Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Muna sauka kuwa cikin mutunci akazo aka d'aukemu zuwa matsakaicin gida dazai d'aukemu babu wata takura.
Har kuka saida nayi a 6oye ganina a inda ban ta6a zato ko tsammaniba, kasa mai tsarki.
Hutun wannan ranar kawai muka samu, washe gari muka duk'ufa ibada da godiyar Ubangiji bisa ga ni'imomi dayay mana badan munfi sauran bayinsa da komaiba.

Tsawon kwana goma muna bautar Ubangiji, a randa ake saran ganin wata jirginmu ya d'aga zuwa k'asarmu ta haihuwa, Abie da Momma sunfi kowa zumud'i da k'aguwa.
Babu wanda yasan da zuwanmu sai Sarkin Mota, shima kuma bashi da tabbacin dawa za'azo d'in, Galadima dai yace ya saka a gyara masa 6angarensa da inda su Aunty Mimi ke sauka.


*****

Jirginmu ya sauka 9ja k'arfe 11:30pm. Mu muka fara fitowa, Abie da Galadima suka zama k'arshe.
Abie na sauka a jirgin yana Murmushi da hawaye, tareda shak'ar iskar k'asarsa daya bari tsawon shekaru, yama fidda ransa da kuma dawowa cikinta har Abadan.

Sarkin Mota da dogaran Galadima suna zaune a airport d'in suna jiran isowarmu.
Ganinmu da yawa yabasu mamaki, amma saisuka zube suna gaishemu, a cikinsu babu Wanda ya gane momma da Abie, Bama zai yuwu su ganesu d'inba, tunda sanda yabar k'arsar duk basa a wannan matsayin, sai dai iyayensu, wanda a halin yanzu mafi yawa acikinsu duksun rasu ma.
Dole saida muka k'ara da motocin haya, Momma da Abie suka shiga wadda sarkin Mota ke ja, Ni da Galadima da Samha muka shiga ta haya d'aya, Aunty Mimi da Yaa Sauban da yara suka shiga d'aya.

Mun Isa Masarautar tsit babu yawan hayaniya alamar mafi yawan al'ummar cikinta sun nutsu waje d'aya, sai wasu tsirarun hadimai dake kai kawo mussamman masu tsaro.
Duk muka fito amma banda su Momma, Galadima ya nufi mortar dan son taimakawa Abie fiwo, Sarkin Mota kuma na k'ok'arin biyan masu motarnan kud'insu.
Fir Abie yak'i fita, yace d'an uwansa mai martaba ne kad'ai zai fiddashi a motar, duk rok'on da sukai masa fir yak'i, gashi yanata sharar hawaye da handkerchief.

Galadima yasan yanzu Mai martaba ya shiga ciki, maybe ma matar dake dashi taje.
Rasa yama zaiyi yayi.
Momma Ce tabashi shawarar kiran wayar mai martaba, cikin damuwa Galadima ya kar6a wayan Sauban dabe dad'e da barin k'asarba, sim card d'insa zaifi saurin aiki fiye da nashi.
Hadiman gidan sund'an fara fuskantar akwai matsala gameda tsayuwar su Galadima, dan wannan ba halinsa bane.

ALLAH ma ya taimaka Mai martaba baiyi barciba, yana zaune ne yana duba wasu takardu, matarsa ta biyu na tare dashi dan yau kwanantane. Ya dad'e yana kallon wayar da nazarin mai kiransa, dan ba kowane keda Number mai martaba, sai jiga-jigai irinsu Galadima d'in.
Tamkar bazai d'aukaba yad'ai d'auka tana gab da katsewa a kira karo na biyu.
Cikeda girmamawa Galadima ya gaishesa sanann yay masa bayanin shine.
Da farko mai martaba tsorata yayi, dan babu Wanda yasanar masa Galadima ya dawo, cikin hikima da girmamawa Galadima yayma mai martaba bayanin yafito yaga abin mamaki a k'ofar sashensa.
Sosai mai martaba yayta juya kalmar abin mamakin, hakama matarsa, alk'yabba ta d'akko masa ya saka sannan suka fito a tare.
Jakadiya na niyyar tafiya makwancinta taci karo da mota a k'ofar turakar mai martaba, mamaki ya kamata, zatayi magana saitaga Galadima dake tsaye a jikin motor, ta rusuna tana gaisheshi, kamar yanda yasaba ya d'aga mata hannu cikeda izzar mulki.
Bata fita a mamakinba taga mai martaba da matarsa sun fito.
Galadima baice komaiba sai bud'e murfin motar da yay yana nunama mai martaba ciki da hannu.

Jikin baiwar mama Fulani mai kai mata rahoton motsin kowa na rawa ta nufi sashenta, hartayi shirin barci ma ta sallami Kuyanginta, amma dayake baiwar tanada fada sosai a wajen ta saita mata knocking k'ofa.
Cikeda masifa da izza mama Fulani ta bud'e k'ofar, jikin baiwarnan na rawa ta zube k'asa tana fad'in “Ki gafarceni ranki ya dad'e, abinda nagano yafi k'arfin barinsa zuwa safiya, yalla6ai Galadima ya shigo fada shida sauran iyalan tsohon sarki, maimakon yawuce sashensa tamkar yanda ya saba saiya nufi turakar mai martaba kai tsaye, gashi can naga yana nuna masa Abu amota, ban tsaya ganiba na nufo gareki ya uwar gijiyata”.
Ai mama Fulani bata tsaya bata amsaba ta figi alk'yabba ta saka tana fitowa, baiwarnan ta take mata baya.

A can kuwa Mai martaba da mamaki ya kalli Galadima, amma sai Galadima ya girgiza masa kai yana sake nuna masa cikin motar.
Matsawa mai martaba yayi sosai domin ganema idonsa abinda d'an d'an uwansa keson ya gani, Momma ta kunna fitilar dake motar dukda haske mai k'ayatarwa daya haske ko ina na masarautar.
Koda mai martaba ya lek'a saiyay baya a zabure, cikin rawar baki da nuna motar yace, “Sameer yaushe kuma ka fara shirya min wasa da hankali har irin haka?”.
“Ka gafarceni ranka ya dad'e, abinda kagani zahirin gaskiyane, wannan d'an uwankane ya dawo gareka cikin k'oshin lafiya da hukuntawar Ubangiji”. Galadima ya k'are maganar da rank'wafawa ya taimakama Abie ya fito, itama Momma ta fito.
Hakan sai yayi dai-dai da isowar mama Fulani wajan. Da fuskar Momma mai d'auke da k'asaitaccen murmushi tafara tozali, ta k'araso gabanta da sassarfa tana rik'o hanunta da fad'in “Zeenah!”.
A take Momma ta juya gareta, dan ko a mafarki bazata manta mai wannan muryarba, batareda tunanin komaiba ta rungumeta.
Yayinda shima takawa ya rungume Abie daga can.

Tun a wannan daren labari yafara karad'e masarautar, wasu kan basu aminceba kwata-kwata, burin kowa gari ya waye yayi kallon zahiri ba jita-jita ba.
Dole matar mai martaba ta koma sashenta, dan mai martaba yace Abie a sashensa zai kwana, jiyake idan ya barsa zuwa wani sashe tamkar da safe zai wayi gari yaga ba hakaba.
Itama Momma a sashen mama Fulani ta kwana tilas, yayi da mukuma muka nufi namu da yasha gyara ko ina yake need tamkar muna k'asar.

Yau dai kam na murzu wajen Galadima, acewarsa murnar sallah ce, dukda gajiyar tafiya darashin samun isashen barcin da muka tara a Saudia bai d'agan k'afaba, a cewarsa yamayi k'ok'ari, kwana nawa.

WASHE GARI

A Washe gari antashi da farin ciki guda biyu a masarautar gagara badau, Murnar Salla da dawowar Abie.
Dan zuwa safiya kam tabbataccen labari daga bakin sank'ira ya isa kunnen kowa, harma da k'yak'yk'yawan albishir na halattar sallar idi tareda Abie.
Kafin kace mi labari yafara fita wajen masarautar, su papi ma tun a Daren Galadima ya kirasu da wayar Sauban dake hannunsa.
Batareda sanin ya akayiba saiga magana tafara shiga kunnuwan jama'ar gari da y'an jarida, wasu gidajen TV Dana redio suka fara sanar da wannan zance dawasu ke k'arya tawa kansu tsaye................✍🏻





ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏🏼
[7:09 PM, 8/21/2019] +234 813 508 4146: Typing📲



💡HASKE WRITERS ASSO....


♦RAINA KAMA...!!♦
(Kaga gayya)


Bilyn Abdull ce🤙🏻
_______
Tawan miss xoxo tawa ni kad'ai, wannan gaisuwar takice ke kad'ai da babbar murya my dear, ALLAH ya bar mana zuminci mai d'orewa har Abadan, ke ta dabance a zuciyar bilyn Abdull, ina yinki irin Trillion's d'innan wlhy, na gaisheki da gaba d'ayan ahalinki da tawagar y'an Group d'inki na HOME OF NOVELS baki d'ayansu, alkairin ALLAH yakai gareku har gadon barci My Hafsy🤸🏻‍♀😘👍🏻.

_________



BOOK 3 👉🏻3⃣0⃣


...............Da asubahi na tashi jikina cike da gajiyar tafiya da wadda boss ya k'aramin, daga sallar asubahi bai samu dawoba, Dan ana fitowa salla dukan ahalin gidan mai ruwa da tsaki sun hallara ne ga yima Abie barka da zuwa dakuma tabbatar da gaskiyar zancen, domin tabbatar musu da kokwantonsu mai martaba yabasu damar ganin Abie d'in tareda shelar Sank'ira. Wannane dalilin yad'uwar zancen dawowar ta Abie har a wajen masarauta.

Dukda gajiyar dake tare dani bansamu komawa barciba, nashiga k'imtsa gidan iya bedrooms d'inmu zuwa nashi sashen da babu wata baiwa dakeda lasisin shiga. Sauran guraren zuwa kitchen kuma bayina dasukayo asubancin zuwa sashen saboda jin nadawo ne keta k'ok'arin gyarawa.
Na fito da nufin komawa d'akina na tashi yara na musu wanka cikin bayina d'aya ta zube Guywoyinta a k'asa tana fad'in “Ranki ya dad'e ga sak'on kayan abincin salla nan daga sashen mama fulani”.
Cikin d'an mamaki Na kalleta tareda kayan abincin dake jibge, sai naman kaji cikeda k'atuwar roba irin wadda ake tarama mai jego ruwan wanka. Katsemin tunani tayi da kuma fad'in,
“Ki gafarceni ranki ya dad'e, wannan al'adar mama Fulani Ce, a duk daren salla takan aikama kowanne sashe Na y'ay'anta da manyan gidannan irin wannan kayan, yanzu zama a k'araso da sauran, kowane sashe dasu yake abincin salla”.
Kaina Na jinjina tareda zama bisa kujera ina d'ora k'afa d'aya kan d'aya da kallon baiwar dani nama mance sunanta a yanzu. Nace, “Oh, yama sunanki?”.
“Ranki ya dad'e Umimi”.
“To Umimi wace shugabar hadiman sashen nan?”.
“Nice rankai ya dad'e”.
“Ok, ya zamuyi kenan? gashi mun kasance lokacj a k'ure, Dan yanzun kinga kusan 6:23am, bamuda isashen lokacin abincin salla kenan”.
“Ranki yadad'e ki gafarceni, zamu iyayi insha ALLAH, tunda kinga ai munada yawa”.
Shiru nayi inad'an nazari, saikuma Na sauke numfashi ina mik'ewa damata nuni muje kitchen d'in.
Alhmdllh inada kaso mafi yawa Na buk'ata, saidai abinda ba'a rasaba, Umimi nasaka ta tattaro sauran suka shigo da kayan, Dan danan suka fara rage aikin, ni kuma Na fito nad'an rubuta sauran abinda nake buk'ata nabama baiwa d'aya da kud'i takaima Sarkin Mota yabama wani ya sayomin.
Badansu Abdurrahman sun tashiba Na tadasu duknai musu wanka, shirin sune yad'an jani lokaci abinka daba d'ayaba, gashi sunfara wayo, sauk'i nama d'aya Umimi babbar macece kuma Na yaba da tsaftarta. Duk da dai namusu gargad'in jira nazo Na had'a komai da kaina. A gurguje nayi wanka nasaka simple gown dabazata takurani wajen aikiba, nasaka k'aramin hijjab Na fito nabarsu Abdurraheem a d'akin, insha ALLAH bazasuyi kukaba, Dan saida cikinsu yay taf sannan Na fito.
Naji dad'in iskesu sunci rabin aikin, to kusan su 15 kowa da abinda yakeyi. Dannan nasaka hannu nima wajenyin abinda yakamata ace ni nayi d'in, Dan Sarkin Mota yakawomin sak'ona tuni. Sannan ankawo sauran kayan daga sashen mama Fulani.

8:00am dai-dai Galadima ya shigo sashen, saboda yazo yay shirin massalaci, mamaki ya kamashi jin k'amshi ya baje ko'ina, shidai yasan bai tanadi komai d'aya danganci abincin salla ba.
Yana cikin tunanin Sauban ya shigo d'auke da k'atuwar ledar kayanda zai saka, Wanda tun muna India yabada umarnin a dink'a masa su.
Tare suka shiga sashensa da tunanin ko inacan, dukda yasan bazanbar y'an aiki akan girkiba, Dan yakula inada son komai naima kaina musamman girki.
Babu abinda ke tashi sai k'amshi mai dad'i anan d'inma, ga ko ina yayi k'al gwanin sha'awa da birgewa, saidai kuma tsit alamun babu kowa.
Sauban ya Shiga bedroom d'insa da kayan shima yana biye dashi.
Cikin sigar tambaya Galadima yace, “to ina take itada yaran?”.
K'aramar dariya Sauban yayi, yace, “Yaa Sam kasan halin auntyn tamu dai, Na tabbatar k'amshin girkinnan daga sirrin iyawartane, kaga kenan tana kitchen ”.
Hararsa Galadima yayi, Sauban ya rufe baki Dan tuna ta6argazar da yayi.

Ina cikin aikin Sauban ya shigo, bayin duk suka zube suna gaisheshi, da farko nama zata ko Galadima ne, saida Na waigo naga Sauban.
Bayan ya d'aga musu hannu dabasu izinin tashi ya kalleni yana fad'in “Aunty gimbiya kinsani jin yunwa mai yawa da wannan k'amshin girkin naki”.
Murmushi nayi kawai ina wanke hannayena, nace “ALLAH Yaa Sauban akwaika da tsokana, ya gajiya”.
“Ai tabi gado wlhy, tare muka shigo da Yaa Sam fa”.
Nace, “Ok". Coffee Na had'a masa a k'aramin filas Na d'ora a tire mai k'yau da mug daduk abinda zai iya buk'ata.
Kar6a Yaa Sauban zaiyi nace, “A'a kabarsa Na hutar dake nikam”.
Yay murmushi, “shikenan Aunty, inagafa nima zuwa zanyi Na shirya yau idin Na musamman ne ga jama'ar masarautar gagara badau”.
“Gaskiyane Yaa Sauban, ALLAH yasa yau asamo mana amaryarmu”.
Dariya yayi yana yunk'urin fita, “lallaima Aunty d'an k'araminnan dani wazai ban y'arsa?”.
Ban samu bashi amsaba ya fice, Nima sashen Galadima Na Shiga INA murmushi.
Babu kowa a falon, Dan haka Na wuce bedroom d'insa.
Sallama nayi kawai Na shige. A bakin gado Na iskeshi zaune d'aure da towel, da alama wanka zai Shiga. Murmushi mukaima juna. nace, “Afuwan my King, aiki ya d'auke hankalina bansan ka shigoba”.
Murmushi ya kumayi yana wani lumshe ido, Na ajiye tiren saman k'arim copy table d'in gabansa sannan Na zauna kusa dashi Na kwantar da kaina gefen kafad'arsa bayan Na sumbaci damtsen hannunsa”.
Shima saiya karkato fuskarsa gareni ya shafa tawa fuskar da tattausan hannunsa, cikin magana rad'a-rad'a yace, “miya kaiki aiki keda ke tare da gajiya?”.
Idanuna na d'ago na kallesa ina murmushi, nace, “my king ai yakamata ace anyi abincin salla a sashen Galadima, wannanfa shine karon farko da zakayi bikin salla da matarka a masarautar nan, bai kamata ace anyishi babu wasu alamuba ai OK?”.
Yanda nai maganar da kashe ido d'aya saida tsigar jikinsa ta tashi, yad'an lumshe ido da sumbatar goshina, sannan ya rad'amin “ALLAH yay miki albarka” acikin kunne.
A saman la66a na amsa da “Amin”.
Ya tambayeni yara nace, “suna d'akina, maybe ma sunyi barci. Bamu tsaya 6ata lokaciba muka Shiga na taimaka masa da wanka, sannan muka fito nahau shiryashi, dukda lokaci yaja a nutse nake masa komai, danshi ma'abocin son komai a nutsene, bayason gaggawa ko yawan sauri koda a magana ne kuwa.
Inamasa shiri yana shan coffee, kaga d'an gatan Munaya.😂
Tsaf na shiryashi cikin farar shadda daduk salla yakanyi amfani da ita wajen idi, nakawo babbar riga na saka masa sannan na fesheshi da turare, ajiye mug d'in hannunsa yayi yana d'aukar hularsa zanna bukar daketa maik'o yay mata kari ya kafa bisa kansa yana dai-dai tawa.
Alk'yabbar dazai sa nagama feshewa da turare sannan na matsa ina kwantar masa da sajensa dayasha gyara da cumb, shikuma yana saka link d'in hannunsa.
Kusan tare muka gama, na kama hannunsa na d'aura masa agogon dabai San da shiba.
Da mamaki ya kalleni amma saina janye idona ina murmushi da fad'in “Happy salla nane nida triplets d'inka”.
Rasama mi zaice yayi, sai kallon agogon da koshi da kansa iya mak'urar za6ensa kenan. Yakai hannu zai rik'oni nai baya kad'an ina girgiza masa kai, Dan nasan makomar rik'onin.
Cikin marairaice face nace, “please kabari saika dawo kawai”.
Wani miskilin murmushi yayi yana cije lips.
Nima na murmusa da nuna masa Alk'yabbar.
Kansa ya girgizamin a hankali yana mai shafa agogon Dana d'aura masa da d'ayan hannunsa. “kibarta zasumin nauyi da yawa, idan zamu fita gaida Governor zan saka”.
Ido d'aya na kashe masa da had'e yatsuna👌🏻alamar yayi.
Ya murmusa shima yanamin jinjina👍🏻.
Ban barsa ya fitaba saida namasa photo biyu, sannan na rakoshi har falon k'arshe, inda Muftahu da Matawalle ke jiransa, suma sunsha wanka mai birgewa, tamkar ka sacesu ko anguna ranar aurensu.
Galadima ya kareni da bayansa tareda min alamar na koma. Baya buk'atar su ganni kenan. Nima saina juya ciki kawai. Yayinda nake jiyosu suna masa Sheri da kod'a wankan nashi.

Na lek'a yara naga barci sukeyi, Dan haka na koma kitchen muka cigaba da aikin da fatan mu kammala akan lokaci.

Tunda matasan samarin masu d'anyen jini suka fito sai kallo ya koma sama, bayi sai zubewa suke suna gaishesu, sukam sai d'aga hannu dad'an murmushi.
Haka kawai sai Galadima yaji kewar Harun, aduk irin wannan ranar shike zuwa ya fiddoshi daga sashensa, amma yau gashi bak'in halinsa yasa a gidan yari zaiyi tasa bikin sallar dagashi har ubansa. Ya k'aunacesa saboda ALLAH ashe shid'in ba haka bane a tashi zuciyar.
Motocin da aka tanada domin su suka shiga.
Wambai da talba haushi ya kamasu, ganin wai yau d'an uwansu matawalle ne zai tafi salla tareda Galadima.
Oho, daga matawallen har Galadima basusan sunayiba.

A 6angaren Abie da mai martaba shiga sukayi iri d'aya, Abie ya fito a ainahin sarakinsa na asali, sai rama wadda kayan jikinsa suka 6oye, idan ka gansu bazaka ta6a banbanta wanene sarkin ba.
Mai martaba ya fito rik'eda hannun d'an uwansa Abie, nanfa aka fara ruwan cameras dukda dogarai na karewa ma, cikin lullu6esu da manyan riguna da musu kirari da busar algaita suka shiga mota d'aya.

Masallaci yacika mak'il da al'ummar manzon ALLAH (s.a.w), isowar Sarki da tawagarsa kawai ake jira.
A dai-dai k'ofar baya ta musamman motarda ke d'auke dasu Abie ta tsaya, mai martaba ya taimaka masa ya fita suka shige cikin massalaci.
Nan take aka d'auki kabbara bisa umarnin liman domin nuna godiya da al'ajabin hikimar ubangiji na dawowar tsohon Sarki cikin k'oshin lafiya, bayan tsahon shekaru daya d'auka baya k'asar. Duk matashin dake k'asa da shekara talatinma bai sanshiba.
Mak'iyan 6oyefa da sukaga tabbas sai tsoro ya kamasu, ashedai zancen daya karad'e gari gaskiyane, yau ga Sarki Saifudden Abubakar a gabansu ko sunaso ko basaso kuwa.

An gabatar da Kud'uba tamkar yanda addini ya tanada, mai ratsa jiki da 6argo, mai k'arama muminin kwarai imani da tsoron ALLAH.
Su Galadima suna jerin sahun farko, saidai na kusada su Abie ba.
Alhmdullah, sallar idi ta gudana bisaga farincikin kasantuwar bayin ALLAH wannan rana da ko yaro k'arami ke d'okantuwa da zuwanta, bare su Galadima da jama'ar masarautar gagara badau da farin cikin ya had'e musu biyu.
Bayan idar da salla akaja addu'a mai tsayin gaske ga Abie, sannan aka bashi microphone daga zaune yay bayani mai gamsarwa da ratsa jini da jijiyoyi Wanda yasaka mafi yawan jama'ar dake massalacin hawaye.
Hatta da Galadima k'asa kawai yayi dakai yana murmushi da share hawayensa da handkerchief.
Yau dai kam ai saida aka kai kusan 11:30 a massalaci kafin a sallami jama'a.
Yayinda manya kuma suka samu yin gaisuwa ga Abie da masa murna da addu'a.

A can kuwa jama'ar gari kowa ya gumtsi labari yatafi fesarwa, hakama y'an jarida masu zuwa kallon zahiri, kafin kace mi labari ya cigaba da shiga lungu da sak'o, hakama hotunan Abie da nasu Galadima.
Bisa ga wannan labarine su Ahmad tahowa Masarauta dukda basuda tabbacin ganin Galadima d'in.

K'arfe 12 aka shirya liyafar cin abincin a masautar, wadda har governor zai halarta, itace madadin hawa da akeyi zuwa gaida Governor.
Duk yanda Galadima yaso komawa ga iyalansa hakan ta gagara, yawan jama'a ya hanashi matsawa konan da can, kowa soyake ya nuna masa kansa a jerin masu tayasa murnar dawowar mahaifinsa cikin k'oshin lafiya.


****

Alhmdllh munsami kammala komai, Na barma su Umimi sauran aikin suka k'arasa, niko nanufi tsaftace jikina kafin mijina ya shigo, dukkan abincin da za'a fita dashi kuwa nabama su Umimi umarnin kaisa duk sashen daya dace.
Galadima daya tuna da batun abincin da Munaya keyi yad'an fita daga cikin mutane yana kiran sarkin Mota, Umarni yabashi akan zuwa birnin gayu ya kar6o drinks wajen manager, yanason kiran Munaya amma babu dama, Dan dawuyama idan ta maida layinta Na 9ja bisa waya, gashi bashida damar tsallakewa ya taho gareta.


****

Sosai Momma take samun tattali ga mama Fulani, ita abinma mamaki yabata, saida aka sakko idi sannan aka kaita sashe Na musamman da akayi aikin gyarawa da safiyar, zasu d'an zauna anan itada Abie kafin asan abinyi gameda sarautarsa dake kan d'an uwansa.
A tsorace mama Fulani take, dukda kaffa-kaffa da take dasu Momma, ko kad'an batason mulkinan yabar hannun d'anta, har yanzu burinta jikokinta su gaji masarautar gagara badau.
Amma dai taita danne zuciyarta Dan karta nuna hali.


******


Bayan mai martaba da Abie sun huta aka fara gudanar da liyafar cin abincin a babban d'akin taro Na masarautar.
Wanda yasamu halartar manyan mutane dake cikin binin, duk wani mai fad'a aji ya garzayo masarautar Dan kar ayi babushi, kokuma ya shiga black list.

Matawalle ya kalli Galadima dayak'i cin komai sai drink yake sha. “Lafiya kuwa Sameer?”.
Galadima ya kallesa da alamar tambaya, amma baice komaiba.
Da hannu Matawalle ya nuna masa abincin gabansa.
Murmushi Galadima yayi yana shafa kumatunsa, cikeda k'asaitarnan tasa yace, “Bazaka gane bane d'an uwa, my mata tayi abincin salla, idan naci wannan cikina ya cika naje can kuma babu space ai sai a hanani.......”. Sai yay shiru bai k'arasaba.
Mi Matawalle da Muftahu zasuyi inba dariyaba, har mutanen dake d'an gefensu suka juyo suna kallonsu.
Galadima kam murmushi kawai yayi ya maida eyeglasses d'insa a ido yana kallon inda su Abie ke zaune.

Anci ansha kowa yay mak'il cike da

Please Login or Register in order to submit comment