Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sallama munji a k'ofar d'aki.
Matashin saurayi ya shigo, Wanda Munaya bazata ta6a mance fuskarsaba, wato Haidar, hakane ya sakata zabura ta mak'alk'ale Galadima.
Haidar yay murmushi kawai yasamu waje ya zauna, saiga kuma dattijo da Galadima yata6a had'uwa dashi a India, shima dai da kallon k'urilla ya bishi, basu fita a mamakiba saiga Driver daya ta6a d'akko Munaya lokacin dayace suyi auren Contract shima ya shigo, saikuma mabanbanta fuskoki Wanda sun had'u dasu a mabanbanta gurare, harda masu zuwama Munaya a k'awaye, saida duk suka zauna suka nutsu sannan suka gaisa da baba mai kanwa, Galadima ma dai a d'arare ya yarda yabasu hannu sukayi musabaha, nikam uwar y'an tsoro ai ina mak'ure a bayansa, ALLAH ma yasoni banzo dasu Abdurraheem ba, suna gidanmu.
Baba mai kanwa ya nuna manasu yana fad'in, “Ina fata duk kun ganesu?”.
Duk muka amsa da eh a d'arare.
Dattijon daya had'u da Galadima a India ne yafara magana a nutse, “Muhammad Sameer ya bayan rabuwa da gwagwarmayar rayuwa?”.
Galadima ya amsa da “Alhmdllh”.
Tsoho mai sihirtaccen k'yawu zam jinin indiawa yace, “ka tuna na fad'a maka matarka Ce fitilarka? zuwa yanzu ka tabbatar?”.
Galadima ya gyara zama yana Murmushi har hak'waransa na bayyana, yace, “Lallai ban mantaba kaka, saidaima nabama wasu labarin, nakuma mik'a godiya ta musamman agareku da fatan ALLAH ya had'amu daku a aljanna, ya kuma biyaku da mafificin alkairi bisaga taimako na mussaman da kuka bama rauwarmu ni da matata, duk da kasancewarmu ba jinsi d'ayaba”.
Gaba d'aya suka amsa da amin, haidar ya nema izinin Galadima domin Neman afuwar Munaya. Galadima ya bashi izini.
Haidar yace, “ki gafarceni bisa ga kalmomi masu zafi dana fad'a a gareki a wancan lokacin, hakan ta farune bisa k'ok'arin janyo hankalin mijinki domin jin tausayinki, kasancewarsa mutum mai tausayi da gudun shigar wani matsala ta dalilinsa”.
Munaya ta murmusa tana kallonsu. Tace, “na yafe maka wlhy, kuma komai yawuce, fatana ALLAH ya tabbatar da addu'ar mijina a garemu baki d'aya”.
A tare aka amsa da amin. Mun dad'e muna tattauna abubuwa da dama, kafin daga bisani sumana sallama su tafi, Wanda bai saniba saiya d'auka da gaske mutanene, baba mai kanwa yay mana doguwar nasiha mai ratsa jiki, wadda harta d'arsa tsoro a ranmu, yakuma ja mana doguwar addu'ar. Galadima ya ajiye masa alkairi mai tsoka mukayi masa sallama muka fito, bamu dad'e a gidanmuba muka koma gida jikinmu a sanyaye da abubuwan da suka faru tsakaninmu da baba mai kanwa da su Haidar.

Kwanaki uku da faruwar haka labarin rasuwar baba mai kanwa ta riskemu, mutuwarnan itama ta girgizamu k'warai da gaske, munkuma jema iyalansa gaisu.
Manyan dake kula da matsalolin gidanmu duk Ubangiji ya d'aukesu, yau babu Innaro babu baba mai kanwa.
Zuwa yanzu kam ko ina su Amaturrahman zuwa sukeyi, sunyi wayo sosai da girma, hakama yaran Munubiya danasu Safara'u datai hak'uri takoma gidan mijinta suke zaune lafiya da kishiyarta da haihuwa yau ko gobe.
Ayusher ta haihu namiji, dan haka muka d'unguma Niger suna k'wanmu da kwarkwata, hardama y'an gidanmu Wanda wanannne zuwansu na farko, sunkuma gano abinda yafi k'arfin shirmensu kuwa, yayinda girman Innarmu yakuma yawaita a zukatansu.
Mun dawo da kwana hud'u Aunty Salamah da Badeerah matar Yaa Fadeel suka sauke, babu nisa tsakaninsu Farhat d'in Nurenma ta juye, Saiga Samha ma ta haife yaranta y'an biyu duk mata, hakama matar Matawalle. Kai wannan abun dad'i da yawa yake, munsha shagulgula sunan kam babu k'arya.
A lokacin ne kuma Galadima yafara k'orafin na yayaye su Abdurrahman wai kona samu nima. Dan gatan da ALLAH yay mana ni da Munubiya muna jerin mata da al'ada ke d'auke musu bayan jinin bik'i har sai sun yaye, amma nasan murzar da Galadima ke min da tuni k'ila ciki na uku na d'auka🤭🤣.
Yanzuma danake kwance a jikinsa dariya kawai nayi. Nace, “su Abdurraheem basu gama yin k'wariba my king, inama laifin sud'anyi 4years haka?”.
Harara ya zubamin da fad'in, “yarinya kinma isa, insha ALLAH gab kike da d'aukar wasu ukun”.
Bance komaiba sai dariya da nayi ina sumbatar goshinsa domin kauda zancen, dan inhar yay zurfi zai zama rigimar da muka sabane kawai, nikuma bana buk'atar hakan.


★★★★★★★★★

Rayuwa ta cigaba da gungurawa dai-dai gwargwadon iko, yau da dad'i gobe babu, soyayya nida mijina ba'a magana.
Shekarun Abie biyu kenan da dawowa cikin ahalinsa, yayinda kunnen kowa na masarautar gagara badau yake a bud'e dan sonjin makomar sarautarsa. Saidai kuma tsit babu wani bayani.
Yay shiri yaje har prison wajensu Harun jikin su Alhaji Mansur yayi sanyi matuk'a, Wanda sukaso ya k'are rayuwarsa tamkar gawane a gabansu, lallai duk saurin Bawa da son nuna k'arfin iko sai ya jira ALLAH, Abie baice dasu komaiba ya juyo ya fito, shiruma maganace ga mai hankali.

A 6angaren mai martaba sunata fafatawa ne shida mama Fulani tun dawowar Abie, yanason tado da maganar sarauta amma mama Fulani ta kasa ta tsare, ta hanashi.
Yayinda gimbiya zulfah keta k'ulunboton asirce-asirce agefe dan kar mulki ya koma wajen Abie, duk da batada wata fawa a masarautar yanzu, saboda tunda wancan abun ya faru mai martaba ya hanata shiga turakarsa, babu kuma wani Abu dayake mata a matsayin matarsa, bai kumace ya saketa ba, dan kowa yasan Sarki a k'asar Hausa baya saki, saidai idan mutuwa ta raba. Da farko tashiga damuwa tamkar tayi nadama, amma dawowar Abie saita kuma birkicewa, musamman da Matawalle yay aure matarsa kuma ta haifi mace, duk zugarta dason 6ata Galadima a wajen y'ay'anta Matawalle baya d'auka, saima yakuma kusantar Galadima suka d'inke waje d'aya, su wambai ne dai ma sai kuma rura k'iyayyarsa suke a ransu, har Momma da Abie haushi sukeji, duk da jansu a jiki da sukeyi a banza, uwarsu da mama Fulani sun rigada sun hure kunnuwansu.
Ganin abin zai kwa6e mai martaba ya shirya taro na manyan masarautar, harda gayyar papi Wanda ayanzu shima lafiya take Neman yimasa k'aranci, saboda girma, dan yanama shirye-shiryen yin murabus ya d'ora mahaifinsu Nuren.
Mama Fulani batasan da wannan taronba ko kad'an, dan mai martaba bai nuna mataba ko da a fuska.

Galadima na kwance a tsakkiyar falonsa yana wasa da yaransa daketa hawa jikinsa yana musu doki, ni dai ina gefe zaune ina danne-danne a laptop. Nakan kallesu nai dariya idan sukai masa wani Abu.
Wayarsa dake kusa dani tayi ring, d'auka nayi na mik'a masa, ya sauke Amaturrahman dake saman fuskarshi yana duba wayar, ganin mai martaba sai ya mik'e zaune sosai yana musu alamar suyi shiru.
Duk da ba wayone dasuba yariga ya koya musu hakan, duk kuwa sai suka rik'e bakinsu. Ni dai dariya nayi kawai na kauda kaina.
Galadima ya amsa kiran cike da girmamawa.
Yana yanke wayar ya mik'e.
Kallonsa nayi da mamaki, “My king lafiya kuwa?”.
“Duk'owa yay ya sumbaci goshina sannan ya zauna a hannun kujerar da nake zaune. yace, “Mai martaba ne ke buk'atar ganina wai yanzunnan”.
“Tofa ALLAH dai yasa lafiya?”.
“To amin, bara na kimtsa naje naji”.
Na amsa masa da to.
Yaran duk suka mik'e zasu bishi na kamosu ina lalla6arsu. “Haba my sweetness kuzo kuji, Abbu wanka zaiyi kunji”.
Abdurraheem ya kwa6e fusaka zaiyi kuka, danshi duk yafi sauran y'an uwan k'ulafucin uban, ko barci yake Galadima yay magana saiya farka, gashi bashida yawan kwaramniya, yanda Amaturrahman da Abdurrahman zasu saki jiki suyi wasa Abdurraheem bayayi, idan har Galadima na gida to yana manne dashi.
Koda ya fito zai tafi sai suka sanya kuka, lalla6asu yayi yay musu wayo ya gudu, amma Abdurraheem saiya saka kuka harda shashsheka yana shid'ewa, dole Galadima ya dawo da baya ya d'aukesa suka fita. Nikuma naita lallashin su Amaturrahman har suka saki jikinsu kuma.


Abdurraheem yana ganin Abie sai kuma ya mak'ale masa, ya d'aukesa ya d'ora a cinya yana murmushi.
'Dakin taron yayi tsit kowa yana sauraren Mai martaba.
Cikin nutsuwa da halin dattako yafara jawabi kamar haka.
“Inama kowa fatan alkairi, nasan kowa zaiyi mamakin wannan taro na gaggawa, wasu dalilaine suka saka yinsa tilas, tun bayan kama mutane da suka cutarmin da d'an uwa babu wani zama da mukayi ko magana akan wannan matsalar, duk da kasancewar akwai namu mutane a ciki, waziri da d'ansa, da kuma sirikina, sai mahaifin mahaifiyata wato kakana kenan, tabbas abune da musalta bak'in cikin da mukayi 6ata lokacine, amma mun tura komai ga Ubangiji ya musu hukunci dai-dai da yanda suka aikata mana, a kullum kuma cikin yaba k'ok'arin d'anmu mukeyi bisa ga jajircewa akan tonuwar asirinsu, ALLAH ya albarkaci rayuwarsa da ta zuri'arsa, akwai wad'anda suka bashi taimako sosai, amma bamuyi musu komaiba. Bawai mun manta dasu baneba, sunan cikin zukatanmu. To a yanzu dai mak'asudin zamanmu anan shine inason maida sarautar dake kaina ga d'an uwana, tunda ALLAH yabashi lafiya, sai a d'ora daga inda aka tsaya”.
Cikeda mamaki Abie ya kalli mai martaba, cikin Dakatar dashi ya d'aga masa hannu yana 6ata fuska. Sannan ya yunk'ura ya mik'e yana mik'ama Galadima Abdurraheem dayay barci, har yanzu bawai ya dawo normal bane, da taimakon sanda yake tafiya. Yace, “Ku gafarceni bisa katse hanzarin d'an uwana danayi, maganar gaskiya bazan kuma wani mulkiba, akwai iyayenmu anan yakamata su dubi lamarin bisa ga idon basira, har zuwa yanzu bawai lafiya Ce ta gama isataba, saidai muce Alhmdllh domin Ubangiji yamana dukkan Ni'ima, ai ko lafiyata k'alau zan iya sauka a wannan shekarun nawa na bashi dama, munyi maganarnan ni da shi nace yabarta anan, amma saida ya kawota, to wlhy, wlhy kunji dai na rantse ko, bazan sake hawa karagar mulkiba, kwanan nanma nake shirin komawa India ni da iyalina, dan ALLAH wannan maganar ta tsaya iya haka, karmu sake jayayya a kanta”.
Shiru kowa ya kasa motsi, domin wannan rikici yazama na manya, hakanne ya saka papi mik'ewa ya sallami kowa, ya rage daga shi sai mai martaba da Abie a d'akin taron.


*****

Na fito wanka na iske Galadima zaune a bakin gado hannunsa dafe da kai, da sasaarfa na k'araso dan nasan akwai matsala kenan, musamman da acikin y'an watannin nan sau biyu ciwonsa na tashi, duk da akowane bayan watanni uku sai munje India ganin likita shida Abdurraheem, dayake yanzu hankalinsa yana nan Nigeria akan Company da suketa k'ok'arin ginawa, zuwa India saiya zame masa sai time to time kokuma wani gagarumin Abu ya taso daya zama tilas saiyaje.
Laimar ruwa da yaji a jikinsa ya sashi d'agowa da hanzari ya kalleni, kafin nace wani Abu sai kawai ya rungumeni tsam a jikinsa, sai kace zai maidani cikine, kusan mintuna 3 muna a haka, sai sauke tagwayen ajiyar zuciya yakeyi, nikam ina shafa gadon bayansa a hankali.
Nutsuwar daya samu ta sakashi d'ago muka zubama juna ido, murmushi mai kashe zuciya namasa ina shafa sajensa, cikin sanyin murya nace, “Waye ya ta6amin Barden gagara badau ne?”.
Lips d'insa ya ciza yana rik'e hannuna, cikeda damuwa yace, “Munaya sosuke kawai sudawo da abinda ya wuce”.
Nace, “Mikenan?”.
Ya sauke nannauyan numfashi ya zamewa ya kwanta, kansa bisa cinyata muna kallon juna yacigaba da fad'in, “Akan mulki mana, tun sanda Abie ya dawo na fuskanci Abba nason maida masa mulki, amma mama Fulani na hanashi, sannan a gefe mahaifiyar su Matawalle tana nata k'ulle-k'ulle, dama kwanaki mun fara maganar ni da Momma da Abie, saboda rikicin dake Neman 6arkewa tsakanin mama Fulani da mai martaba, a lokacin bansan kuma miya dakushe lamarinba, sai yau da rana tsakarnan mai martaba yace zai maidama Abie sarauta, wannan shine mak'asudun zaman gaggawar, kinsan kuwa wannan kujerar itace ke hana kowacce masarautar zaman lafiya da hargitse-hargitse, harta kai ga asarar rayuka, shiyyasa da Sarki yafara ciwo burin kowa ya mutu hattada y'ay'ansa da matarsa mai manyan y'ay'a saboda burin y'ay'anta su gaji mulki? Wlhy ina cikin tashin hankali, hankalinmu ya kwanta kowa yasamu nutsuwa a masarautar nan gawani bala'innan zasu 6alloma mutane, inaga kawai zamu tattara mu koma India harsu Abie da zaran anyi bikin Sauban. Da aunty mimi”.
“Ina bayanka wlhy my king, wannan itace babbar mafita kawai, domin cigaba da samun zaman lafiya mai d'orewa, hukuncin daka yanke yayi sosai”.
Ya lumshe idanu da shafo fuskata saboda jin dad'in goyon bayan dana bashi, domin k'ara masa nutsuwa saina d'ora bakina akan nashi nashiga masa wani salo mai cikeda kwarewa fiyeda yanda ya koya min, tamkar jira yake ya birkicemin, kafin kicemi labari ya canja salo, saigani da sake sabon wanka babu shiri.🤭

Tun daga ranar bamu sake jin maganarba daga bakin manya, sai munafunce-munafunce da sukaita wanzuwa, bakuma mujiba daga bakin Abie ko papi, dan aranarma ya koma inda ya fito, wannan dalilin Galadima ya samu yafara shirin komawarmu India da Zarar an kammala bikin Sauban daya rage sati biyu kacal.
Ana saura kwana biyu d'aurin aure ya zauna da bayin ALLAH da suka hidimta masa akan su tanderu.
Baffi, Baba Rabilu, Badi, Muftahu, Nuren, Saleem, Sir isa, su Ameer.
Dukansu ya bisu da k'yauta ta girma, tare da musu godiya ta musamman mara iyaka, yakuma y'anta Badi tare da k'yautar muhallin zama mai nagarta a cikin masarauta, hakama sarkin mota, ya basu hak'uri bisa ga jinsa shiru, abaya tattalin arzik'insa ya raunana ne, koyace zai karramasu bashida k'arfin hakan, amma yanzu kam alhmdllh komai ya dai-daita.
Suma sun masa godiya ta musamman a garesa da k'yak'yawar Addu'a, daga k'arshe ya kaisu ga Abie da Momma, sunci abincin rana tare da adalin tsohon Sarki wato Abie, sannan suka sha hira, dama kowa yasan Shiba mutum bane mai girman kai, ga yawan tsokana, shima yamusu k'ayuta ta musamman, hakama Momma tayi nata.

Washe gari ana gobe d'aurin aure kenan da tashin hantsi yasakani shiryawa wai namasa rakiya wani waje.
Kamar ko yaushe Sarkin Montane ke Jammu, yayinda dogaransa ke binmu a baya.
Mun Isa wani waje kusada birnin gayu plaza, wajen ya had'u iyakar had'uwa, a da shagunane kawai a wajen, amma yanzu kamar an rushe anyi wani gini na musamman. An saka k'aton allo mai d'aukeda hotunan kayan gyaran gashi dana kwalliya, an rubuta LADIES MIRROR da manyan haruffa, hakama jikin k'ofar wajen dayasha glass, an saka babban allo a sama mai kawo wuta da d'aukewa, shima dai irin rubutun farkone a nan, wato ladies mirror, abin ya k'ayatar dani, yana rik'e da hannu na muka shiga.
Ashe wajene na musamman na gyaran irin duk Wanda mace take buk'ata, gyaran jiki, saloon, kwalliya, kunshi, dakuma waje na musamman da kayan shafe-shafe na kwalliyar mata ake siyarwa, da glasses aka rarraba shagon, kowanne da 6angarensa, bayan ka fara iske reception a farko, sai office dayaji komai zam dake can k'arshen shagon, shima dai duk glass d'inne, amma daga ciki zagaye yake da labuloli, ba'a buk'atar ganin Wanda zai zauna a ciki kenan.
Bayan mun gama zagaya ko ina muka Isa Office d'in, Galadima ya saka hannu ya yaye wani allo da aka lullu6e da farin k'yalle.
Kallonsu nayi da mamaki, saiya nunamin rubutun jikin allon..
“Wannan tukuycine a gareki my mata, badan biyanki hidimar da kike daniba, dan idan biya zanyi abinda na mallaka kaf bazai iya biyankiba matata abar k'aunata, bugun zuciyata komaina Munaaya”.

Da tsantsar mamaki na d'ago ina kallonsa, yad'an ta6e baki da d'agamin kafad'a alamar gaskiyar kenan.
Kawai jinai hawaye sun gangaromin, na fad'a jikinsa ina sakin wani kukan farin ciki.
Hannu biyu ya saka ya rungumeni yana murmushi, sannan ya jani muka zauna bisa sofa guda d'aya dake a office d'in, ban tsaya wata-wataba na manna la66ana saman .....🤭.
Caraf ya cafke tamkar dama jira yakeyi, gaba d'ayama mun manta a inda Muke, mun tsunduma duniyar masoya wad'anda suka soyu a soyayyarma, saida naji yana Neman kauce hanya sannan na dawo hayyacina.
Na kuma rungumarsa tsam ina jero masa godiya wadda nama rasa wace iriya zanyi masa yasan naji dad'i.
Ya rik'e fuskata cikin tafin hannunsa yana bina da kallo, “My mata babu godiya a tsakaninmu, inma akwaita to nine ya cancanci nayi miki, domin kinmin abubuwa da baki bazai iya lisafosuba, kedai kawai ki rik'eni Amana ni da yaranna da k'anensu masu zuwa, idan kinkai hakan kin gamawa Muhammad Sameer komai, na haramta miki yimin godiya inhar akan wannan d'an wajenne”. Ya kamo hannuna yana zaro key d'in mota a aljihu ya d'oran a hannu.
Kallonsa nayi sannan na kalli hannayenmu, ya d'aga min gira da cije lips sannan ya mik'e.
Tamkar sokuwa haka na bisa da kallo, gaban loka k'arama dake office d'in ya nufa, ya kwaso wasu file ya dawo inda ya barni tamkar wata gunki, d'ayan hannun nawa ya kamo yana d'oran files d'in, “Wannan sune bayanai da form na ma'aikatanki, angama d'aukar kwararru a kowanne fanni, wannan takardun wajene da kowanne lasisinsa, ko gobe kika shirya ma'aikata zasu fara aikinsu.................✍🏻






ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏🏼




BOOK 3 👉🏻3⃣2⃣


🔚END!! 😢✋🏻


...............Ban San yanda zan musalta muku halin dana tsinci kainaba bisa ga wannan tukuyci na Galadima, saidaifa kafin wani dogon lokaci dukkan Wanda keda alak'a dani yasan da zaman wannan k'yauta, y'an uwa sai tayani murna sukeyi.
Y'an gidanmu dai saida sukaji wannan bak'ar al'adar tasu ta hassada, amma sun d'an danne zukatansu sukaimin murna.

Washe gari bayan d'aura auren Sauban da aunty mimi Galadima yaja gayyar abokansa da yayuna sukaje aka bud'e wajen saloon d'ina. Akuma ranar ma'aikata suka fara gudanar da aiki, dan a can naje na iske Galadima ni da tawa tawagar, na gana da dukkan ma'aikatana tare da basu umarnin duk Wanda ya shigo wajen a ranar amasa abinda yakeso k'yauta, Washe gari sai a fara na kudi.

Bikin Sauban ya gudana cikin k'ayatarwa, itadai aunty mimi koda aka d'aura auren shikenan, tace wane biki kuma a shekarunta, ana gama shagalin na Sauban tareda amaryarsa Ni'imatullah d'iyar Mom da biyu, itama ta tare gidan mijinta professor Ibraheem Macid'o, musalta muku yanda mukasha shagali 6ata lokacine.

Bayan bikin da kwana biyu Galadima ya fara koya min mota, koya motar da taso zama shiririta, wai dole saidai na zauna a cinyarsa ahaka za'a koyan, banida yanda na iya dole nayi hakan, cikin amincin ALLAH a sati biyu nagama kwarewa, kwana biyu da faruwar hakan na yaye su Amaturrahman bisa dagewar Ubansu akan shima k'annensu yakeso, danga Munubiya da ciki🤭🤣.
Dole nayi wannan yaye yara suka koma wajen Momma.
Kwanaki 10 cif dayin yayen saiga bak'ona yazo, karkuso kuga murna wajen Galadima, wai hanyar samuwar ciki ta bud'e.
Ni dai shiru namasa ban tankaba. Randa kuwa nayi wanka ai babu d'aga k'afa, ALLAH mai iko da falala kuma ya amince masa, koda wata ya dawo babu jini babu alamarsa, hankalina ya tashi na birkice masa, sai yayta tuntsuramin dariya da fad'in “Yarinya an fad'a miki nid'in na wasane, zan zama Abbu a karo na biyu, ALLAH yasa su zama 3+3=6”.
Tashinai nabar masa falon ina zun6ure-zun6ure, shikam yayta tuntsura dariya.
Nima nayi farin ciki da samuwar cikin, tunda naga hakan shine burin mijina da farin cikinsa, sai kuma fatan ALLAH ya sauke mu lafiya, dan wannan karon dai mun sa6a ni da Munubiya.



BAYAN WATA 6

Cikina ya fito sosai, ina samun tattali da kulawar mijina, kai kace wannan shine cikin farko daza'a Haifa masa, ga shak'uwa mai yawa dake tsakaninsa da yaransa, abin akwai birgewa mai yawan gaske.

Ranar wata juma'a kawai mukaga an tashi da wani gagarumin biki dabamusan na miye ba a masarautar, dama kusan kwanaki uku kenan bak'i nata sauka, ni dai harna kasa hak'uri na tambayi Galadima, yace, wlhy shima bai saniba.

Ana sakkowa daga massalaci sallar juma'a aka hana Galadima shigowa gida, papi ya umarcesa da zuwa ya zauna inda aka tanada dominsa.
Mamaki ya kamasa ganin gurin dank'am da jama'a, addu'a kawai aka gudanar papi yabada umarnin fara abinda ya tara mutane, daga baya koma mikenan jawabi zai biyo baya.
An umarci Galadima da tasowa zuwa saman daddumar dasu Abie da manyan sarakuna ke zaune, ya zauna a tsakkiya shidai zuciyarsa na faman tsitstsinkewa da bugun mamaki.

Turaki ya mik'e a tsanake zuwa gaban mai martaba Sarki Jalaludden Abubakar, yay gaisuwa tare da risinawa sannan ya zare rawanim dake kansa, gaba d'aga wajen aka d'auki kabbara, Abie yay k'asa da kansa yana share hawaye, shidai dan anfi k'arfinsane kawai, amma daba yanke wannan hukuncinba wlhy.

tuni bugun zuciyar Galadima ya k'aru ganin Turaki ya nufo garesa, zaiyi maganar papi yay masa alamar yay shiru🤫.
Dole ya maida bakinsa ya tsuke yana had'iyar yawu da k'yar.
Tsohon Sarki Jalaludden ya taso da taimakonsa Turaki ya cire hular saman kan Galadima aka d'ora masa sabuwa dal, sannan aka fara nad'a masa rawani akai, jikin Galadima sai tsuma yakeyi, ya kafe papi da Abie da ido ko k'yaftawa bayayi, shikad'ai yasan a halin dayake ciki, zufa sai tsatstsafo masa take a kowacce mahudar gashi dake a jikinsa.
Tsaf aka gama nad'a masa rawani jama'ar wajen suka d'auki kabbara, yayinda za'a saka masa alk'yabba sai dogarai suka baza riguna ana masa kirari.
Galadima yay k'asa dakai idonsa na kwararar hawaye lokacin da kunuwansa ke jiyo masa jawabai daga bakin sank'ira.

“ALLAH ya d'auki rawani ya maida bisa kan matashi kuma adali tsohon Galadima a yau yazama Sarkin wannan masarauta ta gagara badau bisaga adalcin tsohon Sarki mai murabus a yau, masarautar gagara badau tayi sabuwar amarya, a halin yanzu Mai martaba Muhammad Sameer Saifudden Abubakar shine Sarkin wannan adalar masarauta, ALLAH ya tayashi rik'o, yabashi ikon koyi da k'yawawan halaye irinna manyan wannan gida”.

Tuni waje

Please Login or Register in order to submit comment