Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Cikin fad'in “Alhmdllh” ya amsa musu, yabasu labarin cigaban da aka samu, farin ciki na manaye zukatansu.
Ajiye ruwan da baiwar tamasa yay dai-dai da fitowar Munaya cikin matsakaiciyar kwalliyar data k'ara mata kwarjini da cikar haiba, dan zani da rigane na atanfa, ta fito asalin bahaushiyarta jinin buzaye tawani fannin.
Lokaci d'aya idonsa ya sark'e cikin na juna, kowanne sirrikan kewar d'an uwansa na fita daga cikin nasa, Munaya tafara d'auke kanta, yayinda shima Galadima ya janye nasa cikeda basarwa. Jitai tamkar karta k'araso, amma kowa yarigada yaganta, tadai k'araso tana masa sannu da zuwa. Amsawa yay cikin halin ko in kula.
Ita Momma dariyama suka bata, hakama aunty Mimi data maidasu television.
Ajiye Abdurraheem d'in yayi yatashi wai zaije ya watsa ruwa.
Munaya tabisa da kallo a sace, sanye yake cikin k'ananun kaya, wando ruwan toka da farar riga mai d'ishi-d'ishin ruwan goro.
Tad'anyi 6oyayyar ajiyar zuciya tana kauda idonta lokacin daya juyo, dan jiyay a jikina kallonsa akeyi, aiko saigashi ya kama yalla6iyarsa dumu-dumu.
Baki yata6e ya ida hayewa yana sak'ama zuciyarsa matakin daya shirya d'auka akanta.


****

Ba'a zauna zaman cin tuwonba saida Galadima yay wanka ya sakko, duk suka hallara wajen cin abincin, Momma tama Munaya nuni da ido tayi saving nashi.
Babu musu tabi Umarnin Momma, yanata latsa waya tamkarma baisan hidimar da sukeba, ga fuska cinkus babu walwala, dukda zuciyarsa na kwad'ayin fara cin abincin da k'amshin ya addabi hancinsa tun d'azun.
Tana gamawa takoma mazauninta da Samha ta shiga tsakkiyarsu, ya ajiye wayar yana kuma wani d'aure fuska dacin Magani, yayi mamakin ganin tuwo, dukda dai Dama akanyi musu amma sai time to time, shiyyasa yake sonsa sosai.
Hannunsa ya wanke a ruwan da aka ajiye masa, baici da tsokalin data ajiyeba. Tun a laumar farko kunnensa ya nemi tainkewa, 100% yaji yakamata ya baima mai wannan girkin maki.
Momma da Aunty Mimi dai kam kasa hak'uri sukayi, suka shiga santi da yaba wannan tuwo, Galadima dai yayi tsitt, sai a zuciyarsa yake yabawa, cikeda tsokana Momma tace, “wasuma dai santin nasu na shirune, suna tsoron yin magana dad'in ya yanke”.
Dariya su aunty Mimi sukayi, Munaya ta saka d'ankwali ta kare bakinta tana murmushi, dan kowa yasan dashi Momma take.
Galadima da yasan dashi Momma take shima saiya murmusa yana satar kallon Munaya.

Saida suka gama tsaf Momma ke cewa lallai d'iyata sannu da k'ok'ari, rabon danaci tuwo irin wannan mai dad'i tunna inno, har k'yauta yau saina miki”.
A kunyace Munaya tace, “godiya nake Momma”.
Dukda Galadima ya fahimci girkin Munaya tayishi baice k'alaba, saima ya d'auki waya yay kira, ya mik'e ya fice harabar gidan.
Aifa nan suka shiga gulmarsa suna dariya, Samha harda cewa tana ganinsa yana lumshe ido lokacin fayakecin tuwo.
Aiko mizasuyi inna dariyaba.
Koda yagama wayar bai koma cikin gidanba, saiyay ficewarsa saboda gabatowar lokacin salla.


9:30pm

Galadima ya sakko daga samansa, fuskarsa kawai zaka kalla kafahimci yana tare da damuwa, sanye yake da kayan barci farare sol, wandon yaje har k'waurinsa amma baikai k'asaba, sai k'amshi mai sanyi yakeyi.
Cikin sand'a ya tura k'ofar Momma yad'an lek'a kansa, Munaya kad'ai ya hango zaune abakin gado tana tofama yaran addu'a a tafin hannunsu tana shafa musu a jiki, ya kalli ko ina babu alamar Momma saiya ida shigewa.
Shigowar Mutum kawai Munaya ta gani, tsorata tayi, ta kware baki zatayi ihu yay azamar saka tattausan hannunsa ya toshe bakin, k'amshin turarensa ya sakata fahimtar shine, d'aukarta yay gaba d'ayanta tanata mutsu-mutsu da k'afafu dason yin magana amma babu dama.
Yanufi k'ofa da ita zai fice Momma ta fito daga bayi, daga bayansa kawai yaji ance,
“Sannu shugaban masu iya satar mutane, to saika ajiyeta ai”.
Fad'uwar gaba da kunya dukta lullu6eshi a lokaci d'aya, ya dire Munaya yana susar k'eya saboda kunya, yama kasa kallon Momma d'in.
Itakam bata kuma cewa dashi komaiba tazo ta gabansa ta fita d'akko abu.
Yana ganin Momma ta fita saiya juyo ga Munaya da hanzari. A matuk'ar fusace yay kanta, “K! y'ar rainin hankali ALLAH yau saikin sanarmin minayi miki, inba hakaba a d'akinan zan kwana, bar ganin Momma ta tsaya miki”.
Ja da baya Munaya tayi ganin yana Neman maketa, idonta cike da kwalla tace, “Ai kaima kasani”.
Hannu ya d'aga tamkar zai maketa saikuma ya fasa, ya dunk'ule hannun, “ke wai wace irin mutumce birkitacciya?, ba'a ta6a zama dake lafiyar ALLAH?, kinsan ALLAH wannan karan Abban zan kira Na sanarmawa idanni kin rainani.......”
Cikin kuka munaya ta katseshi, “Dama kasanar masa ai shine ya kamata, kaga shima zaisan tayaya ka aurar masa yarinya, Papi da mai martaba zasusan Neman auren shekara biyu sukaje suka nema kuma suka d'aura.....”
Kansa ya dafe cikin tsantsar takaici, miye kuma nadawo da wannan maganar bayan ta wuce? Kai yarinyarnan y'ar matsalace. Duk a zuciyarsa yake zancen.
Momma da dama duk cikin shirinsune ta fita tai saurin shigowa tana fad'in “Minakeji haka? Waye yayi auren shekara biyu?”.
Duk kasa magana sukayi, munaya Na kuka shiko kunya da nadama dukta rufeshi.
“Waishin bakujini baneba?!”. Momma tayi maganar a tsawace.
“Momma please cool down”.
“Nayi cool down a ina Muh'd, dama abinda ka aikata kenan bamu saniba? Yanzu nan da hankalinka da iliminka Na addini da tarbiyyar da muka baka zakaje kayi auren yarjejeniya da d'iyar mutane? Shekara biyu ta cika kasaketa saboda son zuciya? Wannan d'abi'ar daga ina kuma ka samota? Danba koyarwar addininmu bace balle al'adarmu”.
Jiki a sanyaye Galadima ya zauna a bakin gadon kansa a dafe, itama Momma saita zauna tana kiran Munaya data mak'ure jikin bango tana kuka maiban tausayi. Takowa tayi tazo inda take, saita zauna a k'asa kusada ita.
Momma ta kallesu dukansu, saima suka bata tausayi, Dan takula kowannensu yakamu dason d'an uwansa Na gaskiya, tad'anyi gyaran murya tana fad'in “Muh'd!”.
Kallonta yayi idonsa ya kad'a zuwa jaa kad'an, jijiyoyin kansa da gashin jikinsa duksun mik'e saboda damuwa, sai faman cizar lips yakeyi.
Momma datasan bazaiyi magana ba tunda yahau sama saita cigaba da maganarta, “Muh'd ka fad'amin gaskiya ya akayi ka auri Munaya?”.
Kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru yana kallon Munayar da kanta ke a duk'e tana kuka har yanzu.....
“Ba kallonta nace kayiba, amsar tambayata nake buk'ata”.
Zamansa ya gyara a sanyaye yace, “Momma ku gafarceni, dama nasan duk daren dad'ewa wannan ranar saitazo, nasan nayi kuskuren aikata abinda Addinina bai koyar daniba, hakama al'adata idan taji zata k'yamaci hakan, saidai wlhy a wancan lokacin banida za6in daya wuce hakan, ban ta6a tunanin son wataba, damuwar mahaifina da ciwonsane kawai agabana, banta6a kallon mace dawata siga ta soyyayaba balle tunanin aure, dukda fad'a da kukemin akan nayi aure a kullum. Bayan jaridar nan ta fita saina shiga rud'ani da zargin an aikotane dama gareni, wannan daliline yasani tunani sakawa a satomin ita Na ajiyeta harsai ta sanarmin wanene ya sata, amma sai Muftahu ya nunamin Sam hakan ba mafita baneba, dama kawai Na aureta, maganarsa ta sakani d'aukarsa mahaukaci, Dan haka namasa gargad'in karma ya kuma yinta, nidai kawai a d'akkomin ita Na tuhumeta. Shikuma yace Sam bazai bani goyon baya bisaga wannan gangancinba, k'yalesa nayi da nufin zan nemo Wanda zaimin aikin. Saidai kuma Nureddin kawai gareni, shikuma a time d'in yana Italy. Kwatsam sai wani tunani yazomin a zuciya da gamsuwa da shawarar Muftahu, Dan gaskiya yafad'amin, inhar wani yasan tana hannuna duniya zata d'auka abinda yafaru a jaridar nan gaskiyane Na aikata d'in, amma idan aurenta nayi bakin kowa zai mutu, inada kuma ikon sata tayi komai takuma sanarmin Wanda ya sata. Wannan ne dalilin dayasani bincike akanta, har nasamu aka d'akkomin ita Na sanar mata buk'atata. Da farko k'in abincewa tayi, amma daga baya bansan dalilinta Na amincewarba. Wlhy Momma kinji Na rantse ban aureta dannaci zarafinta ba, kuma harga ALLAH banso kutse cikin mutuncintaba, wlhy Muftahu ne ya zuba mana pills a hollandia muka sha, ALLAH kuma ya k'addara zuwan yarannan ta wannan silar, tundaga randa Na aikata mata abinda babushi acikin yarjejeniyarmu nayi nadama, nakuma gane kuskurena, tunkuma a lokacin nafara tausayinta, tsakanina da ALLAH badan Na amfanu da itaba Na aureta, saidai nasan koda fad'a mata nayi bazata aminceba, zata d'auka bisa wancan dalilinne nace ina sonta, amma nasha nuna mata inason nata, saita dunga sharewa, bansaniba ta fahimcenine kokuwa bata fahimtaba, wlhy Momma tsakanina da ALLAH nakeso Munaya, kuma nayi nadamar aikata abinda Na aikata, na tabbatar bazanma ALLAH wayoba, ikonsane ya aikata yanda yaso a lokacin dayaso d'in”.
Momma tayi murmushinsu na manya tana kallon Munaya, “Na fahimceka Muh'd, amma adalci d'aya zan maka bisaga wannan gangancin naka, adalcin kuwa shine ka saki Munaya a warware auren Contract, saika koma ka kuma Neman aurenta na gaskiya ga iyayenta, ka kuma sanar musu mika aikata musu a farko, kanemi afuwarsu, shima takawa da mai martaba kaje ka sanar musu abinda ka aikata, nikuma namaka alk'awarin zan tsaya maka wajen ganin dawowar Munaya gareka”.
Kasak'e yay yana kallon Momma da wannan tsarin nata, toshi mahaukacine dazaiyi wannan gangancin? Ai kowane irin hukunci zai d'auka amma banda na saki wlhy.
“wai kobaka jini bane?”. Momma ta katse masa tunani.
Narke mata fuska yayi tamkar zaiyi kuka, “Haba Momma Dan ALLAH, yanzunan dakanki kike fad'ar haka? Nidai kimin dukkan hukunci dakikeso amma wlhy banda na saki, bazan iya aikata wannan gangancinba, nayi kuskuren farko amma na biyu kam yana dai-dai daku rasani baki d'aya, wlhy inason matata ina k'aunarta har cikin raina, ni na amince zanje nasami su Abba da papi na sanar musu, nakuma nemi afuwarsu amma banda maganar saki please ”.
Shiru Momma tayi tak'i tanka masa, saikuma yabama Munaya tausayi, ita dama burinta ya amince yayi kuskurenne.
Haka yaytama Momma magiya amma tak'i tanka masa, shikuma ya nace.
Saida Momma ta tabbatar yayi ligif sannan tace, “To ga adalci na biyu tunda ka nace, idan Munaya ta amince ni banida matsala ai, nabaka minti goma kacal zanje na dawo”.
Tashi Momma tayi ta fita tana gumtse dariya, saida ta fita tayita sosai, dama akwai randa Muh'd d'inta zai risina irin haka akan mace, Muh'd dazai aikata laifi bada hak'uri ya gagaresa koma yafi Wanda yayma laifin zuciya da fusata, itakam babu abinda zatace da ALLAH sai godiya, Munaya tagama mata komai data zama sanadin canjawar yaronta mai masifar tauri da tsauri.

A d'aki kam Momma na fita Galadima ya sakko k'asa wajen Munaya, matsawa tayi baya, ya bita, takuma matsawa, yasake binta, sai kawai ta saka masa sabon kuka.
Kansa ya dafe yana fad'in “O ALLAH, Munaya please and Please kiyi hak'uri, nasan nimai laifine amma ki gafarceni, wlhy tun kwananki biyar kacal dakikayi a gidana nayi nadamar aurenki ta sigar yarjejeniya”.
Cikin kuka Munaya tace, “saboda kashiga mutuncina ba”.
Huci Galadima ya furzar, “Haba Munaya yakike fad'ar haka? Ke shaidace dagani har ke babu mai nutsuwar banbance wani Abu a waccan ranar, sai wahaltuwa da mukayi muduka, wlhy kinji namiki rantsuwa badan na lashi zumarkiba nafara sonki, a lokacin nadamar auren contract da mukayi nayi, amma soyayyarki tafara tsiro da yad'one a zuciyata tamar yanda tushiyar bishiya keyi, wasu k'yawawan halayyarkine suka jani a k'aunarki, rashin tsoronki da d'aukar raini, dukda kasantuwata a gidan dana fito baki amince na takaki yanda nasoba, hakan ya tabbatar min bak'ya cikin mata masu kwad'ayi dason wani Dan d'aukakarsa ko dukiyarsa, yawan ibadarki ya tabbatar min da tarbiyyarki, babbar mallakata da kikayi shine damuwa da ciwon mahaifina, wannan Ce babbar hanyar dakika cusan k'aunarki cikin sauk'i, Munaya kin bada gudunmawa a arayuwata wadda bazan ta6a mantawa da itaba, aduk lokacin da raina ya 6aci kafin shigowarki rayuwata nakan azabtu da motsawar ciwona, na fita hayyacina, bana sauraren kowa sai damuwata, amma kece kika canja wannan matsalar tawa ta k'yak'yk'yawar siga, cikin hikimarki da ilimin da ALLAH yabaki, da kasancewarki mai tarbiya, Dan kowanne tsuntsu da gaske kukan gidansu yakeyi, nasha gwadaki akan abubuwa daban-daban amma kina cinye wannan gwajin nawa saboda zuciyarki a tsarkake take, please ina rok'onki a karon farko ki yafemin, kiyi hak'uri kiyi hak'uri kiyi hak'uri, nimai laifine amma mai nadama, tabbas zanji ciwon wani ya k'ulla alak'ar aure da Samha ma ba Amaturrahman ba ta sigar dana k'ulla dake, amma wlhy inhar kince naje gabansu Abba na sanar dasu komai zanje, nidai karki bari aurenmu ya girgiza koda da igiya d'ayane, namiki alk'awarin samuna fiyema da yanda kike tsammani matata”.
Idanu Munaya ta d'ago tana kallonsa, ya jinjina mata kai da lumshe idanu alamar tabbatarwa.
Batace komaiba ta maida kanta k'asa.
Hanunta ya saka anashi yana matsawa, a marairaice yace, “Kokinason Muhammad Sameer yamiki kukane Munaya? Sannan ki yarda nayi nadama? Wlhy nayi nadama da gaske”.
Jikinsa kawai ta fad'a takuma sanya masa wani kukan, shima ya rungumeta yana sakin wasu mugayen ajiyar zuciya, jiyake kamarma ya had'iyeta gaba d'aya ya huta, suzama abu guda d'aya kawai.
Momma dake bayansu tashiga tafi tana takowa cikin d'akin. Da sauri Munaya tabar jikinsa tana 6oye fuska, shikansa Galadima yaji kunya, yay k'asa da ido tana murmushi.
Momma ta zauna tana fad'in “Alhmdllh ya Ubangijin talikai na gode maka, ALLAH ka d'orar da wannan zama har'a aljanna”.
A saman la66a Galadima ya amsa da amin. Munaya dai kunya ta hanata kallon kowa.
Momma tace, “Nima yau zan sanar muku abinda baku saniba”.
Daga Galadima har Munaya kallonta duk sukayi.
Ta gyara zamanta tana murmushi. Tace, “Tun farkon Aurenku nasan komai”.
Da mamaki duk suka kalli juna sannan suka maida kallonsu ga Momma.
Murmusawa takumayi, “Lokacin da Muh'd ya yarda zai auri Munaya amatsayin auren contract Muftahu ya sameni ya sanarmin komai, danshi burinsa Muh'd ya Auri Munaya ne aure na gaskiya tamkar kowa, a lokacin kuma yasan cewar Gimbiya Zulfa itace ta saka aka muku wannan 6atancin, domin 6atama Muh'd suna, abinda yasa Munaya ta shiga matsalar ranar da kuka had'u a filin idine, shikuma Erfan dayazo miki da suna Fu'ad an sakashi sakama Muh'd idone, saikuma ya ganku tare, duk zatonsa akwai alak'a a tsakaninku shiyyasa yayta bibiyar lamarinki harya kaiku plaza, saidai kuma ya rikice yagaza banbanceku lokacin daya fahimci sewar Ku y'an biyune, shi Muftahu a lokacin bazai iya tunkarar Muh'd da ainahin gaskiyar abinda ya saniba gameda Gimbiya Zulfa da Harun, shiyyasa yayta cusamasa ak'idar aurenki a zuciyarsa, Dan aganinsa hakan zai girgiza zuciyarsu gimbiya zulfa, maybe su aikata abinda Muh'd zai iya farga dasu, ammashi sai rashin yardarsa ta tsiya ta hanashi aminta dake kanki. Gudun karta kwa6e agaba yasaka Muftahu zuwa ya sanarmin komai, yakuma fad'amin nagartarki data ahalinki, ya tabbatar min sai kowa yayi alfahari dake acikin masarautarnan, dansu suna ganin idan Muh'd ya auri y'ar talaka zai k'ask'anta bazaiyi sarauta ba, sun manta ALLAH shine mai komai da kowa. Muh'd yanada tausayi sosai Na tabbata inhar wani Abu ya shiga tsakaninku bazai ta6a sakinki ba, wannan dalilin ya sakani bama Muftahu pills ya saka muku, Dan ta wannan hanyar ne kawai zaku iya zama Abu guda”.
Munaya da Galadima duk suka kalli Momma da mamaki, saikuma sukayi k'asa da kai saboda kunya.
Murmushi Momma tayi. Tace, “Yes nice nabashi danna kafeku a waje d'aya, nakuma san Munaya zata iya bore akan ka saketa, shiyyasa a washe garin faruwar abin nasaka ka tilas ku taho nan, wannan shine mataki na biyu, mataki na uku saka Munaya tak'i kwantar maka dakai dannasan halinka da bak'in rashin yarda Muh'd, wannan na kula itakuma bata d'aukar saita kwana, shiyyasa abin yamin dai-dai, nadad'e da fahimtar son dakake mata, amma na shareka harsai ka gano dakanka ka fad'a mata. Cikin Munaya shine babbar ribar danaci, wadda nakema ALLAH godiya akowace dak'ik'a ta rayuwata, nake kuma jin k'aunarta har cikin jinina, badan na rabaku na rik'e Munaya ba, nayine dama danna tabbatar da nadamarka, itama ta kuma tabbatar da lallai da gaske kana k'aunarta, ta daina kokwanto a ranta, ALLAH yayi muku albarka, ya k'ara baku zaman lafiya da zuri'a d'ayyiba, yabama Sauban mace tagari shima irin Munaya, itama Haneefa yabata miji nagari kamar mijinta daya bar duniya koma Wanda ya fishi, jikata Samha itama ALLAH yabata miji nagari Wanda zai rik'e mana ita”.
Atare muka amsa da amin.
Galadima zaiyi magana Momma tace, “kaga d'auka matarka ku tafi dare yayi, da safe ma k'arasa, nikam barci nakeji”.
Kunya ta kama Galadima da Munaya, amma Momma saitayi tamkar batasan sunaiba.
Tamkar munafukai haka suka mik'e sum-sum suka fice a d'akin, yanda basuyi yink'urin d'aukar yaro ko d'ayaba haka Momma bata tuna musuba itama🤣👍🏻...................✍🏻


Masoyan Raina kama amin afuwa dajina shiru, wlhy abubuwane sukaimin yawa, amma Alhmdllh yanzu nafara daidaita, kuma zanyi k'ok'arin gamawa nan kusa da izinin ALLAH, ina muku barka da salla baki d'aya, inakuma jiran naman layya😅🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀.


wad'anda suka tura hoto kuma Na yafe muku wlhy har zuciyata, wancan write up nayisane lokacin raina a matuk'ar 6ace, yanzu kuma Na huce😅, nayi HAK'URI bisa koyarwar manzon ALLAH, Maman Haneefa ngd kema sosai ALLAH yabar zuminci, yakuma yafe mana baki d'aya, dama raina ya 6acine saboda bansan iya inda hotunan zasu kaiba, idan wani ya gani da k'yak'yk'yawar zuciya wani zai iya munanani ta mummunar hanyar dabanjiba ban ganiba, duk mace tagari bazataso pictures nata suke yawo a social media ba, musamman ma mai aure, kobaka da aure mace darajane da ita, saikuma mutunta kanka ALLAH zai kareka, masu ganin Abu kuna yad'awa jikinku Na rawa kubari wlhy, kokad'an hakan bashida k'yau, Dan kuma bazakuso hakanba, ALLAH ya k'ara mana hak'uri baki d'aya.👏🏻😘😘






ALLAH ya gafartama iyayenmu😭👏🏻
[4:56 PM, 8/17/2019] +234 813 508 4146: Typing📲



💡HASKE WRITERS ASSO....


♦RAINA KAMA...!!♦
(Kaga gayya)


Bilyn Abdull ce🤙🏻
________

Gaisuwa da fatan alkairi.😘👌🏻

Takwara Billy Badaru, Maman Haneefa, Jameesha, my Hussy, my Dee.., Maman sayeed, Maman Sa'eed, Rahila Abba, Umman Murtala, lalai, Melerh zbi, Rally garba, Nana yakaku, Aysha Umar Abubakar, Aysha Galadima, Aunty Fareeda (ta group d'in Rano) Ameerah Ibraheem, xeecul, Bilkisu Ogun, Maman Mu'allim, zaujatu takwara Hussain 80k, Dan Mom.

Masha ALLAH akwaiku da yawafa my sweet sister's and brothers😅😘😘👍🏻
________

BOOK 3 👉🏻2⃣7⃣


....................Koda muka fito daga d'akin momma tamkar kwai ya fashemin a ciki haka nake tafiya, yana gaba ina binsa a baya, yayinda yafara taka steps d'in saiya juyo yad'an kalleni, k'asa nayi da kaina, yayi wani miskilin murmushi mai cike da ma'anoni, oho bansan yanaiba.
A step d'in k'arshe ya tsaya yana nunamin hanya wai Na wuce, ra6awa nayi ta gefensa na shige, yanzu kam ina a gaba yana bina a baya buka shiga bedroom d'in, yana nan yanda Na sanshi cikin k'amshi da tsafta, Na zauna a saman sofa ina sauke numfashi.
Tsaye yay kawai yana kallona, nikuma nakasa d'aga nawa idon Na kallesa, saima naji Na takura kallon dayakemin d'in. Kusan mintuna biyu sannan ya zauna a teble d'in dake gaban sofa d'in, ya kamo hannayena danake wasa da gefen siririn gyalen kaina. Cikin wata tattausar muryarsa mai cikeda nutsuwa da tarin k'asaita yace, “My Mata”.
Kasa d'ago idanu nayi Na kallesa, saida Na amsa a sanyaye.
Yad'an murmusa tareda saka hannunsa a ha6ata ya d'ago face d'ina. Kallo d'aya namasa Na risinar da idanuna, murmushi yayi mai sauti, yakuma sanyaya murya tamkar mai rad'a yana fad'in “Kin huce?”.
Kamar bazance komaiba dai saina d'aga masa kai siraren hawaye na ziraromin a kumatu.
Baice komaiba sai zubamin ido da yayi kusan seconds 30, ya sauke 6oyayyar ajiyar zuciya yana saka hannayensa biyu ya tallafe fuskata a cikin tafin hannun, ya gogemin hawayen da babban d'anyatsansa guda biyu.
“A d'an kalleni mana my Queen, a kuma min murmushi ko kad'an na tabbabatar an huce d'in”. Yay maganar yana Raba idanu akan fuskarta.
Yanda ya marairaice sai bansan lokacin da murmuahin ya kufceminba ma.
Shima murmusawa yayi da d'an jan hancina, “Haba kokefa my heartbeat”.
Hannu na saka na kare fuskata saboda naji kunya.
Yawani lumshe idanu da sakin murmushin gefen baki, tareda maida kallonsa ga k'aramin agogon dake bisa dirowan gefen gadon. Time yaja Sosa, kallonsa ya maida ga Munaya data kasa kallonsa. “tashi kiyi shirin barci mu kwanta, ga dare na Neman rabawa”.
Kallonsa nad'an sata ina janye idona. Nace, “To yaranfa?”.
Bai amsaminba saida ya mik'e tsaye, “karki wani damu kanki, tunda kikaga Momma bata bamuba aikinsan ranar ta musamman Ce yau”.
Ban sake maganaba danjin ya kamo wata tashar, na mik'e tsaye zuwa wardrobe na d'auka kayan barci.
Duk abinda take idonsa a kanta, yana zaune a bakin gado yana binta da kallo.
Ina juyowa muka had'a ido, nai azamar janye nawa, shikuma ya jehomin tambaya.
“Wad'annan kayanfa?”.
Kallon kayan nayi sannan Na kallesa da mamakin tambayar tasa, idonsa a kaina Dan haka Na janye nawa.
Nace, “Zan sakane”.
Baicemin k'alaba, sai mik'ewa da yay ya tako gareni cikeda izza da k'asaita, saina samu kaina da fad'uwar gaba, jinake tamkar nama zura da gudu. Kayan ya kar6a yana matsowa jikina, nad'anja baya amma saiya taro k'uguna da hannunsa yana kallon fuskata, cikin magana rad'a-rad'a daf da fuskata yace, “basu nake buk'atar ki sakaba yau, ke kad'anki nakeson gani babu wani shamaki a tsakaninmu”.
Da mamaki na kallesa saiya d'agamin gira, nai azamar

Please Login or Register in order to submit comment