Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

faɗin"wahalalliya",ita dai zuby bata bi ta kanta ba.




Ita kuwa zuly abin ne ya fara ɓata mata rai,haba ace abu yaki ya kare,gaba ɗaya shi ɗin nawa ne da wai ta kasa juya shi.





Rayuwa nata tafiya yadda bama tsammani,yanzu haka muna exam ɗin ƙarshen zango na canza aji.





Idan ka ganni na rame sosai,ga matsalolin gidan mu ga kuma karatu,duk yadda ummi ke ɗauke kai akan karatu na wannan karan sai da ta nuna damuwar ta a fili.





Mun fara babu daɗewa tace na koma sabon gari kawai domin samin sauƙi,cikin farin ciki na tattara komai nawa.





Abdul'azeez yace"kije makaranta kawai sweet insha Allahu zan kawo miki kayan ki anjima",ummi dai bata ce komai ba.





Jiki na sanye da pink ɗin doguwar riga na ɗora hijab ɗina fari ƙarrr,takardar assignment na ɗauka wanda wani lecturer ya bamu saboda bamuyi test ɗin shi ba.




Sai yace to ga assignment nan ya bamu idan munzo muyi submitting ƙarfe takwas,jiya kusa dare na raba ina yin assignment ɗin Allah ya taimaka ma da babbar waya kuma ina da data,dan duk one week sai yaya Khaleel yayi mini transfer na dubu biyar.





Sauri nake in tafi domin dai bakwai tayi ga kuma go slow dana sani da wuya bamu samu ba a ƙofar doka,pz da kuma fly over.




Dai dai harabar gidan mu,ina tafiya cikin sauri da kuma natsuwa,ban yi aune ba naji saukar abu a jiki na.





Cikin sauri na ɗaga takardar assignment ɗin,amma ina ta riga da ta sami rabon ta,jiki na nabi da kallo.




Manja ne irin me tiri ɗin nan,zaro idanu nayi sannan na juya na kalli takardar dake hannu na,gaba ɗaya takardar ta lalace gaban ta,gashi yama taɓa hand out ɗin dake baya sauƙin ta ma akwai banding a jiki.





A matuƙar razane na ɗago na kalle ta,kamar yadda na zata Khairiyya ce riƙe da roba ta manja kallo na take cike da tsiwa tace"dan Allah malama ki dinga kallon gaban ki idan kina tafiya,yanzu kin saka nayi asarar manja na mtseww aikin banza mutum daga fara makaranta har ya fara girman kai,da dai bamu san asalin angulu ba da sai muce daga masar take",gaba tayi tana cigaba da magan-ganun ta.






Har wani ɗaci nake ji maƙogoro na yake yi tsabar ɓacin rai,ƙara kallon takardar nayi bama ta kaya na nake yi ba.








Kallon agogon hannu na nayi,ƙarfe bakwai da minti goma sha biyar,da sauri na koma cikin gida domin canza kaya.




Ummi ta kalle ni kawai bata ce komai ba,dama ban saka ran zata yi magana ba,ɗaki na shiga ina share hawaye,abinda ƴan gidan suke mini baya damuna kamar yadda ummi ke nuna halin ko in kula a kaina.






Idan tayi kamar ta dawo kan dai dai sai kuma ta kauce daga baya,hijab ɗin na cire na jefa cikin laundry basket,hakama sauran kayan.




Da sauri na shiga bayi nayo wanka shaf-shaf,wani kayan na kuma ciro wa doguwar rigar atamfa duk da tayi mini yawa saboda ramar da nayi haka dai na saka ta.





Hijab kalar orange na saka,sannan na ɗauko handkerchef na goge bayan banding ɗin da manja ya ɓata,ita kuma takardar assignment ɗin ɗauka nayi kawai na sake fitowa.





Babu abinda ummi tace mini haka na wuce ta na kuma fita,sauri-sauri nake yi domin naje na sami mota na hau.




Babu wani daɗewa na sami mota na hau,na dai isa makaranta ƙarfe takwas saura minti biyar.





Har class rep ya fara tattara assignment ɗin domin kaiwa,haka na roƙeshi ya ɗaga mini ƙafa na ɗan rubuta.





Cikin gajiyawa yace"gaskiya ba zan iya wannan kasadar ba,kin san waye dr sadik dama wani ne bashi ba kada jiran naki ya jawa asarar mutane da yawa".





Haka ina kallo ya tafi,banyi ƙasa a gwiwa ba naje na siyi fullscap paper na zauna kwafewa,ina gama wa ƙarfe takwas da minti goma sha biyar.





Cikin sauri na nufi office ɗin shi,ina ƙwanƙwasawa yace na shigo,ɗan dattijo ne wanda a ƙalla zai kai shekara hamsin da wani abu.





Tun daga kallon da yayi mini na san babu sa'a,cikin ɗaure fuska yace"dame zan taimake ki??",cikin in-ina nace"dama assignment ne na kawo".






"banda wannan lokacin na tsayawa amsar naki ki fice kawai",kamar zanyi kuka na fara roƙon shi.





Kallo ya bini dashi kafin ya lashe baki yace"kin gane zan iya amsa amma da sharaɗin anjima zamu haɗe".





Cikin rashin fahimta nace"bangane ba malam",washe baki yayi yace"ki gane mana ƴan mata,ki yarda dani kawai sai na amsa".






Zufa na fara keto mini na shiga uku me wannan yake nufi dani ne?,girgiza kai nayi sannan na saki kuka,ina faɗin"wallahi ni ba ƴar iska bace".




Ɗaure fuska yayi yace"then out!!!fita nace"ya faɗa cikin daka tsawa,ai jikina har rawa yake yi wajen ficewa.





Har harɗewa nake yi wajen tafiya,can bayan masallaci naje na zauna naci kuka na ma'ishi ya Allah daga wannan sai wannan.






Na daɗe a wajen sannan gaba na ya dena faɗuwa,wanke fuska ta nayi a lokacin saura minti goma mu shiga jarabawar.





Ina zuwa invigilator ɗin yana zuwa,ajiyar zuciya nayi sannan na shiga,gaba ɗaya nabi na tsargi kaina.





Koda aka bani paper ɗin jiki na rawa ya fara yi,ban taɓa shiga jarabawa bani da hope ba kamar wannan.






Matsalolin sun saka gaba ɗaya kaina har juyawa yake yi,rubutun ma biyu-biyu nake ganin shi.




Kifa kaina kawai nayi akan desk ɗin na kuma sakin kuka,da ƙyar na iya amsa ɗaya da rabi a cikin tambayoyi biyar.







Gashi bani da ƙawa,gashi babu wanda na sani ko ya sanni,bani da wanda zan gayawa matsala ta.





Har aka gama jarabawar ina kwance,zuciya ta kamar ta tsage ta fito saboda zullumi,kowa kuwa harkar gaban shi yake yi.




Waya ta na ciro hannu na yana rawa na lalubo number,kawai na danna kira.





Lokacin yana zaune a office ɗin shi,ayyuka sun sha gaban shi,wayar shi ta hau ringing,ya daɗe yana kallon wayar har ta kusa tsinkewa yana wasi-wasin meya same ta ne?.







A nutse ya ɗauka sannan ya kara a kunnen shi,ni kuwa jin an ɗaga da ƙyar nace"sweet ka bar kai mini kayan sabon gari bani da lafiya gani nan dawowa",ina faɗin haka na ajiye wayar.






Gaban shi ya buga,miƙewa yayi da sauri,meke faruwa gashi kanshi ya shafa,ya ilahi,tunowa da yayi cewa likita ya faɗa mishi cewa jinin ta na daf da yawa ya ƙara ɗaga hankalin shi.






Wayar shi ya ɗauka yana nazarin waye zai kira,Yaya Abdulfatah ya faɗo mishi a rai,cikin sauri ya danna kiran shi.





Bayan ya ɗaga be tsaya sauraran gaisuwar shi ba,cikin fushi yace"wannan wane kalar iskan ci ne zaku bar yarinya da ciwo an rasa me kula da ita".






Yaya Abdulfatah yayi shiru yana sauraran shi,shi kuwa ya dage sai faɗa yake yi"idan da ace Rufaida ce ko Khairiyya ai da kun kula da ita amma da yake wannan ita bata da kowa sai Allah kun zuba mata idanu to ku sani idan har wani abu ya same ta duka sai nayi shara'a daku,kuma yanzu ka tashi kaje Abu ka dauke ta ka kaita asibiti idan an duba ta ka wuce da ita sabon gari inda aka san mahimmancin ta,yanzu ka fara zuwa part ɗin ummi ka amshi kayan ta,zan maka tranfer na kuɗi yanzu"yana faɗin haka ya kashe wayar.





Yaya Abdus-samad da Al'ameen dake tsaye a bakin ƙofa baki buɗe suna mamakin wannan abu haka.





Ciki suka ƙarasa shigowa,Yaya Abdus-samad ya dafa shi yace"haba my man ka kwantar da hankalin ka mana".





"in kwantar da hankali na bayan kanaji wannan yarinyar ba lafiya ta cika ba,sannan kana maganar in kwantar da hankali ai duk abinda ya faru sai na hukunta su duka gidan".





Wannan karon duka kasa riƙe dariyar su,suka yi sai da suka dara,jan dogon tsaki yayi kafin yace"ku fita dan Allah ban son ƙarin damuwa".






Al'ameen yace"kaga Abokina angon juwairiyya Ka bar wannan abun kayi mata Addu'a kawai".





"wai waye yace muku sonta nake yi ne,kawai dai ina tausayin ta ne sannan kuma ni Alhakin kula da ita yake kaina".





Al'ameen zai yi magana,Yaya Abdus-samad ya hana shi,shu kuwa oga zama yayi ya ɗora hannun shi a haɓar shi yana tunani.





Wayar shi ya ƙara ɗauka ya kira Yaya Abdulfatah yana tambayar shi koya isa,Yaya Abdulfatah yace"Yaya gani nan a Aviation na kusa".





"wai wannan wace kalar tafiya ce,ya isa ace ka kai amma ka zauna kana nuƙu nuƙu wallahi wani abu ya same ta sai na ɓata maka rai",shi dai ƙoƙarin bashi haƙuri kawai yake yi.





Ajiyar zuciya ya sauke,ji yake yi kamar yayi tsuntsuwa ya ganshi ya zaria,gani yake yi kamar basa mishi aikin daya kamata,minti nawa yake ɗauka a kai samarun.





Kallon wayar shi yayi kan ya kuma jan tsaki,zama yaya ya ɗora hannayen shi saman sumar kan shi.






Su dai su Al'ameen kallon shi kawai suke yi ba tare da sunce komai ba.





Ni kuwa baiwar Allah har na tattara kaya na,cikin dauriya na fara tafiya hannu na saman goshi na.





Allah yama taimake ni daman jarabawar guda ɗaya nake da ita,me mashin na tare domin ya fitar dani bakin get.






Ina fita bakin get yayi dai-dai da isowar yaya Abdulfatah,shi ya taro ni na sauka,ya biya me mashin ɗin kuɗin shi sannan yazo ya buɗe mini ƙofa na shiga ciki.





Ya fara tuƙi kenan wayar shi tayi ƙara,girgiza kai yayi sanna ya ɗaga yace"yaya gata na ɗauko ta,yanzu asibiti zamu wuce",banji me aka ce daga ɗayan ɓangaren ba.






Kai ban ma san da waye yake wayar ba,ji nayi yace"eh to zamu tsaya koda a Salama",shiru ya kuma yi kafin yace"to yaya insha Allah".




Daga haka ya kashe wayar,be daɗe da ajiyewa ba wayar tayi ƙara alamar shigowar saƙo,be duba ba kawai ya cigaba da tuƙin shi.








Dai dai ƴan goro ya ɗauke hanya,muka shiga salama hospital,asibiti ne babba wanda yake private,har lokacin ban wani dawo hayyaci na sosai ba.





Muna shiga muka sami likita available,mutum me fara'a,tambayoyi yayi mini ina bashi amsa.




Bece komai ba ya rubuta magun-guna,ya miƙawa receptionist domin a kawo,zama muka yi muna jiran dawowar shi.





Wayar yaya Abdulfatah ta kuma ɗaukar ƙara,"aifa yau ni kuma na shiga uku da yaya Khaleel"haka ya faɗa kafin ya ɗaga wayar.







Ni kuwa jin sunan daya ambata yasa gaba na ya kuma faɗuwa,taya akayi ya san bani da lafiya,wani abu naji yana mintsilina a rai.





Idanu na kamar zai kawo ruwa,kallo na na mayar kan yaya Abdulfatah kamar nace ya bani wayar,ban san meya sa ba sai nake jin ina ma ya dawo na gan shi.





Tunani na ya katse ne lokacin da yaya Abdulfatah ya miƙo mini wayar,a kasalance na amsa murya na rawa nayi sallama.





Muryar shi ta ratso dodon kunne na yana amsa wa sannan ya ɗora da faɗin"ya jikin",kai na ƙasa har wani ajiyar zuciya na sauke kafin na bashi amsa nace"jiki yayi sauƙi","Allah ya ƙara sauƙi"Abinda yace kenan,duka muka yi shiru.






Can kuma yace"bawa Abdul wayar",miƙa mishi nayi shi kuma suka yi sallama,a lokacin har an kawo maganin,sai da ya tsaya yayi musu tranfer na kuɗin su sannan muka tafi.








Muna zuwa MTD ya ɗauke hanya,kallo na na maida kan shi kan nace"yaya gida nake son zuwa",mumushi yayi yace"rufa mini asiri na kai ki inda aka umarce ni,kada wani abu ya same ki ayi shara'a dani".





Ban wani fahimci maganar ba,hakan yasa kawai na share maganar,muna zuwa ƙofar gidan yayi parking.




Da sallama na shiga,ina gaba yana bina a baya,hajjaju dake zaune tana iza wuta tace"lale maraba da ƴan makaranta".





Gani na tare da Abdulfatah tace"ah kice tare kike da ɗan uwanki,ni dai ɗakin ta kawai na shige na kwanta.





Nan suka gaisa da yaya Abdulfatah sannan ya bata magun-guna da kuma jaka ta,ya kuma yi mata bayanin banda lafiya kawai ya fice.





hajjaju ta shigo ganina a kwance yasa tace"assha,wannan ciwo be kyauta ba,Allah ya baki lafiya".






Ni dai bance komai ba,sai yanzu da nake kwance nake tunanin jarabawa ta,banfa yi wani abu na azo a gani ba,gaskiya dole ma nayi ƙawa dama yaya Khaleel ya hana ni kuma yanzu ya kama ta nayi ɗin taya zai gane haka Rufaida ta faɗa mini kuma hakan ne gaskiya,sai idan ni naso ya gane.






Khairiyya tana shiga lart ɗin su ta fashe da dariya,jikin momma ta maƙale tana dariya tace"momma kinga yadda na maida ta,gaba ɗaya na ɓata ta".





Momma ta rungume Khairiyya tace"yauwa ƴar Albarka,haka nake so muyi ta ƙuntata mata har ta haƙura da karatun,tunda kema baki cigaba ba wallahi itama ba zata cigaba ba".






Ihu khairiyya tayi tana faɗin"yauwa momma na,shi yasa nake sonki",momma tace"yanzu kuma sai da yamma idan ta dawo sai mu canza me za'a yi mata".





"ai tana dawowa zan fincike littafan ne ko kuma na sheƙa mata ruwan zafi kawai",momma tace"yauwa ƴar Albarka ruwan zafin kawai zaki sheƙa mata".





To juwairiyya na sabon gari ma sai kuyi mu gani munasirai kawai😏






Zuby tace"dan Allah ki taya ni neman number ɗin nan,kin san yanzu daddy zai fito ko,kuma bana so ya zo ya tarar babu wayar shi".






Zuly ta amshi wayar dake hannun zuby contact ta shiga ta fara bincike,can tace"kaf nan ni dai banga wata number me suna khaleel ba".






Shiru zuby tayi kan tace"yauwa ranar nan daddy naji ya kira shi da cewa,K.A",da sauri zuly ta fara dubawa cikin sa'a kuwa number ɗin tayi appearing.





Cikin sauri zuby ta kwafe number ɗin,cikin murna ta rungume zuly,zuly ta ɓata fuska tace"kada ki karya mini Alwala".







"mtseww,ƴar iska kawai",tana faɗin haka tayi ficewar ta,koda ta shiga be fito daga wankan ba hakan yasa har ta ajiye be fito ba.





Tana dawowa ta sami zuly a zaune,amsar wayar tayi,sannan tayi saving da *miji na* 😌.








Duba shi tayi a whatsapp kusan sati be hau ba,sallama ta tura mishi dashi sannan itama ta sauka.



Ni kuwa ina kwance ina zubar da hawaye,hajjaju kuwa ayyukan ta take yi sai dai idan ta shigo tayi mini sannu ta fice kawai.





Na riga da na san faɗuwa zanyi,me zance wa yaya Khaleel,hawaye na goge ina faɗin"tawa ta ƙare ya Alƙah ka taimake ni.





Ban san hajjaju ta shigo ba sai ji nayi tace"au har yanzu baki bar yiwa zazzaɓi kuka ba?",cikin kuka nace"hajjaju faɗuwa zanyi a jarabawa,ban rubuta wani abu me yawa ba,hajjaju me zan cewa yaya khaleel?".





Zama hajjaju tayi ta kamo ni tace"juwairiyya ki kwantar da hankalin ki,in dai dan jarabawa ne ai addu'a ita ya kamata kiyi sannan ki cire abinda yake faruwa a gidan ku daga ranki ki fuskanci karatun ki kawai".





Sosai naji daɗi abinda ummi bata mini kenan kona mutu ko nayi rai,cikin ƙunar rai nace"hajjaju dole na damu yanzu ummi fa bata damu dani ba".





Girgiza kai tayi tace"ita kuws ta damu dake kawai dai tana kauda kai ne a gare ki,kinga kullum sai ta kira ni tana faɗa mini abinda yake faruwa a gidan ku,ɗazu ma har kuka sai da tayi wai khairiyya ta zuba miki manja har a jikin takardar da kika kusan kwana kina aikin".






"ni na lallashe ta na kuma kwantar mata da hankali,",shiru nayi wato ashe ta san cewa jiya banyi barci da wuri ba kenan?.





Ashe ta san duk abinda ake yi mini kenan a gidan?,har zance wani abu waya ta ta hau ƙara.




Janyo ta jayi daga ƙasan filo sannan na ɗaga",ya jikin naki",cirewa nayi da sauri na duba number ɗin yaya khaleel ne.






"da sauƙi",na bashi amsa Murya ta tana rawa,"ki kwantar da hankalin ki,kinji Allah zai baki sauki".




Kan nace wani abu hajjaju ta amshi wayar,sai da suka gaisa ya ɗan tsokane ta sannan tace"gata nan duk ta ɗaga hankalin ta wai tana tsoron faɗuwa a makaranta".






Ban san me yace ba naga dai ta miƙo mini wayar sannan ta fita,karawa nayi a kunne na.





Shi kuwa shiru yayi jin saukar numfashi na a kunnen shi ya gane na amshi wayar,"juwairiyyyyyyyyya",ya ƙarasa kiran sunan da jan shi kuma can ƙasan maƙogoro.






"kallon wayar na kuma yi sannan nace"na'am","kada ki damu ki kwantat da hankalin ki,Addu'a ya kama ta ki cigaba da yi kinji komai zai zo miki da sauƙi sannan ki ƙara haƙuri da abinda momma da kuma khairiyya suke miki wata rana sai labari".






"umm",kawai nace,murmushi yayi kafin yace"ga saurayin ki",cikin sauri nace"waye?",cikin ƙasa da murya yace"Al'ameen".





Murmushi nayi,shima haka kan yace"yauwa smile always,bari na bashi",bance komai ba sai murmushi kawai da nake yi.




"hello ƴan mata na"ya faɗa yana kallon Yaya Khaleel shi kuwa ta ƙasan ido yake kallon shi,Yaya Abdus-samad ya fashe da dariya.





Kasancewar wayar a hands-free ya saka ta da zai bawa yaya Al'ameen ɗin ya saka ina jiyo abinda suke yi.




"ya gida,an koma lafiya",murmushi yayi kafin yace"na dawo wallahi gashi yayan mu sai wahalar miki dani yake yi".




Dammƴar dariya kawai nayi,haƙiƙa ya iya gusar da damuwa,be damu ba ya kuma cewa"naji ance baki da lafiya nima naji zazzaɓi ya fara kama ni,ki roƙar mini yayan ki ya ƙyale ni nazo na gan ki".






"ai ba zai hana ka ba",na bashi amsa,cikin sauri yace"waya faɗa miki ai yayan kin nan a zaria yake da sauƙi amma a borno Allah rombo yake komawa".




Dariya abin ya bani aikuwa na dara,sosai wannan karon yaya khaleel ke kallon Al'ameen ɗin jin yadda nake dariya abin ya fara damun shi,dan danan yaji ranshi ya ɓace.






"kice mishi ba zaki iya barci ba idan baki ganni ba",dariya na kuma yi,zai kuma magana yaya Abdus-samad ya amshe wayar.




Al'ameen ya kalle shi,da ido ya nuna mishi yaya khaleel juyawa yayi ya kalle shi,yadda yaga idanun shi ya koma yasa yayi dariya.






Miƙews yayi ya sara mishi yace"easy sir",biron dake hannun shi ya jefa mishi yana faɗin"wata rana idan ka cigaba sai na harbe ka da bindiga".





"haba ya zaka yi da juwairiyya,kashe mata ni zaka yi",yaya khaleel yace"sunan nan ba zai fita a bakin ka ba kenan?".





Murmushi nayi sannan na kashe wayar,lallai ma yaya Al'ameen kenan,hajjaju tace"ja'ira dama ciwon nashi ne kenan".






Kallon ta nayi nace"waye kenan?",tace"shi Ibraheem ɗin mana",murmushi nayi cikin ƙunƙunai nace"wai ciwon shi ne".





Me kika ce"hajjaju ta tambaya,girgiza kai nayj kafin na kwanta kawai ina tunane tunane.






*hajjaju ina godiya sosai da sosai,kema bloody dake da lipton girl,fareeda ƙafar yawo kema ina godiya sosai*.





#LIƘE
#SHARE
#COMMENT





*babyn Abdul,maman meenal,elham da farouk*.







*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.


♥ ❤

♥♥❤
*~K'AREENATEEY~*
(K'AWATA)

(It's all about friendship)

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*





*written *✍
-by-
*Deeja one love*




*JAKADIYAR GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION👸*



Wattpad 13deeja.


Daga wannan page d'in har zuwa k'arshe sadaukarwa ne gare ki *AISHATU BABAYO* saboda kaunar da kike wa *GOLDEN PEN WRITERS* ba muda abinda zamu biya ki dashi, dan haka *K'AREENATEEY* har zuwa k'arshe ya zama naki sis kiyi yadda kike so dashi, *JAKADIYA* ta baki wannan yan shafukan har zuwa karshe, muna godiya sosai da irin kaunar da kike mana.




_tabbas Allah zai iya sanya Ƙauna tsakanin ku da wa'inda kuke gaba dasu,Allah shike ƙaddara komai,Allah shine mai gafara kuma me rahama_.


*suratul mumtahana aya ta 7*.





_wa'innan da suke riƙar kafirai masoya saɓanin mumunai,shin suna neman ɗaukaka ne daga wajen su?,haƙika ɗaukaka ta Allah ce gaba ɗaya_*.





*Suratul Nisa'i,aya ta 139*.



Manzon Allah tsira da amincin Allah sun tabbata a gare shi yace"kada ka ƙi maƙiyin ka da yawa domin wata rana zai iya zamowa masoyin ka,haka kada ka so masoyin ki da yawa domin wata rana zai iya zama masoyin ka.


*_AL-ƘABEEƊU_*


*_18_*







Koda Hajjaju ta gama abincin sannan ta ɗora mini ruwan wanka nayi wanka,ina fitowa na shafa mai sannan na saka kaya na.






Abinci ta zubo mini na fara ci,waya ta na janyo na buɗe data domin ganin meke faruwa.






Yaya Khaleel bayan ya koma gida yana zaune ya ɗauko wayar shi ya buɗe data,ajiye ta yayi domin messeges su gama shigowa.





Ni kuwa ina cin abinci ina chatting,Hajjaju tana mini magana tunda ta lura ga inda na tafi yasa kawai ta ƙyale ni.





Sai da messages suka gama shigowa sannan ya ɗauki wayar,dubawa ya fara yi yana yawanci abokan shi ne na zaria sai kuma ƴan uwa.





Wata number da ya gani an mishi sallama,shiga yayi ya duba waye babu suna sai dai kawai ƴan aljanun whatsapp.






Fita yayi ya duba kuma last seen,be wuce minti uku da saukar me lamba ɗin ba,sai da ya daɗe yana tunani sannan ya maida sallamar.






Ya fita message na kuma shigowa daga number ɗin,dubawa yayi"ya gida?",be bada amsa ba ya cigaba da duba na sauran mutane.






Cikin group ɗin mu na iyali ya shiga,ganin muna fira dani da kuma Rufaida sai yaya khaleed Abdulfatah sai kuma Abdus-samad.





Kusan duka firar a kan shi ake yin ta na wannan maganar wai zai yi shari'a dasu,babu abinda nake sai dariya.





Khairiyya kuwa tsaki yaja wanda sai lokacin ma muka fahimci tana online,babu wanda ya kula ta.





Yaya Khaleel yayi murmushi number na yabi ta private.



Aslm

Ganin lambar shi ya bani mamaki,zaro idanu nayi nace "yau kuma wannan mutumin ya hau kenan",mai da mishi da amsa nayi.


Wslm,an yini lafiya?".




Lafiya lau,dake ake gulma na ko?".



Zaro idanu nayi sannan na bashi amsa da"wallahi labarin abinda ya faru suke mini".




Hmmm,saurayin ki yace ki turo mishi da hoton ki",dariya nayi wanda ya saka Hajjaju kallo na tayi ta girgiza kai.




Kundin waya ta na buɗe sannan na fara binciko hoton da zan tura,wani na zaɓo wanda na saka riga doguwa purple na ɗaura veil fari.




A ƙofar part ɗin mu Abdul-azeez ya ɗauke ni,nayi kyau sosai don ina tsaye ne hannu na da biro,na saka a ƙasan a baki na.





Tura mishi nayi nace"gashi ka bashi",zaune ya miƙe sosai gani yake kamar hoton yaƙi saurin buɗe wa.




Yana buɗe sai da yayi tasbihi,ya ilahi! Wannan hoto yayi kyau sosai,hoton yake kallo sosai a gaskiya yana kewar yarinyar jo yake kamar ya ture ayyukan shi ya je ya gan ta.






Ajiyar zuciya yayi sannan ya ƙara ce mini"wannan zaki bashi ba kiyi kyau ba,ki nemo wani wanda kika yi kyau sosai".






"Na shifmga uku na da Yaya Khaleel!,wai meya saka hakan ne?",haka na sake dubo wani wanda na saka lace kalar lemon green da kuma ɗigon silver sai fari.





Mayafi fari Rufaida ta yafa mini domin kuwa dai cikin gidan mu,wajen part ɗin Baba malam.





Hannu na ɗaya na ɗaura saman kai gira ta,ina dariya wanda hakan ya faru ne saboda wani labari data bani.





Idanu na sanye da ƙaton tabarau,wanda ya rufe kusan rabin fuska ta,tura mishi nayi.





Miƙewa tsaye yayi don wannan yama fi wancan kyau sosai,ni kuwa ni can ina jin wani abu a raina,wai yaya Khaleel ban yi kyau ba".




Na ƙosa naji me zai ce akan hoton da sauƙi ma tunda yakan duba hoton ai,ba wai yaya Al'ameen yake turawa ba ko kuma bashi wayar.






Zuby dake zaune taja tsaki wannan guy ɗin wahalar da ita yake yi kawai,saƙo na goma kenan data tura mishi amma yaƙi ya bata amsa gashi tana kallon shi online.





Emoji na kuka ta tura mishi,ɗan ƙaramin tsaki yaja sannan ya maida mata da tambaya,me kike so ne?".




"mu zama abokai",



Amma ai babu kyau hakan a musulunci".





Ni dai ka taimaka wallahi kana birge ni ne kawai".



Koda ya gani be kuma yi mata magana ba.



Ni kuwa ina zaune ina jiran naji me zai ce tunda naga alamar ya gani amma kuma be bani amsa ba.




Wannan ɗin zak bawa saurayin ki,ki canza wani",abinda yace mini kenan.




Ƙara komaqa nayi domin dubo wani hoton,shi kuma ya zauna zaman jira na,fatan shi na turo wanda yafi na biyun kyau.




Wani dana ɗauka a falon mu na tura mishi wanda nake sanye da baƙar abaya nayi rolling da veil kalar ash,idanu na sanye da space ƙarami.




Na sauke idanu na sama fuska ta da alamun mamaki wanda hakan ya nuna wani abu nake kallo,shima wannan Rufaida ta ɗauke ni.




Rigar taji stones tun daga sama zuwa ƙasa,lokacin da Ammie tazo ta kawo mini ita a matsayin tsaraba.





Kasancewar ina jingine da bango yasa rigar ta koma ta kwanta a jiki na.







Yana ganin hoton ya tsura mishi idanu,zuciyar shi na bugawa da ƙarfi,da sauri yayi off sannan ya zauna ya saka hannun shi cikin sumar kan shi.






Lumshe idanu kawai yayi wannan wane irin abu ne yake ji a kanta shi kam ya kasa banbacewa.




Ni kuwa ina zaune ina tunanin kada ka kuma kushewa ganin ya sauka gaba ɗaya sai naji babu daɗi.




Koda kushewa yayi ina jin daɗi alamar ya gani kenan,wataƙila wannan ko buɗewa be yi ba😌.





Ganin hakan ba zai fisshe ni ba yasa na ɗauki waya na kira shi.




Ɗago kan shi yayi jin ƙarar wayar shi wanda yayi dai-dai da shigowar Yaya Abdus-samad da kuma Yaya Al'ameen.





Ɗagawa yayi kuma yayi shiru,ni kuwa cikin inda-inda nace"dama na kira ne ince maka na turo".




Idanun shi a lumshe yace"na gani ai",gaba na yana faɗuwa nace"amma nayi kyau kuwa?",na ƙarasa murya a sanyaye.





"A'a baki yi ba,kuma ba zan iya bashi hoton da baki yi kyau ba".





Ajiyar zuciya na sauke,jin muryar shi nayi yace"ya jikin",a

1 Comments On KAREENATEEY
avatar
hauwa-8-2

1 year ago

Reply

Mashaa Allah

Please Login or Register in order to submit comment