Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

har lokacin idanun shi na kansu yana kallon ikon Allah, ajiyar zuciya yayi sannan yaja hannun ta suka shiga motar.





Tabbas itace dokin hasken bulb na cikin motar a kunne yake,gashi tak'i sakin shi,to ita meya fito da ita a wannan daren "pub" wata zuciyar ta bashi amsa.




Kallon Abdus-samad ya kuma yi a karo na biyu sannan yace"my guy ka ja motar mu tafi",yana fad'in haka ya juyar da kai domin ya lura tambayar shi yake son yi shi kuma wasu tambayoyin baya da amsar su a halin yanzu.





Kan su isa gida har tayi barci,sallama Abdus-samad yayi mishi sannan ya tafi nashi gidan dan ma block d'in su d'aya.





Hannu ya saka ya d'auke ta duk da k'yamar ta da yake ji,kan gadon shi ya kwantar da ita sannan ya wuce toilet domin yin wanka.






Alwala yayi sannan yazo ya tada sallah,dan hakan yana cikin abinda ya saba yi wato nafila ta dare.






Sa da ya gama sannan ya nemi couch ya kwanta, kallon gadon yayi sannan yaja tsaki k'asa-k'asa ya juyar da kan shi daga nan barci ya d'auke shi.







Sai da gari yayi haske dan har ya dawo morning exercise sannan ta farka, dafe kan ta tayi tana bin wajen da kallo.





Koda ya shigo kallo d'aya yayi mata ya kauda kai, ita kuwa ganin shi ta hau murmushi wato shine jiya ya d'auko ta kenan.







Bin shi take da kallo, shiryawa yake yi cikin khaki komai nashi a nutse yake yi,yana gamawa ya d'ago ya kamata tana kallon shi.






K'asa-k'asa ya ja tsaki sannan yace"ki tashi kiyi sallah", babu musu ta mik'e ta shiga bayin bata dad'e ba ta fito.




Kallon kan ta tayi sannan ta kalle shi,shi bama ita yake kallo ba domin ba zai jure kallon ta a haka ba.





A sanyaye tace"kalli kayan jiki na",oh ashe kin san ba zai miki sallah ba kenan?, amma kika saka kika je party dasu kuma till down, kina 'yar musulmi amma kina wannan banzar shigar".





Mik'ewa yayi ya bud'e jakar shi ya d'auko mata riga jallabiya coffee colour me gajeren hannu.




Duk da rigar tayi mata tsayi da yawa haka ta saka,to babu hijab kuma kamar zai share ta sai kuma ya kira wani abokin su wanda shi yana da mata.






Da kan shi ya fita ya amso mata hijab d'in lokacin da shi abokin ya kawo hijab d'in mika mata yayi ta amsa.




Ta tada kabbarar sallar Abdus-samad yayi sallama ya shigo, gaisawa suka yi sannan ya d'auki phone d'in shi.




Juyawa yayi yana kallon ta har ta idar da sallar ba tare da yace komai ba ya nufi hanyar fita.




Kallon kallo suka yi da Abdus-samad sannan ya tab'e baki ya juya shima ya fita, bata da zab'in daya wuce bin su ita ma.






Yana cikin mota shida Abdus-samad ganin fitowar ta yasa ya kalli d'aya dqga cikin sojojin dake gadi.




Umarni ya bashi akan ya rufe gidan, daga haka be kuma kallon ta ba yaja notar shi ya fice daga gidan.





Motar tabi da kallo kamar idanun ta zasu fad'o,ahiyar zuciya ta sauke sannan ta fara tafiya a hankali.




Koda tazo bakin get sojojin suka bud'e mata k'ofar ta fice,sak'e-sak'e take a zuciyar ta,bata san dalili ba kawai hawaye ya zubo mata daga idanu.




Gogewa tayi tana cigaba da tafiyar ta,gidan mahaifinta kawai ta wuce,kamar yadda tayi expecting yana zaune yana shan tea.





Yana ganin ta ya bita da kallo,saukar da kan ta k'asa tayi, murmushi yayi gudun kada ta zargi wani abun yace"baby kin ganki kuwa cikin dogon hijab".





Murmushi kawai tayi tana saukar da b'oyayyiyar ajiyar zuciya domin ita a tunanin ta ya fad'awa mahaifin ta.




"Ya kika baro auntyn taki? ",cikin waskewa tace"tana lafiya lau tama ce na gaishe da kai".




"Amma baby tafiya da sassafe kamar babu lafiya duk da na san halin ki amma gaskiya ki dena",ya k'arasa yana d'aga mata hannu.





K'arasowa tayi ta mishi side hug sannan tace"zan kiyaye my dad",murmushi yayi mata ita ma ta maida mishi sannan na hau sama.





Tana zuwa d'aki tayi saurin cire hijab d'in domin duk ya dame ta,bayi ta shiga ta sakarwa kan ta shower.





Ashe yana da good heart?, Babu dai abinda yayi mini ko? ",na shiga uku! ",ta fad'a tana dafe k'irjin ta.





Haka ta gama wankan tana tunane-tunane,wata dai rigar iya gwiwa orange colour ta saka, kan nan ko d'an mayafi babu haka ta fito.







Masu aiki ta samu tayi musu umarnin su kawo mata abinci,cikin k'ank'anin lokaci suka cika gaban ta da kayan ciye-ciye.





Wayar ta ta d'auko tana dailing number,sai da ta kusa katsewa sannan aka d'auka,cikin masifa tace"wai kuwa zuly kina da hankali kuwa kinga baki ganni ba ai kya kirani dai ko".




Jin shiru babu amsa yasa ta kasa kunne sosai, k'asa-k'asa take jiyo nishinsu, tsaki taja tana fad'in " shegiya kawai", ta kashe wayar ta.





Abincin ta kai baki domin ci ta tuno shi, yadda ya d'aure fuska da yadda yake shirin shi da komai a natse ya burge ta.




Maida abincin tayi ta jingina da kujerar da take zaune ta lumshe idanu tana faman murmushi.




B'angaren oga kuwa sai da ya bar gidan sannan yaja wani dogon tsaki,shi yarinyar taja ma ya k'ara tsanar tane.





yana son mace mai tsiwa amma kuma ba mai shaye-shaye ba a farko da suka had'u ta burge shi yadda take gadara amma ganin da yayi mata jiya da daddare yasa yaji ya tsane ta.




"Wai wacece ita ne? ",Yaya Abdus-samad ya katse mishi tunani ta hanyar tambayar shi, sai da ya kuma jan tsaki sannan yace"yarinyar major A.i indimi ce".




Zaro idanu Abdus-samad yayi yace"kai wannan dattijon mutumin arzik'i shine yake da wannan yarinyar tambad'add'iya? ".




Be bashi amsa ba dan ji yayi ranshi ya kuma b'acewa ya rasa meya saka mata ke shaye-shaye.





____________________________________________________________________________________________________________________________________






Ni kuwa yau shirin zuwa sabon gari nayi domin zamu shiga kasuwar sabo da rufaida daga can sai na wuce.






Atamfa na saka me kalar ruean hoda da lemon green a jiki,hijab d'ina ruwan hoda har k'asa.





Nik'ab na d'aura shima a fuskata, sannan na fito, rufaida ta kalle ni tayi tsaki tace"yanzu duk wannan gayun da kika d'auka amma zaki rufe shi.





Murmushi nayi kawai bance mata komai ba,duk da a yanzu ta canza amma wasu abubuwan suna nan.





Dai dai bakin get khairiyya tsaye tare da yaya khaleed, da alamu magana yake yi mata ko kuma nace fad'a dan naga ran ta a b'ace.




Rufaida ta kalle ni tace"au koma ki d'auko wayar ki",d'ago mata k'aramar nayi wacce itace sim d'ina da aka fi kira na kuma nafi yawo da wayar saboda waccen ma ko fita da ita ban tab'a yi ba.




Harara ta tayi tace"ai wallahi sai kin d'auko gayu zamu yi da ita",dariya nayi ina fad'in"rufauda akwai ki da takura wallahi".




"Eh koma meye wallahi sai kin d'auko", ta fad'a tana jan hannu na domin mu koma, ya na iya da rufaida haka muka koma na d'auko ummi dai sai dariya take yi mana.







Mun fito khairiyya ta taho ta bagaje ni, hakan yasa wayar ta fad'i, duka wayar muka bi da kallo.





Cikin mamaki khairiyya ta tsuguna ta d'auko wayar, kallo na tayi da alamar tambaya sannan ta maida kallon ta ga wayar, jujjuya ta takeyi cike da mamaki.




"Wato yaya khaleel wata wayar ya siyawa wannan yarinyar kenan"ta fad'a tana shafa jikin wayar.




"Kuma sabuwa", ta fad'i hakan a fili,Rufaida tayi wani munafikin murmushi, dama da gayya tasa aka d'auko wayar dan khairiyya ta gani.





Ganin ta gani d'in yasa taji wani sanyi a ranta,ganin khairiyyar na k'ok'arin juyawa da wayar yasa tayi saurin k'arasa gaban ta tasa hannu ta fuzge wayar tace"haba khairiyya kunyi karo ai ke bata hak'uri yanzu kuma da kin fasa mata waya fa,waya ce me tsada fa dubu hamsin da takwas", ta fad'a tana yin murmushi.






Har idanun khairiyya ya kawo ruwa domin Allah ya yita da hangen na sama da ita, tun suna k'anana haka take weak point d'in ta kenan.





Shafa wayar Rufaida tayi tace"Sister muje ko, da alamu khairiyya yau bata magana,zamuje kasuwar sabo ne ko zakije mu jira ki".






Wani abu me d'aci ta had'iye da k'yar ta iya bud'e baki tace"kuje kawai ina da abin yi",ta k'arasa murya na rawa.




Rufaida ta rik'o hannu na da na zama mutum-mutumi tana fad'in "muje sister kin san muna da abin siyowa da yawa Allah yasa ma kud'in da yaya khaleel d'in ya turo miki da yawa koda yake idan be isa ba sai ki kira shi ya sake turo wasu, dan ni dubu d'ari da hamsin ai na raina su", ta k'arasa maganar tana d'ago atm card wanda ban ma san a inda ta same shi ba.





Wacce akayi dan itan kuwa sai da ta waigo ta kalli Atm d'in sannan ta k'ara gaba da sauri,kallo na na mayar kan rufaida.



Ita kuwa ganin khairiyya ta wuce yasa taja tsaki sannan ta kalle ni tace"sai muje ai ko", bin ta kawai nayi a baya ina hasasho drama d'in da za'ayi anjima.






Sai da muka kusa fita titi sannan na kalle ta nace"Rufaida kin san me kika yi kuwa",ba tare da damuwa ba tace"na sani mana, wani abu ne? ".





"Kina sani fa khairiyya momma zata je ta fad'awa,kuma kin san me zai faru idan hakan ya kasance".




Tsaki taja tace"aike matsalar ki tsoro wallahi,ai ni na fiso taji saboda ta san k'unci da damuwa ta haka ya kamata ki rink'a muzguna mata amma ke kullum aka yi miki sai dai kuka".




"Yanzu dan Allah ina kika sami Atm",dariya tayi tace"wallahi na umma ne,d'azu ta bani na rik'e mata sai na manta na saka a aljihu shine fa yanzu da wannan ta taso kawai na tuna"dariya muka yi gaba d'aya.





Muna shiga mota na d'aga nik'ab d'in domin yanayin zafi da sauransu,muna sauka a kasuwar.






Rufaida taja hannu na muka shiga wata plaza, nan muka baje ta dinga kwasar kaya,ni dai idanu na zuba mata.







Sai da ta kwashi son ranta sannan ta fito, kasuwar mata muka wuce, takalma nan ma ta kwasa ya kai k'afa biyar.




Haka muka shiga dogon layi,kayan kwalliya da sauran tarkace haka ta dinga jida,sai da ta gama sannan na rakata ta hau mota.




Ni kuma na juya na nemi okada da zata sada ni da chikaji,inda ainihin familyn mama na wato gidan su kenan.






Da yake babu nisa da bakin titi yasa ina sauka tafiya kad'an nayi na isa gidan,ina shiga gidan na fara jiyo hayaniya.





Ina shiga muka had'a ido,da sauri na k'arasa na rungume ta ina fad'in"oyoyo ammie na ashe kin zo,Allah ya kawo ni a sa'a".




Yar dattijuwa fara kuma mara jiki sai dai tana da tsayi ce ta fito daga kitchen tana washe baki tana fad'in "ga juwairiyya ta ta iso".




Rungume ta itama nayi ina fad'in"hajjaju gani na iso wallahi kwana biyu nayi kewar ku",d'an saki na tayi tana fad'in "kece baki son zuwa ai ina nan ina cikin zaria".





Ammie tace"au ashe kina nan da wannan halin naki, koda yake laifin fatima ne",ni dai ban tanka musu ba.




Kallon tsakar gidan nayi,babu siminti amma kuma a share yake tsaf,Alllah sarki hajjaju akwai tsafta.





D'aya daga cikin d'akunan dake jere,na shiga 'yan mata guda biyu na tarar sai kuma saurayi d'aya da yara k'anana guda uku biyu maza d'aya mace.






D'aya daga cikin 'yan matan tana kwance tana danna waya, d'ayar kuma na zaune kusa da wannan saurayin suna fira.





Sai yaran da su kuma suke cin abinci, suna gani na duka suka hau murna,hijab d'in na cire ina dariya.




Wacce ke kwancen tace"waye ya fad'a miki mun zo? ",nayi murmushi nace"wallahi babu kowa kawai yau naji ina son zuwa ashe 'yan uwa na ne suka zo".




Kallon namijin nayi nace"ashe kaima kazo",jinjina mini kai yayi yace"eh nima nazo".






Ammie dake waje tana alwala itace tayi sallama ta shigo kallon su tayi tace"wai ku ba zaku tashi kuyi sallah bane".




Mik'ewa wacce ke tare da saurayin tayi, shima haka,"zuhra magana fa nake yi miki",dariya tayi.




Ammie ta d'auki mayafin ta tana fad'in "ki zauna kada ki tashi kiyi sallar",d'ayar tace"kai ammie kika sani ko bata yi ne".





Bani na fad'i maganar ba amma kuma ni naji kunya,sai na lura su bama ta ni suke yi ba,wannan dai itace ta kuma cewa"juwairiyya ko kema bakya yi ne".





K'asa nayi da kai ina fad'in"kai aunty shukra", dariya suka yi gaba d'aya harda wannan saurayin.




Nima fita nayi nayo alwala nazo nayi sallar sannan aka kuma gaisawa.





sunan wacce ta haifi mahaifiyar mu, fatima amma muna ce mata hajjaju,mijin ta kuma Mus muna ce mishi Alhaji.





Yaran su kacal guda uku ne duka mata,babban su itace Aisha(Ammie)kenan,tana aure a jahar jigawa,mijin ta babban lauya ne me zaman kanshi tana da yara guda hud'u,Shukra itace babba sai mai bi mata fatima suna kiranta da shukra tsakanin su babu nisa shi yasa suka taso kan su d'aya.



Daga kan zuhra sai haihuwar tayi mata jinkiri, sai bayan shekara takwas sannan ta haifi yara uku,Ihsan, muhsin da kuma islam.






Daga ammie sai mama na, baban ta ya maida sunan matar shi wato fateema,(gabatarwar yaran ta ya nayi a page one).




Daga nan sai auta khadeeja wato mamie,ita tana aure a Gombe mijin ta me kud'i ne kuma d'an siyasa ita kuwa yaran ta takwas ne yaya fahad wanda dalilin rashin haihuwar Ammie da wuri ta bata shi.




Sai mukhtar,muhammad,Al'ameen,Aisha amma ana ce mata humaira,khaleed,zainab, Ummul khairi, sai auta ummus salma.




Wannan shine tak'aitaccen labarin gidan su mahaifiya ta.






Abinci naje na zubo mana a k'aton tray shinkafa da wake da miya,sannan na kawo mana duka mu ukun muka saka hannu.





Muna ci muna fira, yaya fahad yayi sallama ya shigo, zama shima yayi ya saka hannu a namu.




"Da ka bari zuhra taje ta zubo maka",Hajjaju ta fad'a, ya mutsa fuska yayi yace"barshi kawai amarya ta naci tare dasu",daga nan bata kuma cewa komai ba.





Zama na cikin 'yan uwa na sai na manta da duk wata damuwar gidan mu,Fira muka yi sosai suna bani labarin garin su.





Haka har yamma tayi sannan na mik'e domin tafiya,zuhra ta b'ata rai tace"ba dai tafiya ba",murmushi nayi nace"eh tafiya zan yi mana".





"Wallahi gobe zan fara zuwa makaranta ne amma dana kwana",na bata amsa,da sauri suka ce"ba dai a gidan ku an barki zaki cigaba ba? ".





"Eh an barni",na basu amsa kallon juna sukayi suka kwashe da dariya,yaya fahad yace"gaskiya sun kyauta, yanzu sun ajiye ak'idar tasu ne? ".





"A'a, nice dai kawai aka bari amma sauran duk aure zasu yi",k'arar wayar dana ma manta da ita shi ya yanke ni.




Wayar na ciro, sunan ummi na gani, da sauri na d'aga,ina jiyo hayaniya k'asa-k'asa, cikin sanyin murya ummi tace"kin taho ne? ".






"A'a, ummi meke faruwa ne",na tambaye ta, "tunda baki taho ba ki zauna anjima kad'an zan turo Abdul'azeez ya kawo miki abinda zaki buk'ata ki kwana a nan kawai".




Gaba na ya fad'i domin na san ko da gidan su ne ummi bata fiye son muna zuwa muna zama ba,cikin rawar baki nace"ummi ki fad'a mini meke faruwa".




Bata bani amsa ba sai cewa da tayi"ina yaya bata wayar",kallon Ammie nayi da tun farkon wayar duka suka zubo mini idanu.





Jiki a sanyaye na mik'a mata wayar, bana jin me suke cewa naga dai ta mik'e ta bar d'akin, zama nayi ina sak'e-sak'e a raina.






"Waye ya baki wannan zazzafar wayar? ", yaya fahad ya fad'a cikin k'ok'arin kaudar mini da damuwa.




"Yaya khaleel" na bashi amsa a tak'aice,shukra tace"ko dai 'yar gida za'a yi ne?".





Murmushi nayi na saukar da kaina k'asa, d'agowa nayi na kalli hajjaju itama d'in ni take kallo,duk da azahiri haka zaka ce mu take saurara amma daka kalle ta zaka san hankalin ta ba'a kan mu yake ba.





"Babu wani 'yar gida kawai dai ya siya mini ne saboda karatu",na basu amsa,"hmm ya kyauta amma kuma ai wayace me tsada fa, wajen 75k take fa".




Zaro idanu nayi nace"da gaske",dariya suka kwashe dashi ni kuma nayi murmushi, hajjaju kam kasa hak'uri tayi ta mik'e tabi bayan Ammie.





Ni kuwa 'yan uwana sai k'ok'ari suke wajen mantar dani, nima kuma ganin hakan sai kawai nayi k'ok'arin danne damuwar.





Sai bayan minti ashirin, Ammie ta shigo,miko mini wayar tayi Ranta a b'ace,gaba na ya fad'i Ammie Allah yayi mata hak'uri kan kaga ranta ya baci ana dadewa dama mamie ce ita keda saurin hawa yanzu nan.






"Ki tura mata da text na abinda kike buk'ata, sai ta aiko miki dashi",daga haka ta kuma fita, shiru nayi ina tunani.






Ganin hakan ba zai mini bane yasa na tura da text d'in,firar kawai nake yi amma hankali na baya kan firar.




Da yamma aka aike mu siyo kayan muya domin d'aura abinci,mu hud'un mu muka tafi, muna fira.






K'ara waya ta tayi,kallon me kiran nayi,zuhra tayi dariya tana fad'in "yaya na",da sauri na d'aga ina murmushi.






Muryar shi ta doki kunne na yana fad'in "kina ina ne",cikin sauri na bashi amsa da"sabon gari",kashe wayar kawai yayi.







yanzu kam na tabbatar akwai matsala,jiki na har rawa yake yi tsabar tsorata, yaya fahad yace"nifa matsala ta dake kenan, tsoro",murmushi nayi hawaye ya zubo mini.





Kawai tsugunawa nayi na fashe da kuka,ni na san da matsala,shukra ta dafa ni tace"haba sis kiyi hak'uri mana bama fa ki san me yake faruwa ba".






Cikin kuka nace"shukra wallahi ina ji a jiki na wata matsalar ta faru ne", yaya fahad yace"ya isa haka yanzu goge hawayen ki".




Mik'ewa nayi na goge hawayen nawa, waya ta na amsa na kira Rufaida amma bata d'aga ba,number d'in Abdul'azeez na kira a kashe.




Shiru nayi ina tunani,waye zan kira yanzu, number din yaya khaleed na kira shima har ta katse ba'a d'aga ba.





To wai me yake faruwa ne a gidan namu????





Domin jin wannan amsar sai ku biyo yar mutan zazzau.





*Babyn abdul maman meenal,elham da farouk*.

#COMMENT
#LIKE AND SHARE.

*YAR MUTAN ZAZZAU*









♥ ❤
♥♥❤
*~K'AREENATEEY~*
(K'AWATA)

(It's all about friendship)

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*





*written *✍
-by-
*Deeja one love*




*JAKADIYAR GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION👸*




~Dedicated~

To


*~Aisha yunus(eesher lurv)~*


Wattpad 13 deeja





*ADDU'AR TASHI DAGA BARCI*

*_Alhamdulillahil lazi ahyana ba'ada ma amatana wa'ilay hinnushuur_*.



An karb'o daga Abu huraira Allah ya k'ara masa yarda yace"manzon Allah tsira da amincin Allah sun tabbata agare shi yace" *na abin hawa shi zai yiwa na me tafiya a k'asa sallama,mai tafiya a k'asa shi zai yiwa na tsaye sallama, kad'an su zasu yiwa wanda suke da yawa sallama* ".



Abin dariya to abin tambaya anan "zee baby* ya kike so ki ganni, wai ance mata ga one love wai *dama wannan ce one love d'in* na miki yarinta ko me??? Ni abin ma dariya ya bani amma duk da haka na gode sosai da ziyara Allah ya k'ara zumunci naji dad'i sosai da fatan kin isa gida lafiya.

Ba zan iya mantawa daku b *maman fulani,hajjaju da kuma imam ruqayya (mama na) hak'ika muna jone na kuma san son da kuke yiwa wannan littafin kuma ina jin dad'i sosai*.



*ina jin dad'in comments d'in ki zainab bala abubakar ta group din princess zahra, wannan dalilin yasa na baki wannan page d'in kyauta naki ne kiyi yadda kike so*.


*_AL-JABBARU_*


*_11_*




shukra tace"pls ki kwantar da hankalin ki, babu abinda ya faru insha Allah".





Jiki na har rawa yake yi,bance komai ba haka har muka dawo gida.





Magana hajjaju da ammie suke yi amma suna ganin mu suka dena,jiki na ya kuma yin sanyi.






Ina cikin jajjage yaya Abdul fatah(k'anin yaya Abdus-samad na biyu)sai da ya shiga suka gaisa da hajjaju da Ammie ban san me yace musu ba.





"Be kama ta ba haba ya za'ayi a bari taje gidan yanzu",na jiyo muryar Ammie tana fad'a,muryar hajjaju ita ma ta ratsa kunne na"Amma dai can d'in ne gidan su ko? ".





Sai kuma ban k'ara jin komai ba, sun fi minti goma sannan Ammie ta fito fuska a had'e tace"kizo ki tafi d'an uwan ki yazo tafiya dake", daga haka ta juya.





A sanyaye na shiga d'akin,Ammie na tsaye tana gyarawa islam botir na riga hajajju kuma tana lazimi(tsohuwar Allah yayi mata Yawan bauta).




hijab d'ina da nik'ab na d'auka sannan nayi musu sallama na fita,zuhra da shukra dake tsakar gida suma muka yi sallama.






A waje na tarar da yaya Abdulfatah da yaya fahad, suna fira yana gani na ya mik'e, sallama muka yi da yaya fahad akan sai sun zo.





Motar muka shiga shi kuma yaja muka tafi, babu wanda yayi magana har muka kai pz,wayar shi tayi k'ara kasancewar ya ajiye ta saman radio ne yasa naga sunan daya fito.




*yaya khaleel*,duk da bani ya kira ba sai dq gaba na ya fad'i,A handsfree ya saka wayar kawai ya cigaba da tuk'in shi.





Muryar shi ce me cracking amonta ya daki kunnen mu yana fad'in"Ka d'auko ta din? ",Yaya Abdulfatah ya bashi amsa da"eh na d'auko ta amma inaji zamu shiga ta k'ofar baya ne".





"No Abdulfatah ku shiga ta get, idan sun so su tab'a ta d'in,kada su fasa",ya fad'a cikin fushi sannan ya kashe wayar.





To fa! Na shiga uku ni juwairiyya,aifa nan da nan jiki na ya d'auki rawa,zuciya ta ta canza bugu har yaya Abdulfatah sai da ya fahimta Amma kasancewar shi bane hayaniya ba kawai cewa yayi na natsu.






Kaji mini mutumi na san me zan je na tarar,hawaye ya zubo daga idanu na cikin kuka nace"yaya dan Allah kayi hak'uri ka ajiye ni a nan, na koma".





Murmushi yayi yace"bafa ki san meya faru ba kuma ni umarni aka bani naje na d'auko ki dan haka kiyi shiru kawai ki natsu".




Kuka ya kufce mini, kaina na saukar k'asa ina rerawa,ban san ya d'auki wayar shi ba sai ji nayi yana cewa"to fa kuka take, duk ta tada hankalin ta".




D'agowa nayi wanda yayi dai-dai da mik'o mini wayar da yayi,amsa nayi duk da ban san waye ba,ina sheshshek'ar kuka nayi sallama.





Amsawa yayi sannan yace"kalli kiyiwa mutane shiru kada ki dama mini lissafi ki bari kije gidan mana".





Cikin kuka nace"yaya ina tsoro fa ban san me nayi musu ba ka bari na koma sabon gari",cikin fusata yace"tunda sabon garin gidan uban ki ne ba, ga gidan ku zaki ce zaki zauna a nan, kije mana idan sun ga dama su kashe ki ma nan ne gidan ku ba sabon gari ba", be bari nace komai ba ya kashe wayar.




Ajiye wayar nayi a inda take na maida kallo na kan titi har mun iso k'ofar doka, shiga cikin zaria dai tabbas kenan, hawaye na kuma sharewa.






Muna zuwa bakin get gaba na ya fad'i,yaya Abdulkareem dake tsaye a bakin get d'in ya bi motar da kallo ni kuwa sai zare idanu nake kamar sardauna yayi k'arya 😂.






Harabar gidan kamar anyi shara,babu kowa yana yin parking na fito kamar munafika lallai na tabbatar babu lafiya domin babu yadda za'ayi ka shigo gidan mu kaga babu kowa a filin harabar gidan.






Cikin sanyin jiki na nufi hanyar b'angaren mu, daf da zan shiga na juyo na kalli b'angaren su yaya momma.




Sannan na shiga ciki,da sallama na shiga a baki na,ummi dake zaune ta zuba uban tagumi gefen ta Abdul'azeez ne da hafeeza kowanne yana zaune yayi shiru.




Ina shigowa duka suka bini da kallo,kamar munafika haka na k'araso,har lokacin kuma kallo na suke yi,hakan ya k'ara fad'ar da gaba na.






Zama nayi sannan nace"ummi sannu da gida",sai da tayi ajiyar zuciya sannan tace"yauwa ya kika baro su".





A takaice na bata amsa da "lafiya lau suke suna ma gaishe daku",muna amsawa jeki kiyi wanka kizo ki d'ora abincin dare", ummi ta fad'a tana mikewa.




Kallona na mayar kan abdul'azeez wanda ya mik'e shima domin barin wajen na

1 Comments On KAREENATEEY
avatar
hauwa-8-2

1 year ago

Reply

Mashaa Allah

Please Login or Register in order to submit comment