Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

akwatin’.
Jawowa tayi ta bud'e, duk an d'inka kayan, kayane masu tsadar gaske Na mace y'ar gata, bama tasan ta rungumeshi ba Dan dad'i, sai jero masa godiya da addu'oin fatan alkairi takeyi.
Shima tuni ya manta da fushin ya rungume kayarsa yana murmushi. cikin kunnenta yace, “kinfi k'arfin komai a wajena friend dan kin gamawa Muhammad Sameer komai”.
Munaya ta murmusa tana d'an dukan k'irjinsa, tace, “kana shamin k'amshin ne nagama maka komai?”.
Hannunta ya rik'e yana murmushi, yamatso da fuskarsa gab da tata, murya k'asa-k'asa yace, “ke d'ince Zuma ce...... ”
Harar data dalla masa ta sakashi fasa k'arasawa ya wani basar yana kashe mata ido d'aya, “dad'ina dake akwai mazurai, gaki babu k'arfi ga tsoron tsiya”.
Munaya tayi dariya, “aka gaya maka banida k'arfi? kabari nakuma samun lafiya sai a gwada kwanji”.
Wata dariyar mugunta Galadima yayi yace really?”.
“yes” ta fad'a cikeda karsashinta.
Ya mik'a mata d'an yatsansa alamar su k'ula.
Babu musu tabada nata itama suka k'ula. Murmushi yaytayi saboda muguntar dayasan yana shiryawa, wadda ita Munaya bata fahimci komaiba a ciki saboda wauta.🤣


*_Washe gari_*

Ta kasance safiyar suna, inda aka rad'a sunan yara bayan sallar Asubahi, *_Abdurrahman, Abdurraheem, and Amaturrahman_* masha ALLAH Babies ALLAH ya raya Ku akan sunnah da tafarkin addinin Islam.
Yara sunsha Addu'oin fatan alkairi sosai, tun kuma a safiyar shagalin suna ya fara, dan kowa yana cikin walwala da farinciki, mai jego munaya ansha k'yau itada babies har an gaji, kamar ka sacesu ka gudu, hotuna dai suna shansu kala-kala a yau d'inan, Su Momma ma da basa kusa anata sambad'a musu, dan duk wani motsin da za'ayi Sauban da Samha basa gajiya da tura musu, sai sukaji tamkarma suna nan suma, saboda kallon komai suke tamkar live, farin ciki da walwala sun yalwatu a zuciyar Abie, bakinsa yakasa rufuwa dan tsabar nishad'i daya tsinci Kansa yau aciki.

Hummm babbar magana, kayan barka dai sun iso, fans yaufa nasha kallo, kaga Inda akeyi don ALLAH, ta bakin Munaya tace INA zasu da wad'annan kaya haka, lamarin tamkar fariyya, gashi kowanne sashe sai kawo nasu sukeyi, gidan sarauta manya, babu Wanda zaiso aga kasawarsa, ballema wannan kana k'inyi za'a CE bak'inciki kakeyi, shiyasa mama Fulani aka ware aka zuba kayan barka Na gani Na fad'a, daga gidansu Munaya ma su inna sun taka rawar gani dai-dai k'arfinsu, daga ita har Munubiya komai iri d'aya aka musu, kayan babies ne kawai Na munaya yafi Na munu saboda su su uku ne ita kuma Nata biyu.
Nanfa y'an gidan suka Shiga k'us-k'us d'in gulmar Ina inna ta samu kud'in yin wannan hidima haka? dansu basuyi zaton hakanba, musamman da abin yazo da yawa ma, itadai inna ma ko kallo basu isheta ba, hidimar gabanta da farincikin datake cikine a gabanta, bakinta yakasa rufuwa saboda farinciki da godiyar ALLAH mai sassauya al'amura a yanda yaso a kuma lokacin da yaso, idan ALLAH ya jarabceka karkayi bak'in ciki, hak'urinka zai iya zama sauyin alkairi a gareka, inama iyayensu Nada rai suga wannan k'yak'yk'yawar rana, ta share hawayenta tana murmushin farin ciki, sannan ta kira y'ar uwarta a waya suka cigaba da tattaunawa.


*****

K'arfe uku da rabi kuma za'a gudanar da gagarumar walima da aka kama babban hall Na musamman.
A wannan rana yara dai har fada aka kaisu sukayo gaisuwa da hotuna da mai martaba da gayyar y'an uwa da abokan arzik'i, su Harun dai sune gaba-gaba, uban gayya kuwa Muhammad Sameer Saifudden Galadima Baban y'an uku😂 ai ba'a cewa komai, koma ganinsa ba'ayi saboda tsabar shiga hidima, wannan suna ko bikidai iyaka kenan.
Nasan kuma fans duk kunyi shirin wannan walimar baje dad'i😋😋. Nifa buhu Na tanada walle😆, saura kuce Bily tacika zari da son banza kuma🙄, har y'an anguwarmu saina kar6oma gifts d'insu😜😂🤸🏻‍♀.


****************

Alhmdllh yaran Mununbiya ma an rad'a musu suna bayan sallar Asubahi, Namijin *_Aminudeen macen Ameenatu_* ALLAH ya raya wad'annan yara masu albarka😘😘🥰.

Yau daikam farin cikin da Abba da innarsu suke ciki 6ata lokacine ma, kai da dukkan masoyansu irinmu, masu bak'inciki kam Ku k'ara himma, hassada ga mai rabo takice😏🤷🏻‍♀.

Kowa nabashi dama ya k'iyastama zuciyarsa yanda bidirin suna yake guna, dan Alk'alamin Bily yau yayi k'ank'anta wajen wallafowa, sai mugama Na wannan satin bikin sunan bai k'areba😁.................✍🏻



Kuyi manage da wannan yau inada uzuri🤦🏻‍♀.



☺my Guy's a kafta kawai danjin yanda bikin suna zai gudana gobe idan ALLAH ya kaimu, kowa dai ya k'ure adaka dan karfa a kawo mana raini😕, kunsan dai halin mama Fulani, tana iya hanawa abarmu shiga😩🥺.








*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭👏🏻
*_typing📲_*


💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._*


*_♦RAINA KAMA.....!!♦_*
_(Kaga gayya)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*



~Book 2~ 👉🏻2⃣5⃣


................Aunty Salamah da kanta tazo yima Munaya kwalliyar zuwa wajen walima, saida tafara biyawa tama Munubiya sannan ta wuto nan, ta iske su duk a damuwar kukan da Abdurrahman ketayi, sai faman jijjigarsa akeyi amma yaro yak'i yin shiru, an basa nono yak'i kar6a, innro ta kar6esa ta hura masa kunne, ya kuma k'yak'yacewa da sabon kuka yana dunk'ulewa waje d'aya, tace “inaga kunnensa ke ciwo yaronnan”.
Munaya Na gefe zaune ta zuba tagumi kawai tana kallonsu, ita kad'ai tasan suyar da ranta ke mata, gashi Galadima baisan wainar da ake toyawa ba, yanacan tareda su Akash da suka iso yanzu.
Innaro ta dungureta, d'ago idanu tayi ta kalleta, ta mik'a mata Abdurrahman daketa sauke ajiyar zuciya, “d'iga masa ruwan nono kad'an acikin kunnen insha ALLAH idan aka dace zai daina”.
Kar6arsa tayi, ta d'ora kan cinyarta, dukma ta rikice ta rasa yanda zatayi, saboda sai mimmik'ewa yakeyi azaba na cinsa, ga Amaturrahman itada Abdurraheem suma sun d'akko nasu kukan, laraba ta rik'e matashi ta samu ta d'iga masa, ruwan nonon Na shiga yakuma mimmik'ewa yana kwalla ihun sabon kuka.
Saiga hawaye a na zuba a idon Munaya, tasaka hannu ta toshe kunen ta kozataji sassaucin jin kukan nasu dake d'aga hankalinta.
Tausayinta saiya kama laraba, tasan indai wannan ne yanzu ma aka fara, yaro d'aya ma ya kake k'arewa balle yara uku.
Cikin amincin ubangiji kuma duk sai sukayi shiru, innaro da laraba sunata faman jijjiga, itama Aunty salamah ta kar6i Na hannun munaya, tun suna ajiyar zuciya har barci ya kwashesu. Munaya ta shige bayi tana share ragowar hawayenta.
Baki innaro ta ta6e tana fad'in “lallai aiki yasamu mata, yo indai kukane yanzu ma kika fara”.
Daga Aunty salamah har laraba dai babu Wanda ya tanka.
Munaya kuwa data jiyota daga bayi tace “aniyarki ta biki, mai mugun fata kawai”.
Wanka tayo ta fito, Aunty salama kawai ta tarar a d'akin sai bayi biyu dake morping, suka durk'ushe k'asa suna gaida Munaya.
Hannu ta d'aga musu kawai dan batasonyin magana, har yanzu raunin tausayin Abdurrahman baibarta ba. ta kallesu duk suna kwance kan gado barci ya d'aukesu, yayinda Aunty Salamah ke zaune kan sofa tana warema yaran kayan da za'a saka musu.
Ta d'ago ido tana kallon Munaya, “haba auta kuka kikayi da gaske? Please kidaina musu kuka, ba'ason uwa Na zubarma d'a hawaye dukda wannan Na tausayine kinji”.
Munaya ta had'iye abinda yamata tsaye a mak'oshi tana gyad'ama Aunty salamah kai.
Saida Aunty salamah ta gama ware kayane sannan ta taso suka fara kwalliyar, anutse sukeyin komai, dan da sauran time, hakama Munubiya a nutse aka mata tata, anama Munaya tana kallon hotunan Munubiya, taji dad'in yanda y'ar uwarta tasha k'yau, dukda ma batakai ga saka kayaba.



★★★★★★★★★★★


Muftahu nata kai kawo a tsakar d'akinsa, tunanin tawace hanya zai fargar da Galadima kawai yakeyi, dan dolene saida hannunsa zaiyi wannan aikin, saboda had'arinsa, gudun kar reshe ya juye da mujiya, sannan aikin yana buk'atar takune da sirri.
Fitowa yay yanufi can cikin k'aton lambun masarautar indasu Galadima suke tareda mafi yawan y'ammata da samarin masarautar.
Wasu sunata hirarsu in group, wasuko hirar tasu ta masoya ce, Muftahu ya k'araso inda su Galadima suke, sun baza babbar darduma anata hira, Bama zaka ta6a Sanin suna lambun ba saboda sunacan ciki nesa da sauran yaran.
Galadima na zaune a gefe cikin kujera, ya d'ora k'afafunsa a wata kujerar, sanye yake da farar shadda d'inkin boda, fuskarnan babu walwala ko kad'an, gaba d'ayan hankalinsa yanaga system d'in daya d'ora bisa cinya yana latsawa.
Muftahu ya mimmik'a musu hannu sukayi musaba cikin fara'a. Amma tsakaninsa da Harun ba hakan baneba, kowa murmushi mai cikeda ma'anoni yay ma d'an uwansa, kafin su saki hannun juna. Muftahu ya matso kusada galadima shima ya bashi hannu sukayi musabaha, k'aramar takardar dake mak'ale a hannunsa ya sakarma galadima a hannu.
Kallonsa galadima yayi, sai yay masa murmushi yana signal da ido alamar ya duba.
Galadima bai ce komaiba ya cigaba da abinda yake ya basar da takardar. Muftahu kuma ya koma cikin su Harun aka d'ora hira, tamkar babu abinda ke damunsa.
Galadima baibi takan takardar da Muftahu ya basaba har tsawon wasu adadin mintuna, sannan ya bud'e ya duba.

_Ranka ya dad'e ina buk'atar muyi magana kafin a zauna wajen walima, magana mai muhimmanci please._

Iya abinda ke jikin takardar kenan.
Galadima ya d'an ja eyeglasses d'insa k'asan ido ya kalli Muftahu, cije lips nashi yayi yana janye idonsa.
Ya sauke k'afafunsa yana d'ora laptop d'in saman kujerar, ya d'auki ruwan gabansa yana sha da maida hankali garesu. jin hirar tasu ta y'ammata ce sai ya zuba musu ido kawai bai saka bakiba, dan shi dama ba'a wannan hirar dashi tun can da, suma duk sunsan haka, shiyyasa ko suna shirmensu basa sakoshi.
Ganin zasu saka masa cinwon kai saboda hayaniyarsu Na Neman yin yawa saiya mik'e d'auke da Laptop d'insa.
Duk kallonsa sukayi, Zayyan yace, “ina zuwa daddyn Triple's?”.
K'aramin tsaki yaja, da k'yar ya bud'e baki yace, “zaku samin ciwon kaine, zanje nad'an huta kafin time yayi”. ya k'are maganar da kallon agogon hannunsa.
Matawalle yay murmushi yana salute nashi, shima murmushin ya masa yana kaimasa rankwashi, ya kauce gefe yana murmushi, (dayake shima bai cika hayaniya ba).
Wuce warsa yay cikin takun nan nasa Na izza da k'asaita, da sauri wasu yaran masarautar dasuka had'a tasu dabar agefe biyu aciki suka taso suka k'ar6i laptop d'in hannunsa saboda girmamawa, ya mik'a musu yana murmushi, yana gaba suna binsa a baya, sai zuba masa surutu suke akan shagalin daza'a sha yau, shidai murmushi kawai yake musu babu magana, basu damuba, dan kowa yasan halin galadima a masarautar nan, haihuwar nan ma wasu da yawa zasu iya cewa sunga hak'oransa a waje. duk inda suka gitta ana kwasar gaisuwa, bayi kam zubewa suke domin girmamawa a garesa.
Har sashensa suka masa rakkiya, sarkin mota ya kar6a laptop d'in ya k'arasa masa da ita zuwa ciki..
Baibi ta ainahin k'ofar da zata kaishi babban falonsu ba, saiyabi wata k'aramar k'ofa da kai tsaye nasa sashen zai shige basai mata y'an suna sun gansa ba.
A falo ya iske Sauban kwance yana barci, da alama yagama yawonsa ne gajiya ta makesa, da kallo Galadima ya bisa, amma dan ya tabbatar da lafiyarsa saiya d'ora yatsunsa biyu a wuyan Sauban d'in, babu zafi, ya maida goshinsa saiyaji zafi sosai, Galadima ya girgiza kai, yasan dama ba lafiyace zata saka Sauban barci a irin wannan lokacin ba ana wannan hidimar.
Bai tasheshi ba ya shige cikin bedroom, zama yay a bakin gadon yana cire bottom d'in rigar guda uku, ya huro isaka daga bakinsa yana zamewa ya kwanta batareda ya cire rigarba, zuciyarsa tana ta jujjuya mi Muftahu yake nufi ne? wace magana zasu tattauna?. waya ya jawo da nufin kiransa, sai kuma ya fasa, jefar da wayar yayi yamik'e yana ida cire kayan gaba d'aya. ya shige wanka.
ya ja adadin wasu mintuna masu tsayi kafin ya fito sanye da bathrobe fara sol, sai k'aramin towel a hannunsa yana goge fuskarsa zuwa wuyansa.
Yana tsaye gaban mirror zai fara shafa mai ya jiyo ana knocking d'in k'ofar falonsa, Computer d'in daya ajiye wadda yake kallon kowane 6angare na sashen daga cctvs cameras d'in daya zagaye ko ina, tun zuwan dayayi Na k'arshe ya saka akayi masa wannan aikin, sannan ya d'auki mataki akan waccan cctv d'in da Munaya tamasa hannunka mai sanda da ita.
Sarkin k'ofa ya gani, sai kuma Muftahu daga can waje alamar yana jiran iso ne.
Guntun tsaki Galadima yayi, ya fito zuwa falo, Sauban dake barci ko motsi baiyiba balle yasan ana knocking d'in. yana daga tsaye yabama sarkin k'ofa izinin shigowa.
Cikin girmamawa yace, “ranka yadad'e yalla6ai Muftahu ne ke Neman iso”.
Da hannu Galadima ya masa nuni da ya shigo.
Sarkin k'ofa ya amsa da to sannan ya fice.
Komawa Galadima yay ciki yacigaba da shafa mansa, saida ya gama tsaf sannan ya zira jallabiya Brown ya fito.
A falo ya iske Muftahu zaune yana control d'in television da remote.
Galadima ya zauna a kujera mai zaman mutum d'aya, sai wani d'aure fuska yake.
Muftahu bai wani damuba, dan yariga ya saba da wannan ai.
Kallonsa Galadima yayi cikin lumshe ido yana fad'in “Mike faruwane?”.
Ajiye remote d'in Muftahu yayi, ya kalli Sauban dake barci.
d'an ta6e baki Galadima yayi, yace, “karka damu, kayi maganarka kai tsaye kawai”.
Cikin jinjina kai Muftahu yace, “Ok, babu abinda ke faruwa saidai shirin faruwar kam, Ranka ya dad'e bamuda isashen lokacin wata magana mai tsawo yanzu, saidai ga wannan takardar ka duba, so yanzu wannan ne akan ga6a, shine yakamata mu d'au mataki akansa, daga baya komi kenan namaka alk'awarin warware makashi, fatana dai ka fahimci wannan d'in saboda had'arinsa”.
Kar6ar takardar Galadima yayi, ya d'auki medical glasses d'insa daya ajiye a teble glass d'in dake gefen haggunsa ya saka, duba takardar yay a tsanake, cikin wani yanayi dake nuna tsantsar tashin hanki yace, “Muftahu wannan maganar gaskiya ce kokuwa? karkamin wasa da hankali a wannan karon dan bazan d'aga maka k'afa ba a wannan ga6ar alwashi nane”.
Murmushi Muftahu yayi, ya sauke ajiyar zuciya yana fad'in “Nabaka wannan damar, inhar kayi gamo da sa6anin hakan karka barni da numfashi ranka ya dad'e”.
Wani shegen Murmushi Galadima yayi, yamik'e d'auke da takardar ya koma bedroom batare da kuma kallon Muftahu ba.
Tausayin Galadima ya kama Muftahu, mik'ewa yay shima ya fice.

Jefar da takardar Galadima yayi akan gado yana taune lips nashi tamkar zai huhhudashi, wata irin suya zuciyarsa ke masa, lallai dolene ya jinjinama Munaya, dan ta taka rawa wajen shagaltar dashi wanene shi? minene burinsa?, ganin tunani bazai masaba yatashi jikinsa Na rawa yafara wasu had'e-had'en abubuwa, waya ya d'auka ya kira Ayusher, ta d'aga cikin hanzari tana mik'ama Munaya dake shayar da Amaturrahman data tashi daga barci tana kuka.
Kallonta tayi da mamaki tace, “wace Ayusher?.......”.
Galadima ya katseta da fad'in “ki kawomin kayanda su Abdurraheem zasu saka”. iyakar maganar da yay kenan ya yanke wayar yana cigaba da latse-latse, zuwa can kuma ya ajiye ya mik'e yana cire jallabiyar jikinsa.

Baki sake Munaya tabi wayar da kallo, mike damun galadima haka? Muryarshi irin wadda tasan asalin galadima ce, hakan na nufin akwai matsala kenan? to mine zaiyi da kayan da yara zasu saka?. batada mai bata wad'an nan amsoshin dan haka ta mike tana ajiye Amaturrahman d'in, aiko ta fashe da kuka an cireta bata k'oshiba, tsaki Munaya tayi tana fad'in “ai saikiyi tayi, ku matsala ubanku matsala mutum yarasa wazai kama.
Ayusher da Aunty Salamah suka kalli juna suna gumtse dariya.
Gyale taja ta lullu6a, dama tasaka doguwar rigar matirial kafin dai time ya k'arasa. ganin zata wuce yarinya na kuka Auntu Salamah tace, “dawo ki d'auketa mana, idan kinje can saiki bata nonon”.
Tamkar Munaya zata saka kuka haka ta dawo ta kwashi Amaturrahman ta fice tana k'unk'uni.
A falo ta iske Sauban Na barci, wucewa tayi cikin bedroom d'in kanta tsaye, amma saida tayi sallama ya bata izinin shiga.
Tun da ta shigo taga yanayin da yake sai gabanta ya dad'i, tamkar kazar da kwai ya fashema a ciki ta mik'a masa ledar data zubo kayan sannan ta zauna a kunyace saboda yanayin da yake babu kaya.
Ba tare da ya kalleta ba ya hau Fiddo kayan, ya zubesu saman gado yana d'aukar hotonsu a waya, yay latse-latse nawasu mintuna kafin yasaka wayar a kunne.
“Saleem ka dubamin kalar kayannan, koda basu kaisu tsadaba, yanzunan kataho ka kawominsu”.
Bataji mi Saleem yafad'a daga canba.
Muryarta a raunane tace, “yalla6ai mike faruwa wai?”.
Jajayen idanunsa ya d'ago ya kalleta, k'ala baice mataba ya mik'e ya d'akko wani k'aramin box ya dawo ya zauna, ita duk saima kunya takuma kamata, saboda dagashi sai boxer, amma taga ko a kwalar rigarsa bai damuba, hidimar gabansa kawai yakeyi.
Kwantar da Amaturrahman tayi kusa dashi ta tashi zuwa wardrobe d'insa, k'aramar t-shirt ta d'akko, tazo ta mik'a masa.
Ya d'ago ido yana zuba mata harara, dukda ta tsorata saita daure tace, “please mana yalla6ai”. tayi maganar muryarta a raunane.
Saida yayi k'aramin tsaki kafin ya amsa ya saka, wani abu da batasan minene ba taga yana mak'alawa jikin kayan yaran, saida yagama tsaf sannan ya maidasu a ledar, kallon Amaturrahman dake k'yalla y'an idanu zata fara k'aramin kuka yayi, ya shafa kumatunta batare da ya d'auketa ba.
Laptop d'in sa ya jawo ya saka eye glasses d'insa, ya kalli Munaya yamata alama da ido akan tazo.
Babu musu ta taso zuwa kusa dashi ta zauna.
Laptop d'in ya d'ora mata akan cinya yace, “wanene SD a cikin su?”.
Nutsuwa Munaya tayi tana kallon hotunan, cikin waro ido tace, “kai ga Fu'ad ai”.
Da mamaki Galadima yace, “Fu'ad!?”.
“eh wlhy yalla6ai, Wanda ya kaimu birnin gayu plaza ranar da abunnan ya faru”.
Kar6a laptop d'in Galadima yayi yakuma kallon hoton da k'yau yana taunar lips, kuma mik'a mata yayi batare da yace komaiba. itama batace dashiba tacigaba da bin hotunan da kallo sannu a hankali. Harta kai k'arshensu babu SD. ta kalleshi cikin damuwa, “yalla6ai babushi fa anan gaskiya”.
Kansa ya jinjina mata yana kar6ar laptop d'in, cigaba yay da danne danne, itadai Munaya tana kallonsa.
Kuma d'agowa yay ya kalli Munaya, “duba annan kuma fa”.
Kallon hotunan ta shigayi, canko saiga hoton SD, tace, “Alhmdllh gashi anan”.
Kallon hoton Galadima yayi, da mamaki yace, “kinsan wanene wannan kuwa?”.
“Ah! yalla6ai SD ne mana”.
“Munaya kin tabbata wannan ne kika gani a wajen Abba?”.
“Wlhy shine yalla6ai, bazan ta6a manta fuskarsa ba ai komai dad'ewa. balle acikin abinda bai rufa 2years ba, amma kasanshi ne?”.
Bai iya cemata komaiba, sai zuciyarsa dake wani irin bugawa da sauri-sauri kamar zata fad'o, mamaki ya hanashi motsin kirkirma, Alhaji Shehu Darma shine SD kenan, babban Amini kuma d'an uwa ga Mahaifin su Samha, innalillahi, ya abubuwa keneman koma masa rikid'ar hawainiya haka?, wannan fa Fu'ad d'in d'ane ga yayar Uwargidan Sarki mahaifiyarsu Matawalle, cikin cije lips ya buga hannunsa akan gadon yana fad'in “Kai!!!! miyasa hakane? miyasa duk Wanda Na yarda dashi shike fara bayyana a maicin dunduniyata?!! miyasa rayuwa tazomin da irin wannan rikicin ne?, oh God!!”. ‘ya k'are maganar cikin matsanancin k'araji, tareda runtse hannayensa waje d'aya.
Tsoro ya kama Munaya, ganin yanda duk ya rikice kamanninsa suka canja, idonsa yayi matuk'a jajur, jijiyoyinsa da gashin jikinsa duk sun mimmmik'e, ga Amaturrahman data tsorata lokacin daya buga gadon, d'aukarta tayi tahau jijjigawa.

Sauban ma a firgice ya tashi, ya hau waige-waige, ganin babu kowa a falon saiya nufo hanyar bedroom d'in Galadima, tabbas muryarsa yaji a yanayin da ba'aso. harzai murd'a k'ofar saiya fasa saboda jin kamar muryar Munaya tana magana.

Tunda tasamu Amaturrahman tayi shiru sai ta d'auki towel d'insa ta goyata, ta matsa kusadashi a tsorace, hannunta ta d'ora akan nasa daya dafe mirror, ko motsi baiyiba balle ya kalleta.
Murya a d'arare kuma a sanyaye tace, “please yalla6ai, fushi baisa a samu sauk'i saidai ya k'ara zafi, kaine kasha gayamin wani karatun baya buk'atar fassara ko dogon nazari, akan barsane kawai a yanda yazo, dukda bansan tushen matsalarba zan iya bada gudunmawa wajen kama bakin zarenta, kayi hak'uri ka kwantar da hankalinka, ita fahimta fuskace, ba fushinka ko tsantsar damuwa ne abin buk'atarba yanzu, d'ana tarkon dazai fara kamo maka hannun mak'iya shine jarumta, ka danne kuma ka daure, ni dama Dan banida ikon hana walimar nanne kawai, amma inaji a jikina akwai lauje cikin nad'i, saidai wad'anda suka nad'a d'inne bamuda ilimin saninsu sai ALLAH yaso Samar damu, amma ai duniya makarantace, idan su a can suka yini kaikuma saika nuna musu kwana kayi, lokuta da dama fushinka ke lalata maka aiki, dan inhar kana cikin fushi dukkan aikinka tafiyar hawainiya yake, wannan lagon naka suka samu suke

Please Login or Register in order to submit comment