Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya zama naki sis kiyi yadda kike so dashi, *JAKADIYA* ta baki wannan yan shafukan har zuwa karshe, muna godiya sosai da irin kaunar da kike mana.



Babu komai wannan ma mungode nadade ina fatan marubuta masu kishin addini Da al,adu masukyau to dakyau kyakkyawar niyar Allah ya biya kurakuran ciki yacgafarta mana gaba daya,ban sanki amma ina kaunar har agurin mahaliccina nagode *zulaihat isma'il*



*Ki sani nima ina sonki kamar yadda kike so na Allah kuma ya ƙara mana son juna,haƙiƙa naji daɗin Addu'arki sosai da sosai ina godiya*



*_ka faɗi magana ta gaskiya,da badan dacewar ra'ayin mutane ba da kuma dacewar rayukan su da juna ba_*



*_Da mutane sun halaka dukkan su wajen yin saɓani da kuma gaba_*



_*ka rayu kana me amintacciyar zuciya(zuciyar ka babu wanda ka riƙe)game da giba kuma ka ɓoƴu(kada kayi ta)*_



*_sai ka shiga shingen tsarki(Aljanna)halin kasancewar ka wankakke tas*_



*Faɗar shaɗubeey kenan a cikin littafin sa Hirzul.amaneey(shaɗubiyya)*.



Haƙiƙa abin dubawa ne a cikin wa'innan abiyat ɗin.


Da ace muna haɗa kan mu,da babu wanda zai shiga tsakanin mu,mutum idan yayi maka abu uzuri zaka bashi ba wai kuyi ta rubuce rubuce kuna zagin juna ba meye amfanin hakan.



Wallahi duk abinda yake faruwa a duniyar online writers yawanci mu muka fara buɗe ƙofa,har ace wai wani wanda be taɓa rubutu ba yazo ya zage mu ke kuma kina washe baki saboda bake aka zaga ba,ko kina group a zagi ƴar uwar ki amma sai ki share abin kunya wata ma ita ke taimakawa ko ta shiga a zagi wata da ita.

*Allah yasa mu dace ameen*

*_22_*




Baba malam da kanshi ya dinga yi mini tofi haka har na samu na dena jin raɗaɗi,Ummi bata ce komai ba hakan kuma ya ƙarasa na jinjina mata sosai.




Baban gida kuwa yanzu zuba mana idanu yayi dan abin ya fara bashi tsoro,washe gari Abba ya diro garin aikuwa sun sha ruwan faɗa ya kuma yi musu gargaɗi me ƙarfi akan faruwar hakan.



Kuma ya tilasta Khairiyya da Momma suka zo suka duba ni,sannan ya saka Yaya Abdul-raheem ya zane ta daman shine me zafi bayan Yaya Khaleel.




Alhamdulillahi ban haɗa kwana biyar ba na sami sauƙi sosai da sosai,haka na cigaba da rayuwa da kuma harkokin yau da kullum.




Yau da yamma ina zaune a ƙofar part ɗin mu da yake akwai balcony a jiki,kujera na saka na zauna.



Jiki na sanye da pakistan kalar white and black,sai farin ƙaramin hijab dana saka akai,hannu na riƙe da waya ta ina jin ƙira'ar Abdullahi Abba Zaria,idanu na lumshe ina saboda earpies na saka.


Ɗayan hannun nawa kuma riƙe da glass cup cike da hollandia ina sha lokaci zuwa lokaci,yau nishaɗi nake ji sosai,dan fuska ta ɗauke da murmushi.




Ni kaɗaice saboda Rufaida tana makaranta hakama Abdul'azeez saboda exam ɗin su daya matso.



Get aka wangale musu,motar su ta shigo,yana gefen me zaman banza yayin da Yaya Al'ameen ke tuƙawa.




Sai da ya dai-dai ta parking sannan suka fito daga ciki,har yayi hanyar part ɗin su kamar ance ya waiga ya hango ta zaune.



Zuba mini idanu yayi gaskiya yayi kewar ta sosai,gani yayi kamar canza ta aka kuma yi zuciyar shi ta fara bugawa da ƙarfi.



Juwaya yayi ya kalli su Al'ameen yace"kuje kawai gani nan zuwa",a tare suka amsa da to daga nan suka juya suka tafi.





Wajen da nake zaune ya nufo cikin tafiyar shi ta cikakken soja wanda yake da karsashi.






Tun daga nesa hanci na ya fara jiyo mini ƙamshin turaren shi,kasa gasgatawa nayi domin loksci zuwa lokaci hakan ya kan faru.




Hannu yasa ya cire earpieces guda ɗaya ya mai da kunne shi,cikin sauri na buɗe idanu ganin shi a gaba na,yana tsugunne a gaba na fudkar shi ta ƙara fayau da haske sannan ya ƙara kyau.




Idanun shi ya sake haske sosai,ya ƙara kwarjini kallon kallo muke wa juna,shiru ya ziyarci wajen.




Murmushi yayi sannan ya saka hannu ya amshi glass cup ɗin dake hannu na,bakin shi ya kai ya kurɓa.





Lumshe idanu yayi alamun da daɗi,baki na ya matso da kofin,da ido na nuna mishi na ƙoshi,haɗe rai yayi ya kafa mini idanu wanda yasa na kasa yi mishi musu.





Buɗe baki nayi ya zuba mini,lumshe idanu nayi alamun yayi daɗi,a tare muka saki dariya.




"barka da dawowa Yaya,ya hanya?",na faɗa,sai da ya ajiye numfashi sannan yace"hanya lafiya ya karatu".





"muna hutu ai",ɗaga mini gira ɗaya yayi yace"sai next level ko?",nima gira na ɗaga mishi,kashe mini ido yayi kafin ya miƙe yace"a taimakawa bawon Allah da abinda zai ci",daga haka ya wuce ya tafi.




Cike da farin ciki na miƙe da sauri na shige part ɗin mu,kitchen kawai na wuce na fara ƙoƙarin girka wani abin.





Shinkafa da miya nayi sai latas da tumatir dana yanka harda kokomba,sai kuma farfesun kifi dana yi wanda yaji kayan ƙamshi sosai.




Jerawa nayi a cikin basket sannan na fita,a falo na sami Ummi kallo na tayi tace"ikon Allah da alamu dai Khaleel sun dawo wannan zumuɗi haka".




Ƙasa nayi da kai ina murmushi,sannan na fice daga ɗakin ina dariya.




Da sallama na shiga,yana tsaye hannun shi riƙe da waya da alamu akwai abinda yake yi,Yaya Abdus-samad kuma yana zaune a kujera ya ɗora ƙafa saman tebur ɗin falon.




Shiga nayi sai da na gaishe da Yaya Abdus-samad sannan na ajiye abincin,Yaya Al'ameen ya fito daga cikin ɗakin.





Kallon juna muka yi sannan muka yi dariya,da sauri ƴa ƙaraso yace"budurwa ta ashe dai zaki zo waje na".



Ta gefen ido na kalli oga,kamar yadda na zata idanun shi yana kaina,murmushi nayi nace"ayya ai zan zo kodan ka san cewa ƴan zaria sun iya karrama baƙo",dariya yayi sannan ya tsigunna ya buɗe kular dana zubo abincin.




Murmushi yayi sannan ya ɗaga mini yatsu biyu 👌 yace"lallai na yarda da hakan,amma kizo gombe kiga ainihin karrama baƙo".




Juya idanu nayi nace"shikenan",Yaya Khaleel wani ɗaci yaji a maƙoshin shi ganin yadda ta juyawa wani ido.




Yaya Al'ameen yace"ah lallai budurwa na wannan fari haka ɗan sake yi mu gani",kallo na na mayar kan oga da ido yayi mini nuna dana fita.




Cikin sauri na juya na fice ina faɗin"sai anjima kawai",dariya yayi inajin shi yana cewa"Allah K.A kana takura mana da yawa yanzu sai ka korar mini ita",banji amsar daya bashi ba.




Ina komawa na faɗa wanka,sai da na ɗauro alwala sannan na fito banyi kwaliyya da yawa ba,doguwar riga na saka ƴar kanti sannan na saka hijab na tada sallah.




Anan na zauna har aka yi kiran isha'i nayi tukunna na fito,a falo na sami sauran ƴan uwa na.



Tare muka ci abinci sannan muka zauna fira da ƙani na Abdul'azeez,har Rufaida ta shigo ta same mu itama nan ta zauna muka cigaba da firar tare da ita.





Ƙarfe tara da rabi waya ta,ta hau ƙara ganin me kiran yasa banyi jinkiri ba na ɗauka,cewa kawai yayi kizo ya kashe wayar.




"sis bari naje Yaya Khaleel na kira na",daga haka na ɗauki hijab ɗina na saka sannan na fice.




Da sallama na shiga yanzu babu Al'ameen sai dai su biyu a ɗakin,zama nayi a gefe bece komai ma ya tashi ya shiga bedroom be daɗe ba ya dawp hannun shi riƙe da ƙaramar laptop ƙirar Apple.




Ɗayan hannun kuma riƙe da ƙatuwar leda,miƙo mini yayi yace"tsarabar ki",kasa ɓoye murna ta nayi,ina ta godiya.



Shi kan shi abin ya bashi mamaki,da sauri nayi waje ina sauri inje in nunawa su Ummi.



Karo muka yi,da yake haske kaɗan ke wajen,da sauri na taro laptop ɗita da ta kusa faɗuwa.




Ɗagowa nayi ganin mutumin da muka yi karo yana tsaye yana kallo na,gaba na ya yanke ya faɗi,cikin rawar murya nace"Khairiyya!".




#LIKE
#SHARE
#COMMENTS


*babyn abdul maman farouk,elham da meenal*.




*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.


♥ ❤

♥♥❤
*~K'AREENATEEY~*
(K'AWATA)

(It's all about friendship)





https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/



*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


*YAN UWA MUNA KARA KIRA DA MABIYA LITTAFAN GOLDEN PEN WRITTERS ASSOCIATION DA SU KIYAYE DA WANNAN MAI CUTAR TASU DA SUNAN YANA SAIDA LITTAFAN KUNGIYARMU,TO KARYA YAKE MACUCI NE KAWAI LITTAFANMU IS FREE 1 NE KAWAI NA KUDI,KUMA DA YACE YANA BA KUNGIYARMU KUDIN REGISTER DIN DA KUKE BIYA DOMIN MU TURA MASHI SABBIN LITTAFAN MU,TO WALLAHI DUK KARYA YAKE MANA MU BAMU DA MASANIYA AKAN WANNAN B'ARNAR DA YAKE MANA SAI DAGA BAYA MUKA JI,SANNAN KUMA INA SON KUSAN NUMBER DIN SHI SABODA YANA NAN YANA SHIGA GROUPS NA MATA DA SUNAN MACE SABODA HAKA KU KIYAYE GA NUMBER DIN SHI NAN (08107707692)*




*written *✍
-by-
*Deeja one love*




*JAKADIYAR GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION👸*



Wattpad 13deeja.


Daga wannan page d'in har zuwa k'arshe sadaukarwa ne gare ki *AISHATU BABAYO* saboda kaunar da kike wa *GOLDEN PEN WRITERS* ba muda abinda zamu biya ki dashi, dan haka *K'AREENATEEY* har zuwa k'arshe ya zama naki sis kiyi yadda kike so dashi, *JAKADIYA* ta baki wannan yan shafukan har zuwa karshe, muna godiya sosai da irin kaunar da kike mana.



An karɓo daga Abu huraira Allah ya ƙara mishi yarda yace"daga manzo Allah tsira da amincin Allah sun tabbata agare shi yace"Alƙiyama ba zata tsaya ba har sai mutum ya wuce ta kabarin wani sai yace"ya kaico na inama nine a cikin kabarin nan".




Manzon Allah ya kuma cewa a wani hadisi"ku dinga yawaita tuna me yanke jin daɗi itace mutuwa".




Ƴan uwa muna tuna mutuwa kuwa???,yawan kuɗi manya-manyan mota da kuma dogayen gidaje sun mantar damu,Abinda muka fi tunani yanzu shine yadda zamu tara kuɗi mu sayi gidaje manya mu hau manyan motoci mu riƙe manya manyan waya.



Ko kin san duk abinda kika aikata za'a tambaye ki ranar ƙiyama da wanda kika bayyana da wanda kika ɓoye dan haka shin ƴar uwa ɗan uwa kin/ka shirya amsa tambayoyin da za'a miki???.




Allah kasa mu dace Ameen.



*_23_*




Laptop ɗin dake hannu na take bi da kallo,ni kuwa ɗan fuskewa nayi domin wucewa,hannu tasa zata fuzgo ta tana faɗin"kwaɗayayyiya kawai,daga dawowar shi anje an ƙwaƙule shi waya sani ma ko sato mishi kika yi".





Taɓ ina zan ga samu inga rashi me raba ni da laptop ɗin nan ai sai ya shirya,hannu na na ɗaura saman nata sannan na fincike.




Shafa laptop ɗin nayi sannan nace"ai wallahi baki isa ki amshi wannan ba,sannan da kika ce kwaɗayayya ai gwara kwaɗayayya da kuma me hassada,ki sani bafa tsoran ki nake ji ba da yasa nake ƙyale ki kawai dai ina kauda kai ne",na ƙarasa murya ta na rawa,to abinda ba'a saba ba.





Juyawa nayi itama ta ƙara biyo ni,ta janyo ni,cikin ƙarfin halin dana ɗan tattaro na juyo na wanke ta da mari.




Da bango na haɗata na matse,jin zafi yasa ta ƙwala ƙara tana kiran"wayyo Momma",jin haka banyi la'akari da cewa akwai nisa tsakanin nan da part ɗin su ba tunda muna part ɗin su Yaya Khaleel ne amma daga bakin ƙofa,ai sakin ta nayi na fita a sittin ko waiwaiye babu domin kuwa ban shirya rabuwa da laptop ɗina ba na kuma san idan ta kira Momma shikenan.




Yaya Khaleel daya fito ya daka mata tsawa yace"ke baki da hankali ne kike mini ihu,uban me aka yi miki?".




Ta san idan yaji meya faru ƙaniyar ta zai ci yasa tace"Yaya bugewa nayi fa",ƙara haɗe rai yayi yace"me kika zo yi",cikin rawar jiki tace"Momma na kiran ka",hanyar waje ya nuna mata.




Cikin matuƙar jin haushi ta fito daga part ɗin,sauri take taje ta faɗawa Momma meya faru.




Tana shiga ta saki kuka,Momma tace"lafiya ba dai dukan ki yayi ba",zama tayi sannan tace"Momma ba.....",ranar da yayi mata kashedi ta tuna da sauri taja bakin ta ta tsuke.





Momma tace"ina tambayar ki meya faru ne?",zunɓuro baki tayi tace"bugewa nayi ai ni",Momma ta janyo ta jikin ta tace"ayya sannu ina Khaleel ɗin".




"na faɗa mishi bece komai ba",kan Momma tace komai yayi sallama ya shigo,bayan shi Yaya Abdus-samad ne.




A ƙasa suka zauna sannan suka gaidhe da ita,yace"Momma gani",kallon ta ta mayar kan Yaya Abdus-samad,miƙewa yayi kawai ya fita Khairiyya ta bishi da sauri.




Bakin harabar part ɗin ya tsaya,itama tsayawa tayi kusa dashi tace"Yaya ina wuni",kallon ta yayi sannan ya taɓe baki yace"lafiya,bana ce ki fita harkar Khaleel da Juwairiyya kin ƙi ko".




Saukar da kanta ƙasa tayi tace"ai ban yi nata komai ba",kallon ta yayi up and down sannan yace"waye ya zuba mata ruwan zafu da manja,kina ganin dan bana nan ban san meke faruwa bane,kin ga sai da na miki warning amma baki ji ba,wallahi sai na saɓa miki idan hakan ya kuma faruwa tunda ke bakya jin magana,sannan duk ranar da kika kuma ɗauko ƙafar ki kamar ta sauro kika biyo ni sai na karya ta,wawiya kawai,idan kin so kije ki faɗawa maman ki wannan matsalar ki ne ki sani time yana zuwa da zan kama ki a hannu",daga haka ya juya ya bar wajen.



Sai da ya ɓace ta taɓe baki tace"aikin banza aikin wofi wai ni za'a faɗawa ƴan uwan taka shi nan wai ya san daɗin ƴar uwar shi amma ni Yaya Khaleel da yake beda wayo shi baya kishi na".




Daga haka ta juya itama tana faman banbami kamar mahaukaciya sabuwar kamu.





"abinda nake faɗa maka bakya ji Khaleel na faɗa maka ka dena yiwa wancan jikar karuwan hidima amma kaƙi ka dena".




Haka tayi mishi faɗa sosai tana aiban tani da Ummi shi dai bece mata komai ba sai da tayi shiru dan kanta sannan yace"kiyi haƙuri Ummi ba zan kuma ba,daga haka ya miƙe ya fice.




Ni kuwa ina can muna murna sai fama dangwale-dangwale muke yi,Rufaida tace"amma dai Allah yayiwa yaya Khaleel albarka gaskiya naji daɗi sosai wallahi,kai mun zama manyan gayu".




"ai kedai Aunty Rufaida selfie zan dinga kashewa idan na ɗauke ta,kinga kowa ya ganta a hannu na zai san na girma ga games da sauran app da zamu sauke",Abdul'azeez ya faɗa.




"kai ta karatu ce bata game ba,ni da zan wuce school ai ba kullum zaka dinga ganin ta ba".



Ummi da sai yanzu ta saka baki tace"baban ku fa be yarda ki zauna a hostel ba".




Cikin sauri nace"Ummi kin yi mishi magana ne?",Murmushi tayi tace"Yayan ku Khaleel ya faɗa mishi shine yace be yarda ba".




Cewa nayi "shikenan Allah yasa hakan shi yafi",duka suka amsa da ameen.





Ranar kam da ƙyar nayi barci tsabar murna,haƙiƙa na san cewa Yaya Khaleel ya tsaya mini akan abubuwa da dama.





Washe gari ni na haɗa musu abin kari,kunun gyaɗa da doya da ƙwai,sai indomie da tea.




Yaya Al'ameen kuwa santi ya dinga yi,ni kuwa dariya na dinga yi,oga kuwa idanun shi yana kaina.




Ƙara gyara hijab ɗina nayi na maida hankali na kan Yaya Al'ameen da yake bani labarin garin su.



Babu abinda nake sai murmushi,sosai nake jin daɗin firar cikin farin ciki nace"Yaya ni kuwa ina son zuwa garin nan".




Ƙara kurɓar kunun yayi sannan yace"kada ki damu idan anyi bikin mu can zamu tafi",jin haka yasa Yaya Khaleel ƙwarewa.




Da sauri muka juya tari yake sosai,cikin sauri na ɗauko ruwa na miƙa mishi ina mishi sannu,wata uwar harara ya balla mini.




Be amshi ruwan ba ya miƙe maida kallon shi yayi kan Al'ameen yace"tashi mu wuce",Yaya Abdus-samad dama shi yaci indomien ya miƙe shima.




Kallo na yayi fuska ya ɗaure yace"ki gyara mini ɗakin kan ki tafi",ƙasa nayi da kai su kuma suka fice.




Bin bayan shi nayi da kallo,wato yaya Khaleel duk kayan daya saka kyau suke mishi.



Yanzun ma jikin shi sanye da jar riga da farin wando ƙananan kaya,Rufaida na makaranta balle na kira ta tazo ta taya ni.




Ina shiga bedroom naji ƙarar waya,kallon wayar tayi dake kan mirror,matsawa nayi kusa *friendy* abinda ke jikin wayar kenan.




Ina zuwa ma ta katse,juyawa nayi na fara aikin dakw gaba na,kan na gama wanke bathroom ma an kira ya kai sau uku.



Ina fitowa na fara gyaran gado aka sake kira,cikin jin haushi naje na ɗaga"hello Hubby na",can ɓangaren aka faɗa.




A cikin zuciya ta na maimata wai Hubby na,cikin jin haushi nace"wai wacece".



Da sauri Zuby ta miƙe tana faɗin"ke wacece a ina kika sami wayar nan",taɓe baki nayi nace"ke dai wacece".




"ni ce wacce me wayar zai aura",wani ɗaci naji a raina,dariya nayi kan nace"Allah sarki ashe wacce yake faɗa mini cewa ta nace mishi ne,to yanzu ya akayi gashi ya shiga wanka".




Da mamaki Zuby tace'wanka kuma?",dariya nayi nace"wanka mana wankan tsarki ko baki san shi bane,kin san na kai macen da za'a yi wankan tsarki a kaina,ko baki sani bane".




Daka tsawa Zuby tayi tace"Wallahi ƙarya ne soja na ni kaɗai yake so,kuma ni kaɗaice wacce zai aura".




Cikin tsiwar da ban san ma ina na samo ta ba nace"au Allah ɓoye miki yayi kan cewa yana da mata,ko zaki ce mini baki taɓa jin sunan Juwairiyya a bakin shi bane to ai nice uwar gida sarautar mata,dan na san dai duk inda yake za kiji suna na a bakin shi.....".




Kamar ance kalli madubi yana tsaye a jikin ƙofa ya rungume hannayen shi saman ƙirjin shi,ya zubawa baya na ido.




Wani mugun yawo na haɗiye,jiki na ya fara rawa ina jin yarinyar tana faman ɗura mini zagi tama faɗin ƙarya nake karuwa ce ni,ina nake ta tata ma.




Ji nake kamar na saki fitsari,shi kuwa be bar kallo na ba haka be motsa ba,runtse idanu nayi ina fatan Allah yasa mafarki nake.


Cikin sanyin jiki na juyo ina fatan ya kasance mafarki ne ba gaskiya bane.



Shi kuwa har ya shiga mota ya tuna ya manta wayar shi abinda ya sashi dawowa kenan daga farkon wayar har ƙarshe yana tsaye yana ji.





Mamakin yaushe baki na ya buɗe yake yi,ya rasa me yasa idan naga macen da yake da alaƙa dashi nake samin ƙarfin da ƙwarin gwiwa amma a sauran al'amura kuwa bana iya taɓuka komai.




Ita kuwa Zuby sai faman zuba bala'i take,ni bata san halin da nake ciki yafi masifar da take yi ba.



Takowa ya fara yi zuwa inda nake,nama kasa motsi banda jiki na dake faman rawa kamar mazari.




Sai da ya matso daf da fuska ta,kamar me raɗa yace"kin raina ni ko?",girgiza kai nayi gumi duk ya rufe ni.




"wankan tsarki,uwar gida,Sunna duk meya kawo wannan",girgiza kai nayi,hannun shi ya ɗaga da sauri na runtse idanu.




Ina jiran naji ya sauke mini mari,amma sai naji akasin haka,saukar kiss naji saman lips ɗina da sauri na buɗe idanu,hannu yasa ya shafa gefen fuska ta sannan ya zare wayar daga kunne na ya juya ya fice.




Nafi minti goma ina tsaye yadda ya barni sannan na sami damar motsawa,zama nayi bakin bed ɗin shi.




Cikin sauri kuma na miƙe,hannu nasa na goge saman lips ɗina ina faɗin"astaghfurullah wai shi Yaya kamar be san abinda yake yi babu kyau ba.




Zuby tayi ihu sannan ta jefar da waya,kan gado ta faɗa tana fashewa da kuka,kamar tayi tsuntsuwa taje zaria haka take ji.




"lallai sai na wulaƙanta rayuwar ki,sai na zama ajalin ki sai kowa ya tsane ki,Allah ya isa shegiya ƴar iska",zage zage ta cigaba kamar mahaukaciya.




Ni kuwa sauri nayi na gama gyaran ɗakin dan gani nake kamar zai dawo yayi mini duka.




Shi kuwa tunowa yake da yadda take faɗan magan-ganun yana kuma mamakin ta,tuno wacce suka haɗu a republic yayi,yayi murmushi yana shafa gashi kan shi.




Al'ameen yace'"ya dai Yayan mu ko an baka Raheela ne",yayi dariya yace"fiye da haka dai".



Al'ameen ya kwashe da dariya yaya Abdus-samad kuwa murmushi yayi kawai bece komai ba.




Washe gari suka ɗauki hanyar borno hakan yasa ko haɗuwa bamu yi ba,tafiyar tasu ma a wajen Rufaida naji.




Addu'a nayi musu daga inda nake na san ko ina addu'a to addu'a ce kuma Allah zai amsa.




Yaya Khaleel kuwa tunda ya kira Raheela bata ɗaga ba ya ƙyale ta,ita kuwa ta kasa manta wankan tsarki ne 😂.



Kwanki fa tafiya duke yi gashi yanzu har mun cinye hutun mu,yau na shirya naje nayi registration ban kama ɗaki ba dan na san Baba ya hana.





Haka ranar litinin zamu fara ɗaukar darasi,Wanda yayi dai dai da saura kwanaki hamsin da shida bikin su Rufaida.





Haka kuma saura kwana ashirin a yaye su Rufaida daga school of nurse data shiga,Auxillary na wata shida.





Shirye shiryen zuwa makaranta duka nayi shi,su Abdul'azeez kuma saura kwana Arba'in cif su fara jarabawar wa'ec.




Yanzu na san abubuwa da yawa a system tunda Aliyu yana koya mini dan abinda yake karanta kenan.




Har graphics sai da ya koya mini kuma na iya babu laifi,wanda hakan ina jin daɗin shi sosai.




Bayan sallar isha'i,ina zaune na saka sim a system ɗin ina chat kuma ina karatu haka sama sama.




Call ya fara shigowa,ganin me kiran yasa na tsaya ina kallon system ɗin dan tunda suka koma bamu yi waya ba.




Shi kuwa suna komawa suka fara shirye shiryen tafiya Abuja inda za'a rantsar da sojojin da suka horar wa'inda zasu tunga kula da shugaban ƙasa.




Sosai aka yaba musu har sai da aka bashi rank ta ɓangaren horarwa,anan ne ya kira raheela yace mata gashi a Abuja ta faɗa mishi makarantar da take yazo.





Nan fa ta fara kame-kame dan bata san da tafiyar tasu ba dan Baban ta baya gida yana kaduna daga can kuma ya wuce.



Cikin ɓacin rai yace"Raheela na gaji da ƙaryar da kike mini,a duk lokacin dana ce mu haɗu sai kin kawo abinda zaki kare kan ki dashi,to ki sani daga yau kada ki kuma nema na har sai ranar da kika shirya haɗuwar mu"yana faɗin haka ya kashe wayar shi.




Hankalin Zuby ya tashi domin ta san dabarar ta ta ƙare,daya ta samu ya sauko akan ƙin ɗaga wayar shi da bata yi ba bayan sun gama cacar baki da Juwairiyya a waya.




Duk kiran da take mishi yaƙi ɗauka,hakan kuma tada mata da hankali dan haka ta kasa sukuni kuka kuwa tayi shi kamar me.



Gashi Zuly bata nan ta tafi dubai ita da saurayin ta,ga Fa'iz shima ya koma ga Daddyn ta baya nan.





Duk ta rame ta bushe,gaba ɗaya hankalin ta ya tashi ji take kamar ta bayyana mishi kan ta amma ta san abu ne me wuya.




Shi kuwa yana zaune ne sai ya buɗe data,messages suka dinga shigowa wasu ya buɗe wasu kuma be buɗewa.



Duba dpn ta yayi hoton Abdul'azeez ne da Rufaida,yana dubawa ya ganta online kamar yayi mata magana sai ya tuna tana son video call hakan yasa kawai ya yanke shawarar kiran ta.




Clicking answer nayi,yana zaune a kan kujera ya jigina,jikin shi sanye da singlet wanda ya nuna hutawa yake yi a gida kenan.




Dariya nayi baki buɗe ,shima dariya yayi yace"to rufe bakin mana",ƙasa nayi da kai ina murmushi.




"Yaya barka da dare,ya aiki?",fuske ya ɗaure yace"haka ake gasiuwa a zaria",girgiza kai nayi nace"yi haƙuri yaya ina wuni".




"ys makaranta",na bashi amsa da"yau naje nayi registration ma,zamu koma ramar litinin",Allah ya kaimu",na amsa da ameen





"zaki je ki rame ko?",kallon kaina nayi nace"ai dama banda ƙiba fa",amma ai kinfi kyau a haka".kallon shi nayi kamar bashi yayi maganar ba.




Ajiyar zuciya yayi yace"ke bakya kiran mutane ko,sai dai a kira ki",shiru nayi,can yace"bye sai da safe".



Da sauri nace"yaya ka gaishe da Al'ameen",Murmushi yayi yace"bayan kin ƙi ki kuma turo mishi da hoto nan ki,haka yace wai ya manta daya zo be amsa ba".




"to ka bani number ɗin shi sai na tura mishi",girgiza kai yayi yace"a'a sai dai ki turo mini dashi",daga haka ya katse kiran.



Komawa nayi na kwanta ina mamakin halin shi idan yaso kuyi ta fira idan be so ba kuma ys ɗaure fuska,nayi dariya dana tuna wai *Rambo* inji Yaya Al'ameen,kuma fa sunan ya dace dashi.




Yau major Aliyu ya dawo daga india,Khaleel yaje ya ɗauko shi daga airport,mutum me karamci da kuma mutunci.




Har gida ya kawo shi,Zuby ta fito da gudu ta rungume mahaifin ta,haka kawai taji hawaye zubo mata.




Kuka ta fashe dashi ko zata sami sauƙi,ya ɗago ta yace"baby na meya same ki?",kai ta girgiza tace"Daddy i missed you".




Ya shafa kanta yace"oh baby ai gani na dawo ko,kiyi shiru",Khaleel dake kallon su ya taɓe baki kawai.



Gida suka shiga,shi kuma ya biyo su da jakar major ɗin,a falo suka zauna,Major yace"baby zauna ki jira ni bari na shiga nayi wanka na fito",ya maida kallon shi kan Khaleel yace"K.A ka jira kaima".




Yes sir ya faɗa yana sara mishi,sai da ya haye sama sannan ya zauna,ɗagowa tayi ta kalle shi kamar bema san da zaman ta a wajen ba.




Juyar da kai yayi yana danna wayar shi,maida hankalin ta tayi kan plasma ɗin ɗake manne a jikin bango.





Ƙarar wayar ta taji,kallon wayar tayi dake kan center table,idanu ta zaro ganin me kiran,satar kallon shi tayi shima dai wayar yake kallo.




Mamaki ɗauke a fudkar shi ganin number ɗin shi ɓaro-ɓaro akan screen ɗin anyi

1 Comments On KAREENATEEY
avatar
hauwa-8-2

1 year ago

Reply

Mashaa Allah

Please Login or Register in order to submit comment