Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[6/1, 3:39 PM] Rasheeda S Director: *🌺HAMDAH🌺*

*NA*

*RASHEEDA S DIRECTOR*


_(Book one)_


*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*



*Free page*


*Labari mai tsada farashi mai sauki ɗarin ki-ka 200 yabiya miki-ka bukata*
*Turo 200 ta wannan asusun bankin 3170524141*
*Rashida Salihu First bank*
*Ko katin waya na MTN 200 ta wannan Number 08034690723*
*tsiyan nagari mai da kuɗi HAMDAH labarine mai tsa da na baku shi a farashi mai rahusa👌🏻*



🅿️1



Karar tsayuwar mota danaji ne yasani saurin wanke kunfar sabulun Dana goga a fuska ta,namike dasauri na Kama jikin karfen window'n bayi nad'ale saman toilet naleka,
karar murna nayi harda d'an tsallena kad'an yarage kafata tawuce cikin toilet,
Naduru da sauri nad'au soso nafara wanke jikina da sauri-sauri wani gunma baisamuba nad'au langar ruwan najuye a jikina dasauri naja zanina nad'aura nafita a bayin hijjab nasaka nafita waje da gudu,
a kofar parlour mukayi Karo da Aunty Rafee'at salle natuma nad'ale jikin ta natukui kuyeta ina fad'in "oyoyo Aunty Rafee'at"
"Ummi dake biye da ita ta ce "ke saketa yadata zakiyi"
Sauka nayi ajikin Aunty Rafee'at nad'ale jikin Ummi "oyoyo Ummi na"
nafad'a Ina dad'a d'alewa jikin ta,
Ummi ta ce "ni da Alla sakeni Sam baki da hankali".
Ganin su Abba da Abbu da Mamie da Aunty Jaleela Ya Masa'ud Nusaiba Fauzan da nayi ne yasani sakin Ummi nayi gurinsu a guje nashe ge cikin su kowa Sai da nad'ale jikinsa harda Fauzan da Nusaiba Sai da na rungumesu muka fad'i kasa, Aunty Rafee'at ce tad'agoni a kansu tana dariya tare da fad'in "Kai Hamdah ai Zaki karyasu kefa bakida girma saina jiki
ko yaushe Zakiyi girman gaskiya oho"
washe baki nayi nace "ai Abba yace saura kad'an nakara girma sai a mai da ni gi da a kawo wa Inna wata kinga yanzu nakusa zama katuwa kamar ke da Aunty Jaleela".
Aunty Jaleela ta harareni ta karasa cikin parlourn tazauna tuni su Ummi sun zazzauna Ina rikeda hannun Aunty Rafee'at muka Isa muka zauna, Ya Masa'ud ya ce "ai kuwa saura kad'an kikamo Jaleela 'yargidan Inna"
Dariya nakuma tunsurewa da shi nace "da gaske Ya Masa'ud?"
Yace "sosai ma"
Aunty Jaleela tace "zamu Sami masala da kai Masa'ud i'dan kasa yarinyar Nan tarai Nani".
Tafad'a tare da gimse fuska Ya Masa'ud kuwa 'yar karamar dariya yy yace "to da nawa kk fi Hamdah'n"
Mamei tace "Kai Masa'ud zaka fara niman ta ko tun amota kk neman ta da sokana kaid'in danawa kagirme tan"
Masa'ud yace "haba Ammi karkisa ma taji dad'i ta da d'a d'aukar kanta wata babba, yarinya shekara shabiyar nabaki dan haka kidaina d'aukar kanki wata babba"

Aunty Rafee'at ta ce "kafad'i kwanakin da ka Bata da kanka kwana shabiyar ba"
Ya ce "Allah Aunty Rafee'at kinga wannan yarinyar ko gyanbo Yabata lfy sabo da tsabar son girman ta in da itace gaba da ni narantse da kullum d'aukar bulala za'tayi tace zatarika yimin duka"
"Yanzuma kayi abun dukan Mana kaga ko bazan ma hukun ciba" Jaleela tafad'a"
Inna ta ce "to jarababbu masu ganin hanjin juna kun iso ba"
Ya Masa'ud ya ce "Eh mun iso Inna'r korafi"
Inna tace Kai Masa'udu kafita a'ido yo shed'anan ci zaka yimin ja'irin yaro kawai"
"Wlh mutum koyayi marmarin yazo yagan kima da zaran yazo da masifa Zaki karb'e shi garama nakoma inda nafito"
Masa'ud yafad'a Yana kokarin mike wa, Inna ta ce "maza ad'au hanya"
Ya ce "ba'inda zani tunda bakisan yadda mukayi muka had'a kud'i da Abdullahi muka gina gidannan ba ganin gari kawai zanyi nadawo nabaje"
Abba ya ce "Kai Masa'ud kaci kaniyar ka uwar tamu kk fad'awa haka"
Ya Masa'ud yy dariya tare da fad'in "Abba wannan tsohuwar tafiye mita daga zuwan mutum koruwa Bata bashiba tafara balbaleshi,garama naje waje abina"
Yafita Yana dariya.

Inna ta ce "yara sai iya bakin magana tun da kuka kwaso Lantai kunshiga uku kud'inama da tamutu dashi Dan siya hargi da tazo takarb'i daddawata girma da arziki harna murtala shida na'ai'ka barb'a tayab'a min banzan magana".
Murmushi Mamie tayi tareda girgiza kai zuwa nannan lokacin Bata da muwa da duk abin da Inna zatace a kan mahaifiyar ta tun kimanin shekaru talatin da suka wuce Inna take nanata wannan maganar harkuma yau Bata fasaba tun tana damuwa harta cire abun aranta.
Abbu najin Inna tafara wannan maganar saiya zaro kud'i a aljuhun sa yamikawa Inna yace "Inna ga kud'in daddawar taki"
Karb'ar kud'in tayi tawurgashi gefen kujerar datake Kai tace "yo anrigada an kuntatawa maishi".
Bb dai Wanda yatan ka Mata.

Bayan gaishe gaishe da ya gudana Hira yabiyo baya,
Ni dai bakina yaki rufuwa sabo da murnar ganin iyayena da 'yan'uwana Ina like a jikin Aunty Rafee'at Dan munfi shiri da ita Aunty Jaleela Kam takame can gefe sai lasar waya take idan nayi magana ta harareni waini nafiye magana Niko namurgud'a mata Baki dan bama shiri da'ita,
Sai da lokacin sallah yy kafin su Abba da Abbu suka fita,
Aunty Rafee'at ta ce "Hamdah zomuje d'akinki nayi sallah a can ina dai bb datti"
dariya nayi na ce "habadai Aunty Rafee'at ai kullum saina gyara d'akina harfa turare nake sawa ko yanzuma muje kiji kamshi"
Najanyo hannun ta
Muka shige d'akin Aunty Rafee'at tace "ah lallai Kam 'yargidan Inna ta'iya gyara"
Dariya nakumayi cikeda Jin dad'in yabawar da Aunty Rafee'at tayimin,
Bayan munyi sallah muka zauna bakin gado Na ce "Aunty Rafee'at wannan zuwan Kam kwana zakuyi ko"
tace "a'a yau zamu koma" b'ata Rai nayi naturo Baki gaba na ce "yanzu tafiya zakuyi to Nima saina biku"
Tace "a'a kibari sai lokacin bikin Ya Salim saikuje da Inna"
Nabud'i Baki zanyi magana sai Aunty Jaleela tashigo tawuce tashiga bayi tayi alawala tafito tahaura kan sallaya.

A can parlour bayan dawowar su Abba daga masallaci a parlour suka tadda Inna su Ummi da Mamie Nusaiba Fauzan kuwa suna d'akin ba'i dake Nan cikin parlourn,su Abbu suka zauna sunad'an tab'a Hira,
Abba yanisa ya ce "Inna adad'a sa Ido a kan Hamdah da kyau kinga yanzu tanakan tasowa Dole akara sanya Mata Ido"
Inna tace "yo kana nufin kace tarbiyya ce ban iyaba ko me? ba Hamdah ba Kai kanka Nan ni na tarbiyan tar dakai"
Abbu ya ce "a'a Inna ba abin da yake nufiba kenan"
Ta ce "to banason iyashegin banza da hofi tarbiyyar danake baiwa yarinyar Nan ko ku baku Isa kubata irin shiba"
Hakuri suka shiga baiwa mahai fiyar tasu harsaida sukaga ta sauko.
Bayan sallar la'asar suka fito domin komawa gi da kamar yadda duk karshen wata suke tattaro iyalen su suzo suwuni wa Inna da yamma sukoma.
Harsai da naga tashinsu kafin nakoma ciki.


Yau lahadi
damisalin karfe 1 narana aka tashemu a islamiya
muka fito da ga cikin makaran tar wata lambun tumaturi da ke gefen makarantar muka nufa aguje Rabi nafad'in "yaukam ni zanfara ban ruwannan tunda ke jiya kk fara"
Na ce "ai baki isaba, Baba na lambu ni zaka fara bani tiyon"
Dai-dai Nan muka shiga cikin lanbun tasaman tumaturin mukarika bi duk muka tattake tumaturin.
Cikin hanzari dattijon dake ban ruwa wa kayan lanbun sa yajuyo kafin yy wata magana tuni muka wafce tiyon da ke hannu sa inaja Rabi naja na ce "garama kisake Dan wlh ni zan fara"
Ganin yadda muketa faffasa masa tumatur yasa Baba na lambu kwatar tiyon da sauri a hannun mu ya ce "ke Rabi'atu barta tafara yau gobe ke Zaki fara"
tsalle nayi ina murna na nad'e hijjab Ina natattareshi narayata shi tabaya na nad'e kafar wando na,
Baba na lambu yamika min tiyo narika bin layi layi inayiwa kayan lambun banruwa inayi Ina d'an salle sabo da hakan bakaramin burgeni yakeba ko agida ne idan naje wanka saina b'ata lokaci Ina wasa da ruwa kafin nayi wankan.
Sai da nazaga d'an madai-daici lanbun tas da ruwa kafin nazo namika Mata tiyon inayima dariya nariga ta.
Itama takarba kamar yadda nazaga lanbun itama Sai da tazaga shi kafin tazo tamikawa Baba na lambu tiyon sa,
Ya ce "to maza a yi gida Kuma saigobe".
Mukace to muka fita tayi hanyar gidan su Nima nayi hanyar namu gi dan,
Tunda nad'au hanyar gi dan nafara Jin kirjina yafara bugawa Dan nasan yanzu karfe 3 tayi mu da aka tashemu tun karfe 1,a bakin get natsaya naleko kaina can nahango Fatu tsaye tana shanya kan igiya da sauri nashigo ganina yasa Fatu bud'e Baki za'tayi maga nayi saurin d'aura hannu na kan baki na nayi Mata alama da tayi shiru
Na karaso in da take
Cikin kasa da murya nace "Fatu Inna tana d'akine ko waje?"
Ta ce "tana d'aki"
Da sauri nawuce ta nanufi kofar da zai sadani da cikin gi dan nanma Sai da naleka natab batar da Bata tsakar gi dan kafin nashiga cikin sand'a, nashige cikin parlour dasauri nashiga d'akina.
Numfashi nasauke Allah yasoni yau da Inna taga shigowa ta da ta taramin jama'a,
Natub'e hajjab Ina nashiga bayi alawala nayi nafito nagabatar da sallar azahar Ina idarwa ko takan abinci banbiba nahaye gado narufe idanuna, nayi hakanne sabo da idan Inna tashigo tayi zaton tuntuni nadawo,har bansan sanda bacci yad'aukeni ba.


"Hamdah Hamdah Hamdah" can cikin bacci nakejin kiranda Inna taketa faman laftamin juyi yanaji cike da Jin da d'in baccin da nake nadad'a gyara Kwan ciyata.
Inna taturo kafa tana fad'in
"Kai Allah wadaren naka yalalace Wai ace yarinya bata da aikin yi sai bacci
dubi uniform in ma ko cireshi batayiba sabo da tsabar lalaci"
Dai-dai Nan Inna ta'iso bakin gadon tad'aka Mata duka
abaya.
Firgigit nafarka namike zaune da sauri Ina mussuke idanu,
Inna tace
"Mike da Allah bakida aikin yi sai bacci taya jiki zaiyi kwari kullum kina tafiya lagwai-lagwai kamar lagwani".
Turo Baki gaba nayi "to mezan Miki idan natashin?"
Tace "ko shara kije kiyi ai dai yafi kwanciyar Nan Kuma gashi almuru ta gabato inba so kk ki kwashi bakaken aljanu ba"
"Kai Inna Dan Allah ni kibarni nayi bacci na baga Fatu ba ai ai kintane basai tayiba ke bakya kaunar kiga mutum nahutawa saikin kwakulo Masa wani aikin."
Inna ta ce "kinci gidan ku yo dan da maiyi saike kizauna bazaki tab'uka komai ba sabo da son jiki irin naku na 'ya'yan yau"
Baki nakuma turowa gaba namike tsaye,
Sam matarna Bata kaunar taga mutum nahutawa kullum tafison tarika ganin mutum tsaye saikace wani soja.
nashige bayi nagara murfin kofar bayin da karfi, Inna tafice ad'akin tana cigaba dafad'in "iya shegen banza dan da maiyi saike kizauna bazakiyi ba"
Tub'e uniform nayi nayi wanka had'eda alawala sannan nad'auro towel nafito, Ina idar da salla namike nasaka Kaya yafito
sakar gida.

Nan na'iske Inna zaune kan tab'arma tana Jan jarbi wuceta nayi naje kicking nazubo a binci nadawo nazauna gefen ta nafara cin a bincin.
Sallama akayi dukan mu muka d'ago Rabi ce takaraso inda muke ta gaida Inna can kasan makoshi Inna ta'amsa gyara zamata nayi na ce
"Rabi zauna muci"
Ta ce "a'a nakoshi dama nazone kirakani kasan layi Mama ce ta'ai keni"
Nace "to Bari nakarisa cin a bincin saimuje"
"Kije gidan uban wa? Ke Rabi tashi kib'ace min da gani
yo nizaki kawo wa iyashege kizo kirika
kwasar yarinya kina kaita layi-layi salon
kiyab'amin kashin kaza a gari a ce ban'iya tarbiyya ba haryakai kunnen ubanta to bb inda zataje tashi maza kitafi"
Inna tafad'a tana nunawa Rabi hanya,
Rabi tamike tafita
Nace "haba Inna meyasa kk yin hakane Dan Allah kawai rakiyar dazan Mata shine yawon?"
"Au nazuba Miki Ido kirika yawo a wannan duniyar da mutanen cikinta suka gurb'ace Ina a nan ubanki yasani gaba yana yimin bita a kan ki kamar shi yahai feni,nifa wannan Rabin datake wurga kafa kamar shamuwar Nan Bata kwan tamin a rai ba, yaran yanzu kasaka musu ido ma ya'aka kare bare kakawar da Kai".

Ture plt in a bincin nayi namike nashige ciki,
Cikin d'aga muyar Inna take fad'in "shashancin banza"

Washegari Monday nagama shirina saf nazuwa makaran ta nad'au jakar makaran tana tafito
A kafa nahaura makaran tar namu saboda bb nisa saka ninmu,
A kofar shiga makaran tar muka had'u da Rabi Dan makaran tar bokon muma d'ayane da ita tare muka shiga,
a natashi muka fito
Har nad'au hanyar gida Rabi tabiyoni da sauri tana Kiran sunana
natsaya takaraso inda nake ta ce "Hamdah Dan Allah kirakani gidan Adda Samira dama can jiya Mama ta'aikeni"
Nace "to muyi sauri muje kinsan Inna tasan lokacin tashin mu yanzu idan taga ban koma gi da a lokacin ba zata biyoni"
Ta ce "tom"
Muka juya dasauri muka d'au hanyar gidan yayarta a kafa mukarika tafiya ga gidan da uban nisa Sai da muka gaji tilis kafin muka Isa gi dan aikuwa mukayi rashin sa'a Bata Nan haushi kamar nayi ya wahalarmu ta banza ko zama ban Bari munyiba nace mukoma Dan gabad'aya hankalina yakoma gida,haka muka Kuma dakawa da kafarmu bakaramar gajiya nayiba saijan kafa nake sabo da tsamin dakafar yy ga cinyoyina dasuke gogar juna sai zugi sukeyimin dakyar muka karasa gida.

Atsakar gida na tadda Inna da mayafi akanta
Baki tabud'e tana Bina da kallo nikuwa nawuceta nashige cikin parlour da sauri tabiyo bayana tana fad'in
"Mezan gani haka ke Hamdah wace irin tafiya naga kkyi" salati tashiga yi tana tafa hannu tare da fad'in "nashiga uku ni A'i wani al gungumin kk had'u dashi yy miki wanna irin zaluncin
Yau yankaki zanyi kafin ubanki yazo yakarasa ki
Ni tunda naga lokacin tashi yy Baki dawoba hankalina yakasa kwanciya ashedai darabon ganin bakin ciki shikenan kinjamana abun fad'a a gari".

Ido naware Ina kallon Inna cikeda mmk
Saikuma nabi jikina da kallo nakuma mai da dubana kan Inna da taketa buga kirji da sharb'e hanci,tana fad'in yankani zanyi,sorone ya lullub'ene lokacin da nagane abin da Inna take nufi,
Inna kuwa kwad'awa Fatu Kira tashiga yi tana fad'in tazo Mata da wuka,
Kara nakwalla tareda tuma tsalle narika zaga cikin parlour Ina fani "Fatu karki kawo wlh Inna banyi iskan ciba karki yankani"

Inna tarikoni tace "fad'amin d'an gidan uwan wayene shi?"
Na ce "wlh Inna babu kowa naraka Rabi ne gidan addan ta akafa shine kafata yakemin zafi"
Numfashi Mai karfi Inna tasauke saita sakeni ai da gudu nashiga d'aki Ina waigen kofa ko Fatu nazuwa da wukar.


Inashiga d'aki nahaye kan gado
shigata baifi da minti 10 ba Inna tashigo d'aukeda plt, nasan za'ayi
haka Inna wata irin mutum ce tanada fad'a yanzu zatayimin fad'an idan taga nab'ata
Rai zata biyoni ta
lallab'ani Amma fa bashi zai Hana anjima
takuma balbalamin masifa ba Kuma Bata son wani yayi min,kullum maganar Inna d'aya ce a duk san da
tatashi yimin fad'a
sai tace narufa Mata asiri ta dankani hannu iyayena ko gidan
mijina lfy,abun da kesa Inna fad'ar haka tun akan wata 'yar makotan mu
da tayi ciki a waje shikenan Inna tasinke kullum a cikin tsaro da
barazanar ta nake.

Plt maid'aukeda a binci ta'aje tazauna gefena tace "tashi kici takwara ta kinsan zama da yunwa bb kyau.........


Mommyn Twins ce
[6/1, 3:39 PM] Rasheeda S Director: *🌺HAMDAH🌺*

*NA*

*RASHEEDA S DIRECTOR*


_(Book one)_


*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*



*Free page*



*Labari mai tsada farashi mai sauki ɗarin ki-ka 200 yabiya miki-ka bukata turo 200 ta wannan asusun bankin 3170524141*
*Rashida Salihu First bank*
*Ko katin waya na MTN 200 ta wannan Number 08034690723*
*tsiyan nagari mai da kuɗi HAMDAH labarine mai tsa da na baku shi a farashi mai rahusa*👌🏻



~wannan page ɗin na sadaukar dashi wa tsohuwa kakata Innar mu tsohuwa mai ran karfe madubin Director family~🥰🤗



🅿️2



Huf namike Dan dama yunwace sur cikina Sai da nafara cin a bincin kafin Inna tafita, Ina gamawa naje nawanko hannuna nadawo nakuma Kwan ciya.
Muryar Inna naji tana rafka
Salati sai kuma
Magana narikaji kasa-kasa da sauri namike zaune Jin muryar goggo Hauwa da a lamun fitar sautin kuka,
Cikin hanzari nadiro a gadon nafito,
Ido naware ganin goggo Hauwa shin fid'e atsakiyar parlour'n sai numfashi take fiddawa d'aya nabin d'aya nakuma Kai dubana takasa inda take kwancen dafe kirji nayi ganin jini nafita tacikin zanin ta, Inna tace
"Subhanallahi mezan gani ni A'i shekenan tayi b'ari"
A binda Inna naji take fad'ane yasani mai da duba na gareta dakyau, "B'ari" nanatata kallamar a raina,
Inna ta dubi Fatu da yanzu shigowar ta ta ce "yimaza kije ki taro Mana Mai a bin hawa mutafi asibiti"
Da sauri Fatu tafita Inna tashiga d'aki tafito da zani a hannu tazo kanta tana kokarin canza mata zanin,
Kara nakwalla lokacinda Inna tamirgina goggo Hauwa ganin yadda jini yakwanta a'inda ta kwanta nayi kan gaggo Hauwa ina fad'in "wayyo Allah goggo Hauwa karki mutu"
Fatu tashigo dasauri tace "Inna nataro Mai abin hawan"
Inna da Fatu su suka d'aga goggo Hauwa suka fita da ita nabi bayansu dasauri Inna ta ce nakoma gida suka haye a bin hawa suka tafi asibiti ina shiga gi da d'aki nawuce Dan gabad'aya ganin jinin Nan yatsora tani.


Sai yamma Inna ta dawo inajin da wowarta nafito Dan tun tafiyar su dana shige d'aki bankuma fitowa ba,
Na ce "Inna inasu goggo Hauwa'n?"
Ta ce "tana gidan ta nabarsu da Fatu zata zauna tayi Mata bakwai kafin tadawo"
Na ce "Inna harciwon b'arin tan yawarke?" Kai kawai tagyd'a min,harna juya zan fita sai nadawo dasauri na ce "Inna kikace Fatu saita kwana bakwai kafin tadawo?to waye zai rikayin wanke-wanke da shara da girkin?"
"Ke Mana bagakiba ke aikin me kk ke Zakiyi tayi kafin tadawo".
Jinayi kamar Inna tasa komin dutsai a ka, shara da wanke-wanken Nan basonsu nakeba garama girkin inason yi kodun nayita motsawa
Nace "Inna duk nikad'ai cap yaushe zan iya". Nafad'a Ina tura Baki,
Ta ce "ai dama ba Wanda a ka haifeshi da iyawa kowa Sai da yazo kafin ya'iya haka Zakiyi har ki iya uwar 'yan sonjiki"
"Ni dai wlh Inna bazan iyaba kice Fatu tadawo kawai tunda kince ciwon b'arin goggo Hauwa'n yawarke"
Dasauri najuya nashige d'aki, "yarinya sai shegen son jiki kullum kina gado kamar Mai kar yaiyen baya". Cewar Inna inajin ta nidai nayi shigewa ta d'aki.


Washegari da safe Inna tashigo d'aki inajin shigowar ta nayi saurin rufe idanuna tazo tashiga bubbugani tana fad'in "ke Hamdah Kin mance kinada makaran tane Baki tashi kinje kin d'aura a bin Kariba gashara da wanke-wanke ma kinsan dai Fatu batanan dai ko"
Da sauri namike zaune "Inna nayi latti fa" tace "yo shine kk kwance dan siya" Huf namike nasauko a gadon nashige bayi Dan gudun kada takuma kawo zancen wanke-wanke da shararnan.
Ina gama shiri nafito a kicking nasami Inna harta had'a a bin karyawa tazubo ta mikamin Ina kammala ci tami komin naira 50 nakarb'a inata murna nayi waje.

Karfe 12:00 muka fito daga aji Ina shiga gida Inna tace nayi maza natub'e nazo nayi shara nasan dai batada lfyr baya bazata iya sun kuyoba, ranar duk wata kiuyata Sai da Inna takure Dan kuwa a kaina tatsaya har Sai da nayi sharar, Ina gamawa naci a binci da sauri nayi Shirin isalamiya natafi tun lokaci zuwa isaliyar Bata yiba,
Gidansu Rabi naje nad'au Kota mukayi lanbun Baba na lambu,a can mukayita wasanmu har Saida mukaji haya niyar d'alibai kafin muka nufi makaran tar
Afilin makaranta tar muka tadda d'alibai,
Bud'e Baki nayi Dan gabad'a namance yauce ranar karb'ar hutun mu, kwata-kwata banji dad'in hutun Nan ba Dan tanan ne kad'ai nake samu nafito nayi wasana haka nakoma gida Raina ajagule.

Ina zuwa kofar gida naga wasu maza su biyo tsaye nazo zan wucesu d'ayan ya ce "am da Allah gidannan Zaki shiga?".
Da kai na'amsa Masa
Ya ce "yauwa kice ana sallama da Saleem". Juyawa nayi zan shige sai d'ayan ya ce "am yasunan ki?"
"na mance saina tanbayo" nafad'a tareda shigewa ciki Ina kunku ni "sun Sani gaba saiwani tanbayo yi sukeyi min sai kace wasu 'yan jaridu toni dasuke cewa nayi musu sallama da Ya Saleem so suke naje Bauchi'n nakira wo musu shine ko me".
Ina sakaina ciki naja natsaya da mmk nake kallon sa ko yaushe yazone oho Yana zaune kan taburma Inna na gefensa kan kujera sai juya invitation card take a hannun ta,
Baki nawashe "la Ya Saleem Ashe kazone shiyasa wad'an can gar da yen sukece na kirawo musu kai"
Da sauri na Isa Inna suke
Nad'au iv Mai d'aukeda sunan Saleem Abdallah and Na'ima, Baki nakuma washewa "la sunan matarka kenan Ya Saleem"
Wani kallo yy min dayasa ni saurin suke bakina,
Inna tace "to Mai sunan Malan madadin kazo da goro karaba wa a bokan ar ziki kazo da wad'an Nan takar dun, yanzu Taya zantu rawa makota ta kardar nan ai sai dai nasai goro na raba musu".

Adakile ya ce "ai dama wanna ba naki bane na jama'an nane"
Yasaka hannu a aljuhu yazaro kud'i yamika mata yad'aura da fad'in "gashi saiki siye goron kiraba wa jama'ar naki"
Da sauri na ce "haba Inna ga abun 'yan gayu kice wani goro ni barima naje gidan su Rabi nanuna mata"
Na a je jakata najuya da sau ri.
"Ke zonan!". A han Kali najuyo nazo d'an nesa da shi hannu yamika min a lamar na ba shi Mika Masa nayi kafin yakar b'a nasake yafad'i kasa najuya cikin tura baki na sallake kafar sa d'aya da ya mikar da shi da sauri Inna ta janye kafar ta ganin namiko kafata nayi bal da jakar makaran ta ta nashige ciki. Inna tabi bayan ta da kallo tana girgiza kai
Yun kurin mikewa yashiga yi Inna ta ce "rabu da ita Mai sunan Malan in dai Hamdah ce bakaga komai ba".
"A rabu da ita kenan tayi a bun da take so waini wanna yarin yar yaushe ne zata gyaru".
Ganin yamike tsaye yasa Inna saurin mike wa
Ta ce "yo Hamdah'n nawa take ai sai hakuri idan tagirma duk wad'an Nan

3 Comments On HAMDAH
avatar
zarrah

1 year ago

Reply

Amazing story

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to zarrah

Thanks for your feedback

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Littafi

Please Login or Register in order to submit comment