Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba zata sab'uba, bari naje na amso ta ke baki rik'e ba yayan shi be rik'e ba ita ya bata hakan ba zai yiwu ba".




Momma ta fad'a tana mik'ewa ta fita, khairiyya itama ta biyo ta tana k'ara zuga ta.





Ho khairiyya babu amana kenan🤔.






Ummi na zaune ni kuma ina aikin gyaran kitchen domin d'ora abincin rana ta shigo.





Jin sallamar ta yasa gaba na fad'uwa,da hanzari na fito.




Ummi tace"lale maraba da maman khairiyya ga wajen zama ku zauna".




"Ba zama ya kawo mu ba, ina munafikar 'yar ki take ta fito",dai-dai lokacin na fito.




Hakan kuma yayi dai-dai da fitowar abdul'azeez,ummi tayi murmushi tace"haba maman khairiyya kada kema zuga yayi aiki akan ki mana, ki zauna muyi magana ta fahimta".




"Ba wannan nazo ba maman hafeeza, abinda nazo daban wace maganar fahimta bayan abinda kunnuwa na suka ji haka idanu na suka gani".




"Waya nazo amsa ki bani ku zauna lafiya ina can na hanshare baki ana son yarana ashe ana can an barbad'e abincin da ake kai mishi".





Ummi cikin rashin fahimta tace"maman khairiyya wace kalar waya kuma, ai be bata waya ba, kud'i ne kawai",kallo na tayi tace"kije ki d'auko mata kud'in ki bata".





Kaina a k'asa nace"ai ta riga da ta amsa tun a waje", ummi ta juya tace"to ashe ma kin amsa, kiyi hak'uri insha Allah karatun ma ta fasa, zan je na sami baban gida".




Tsagal khairiyya tace"mu ba wannan muka tambaya ba, waya muka zo amsa, ta bayar kawai".




Ummi tace"haba khairiyya zan miki k'arya ne da kike cewa waya nace miki babu waya a wajen mu".




Fari tayi da ido tace"waya sani ko k'aryar kika yi, musa a baki fir'auna a zuci".




Abdul'azeez da tun farkon maganar yaje ya d'auko wayar ya dawo,jefawa khairiyya yayi a fuska yace"ga kayan tsiyar ku nan, ki sani mu ba'a koya mana rashin kunya ga naga damu ba yau da ace baki girme ni ba da saina zubar da hakoran ki, amma kinci darajar girman ki amma hakan ya kuma faruwa to zan ajiye girmamawan da nake miki na sauke hak'oran da ke bakin ki, ki dauka ku fice".




Khairiyya tace"au to bismillah shege ka fasa",momma tace"au rashin kunya zaka yi mana, khairiyya d'auki wayar mu tafi, ai dama barewa ba zata yi gudu d'anta yayi rarrafe ba,yaran sabon gari dama ai sai da haka rainon karuwai da kwartaye 😭".





Tana fadin haka suka fice,ummi ta fashe da kuka, haka nima da sauri na k'araso wajen ummi ina kuka.





Kaina a k'asa nace"ummi dan Allah kiyi hak'uri duk ni na janyo miki, dana sani ban amsa ba".




Girgiza kai tayi tace"abinda nake gudu shi yake faruwa,ni baki mini laifi ba sai dai meya sa baki fad'a mini maganar wayar ba? ".




Ina zubar da hawaye nace"ummi kiyi hak'uri ba zan kuma ba",abdul'azeez ya k'araso ya zauna yana huci yace"wallahi duk abinda zasu yi sub dad'e basuyi ba amma karatu babu fashi".





Daga haka ya mik'e ya bar wajen, ummi ta raka shi da harara tana fad'in "to uban ta sai ka tilasta mata, ke kuma wannan ya ishe ki kiyi karatun ta natsu ki janye daga karatun da kike niyar yi", ta fad'a tana kallo na.




Cikin kuka nace"ummi ina son karatun fa",mikewa tayi tace"kin shirya d'auke duk wa'innan abubuwan kenan, to sai ki tanaji hawaye dan wannan samfoti ne", daga haka ta wuce ta barni.









*to readers ga gidan malamai ya hargitse da surutu da hayaniya, shin karatun juwairiyya yana yiwuwa kuwa?*



*ko ya take k'arewa auren rauda da yaya khaleed*.




*ko ummi zata yarda da wannan karatun,idan ta yarda me yake faruwa cikin yin karatun*.




*menene hujjar khaleel na dagewa sai juwairiyya tayi karatu? *.




*shin momma tana sauka ta yarda haka kum zaman gidan yana dawowa kamar baya? *.




*Duk sai kun biyo ni domin jin wa'innan amsoshin,kada ku manta yanzu fa aka fara ko ainihin labarin ba'a shiga ba*.




*taku har kullum, babyn abdul maman elham da meenal*.




*_Keep following me_*

*~yar mutan zazzau~*




*#Follow*
*like*
*comments and share*.








♥ ❤
♥♥❤
*~K'AREENATEEY~*
(K'AWATA)

(It's all about friendship)

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*





*written *✍
-by-
*Deeja one love*

~Dedicated~

To


*~Aisha yunus(eesher lurv)~*


Wattpad 13 deeja




*ADDU'AR DA MUTUM ZAI YI IDAN ISKA TA TASO*.


*_Allahumma inni as'aluka khairaha wa khaira ma fiha wa khaira ma ursilat biha,wa'a uzubika min sharriha wa sharri ma fiha wa sharri ma ursilat biha_*.




An karb'o daga abu huraira Allah ya kara mishi yarda yace"manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yace"*kada d'ayan ku yayi tafiya da takalmi guda d'aya ko dai ya sanya su duka, ko kuma ya cire su duka"*.


*_AL-QUDDUSU_*.



_*6*_

Kifa kai na nayi ina rera kuka,haka nayi na gaji babu me rarrashi.






Sai da na gama sannan na mik'e naje na dora mana lunch,koda na gama jerawa nayi akan table sannan na wuce d'aki.





Wanka nayi na dama bana sallah hakan yasa na kwanta kawai,ban farka ba sai la'asar wani sabon wankan nayi.





Doguwar riga ta atamfa na saka pink da rastin brown and coffee,hijab na saka coffee colour har k'asa.






Sai da na tsaya na d'aura nik'ab sannan na fito, yadda na bar abincin haka yake wato alamu dai babu wanda yaci kenan.





Har nayi niyyar fita sai kuma na dawo,kofar d'akin mama nayi sallama daga ciki ta amsa mini.





Akan sallaya na taradda ita, kallo na tayi tace"har kin shirya",cike da feeling guilty na amsa da eh.





"To Allah ya kiyaye hanya, ya tsare kuma dan Allah ki k'ara kulawa",d'aga kai nayi nace"insha Allah ummi, naga baku ci abincin ba? ".






"Barci ne ya d'auke ni amma yanzu idan na fita zan ci, abdul'azeez be dawo ba kenan? ",nima ban sani ba amma yanzu idan na fita zan duba shi, su hafeeza basa nan ne".






"Eh sunje sabon gari ne amma na san sun kusa dawowa",ummi ta bani amsa, ajiyar zuciya nayi nace"Allah ya dawo dasu lafiya".





Daga haka na fita, d'akin su adul'azeez na lek'a babu kowa a ciki,hakan yasa na juya na fita kawai.







Kamar mara gaskiya haka na k'arasa b'angaren,kwankwasawa nayi an jima sosai kafin a zo a bud'e.





Ganin yaya abdulfatah(me bin yaya abdus-samad), gaishe dashi nayi ya amsa cikin sakin fuska.




"Yaya khaleed fa? ", na tambaye shi, da mamaki yace"ai ya tafi makaranta be dad'e da fita ba", bance komai ba na juya.







Ina daf da fita get khairiyya ta shigo tare da Aliyu, kallo na suka yi suka kwashe da dariya kafin tace"a'a kaga 'yan bokon gidan mu".





Bance da ita komai ba nayi hanyar fita da sauri, karo mukayi da yaya usman,babu b'ata lokaci ya wanke ni da mari.





Dafe kunci nayi hawaye yana zuba daga idona, a gaskiya tun yanzu na fara dana sani,fauza dake tsaye a wajen ta zaro ido tace"kai yaya usman kana so kayi frog jump kenan? ".






Khairiyya tace"to ai wanda take tak'ama dashi d'in baya nan, sai muga me rama mata".




Cikin kunar rai nace"khairiyya kin kyauta, koda wasa ban tab'a tunanin zaki juya mini baya ba, ashe d'an adam baya kuskure ashe kowa ba da tashi k'addarar ba, da kike cewa babu mai rama mini ki sani Allah yana nan kuma shi zai rama mini".





Cikin hargagi yaya usman yayo kai na wai zai dake ni, yaya abdulfatah ya dakatar dashi"kada ka soma marin daka mata ma kaji da hakkin shi".




Kallo na yayi yace"juwairiyya kiyi hakuri wuce ki tafi Allah zai saka miki",juyawa nayi na tafi ina mamakin halin d'an adam me sauyawa kamar walk'iya.







A haka har na isa makarantar abin mamaki yaya khaleed na tarar zaune shida Rufaida suna fira.




Yana gani na ya d'auke kai, Rauda kuwa dariya tayi tace"ga 'yan boko sun iso",hawayen dake k'ok'arin zubo mini na tare.





Abinda ya bani mamaki yadda yaya khaleed ya d'auke fuska a gare ni,cikin sauri na wuce ajin daya kasance nawa.




To kosu kansu d'aliban sun fahimci ina cikin damuwa haka karatun ya tashi babu wani armashi.



Yanzun ma ni kad'ai na taho gida, a hanya na had'u da Aliyu da ameer sun dawo k'wallo, tare muka jero dasu.




Aliyu nata bani hak'uri akan abinda ya faru d'azu wannan shine ya sanyaya mini rai.





Koda nazo na tarar dasu hafeeza sun daw cire hijab nayi kawai na d'ora abinci.





Sai bayan magrib sannan abdul'azeez ya dawo, harara na aika mishi nace"ai wallahi ka nuna babu amana na d'auka damuwa ta taka ce ashe ba haka bane? ".





Murmushi yayi ya ciro waya yana mik'o mini yace"kiyi hak'uri sweet wallahi kasuwar sabon gari na shiga, to kuma sai wani aboki na ya rik'e ni shine dana dawo na tsaya a pz na siyo miki wayar".




Amsa nayi ina kallo"kai aikuwa waya me kyau",na fad'a ina washe baki"a ina ka sami kud'i kuma? ",na k'ara jefo mishi tambaya.





"Kai sweet kin manta ina aiki ne, ko angaya miki nima cima zaune ne🤓? ", girgiza kai nayi nace"thanks sweet bro",any thing for you sweet sis".




Daga haka muka mik'e muka nufi wajen cin abinci,ummi ta kalle mu da fara'a domin tunda abinda ya faru da safe ban kuma fara'a kalar na yanzu ba.




"Ni dai wallahi haifar ku kawai nayi amma ban isa naji cikin ku ba yanzu meya faru kuma? ".




Abdul'azeez yace"ummi waya ce fa na siyo mata saboda kinga be kamata ace yaya khaleel ya san abinda yake faruwa ba ko? ".





"Eh lallai kana da hankali, wato shiyasa bana damuwa idan ban san sirrin ku ba domin nasan cewa kuna bawa juna shawara me kyau, Allah yayi muku albarka", duka muka amsa da ameen.








B'angaren khaleel kuwa koda suka tafi sunyi nisa kafin yaya abdus-samad yace"man kasan wacce wayar ka bawa yarinyar nan",b tare da damuwa ba yace"na sani mana".





"My man ita fa na dinga rok'on ka akan ka bani amma ka hanani har canje da tawa nace muyi amma ka k'i shine ka bata, wanda kasan rigimar da hakan zata b'allo".





"my guy na d'auka kai baka a cikin shirmen gidan ashe kaima kana bi?, ka sani yarinyar nan tunda na dawo take kula dani,meye dan nayi mata abinda yafi haka? ".





"Ka fahimce ni ba wai ina nufin wani abu bane,a'a ina gudun maganar ne a gidan da kuma irin abinda zai biyo baya", abdus-samad ya bashi amsa.





"Kada ka damu dai-dai nake dasu kowa yazo ya tare ni da maganar zai ji amsa me kyau kuwa", to ita yarinyar kuma fa",abdus-samad ya tambaye shi.







"Ai wallahi duk wanda naji yayi mata wani abun sai na hukunta shi", ya fad'a cikin fushi.




"Babu yadda za'ayi kace baka son ta tunda gashi nan yanayin furucin ka ya tabbatar, ka yarda ka aure ta kawai".




Kallon baka da hankali yayi mishi sannan yace"ka san dai ba zan auri k'aramar yarinya kalar ta ba nafi son mace mai tsiwa wacce bata da tsoro amma ita wannan ta cika tsoro".






Murmushi kawai abdus-samad yayi yace"amma koda a hakane daka aure ta kaga idan ta gama karatu sai ka sake ta".






"Ka san dai manzon Allah(SAW)ya hana kalar wannan auren ko, bana fatan na lalata rayuwar ta".





"Shikenan yadda kace dama maslaha nake nema muku",kai da da za'a baiwa k'aramar yarinya sai ka bada himma",wata dariya yaya abdus-samad yayi yana shafa fuskar shi.





*GIWA BARRACK,MAIDUGURI*.





sai bayan isha'i suka isa wai ma a haka sunyi sauri kenan,sojojin dake barrack din ne suka dinga sara musu wanda hakan ya alamta cewa su din manya ne a wajen.









Wani dake zaune sanye da shadda mai ruwan toka,gaban shi sojoji ne haka ma bayan shi, sanye yake da eye glasses irin medicated d'in nan.





Suna zuwa suka sara mishi, mikewa yayi cikin farin ciki yace"kaga mazaje, sadaukai masu saka gaban maza faduwa kun karaso kenan? ".






A tare suka amsa da eh,jaridar hannun shi ya d'auka yace"muje daga cikin office d'ina",a tare suka kuma amsa da yes sir.





Cikin sauri suka d'auki jakar dake gefen shi da kuma sauran tarkacen shi suka bishi a baya.





Da dare suna zaune suna fira momma ta kira shi kamar ba zai d'aga ba sai kuma wata zuciyar tace ya d'aga mana.






Kallon shi ya mayar kan al'ameen da abdus-samad,murmushi abdus-samad yayi mishi domin shi yasan meye yake gujewa.






A hankali ya d'aga, tun kan yace komai momma tace"ka kyauta wallahi,shin dama ashe ban isa da kai ba, ni zaka wulak'anta na ce kazo shine ka sulale ka tafi".





Cikin kwantar da murya yace"kiyi hakuri momma nan da one week zamu dawo,kinga tafiya ce me nisa tsakanin zaria zuwa borno".






Ba tare da tace komai ba ta kashe wayar, komawa yayi ya zauna yana faman nazarin abubuwa.







a yau zamu je post ume da wuri na shirya wanda har lokacin ban sami sauk'in abinda ake mini a gidan ba kawai dan wai yaya khaleel ya nuna mini kulawa.





Jar atamfa na saka,hijab na saka shima ja tare da takalmi na fari.






Sauri-sauri nayi na tafi domin gudun yin latti, sai da na fito na tuna banda ko naira biyar, wajen ummi na koma tunda na shiga ta kalle ni ta kauda kai.






Kaina a k'asa nace"dan Allah ummi kud'in mota",ba tare data kalle ni ba tace"duba kan frodge akwai d'ari biyu ki d'auka".


Godiya nayi bata ce komai ba, na je na d'auka sannan na fito.





ina fitowa bakin get muka had'u da yaya khaleed.



Tunda ya kalle ni ya kauda kai,nima kuma kauda nawa kan nayi na wuce ina mamakin halin 'yan gidan mu.





Ina fita yaya abdulfatah yana shigowa,gaishe dashi nayi domin dai yana d'aya daga cikin wanda yanzu nake samun sauk'i a wajen shi.




A bakin titi na samu mota kasancewar ranar monday ne kuma da safe yasa ban sami wata wahala ba wajen samun mota.





Sai k'arfe hud'u muka baro wajen hall d'in, pure water na siya shi kan shi ruwan d'umi gare shi.




Kai talaka na wahala haka nayi alwala sannan naje nayi sallah,ina fitowa na hau mota sai gida.




Ban shiga makarantar islamiyya ba yau saboda gajiyar da nayi, ina tura get na tarar da khairiyya da rufaida suna magana.




Da alamu maganar ta shafe ni ganin yadda ina shigowa suka zubo mini idanu,kauda kaina nayi na wuce.





Ina bada baya suka saka shewa,ban bi ta kansu ba na wuce kawai.





Wanka nayi na canza kaya sannan na kwanta,ko ummi sai da ta shigo d'akin sannan ta ganni.




Abinci da ruwa ta aiko abdulmalik dashi,ina kwance ban mike ba bare ma naci abincin,barci ya d'auke ni ina a haka.



Ummi ta aiko abdulmalik ya tashe ni,wai yamma yayi,alwala nayi nayi sallar magrib sannan na fito.





Ina fitowa abdul'azeez yana shigowa,murmushi muka yiwa juna sannan yace"yan makaranta ai na shigo na tarar kina barci".






"Eh na gaji ne shi yasa ina kwanciya kuma barci ya d'auke ni",to ya exam d'in? ",Alhamdulillahi sai dai jiran sakamako".





Tare muka k'arasa wajen cin abincin, muna gamawa baba malam ya shigo.




"Barka da dare baba",na fad'a, "yauwa barka mama na ya jarabawar? ",alhamdulillahi baba",to Allah yasa muji Alkhairi".




Muka amsa da ameen,sannan muka tashi muna komawa falo nace"sweet wai ya akayi ummi ta sauko ne? ".




"Ba dama nace ki bari zamu shawo kanta ba, to ina zuwa nayi mata magana ta amince ina ji baba malam dama yariga da yayi mata maganar ".





Murmushi nayi bansan me yasa nake matuk'ar son wannan karatun ba.





Lokacin da na shiga d'aki dai-dai kiran yana yankewa, sai lokacin na tuna da wata waya, oho ina ruwan bintalo😀






Ina d'aukowa wani kiran na shigowa *yaya nah* sunan daya fito kenan,gaba na ya fad'i kallon kiran nake yi ina zullumin na d'auka ko kuwa kada na d'auka.




Sai da ta kusa katsewa sannan nayi bismilla na d'auka,shiru nayi zuciya ta tana bugawa.





Khaleel kuwa jin an d'aga yasa yayi shiru, jin tak'i magana yasa yayi ajiyar zuciya yace"ya exam d'in, dan a lissafi na yau zaku yi".




"Alhamdulillah sai dai jiran sakamako",na fad'a baki na yana rawa,"to shikenan idan da wata matsala ki kira ni kawai",ba jira nace komai ba ya kashe wayar.





Rik'e wayar nayi ina juya ta, na kasa motsawa ma kwata-kwata,jin nayi an tab'a ni,da sauri na juyo ina fadin"innalillahi! ".




Dariya yayi yace"sweet kin cika tsoro wallahi ki rage idan ba haka ba wata rana zuciyar ki zata buga ki mutu".



ajiyar zuciya nayi nace"sweet Ai tsoro halas ne", hakane amma naki ya cika yawa, yanzu dai zamu iya magana".





"Why not? ",gefen gado muka zauna,cikin kwantar da murya yace"sis wai meya faru ranar dana ganki kina kuka ko dai yaya khaleel yayi rapi...... ",k'asa yayi da kai.






Murmushi nayi nace"a'a kaima ka san da hakan ya faru zan fad'a maka kawai tsorata ni yayi",nan na k'arasa bashi labarin abinda ya faru.






Dariya yayi yace"sweet kin san raunin ki", girgiza kai nayi"tsoro shine raunin ki sis",ya fad'a yana dariya.




Duka na kai mishi ina fad'in Allah ka raina ni,shigowar ummi tare da hafeeza yasa muka dena dariyar.





"Ka tashi kaje ka kwanta dare ya fara yi",daga haka ta juya,abdul'azeez ya mik'e yana fad'in"sleep tight my sisto",jinjina kai kawai nayi shi kuma ya fice.







Khaleel kuwa yana kashe wayar ya maida kallon shi kan Abdus-samad,shi kuwa ganin yana kallon shi yasa ya juyar da kan shi.






Be san me yasa yake damuwa da abinda ya shafi yarinyar ba,ya kamata ace ya zurfafa tunani akan al'amuran ta.






Yanzu dai duk girman gidan mu na koma rayuwa ni d'aya, ummi bata cika kulani sosai kamar da ba, daga ni sai 'yan uwa na wanda muka fito ciki d'aya.





Bani da damar na fita waje sai k'ananan magan-ganu da kuma gulmace-gulmace, da hantara da gori.






Haka kuma babu me shigowa inda nake, kasancewar bana zuwa ko'ina sai makarantar islamiyya da yamma hakan yasa nake yawan zaman d'aki.






Ina zaune nayi tagumi hawaye yana gangarowa daga idanu na,ba komai ya fiye damu na ba sama da share ni da mahaifiya ta take yi.





Abdul'azeez namiji ne ba zai yiwu ace koda yauyazomuna tare ba yana buk'atar fita,Allah yasa yanzu da waya ma a waje na haka nake wuni game.




Ummi dake tsaye saman kaina wanda ni ban ma sani ba tayi ajiyar zuciya tace"wai ke me yake damun ki ne?,kwata kwata yanzu baki da walwala kamar da".





"To ummi ya zanyi rayuwa takan juyawa mutum ba yadda ya so ba,ummi gaba d'aya rayuwa ta ta sauya,ke kanki yanzu bakya damuwa dani, ummi idan baki bani goyon baya ba waye zai bani, baba ba zama yake yi ba ummi bana so nayi abinda ba zai saki farin ciki ba".





Na k'arasa maganar cikin kuka me tsanani,rungumo ni ummi tayi tace"abinda yasa kika ga ina miki haka saboda ina duba halin da zaki shiga ne, kada ki manta ni na haife ki karatun da zakiyi zai amfane ki amma kuma me nafi so kiyi a gidan ki kamar yadda duk sauran 'yan gidan nan suke yi".





Girgiza kai nayi cikin kuka nace"ummi indai hakane na hak'ura zan fad'awa yaya khaleel idan ya dawo".




Murmushi tayi tace"yauwa yar gidan ummin ta kinga yanzu zamu tsira da mutuncin mu, yanzu ki cire komai a ranki kinji", d'aga kai nayi gaba na na fad'uwa taya zan tari yaya khaleel nace mishi na fasa karatu.




Aikuwa ranar naga bambanci wajen ummi dan yadda ta dinga nan-nan dani,hakan ya k'ara mini k'arfin gwiwar tunkarar dodan nawa😀.




Ina aji bayan na tashi d'alibai na,sai ga yaya khaleed da alamu be san ina ciki ba sai da ya matso kallon-kallo muka yiwa juna sannan na d'auke kaina ina k'ok'arin had'a kaya na domin tafiya gida.





Bai tafi ba haka be k'araso ba,yi nayi kamar ban san da zaman shi ba har sai da nazo kusa dashi.



Cikin sanyin murya yace"juwairiyya kiyi hakuri da abinda yake faruwa",kallon shi nayi nace"hak'uri akan me yaya khaleed,baka yi mini komai ba haka kowa beyi mini komai ba,nice me laifi saboda da ban amince ba da hakan bata faru ba Allah ya baku hakuri".




"Sai dai ka sani a dalilin hakan na san wa'inda suke sona tsakani da Allah na san wa'inda suke sona akasin haka, wallahi ka bani mamaki ban tab'a tunanin hakan daga gare ka ba".




"Ashe duk yaudara ta kake yi ashe ba zaka iya kasancewa tare dani a cikin halin k'unci da walwala ba,saboda kawai yaya khaleel ya nuna kulawar shi a kaina shikenan kuka d'auki karan tsana kuka d'ora mini, wai abin har yana shafar mahaifiya ta".






"Meye nata? Me tayi muku, karatu ai ba k'arya bane, amma har wa'inda basu kai su tsaya suyi mata magana ba yau a dalilin wannan matsalar sun mata".




"Kada ku manta we are all family,jinin dake yawo a jikin khairiyya shi yake yawo a jiki na haka jikin rufaida da usman haka naka amma duk kun manta haka,idan har ina da hakki akan ku Allah ya fitar mini haka idan ku kuke da hakki akaina Allah ya fitar muku", daga haka na juya ya bar wajen.






Shiru ya tsaya yayi kawai jikin shi duk yayi sanyi, ni kuwa duk da hawayen da yake zuba daga ido na amma zuciya ta wasai take domin yau na rage damuwar dake rai na.





A bakin get saura kad'an muyi karo da khairiyya kallon up and down tayi mini kafin tace"an shiga sabon garin ne anje an amso saboda anji cewa gobe suna hanya,lallai malamin naku yana k'ok'ari".




Ban kulata ba na wuce ciki,ni ban ma san gobe zasu dawo ba sai a bakin ta,duk wannan haukar da suke yi jarabawar ma ba cin ta nayi ba.





Kuma nayi alk'awarin yana dawowa zan tattara na kai mishi abinda yake nashi a waje na nace mishi na fasa karatun.





*_GIWA BARRACK,MAIDUGURI_*.




"Ya yarinya ta tana hanya,AK ko zaka taimaka kaje ka d'auko mini ita? ",cikin masa umarni yace"yes sir! ".




shafa kanshi yayi yace"yauwa na gode khaleel jirgin zaiyi landing nan da awa d'aya,kuma bana so tayi ta jira idan ka d'auke ta ka kai ta gida".




"Ok sir! ", ya sake fad'a,daga haka ya sara mishi sannan ya juya ya fita.




A can kusa da gym ya sami al'ameen da Abdus-samad da alamu ma fira suke yi,"My guy bari naje oga ya aike ni naje na d'auko yarinyar shi a airport".





Abdus-samad yace"ko muje mu raka ka ne? ",nop ku barshi yanzu zan dawo", daga haka ya juya ya tafi su kuma suka cigaba da firar su.





Jikin shi sanye da black jeans da blue t-shirt,takalmin k'afar shi ne kawai zai fahimtar da kai cewa soja ne.





Wani k'aton shade bak'i ya saka a fuskar shi yayi kyau sosai daka ganshi ka san cikakken namiji ne gwarzo kuma jarumi.





Da kanshi yake tuk'a motar,cike da k'warewa koda ya isa airport d'in agogon hannun shi ya kalla jirgin yayi landing da minti biyar kenan.





Waige-waige ya fara ta ina zai hango ta,wata siririya fara ya hango sanye take da riga da wando na nylon.




Fuskar ta babu fara'a idanun ta sanye da shade,hand bag ne rataye a hannun ta sai trolley dake gaban ta.




Ba mummuna bace domin dai fara ce kuma tana da hanci kasancewar idanun ta yana cikin shade ba zan tantance yanayin girman su ba.




Kanta sanye da gashin roba wato roba attach anyi mata ghana weaving manya-manya, yayinda ta bazo shi har kafad'a.






Wayar ta ta ciro da alamu wani zata kira,tunda ya hange ta jikin shi ya bashi itace,yana k'arasawa tana fad'in"haba dad har yanzu bai k'araso ba ya hanya ni da yawa gaskiya dole ma a kore shi kawai kasan ai bana son delay".





Yatsun shi biyu ya d'an kad'a suka bada d'as,juyowa tayi tana kallon shi,a zuciyar ta tace"ashe 'yan naija sun fara iya wanka kenan😀? ".





"Zo mu tafi",daga haka yayi gaba, bud'e baki tayi tana mamaki lallai

1 Comments On KAREENATEEY
avatar
hauwa-8-2

1 year ago

Reply

Mashaa Allah

Please Login or Register in order to submit comment