Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba ya tako har inda nake, hannu yasaka a kafad'una ya d'agoni, fuskarsa babu walwala ko kad'an, idonsa akan fuskata, kusancin damukai da juna sosai yasaka numfashinsa ke sauka akan fuskar tawa, janye idona nayi na maida kan design d'in gaban rigarsa, yayinda shikuma ya warware alk'yabbar hannunsa mai k'yau ya sakamin, d'agowa nai muka k'ara had'a idanu, ya jinjina min kansa kawai.
Jinai tamkar in fasa ihu, banason saka alk'yabba d'in nan nidai, dan nauyi sukemin, garama wannan batada nauyi gaskiya, dan tamkar riga After dress take, saidai suffar alk'yabba aka mata, kuma tanada kaurin dabaza'a ga jikin mutumba.
Hannunsa yakuma d'orawa akan kafad'una ya d'ago hular alk'yabbar dake kwance a baya ya sakamin, ni kaina koba'a fad'aba nasan nayi k'yau, yanzunma baice uffanba ya juya ya fita yana nunamin agogon hannunsa alamar time yana tafiya.
Handbag d'ita na d'auka da wayata nabi bayansa, dauriya kawai nakeyi na hana kuka tasirin zubowa.
A falo na iskeshi shida Sauban dake zaune a kujera shima cikin manyan kaya, dayake ba sakawa yakeba sainaga ya canjamin, ya kalleni cikin halinsa na tsokana yana fad'in “kaga sarauniya gagara badau ta gobe, takawarki lafiya 6auna mai tafiyar k'asaita.......”.
Harar da Galadima ya zuba masa ce ta sakashi gimtse bakinsa yana had'iye dariya.
Nidai banma tankaba, dan yau zuciyata babu dad'i.
Galadima ne yay gaba mukabi bayansa, tunda muka fito hadimansa suke zubewa gaishemu, Sauban kawai ke amsa musu, shikam Galadima saidai d'aga hannu, Niko ko kallonsuma banayi. Hakan yasa suka fahimci har yanzu akwai matsala kenan, dansu bama Susan munzo nida Sauban ba.

Muna k'ok'arin shiga mota Harun ya iso wajen, gaidashi Sauban yayi, nima na gaidashi, ganin ni da Galadima kowa fuska a tamke sai abin yabashi mamaki, hannun Galadima ya kama suka koma gefe.
Nikuma da Sauban muka shiga mota.

“Sameer babu fad'a miya kawo gaba?”.
Murmushi Galadima yayi, ya cije lips nashi kad'an yana kallon Harun, “bazaka ganeba Harun, na iske abinda ya dagula lissafinane kawai, naga kiranka jiya, amma ina cikin rud'ani a time d'in shiyyasa ban d'agaba”.
“rud'ani? mike faruwa ne?”.
“mahaifin munaya ne yay Accident, a time d'in ina hospital wajensa”.
“ya salam, ya jikin nasa to?”.
“Alhmdllh, zamuje canne bayan mun gaida jama'ar gidan”.
“ok bara na k'arasa abinda zanyi kafin Ku fito saimuje”.
Kai kawai Galadima ya jinjina masa.

Bud'e masa gefena akayi ya shigo, yad'an kalleni, kamar zaiyi magana saikuma yayi shiru.
Sashen mama Fulani muka fara Isa, amma sai aka sanar mana tasha maganin mura ta kwanta, daga nan muka nufi sashen matan Sarki, inda yafi ko ina k'awa da ado a gidan kenan.
Mun sami tarba ta musamman ga Uwar gidansa, nidai matarnan tana k'aunata na lura, kuma tafi sakarma Galadima fiye da kowa a Matan sarki, tanada kirki sosai, haka taita jan Sauban a jikinta, nakula suma sunfi sakewa da ita.
Sosai ta nuna damuwarta akan Accident d'in mahaifina da Galadima ya sanar mata, taita jinjina maganar tana lallashina da jerama Abba addu'ar tashi cikin k'oshin lafiya.
Tasa aka kawo mana break fast wai saimun karya anan, Sauban ne kawai yaci, amma Galadima cewa yay ya k'oshi, nima nace bazan iya ciba. dan burina kawai naga mahaifina, gaisuwarma duk akan k'aya nake.
Shima Sauban d'in bai wani ci abun kirkiba yace ya k'oshi, mun fito muka shiga sauran sassan, amma ba ko inaba.


Sauban da harun sun tafi a mota d'aya, nikuma ni da Galadima. Sai motar dogaran Galadima guda biyu, sai kuma kuyangi hud'u da Uwargidan sarki gimbiya Zulfah tahad'oni dasu, wai kafin mu dawo nima a turamin bayina da zasu ke kula dani, ni dai da to kawai na amsa, Galadima kam baima ce uffanba.
Babu mai magana a cikinmu daga ni harshi, sai saukar ajiyar zuciyata da share kwalla time to time danakeyi.



............................................


Innarmu na fitowa daga bayi Aiyaan ya sanar mata na kira, da mamaki tace masa kodai Munubiya ce?”.
“wlhy Innarmu aunty Munaya ce, kuma batasan Abba bashida lafiya ba”.
“ka sanar mata ne?”. tafad'a a rikice.
“eh innarmu na sanar mata, kumafa naji tana kuka”.
“innalillahi Aiyaan wayace ka sanar mata? da wace Number ta kira?”. Tayi maganar tamkar zata make Aiyaan.
Runtse idanu yayi yana k'ank'ame jiki saboda tsoro. innarmu dukta rikice, tasan su Munaya da shiga Rud'ani akan Abu, yanzu haka tana cikin damuwar Munubiya itama, dan jikinta yakuma janga6ewa, ga laulayi ga wannan damuwar Abban.
K'ok'arin kiran Number tashigayi danta kwantarmin da hankaki amma sai tak'i shiga.
Har suka gama shirin asibiti wayar bata shigaba.
Koda suna mota taita gwadawa.

A asibitin suka had'u da mama Rabi'a suma sunje, ganin innarmu a cikin damuwa yasata k'ok'arin fara kwantarma 'Yar uwarta da hankali.
Innarmu ta sanar mata kato6arar da Aiyaan yayi.
“to Yaya ko su Munaya sunzo k'asarne?”.
Anya kuwa Rabi'a, naga jiya mijinta na nan amma baiyi maganar zata zoba”.
“ito da wannan dan wanann, amma ai bama fidda raiba”.
“hakane”. cewar innarmu.

Babu dad'ewa da zuwansu saiga gwaggon Haleematu da matan k'annen ta sunzo duba Abba, (dayake har yau bata dawoba ita). k'in gaisawa tayi da innarmu da mamansu yaa hameed, innarmu bata damuba, amma mamansu yaa hameed saida taja tsuka, babu dai Wanda ya tanka. Sukuma suka shiga suka ga Abban, dayake yau ana barin na jikinsa zuwa su duba shi.
Koda suka fito harda kuka takeyi, matan k'aninta suka tafi amma ita saita zauna, kaf 'yan gidanmu babu Wanda yace mata danmi, kowama tasa ta isheshi aransa.


★★★★★

Tunda motocinmj suka shigo harabar asibitin sai kallo ya koma sama, 'yan gidanmu dakeda yak'in Galadima ne kowa tsumayen fitowarsa yakeyi, sauran jama'a kuma da 'yan dubiya son ganin wad'anda zasu fito sukeyi.
Sai da aka bud'e mana sannan muka fito, suma su Harun duk sun fito.
Su yaa Hameed suka taho garemu sunama Galadima sannu da zuwa, cikeda kulawa yake amsa musu.
Kowannensu fuskarsa ta nuna farin cikin ganina, yayinda nikuma naketa faman zirar da hawaye.
Cikin d'okin ganina Fauziyya tazo ta kama hannuna itada Safara'u, saina rungumesu na fashe da kuka, kukana ya karyar musu da zuciya suma suka fara, sauran 'yan uwanama duk suka taso gareni, dama duk sun zo, ni kad'aice wadda nake nesa.
Saida baba k'arami yamana magana sannan suka sakeni, na matsa ina sharar kwalla na gaida iyayena, Munubiya ce kawai ban ganiba, ina share hawaye na tambayi tana ina?.
Aunty khalisat tace “sunje ganin doctor itada yaa marwan, dan batajin dad'i itama”.
Kaina kawai na jinjina, na k'arasa gabansu innarmu na durk'usa ina gaishesu, duk sun amsamin cikeda kulawa, da tambayata ya hanya?, nace “Alhmdllh”.
Matan gidanmu kowacce kallona take da mamakin canjawata a cikin wata 1 kacal. Na katse musu tunani da tambayar d'akin da Abba yake.
Aunty Ramlah ce taja hannuna muka shiga corridor d'in dazai sadamu da d'akin da Galadima yasa aka canjama Abba.
A ciki na iske Galadima da Harun da Sauban, sai doctor da yaa Shafi'u yaa Hameed.
Takun takalmanmu yasakasu juyowa suka kallemu, na zare hannuna daga na aunty ramlah ina toshe baki saboda kukan dake Neman kufcenin, taka wa nayi gaban gadon da Abba yake, na durk'ushe ina sakin kuka mai tsuma rai da zuciyar mai saurarona, tare da kife kaina jikin gadon.
Kukana babu zuciyar Wanda bai karya ba, Galadima ya tako a hankali inda nake, hannayensa biyu ya saka ya kamoni na mik'e tsaye, fad'awa nayi saman k'irjinsa na kuma sakin wani sabon kukan.
Bashida za6in daya wuce kar6ata, dan haka shima saiya saka hannayensa ya zagaye bayana dasu, ya d'ora ha6arsa saman kaina yana lumshe idanu da cije lips. kad'an-kad'an yake buga bayana alamar lallashi.
d'ai-d'ai su yaa Hameed suka zare jikinsu suka fice daga d'akin, aka barmu mu kad'ai sai Aunty Ramlah da muka birgeta, itama ganin sun fita saita fice taja mana k'ofar.

Munkai tsawon lokaci ahaka, saida na tsagaita da kukan sannan Galadima ya d'ago kaina daga jikinsa, hannunsa yasa yana gogemin hawayen fuskata, amma ya gaza cewa komai. sai girgiza min kai kawai yakeyi.
Ajiyar zuciya kawai nake saukewa a jere, da hannu ya nunamin hanyar fita.
Banyi musuba nabud'e k'ofar muka fito, ina gaba yana bina a baya. tafiya nake a hankali saboda juwar dake Neman fara hajijiya dani, burina kawai nakai inda 'yan gidanmu suke zaune akan kujeru nima na samu na zauna.
Muna gab da k'arasawa wajen na dafe kaina, sai nayi baya luuuuuu.
Da sauri Galadima dake bayanta ya tareta ta fad'o jikinsa, gaba d'aya 'yan gidanmu da mutanen wajen suka mik'e tsaye cikin ambaton sunan ALLAH.
sosai Galadima ya tallafota jikinsa, yayinda wasu Nurses biyu suka iso da gudu domin kar6ar Munayar.
Amma saiya hanasu yana daka musu tsawa da ambatar su kira Doctor.
Basu ba kowama a wajen saida tsawarsa ta rikitashi....................✍🏼



*_Comments d'inku shike k'aramin k'arfin guywar rububutun nan wlhy, amma da tuni na ajiye saina samu lafiya🤦🏻‍♀, amma yanda kuke k'ok'arin Comments sai bana iya barinku banyiba😃, ina godiya kwarai da gaske, I love you all🥰🥰🥰🥰🥰🤝🏻👍🏻❤_*






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
*_Typing📲_*



*_Haske writer's asso...._*💡




*_♦RAINA KAMA......♦_*
_{Kaga gayya}_



*_Bilyn Abdull Ce_*🤙🏻



~Book 2~ 👉🏻7⃣


................Gaba d'aya ya rikice ya rikita Nurses d'in da jama'ar wajen, cak ya d'auki Munaya, gadonma da aka kawo masa domin d'orata ko kallonsa bai yiba. Wani d'aki suka nuna masa ya shiga da ita.
Da sassarfa doctor dazai duba munayar ya iso, dan dogaran Galadima tasoshi gaba sukaje sukayo.
Kai tsaye Galadima yace baya buk'atar namiji mace yakeso ta duba masa matarsa.
Hak'uri doctor d'in ya bashi, sannan yakira wata likita mace mai suna doctor Farida.
Isowarta yasaka Galadima da yay bake-bake a k'ofar bata hanya ta shiga.
Duk yanda taso yabata waje tayi aikinta yak'i, gashi duk yabi yagama rikitata da tsawarsa.
Doctor d'in da Galadima ya hana ya duba Munaya ne ya matsa kusada su harun yana fad'in “dan ALLAH sir Ku lalla6a yalla6ai ya fito danta samu damar aikinta, wlhy dukya rikitata”.
Murmushi Nuren da isowarsa kenan asibitin aka masa bayani shima yayi, suma su harun duk murmushi sukayi.
Nuren ya kalli baba k'arami yana murmushi, “Abbanmu inharfa bakai kamasa magana ba bawai zai fito baneba”.
Shikansa baba k'arami murmushin yakeyi, koba komai hankalinsu Yakuma kwanciya da zaman 'yarsu inda suke tunanin anfi k'arfinta.
Bayan doctor yabi zuwa d'akin, Galadima dake zaune, kan Munaya na bisa cinyarsa sai murza tafin hannunta yakeyi wai kozata farfad'o, yayinda doctor Farida ke k'ok'arin lik'a mata oxygen ita kuma”.
Shima baba k'arami da k'yar ya lalla6ashi ya fito.

Tsawon lokaci doctor Farida tana ciki bata fitoba. Galadima dukya damu, danma ankawo masa kujera ya zauna, amma sai jan tsuka yakeyi time to time.
Hankalin 'yan gidansu Munaya ma duk a tashe yake, jiran fitowar doctor Farida kawai akeyi dan aji mike damun munayar.
Innarsu Munaya kam gefe ta koma tana sharar kwalla, itakam batasan yazata misalta wannan tsakaniba, miji da 'ya'ya duk babu lafiya, Munubiya ma fa sunacan ana k'ara mata ruwa.
Fitowar doctor Farida yasaka kowa mik'ewa anason jin bayani, Galadima dai yana daga zaune ya zuba mata idanu shima. Doctor Farida tace su kwantar da hankalinsu ta farfad'o, amma tamata allurar barci, yanzu tanason ayo gwajin jinin Munayar data d'iba.
Galadima ya lumshe ido yana ambatar “Alhmdllh” akan la66ansa.
Sauban ne ya kar6a suka tafi shida Sarkin mota lab d'in.
Dr Farida ta kalli Galadima tana murmushi, “ranka ya dad'e zaka iya Shiga ka ganta yanzun”.
Nuren ya kalli Galadima ya jinjina masa kai alamar yaje.
Saida yaja wasu seconds sannan yamik'e cikin takun nan nasa na k'asaita da izza, duk idon jama'ar wajen akansa yake, yana birge kowa.
d'akin ya tura ya shiga, ya taka har gaban gadon da Munaya ke kwance, idanu ya tsura mata, tayi wani fayau da ita, ya jawo kujerar dake wajan ya zauna, har yanzu idonsa na kanta, cikin cije lips da lumshe idanu ya d'ora hannunsa bisa sumar kanta da d'ankwalinta ya zame ta fito, saikuma yasaka d'ayan hannunsa ya shafi kumatunta, a kan la66ansa ya furta “sorry my friend, ALLAH yana tare da masu hak'uri kinji”.
Daga haka bai sake cewa komaiba, ya janye hannunsa daga kanta ya mik'e ya fito.
A k'ofar d'akin ya iske Doctor Farida tsaye, kallonta yayi cikin maganarnar tasa mai kama da an masa tilas yace “zata iya kaiwa wane lokaci bata farkaba?”.
“Ranka ya dad'e inaga daganan zuwa kamar awa d'aya”.
Kansa ya jinjina mata, bai sake magana ba yanufi d'akin da Abba ke kwance. ya Tatar da doctor d'in dake kula da Abban a d'akin.
Da sauri doctor yabashi kujera ya zauna, k'afa d'aya kan d'aya ya d'ora ya Ciro waya a aljihu yana danne-danne. batare da ya kalli doctor ba yace, “kunyi gyaran karayar?”.
Doctor yace, “eh ranka ya dad'e duk an gyara, saidai na hak'ark'arinsa yaso kawo matsala, amma Alhmdllh komai ya dai-daita”.
“humyim, maganar bayanan danace a tattara minfa?”.
“shima komai ready ranka ya dad'e ”.
“o right, insha ALLAH zuwa jibi nakeson mu tafi, amma wai har yanzu bai ta6a farfad'owa bane?”.
“ai ba'a sume yakeba, allurar damuke masace kawai takesakasa yawan barci”.
d'ago ido Galadima yayi yana kallon doctor d'in, yace “amma danme ake masa?”.
“ itace ke taimaka masa wajen rage masa rad'ad'in ciwukan, dan maganar gaskiya yana cikin matsanancin ciwo”.
Cije lips Galadima yayi kawai, yace “ALLAH ya bashi lafiya”.
“amin ya rabbi”. ‘cewar doctor.

Daga haka suka fito shida doctor d'in.
Inda Harun yake Galadima ya nufa, “brother yau ba zakaje aikiba kenan?”.
Kallon agogon hannunsa Harun yayi, sannan ya kalli Galadima, “ka rikitamu ne ranka ya dad'e shiyyasa ban kula time ya tafi hakaba”.
Murmushi kawai Galadima yayi amma baice komaiba.
Harun yay musu sallama ya fita da nufin zuwa anjima idan yatashi aiki zai dawo.
Su yaa Hameed sukai masa godiya da fatan alkairi sannan yatafi.
Daddy ya kalli su yaa Hameed d'in yace ai kuma da tafiyar kukayi, karku makara wajen aiki”.
A ladabce suka amsa masa da to, suna shirin barin wajenne saiga motocin su waziri sun shigo, dole su yaa hameed suka dakata.
Waziri ne da matawalle, sai Garkuwa da baraya, sai kuma wasu manya-manyan 'yan majisar Sarki. dogarai duksun kasa sun tsare, wasuma zato suke sarkinne yazo da kansa.
Su daddy ne suka musu iso har d'akin da Abba yake kwance, sosoi suka nuna tausayawarsu gareshi, sunja doguwar addu'ar samun lafiya da fatan alkairi ga Abba. Sannan suka Isar da sak'on Sarki.
Sun d'an jima a d'akin suka fito da nufin tafiya, a dai-dai time d'inne kuma doctor Farida ta iso gaban Galadima cikeda sassarfa. Bakinta a washe tamkar gonar auduga. Wani dogari Na k'ok'arin dakatar da ita Galadima ya d'aga masa hannu alamar ya barta tazo.
Cikin girmamawa doctor Farida tace “wannan asibiti da dukkan jama'ar cikinsa suna taya masarautar gagara badau murnar samun k'aruwa daga jikin gimbiya Munaya, insha ALLAH nanda watanni 7 dawasu satittika zata zama uwa, ma'ana tana d'auke da cikin wata 1 da sati uku”.
Atare dogarai suka d'auki kabbara, Galadima dake tsaye baki bud'e cikin tsantsar mamaki ya kafe doctor Farida da idanu, sai kawai yashiga zame agogon hannunsa mai masifar tsada da k'yau ya mik'ama doctor Farida.
Sauban yazo ya rungumesa, hakama matawalle.
'Yan gidansu Munaya sai suka koma 'yan kallo kawai, amma bakin kowa yakasa rufuwa.
Doctor Farida ta kalli Galadima cikin mamaki da al'ajabi, “ranka ya dad'e ni Na cancanci wannan agogon mai d'unbin tsada kuwa?”.
Wani murmushin Daba a cika gani Galadima yayiba ya saki, ya gyara tsayuwarsa yana fad'in “idan duk abinda na mallaka a duniya kike buk'ata zan baki shi, saboda wannan shine albishir Na farko da aka ta6amin Na farinciki a rayuwata, kifad'i dukkan abinda kike buk'ata inhar baifi k'arfina ba kafin nabar asibitinnan za'a kawo miki shi”.
Kanta ta shiga girgizawa, kafin ta d'aga agogon ga mutane su gani.
Mamaki ya cika kashe matan gidansu Munaya hassada da al'ajabi ya cika zukatansu, tunma ba'a haifi cikinba Galadima yake wannan rawar kan inaga an haifoshi?, Kansu bai kuma kwanceba saida sukaji waziri da baraya Na sanarda tasu k'yautar ga doctor Farida, hakama matawalle da Nuren.
Doctor Farida fa ta rikice, itakam yau taga farar rana, (🙄idan ta ALLAH ake niya kamata abama wad'annan k'yaututtuka ma😏).

Nuren da matawalle suka hau rabon kud'i a asibitin, tamkar basu San ciwonsu ba.
Waziri kam d'akin da Munaya take kwance aka musu rakkiya, sun mata addu'a kafin su fito, kowa bakinsa a washe, wasukam ta cikin Na ciki kawai😳🤭.

Kafin kace mi labari yagama zagaye asibitin, gidan Sarki kam kafin su waziri su Isa labarin cikin Munaya yaje.

hakama Sauban ya kira su Momma ya guntsa musu, Momma saida tayi sujudar shukur.
Abie bakinsa yakasa rufuwa, kamar daga sama sukaji yace “ALLAH ya inganta”.
Dukda a hankali yayi maganar hakan bai hanasu ganin motsawar la66ansa ba, Khaleel dake kusa dashi yace “Lah Abie yayi magana Momma!!”.
ba momma ba hatta da jakadiya sakin kwanon hannunta tayi ta waigo tana kallon Abie. Aunty Mimi ta tura laptop d'in gabanta tafad'o, hakama Samha wuntsilowa tayi daga kujerar datake zaune tayo inda gadon Abie yake.
Gaba d'aya suka rufu akan abie, kowa yanason sanin gaskiyar batun Khaleel, murmushi Abie yamusu yana jinjina kai alamar gaskiyane, sannan a hankali yakuma furta “da gaske Khaleel yake”.
Ai yau babu kunya Momma ta rungume Abie a gabansu aunty Mimi ta fashe da kuka mai ban tausayi.
Aunty Mimi ta had'a momma da Abie d'in ta rungume itama.
Jikin Samha har 6ari yakeyi takira Number Galadima ta Nigeria.
Ya rako su waziri da zasu tafi kiran Samha ya shigo, bai d'auka ba, itakuma bata gaji da kira ba.
Saida su waziri suka wuce sannan yaciro wayar a aljihunsa cikeda haushin wanene mai nacinnan. yana dubawa yaga Samha Ce.
Murmushi yayi kawai sannan ya kirata da kansa, bugu d'aya Samha ta d'aga, kuka kawai ta fashe masa da shi, zuciyar Galadima tashiga tsitstsinkewa. tsawa ya daka mata yana tambayar lafiya?.
Share hawayenta tayi, murya Na rawa tace, “Uncle Sam wlhy Abie yayi magana, yanzun nan da Uncle Sauban ya kira yace aunty gimbiya nada ciki sai Abie yace ALLAH ya inganta”..
Galadima ya ciro wayar a kunnensa ya kuma kallon number, tunaninsa wasune kawai keson masa yawo da hankali, ganin dai da gaske number Samha d'in ce saiya maida a kunnen, cikin sanyi murya ya kira ainahin sunan Samha, “Zeenah! banason wasan banza kema kin sani”.
“wlhy Uncle ba wasa nakeba, ga Momma ma kaji awajenta”.
Kafin yace wani Abu yaji muryar Momma namasa sallama, yanayin muryarta yasakashi lumshe idanunsa. Momma tace, “Muh'd! Yau ranace dabazamu manta da itaba a tarihinmu, k'yautar abinda kud'i baya saya, ALLAH kuma yabama takawa damar magana, narasa yanda zan musalta farin cikina Muh'd”.
Wasu hawayene suka gangaro a kumatun Galadima, ga murmushi yak'i barin fuskarsa, cikin nutsatstsiyar muryarsa yace “Momma ko yanzu Ubangiji ya d'auki raina yagama min komai, Momma mizanyi duniya tasan ina cikin tsantsar farincikin da tunda nazo duniya ban ta6a riska ba?”.
Dariya momma tayi, tace “godiyar ALLAH ta wadatar da komai Muh'd, lallai yarona zai zama baba”.
Galadima yayi dariya yana goge hawayen fuskarsa, “Momma bama Abie wayarnan”.
Cikin tsokana tace, “nawa zaka biya? kasan mu yanzu komai Na kud'ine”.
Sosai yasaka dariya, har jerarrun hak'oransa Na bayyana. Dogaransa duk sun saki baki suna kallonsa, duk da bajin maganar da yake sukeba, tunda suke da shi basu ta6a ganin yana dariya makamanciyar wannan ba, Sauban kan ai hotuna yaketa masa bai saniba.
“shikenan Momma, inhar baki had'ani da Abie ba kema kuwa d'iyarki bazata dawo India ba ashe?”.
“a'a miyay zafi? indai takawa ne gashi”.
Nanma dariyar Galadima yayi, Abie da tun d'azu yaketa murmushi shima saboda a Hans free momma tasaka wayar duk sunaji, a hankali yace Daddyn Unborn!”.
Galadima baiji mi Abie ya fad'a ba,

Please Login or Register in order to submit comment