Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ma wannan driver😲 akwai rainin wayo yana nufin ita zata d'auki trolley d'in.




"Heys! ", ta furta, juyowa yayi ya d'an kalle ta ya kuma juyawa, cikin d'aga murya tace"wai kai kurma ne ko baka san aikin ka bane, kayan waye zai d'auko maka".






Ya jita sarai amma yayi banza da ita,waya ta ciro tana k'ok'arin kiran mahaifinta,shi kuwa har ya kusa parking lot sai kuma ya juya ya koma.





Be mata magana ba duk da ya san mahaifin ta take kira trolley d'in kawai ya fara ja,biyo shi tayi cikin tsiwa tace"kai malam d'auka zaka yi, kana wani ja a k'asa irin classy d'in nan".




Dariya taso bashi hakan yasa yayi murmushi kawai,d'auka yayi kamar yadda taso ya yi gaba ya barta tana binshi da idanu.





"Gorgeously,so romantic! ",ta fad'a tana bin bayan shi.




A boot ya saka trolley d'in sannan ya bud'e motar ya shiga,kallon shi tayi a ranta tace"lallai wannan yana da rainin wayo wato ita zama ta bud'e motar da kanta? ".




"Kai ka fito ka bud'e mini mota, anya kuwa kasan aikin ka? ",banza yayi da ita dan shi ba hayaniya yake so ba yanzu.





Ganin bashi da alamar fitowa yasa ta bud'e ta shiga,cize lip tayi ganin idanun shi a lumshe,seat d'in ta d'an bubbuga tace"ka tafi mana am eager to see my dad".




"Oh ba lallai kana jin turanci ba, ka tafi ina so nayi sauri naga baba na",a hankali yace"ki dawo gaba",ah umarni kake bani ko me? ".




"Wannan ke ta shafa bana son hayaniya, ki dawo gaba nace kawai",Tab Allah ya kyauta na zauna kusa da driver kana so nayi downgraded d'in kai....... ", kasa k'arasawa tayi saboda wani kalar juyowa da yayi.





Sosai ta tsorata da yanayin idanun shi,cikin sanyin jiki ta fito ta koma gaban, jinjina kai yayi yana mamaki wato ma driver lallai wannan yarinyar ta raina shi.




Fizgar motar yayi da gudu ranshi b'ace, kallon shi tayi tana so tayi magana amma tana tsoro.



Lallai khaleel ka iya tsorata mutane harda masu tsiwa ma🤔.




Dole tayi shiru tana zazzare idanu, ita harma ya fara bata tsoro wannan daga gani zai yi girman kai.




Suna isa tangamemen get d'in gidan ta fara washe baki,shi kuwa horn yayi aka zo aka bud'e mishi.





Suna shiga gidan ta fara k'ok'arin bud'e motar, kallo d'aya yayi mata ta koma ta natsu😀.




Yana parking ya fito,mik'a mata key d'in yayi yace"idan kin shiga ki bawa maman ki",daga haka ya wuce ya fita.







Tsayawa tayi tana kallon shi,har ya fita murmushi tayi sannan tace"too pride",daga haka tayi cikin gidan da gudu tana k'walawa mahaifiyar ta kira.





*'Ya d'aya tilo kenan ga major sulaiman indabo, ita kad'ai Allah ya basu hakan yasa ta taso cikin gata da shagwab'a,yanzu haka karatu ya kaita k'asar india amma ta gama hakan yasa ta dawo*






Khaleel kuwa yana fita daga gidan ya manta da ita dama ba sanin sunan ta yayi ba, sai da ya biya ya fad'awa oga ya kaita gida sannan ya wuce block d'in su.





Kayan shi ya fara had'awa domin washe gari zasu tafi zaria.


🌠🌠🌠🌠🌠🌠🌠

Ina zaune ummi tace"kizo kije sabon gari ki amso mini sak'o wajen mama",ba tare da wata gardama ba na amsa da to.




"Dan Allah kiyi sauri ki dawo kinji",amsawa nayi da "to",ina fita su aunty fauza na fitowa,karima ta kalla tace"gafa 'yan boko, ke zo nan".




A tsorace na k'arasa kusa dasu,"ina zakije kuma? ",hawaye har ya taru a idanu na nace "sabon gar".




"Oh karima bana fad'a muku cewa can ake zuwa yawon gantalin ba", girgiza kai nayi nace"ummi ta aike wajen mama".





"Oh! To jeki yar gidan ummi",da sauri na tafi ina share hawayen da ya zubo daga idanu na, wannan wace irin masifa ce.





Banyi awa d'aya ba naje na dawo,Tunda na doso get d'in gaba na yake fad'uwa, ban san me zanje na tarar ba.




Tsabar tsangwamar da suke mini har nafi son na fita waje da zaman gidan.




Ina shiga naji kamar fitsari ya zubo mini,ganin rufaida da yaya khaleed,khairiyya, sumayya, fauza, karima,yaya usman da wasu ma daga yan gidan.




A wajen harda momma da hajiya,duka sun zubawa k'ofar idanu,hawaye ya zubo mini ina jan innalillahi wa'innna ilayhir raji'un, Allahumma ajirniy fi musubati wa akhlifni khairan min ha!.





Saukar marin dana ji ya dawo dani hayyaci na,binta nake da kallon mamaki,cike da mamaki nace"Rufaida ni kika mara".





Wani marin naji,kallo na bisu dashi, "khairiyya!,kema? ",kika tsare ni da idanu ai wallahi tunda kuka asirce mini d'an uwa to har abada baku ba kwanciyar hankali a gidan nan".





"Asiri fa kika ce khairiyya? ",ledar dake hannu na ta fuzgo, kukar da kub'ewa bushashshiya da kuma k'ullin bakin magani suka zubo gaba d'aya.






Aikuwa suka d'au salati gaba d'aya,kayan nake bi da kallo cikin k'unar rai, sak'on ummi ne a k'asa.





"Wannan meye eyeh!? ",khairiyya ta fad'a cikin d'aga murya, "ko zaki ce ba abinda zaki zubawa yaya khaleel bane a abinci".



Kasa cewa nayi komai sai hawaye dake zuba a idanu na, tsabar marin da suka yi mini har jini ya taru a gefen idanu na na hagu.




Durk'ushewa nayi ina sakin kuka me cin rai, wannan wulak'anci dame yayi kama,a dake ka a hanaka kuka.




Momma tace"ban tab'a tunanin zaku mallake mini yaro ba ashe haka kuke? ",hajiya tace"to dama barewa tayi gudu d'anta yayi rarrafe 'yan sabon gari ake gaya miko fa, ai sun wuce haka ma, idanun su duk a bud'e yake 😭😭".





Ai idan baki tashi tsaye ba to wata rana sai d'anki ya dena zuwa inda kike",hajiya ta k'arasa tana haki.






Abdus-samad ya kalli khaleel wanda idanun shi yayi ja jijiyar kanshi duk ta mik'e tsabar bacin rai, abin haushi harda mahaifiyar shi a wajen.





Tun d'azu suka shigo wanda tsabar gulma da k'ok'arin cin zarafi na ya hana a gansu.








Kallo na na mayar kan yaya khaleed shima d'in ni yake kallo da alamar tausayi, lumshe ido yayi alamar nayi hak'uri nothing he can do.





Abdus-samad yace"my man kaga abinda nake fad'a maka ko?, kaje ka tsawatar kada bak'in cikin abinda suke mata yasa ta had'iyi zuciya ta mutu".





Khaleel ciki fushi yace"ka bari ya kamata ace ta koyi jarumtar da zata iya kare kan ta, idan na amshe ta yau gobe waye zai amshe ta, kazo muje kawai",.





Fita suka yi daga motar suka nufo cikin gida,tun kan ya k'araso hanci nan mu ya jiyo mana k'amshin turaren sa.




Duk da yadda hawaye ke zuba a idanu na a haka na d'ago ina kallon shi,ba tare da yace komai ba ya wuce haka ma yaya Abdus-samad.




Jikin su ne yayi sanyi ganin be kula ta kan su ba, a hankali d'aya bayan d'aya suka bar wajen dan koda beyi magana ba idanun shi ya tabbatar musu da cewa yana cikin fushi.





Ina tsugunne a wajen na kasa mik'ewa ganin sun bar wajen kawai na kifa kaina a k'asa na cigaba da rera kuka na.



Oh poor juwairiyya life kenan😭.





*na gaida duk masoya na ina ganin sakon nin ku, ku sani one love na sanku a duk inda kuke,na whatsapp ne na facebook ne na wattpad ne duka nima ina ji daku, hope labarin yana tafiyar muku kuma yana sweet*.





*_kada ku manta babyn abdul ce maman farouk elham da meenal_*



*~YAR MUTAN ZAZZAU~*






♥ ❤
♥♥❤
*~K'AREENATEEY~*
(K'AWATA)

(It's all about friendship)

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*





*written *✍
-by-
*Deeja one love*

~Dedicated~

To


*~Aisha yunus(eesher lurv)~*


Wattpad 13 deeja

*ADDU'AR SAUKAR RUWAN SAMA*

*Allahumma sayyiban nafi'an*.


*ADDU'AR TSAWA*
*Subhanallazi yusabbihur ra'adu bi hamdihi wal mala'ikatu mini khifatihi*.



*IDAN AN GAMA RUWAN SAMA*

*Mumd'irna bi fadlillahi wa rahmatihi*



An karb'o daga abu huraira Allah ya k'ara mishi yarda yace"manzo Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace" *idan d'ayan ku ya tashi da daddare to ya bud'e sallar sa da raka'o'i guda biyu masu sauk'i*.



*Ruqayya imam ta group din jinnul aashique dake da meera ta annabi wacce ke group d'in justice ina jin d'ad'in yadda kuke bin novel d'in nan*.




*maman fulani* *hafsat hausa h² novels*



*Bloody(fatima batula) ke d'in ta dabance a zuciya ta, na gode sosai da addu'ar ki*

*_AS-SALAMU_*

_*7*_




Hannu yaya khaleed yasa ya dafa ni, A sanyaye yace"juwairiyya", jin muryar shi yasa nayi saurin mik'ewa na tafi ko waiwayen sa banyi ba.




Hannun shi ya had'a ya matse idanun shi sunyi ja sosai har zufa keto mishi take yi.




Abdus-samad ya kalle shi ya girgiza kai ya fice ya barshi.






Tuno yadda take tsugunne a gaban su yake yi,su kuma suna yi mata abinda suka so,Abdulfatah daya shigo yazo ya dafashi yana fad'in"ka kwantar da hankalin ka........ ".




Be k'arasa ba saboda mik'ewa da yayi ya kai mishi wani naushi,da sauri ya matsa yana mishi kallon mamaki.





Yaya abdus-samad daya kuma dawowa ya kalli yaya Abdulfatah yace"zo ka fita kawai",a sanyaye yaya abdulfatah ya fita.





Shima yaya abdus-samad d'in fita ya kuma yi ya barshi.





Yaya khaleel kuwa ji yake gaba d'aya duniyar juya mishi take, wannan wane irin rashin Adalci ne?




Ganin haka ba zai zamar mishi mafita ba yasa ya shiga bayi ya d'auro alwala yazo ya tada sallah.





Aikuwa yanayi A hankali yake jin fushin da damuwar suna raguwa, kafin ya idar har zuciyar shi tayi sanyi.





Kwantar da kan shi yayi jikin bed ya fad'a duniyar tunani.



___________________________________________________________""""________""""________________




Ina shiga ummi ta d'ago tana kallo na idanun ta sunyi ja wanda alamu ya nuna duk abinda ake yi tana ji.




Kusa da ita abdul'azeez ne ya saukar da kan shi k'asa ba zan iya tantance halin da yake ciki ba.





Girgiza mata kai nayi nace"ummi ki dena zubar da hawayen ki akan abinda be taka kara ya karya ba,bana son zubar hawayen ki".





Waya ta na bud'e na ciro sim da m card daya ciki, nace"yanzu ma zanje na maida mishi kawai",ummi bata ce mini komai ba har na fice.





Tsaye yake ta jikin window yana hango tahowa ta,a zahirin gaskiya a yadda na taho zaka iya cewa zan aikata abinda ke raina, amma ina cikin zuciya ta babu abinda take sai dukan uku-uku, ya zanyi haka Allah ya halicce ni da rauni har hafeeza ta fini k'arfin zuciya.





Da sallama na shigo, juyowa yayi tare da amsa sallamar,ai muna had'a ido na manta mema ya kawo ni.




Zare idanu na fara yi gaba na yana cigaba da fad'uwa,yaya abdus-samad daya kasa danne dariyar shi sai ya wayance da yin gyaran murya.



Shi kanshi ogan yadda nayi sai da abin yaso ya bashi dariya dan haka ya murmusa cike da waskewa yace"ya akayi kika zo kika tsaya a bakin k'ofa shigo mana, lafiya dai ko? ".





Cikin rawar murya nace"dama........ Dama..... Dama nazo yi muku sannu da zuwa ne", wannan karan kam duka sai da suka dara, ni kai na hakan dariya ya bani.





Murmushi nayi hawaye yana zubow daga ido na,cikin sauri nace"sai anjima", fice.



Ina fita na zauna bakin wajen ina kuka wannan wane kalar bala'i ne?, banji zuwan mutum ba sai hannu danaji a kunci na.



Da sauri na d'ago yana tsugunne hannun shi d'aya ya d'ora saman cinyar shi d'ayan kuma yana kan fuska ta.





Murmushi yayi mini yace"meya faru? ",cuno baki nayi nace"babu komai,dama zan ce ne banci jarabawar ba".





Murmushi ya kuma yi sannan yace"na sani ai, sai me kuma",dama zan baka wannan ne", na fad'a ina d'ago sim da m card.




Murmushi ya kuma yi sannan yace"me hakan yake nufi? ",kaina a k'asa nace"kayi hak'uri ba zan iya rik'ewa ba".




Had'e rai yayi yace"tashi ki bar nan kafin na b'allaki",da sauri na mik'e har ina had'a hanya wajen tafiya.




Tsaki yaja sannan ya koma d'akin, Abdus-samad yace"meya faru? ",fuska a murtuke yace"wai sim ta dawo mini dashi".



"To ina wayar? ",ya tambaya, d'aga kafad'a yayi alamar be sani ba,ganin hakan yaya Abdus-samad yayi shiru be kuma magana ba.




Ni kuwa ina shan kwana muka had'u da khairiyya kallon raini tayi mini kafin tace"Har an barbad'o mishi kenan",ban kalle ta ba na wuce.





Janyo hijab d'ina tayi kan tace"juwairiyya kina wahalar da kan ki ne, abinda be yi mini ba nida yaya khaleed da umma ke ba zai miki shi ba",hannu nasa na k'wace hijab d'in nayi gaba abu na.




Umma da hajiya da suke hango abinda yake faruwa suka yi dariya, hajiya tace"wai wannan yarinyar ba zata tanka bane, ni ina so ta tanka ne sai mu samu damar sawa ayi mata duka amma har yau tak'i tanka kowa".




Umma ta tab'e baki tace"nifa bana ganin laifin ta idan ban da haka me khaleel zai yi da wannan wanda yake da matsayi a soja, nifa da ace 'ya tace to da zan ji dad'i sosai amma wai wannan yake rawar jiki a kai".




Hajiya tace"to ai ni kaina bak'in ciki na kenan yadda ba 'yata yake yiwa wannan b'are-b'aren ba, amma ki sani muna zaune auren su ba zai yiwu ba".




Umma tayi dariya tace"matar malam kenan kada dai a kauche hanya", dariya suka yi suka tafa.




"Ni ai yadda kike zuga waccen shike burgeni kin san ni ba cika shiri muke ba, amma daba haka ba da yanzu na tada bom",umma ta fad'a suka saka dariya.




"Ai ita bata da wayo duk abinda na fad'a hawa take ta zauna,ni kuwa ta nan nake samun dama",shewa sukayi harda gud'a.




Ni dai nace"Allah ya shirye ku 🙏.





*kuyi hak'uri da wannan banda lafiya ne sosai*




*daga wannan ku irga iya yadda ya tsaya zamu d'ora daga one-one page naga wasu sun fara rud'ewa*.




*~yar mutan zazzau~*










♥ ❤
♥♥❤
*~K'AREENATEEY~*
(K'AWATA)

(It's all about friendship)

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*





*written *✍
-by-
*Deeja one love*




*JAKADIYAR GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION👸*




~Dedicated~

To


*~Aisha yunus(eesher lurv)~*


Wattpad 13 deeja



*ADD'UAR NEMAN TSARI DAGA ABIN CUTAR WA*

a'uzubi kalimatil lahi tammatin min sharri ma khalaqa.



An karbo dag abu huraira Allah ya k'ara masa yarda yace", manzon Allah tsira da amincin Allah sun tabbatar agare shi yace" *marik'in maraya nashi kona wanin sa, ni dashi kamar haka muke a aljanna*, sai imam maleek yayi nuni da dan yatsar sa manuniya da kuma ta tsakiya.


*_AL-MUMINU_*

_*8*_





Ina zaune rik'e da sim card d'in da kuma m card d'in Abdul'azeez ya shigo murmushi yayi mini nima kuma na maida mishi.





"Ki dena damun kan ki sweet koni ina so kiyi karatu, sai dai kuma kina ganin yadda gidan yake".




"Kada ka damu k'ani na idan da rabon zan yi, sai kaga Allah ya kawo hanya,ni ina ganin rashin cin jarabawar shi yafi mini kawai".





Jinjina kai yayi sannan yace"anjima za'a yi taro a falon baban gida, ina ji za'a saka ranar su aunty khairiyya ne".




"Eh ba zai wuce hakan ba amma ana neman mu ne? ",girgiza kai yayi yace"a'a ba'a neme mu ba, ke ai an gama da taki matsalar".




Haka kuwa aka yi a ranar aka tsayar da lokacin auren su nan da wata takwas, yayin da aunty fauza da aunty sumayya aka k'ara musu lokaci.






Aifa sai d'aga kai ya k'aru haka wulak'anci da k'ananan magan-ganu.





Ni dai abin har mamaki yake bani kafin wannan lokacin idan har ka san gidan mu to gida ne me zaman lafiya da had'in kai amma b'ullowar karatu na gaba d'aya komai ya canza.





Kiran daya shigo waya ta yasa na dawo daga tunanin dana tafi, ganin sunan yasa na gane waye.





"ki zo ina jiran ki"abinda ya fad'a kenan ya kashe wayar, bin wayar nayi da kallo ina mamakin hali irin na yaya khaleel.




Wayar na ajiye sannan na d'auki hijab, sannan na fita.



Ina fita na had'u da yaya khaleed da kuma rufaida suna tsaye suna fira, kallo d'aya nayi musu na d'auke kai domin na lura tunda aka had'a su shikenan kamar dama can suna son junan su.






Kamar na wuce bance musu komai ba sai kuma nace"barkan ku da hutawa", abin mamaki rufaida ta amsa mini"yauwa barka dai sis, sai ina kuma? ".





"Zan je wajen yaya khaleel ne yana nema na",to a dawo lafiya, ina ji anjima zan shigo wajen ki ma akwai maganar da zamu yi".





"Ba dai gulma ta zaku yi ba ko? ", yaya khaleed ya fad'a yana dariya,rufaida tayi murmushi tana rik'o hannu na tace"kinji juwairiyya kije kawai kibar husby ya cika tsokana".





Sai naji abin banbarak'wai wai namiji da suna hajara,ni yau rufaida zata zo waje na, tab lallai kam to idan ma da wani abu zata zo ubangiji ya fita.




Daga haka na tafi na barsu a wajen,da sallama na tura k'ofar, sai da ya amsa mini sannan na shiga.




Kamar kullum yana zaune yana operating system yayin da cewing gum d'in shi ke zaune yana tapping phone d'in shi.





Sau d'aya ya d'ago ya kalle ni ya maida kan shi ga abinda yake yi, nafi minti sha biyar a tsaye kamar me koyon magana yace"ki had'o mini coffee,ki kawo mini".





Ajiyar zuciya nayi abinda ya kamata a fad'a mini tun a waya ba'a fad'a ba sai da na sha wahala na zo.





Kitchen na shiga na had'a masa coffe d'in tare da spring rolls, akan tray na jera sannan na nufi section d'in su.




Suna a yadda na barsu, oh wai su wa'innan basa gajiya ne", na fad'a ina tab'e baki, d'agowar da zanyi muka had'a ido da shi.




Da sauri na dai-dai ta natsuwa ta sannan na k'arasa na ajiye mishi, kamar daga sama naji yace"ina wayar ki".




"Tana d'aki na bashi amsa",ba tare da ya d'ago ba yace"jeki ki d'auko ki kawo mini", ba tare da wani tunani ba nace to", sannan na tafi.




Akan sofa inda na bari anan na tarar da ita, ina tafe ina wasa da ita a hannu na.





Khairiyya ta kalli momma tace"wallahi momma wajen shi zata tafi", momma ta tabe baki tace"Allah ya kiyaye hanya".





Khairiyya ta zaro idanu tace"momma idan yace ina wayar fa? ",kira mini ita maza da sauri",khairiyya ta taho da gudu.




Gaba na tasha tunda na ganta na tsaya, gaba na yana fad'uwa, sai da ta nishad'antu sannan tace"kije momma tana kira".





Tana fad'in haka ta juya ta tafi,ajiyar zuciya nayi sannan na juya na nufi bangaren su.




Khaleel dake jikin window yana hango komai yayi murmushi yana lumshe idanu, lallai dole yarinyar nan ta fara tsiwa idan ba haka ba kuwa za'ayi ta cutar da ita.





Ina shiga na same ta kashingid'e a kan sofa tana kallo,gefe na tsuguna nace"ina wuni? ",ba tare da ta amsa ba tace"ina zaki je? ".




"Dama yaya khaleel ne yace naje na kai mishi waya ta",jinjina kai momma tayi tana murmushi sannan tace"to ki bud'e kunnen ki kiji, wallahi kika sake kika ce mishi ni na amshi wayar ki sai na b'allaki, tashi ki bar nan wajen",


tashi nayi sum-sum na bar wajen, Khairiyya tayi dariya tana jinjinawa mahaifiyar ta👍.





Sai da na tsaya a waje nayi kuka na mai isa ta sannan naje bakin tap na wanke fuska ta sannan na shiga.






Yanzu baya falo ina shiga yaya abdus-samad yace"ki shiga yana ciki", kamar munafika haka na nufi bedroom d'in.





Yana tsaye ya jingina da jikin wardrobe da alamu akwai abinda yake nema, ina shiga ya d'ago ya kalle ni sannan ya maida kanshi ya cigaba da neman abinda yake yi.





Ina tsaye ina k'arewa d'akin kallo,gaskiya yaya khaleel akwai tsafta, ban san ya matso kusa dani ba sai da naji k'amshin turaren shi.





Da sauri na kalle shi,muna daf da juna har numfashin mu yana had'uwa da juna,a hankali ya d'an matsa baya.




Murmushi yayi yana cizar leb'en shi na k'asa, kan yace"bani wayar",hannu na rawa na mik'a mishi.



Amsa yayi ya juya ta sannan ya kalle ni sanin me yake nufi yasa nayi k'asa da kaina gaba na na cigaba da fad'uwa.




Numfashi ya ajiye sannan ya koma gaban k'atuwar katifar shi,d'aya daga cikin wayoyin dake ajiye a wajen ya d'auko sannan ya dawo.





Sabuwa ce dal a kwalin ta damar niyyar shi ya amshi waccen wayar ya bani wannan, amma yanzu ganin babu ita kuma ya san may be baba malam ya amsa dan be kawo momma ba ganin yadda a da take sona.





Wayar ya mik'o mini yace"gashi nan saboda karatu da zaki fara wannan ya kamata ki rik'e kafin na siyo miki system,wannan kuma sai ki cigaba da kira da ita ina fatan dai bakiyi saurayi ba har yanzu".




Girgiza kai nayi ciki sauri,murmushi yayi yace"hakan shi yafi miki,kada ki sake naga kin tsaya da wani karatu zakiyi ok? ",kai na d'aga masa.




Wayar ya sami ni a hannu sannan yace"good girl",kallon wayar nayi kafin nace"na gode yay.......... ", wani kallo daya yi mini ne yasa na tsuke baki na, hanyar waje ya nuna mini.





Cikin rawar jiki na fice ina mamakin halin shi, ina fita nayi ajiyar zuciya sannan na wuce b'angaren mu da sauri.




Ina addu'ar kada na had'u da wani dan yanzu bana son had'uwa da d'aya daga cikin 'yan gidan mu saboda gudun cin zarafi na.






Da yamma ina zaune a falo littafin riyadus-salihin ne a hannu na ina duba wa rufaida tayi sallama ta shigo.




Amsa mata nayi ina kallon ta, murmushi tayi mini sannan ta zauna, ni dai bance mata komai ba ina bin ta da kallo.




Ban d'auka da gaske zata zata zo waje na ba ashe ita da gasken take duk da ban san meya kawo ta ba sai da naji dad'i.




"Ummi bata nan ne",ta tambaya ajiyar zuciya na sauke kan nace mata"eh ta shiga wajen hajiya baku had'u a hanya ba baba malam ne ya kira shine yace ta kaiwa hajiya ya kira wayar hajiyar bata d'aga ba".





Matsowa kusa dani tayi sannan tace"juwairiyya kiyi hak'uri da abinda ya faru sosai yaya khaleed yayi mini nasiha kuma na gane laifi na kiyi hak'uri kinji".





Har cikin raina naji dad'i hakan yasa fuska a sake nace"kada ki damu rufaida ban rik'e kowa a raina ba idan kika yi la'akari da ada gidan ba haka yake ba".





"Eh hakane gaskiya to amma duka rashin fahimta ne da kuma hassada da zuga",rufaida ta fad'a.



Kallon ta nayi nace"bangane ba? ", murmushi tayi kan tace"juwairiyya yawancin 'yan gidan nan kasuwanci suke yi, yaya abdus-samad da yaya khaleel kawai suke yin aikin soja, kuma a hakan yaya khaleel yana sama da yaya abdus-samad matsayin shi yasa kowacce mata a gidan nan take burin ya auri yarinyar ta,babu wacce ta samu sai ke yake kulawa wannan dalilin yasa suke hassada".





Da mamaki nace"to ai rufaida idan suna magana akan kud'i ne naga akwai masu kudi anan gidan", rufaida tace"akwai masu kudi amma babu wanda ya kai shi kudin ba, wallahi na gaya miki wannan abin duk hajiya ke zuga momma".




"Hmm koma meye Allah ya kyauta ni wallahi idan tunanin su wani abu ni babu komai tsakanin mu", rufaida ta kwashe da dariya.



"Allah sis akwai ki da abin dariya wai tsakanin ku babu komai,to kowa ai ya san me yake tsakanin ku".




Zaro idanu nayi nace"wallahi rufaida ba abinda kuke tunani bane ni hasalima tsoron shi nake ji, taya ma zaku yi tunanin kamar yaya khaleel zai iya auren kama ta? ".





"Hmm ai idan kinga kare yana shinshina takalmi to d'auka zai yi kedai kawai ki manta, amma lokaci zai zo komai zaki gani".



Daga haka muka cigaba da firar mu,sosai nake jin nishad'i har cikin raina wato kad'aici babu dad'i koda ummi ta dawo ta same mu munata

1 Comments On KAREENATEEY
avatar
hauwa-8-2

1 year ago

Reply

Mashaa Allah

Please Login or Register in order to submit comment