biyu acikinsu sunada samari”.
A nanma bakin Sa'eed Yakuma ta6ewa. sun d'anci abinda aka ajiye musu, sannan su Abba suka shigo suka gaisa, cikeda girmamawa suka gaida su Abba, hakan yayima Dady da baba k'arami dad'i, sun kuma tabbatarwa yaran sunada tarbiyya, dama basa kokwanto akan zance yayan Nasu.
An musu rakkiya duka Sassan gidanmu, sun Haida iyayenmu mata. ganinsu Yakuma rud'ar da iyayenmu, kowacce addau'arta ALLAH yasa d'iyarta aka za6a, yo wad'annan zuk'a-zuk'an samari haka, ga kud'i ga ilimi, kowacce saida suka ajiye mata kud'i suke fitowa, har innarmu ma.
Tun aiko kiranmu Innarmu taji ajikinta da biyu aka turamu can, amma baiwar ALLAH hakan bai dametaba, tasan dai wata bata aurar mijin wani, dan haka ko'a fuska bata nunama wani bama cikin wad'anda suka je wajen bak'inba.

Saida Innaro takusa awa d'aya sannan tashigo gidan, yinai tamkar ban gantaba, Munubiya kam tanata barcinta, itama sai bata kulaniba tashige bedroom d'inta.
Shigarta baifi da mintuna 3 ba mukajiyo sallama a k'ofar d'akin, nice Na amsa, Basheer yafara shigowa, sai kuma Sulaiman da Sa'eed, irin k'amshin damukaji a k'ofar d'akin baba karami yasani d'agowa dan jinsa anan, hakan ya tabbatar min da sune sukazo gaida Innaro.
Tunda suka shigo idonsu ya sauka a kanmu, sun kasa d'auke kai daga kallonmu.
Cikeda jan aji nace, “ina yininku”.
Duk suka amsa da “lafiya big girl”.
Basheer yace, “kai Aunty dama kuna nan Ku?”.
Kallonsa nayi nace, “eh, ana nemanmu ne?”.
“a'a, amma dai ba'asan badaku akaje wajen bak'iba”.
Hararsa nayi, saboda sanin halin shegen surutunsa, “malam kaje ka kira musu Innaro ka zauna kana zubama mutane shegen surutu uwa aku”.
Baki ya zum6ura sannan yanufi bedroom d'in Innaro.


Wanda tunda suka shigo yakasa d'auke kai daga kallona, saima zama dayayi kujeraf dake kallona yace, “ok dan bakwa buk'atar ganinmu kuka gudonan kenan? Sai kuma gashi ALLAH ya kawomu mun ganku, dama ance rabon kwad'o...... koko my man?”.
Murmushi Sulaiman yayi, yace “hakane wlhy bro, hakanma dasukayi yamana dai-dai”.
Magan ganinmu yasaka Munubiya tashi, Sulaiman yace, “sleeping beauty kin tashi?”.
d'an waro idanu Munubiya tayi, sai kuma ta kalleni dan neman k'arin bayani.

Innaro takatsemu da fad'in “toku kuna ganin bak'i basai Ku tashi Ku basu wajeba”.
“cikin tsokana Sulaiman yace, “a'a Granny idan sun tashi wazamu kalla? Sun gudo wajenki dan karmu gansu kuma sai gashi ALLAH ya kawomu har gida”.
Ba k'aramin k'ona ran innaro maganar tayiba (dama an kawomu nanne dankar bak'in su gammu balle su za6emu, amma kuma sai gashi sun gammu anan d'in. Anyi gudun gara kenan.....🤣🙊).
Bamu tsaya sauraren abinda innaro zata ceba mukayi fitowarmu zuwa gida.
Su Sa'eed sun gaida innaro, anan take tambayarsu kosun za6a acikin wad'anda sukaje gaishesu acan gidanmu.
Sa'eed yace, “eh mun za6a Granny, amma wad'annan dasuka fita yanzu”.
Caraf innaro tace, “ai wad'annan anmusu miji shiyyasa su basujeba, sai dai cikin wad'ancan”.
Bahaka sukasoba, amma yazasuyi, sai dai har sukabar gidan basu sanar da wa suka za6aba.

Koda muka sanarma innarmu cewa tayi babu ko mai, karma hakan ya damemu.



★★★★★★★★

Har tsawon kwana 5 babu wata magana data fito akan suwa bak'in suka za6a, su Abba basuce da kowa komaiba.
Hankalin iyayenmu mata duk atashe yake, kowa takasa kunne taji wacece aka za6a, sai dai babu mai iya tunkarar iyayenmu maza da zancen, dan duk ba suga fuskar hakanba.

Satinsu guda da zuwa saiga bak'i sunzo wai an kawo kud'in aure.
Hankalin iyayenmu fa yakuma tashi, dan ganinsu wani munafurcin akayi shiyyasa aketa k'unbiya-k'unbiya. Nanfa suka shiga 'yan tsugunne-tsugunne Na gulma irinta gidan yawa.
Kwana biyu dayin haka su Abba suka sanar da cewa nida Munubiya sukace sun za6a.
Innaro ce tafara k'aryatawa, sannan tace, Sam bata aminceba, ina jikokin talakawa 'ya'yan bak'in haure suka kai matsayin auren 'ya'yan babban mutun irin sanata halliru, ai k'aryane sannan munafuncine, agabanta su Sa'eed sukace Zarah da Siyama suka za6a. (Zarah k'anwar ya hameed Ce, babanmu d'aya, Siyama kuwa d'iyar momy Hadiza Ce d'iyar dady).
Jin wannan zance yasa kowa ya fahimci akwai munafunci a lamarin, kowa yasan yanda mamansu ya hameed suke da momy Hadiza a gidan, kansu had'e yake. aikam matan gidanmu suka harzuk'a sunata yada magana, harma abin yaso yazama fad'a, innarmu ce batace komaiba, ita cewama Abbanmu tayi dan ALLAH amaida zancen auren kansu Siyamar tunda innaro tace dama su suka za6a.
Banza abbanmu yamata dan yasan innaro tayi hakanne danta k'untatama innarmu, amma tabbas dabakin su Sulaiman sukace 'yan biyunnan suka za6a, shin sai yaushene inna zata bar muzgunama Aisha da munanata a gidannan?, shekara kusan Arba'in ana Abu guda babu sassauci, tunda yake baita6a ganin rana d'aya da innarmu tama innaro koda kallon banzaba bare rashin kunya, sa6anin sauran matan gidan da basa kunyar ya6a mata magana koda ta habaicine.

Kwana kusan hud'u ana d'auki ba dad'i akan wannan zance, saboda akawo k'arshen maganar sai Abbanmu yace su Sa'eed suzo su nuna wad'anda suka za6a da kansu.
Hummm bamusan miya faruba, (konace mi innaro dasu momy hadiza suka k'ulla ba) munga dai sunta murnar zuwansu Sa'eed d'in, sai rawarkan had'a abincin tarbarsu sukeyi, dan ranar su biyu kacal sukayi, kuma abin mamaki wannan karon agidan innaro aka saukesu.
Bayan isowarsu dakamar mintuna 20 sunci abinci sai akace duk muje gidan innaro.
Su Haleematu duk sun rigamu tafiya, mune k'arshen zuwa muda Fauziyya, saidai muna shiga gidan Innaro ta samu mukabi ta k'ofar kitchen nida Munubiya kawai, Fauziyya kuma aka barta tashiga ta falo.
Yanda sukaita zumud'in kallonmu wancan karon a yau ba haka bane, gaba d'aya hankalinsu Na kan Siyama da zahra, abin ya bamu mamaki har sauran 'yan uwanmu.
Tunda mukaga haka duksai muka fice muka koma gida, su Haleematu harda kukansu, mukanmu zukatanmu sun sosu, dan harga ALLAH Sa'eed ya kwantamin arai.
Wanan lamari saida yajawo gagarumin fad'a agidanmu irinma wanda ba'a ta6a yiba, dan saida takai matan gidanmu da 'Yar tone-tone asirinsu yanda suke kulle-k'ulle wani lokaci akan innarmu da junansu.
Sosai ranar saida ran kowa ya 6aci, amma mamansu yaa Hameed da momy Hadiza su wasai sukejin kansu, koba komai sune a sama suke gani, 'ya'yansu zasuje gidan Hutu.

Abbanmu yasamu innarmu yayta bata hak'uri, dan tabbas yanada tabbacin akwai lauje cikin nad'i akan lamarin, tunda su Sa'eed da kansune suka Samar masa za6insu, amma gashi a wannan karon since su siyama ne ba 'yan biyu ba.
ALLAH sarki innarmu sarkin hak'uri, cewa tayi babu komai, dama can su Siyamar ne matansu, Dan haka tunran gini tun ran Zane, suma sauran ALLAH yabasu Na kwarai.
Sosai Abba yak'ara jin jinama hak'uri da tawakkali irin Na matar tasa, abin sonsa, wadda yakejin har duniya ta tashi k'aunarta dabance a ransa, yana sonta harma baisan yanda zai fassaraba, kullum cikin mata k'yak'yk'yawar addu'a yake akan ribar hak'urin datakeyi da kowa agidan har mahaifiyarsa. yana ganin Kimar Aisha sosai da girmanta, tunda suke babu rana d'aya dazaice gawani abun aibu data aikata masa, sai dai abinda ba'a rasaba saboda zomu zauna zomu sa6a, balle shekara kusan 40 ba wasabace.



★★★★★★★

An tsaida bikin Siyama da Zarah dai-dai danasu aunty Hauwa'u, komai kuma ankawo, saura lefe da sadaki kawai.

Ahaka muka koma makaranta inata yak'in fidda Sa'eed daga raina, ALLAH ma ya taimakeni dama bawai yashiga irin cancikin nan baneba.


******

Yau lectures d'in safe garemu, dan haka mukayi shiri da wuri nida Munubiya, a tsaitsaye mukasha kunun da innarmu ta dama mana, Dan yau girkin mamansu ya Hameed ne, idan bata gadama ba sai takai 8 bata kammala ba, har yara saisun makara,
Aiyaan yashigo d'auke da lunch boxs nasu yana tura baki gaba. “kai kuma lafiya kake cuno baki uwa na agwagwa?”.
6ata fuska yakuma yi tamkar zai fasa kuka, ya zube lunch boxs d'in saman kujera “Aunty ba mama bace tace wai yau batayi abincin dazamuje dashi makaranta ba, hakama fa jiya abincin dare ta d'umama ta zuba mana, amma damukaje school saigashi a kulan Haneep Indomi ne da kwai”.
Aryaan ya kar6e da cewar “ALLAH kuma aunty namu tsami yayi kafinma muci, haka mukadawo da yunwa”.
tausayi yaran suka bani, Munubiya tace, “kuyi hak'uri kunji 2 d'in inna, watarana sai labari ai”.
Kansu suka jinjina mata sukace “to aunty”.
innarmu tana jinmu amma uffan bataceba.
Fita nayi batareda nacema kowa komaiba, wani shago dake can k'asan layinmu naje, nasiyo musu yoghurt da cake k'ananu, nahad'o musu da biscuits.
A harabar gidan Na iskesu harsun fito, sauran yaran sunata shiga school bos d'insu da ake kaisu makaranta. School bag d'insu nabud'e Na saka ma kowa nasa, sannan nace ayi karatu da k'yau kunji babys d'inmu”.
Cikeda jin dad'i suka amsa min da fad'in “to auntynmu”.
Kumatunsu Na sumbata sannan na taimaka musu suka shiga motar suma.
Ina shigowa munubiya tamik'e tana fad'in “wai ina kikaje? kinsanfa jarababben lecturer d'inanne zai shigar mana yau”.
“sorry sweetheart tashi muje”.
Dubu 1 innarmu tamik'o mana, kar6a mukai muna mata godiya, muka fito tana binmu da addu'oin fatan alkairi.
Mun lek'ama su Siyama, kowacce sai tace batada lectures d'in safe, fauziyya da Feedausi ce kawai muka tafi, dansu duk department d'inmu d'ayane..........✍🏼







One luv🥰🥰


*_ALLAH ka gafartama iyayrnmu👏🏻😭_*
[4/16, 9:53 AM] +234 811 277 0720: *_Typing📲_*



*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
_(Home of expert and perfect writer's)_




*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_




*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*



👉🏻5⃣

...........Wajen 4pm muka fito daga cikin makaranta, mu 6 ne yanzu, sa6anin d'azu damukazo mu hud'u, bayan tahowarmu Safara'u da Haleematu suka taho suma, duk da mun rigasu gama lectures sai muka jirasu suka fito muka rankayo tare domin tafiya gida, bamu samu school bos ba, dan haka muka da6o sayyadarmu har zuwa babban gate, muna tsaitsaye abakin titi, tareda wasu daga cikin tsirarun d'alibai irinmu, tundaga nesa muka hango tahowar motocin da uban gudu, saika d'auka sukad'aine akan titin saboda gudun dasuke tsulawa tamkar zasu tashi sama. duk baya muka matsa, dan tabbas wad'annan suka sameka babu abinda zai hanasu takeka su wuce batareda sun damuba.
Tamkar wucewar iska haka suka dinga gittamu, jikake shuuuu!! shuuu!! shuuu!!.
Furicin wani mayshin saurayi dake jingine jikin motarsa yazo d'aukar wasu 'yan mata biyu dake gefenmu 'yan matan sunada jin kan masifa, ko'a makarantar bakowa sukema maganaba, department d'inmu d'aya dasu amma ko kallo basu isheniba, dan ko sallama bata ta6a had'ani dasuba..
Saurayin yabi motocin da kallo yana fad'in “tab ashe *_GALADIMA!_* yashigo gari kenan?”.
“Da gaske yaa Usman?”. ‘d'aya acikin 'yan Matan tafad'a cikin matuk'ar zumud'i’.
Yace, “da gaske mana baby, baga motocinsa kuna ganin sun wuceba”.
Dan danan suka shiga murna, kai kace an musu albishir da aljanna ne.
Baki na ta6e inajan k'aramin tsaki. Fiddausi tace, “to waye shi galadima d'in?”.
“oho musu”, ‘cewar Munubiya’.
Budurwar dake tsaye d'ayan gefenmu itada saurayinta suna jiran abin hawa suma tace, “Galadima d'an Sarki kenan, *Yarima Sameer!”*.

“humm lallai kuce manyane, shiyyasa suke gudun da kosunbi takan talaka babu abinda za'ayi”. ‘cikeda 6acin rai nake maganar’.
Dariya su siyama sukayi suna fad'in “toke ina ruwanki?, k'asarfa tasuce, sai yanda sukayi da ita, tsakaninmu dasu saidai mu hangesu cikin mota ko ranar hawan salla”.
Dogon tsaki nakuma ja tareda kauda kaina daga garesu na maida hankalina wajen tare wata taxi dake gabatomu.
A motama firar dasu Haleematu sukaitayi kenan, ta Galadima ne ko uwarmi ne ma Na manta. nidai uffan ban kuma tofawaba, hasalima haushi hirar tasu takoma bani, dan mai taxi d'in yasaki baki sai wani basu labarin Galadima d'in yakeyi dakuma kwarzan tashi, earphone na jayo a cikin lady's bag d'ina na manna a kunne danma nabar jinsu gaba d'aya.
Saida muka iso gida sannan Fauziyya dake kusa dani ta zungureni, d'agowa nayi Na kalleta sainaga duk sun fice, bance komaiba nafito nima.

Mun iske innarmu bata nan, saisu Aiyaan kawai zaune a falo suna kallo, shigowarmu yasasu tasowa da gudu suna mana oyoyo, muma mun taryesu da murnarmu, Munubiya tace, “Aryaan miyasa baku cire Uniform ba kukayi wanka?”.
“yo aunty mun dawo munga Innarmu bata nanane”.
Nace “innarmu bata nan? to ina taje?”.
“muma bamu saniba aunty, munje kuma kitchen bamuga abinci ba, kuma yunwa mukeji”.
Munubiya tace, “ya salam, kujira ina zuwa”.
Fita tayi, babu dad'ewa sai gata tadawo cikin damuwa, ina cirema su Aryaan Uniform, Na kalleta ina fad'in “mike faruwa Munu...? Ina abincinne?”.
Kwallar idonta ta share, ta zauna bisa kujera sannan tace, “naje mama tace wai innarmu ta d'auka abinci tatafi dashi hospital, dan haka shine rabonmu”.
Raina a 6ace na mik'e zan fita, da sauri munubiya ta ruk'oni, “please Munaya, kibarta kawai, yakamata mu kira innarmu muji waye a hospital? Inaga wannan yafi komai muhimmanci nake gani akan abinda mamar tamana”.
“Haba Munubiya, wannan wane irin rashin mutunci ne, wai mi Matan gidannan suke tak'ama dashine? Idan suna tak'ama da Ubanninsu muma ai nan gidan Ubanmune ko, yanzu ace yarannan kamar su Aryaan su dawo school tun 3 amma ahanasu abinci, wannan wane irin zaluncine? Kisakeni kawai naje naci kutumar uban matarnan munubiya, wlhy sai dai yau Abba yace nabar masa gidansa”.
“A'a munaya, duk hakama bata tasoba, idan hankali ya6ata hankali ke nemosa, bai kamata mutaru muzama d'ayaba mu da su. bara kawai naje kicin d'in Na dafa mana wani abun mai sauk'i, kiyi hak'uri dan ALLAH, kinga innarmu bazataji dad'iba idan tatarar da faruwar hakan”.
Badan raina yaso ba Na hak'ura, saman kujera nakoma Na zauna ina huci, nikad'ai nasan minakeji a zuciyata.
Munubiya tafita dan nema mana abinda zamuci, nikuma Na d'auki waya domin Kiran innarmu naji abinda tajeyi asibiti.
Harta katse bata d'agaba, nakuma kira akaro Na biyu sannan ta d'auka, gaisheta nayi da tambayar mitajeyi asibiti?.
Daga can tace min Nafisar mama Rabi'a Ce jikinta ya motsa yanzu hakama jini ake buk'ata amma an Gaza samu, gashi yaa marwan dayakan bata jinin baya nan yayi tafiya shida Abbansu.
Hankalina a tashe nace “innarmu ganinan zuwa yanzunnan insha ALLAH, kuna general hospital ne?”.
“eh muna nan”.
“ok insha ALLAHU ganina zuwa”.
'Dakinmu nashiga da Sauri nad'an watsa ruwa a tsaitsaye saboda naji dad'in jikina, komai ban tsaya shafawaba Na zira doguwar Riga jallabiya Na fice da hanzari. A k'ofar fita falo naci karo da munubiya d'auke da babban faranti tazubo spaghetti tanata turiri.
namatsa baya da Sauri INA fad'in sorry, munubiya bara naje asibitin wajensu innarmu, wai jikin feena ne ya motsa kuma ana buk'atar jini, gashi yaa marwan sunyi tafiya da abba”. Munubiya tace, “toko Na juye mana abincin a kula mu tafi gaba d'aya?”.
Nace, “a'a munu... Ki zauna dasu Aiyaan bara naje ni kad'ai, baikamata mubar wajen ba kowaba”.
“to shikenan, yanda akayi ki ta6oni awaya, amma in kunkai dare zakuganmu muma, abincinfa?”.
“humm munu bar abincinnan, banida wata nutsuwar cinsa, saina dawo”.
Ban jira amsarta ba nafice. ALLAH ya taimakeni INA fita nasamu napep. Mintuna kad'an muka isa hospital d'in, kud'insa na biyashi nashige da hanzari ina k'ok'arin kiran innarmu.
Babu dad'ewa kuwa ta d'aga, nace mata gani acikin asibitin. Kwatance tamin na inda aka kwantar dasu 6angaren masu sikila.
A rikice na iske innarmu da mama Rabi'a, saboda jikin feena ya motsa mata sosai a wannan karon.
Nace, “mama yanzu mi ake cikine?”.
“Rashin jininne matsala yanzu Munaya, sunce kuma anemoshi da gaggawa, to dama can jinin Fadeel baya yimata shiyyasama ko gwadasa ba ayiba, Marwan dake bata kuma sunyi tafiya da abbansu”.
“mama ina zuwa, bani takardar da suka baku”.
Mik'omin tayi nafita da saurina. dukna rikice inata kai kawo dan ganin ansami jinin, amma har magriba ta rufa ba a samuba, saboda jinin feena yanada wuyar samu, ana cikin kiraye-kirayen sallar isha'i saiga Ayusher ta iso itama, dama an barta a gidane saboda babu kowa, to takasa hak'uri tabiyo sahu, da ita muka cigaba da shiga da fita, saida aka fito sallar isha'i ALLAH yasa aka dace da samun leda 1, saura 1, dama biyu suke buk'ata. ana cikin d'aura mata saiga Munubiya ita dasu Aryaan da kulolin abinci.
Koda aka gama sakawa sai muka koma Neman d'ayar ledar data rage, yanzu harda munubiya muke tare.
Muna a lab d'inne muna shawarar ko a d'iba namu jinin idan zaiyi babu damuwa. Takun takalman damuka jiyo yasamu juyawa harda likitan da maganarsa takatse bisa k'ok'arin bamu amsa dayakeyi. wani ni'imtaccen k'amshine ya iso hancinanmu tunkan mamallakin turarenma yakai ga isowa inda muke. d'auke kaina nayi na maida ga mai d'ibar jinin.
Likitan naga yafara gyara kujera yana fad'in “dama yalla6ai ya shigo gari yau? Ni nama manta yaune ranar dayake bada jini”.
Bai samu mai bashi amsaba a cikinmu har tawagar Wanda yakira yalla6ai suka iso wajen.
Munubiya da Ayusher suka matsa gefe saboda wata uwar tsawa da masu take masa baya suka daka mana, nikam koma motsawa banyiba bare nasan ALLAH yayi ruwansu awajen, saima baki dana ta6e na d'auke kaina daga saitin dasuke.
Bulala d'aya daga masu jajayen rigunan ya d'aga da nufin zubamun.
“Wanda suke kira Yalla6ai dake zaune a kujerar da doctor ya ajiye masa ya d'agamasa hannu da Sauri, alamar karya dakeni”.
Cikeda girmamawa yace, “angama zaki s.........”.
Hannu Yakuma d'aga masa alamar baya buk'atar kirarin.
Baki nakuma ta6ewa sannan na ra6a ta gefensu nafice, banga fuskar Yalla6ai d'in nasuba, saboda ya juyamin bayane ni, sananan shima tunda yashigo bai kalli kowaba a lab d'in, yanata aikin danna wayarsa, kuma baiyi magana ba, ko doctor da Norse's d'in da suka gaidashi hannu kawai ya d'aga musu, kuma ko d'agowa baiyiba yanata aikin danna waya kai kace zai danno hanyar zuwa aljannane aciki.

Waje na dawo nayi zamana ina cigaba da game a waya, su Munubuya dai suna cikin, bansan uwarmi suka tsaya yiba awajen.
Kusan mintuna 40 saigasu sunfito, takun takalmansu kawai naji, amma ban d'agoba, sai k'amshin turarensa daya cika illahirin wajen, saikuma gaisuwar da mutane keta faman zubewa sunayi masa, ko sau d'aya banji ya amsaba.
Tsaki naja inamaijin haushin wannan mutumin, to wayema shine? dayakema mutane wannan jinkan., motsooww aikin banza kawai.

Tabbas yaji tsakin da akayi, hakanne yasakashi d'ago k'yawawan idanunsa yakai duba saitin Inda yajiyo tsakin, akan *munaya* dake zaune bisa kujerun dake Jere awajen ya sauke su, sai dai baya ganin fuskanta sosai, saboda ta duk'ar da kai tana danna waya, kuma gyalen jallabiyarta yarufe mata Rabin fuska, ita kad'aice zatayi wani motsi awajen suji, dan tafi kusanci da Inda suke tsaye.
Janye idanunsa yayi kawai daga gareta, yay saurin d'agama bayin dake k'ok'arin tafowa gareni hannu. Cikin Wata tattausar murya mai aji dake cike da k'asaitar masu isa najiyo yana fad'in “Bayta kawai”.
Cikeda girmamawa bawan yace, “ya shugaba tsaki tayi fa”.
Shiru yay kamar bazai tankaba, saikuma najiyo yace, “kasan dawa take?”.
Bawan girgiza kai yayi alamar a'a.
Bai sake cewa komaiba yay gaba suka bishi a baya.
'Dago ido nai nabi bayansu da kallo, sainaga sun nufi 6angaren mata masu haihuwa.
janye idona nayi ina fad'in “kadaiji dashi Malam, kana fama da Girman kai kamar wani Sarki? Abinma dariya ko (R) bai iyaba, wai bayta”.
Dai dai nan su Ayusher suka iso cikeda farinci, hannunsu d'auke da ledar jinin

Cikeda jin haushi nace, “wai uwarmi kuka tsaya yi acikin lab d'inne?”.
“Uwarmu ta gode”. ‘ cewar Ayusher’.
Munubiya kuma tace, “zaman namu aiko yayi amfani, tunda gashi mun samo sauran jinin ko”.
Na kallesu da mamaki, “ina kuka samo jinin kuma to?”.
“Galadima ya bayar”.
Cikin ta6e baki nace, “miye kuma

Please Login or Register in order to submit comment