Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

k'aryaba Badi bazai wuce shekaru 33 ko 35 ba. Amma yau gashi zaune gabansa furfura da girman tsufa duk sun bayyana a garesa......
Sallamar Muftahu ce ta katse tunanin galadima, Muftahu ya zauna suka gaisawa da Baba Rabilu, sannan ya gaida galadima, idonsa dai nakan Badi shima.
da k'yar Galadima ya amsama Muftahu gaisuwarsa.
Badi dakema muftahu kallon sani ya gaisheshi cike da girmamawa (Dan ALLAH yayisa mutum mai yawan rik'o).
Muftahu dai kasa hak'uri yayi, ya kalli baba Rabilu yana neman amsa.
Murmushi baba Rabilu yayi, ya gyara zamansa yana fad'in, “Yalla6ai baka ganesa bane?”.
Muftahu yace, “Banma ta6a ganinsa ba alhaji”.
Badi ya kalli Muftahu sannan yay k'asa da kai. Yace, “Nikuwa kaga Na ganeka yalla6ai, dan bazan manta sanda kukan rako Yarima ba idan za'a fita da shi bakin ruwa shan iska, ka kan nace sai a doki d'aya zaku tafi kai da sauran abokan nashi”.
Murmushi Muftahu yayi, ya kalli Galadima dayay shiru yana kallon Badi kawai, yasan yana tuna bayane, kuma akwai tambayoyi fal ransa sai dai ya kasa furtawa, janye idonsa yayi ya maida ga Badi, yace, “Amma Badi minene ya faru da kai harka bar masarauta? dan bazan iya tuna wani abuba a wad'ancan shekarun namu, yanzu kuma daga ina kake?”.
Zama Badi ya gyara. Yace, “lallai labarine mai tsawo da Nisan zango, amma a tak'aice dai abinda zan iya cewa shine.....”.

“Bayan kwanciyar mai martaba adalin sarkinmu jinyar da ba'asan mafarinta ba da wata biyu kacal ranar wata lahadi da tashin hantsi munje kasuwa ni da mahaifina mun sayo abincin dokuna mun dawo, muna tsaka da sauke kaya a barga saiga wani mutum a tsakkiyar harawar dokunan cikin a kori kurar da muke zubo kayan kenan, dagani har mahaifiyata da mahaifina mun razana matuk'a, harma k'anwata taso tayi ihu amma mahaifiyarmu ta toshe bakinta saboda rok'on da mutumin kema babanmu akan muyi shiru Dan ALLAH, a razane matuk'a mutumin yake dan ko ina Na jikinsa mazari yake, yace a taimaka masa da ruwa yasha zaimana bayani, iya mahaifiyarmu ta nufi d'akunanmu dake cikin bargar dagacan gefe ta d'ebo masa ruwa a randa cikin kwanon sha ta kawo masa, babana ya taimaka masa ya fito daga akori kurar, ya zauna bisa buhun harawar da muka fara saukewa, ruwan ya kar6a ya kafa kai saida ya shanye kusan rabi sannan ya ajiye yana musu godiya, wani Abu irinna d'aukar hoto (camera) ya fiddo a cikin aljihunsa ya mik'ama mahaifina cikin yin magana da k'yar. yace_”.
“Sarkin Barga ga wannan abun, nasan zakayi mamakin miyasa Na bakashi, to banida wajen daya dace Na damk'ashi sai wajenka a kaf masarautarnan, Dan kaine hanyata mai sauk'i, akan wannan abun aka biyoni za'a kashe, shine ALLAH yabani ikon shiga motarku, dan nashigo tacikin kasuwa domin tsira da raina shine Na ganku, karka bama kowa camera d'innan sai d'an Sarki, Yarima Sameer, kokuma d'iyarsa, gimbiya Haneefa, ko matarsa uwargidansa wadda ta haifi su Yarima d'in, harda wad'annan takardunma, nasan ni tawa ta k'are Dan babu makawa saisun kasheni, Dan ALLAH ka tabbatar cikin mutane ukunnan ka bama wani, nasan yarima bashida wayon dazai fahimci minene, amma idan ka nuna masa yabama mahaifiyarsa zai bata, dukkan abinda ya faru da mai martaba yana acikin wannan Camera d'in, ni zan koma, Dan banason wani ya fahimci nama shigo masarautar nan balle har asan Na gana daku”.
“duk yanda mahaifana sukaso tsaida mutuminnan sun gaza, dan ya tabbatar mana dolene yabar masarautar a lokacin, saboda akwai munafukan da sukasan abinda yafaru da Mai martaba. Sai dai kuma abinda bamu saniba shine, Ashe dukkan abinda ya faru akan idon waziri ne, dan haka a wannan dare yabiyo sahun abinda mutumin yabada, mahaifana Na barci ya tashesu akan su bashi, sukace basusan mi zasu bashiba, shine ya kashe mahaifiyarmu wai dan baba yaji tsoro yabashi, dukda baba ya razana hakan baisa ya bashiba, ya yarda d'in gwamma a kasheshi shima da dai yabada , daga k'arshe shima ya kasheshi, k'arar da mahaifina yayi sai dukkan dokuna suma suka d'au haniniya. Hakanne ya sakani farkawa a rud'e Na fito daga d'akina, ina sako k'afata a d'akin mahaifana, Waziri Na cakama baba k'arfe a mak'oshi,, babana ya rik'e mak'ogwaronsa da hannu, yaringa min nuni da d'ayan hannun alamar Na gudu karnayi magana kuma, Na fahimci haka saboda ni baba yabama ajiyar abin d'aukar hoton da takardun, inhar iyayena zasu iya jurar mutuwa akan su bashi ni mezai hana na bi umarnin baba na gudu da abun, ko takan iyalaina banbiba na gudu ta hanya mafi sirri dana Sani, lokacin dana fito zan gudu waziri ya farga dani, hakanne ya sakashi biyo bayana, ganin bazai cinmini ba saiya saka dogarai masu tsaron k'ofa akan su bini wai na kashe iyayena zan gudu. Na rasa Inda zan dosa da wad'annan kaya saboda na tabbata ana bina a baya, saboda mun had'a ido da waziri, na shiga cikin jeji sosai, dan a wancan lokacin gari bai gama dunk'ulewa waje d'ayaba irin haka, Masarautar gagara badau ba tsakkiyar gari takeba kamar yanzu, dabarar hawa bishiyace tazomin dan haka na hau itaciyar wani Kalgo dake kusada k'oramar da mukan raka Yarima hutawa, har dogarannan da waziri ya saka su biyoni suka iso wajen domin nemana, ALLAH bai basu ikon ganinaba, saima suka wuce ni, lokacin sanyine sannan, nasha sanyi dan na wahala, sosai na fita hayyacina, abin mamaki da asubahi sainaji hayaniya a kusa dani, ido na bud'e da k'yar saboda tsantsar jigatar da nayi da muku-mukun sanyin wannan lokacin, wannan bawan ALLAHn nagani tare da Wanda yazo masarauta ya bamu abin d'aukar hoto (ya nuna baba Rabilu), hakanne ya sakani jin dad'i na sakko a nufin maida masa abinsa, nakuma sanar masa dalilin abin d'aukar hoton an kashemin iyayena, sai dai ina sakkowa wasu mutane na isowa wajen a mota guda biyu, yunk'urin guduwa mukayi mu duka ukun dukda su saima lokacin suka farga da ni a wajen, sun sami damar kama Wanda ya bama mahaifana abin d'aukar hoton, saboda kamar yaji ciwo a k'afa bazai iya guduwa ba, shine ya ringa fad'a mana mu gudu karmu sake mu basu abinnan. Iya k'arfinmu muka ringa gudu a lokacin Ranka ya dad'e, nashiga tashin hankali ganin rana tsaka masifa tazo ta haye mini ba tare dana san farkonta ba, gashi na rasa iyayena, na baro iyalina da k'anwata, bansan halin da suke cikiba, na samu damar shiga wani k'auye, Anan ne nasamu taimakon wani tsoho makaho, dan shine yabani mafaka ta tsawon shekaru 4, makahon tsohonnan yana zaune ne da matarsa amma ita tana gani, lokacin da jama'ar gari suka farga dani a gidan sai sukaje suka sanarma mai unguwar yankin, shikuma ya sanarma dagaci, har gida akazo aka tafi dani wani babban k'auyen dake kusa dasu inda dagacin yake akamin tambayoyi nida tsohonnan makaho, koda aka tambayi baba makaho saiya sanar musu ni d'an y'ar uwarsane, nazo ne na koyi sana'a na koma garinmu, dagaci yarigada ya yarda da baba makaho shiyyasa ya amince, aka kuma barni nacigaba da zama a k'auyen, tundaga wannan lokacin nasamu saken zama k'auyen gamji, ban sake waiwayar masarauta ba har tsawon shekaru hud'un nan. Saida ALLAH yayma baba makaho rasuwa sannan, matarsa gudun kar naci gadonsa shine tace yakamata na koma gida hakanan, ban mata musuba na had'o y'an kayana da abinda na samu a k'auyen da wad'annan takardu da abin d'aukar hoto nabaro k'auyen ina kuka saboda sabo. Sai dai abinda ban saniba Ashe anata bibiyata har lokacin, tun a hanyata ta shigowa gari wasu mutane suka farmin, na zubda komai nawa amma banda akwatin dana zubo abin d'aukar hoto d'innan da takarda, a cikin wannan gudu sai Ubangiji ya had'ani da wani bawan ALLAH akan besfa, ya bigeni, naji mummunan ciwo dan alamomin fitar rai sun bayyana agareni, cikin magana da k'yar, na mik'a masa akwatin ina rok'onsa dan ALLAH ya kar6i akwatinnan, ya Isar da shi masarauta amma yarima Sameer ko gimbiya Haneefa zai bamawa, ko mahaifiyarsu, bayansu karya bama kowa, idan bai samu damar badawa a yanzuba yabari sainan gaba inhar Yarima Sameer yay girman mallakar hankalinsa, zai iya kwatama kansa y'anci saiya bashi, na rok'esa karya ci amanata dan ALLAH, na aminta da shine shiyyasa na bashi....., da Sauri ya amsamin da insha ALLAH bazaici amanataba dan shima yana aikin jaridane, iya abinda naji kenan Daganan na suma a wajen, ban sake sanin komiba kuma, sai farkawa nai na ganni tare da wani maharbi jikinsa duk ciwuka, shine yaci gaba da kulawa dani tsawon lokacin ina jiyya, ban ta6a fad'amai ni waneneba, baikuma ta6a tambayata ba har shekaru sukaja, ganin girma ya kamashi sosai ya rok'eni na sanar masa daga ina na fito?, dan karya bar duniya da kokwanto a ransa, banyi nauyin bakiba na sanar masa komai. Yasha mamaki kwarai da gaske, dan suma labarin ciwon Sarki yaje musu, harma da nad'a k'aninsa da akayi ya maye gurbinsa. Shine yabani shawarar fara bibiyar masarauta kozan samu wani labari akan ahalina da jikin mai martaba, daga lokacinne nafara 6adda bamin shiga masarauta, na fahimci k'anwata ta auri wani bawa, matata ALLAH yamata rasuwa wajen haihuwar cikin dana barta dashi, d'an yayata data rasu itama ta bari shine k'anwata tacigaba da rik'o, a yanzu haka shine Wanda yazama direbanka Ranka ya dad'e, wannan shine abinda nasani ALLAH ya k'yautata rayuwarka, ya d'aukaki darajarka da mulkin masarautar gagara badau.”

Daga Muftahu har Galadima ajiyar zuciya suka sauke, kowanne yana jinjina lamarin a zuciyarsa, shi dama baba Rabilu ya fad'a masa kafinsuzo, kafin Galadima ko Muftahu su sami damar magana baba Rabilu ya fara fad'in “Lallai kamar yanda na sanarmaka randa nazo gareka ranka yadad'e d'an uwanane shi wannan daya bada camera d'in, da ni da shi duk aikinmu d'ayane, bayan yakai wannan camera ga mahaifin Badi, gidana ya zarto, amma saiya iske ban dawoba sai iyalina kawai, yabar musu sak'on wasik'a da address d'in inda zan sameshi, wato k'oramar bakin gari inda shi Badi ya gammu, inayin sallar asubahi kuwa na nufi wannan wajen dan ya rubutamin Cewar yana cikin mawuyacin hali, yana tsaka da fad'amin abinda ke faruwa saiga wad'annan mugaye sun biyomu, bansan a ina sukaji muna canba, na gudu ne a tunanina shima Habu ya gudu, Ashe sun kamashi, saida na fara jiyo sautin muryarsa dake amsa kuwwar karmu tsaya mu gudu, badan nasoba na gudu nabar Habu a hannunsu, wasu a cikinsu sun cigaba da bina, amma wani mai lambu ya taimakeni ya 6oyeni, kwanana biyu a cikin lambun, saida mukaga komai ya d'an natsa sannan na fito Na koma gida, duk tunanina ai basu ganniba, shiyyasa nacigaba da y'an hidindimuna domin 6adda kama, a 6oye kuma na shiga binciken wanda Habu ya bama Camera d'in, dan ya gayamin tana masarauta wajen mai kula da barga, Labarin mutuwarsu tazomin shida matarsa a bisa bincikena, saidai a masarauta ance d'ansu Badi shine ya kashesu, Sam ban aminceba, wannan ya sakani Neman Badi domin na kar6i camera d'in hannunsa, inada tabbacin shine Habu ya sanarmin cewa gashi can alokacin da mutanen nan suka iso, saidai kallo d'aya namasa muka fara gudun tsira, daga nan kowa ya kama tsaginsa. Dole na ajiye aikina saboda tsaro, na kawo rigar siyasa na sanya dan nema ma kaina girma, shekarata 6 a rigar siyasa akayi yunk'urin kasheni, ba kowa bane da wannan aikin face Alhaji Shehu Adamu Darma, har gidana ya saka aka satoni, nayi mamakin ganinsa, dan jam'iyyarmu d'aya, wani sa6ani bai ta6a shiga tsakaninmu ba, dan haka na nemi dalilin sanin miyasa zaisa a d'akkoni cikin iyalina? bayan mu y'an jam'iyya d'ayane. Ya kwashe da dariya yana nunani da fad'in lallai Alhaji Rabilu fanisau bakada hankaki, a tunaninka dukkan 6addamin da zakayi bazamu ganoka ba? yanzu dai dukma ba wannanba, ina camera?. Nace wace camera kuma? Wani wawan duka yaronsa yamin, na dafe wajen saboda azaba, Darma yakuma cemin ina camera d'in da Habu idris ya bani? nanma na sanarmasa ban saniba, wannan ne yasakashi kar6ar k'arfe ya kwad'amin a kai saboda haushi, daga nan na fad'i a wajen, ashesu duk sun d'auka a lokacin dukna mutu, shiyyasa suka jefar dani gefen hanya suka tafi, wani bawan ALLAH ne ya d'aukeni yakai asibiti, abinda yasa su Darma basuji labarina ba wanann mutum ba d'an nan yankinmu baneba, fataucine ya kawoshi, daya d'aukeni kuma saiya bar nahiyar wannan yanki dani gaba d'aya, nayi jiyyar shekaru biyu, kafin na dawo dai-dai, duniya sukta d'auka na mutu, saida na d'au shekaru bakwai banzo wannan yankinba, dan bawan ALLAHn nan yazo har nan ya kwashe iyalaina ya kaimin, bayan yamusu bayanin dazasu fahimta, bayan shekaru bakwai nakanzo nad'anyi bincikena na koma cikin 6adda kamanni, a wannan yanayinne na farga da Badi, ban sanshiba gaskiya, amma ganin yanayinsa tamkar mai lek'en asiri shine na fara bibiyarsa harna fahimci wanene shi, hakama waziri da d'ansa, na lura kullum cikin bin diddigin yalla6ai Galadima suke suma, nima wannan abun shine abinda na sani, kunji dalilin Darma na kirana Fatalwa”.

Galadima da Muftahu sunyi shiru cike da tsabagen rud'ani da al'ajabi, da k'yar Galadima ya iya bud'e baki cikin muryar tsananin damuwa yace, “waishin minene a cikin camera d'in nan? Yanzu kuma wanene ke rik'e da ita?”.
Baba Rabilu yace, “Duk wannan muke son sani ranka ya dad'e, yanzu haka muna kan neman wanda badi yabama wannan Camera, dan na sanar masa har yanzu batazo gareka ba”.
Galadima ya sauke ajiyar zuciya yana cije lips, idonsa yayi jazur, ya kalli Muftahu sannan ya kalli Badi dake zaune kansa a duk'e, “Badi yanzu idan ka gansa zaka iya ganesa kenan?”.
“insha ALLAH ranka ya dad'e zan iya, saidai idan har ya mutune, bakuma ma fatan hakan”.
Shiru dukansu sukayi kowa na nazari, Galadima sai ajiyar zuciya kawai yake saukewa, shi kad'ai yasan mi yakeji, ya kalli Muftahu yana fad'in “Sarkin mota ya shigo, dan nasan baisan matsayin Badi a wajensa ba”.
Muftahu ya amsa da “to ranka ya dad'e”.

Cikin y'an mintuna saiga Sarkin mota tare da Muftahu sun shigo, a k'asa ya durk'usa yana musu sannu, Galadima ya kallesa yana nuna masa Badi, “kasan wannan?”.
Badi da Sarkin mota suka kalli juna, a lokacin ne Muftahu da Galadima sukaga kamannin su, saidai shi Badi tsufa ya 6oyesa kad'an.
Ganin sun shagala da kallon juna kowa yakasa magana sai baba Rabilu ya katsesu da fad'in “Badi kamasa bayani mana”.
Dattijo badi ya kamo hannun Sarkin mota kusa da shi, yana zubda hawaye yace, “matso gareni Yunusa, nine babanka yayan mahaifiyarka, Badi ya rungume Sarkin mota suka fashe da kuka, a haka yake bashi labarin alak'arsu. Saida kwalla ta cika idon Galadima, hakanne ya sakashi tashi ya fice daga falon, Muftahu da tausayinsu ya kamashi shima ya bi Galadima da hanzari.
A tsaye ya iskeshi ya tsurama flowers d'in da akama gidan ado dasu ido, hannayensa biyu duk cikin aljihu, gaba d'aya bugun zuciyarsa ya fara canjawa, sai had'iye yawu yake da k'yar, wayarsa ya zaro daga aljihu, rasa wanda zai kira yayi, sai bin numbers d'in yake da idanu yana canki canka, ya tsansa dai ya sauka kan number Munaya.........



**********

Fitowata daga wankan yamma kenan Munubiya ta shiga, yau kwana biyu duk zuciyata babu dad'i, hakannan na tsinci kaina cikin 6acin rai, harzan fara shafa mai Aryaan ya shigo d'auke da Abdurrahman yana kuka, dole na ajiye man na kar6esa, na ta6a jikinsa da har yanzu zafin zazza6in daya yini da shi bai saukaba, saboda tunda asuba ya farka da kuka cibiyarsa na ciwo, kashinsa harya canja kala, saida innaro tazo tabashi magani sannan muka samu nutsuwa, daga nan kuma sai zazza6i, shine har yanzu nake d'an jin jikin nasa da zafi kad'an, nono na saka masa a baki kozai kama, dan duk yinin yau bai shaba, na sauke ajiyar zuciya ganin ya kar6a, ina shafa kansa idona na kallon fuskarsa data fara rikid'ewa zuwa kamannin mahaifinsa wayata ta shiga Ring, d'auke idona nayi daga kan Abdurrahman na maida ga wayar, nayi mamakin ganin yalla6ai, danna canja sunan tun a waccan ranar, na daiyi picking a d'arare na saka a kunne. yau dai banjira k'orafinsa ba nace, “Ina yini”.
A yanda ya amsa min sallamar da gaisuwar saida gabana ya fad'i har na cire ma Abdurrahman nono ban saniba, aikam ya fashe da kuka.
Hakkane yakuma rikita Galadima daga can, yace, “miya faru? Waye ke kuka?”.
K'aramin tsaki naja, nace, “Abdurrahman ne, wai dama ka dawo?”.
Bai amsa min na k'arshen ba saina farkon, yace, “mi'akai masa?”.
“Babu komai, bayajin dad'ine kawai”.
Lips d'insa ya cije yana fad'in “yanzu zanzo gidan”. Bai jira cewar Munaya ba ya yanke kiran.

Sororo nayi ina kallon wayar, kai kace zan ganosa a wajen ne, Munubiya data fito ta katseni da fad'in “mikike kallo haka? ga ruwan nono kin bari yana zuba a jikin yaro”.
Ajiyar zuciya na sauke, sannan na gyara ina kwantar da Abdurrahman d'in dayay shiru.
Munubiya dai takuma tambayata, fad'a mata zuwan Galadima nayi, tace, “oh shine kikema wannan mamakin ko miye?”.
'Dan hararta nayi, amma bance komaiba, itama ta ta6e baki tana kamo hannuna ta zauna a stool d'in Mirror. Wai sai tamin kwalliya.
Da faro k'in yarda nayi, saida naga ta 6ata rai sannan na hak'ura dai tamin inata tura baki gaba.....................✍🏻






ALLAH Sarki, wlhy harna fara missing d'inku, waya tamana tsiya😢, yanzuma da wayar Oga nayi typing, koba komai Comments naku na sakani nishad'i, I Miss you so much all😔😘😘😘❤❤


Insha ALLAH vary soon zan dawo gareku😂.



Bilyn Abdull ce🤙🏻


BOOK 3 👉🏻1⃣1⃣➖1⃣2⃣


.............Mintuna basufi 20 da gama kwalliyar ba saigasu Aiyaan sun shigo dad'an gudunsu, Munaya na cikin d'aki tak'i fitowa, wai kunyar su inna suganta da kwalliya takeyi.
Inna ta dakama su Aryaan tsawa saboda batason wannan gudun.
Nutsuwa duk sukayi.
Tace, “Gudun mi kukeyine?”.
Y'ar rige-rigen fad'a suka fara, kowa yana ture d'an uwansa akan shine zai fara fad'a, ana cikin haka Yaa Anas yay sallama.
Hayaniyar su Aiyaan ta hana aji, sai laraba ce ta farga dashi, shine Yakuma yimasu Aiyaan tsawa suka nutsu, kowa ya zauna gefe yana tura baki.
Yaa Anas ya gaishe da laraba da innarsu munaya, Munubiya ma ta gaisheshi, ya Amshi Ameen dake hannun inna yana fad'in “inna Yalla6ai Galadima ne fa agidan namu, gashi kuma duk su Abba basa nan, shine nace ko'a kawoshi nan ne”.
Inna tace, “A'a Anas, ai ba'ayi hakaba, bara na d'akko makullin d'akin Abbanku saika bud'e masa nan ya shiga”.
Anas yace, “to inna”.
Laraba dake taya Munubiya shirya su Amaturrahman tayi murmushi, a ranta tana yaba yawan karamci na ahalin Munaya, mutanene masu dattako da sanin darajar d'an Adam, shiyyasa kullum take kuma taya Galadima murna da samun tsatson wannan mutane.......
Tunaninta ya katse lokacin da inna tadawo da key ta bama Anas, Ameen ta kar6a a hannunsa shikuma ya fice.
Munubiya tace, “innarmu ajiye wannan ki k'arasa sama Abdurraheem kayan Dan ALLAH, sainaje na had'ama Abbansu abincin, nasan yanzu yayi”.
Inna ta harareta, “kai nifa kunma maidani Nanny d'inku, nizan ke muku hidimar y'ay'ane?”.
“please mana innarmu, basune masu kawo miki kaza kina ciba sannan kin tsufa”.
Laraba tayi dariya tana fad'in “Gaskiyarki kuwa Maman 2, ALLAH dai yaja da rai”.
Inna tace, “iya kema biyema shirmennan nata zakiyi?”.
Laraba takuma darawa tanama Abbdurrahman rawa.
Itadai Munubiya ta fice tabarsu, laraba na bama inna amsa.

Duk ina jiyosu daga d'aki, haka kawai sainakejin wani iri, yanzu dole ta gaban su Innarmu zanbi natafi wajensa? Na kalli kaina a mirror kunya ta kuma kamani, dukda Simple kwalliya Munubiya tamin nayi k'yau, dan d'aurin kaina ya zauna dak'yau, fuskata ta kuma nutsuwa, har rantsuwa tamin inhar na canja wani Abu saitayi 2weeks batamin maganaba, nasan kad'an kenan daga abinda Munu... Zata iya, shiyyasa dole na hak'ura na bari.....
Shigowar Munubiya yasani waigawa na kalleta, ta harareni tana matsowa tamin kallon tsaf, nasan sotake taga mina goge kona canja, ganin komai yana yanda tayishi saita kuma d'aukar soson hoda ta gyara, ta d'akko turare tana kuma fesamin, hannunta nai saurin rik'ewa ina 6ata fuska, “Wai Sweetheart bazaki barshi haka bane? Turaren nan har hawa kaifa yake, Ni wlhy kunyarma fita nakeyi”.
Munubiya ta fisge hannunta tana dariya da fad'in “to kibi ta k'ark'ashin k'asa kawai mana, kuma wlhy ki nutsu, idan yauma tsiwar zaki masa saiki bada himma, anacewa mutum Idan ya haihu yana hankali kedai bakiyiba, saima rashinsa kika k'aro, malama muje yana jiranki”.
Yanda kukasan na make Munubiya haka naji, amma saina k'yaleta, nima nasan ta hanyar da zanbi na rama, gyalen data samin a kafad'a nabi da kallo.
nace, “haba Munu, amma wannan d'an gyalen Dan ALLAH?”.
“Okay, wajen surukinki zakine? ALLAH ki kiyayeni”.
Baki na murgud'a mata.
Tace, “oho dai, kije kimasa kidawo ta cinyayyen lips, danba barinki zaiyiba”.
Juyawa nayi na kalleta, amma saita d'auke kai tamkar bama itace tayi maganarba. Nayi kwafa kawai muka fito.
ALLAH ya soni babu kowa a falo sai su Aiyaan, hakkane ya sakani sauke ajiyar zuciya nad'an saki jikina.

Gwaggon Haleematu dake kaikawo a kitchen da tsakar gida saboda itace ta kar6i girki tabimu da kallo, gulma nacin ranta, daga ni har Munubiya d'auke kai mukayi tamkar bamu gantaba, muka shige falon Abba da takalman Galadima heif cover milk ke a k'ofar.
K'amshin turarensa yafara amsa mana sallama, na shak'a na lumshe ido.
Hankalinsa nakan yaransa da duk suke jikinsa, yana sanye cikin milk d'in shadda harda hular zanna bukar itama milk da d'an kwalliyar Brown kad'an, sosai yamin k'yau amma saina d'auke kai tamkar banma gansa ba.
Munubiya tace, “To Abban 3 gatanan nakawo maka”.
Murmushi yayi, idonsa sanye cikin farin eyeglasses, cikin muryarnan tasa mai kama da anmasa dole yace, “Thanks you Auntynmu”.
Murmushi itama Munubiya tayi, ta jinjina masa kai ta juya zata fita, har takai k'ofa ya katseta da fad'in “Su twins rowarsu akemin?”.
Hannu ta saka ta dafe bakinta, saikuma ta janye tana cewa, “A'a Abban 3 zasuzo su

Please Login or Register in order to submit comment