Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

addu'ar samun nasara hankalinsu bai kwantaba, Dan sai an kunna Computers d'in zuwa wanu lokaci, idan an tabbatar da samun nasara sannan.


*****

   Hankalim Munaya bai kwantaba saida taga su innaro sun dawo k'alau, babu kunya taita d'aukar yaran tana jujjuyawa wai kozataga wani abinda aka musu, saidai kuma bataga komaiba.


*********


     Baffi ya kalli Galadima dayay shiru ido a lumshe, yace, “Sameer dolenefa komai yazo k'arshe yau, kabi ta hanyar da katsara domin zuwansu hannu gaba d'aya, daga baya saimu cigaba da Neman camera, dan Na tabbata bazasu hak'ura ba, shiyyasa tun a jiya Na sanarmaka”.
    Galadima ya jinjina kansa batare da ya bud'e idoba yace insha ALLAH komai yazo k'arshe Baffi,  safiyar gobe zaku tashi dajin yanda ta kasance, Nuren yana hanyar dawowa. Zamu tafi matakin k'arshe yau”.
  
         Atare suka had'a baki wajen addu'ar ALLAH ya bada nasara.
    Galadima ya amsa akan la66a da amin...............✍🏻




Lallai gobe da kallon kenan. Galadima manmu ka cika musu aiki kawai🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀.







ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏🏼


BOOK 3 👉🏻1⃣4⃣


.................Duk da dai sumbar komai a halin k'ila wa k'ala haka kowa yafito jiki a sanyaye, Baffi da Sir Isa suka wuce, Galadima ma kallon Sauban yayi daya zuba uban tagumi, yad'an murmusa yana fad'in “Haba autan Momma, miye kuma Na damuwar haka? katashi kuwuce kawai kar yamma tayi”.
         Shagwa6e fuska Sauban yayi yana kallon yayansa, yace, “please Yaa Sam kabarni sai gobe saina wuce insha ALLAH”.
       Galadima yay shiru alamar tunani, saikuma ya girgiza kansa, “uhm-uhm Sauban ka wuce yau, Dan gobennan akwai riski”.
       Kamar Sauban ya tambaya dai amma yay shiru, yasan halinsa mawuyacine ya sanar masa. Dan haka saiya amsa da to kawai. Badan yasoba yaymusu sallama shima driver dazai kaisa yad'aukesa suka tafi.
       Ajiyar zuciya Galadima ya sauke, zuciyarsa Na k'una da tsantsar damuwa.
      tausayinsa ya kama Muftahu dake zaune shima yayi shiru damuwa da tausayin d'an uwan nasa fal ransa.


★★★★★★

     Gaba d'aya zuciyar Munaya takasa sukuni gameda yanda taji muryar Galadima, tunda kuma aka maido yaran saita kasa zaune ta kasa tsaye, Munubiya dai da innarsu duk suna hankalce da ita, kamar Munu zata shareta saidai tamata magana.
     “Nikam aganina da wannan zagaye-zagayen da kiketayi Sweetheart ai gara ki kirashi kisan damuwarsa, koma ladan kwantar masa da hankali k'yasamu”.
       Munaya dake kwance akan gado ta kifa meenal saman cikinta datai barci ta kalli Munubiya, amma sai munu ta basar tamkarma ba ita tayi maganarba. Ajiyar zuciya Munaya ta sauke, yayinda Munubiya ta tashi tamayi ficewarta daga d'akin duka, harta fice Munaya nabinta da kallo, saida tabar ganinta sannan ta janye idonta a k'ofar tana cigaba da shafa bayan meenal.
           Shawarar Zuciyarta dake cigaba da k'arfafa mata shawarar y'ar uwarta ta addabeta da k'awato mata Galadima a damuwa, da alk'awarin dataima Mahaifiyarsa. Kasa daurewa tayi saboda tausayin ahalinsa dashi kansa daya kamata, ta jawo wayar tana lalubo number sa, dukda k'irjinta Na dukan gama-goma Na tsoron tsawar daya mata d'azu da yanda suka rabu jiya. Haka dai ta dake tayi dialing number sa.

      Galadima suna zaune cikin halin shiru da Neman mafita a zukata shida Muftahu kira ya shigo wayarsa, sharewa yay tamkarma bai jiba, ganin zata tsinke muftahu ya taso yay picking da sauri ganin My Mata yasan dai Munaya Ce, a kunne ya saka masa, Galadima ya bud'e jajayen idonsa ya kallesa, Muftahu yamasa alamar please da fuska.
     Baice komaiba ya kar6a wayar yana maida idanunsa ya lumshe, Muftahu kuma ya fice abinsa.
     Munaya tayi shiru takasa magana, kamar yanda shima yak'i cewa k'ala, sai sautin ajiyar zuciyarsa take jiyowa kad'an-kad'an, daurewa tayi tace, “Assalamu alaika”.
       Dukda yasan itace saida yaji sanyi a ransa, Dan ita kad'aice kemasa haka a waya ya jure, saida ya d'auki wasu seconds kafin ya amsa sallamar.
      Yanda ya amsa sallamar kawai ta tabbatar akwai matsala, Cikin aro jarumta tace, “Ranka ya dad'e barci kakeyi?”.
      Yad'an murmusa, a zuciyarsa yace yarinyarnan a kwai wayo, “Uhm-uhm”. ‘yafad'a a sanyaye’.
       Ganin tafara samun dama saita kuma saita muryarta tace, “'Dan gatan Abie, to mikakeyi ne haka? naji muryar taka can k'asa”.
       Zamewa Galadima yayi ya kwanta cikin kujerar, yanzunma tamkar bazai amsaba, saida ya gama basarwarsa sannan yace, “k mikikeyi?”.
     Munaya tayi murmushi mai sauti har yana jiyowa, ta shafa kan Meenal tana fad'in “kwance kawai nake ina tunanin rayuwa da abinda ta k'unsa, harma da Wanda ke gudana a cikinta”.
     Yace, “Humm kamar mikenan?”.   
       “Kanason ji?”.
 Ya kuma cewa  “Uhm”.

     “humm yalla6ai nakula duk yanda bawa yakai da samun komai Na rayuwa saikaga wata damuwa ko tawaya mai kutse acikin al'amuransa, bana manta maganar nan taka da kata6a fad'amin wani lokacin murmushin da jama'a kanyi iyakarsa fuskane, amma zuciyarsu sune kad'ai sukasan sirinta, lallai wannan gaskiyane, amma kasan mike birgeni da k'aramin k'warin gwiwa a rayuwata koda ace Na tsinci kaina a fagen sanyin jiki?”.
      Galadima yace, “uhm-uhm”.
       Munaya ta sauke wata sassanyar ajiyar zuciya da Galadima yajita har cikin ransa, yayinda wani Abu ya tsarga masa ta cikin kai har zuwa yatsan k'afa, ya gyara kwanciyarsa yana jiran jin mizatace.
        “Komai girman fad'uwa inhar da yak'inin HAK'URI dana k'arfin ZUCIYA to lallai akwai tagomashin sirrin samun NASARA, hak'uri da juriya basa ta6a zama fad'uwa, inhar kaga bawa yayi hak'uri babu kuma NASARA a ciki to lallai hak'un nasa kad'anne, sometimes gaggawa aikin shaid'anne, saikuma ansha wahala ake shan dad'i, abinda kawai muke kasa fahimta shine riba akan sameta ne a muhalli biyu, walau a duniya kokuwa a lahira, duk wadda bawa ya samu sunanta nasara, amma kowa yafi fata da samun ta duniya, saidai ta lahira ita yakamata mufi d'oki da addu'ar samu, meybe tazame mana tsani Na zuwa inda bamuyi zatoba, hikimar Ubangijice yabaka nasarar anan kokuma a can, Dan babu yanda za'ayi a zalunceka mai kowa da komai sarkin Rahma da jink'ai ya bari, bai yarda da zalunciba, yakuma haramtashi agaremu mu bayinsa”.
        Wasu k'ananun hawaye suka gangara ta gefen idon Galadima, fuskarsa d'auke da murmushi, yayinda kalaman munaya ke tasiri adukan magudanar jininsa da zuciya, wata nutsuwa ta musamman daya rasa tashiga ratsashi da bashi k'arfin gwiwa, a hankali yace, “ke y'ar baiwace matar Contract”.
     Dukda maganar k'arshe ta sosa zuciyarta saita murmusa, cikin kuma kwantar da murya tace, “Ni a suwa Mijin contract ”.
      Ya d'an dara batare daya shiryaba. Yace, “one-one kenan?”.
         Munaya tayi dariya tana fad'in “nidai bada manufa na fad'aba”.
      “Fad'i gaskiya dai yalla6iya tsiwa”.
     “Gara mai tsiwa da miskili, koba komai akansan muna waje ai saboda tsiwarmu”.
       Galadima ya kuma Murmusawa. Yace, “ki kiyayi randa zan kamaki ALLAH”.
       Itama dariyar tayi. Tace, “yalla6ai ka fad'i wani Abu nabaka k'yauta mana”.
      Yay d'an jimm tunanin mikenan?, saikuma yayi ajiyar zuciya yace, “mikenan?”.
      Cikin wani salo Munaya tace, “R. Ita kawai nakeson ji a harshenka”.
       Lallai yarinyarnan taga gadon barcinsa wlhy, yay maganar a zuciya fuskarsa na k'awatuwa da murmushi. yace, “Okay, kibari sai ina gabanki”.
        “Tab, Indai ba yanzuba na fasa”.
      “uhmyim, miye na karayar hajiyar tsiwa?”.
       “Aiba karaya nayiba, lokacin kawai kabari ya wuce, ni karmafa yarannan suma su gadoka”.
     “Dai-dai kenan ai y'ammata, kokin manta k'yan d'a ya gaji ubansa”.
     “Humm Alfahari kenan, ita uwa an rainata”.
     Dariya tabashi, amma ya daure baiyiba. Yace, “keda kike gudunsu mizaisa su gadoki?”.
        Munaya ta d'an ta6e baki, cikin juya idanu tamkar tana gabansa tace, “yanzu kana ina?”.
       Murmusawa yayi saboda basar da maganar da tayi. Yace, “kinason ganinane?”.
       “A'a, son sani kawai nake”.
      “Humm, naje tad'i to”.
      Shiru munaya tayi, sai kuma ta d'an dara, “Yalla6ai kasan wani Abu kuwa?”.
     “Saikin fad'a”.
Cikin danne dariya tace, “irinku kwantai kukeyifa, sai anyima y'ammata tallarku asamo mai taimakonku ta aura, kaima nasan saisu takawa sunmaka haka.....”. Sai yaji kitt, ta yanke wayar.
       Wani k'asaitaccen murmushi ya saki yana shafa kumatunsa, ya d'ora wayar saman cikin sa yana fad'in “lallai yarinyarnan kin girma, zaki tabbatar nayi kwantai kuwa”.
       Daga canma Munaya dariya taketa k'yalk'yatawa, harta tada Meenal, Mununiya datun d'azun take kallonta ta bayan labule bata saniba tayi murmushin jin dad'i itama tana share hawaye, tanason y'ar uwarta sosai, sannan wayonta da iya mu'amullarta na birgeta, tabbas Munaya tanada tsiwa, amma tanada wayo, inhar zaka takurata bazata ta6a raga makaba, amma tanada tausayi dason ganin farincikin wani koda ita zata rasa nata farincikine, gakuma son girma uwa gyambo, tanason komi zaka mata ka nuna muhimmancinta a gareka, a fili tace, “ALLAH yakawo farinciki mai d'orewa a ratuwarki kema y'ar uwata”.


  Amin munu😘☺.


★★★★★★★★

     Tunda Muftahu ya shigo yakebin Galadima da kallon mamaki, ganin yasake yanata fara'a tamkar ba shine a matsananciyar damuwa yanzunba, ya zauna zuciyarsa na addu'ar samun mace tagari, dan lallai MATAN KWARAI RABIN ADDINI ce.
       Galadima ya hararesa yana tashi zaune, “malam lafiya ka k'uramin ido?”.
     Dariya Muftahu yayi sosai, yace, “to miye na tsarguwar ranka ya dad'e, wlhy kuna sha'aninku kaida gimbiyarka, yanzu nan harta saukeka daga hawa saman da kayi”.
    Filo Galadima ya jefama Muftahu, shikuma ya cafe yana dariya.
    Galadima ma murmushin yayi yana danna kiran Sauban. Dan yasan har yanzu yanacan cikin damuwa. Hasashen nasa kuwa yayi dai-dai, Dan har yanzu muryarsa a cinkushe take. Amma jin ta Galadima a sake sai farinciki ya kamashi, cike da zumud'i yace, “yaya an dace ne?”.
     Murmushi Galadima yayi mai sauti, yace, “muna fatan hakan autan Momma”.
      Alhmdllh Sauban yashiga jerowa, saiya saki jikinsa kuma harda tsokanar Galadima yana dariyar k'eta.
      Galadima dai murmushi yakeyi yana girgiza kai, ya yanke wayar zuciyarsa na addu'ar ALLAH ya saka farinciki a zuciyar Munaya fiye da yanda ta sakasu. Massage ya tura mata sannan ya kalli Muftahu yana gyara zama.


      Munaya na kwance har yanzu takasa fita, tunda tasamu Meenal ta koma barci saita lumshe ido tana dulmiya duniyar nazari, shigowar sak'one ya sata bud'e ido ta jawo wayar. Ganin Galadima ne saita mik'e zaune babu shiri, sak'on ta bud'e.

         “Kin yaudareni da zance banko tambayi yaya jinin jikina sukeba yalla6iya, to ki shafamin kansu.
      ALLAH ya sanya farinciki a rayuwarki fiye da yanda kika Sani.

     Wasu hawayen farinciki suka gangaro a kumatun Munaya, bata ta6a tunanin shirmen datake masa yanayin tasiri a zuciyarsa ba, Dan bai ta6a nuna mataba, a fili ta furta “ALLAH na gode maka dana zama sanadin saka wani bawa naka farinciki a lokacin jarabawar damuwa ta lullu6e jinsa da ganinsa da zuciyarsa”.
     

  Amin munaya, muma Ya ALLAH kabamu ikon bama bayinka muminai gudunmawar farinciki mai amfani koyaya ne, amma bata hanyar sa6onka ba ko take k'a'idar daka shinfid'a mana, amin👏🏻😭.


*********

        Muftahu da Galadima suka fito, yauma bai zauna bayaba duk yanda Muftahu yaso hakan, dama yay masa maganar zama bayan hararsa yayi, dole yaja bakinsa yay shiru yana murmushi.
       Wani wajen cin abinci Muftahu ya tsaya, ya kalli Galadima dake kwance jikin seat ya lumshe ido yace, “ranka ya dad'e Dan ALLAH ina zuwa”.
       Kai Galadima ya jinjina masa kawai batareda ya bud'e idoba, Muftahu ya fita, mintuna 15 saigashi ya dawo hannunsa d'auke da ledoji, ya bud'e seat d'in baya ya ajiye, sannan yadawo mazaunin driver yana maba Galadima hak'urin jira.
    Baice dashi komaiba, Dan tuni yama lula wata duniyar.
     Gidan gonar Nuren suka nufa, inda su Harun suke a ajiye, a falo suka yada zango, ko ina k'al yake a tsaftace ga k'amshi, cikin masu kula da gidan gonar ya shigo d'auke da wankakkun y'ay'an itatuwa masu k'yau, zubewa yay yana kuma kwasar gaisuwa, Muftahu ne kawai ya amsa, Galadima hannu ya d'aga masa.

      Muftahu ya bud'e abinda ya siyo yana fad'in “Ranka ya dad'e mizakaci?”.
     Cikin d'an ta6e baki ya girgiza masa kai alamar bazaici komaiba.
      “Okay, to bara na kira Gimbiya meybe ita ta saka kaci”.
      Bud'e ido yayi yana zubama Muftahu harara, shikuma ya fuske tamkar bai ganiba.
     Saida Muftahu yasha fama kafin Galadima ya yarda yad'anci abinci, rabima duk fura da kayan itatuwan ne yasha. Sunkai 1hour da shigowa ya buk'aci ganin Harun da SD.
    Sun fara shiga d'akin da harun yake, bayan Muftahu ya saka key ya bud'e matsawa yay yabama Galadima hanya yafara shiga, takun takalmansa ya saka Harun dake zaune bakin gadon d'akin kansa a duk'e d'agowa, kallon ido cikin ido sukaima juna, Galadima ya janye nasa cike da basarwa yana wani miskilin murmushi mai k'ona zuciyar mak'iyi.
    Harun ma janye idanunsa yayi yanajan tsaki, Muftahu kuma ya ta6e baki yana gyarama Galadima kujerar zama.
      Galadima ya zauna idonsa akan harun, hannunsa ya mik'a ya kar6i lap-top d'insa dake wajen Muftahu, ya d'orata bisa cinya sannan ya janye idonsa ga harun dayak'i sake kallonsa, lap-top d'in yafara dannawa cikeda kwarewa, cikin seconds dabasufi 10 ba ya d'ora lap-top d'in saman stool d'in da Muftahu ya sake ajiyewa, sannan yay playing abinda ya kunna yana hard'e hannaye a k'irji da zubama Harun ido.
    Harun har yayi tamkar zai share sai dai ya kalla lap-top d'in, Wato shine a ranar sunan y'an uku gab da za'a sace yaran shida d'aya daga cikin kidnapers d'in.
       “Bibo inaso Ku tabbatar da kun kwashe yaran, karku kar6i wad'anda suke hannun k'annen matarsa, Dan na bogine, baby dolls ne aka sakama kaya irin na yaran domin kauda hankali, Sameer yanada wayo fiye da yanda kuke tsammani, Dan haka kuyi komai cikin kulawa da taka tsantsan, dai-dai lokacin da wutar hotel d'innan zata d'auke, zan kwashe yaran insha ALLAH, harsai nabar cikin hotel d'in ni da ku sannan za'a kunna, ina fata ka fahimta”.
      “Eh na fahimta ranka ya dad'e, namaka alk'awarin ko y'ay'an sarkine bana Galadima ba yau saisun kwana a alahira”.
     “No, banason su mutu yanzu, sai shi ubansu ya d'and'ana d'acin rashinsu, yana gab da mutuwa sai a kawo masa gawarsu, daganan shima kaga ai sai tafiya shida wannan tatsitsiyar matar tasa y'ar bayi”.
      “Okey nagane boss”.
       Mamaki ya kama Harun har Muftahu. Zuciyar Harun tamkar zata fad'o waje dan mamaki, ya akai Galadima ya d'auki wannan video d'in, bayan dukkan CCTV cameras d'in dake hotel d'in saida suka saye mai kula dasu na hotel d'in aka tsayar dasu daga aiki........
     Murmushin da galadima yayine ya katse tunanin Harun , cikin lumshe idanu da kad'a kai ya gyara zamansa, cikeda izza yace, “Abin mamaki ko? haka nake ni dama, kullum cikin bada mamaki, tabbas 6oyen dakai masa bazai yuwu muganiba, saidai kamanta da koda ace banida hanyar ganin naka idan ubangiji bai k'addaro ruhi na kona y'ay'ana ko matata zai salwanta a hannunka ba babu yanda ka iya, kana tunanin duhu da tsayar da cctv d'in hotel d'in zai baka dukkan dama ko? To kayi kuskure dan Muhammad Sameer kansa cctv ne, eyeglasses d'in dake idona komai duhun waje shi zai haskokane, dan camera d'in jikinsa tana tareda komai, kasan miyasa nabaka damar d'aukar yaran? Saboda hakan yana cikin k'addararsu, nakuma barka dasune danna kafa maka tarkon neman hujja da tabbatar da abinda Muftahu ya sanarmin”.
     Muftahu ya d'age gira saboda kallon tsana da Harun ke masa.
     Murmushi Galadima ya kumayi yana cigaba da fad'in “ka kira matata tatsitsiyar yarinya y'ar bayi ko? Saikuma abin mamaki ita wannan y'ar bayin, tatsitsiyar ce ta zame maka RAINA KAMA, dan lallai gashi zakaga GAYYA. itace ta haskomin kai a cikin madubin fik'irarta tunkan Muftahu ya sanarmin, takuma koyamin yanda zan fahimci makircinka da nagartar Muftahu, tabbas na yaba ma basirarka Harun, kanada basira k'warai da gaske, tunda kasan kanka kake a jikina kana cin dunduniyata, ni matsayin aboki d'an uwa mafi kusanci nake kallonka, kamar yanda mahaifina yarink'a kallon mahaifinka, ashe kud'in duk kaskane a garemu, nayi imani da cewar lallai ku jarabawane a garemu, kamar yanda k'addarar auren Munaya tazamema rayuwata alkairi, a kullum cikin aibanta Muftahu da bak'antashi kake a gareni, ashe kaine bak'in ba shiba, mimuka muku ni da mahaifinane haka da zafi? Nawa suka biyaku kuke cutar damu.............?”.
https://2gnblog.blogspot.com/
       “Sameer!!”. Harun ya kirayi sunan galadima cikin fushi, ya mik'e tsaye sunama juna kallon ido cikin ido shida galadima, cikin matsannan ciyar tsanar juna.
       “Kabar alfahari magen matarka tamaka bajinta, shawarama zan baka ka janyeta cikin wannan hargitsin, danko ubanta daya shiga a had'ari yake balle ita karan kad'a miya, wlhy Sameer ban ta6a k'aunarka ba, bakuma zan ta6aba har abadan, domin tsakanina dakai BASHIN GABANE, dan haka banida lokacinka yanzu har sai Camera ta dawo hannunmu, bar ganina anan a rufe, akwai mai sarrafa dukkan tunanina a waje, yarage naka kanemi hanyar kare Surukinka kafin aikinmu yazo kansa...”.
      A fusace Galadima ya mik'e shima yana dunk'ule hannu, amma sai Nuren daya shigo yanzu ya rik'eshi, “relax my brother, kainefa ka ta6a fad'amin ba'a maidama abokin gaba murtani da murtani, sannan ba'a bashi damar sanin sirrin yak'i sai an had'u a filin daga”.
      Galadima ya saki hannunsa daya dunk'ule da bakinsa daya cije, yatsunsa ya kad'a suka bad'a k'ara d'as! 'Das! Sannan ya zagaya hannunsa a wuya alamar I will kill you.
       Cikin d'aga murya Harun yace, “d'an halak ka fasa Sameer!”.
     Daga Nuren har Muftahu da Galadima babu Wanda ya amsa masa, a falo suka tsaya, Galadima ya Nufi d'akin da SD yake batare da yace uffanba,
    Nanma dai Muftahu ya bud'e masa, ya shiga cikin tsananin fusatar da Harun ya sakashi. zauna suka iske Alhaji Darma cikin kujera yana duba jarida, kaikace a d'akinsa yake.
     Galadima ya taune lips nashi tamkar zai hudasu da hak'ori, zuciyarsa Na k'una, lallai sai Harun da ubansa sun k'are rayuwarsu a jail inhar yana numfashi, dan barin irinsu a duniya had'arine babba, musamman a gida irinna sarauta.........
    Nuren ya katse masa tunani ta hanyar yima SD magana.
     cikin ta6e baki Alhhaji Darma ya kalli Galadima yana wani murmushin mugunta, ya ajiye jaridar hannunsa tare da hard'e k'afa.
      A bakin gadon Galadima ya zauna, ya kalli Alhaji Darma, sosai Darma ya tsorata da rinannun idanun Galadima, amma saiya dake.
     Galadima daya lura da rikitar Darma ya murmusa, cikeda k'asaita ya d'age girarsa, “Alhaji Shehu kenan, angaya maka mutum yakanci bashi ya kwana lafiya, duk wata jarumta da zaka aro kasama ranka tuni nagama bitar karatu a kanta, karigada ka shigo ramin damusa iya gudunka babu wajen 6uya, bama duk wannan ba, minene had'inka da surukina? Sanann minene yasa kuka kashe mijin y'ar uwata? Dan ko tantama banayi da hannunka a cikin kisanshi!!”. Galadima ya k'are maganar cikin matsanancin tsawar data rikita Alhaji Darma.
     Dukya rud'e yarasa ina zai kama, cikin in ina yace, “Ni sharri zakaimin bansan komai akan mutuwarsa ba”.
      Galadima yay dariya, saikuma ya gimtse fuska. Yace, “Okay, babu hannunka amma kake tursasa yarinyarsa Samha ta dinga d'akko maka sirrikana tana kawo mata? Kullum kana ma yarinya barazana da mutuwa ko? Alhaji shehu aini tun ranarda mijin aunty Mimi zai koma ga ALLAH naga idonsa ya tsaya cak akanka lokacin da numfashinsa ke bankwana da duniya na d'ora alamar tambaya a kanka, sai kuma yanda kake kaffa-kaffa da Samha a gaban mutane, yayinda itakuma take a d'arare dakai, dukkan wayar dakake mata kana sakata sato maka sirrina INA kan sani, dan nine da kaina nake ajiye mata tagani danta tura maka batareda ita kanta ta saniba, shiyyasa na jata jikina fiye da kowa a gidanmu, duk abinda Sameer zaiyi cikin ilimi yakeyinsa Darma, koda yake bamuzo wannan matakinba, miye had'inka da surikina?”.
       Alhaji Darma dake a rikice saboda tsoro da tashin hankalin zantukan Galadima ya had'iye yawu da k'yar yana fad'in, “B..babu ruwanka da abinda ke tsakanina dashi kuma”.
      “Hummm". Galadima ya fad'a cikin cije lips, wayarsa ya d'akko ya kunna wani recording daya nad'a a wayar Darma ranar da suka kamoshi kafin su d'akkoshi.
        Waya yake da wani cikin tsananin fusata, “Boss wai miyasa bazamu aika shegenan barzahu ba idan yak'i bamu Camera d'innan? Tunda munada hanyar da zamubi mu kar6a d'in, Nibansan miyasa kuke cewa abishi mataki-mataki ba, kasanfa y'arshi yaronan Sameer take aure, yanada hanya mai sauk'i dazai bashi camera d'innan, shi wancan banzan Alhaji Halluru babu tsiyar da y'ay'ansa zasuma mutane, kullum sai tsarin banza yake mana”.
       “Karka damu Alhaji shehu, mu bashi damar k'arshe daya buk'ata, tunda ya tabbatar mana a wannan karon zai kar6o camera d'in ta hanyar matan y'ay'ansa,  yana son takara, yakuma San inhar burinmu bai cigaba shida takarar Governor saidai kallo”.
      “shikenan boss, bara naje ance nayi bak'o”.
     “Ok ngd”.

   Galadima ya gimtse recording d'in dai-dai nan yana murmushi da kallon Alhaji Darma dake tsuma dukan jikinsa na 6ari.
     Cikin d'age gira Galadima yace, “wannan ma ba matsalata bace? Kasanfa shikad'ai ya isheni hujjar gurfanar dakai gaban K'uliya, shikenan babu girma babu mulkin da ake mana Homa da tak'ama dashi right? ”.
      Mi Nuren zaiyi kuwa inba Bushewa da dariya ba, dan yatuna Alhaji Shehu ne yafad'ama Galadima maganarnan randa suka kamoshi.
       Cikin Fusata Darma yake kallon Muftahu da Nuren dake dariya, ya mik'e tsaye yana nunasu da yatsa, “y'an samari lokacin dariyarku baiyiba, dan camera d'in da kuke farfagandar nema tana gab da zuwa hannunmu, kunga kuwa ai kune abin dariya”. Ya k'are maganar da kwashewa da dariya.
     Dukda furucinsa ya daki zuciyar Galadima bai nunaba, saiya mik'e yana murmushi da kallon Darma. Yace, “lallai kaine ka cancanci ayima dariya, indai camera ce tadad'e da zuwa hannuna”.
    Yana gama fad'a ya fice, su Nuren suka kuma sanya dariya, dukda yanayin Galadima ya tabbatar musu akwai matsala. Sunama Alhaji Darma dariya suka fice abinsu daga d'akin.

    A falo suka iske Galadima yanata safa da marwa cikin tsantsar damuwa, sai danna waya yake yana sakawa a kunne alamar Neman wani tak'i shiga.
     Cikin sassarfa duk suka k'araso garesa suna tambayar lafiya?.
       Bai tanka musuba, saboda Munaya ta d'aga wayarsa, “Abba ya dawo kuwa?”. abinda kawai yace mata kenan.
      A tsorace tace, “Miya farune?”.
     Tsawar data rikitata ya daka mata, “ya ina tambayarki kina tambayata?”.
       Cikin in ina tace, “Kayi hak'uri, bai dawoba”.
   “ya salam” yafad'a cikin dafe kai. yace, “Kinyi waya dashi? Ko kinji wani yayi waya dashi?”.
     “A'a gaskiya, Jiya da safe dai nayi waya dashi nida Munubiya, amma yau ko innarmu banji sunyi wayaba.......”
    Cikin katseta yace “kinga maza bincikamin waye yay wayar k'arshe dashi a gidanku, sannan kuma awa nawa dayin wayar”.
      “Okay” munaya tafad'a tana yanke wayar.

     Shima wata Number yashiga nema yana fad'in “Lallai akwai matsala, tunda kukaji Harun da Alhaji Shehu sun fad'a to sunsan misuka shiryama Abba, gashi nabaza su Ameer sumin wani aikin...” ya k'are maganar da saka wayar a kunne saboda daddy ya kira.
          Bayan sun gaisa ya tambayesa ko sunyi waya da Abba a yau?.
       Daddy yace, “eh da asuba yakirashi akan zai dawo yau”.
       Galadima yace, “Alhmdllh Dady wace number ce?”.
      Dady yace bara Na turo maka.
    Koda Galadima ya yanke wayar saiya kira baba k'arami shima, shima ya tabbatar masa sunyi waya da Abba bayan fitowa salla, Dan wannan al'adarsu Ce ko a ina wani cikinsu yake saisunyi gaisuwar safe da bankwanan kwanciya barci, sannan idan wani cikinsu yayi tafiya zai kira y'an uwansa yayin dazai kamo hanya.
          Hankalin su Nuren ma duk a tashe yake, balle uban gayya Galadima.............✍🏻



🙆🏽Turk'ashi, ana wata ga wata kuma🤦🏻‍♀.
       Lallai yaukam tura na shirin kaiwa bango🤦🏻‍♀.







ALLAH ya gafartama iyayenmu😭👏🏻





Typing📲



💡HASKE WRITERS ASSO....


♦RAINA KAMA...!!♦
(Kaga gayya)


Bilyn Abdull ce🤙🏻
__________

Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, ya Ubangijin Al'arshi kama mahaifin takwara (Bily s Fari) rahama, ka yalwata kabarinsa da Ni'ima, ALLAH ka yafe masa, harda iyayenmu😭👏🏻.
Takwara ALLAH ya k'ara mana hak'urin rashinsu, muma ALLAH yasa randa zaka d'auki ranmu muna cikin masu imani da tsoronka, da soyayyay Manzonmu ANNABI MUHAMMADU S.A.W.😭😭👏🏻

__________

BOOK 3 👉🏻1⃣5⃣


.................Duk da Munaya a rikice take haka tayi jarumtar danne zuciyarta, cikin hikima ta dinga bin jama'ar gidan d'ai-d'ai tana tambayar wad'anda tasan Abba zai iya kira kai tsaye, amma kowa yakance tun daren jiya basuyi wayaba, hankalinta a tashe ta sulale gidan innaro ba'a saniba, itama dai tace tun bayan sallar asuba bai sake kiranta ba. Munaya tafito jikinta sai rawa yake, kiran Galadima tayi, lokacin yana waya, tamkar zata fasa kuka ta cire wayar daga kunnen ta, tana niyyar sake kiranshi saigashi ya kirata.
Da sauri ta d'aga.
Yace, “yauwa Yayi waya da wani?”.
Muryarta na zuga alamar tahowar kuka tace, “A'a, innaro kawai ya kira bayan sallar asubahi, amma yau koda su innarmu baiyi wayaba”. ta k'are maganar hawaye na gangarowa a kumatunta.
Galadima ya furzar da huci daga can, a hankali yace, “Munaya”.
Muryarta na zuga ta amsa tana share hawayen da bakin hijjab.
Had'iye abinda ya tsaya masa a mak'oshi yayi da k'yar, muryarsa takuma komawa can k'asan mak'oshi, cikin sigar lallashin da Munaya bata ta6a sanin galadima ya iyaba yace, “insha ALLAH babu abinda zai faru da Abba, kiyi mana addu'a, sanan karki sanarma kowa wani Abu har inna, wayarki tazama kusa dake, Dan zan dunga kiranki idan buk'atar hakan ta taso”.
Munaya takuma goge hawayen dasuka gaza tsayawa, cikin had'iye kukan tace, “ALLAH yabaku nasara, ya tsareku da tsarewarsa”.
“Amin ngd”. Galadima ya

Please Login or Register in order to submit comment