Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Tagumin yacire yana wani k'asaitaccen murmushi, ya mik'e tseye yakoma kan gadon, filolin dasuke k'asa ya d'auka ya jera a tsakkiyar gadon kamar d'azun. nidai duk ina kallonsa, saida ya lullu6ama k'afafunsa bargo zuwa cikinsa sannan yace, “taso ki kwanta sarkin arhan hawaye”.
Harara Na zuba masa batare da Na shiryaba, sai kawai ya ta6e bakinsa yay kwanciyarsa ya barni, tareda kashe fitilar ya maida ta barci.
Kusan mintuna 4 Na zame Na kwanta a kujerar, amma sainaji duk babu dad'i, saboda maganin bai fara tasirin da jikina zai bar ciwonba, tashi nayi nakuma zama, kusan 5munutes sannan natashi sad'af-sad'af tamkar munafuka na haye gadon. Ni duk tunanina yayi barci. Ashe duk abinda nake yanajina da kallona. murmushi yayi kawai yana lumshe idonsa, a ransa yana jinjina irin rashin wayona.

Ajiyar zuciya Na sauke a hankali, sannan naja bargon dayake babbane Na lullu6a, mintuna kad'an nafara zufa, alamar zazza6in ya sauka. Bargon na janye don insha isaka, bansan sanda barci ya saceni ba.
Juyowa yayi ya kalleni, yaga ina sauke numfashi a hankali alamar nasamu barci, k'aramar ajiyar zuciya ya sauke kafin yasake addu'a shima ya gyara kwanciyar sa.


★★★★★★★


Yau gidanmu sun tashi cikin tashin hankali, Abbah yay Accident yayin dawowa gida daga wajen aikinsa, innarmu Na kwance ciwon kai dukya isheta, tunda ta tashi da safe dashi ta tashi, gasu Aryaan sun isheta da ihun fad'ansu, sai mugun wasa sukeyi suna guje-guje a falon, amma takasa d'aga kai ta tsawatar musu.
Zuciyarta cike da kewar su Munubiya, inda suna nan da yanzu suke bata taimako, koyaya tace batajin dad'i zasu rud'e, amma gashi yau ko wanke-wanke tama rasa mai matashi, sai Zainab maman fauziyya tasaka tayi mata, amma 6angarenta ko shara bai samuba yau, kuma tun d'azun tafara jin mamansu yaa hameed tana k'ananun magana akan tak'i fitowa ta aza musu girki, maimakon sunga shiru su lek'o suji ko lafiya? A'a su babu ruwansu, kawai a dafa abasu suci da 'ya'yansu...
Wayarta dake ring ta katse mata tunani, ta kalli su Aiyaan dake danbe Aryaan Na kuka saboda dukansa da Aiyaan yayi a baki. “wani cikinku ya d'akkomin wayata saman freight”.
Cikin kuka Aryaan yace “Innarmu kingafa ya dokarmin baki”.
“kukuka Sani, nidai nace wani ya d'akkon waya acikinku, idan kuma kuka bari Na tashi sai jikinku yagaya muku”.
Aryaan ya d'akko mata wayar ya kawo mata, lokacin harta tsinke, ganin Abbanmu ne yasata bin kiran, bugu biyu aka d'aga, ko gaisuwa bai bari sunyiba, yace mai wayarne yayi Accident, yanzu haka suna general hospital.
“innalillahi wa'inna'illaihirraji'un” innarmu tafad'a tana mik'ewa zumbur, ga wata zufa Na karyo mata, batasan tayo waje tana kwalama matan gidan kiraba.
Kowacce tafito jiki Na 6ari, azatonsu wata acikinmu aka sako, musamman ma ni dasuke kiran aurena auren d'ori d'afini.
tana hawaye ta sanar musu da abinda yafaru. Nanfa gidan ya rikice, yara suka garzaya suka sanarma innaro.
Ko takalmi babu haka tanufo gidanmu tana shar6ar majinar kuka da kiran tashiga uku, Awwalu zai mutu ya barta. wannan kwakwazon natane ya ankarar da jama'ar anguwarmu.

A rikice baba k'arami da Dady suka nufi asibitin, Dan matan gidanmu sun kira suma sun sanar musu abinda ke faruwa.
Kafin wani lokaci jama'ar gidanmu sun gama cika asibitin, sai koke-koke sukeyi suna son ganin Abba, amma an hanasu, Dan bak'aramin buguwa yayiba.


______________________________

Alhmdllh natashi jikina da sauk'i, Dan kuwa babu zazza6in da ciwon jikin, hakama ciwon kan babu, bai tadani ba saida yadawo massalaci, lokacin har gari yafara haske ma.
Na idar da salla ina zaune ina addu'a yafito daga bathroom, da alama wanka yayo, Dan sanye yake da bathrobe sky blue, yana rik'e da k'aramin towel a hannu yana goge ruwan fuskarsa.
Kallo d'aya namasa Na d'auke kaina, shikoma bai kalleni ba ya wuce gaban mirror ya zauna, saida yafara shafa mai sannan Na tsinkayo muryarsa yana fad'in “ya jikin naki?”.
Yanda yay maganar a cinkushe yasakani d'agowa Na kallesa, ganin hidimarsa kawai yakeyi saina d'auke kaina, nace “da sauk'i”.
Bai sake magana ba, harya kammala yabar gaban mirror d'in, wajen wardrobe yakoma, nidai kaina Na k'asa bansan hidimar dayakeba.
Koda ya d'auki kayan saiya koma bayi ya saka tamkar yanda ya saba, ya fito ya iskeni ina gyaran gadon, ta gefen ido Na kallesa, yayi k'yau cikin wani bak'in lallausan yadi, Wanda akaima ado da jan style, nakula yanason kayan al'adarsa, dukda baitashi ya girma cikin k'abilar tasaba, sock's ya d'akko da bak'ak'en takalma sau ciki ya zauna saman sofa, yana sakawa yana magana, “uhm Zanyi wata 'yar tafiya Na kwana 2 kacal, mikike da buk'ata?”.
Tsayawa nayi daga gyaran gadon danake, Na d'ago ina kallonsa kawai, jin nayi shiru kuma yanajin alamun ana kallonsa ya d'ago shima. Ido muka had'a saina janye nawa.
“kallon fa?”. ‘yafad'a yana k'ok'arin saka d'ayan takalmin’.
Cikin la6e baki nace “yoni yalla6ai mizan kalla anan?”.
Banza yamin, saida yagama saka takalminsa sannan yamik'e tsaye yana fad'in “hakanefa, Ashe babu abin kallo anan”.
Nima shiru namasa ban tankaba, ya saka laptop d'insa dawasu 'yan abubuwa a k'aramar briefcase d'insa, ya zuge zip d'in yana fad'in “ki shirya muje kiga likita kafin Na wuce”.
Da sauri nace “a'a kaje abinka, Indai nice Na warke”.
Idanu ya tsuramin alamun tuhuma, nikuma nak'i kallonsa, ya girgiza kansa kawai sannan ya ajiye min kud'i akan gadon, “ni Na tafi, a yafi juna”.
'Dagowa nayi ina kallonsa da mamakin kalmarsa ta k'arshe, bansan sanda bakina ya su6uce nace “ALLAH ya tsare hanya, ya dawo dakai la fi ya”. ‘na k'are maganar da d'aid'aya’.
Cak ya tsaya abakin k'ofar, saboda yanda addu'ar tawa tazo masa a bazata, dan bai tunanin hakan daga gareniba, yajuyo a hankali tamkar maison gaskata abinda yaji, kallona yayi muka had'a ido, amamakina saiya sakarmin wani tsadajjen murmushi, irin Wanda zan iya rantsuwa ban ta6a gani daga garesaba. Baice komaiba yajuya yafice da sauri.
Yabar zuciyata da luguden dabansan dalilinsa ba. Wata ajiyar zuciya Na sauke, tare da zama jagwaf a bakin gadon na dafe kaina da mamakin murmushin da Galadima yamin.


Bai dad'eba sosai a hospital yamusu sallama yafito, dama tun a daren jiya ya sanar musu zaiyi tafiya, ga jirgi kuma ya kusa tashi. yafito sunata binsa da addu'oin dawowa lafiya, yayinda shikuma yake amsawa cikeda murmushi. Saida yafara xuwa sukayi magana da doctors d'in dake kula da Abie, yaji babu wata Matsala sannan yafito.
Dama Khumar ne ya kawoshi, Dan haka yanzu ma shine yatafi kaisa airport d'in. Zaman da baifi 30minutes ba jirginsu yataso zuwa 9ja.
Zaune yake kusa da window, yayinda wata matashiyar budurwa ke gefensa, tunda tazo da nufin zama yawani kuma had'e fuska, a d'age ma ya amsa mata sallamar data masa, yasaka belt tareda bud'e Newspaper yahau karatu.
Budurwar sai satar kallonsa takeyi, tanason masa magana amma bataga fuska ba. Sai da akazo tambayar misuke buk'ata?, yace Coffee.
Itama da sauri tace Coffee d'in. juyowa yayi ya kalleta, ta sakar masa wani tsadajjen murmushi.
Janye idonsa yayi yanajan tsaki a zuciyarsa. duk yanda taso yamata magana ko sau d'ayane Galadima yak'i yayi, ya had'e gabas da yamma abinsa. Haka kawai sai tunanin tahowarsu da Munaya ya fad'o masa a rai, yatuna yanda tadinga wani dakewa irin itafa ta saba da hawan jirgi. jaridar yasaka ya rufe fuskarsa yana murmushi da jinjina jan aji irinnan yarinyar, ita bata yarda aga marenarta ba. ya tuna diramarsu ta daren jiya, wani murmushin yakuma saki...... haka abubuwa da yawa sukaita dawo masa akan Matar tasa ta auren Contract. wani abun nata abin dariya, wani Na mamaki, ita bata yardaba adole big girl Ce.
Koda suka sauka baiko kalli inda yarinyar nan takeba, da sauri tabi bayansa tana fad'in “haba yayana babu sallama? Ai kodan darajar makwaftaka mayi sallama”.
Yana sauka daga step d'in k'arshe Na jirgin ya juyo ya kalleta, aransa yace yarinya sai nacin jaraba. Ta kuma fad'in “kozaka bani Number ka muke zuminci”.
Yanzu kam wata uwar harara ya zuba mata kafin yay gaba abinsa. tsaye tayi tana binsa da kallo, jitake kamar ta tsala ihu, harma tafara tunanin ko shid'in kurmane?. cikin matuk'ar mamaki ta hango wasu masu kaya iri d'aya sunyo wajensa, daka gansu kaga jama'ar masarauta. da k'yar ta had'e yawun bakinta, kenan shid'in jinin sarautane?. Batada mai bata wannan amsar, Dan haka taci gaba dabin motocin Galadima da kallo har suka fice abinsu.
Driver d'in da yazo d'aukarta yak'araso inda take, gaisheta yafarayi kafin ya k'ar6i handbag d'in hannunta. amota take tambayarsa koya San wanene Wanda masu kaya iri d'aya sukazo d'auka?.
Yace, “ma'am Galadima Sameer kenan, d'an tsohon Sarki, kusan 1month kenan da aurensa ai”.
Hararsa tayi cikin daka tsawa tace “ina ruwana dawani aurensa, bashi Na tambayeka ba. Punishment d'inka Na fad'amin abinda ban tambayeka ba shine ka nemomin number sa”.
“ALLAH ya huci zuciyarki Ma'am”.
Banza tamasa, yayinda shikuma zufa keta karyo masa dukda AC n dake motar, tunaninsa a ina shikuma zai Samo number babban mutum irin Galadima Sameer shikam? yasan idan bai samo d'inba yashiga uku, dan yarinyar nan ba mutunci gareta ba.



*********************

Tun bayan tafiyar Galadima saina zama wata sukuku, abin mamaki saigani da kewar Galadima wai, gaba d'aya yinin sai nayishi wani babu dad'i, ga gabana yanata yawan fad'uwa, jinake kamar wani al'amari yana shirin faruwa da rayuwata.
Sauban ma sarkin tsokana kasa shiru yayi saida yay magana.
Bayan ya dawo school sai muka tafi asibiti, tunda Na gaida Abie da Momma da Aunty Mimi saina koma gefe nayi shiru abina, ciwon jikine kawai ke nuk'urk'usata, dan ga6o6ina masifar ciwo sukemin, narasa wannan dalili? zazza6inma banaji yanzun, ga yawan fad'uwar gaban dana yini inayi, sai kasa kunne nake naji ko Galadima zai kira wani a 'yan uwansa yace ya sauka lafiya, dan zuciyata tafi karkata da fargaba a kansa.
Shirun da Sauban yaga nayi shine ya kalleni yana dariya k'asa-k'asa. “Aunty gimbiyarmu har kin fara kewar Hubbin naki halan?”.
Idanu nad'an waro ina kallonsa, ganin su Momma Na dariya saina 6oye face d'ina cikin veil d'ina ina fad'in “kai yaa Sauban ALLAH a'a”.
Dariya suka kuma sanyamin, Abie nata murmushi shidai, Momma tace, “A'a Mrs Galadima kifad'a gaskiya dai?”.
Kunya takuma lullu6eni, saina k'udundune kaina gaba d'ayama a gyalen saboda. ina k'aunar wannan family sosai a raina, saboda nima suna nunamin tsantsar k'auna, ko yau nabar cikinsu auren contract d'inmu yak'are bazan manta da alkairinsuba a gareni.
Haka nagama shirin barci Na kwanta a gadonsa ina shak'ar k'amshin turarensa danakejin dad'insa fiye da da. nadad'e ina juye-juye banyi barciba saboda damuwace cinkushe da raina, ga zazza6i mai zafi ya rufeni, bansan ina Galadima yajeba balle nayi tunanin samun number na kirashi, Na gwada number shi ta nan India tak'i wucewa, dama a wayar Samha Na d'auki number bama ta saniba, yau babu mai kulawa dani, sainaji wata kewar innarmu da Munubiyata sun dawomin sabo fil a zuciya. Sai da dare yakusa rabawa kafin barci mai nauyi ya d'aukeni.



_____ .★. _____ .★. _____


Har yamma ba'abari kowa yaga Abba ba, 'yan gidanmu sunci kuka harsun gode ALLAH, Su Munubiya da dukkan yaran gidanmu Na ma'auri tuni labari ya iso musu, kuma duk sun tattara a asibitin suma.
Doctor d'in dayake kan Abbanmu ne yafito yana basu hak'uri akan suje gida hakanan, dan gaskiya baza'a bari suga Abba ba a yau.
Sabon kukane yatashi, musamman ga innaro, idan ka kalleta dolene tabaka tausayi wlhy, yau babu jarabarnan da rashin mutunci, kuka take da fad'in Auwalu karya tafi ya barta..........
Sambatunta yakuma raunana zukatan mutane da yawa a wajen.
Munubiya tayi yunk'urin kirana amma network yahana, da Yaa marwan yakula da hakan kuma ya hanata, yace karta sake ta sanarmin yanzu. Wannan dalilin yahana a sanar min d'in.
Kowa zuciya babu dad'i suka tattara suka tattafi gida, dady da baba k'arami, yaa hameed yaa shafi'u da ya Naseer aka bari a asibitin zasu kwana.
Ranar duk Wanda yasan gidanmu yasan babu lafiya, Dan gidan yayi tsitt, kowa tashi ta isheshi a zuciya, barcima k'alilanne daga cikinsu suka yisa.



___________________________



Sosai hadimansa sukayi farincikin ganinsa, kamar yanda shima yay farin cikin ganin Nasu, sud'in mutanene masu muhimmanci a rayuwarsa, sunzama wasu 6angare na duniyarsa.
Kwance yake a bayan motar idonsa a lumshe, ya saki guntun murmushi saboda tinano yanda zata k'are masa a wajen Momma, koda wasa bai sanar mata Nigeria zai zoba, yayi hakane kuma dan kartayi yunk'urin dakatar dashi ma. jin alamar motar ta tsaya ya bud'e lumsassun idanunsa tareda furzo k'aramar iska, duk da isowar dare yayi hakan baisa sauran hadimansa sun kwanta ba, ya iskesu zazzune a k'ofar sashensa suna jiran isowarsa.
Dogarin daya bud'e masa k'ofar yafara k'ok'arin d'aukar briefcase d'insa domin shigar masa.
Shima ziro k'afarsa d'aya yayi ta inda aka bud'e masan, ya zuk'i iskar masarautarsa tareda fesota tabaki yana lumshe idanunsa, ko ina kwanyar yake da hasken lantarki tamkar rana, duk lokacin daya zo cikin masarautarsa, mahaifarsa, yakan tsinci kansa cikin tunano abubuwa masu d'aci da rad'ad'i a zuciyarsa, yakanji inama ace shid'in ba kowa baneba, inama ace shid'in talakane fitik mai tarin kwanciyar hankali, da za'ace yaza6i rayuwar dazaiyi, da zai za6ama kansa zama talakane, dan babu Wanda yakai talaka kwanciyar hankali inhar yanada k'yak'yk'yawar zuciya da wadatar zuci, amma babu komai a cikin dukiya da mulki sai damuwa darashin kwanciyar hankali, kai kenan kullum cikin rashin nutsuwa, idan kayi wasama ibadar da ubangiji ya halicceka dominta bazakayiba, ya had'iye wani Abu mai d'acin gaske a mak'oshinsa. sannan yashiga k'ak'aro murmushin dole ga sauran hadimansa dake gida basuje tarbarsaba. daka kallesu kasan suna cikin tsantsar farincikin ganinsa, dan sunyi kewarsa, shima hakance agaresa. bayan sun gama gaggaisawa ya tambayesu lafiyarsu sannan yashige ciki.
Ko ina k'al yake tamkar yanda yake buk'atar ganinsa, (hadimansa nada k'ok'arin tsaftace sashensa koda baya k'asar).
Zama yay bisa kujera yana fad'in “ya ALLAH! Alhmdllh”.
Dogarin daya shigo masa da jakka yakuma masa sannu da zuwa sannan yafice.
Yakai mintuna 5 a wajen zaune, sai k'ullawa da kwancewa kawai yakeyi, ga gajiyar zaman jirgi na nuk'urk'usarsa data rashin isashen barci dabasa samu shida Munaya. da k'yar dai yamik'e zuwa bedroom d'in, komai need sai k'amshin mayen turarensa da air fresheners mai sanyin dad'i ke tashi, ya ajiye jikkarsa a kan gadon sannan yafara zame kayansa danya samu ya watsa ruwa.

Ya d'an jima a bayin sannan ya fito d'aure da towel, yana tsane fuskarsa zuwa kai dawani. wardrobe yabud'e ya d'akko boxes kawai yasaka, sannan ya saka jallabiya, sallolin da suka riskesa a hanya ya rama, yana idarwa yacire jallabiyar, matsawa yay jikin mirror ya fesa turare kad'an ya hau gadonsa da yay missing. harya kwanta yatashi zaune, briefcase d'in dayazo da ita ya bud'e, ya Ciro wayoyinsa tareda layinkansa na Nigeria duk ya saka, sannan ya ijiye wayoyin, insha ALLAH zuwa lokacin da zai tashi yana fata komai ya dai-daita.
Addu'ar barci yayi ya gyara kwanciya, amma sai barci yace bai gadaba, tunanin ahalinsa daya baro wata k'asa ya dabaibaye zuciyarsa, wata kewarsu ke tsikarar zuciyarsa, yanzu yasan Abie yayi barci, hakama Momma watak'il ta kwanta, dan macece mai yawan k'iyamull laili, duk da a asibiti takan kwana hakan baya hanata kusanta kanta ga mahaliccinta, Aunty Mimi da Samha ma yasan sunyu barci, Sauban ne dai dakamar wahala ace ya kwanta, ya juya kwanciyar sa yana murmushi, zuciyarsa tace “to matar contract fa?”. ya d'age kafad'a da ta6e bakinsa kad'an, saikuma yasaki k'aramar dariya, daren jiyane kawai ya fad'o masa a rai, yau kuma koyaya ta yini ta kwana? (danba time d'inmu d'aya da India ba), a fili yace, “ALLAH yasa yau dai babu zazza6in, my Friend kin cika taurin kai, dakin yarda nakaiki asibiti zanfi samun nutsuwa, oh god🤦🏼‍♂”. ‘ya k'are maganar da dafe kai’.
Shima yajima baiyi barciba, sai can dare yaja da nisa sannan ya saceshi.


Da asubahi da k'yar ya iya tashi, alwala yay yafita massalaci, bayan an idar da salla yafito suka had'u da Sarki da jama'a keta zubewa suna kwasar gaisuwa.
Sarki yayi mamakin ganinsa, dan har saida fuskarsa ta nuna hakan, murmushi kawai Galadima yayi yana rissinar da kansa k'asa.
Sarki baice masa komaiba yanufi sashensa, sai Galadima yabi bayansa, dogarai kuma suka take musu baya, bayan sun gaida Galadima d'in.

A hamshak'in falon mai martaba na farko suka yada zango, Sarki na zaune bisa kujera mai zaman mutum biyu, Galadima na k'asa kusada k'afafunsa. Kukun Sarki ne suka shigo shida jakadiyya bayan sunyi sallama..
K'aramin tire suka ajiye dake d'auke da butar shayi, sai mug da wani k'aramin bowl mai k'yau anzuba sukari, sai jug k'arami shima an zuba tataccen lemon tsami, saikuma Zuma shima a k'aramin bowl.
Kuku da jakadiyya suka zube gaban mai martaba suna kwasar gaisuwa, sannan suka gaida Galadima shima da masa barka da zuwa.
Cikeda kulawa ya masa musu, har kuku ya durk'usa zai had'ama mai martaba shayin Galadima ya dakatar dashi, tareda masa nuni dayaje abinsa.
Kuku ya rissinar da kai alamar girmamawa sannan suka fice shida jakadiyya suka basu waje.
Galadima ya had'ama Mai martaba shayi da ruwan lemon tsami kamar yanda yasan yana sha a kowacce Safiya, (ada mahaifinsa yasani da wannan al'adar, dan awajensa Sarki jalaludden ya koya). cikeda girmamawa ya mik'ama mai martaba mug d'in, kar6a yayi yana masa murmushi, sannan yace “kaifa?”.
Girgiza kai Galadima yayi, yace “a'a Abba, wannan sai ku”.
Mai martaba yay murmushinsu na manya sannan yace “Saukar yaushe Sameer?”.
Galadima yad'an shafa wuyansa, cikin tsantseni yace, “da daddare Abbah, wani business ne ya kawoni, inaga insha ALLAH zamu bud'e company anan Nigeria saboda muma matasanmu su Mora daga guminmu”.
Murmushi mai martaba yayi, ya kur6i shayinsa sannan yace “tunani mai k'yau yarona, ALLAH yasaka hannu a lamarin. ya jikin d'an uwana dasu auntyna Zeenah?”.
“jikin Abie Alhmdllh Abba, dan bayan tahowarku sauk'i yakuma samuwa gaskiya, Momma kam suma lafiyarsu lau”.
“to Masha ALLAH, tareda iyalin naka kazo kenan?”.
“a'a Abba, ni kad'ai nazo, saina kammala abinda nazoyi itama idan zan dawo zamu dawo tare”.
“to ALLAH ya tabbatar”.
“Amin Abba, bara naje nad'an kimtsa mu gaisa da jama'a, dan zan d'an fita”.
“ok, ALLAH yayi Albarka”.
“amin Abba, a huta lafiya”.
Hannu kawai mai martaba ya d'aga masa, Galadima kuma yafita.

Babu inda ya Shiga, ya koma sashensa domin yayi shiri. saida ya had'a coffee da kansa kamar yanda ya saba idan yazo k'asar, ya zauna yasha danba abincin kowa yakeci a masarautarba, ko Ummu hasheem bayacin abincinta kota kawo, duk da kuma kulawa datake nuna masa fiye da kowa a gidan, gimbiya zulfah uwargidan sarkima tanada k'ok'arin aika masa abincin inhar yazo, amma ko kallon kulolin ma bayayi, saidai bayinsa su cinye.

Yafito wanka yana tsane jikinsa wayarsa tayi k'ara alamar shigowar sak'o, wayar ya d'auka danya duba ko company ne, dan yana fatan ace komai ya daidaita ne, yanason kiran su Momma yaji Yaya jikin mahaifinsa.
Ganin number ce sai abin yabashi mamaki, bud'e sak'on yayi kawai azatonsa ko Nuren ne.

_Gargad'i!! tabbas sirikinka ya tsira a wanan karon, amma ka tabbatar masa next time bazamu barsaba, saimun raba ruhinsa da gangar jikinsa!!!!.................._✍🏼












*_ALLAH ya gafartama mahaifanmu😭🤚🏻✋🏻_*
*_Typing📲_*



*_Haske writer's asso...._*💡




*_♦RAINA KAMA......♦_*
_{Kaga gayya}_



*_Bilyn Abdull Ce_*🤙🏻



~Book 2~ 👉🏻5⃣


..............Bayan an idar da salla Galadima yace wanne office yakamata su fara zuwa?, mtn ko glo?.
Shiru Nuren yay yana tunani, zuwa can ya kalli Galadima “Sameer mizai hana mubari sai zuwa gobe, kasamu kaje kad'an kwanta ka huta, kaga yanda idonka yay jazur kuwa, ga jijiyan dukta tashi”.
Lumshe idanu Galadima yayi yana furzar da huci mai zafi a bakinsa, “Nuren muje kawai, kona kwanta bazan samu nutsuwa ba, kaga fa yanda suka jigata bawan ALLAHn nan”.
“hakane, amma karka damu muje kai dai kawai”.
Galadima bai musaba, suka jera shida Nuren zuwa wajen mota, bayan anbud'e musu sun shiga sai Nuren yacema Sarkin mota suje hotel d'in daya sauka.
Galadima yanajinsu amma baice uffanba, yayi shiru kawai yana kallon jama'a ta glass.
Koda suka isa hotel d'in sai Nuren yace su sarkin mota suje abinsu, zuwa anjima zai kirasu su maida Galadima d'in gida.
Cikin girmamawa sarkin mota ya amsa da to, yamusu sallama suka tafi.

Koda suka isa d'akin da Nuren ya sauka Galadima cire rigar shaddar yayi ya kwanta dagashi sai dogon wandon da vest, kwanciyar mintuna 5 kacal barci yay gaba dashi. Sosai tausayinsa yakama Nuren, yanason d'an 'yar uwar mahaifinsa sosai, (Nuriddeen d'ane ga Abubakar yayan Momma, babban d'an Sarki

Please Login or Register in order to submit comment