Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tadda ta,Rufaida ta dafa ta tace"haba khairiyya ƴar uwar ki ce fa,kin kasa taya ta murna wannan baƙin cikin har ina".





Idanun ta yayi ja sosai,ta kasa ma yin magana,Rufaida tayi wani munafikin murmushi kafin tace"kin gani sister dama nace miki zaki cinye yaya Khaleel akan gasar ku ta cewa Khairiyya ba zata iya taya ki murna ba shi kuma yace zaki iya,yanzu kinga canza wayar ki da kuma siya miki laptop ya tabbata".




Ai sakin baki da hanci nayi ina kallon ta,ita kuwa Khairiyya kasa haɗiye kukan ta tayi hakan yasa ta fashe da kuka a wajen.





Girgiza ma Rufaida kai nayi nace"a'a Rufaida bana son",tara ta tayi tace"na sani rabin raina bakya son Hp ƙirar Apple kike so,ai naji kina waya dashi ɗazu".




Wani mugun yawo na haɗiye idanu na ya kawo ruwa,Momma dake bayan mu tace"me kuke mata ne?".




Rufaida tace"Momma nasiha muke mata shine take kuka,kin san har yanzu a zamanin nan akwai masu ragowar imani,amma yanzu tunda kin zo bari mu ƙarasa daga ciki mu cigaba da murnar da muke ai samun nasara a rayuwa yana daɗi,kuma fa ta mahassada kake gane ci gaban ka,momma shi yasa koda yaushe nake Alfahari da mahassadi na koba haka ba?,muje rabin raina daba dan baba malam ba ai yau dj zamu sha a gidan masoya suyi rawa maƙiya kuma suyi kuka,Khairiyya ban san wanne zata yi ba,kuka ko rawa",ta kalle ta.




Banza tayi da ita,murmushi tayi sannan ta kalli Momma tace"Momma ke dai kin manya ta da rawa amma son samu ne kiyi kuka saboda shi komai tsufan ka kana yin shi",daga haka taja hannu na wacce ni a lokacin ban ma san wace duniya nake ba.






Yau zasu je training kaduna hakan yasa yake ta faman shirin shi,duk da yana murna amma kuma yaso ace zaria zasu je.




Cikin complete uniform yake,Al'ameen da Yaya Abdus-samad suka na take mishi baya,sai bayan su wasu sajojin.





Mota wani ya buɗe musu suka shiga duka su ukun,sannan drivern yaja motar,bsbu nisa suka isa gidan.




Hannun shi riƙe da wata takarda,shi kaɗai ya shiga cikin gidan,a zaune ya same su akan table zasu yi breakfast.




Sara mishi yayi sannan ya gaida shi,cike da farin ciki ya amsa mishi.,miƙa mishi takardar yayi,kasancewar ya san ta meye kawai ya amsa.




Ƙara sara mishi yayi sannan ya juya,Zuby dake zaune tayi saurin mikewa tabi bayan shi,a bakin ƙofa ta tadda shi.





"heys",tsayawa yayi ya juyo ganin itace yaja wani dogon tsaki sannan ya juya,cikin ɗaga murya tace"Allah ya kiyaye hanya",ɗan juyowa yayi sannan ya buɗe mota ya shiga.






Sun fara tafiya sai ga saƙo ya shigo daga Raheela na fatan sauka lafiya,da mamaki yake kallon message ɗin taya akayi ta san zai yi tafiya.




Kiran ta yayi shi yama manta da ita kwana biyu,cikin sauri ta ɗaga,bayan sun gaisa yace"sorry fa ranar nan wallahi mun ɗan jima muna waya da ƙanwa ta ne,sannan kuma muna gamawa nayi barci washe gari kuma ayyuka sun mini yawa".





"babu komai,yanzu dai ya hanya?",gyara zama yayi sannan yace"amm yauwa yanzu dai ya akayi ma kika san zan yi tafiya?".




Dafa ƙirjin ta tayi sannan tace"ina zaune kawai zuciya ta ta fara bugawa",waskewa yayi da maganar yace"yanzu dai ya school".




"gata nan babu daɗi,yanzu ma zan shiga ciki",Allah ya bada sa'a",ya faɗa sai da ta ɗan dara sannan tace"Ameen".





Daga haka ya katse wayar,Yaya Al'ameen yace"wai ita kuma wannan maƙale matan fa?",kallon shi yaya Khaleel yayi har zai yi magana sai kuma ya fasa.




Shima sanin hali be sake ce mishi komai ba,sun yi tafiya ta wajen kilo mita ɗari uku sannan yace"a social media muka haɗu sai muke gaisawar mutunci",taɓe baki Yaya Al'ameen ɗin yayi kawai dama yaya Abdus-samad bece komai ba.





Ta kano suka bi hakan yasa suka tsaya a kanon,sai da suka yi sallar azahar da la'asar sannan suka kuma ɗaukar hanya.





Sun iso zaria wajen biyar da rabi da kallo yabi garin ji yake kamar su tsaya amma babu dama dan a hakan ma sai faman kiran su ake yi.




Wanda za'a kwashe akai wajen shugaban ƙasa su ake so suje su bawa horo,yaso ace a zaria depot za'a yi amma ba hakan bane.




Ajiyar zuciya ya sauke ganin an wuce garin,"Juwairiyyyyyyyyya",ya faɗa yana jan sunan tare da lumshe idanu,domin yadda zuciyar shi ke bugawa da sauri.



Al'ameen yace"ka bani ita aure ne na faɗawa Baffa da Inna",wani banzan kallo yayi mishi sannan yace"wallahi zan fasa bakin ka wata rana waye zai ɗauki ƙanwar shi ya baka".





"sanin ba za'a banin bane yasa ai nake roƙon ka bani taka ƙanwar,kaga shikenan baki a rufe babu wanda yaji ba wanda ya gani,tunda itama dai naga tana sona".





Saukar naushi yaji a bakin shi,da sauri ya dafe wajen yaya Abdus-samad ya fashe da dariya.




"kai-kai-kai zaka nakasawa Juwairiyya miji ne?",ya buɗe baki da niyar yi mishi magana wayar shi tayi ƙara.




Hoton ta ya bayyana akai,tsayawa yayi yana kallon hoton,Yaya Al'ameen ya kai hannu zai amsa yana faɗin"Allah sarki soyayyar gaskiya kenan har taji a jikin ta an daki masoyin ta".





Kallon shi yayi da sauri sannan ya kalli wayar data katse,janye idanun shi yayi sannan ya fara ƙoƙarin kira.




Ni kuwa na maida kallo na kan Rufaida wacce dama ita ta tilasta mini akan na kira shi na faɗa mishi naci jarabawa.




Na buɗe baki zan yi magana wayar tayi ƙara,da sauri na ɗaga,"Yaya ina wuni",a taƙaice ya amsa da"lafiya".





"amm dama zance maka ne naci jarabawa ta",murmushi yayi wanda sai da na jiyo sautin shi hakan ya saka har cikin zuciya ta naji daɗi domin wanda yake ƙoƙari akan abin yaji daɗi.




Yace"Allah ya taimaka,ga saurayin ki ma yana taya ki murna",nace"na gode sosai",shiru yayi kafin yace"yanzu muka wuce zaria sai naji kamar na shigo".





"dan Allah Yaya ku ƙaraso,dan Allah koda minti goma kuyi,dan Aƙƙah kaji",murmushi yayi yace"saboda me?".




Babu wani tantama nace"kawai ina so na ganka ne,kwana biyu fa baka zo ba,dan Allah kaji",har ran shi sai da yaji wani abu.



Ajiyar zuciya yayi sannan yace"naso ace zan sami shigowar ko dan ke amma hakan ba zai yiwu ba,sai dai nayi miki Alƙawarin nan da sati na sama ki saurari zuwan mu".




Murna nayi sosai ina sambaɗa mishi Addu'a kafin ya katse wayar,Rufaida da ta zuba mana idanu tayi dariya tace"wallahi wasa-wasa ku fa wasu layla da majnoon ne a gefe".




Bance da ita komai ba dan na san magana take nema,sannan kuma zuwan Ummi wajen ya saka ni yin shiru.




Khairiyya kuwa tana ganin mun shige part ɗin mu ta zuba da gudu zuwa nasu part ɗin,Momma da har lokacin take haɗa maganar da Rufaida ta faɗa mata,ta bi bayan Khairiyya da kallo.




Hajiya da akayi komai a gaban ta,tayi shewa tace"Ai dama haka Rayuwa take kai Allah ka raba mu da girman kawai".




Cikin fushi Momma tace"wallahi ki fita harkata idan ba haka ba zan wulakan taki",Hajiya ta kuma shewa tace"wallahi girma ya faɗi yara na cikin ka su faɗa maka magana".





"ke kike faɗin haka komai ma ya faru ai da saka hannun ki munafika sheɗan kawai,kuma ki sank daga su har ke sai nayi maganin ku".




"ta Allah ba taki ba,yarinya ta tafi ƙarfin ki,idan ke sammako kika yi ni a hanya na kwana",Umma ta faɗa tana huci.




Nan fa gida ya kuma kacamewa Aunty dai da Ummi babu wanda yayi magana,Baba malam ya shigo cikin fushi yace"Wallahi kun kyauta,Halima(Umma)da ke kaltume(Hajiya)yanzu ko dan auren ta da yaya na ai kwa raga mata wani abun amma kuka zauna kuna cin mutuncin ta".





Hajiya tace"dakata malam bafa mu muka fara ba yaran ka suka fara dan ƴar ka Juwairiyya da Rufaida sune suka zage ta tas".




Baba malam cikin mamaki yace"Juwairiyya kuma",Umma tace"tabbas dan ita tafi zagin nata ma ita dai Rufaida tace Allah ya kyauta".





"meya haɗa su",nan aka kwashe ƙarya da gaskiya aka faɗa mishi abin mamaki duk a kaina wanda ko ƙala bance ba,Ummi kuma tana ji bata ce komai ba.




Daga haka ya fasa taron kowa da abinda yake faɗa,masu jin daɗi suna yi masu baƙin ciki suna yi.





#LIKE
#SHARE
#COMMENTS

*Babyn Abdul Maman Farouk,Elham da Meenal*




*ƳAR MUTAN ZAZZAU*


♥ ❤

♥♥❤
*~K'AREENATEEY~*
(K'AWATA)

(It's all about friendship)





https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/



*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


*YAN UWA MUNA KARA KIRA DA MABIYA LITTAFAN GOLDEN PEN WRITTERS ASSOCIATION DA SU KIYAYE DA WANNAN MAI CUTAR TASU DA SUNAN YANA SAIDA LITTAFAN KUNGIYARMU,TO KARYA YAKE MACUCI NE KAWAI LITTAFANMU IS FREE 1 NE KAWAI NA KUDI,KUMA DA YACE YANA BA KUNGIYARMU KUDIN REGISTER DIN DA KUKE BIYA DOMIN MU TURA MASHI SABBIN LITTAFAN MU,TO WALLAHI DUK KARYA YAKE MANA MU BAMU DA MASANIYA AKAN WANNAN B'ARNAR DA YAKE MANA SAI DAGA BAYA MUKA JI,SANNAN KUMA INA SON KUSAN NUMBER DIN SHI SABODA YANA NAN YANA SHIGA GROUPS NA MATA DA SUNAN MACE SABODA HAKA KU KIYAYE GA NUMBER DIN SHI NAN (08107707692)*




*written *✍
-by-
*Deeja one love*




*JAKADIYAR GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION👸*



Wattpad 13deeja.


Daga wannan page d'in har zuwa k'arshe sadaukarwa ne gare ki *AISHATU BABAYO* saboda kaunar da kike wa *GOLDEN PEN WRITERS* ba muda abinda zamu biya ki dashi, dan haka *K'AREENATEEY* har zuwa k'arshe ya zama naki sis kiyi yadda kike so dashi, *JAKADIYA* ta baki wannan yan shafukan har zuwa karshe, muna godiya sosai da irin kaunar da kike mana.



*ALKUNYA*
haƙiƙa kunya wata abace me kyau kuma ado ce ga mace,ki sani babu wayewa akan rashin kunya,meye ribar ki dan kin saka gyale kin taho hanya kina cin abinci kuma kin tsaya tsakiyar titi kina cacar baki da maza???.





Meye wayewa a ciki kin sanya gyale an Figo ki a bayan mashin ko kuma kunyi two parking bayan wani ƙato ya karkace yana watsa gudu a tsakiyar titi???



Ki sani abu da yake a buɗe shi yafi araha,sannan kuma ko ɗan iska yana nemawa ƴaƴan shi mata ta gari ne.



Babu namijin da zai aure ki bayan kun gama yawon ta zubar ya shafa ki ya kuma tsotse ki ya bawa abokan shi labari kuma.


A idanun shi a banza kike a idanun abokan shi a banza kike amma duk baki san da haka ba kin biyo hanya kuma kina sisi.



Gaskiya zan faɗa miki sai dai kin so ki ƙi yarda amma ki sani wallahi duk abinda mutum ya taɓa shi ko kuma ya san shi a waje ba zai yi wani ɗokin shi ba,kin bashi kanki a waje kina tunanin zai wani martaba ki ne idan kuka yi aure??



Manzon Allah yace"kunya tana daga cikin imani".


Sannan ya kuma cewa"idan baka jin kuya to ka aikata abinda kaso".



Wai saboda lalacewa yanzu har abin alfahari hakan ya zama,wai na fiki rashin kunya,ma'azallah!.


Allah kasa mu dace.



*mama na naga yaya ta zance ko ƙanwa ta ubangiji Allah ya dafa mata a karatun ta da sauran Al'amuran ta,Allah ya kiyaye ta da kiyayewar shi da ita da sauran ƴan uwan ta*.



*Aishatu babayo ki ƙara haƙuri haƙiƙa haihuwa ba'a siyan ta da kuɗi ubangiji ke bada ita shekara goma sha ɗaya ba kwana goma sha ɗaya bane,na san da ciwo hakan amma ki ƙara haƙuri ubangiji na sane dake insha Allah rabon ki na kusa*.



*Ya Allah muna tawassali da sunayen ka kyawawa da siffofin ka tsarkaka ya Allah ga baiwar ka nan Allah kai kake bada haihuwa ga wanda kaso Allah kai ka san dai-dai ka dube ta,Allah ka zaɓa mata wanda yafi Alkhairi Antal Razzaqu wa'antal Raheemu*.



*da ita da duk wanda Allah be basu haihuwa Muna musu Addu'ar Allah ya basu suma nasu wanda zasu ji ƙan su,Ameen ya Allah,dan Allah fans ku saka ta da sauran irin ta a addu'o'in ku,hakan shine kuka biya ni,kuma shine cinikin nawa novel din pls ku taya mu da Addu'a,idan kika yi na yadda ki turawa wata itama ta turawa wata novel ɗin duka na yarda,amma idan bakiyi ba to ki sani ke ba abin zargi bace sai dai kuma Allah zai iya jarabtar ki da fin wanda ya jarabce ta dan haka nawa roqon kenan*.



*_21_*



Muna zaune sai ga saƙon kira daga baba malam,nayi mamaki sosai amma haka na miƙe muka tafi.




Wannan karon ɗakin hajiya aka haɗu,kusan duk ƴan gidan mu suna wajen,kusa dashi naje na tsuguna Rufaida kuma tana gefe.





"Baba ina wun....... "ban ƙarasa ba naji saukar mari,da mamaki nake kallon shi ganin yadda fuskar shi ke ɗaure ya sa na sunkuyar da kai na ƙasa.




Nuna ni yayi cikin fushi yace"yaushe kika zama haka ban sani ba,ashe kema kin fara lalacewa ashe tarbiyar da aka baki kenan,ke yanzu kin fitsare ƙafar ki,kenan zaki iya zagi na tunda zaki zagi matar yaya na".




Girgiza kai kawai nake yi hawaye yana zuba daga idanu na,kallo na na mayar kan Ummi fuskar ta bata nuna komai ba,hakan yasa na kuma saukar da kai na ƙasa.




Sosai ya rufe ni da faɗa,ƴan gidan mu kuma an sami abinda ake so,cikin daka tsawa yace"me tayi muki,meya faru tsakanin ku?".




Aifa nan ɗaya,ina da haƙuri sosai amma idan aka kaini bango ban iya zuciya ba ga kafiya kamar me,wato bema tambayi meya faru ba ya fara faɗa kenan a gaban ƴan gidan mu wanda hakan dama suke so,ban so banyi laifi ba a hukunta ni.




Ƙara maimaita tambayar shi yayi ni kuma nayi shiru,ya san ba zan amsa ba hakan ya ƙara baƙan ta mishi rai dan haka ya ɗauko bulala.




Ina yadda ya barni haka ya dinga zuba mini bulalar ina tsugunne a wajen,ko motsi kuma babu hawaye.





Ga ƴan gidan an rasa me yin karar amsa ta ko ya bashi haƙuri dan Yaya Khaleed baya nan shi dama.




Ummi kuma ta kasa magana kawaici,sai dai yanzu daka kalle ta ka san tana cikin damuwa,Hajiya kuwa da Umma an gama faranta ran su haka Khairiyya da Momma.




Abdul'azeez kuwa kuka yake shida Rufaida,ganin dukan ba zai tsaya ba yasa Rufaida zuwa ta rungume ni.




"ba zaki tashi ba sai na haɗa dake",girgiza kai tayi cikin kuka tace"wallahi baba sai dai ka haɗa dani",ganin zai kuwa haɗa da ita yasa Umma miƙewa cikin sauri ta fizge wayar tace"haba baban Abdus-samad ayi musu haƙuri".




Juyawa yayi ya kalli Ummi,ita kuwa cikin sauri ta miƙe ta bar ɗakin,Hajiya ta kwashe da dariya sannan itama ta fice.




Rufaida ta kama ni ta miƙar dani mun nufi hanyar waje na dawo da sauri ƙasa na tsugunna nace"Dan Allah baba kayi haƙuri ka yafe mini",sannan na fashe da kuka.



Juyar da fuska yayu,Rufaida ta dawo ta kama ni muka miƙe sannan tace"Baba haƙiƙa babu laifin Juwairiyya a ciki domin nice ma na faɗawa Momma magana,kuma hakan ya faru ne saboda matsanta mata da suke yi wanda hakan ke bani haushi".




Nan ta kwashe komai ta faɗa mishi,har yadda suke tozarta ni sai da ta bashi labari sannan tace"idan da wanda ya kama ta ka hukunta Baba nice domin babu abinda Juwairiyya ta taɓa cewa,sannan ina bada haƙuri akan kuskuren da nayi ba zan sake ba".



Daga haka ta riƙe ni muka fice daga ɗakin,Baba malam kuwa zama yayi yana mamakin irin abinda yarinyar take fuskan ta a cikin gidan amma ya kasa gane cewa ƙarya aka yi mata.




Miƙewa yayi da sauri ya fito,mu kuwa har mun shige part ɗin mu,shima hanyar part ɗin namu yayi.




Muna shiga babu kowa a falon dan haka ɗakin mu,muka wuce muma kawai.




Baba malam daya shigo ganin babu kowa a falon yasa ya wuce ɗakin Ummi,a zaune ya same ta,tana share hawaye.




Sallama yayi sannan ya shigo,cikin sauri ta miƙe tana faman murmushi tace"barka da zuwa Baban Abdus-samad".




Hannun ta ya riƙe cike da ƙauna yace"kiyi haƙuri nayi hukuncin da be dace ba,na manta cewa ɓangar biyu aka umarce mu da muji kafin zartar da hukunci amma ni kuma nayi amfani da ɓangare ɗaya".





Dafa hannun shi tayi tace"kada ka damu komai zai wuce sannan ka sani ƴar kace ita kana da damar da zaka hukunta ta,dan haka babu komai ya riga ya wuce".




Shi yasa yake ƙaunar Fatima saboda Allah yayi mata hankali,haƙuri da juriya ga kawaici,idan wata ce ko a fuska sai ta nuna mishi amma ita ba haka bane.




Murmushi yayi sannan yace"shirya muje wani waje",dariya tayi tace"angama yallaɓai",daga haka ta wuce kawai don ta shirya.




Ni kuwa muna shiga ɗaki rigar jiki na na cire gaba ɗaya duk shatin bulala a jiki na,bayi na shiga na ɗan gaggasa jiki na sannan na ɗauro wanka na fito.




Riga armless kalar orange na saka sannan na kwanta,Rufaida tace"dan Allah kiyi haƙuri kinji,gaskiya banji daɗin abinda ya faru ba".





Murya a dashe nace"kada ki damu,yanzu dai bari nayi barci na san zan sami sauƙi",girgiza kai tayi sannan ta miƙe ta fita.




Kaina na mayar na kwanta hawaye yana zubo mini daga idanu,wani ƙululun baƙin ciki naji a raina,kuka na fashe dashi ina tausayin kaina.





Ummi tayi sallama ta shigo,da sauri na rufe fuska ta kamar ina barci.




Ummi kuwa ganin haka ta ɗauka barcin nake da gaske dan haka kawai ta juya ta fice da sauri.




Kuka na,na cigaba wata ƙila hakan ya rage damuwar dake raina,na daɗe ina kuka a haka har barci ya ɗauke ni.





Zaune yake saman kujera fara irin ta roba ɗin nan gaban shi kuwa ƙaramin table ne saman shi kuwa glass cup ne cike da hollandia.



Sanye yake da wando kalar ruwan ƙasa jeans da kuma light green ɗin riga,waya ce kare a kunnen shi.




Abdus-samad da Al'ameen suka ƙaraso wajen zama suka yi,jikin su sanye da khaki.




"haba yanzu nufin ki inzo kaduna har in tafi ba zamu haɗu ba kenan?",Yaya Abdus-samad ya taɓe baki.





Ita kuwa Zuby dake zaune cikin mota tace"haba Hubby ai na faɗa maka na koma school".



Ajiyar zuciya yayi yace"hakane amma kuma ki mini alfarma ɗaya mana yau mu ɗan yi video call mana".




Girgiza kai tayi tace"gaskiya ba zai yiwu ba amma kuma insha Allah zuwa lokaci kaɗan zamu haɗu".




"To Allah yasa hakan,kawai ina so na ganki ne","kada ka damu zuwa lokaci kaɗan zamu haɗu,ina Juwairiyya",ta faɗa domin kauda maganar haɗuwar su.







Murmushi yayi wanda sai da taji sautin shi,zuciyar ta yayi zafi yace"tana nan,ina ji sati me zuwa ma zan shiga zarian dan na gaji ina so naje na ganta".




Haɗiye haushin ta tayi tace"wai ita kuwa ta damu da kai kamar yadda ka damu da ita?",cikin farin ciki yace"sosai ma kuwa kuma na san taji zan je zata yi murna sosai".



"hmm Allah ya taimaka"daga haka ta kashe wayar,steering motar ta daka sannan tace"sai na zama ajalin ki",daga haka ta figi motar ta fice daga gidan.





Shi kuwa ajiye wayar yayi ya kalli su Al'ameen yace"ya akayi kun gama round ɗin yau",miƙewa suka yi suka sara mishi suna faɗin"yes sir".





"okay,to sati me zuwa nake so mu gama dan mu koma ɗazu munyi waya da major yace,bikin rantsar dasu upper week ne dan haka ya kamata ace mun gama da wuri".




A tare suka kuma cewa"yes sir",miƙewa yayi da sauri Abdus-samad ya kwasar mishi wayoyin shi sannan ya biyo shi haka Al'ameen shima ya biyo bayan su.




Ummi tace"lafiya wannan take kuwa",ta faɗa tana bubbuga filon da nake kwance,da ƙyar na iya buɗe idanu.



Babu shiri na maida na rufe saboda wani azabar ciwon kai da naji,Ummi tace"ke anya kuwa lafiyan ki".




Dafa kai na kawai nayi,"Ayya sannu yanzu tadhi kiyi sallah dai kizo kici abinci sai kisha magani Allah ta sauwaƙe".




A hankali na miƙe hannu na dafe da kaina haka na dafa na shiga bayi,na daɗe tsugunne sannan na iya samu nayi alwala na fito.




Zama nayi na jigina da gadon mu a haka nayi sallar,ina idar wa Hafeeza ta shigo bayan Rufaida ce.




Abinci Hafeeza ta ajiye mini,Rufaida tace"ya jikin,ai na shigo sau uku na tarar kina barci",jinjina mata kai nayi.




Da kyar nayi loma uku na abincin wai dan ma tare da Rufaida ne,magani ta ɓallo ta bani na amsa na sha.




Sannan na koma na jingina,muna ɗan taɓa fira da ita,a haka Ummi ta shigo ta same mu,ƙarasowa tayi fuskar ta da damuwa tace"ya jikin,har kin ci abincin kenan?".






Murya a dashe nace mata"eh naci kuma na sha magani",zata kuma magana baba malam yayi sallama ya shigo.



Sai da ya zauna sannan nace mishi"barka da dare baba",da damuwa a fuskar shi yace"ya jikin,nine sila ko,kiyi haƙuri kinji komai zai wuce".




Ɗaga kai nayi nace"Baba nima kayi haƙuri da abinda ya faru",dafa kaina yayi yace"kada ki damu komai ya wuce,Allah yayi miki Albarka".



Duka muka amsa da ameen,be daɗe ba ya tashi ya fice daga ɗakin,muna haka aka kira sallar isha'i,dama da Alwala hakan yasa sallah kawai nayi na kwanta.





Har barci ya fara ɗauka ta,daman su Rufaida ganin na kwanta yasa suka fice kawai,waya ta ya ɗauki ƙara.




Janyowa nayi idanu a rufe kawai na kara a kunne,dama gashi barci na fara ga rashin lafoya hakan yasa murya ta gaba ɗaya ta canza.




Sallama nayi,Yaya Khaleel dake zaune sai da ya miƙe,lumshe idanu yayi zuciyar shi na bugawa,cikin sauri ya amsa.




Jin muryar shi yasa na buɗe idanu na,kallon screen ɗin wayar nayi tabbas shine,maidawa nayi sannan na gaishe dashi.




"meya same ki?",ya jefo mini tambaya,dafe kaina nayi da yake sara mini nace"kaina ke ciwo".




"Ayya Allah ya baki lafiya",ya faɗa cikin damuwa,murya ta a ƙasa nace"ameen na gode yaya".





Daga haka ya kashe wayar kawai,nima da yake ta kaina nake yi ban wani tsaya tunane-tunane ba na koma barci kawai.



Washe gari kuwa jiki na yayi sauƙi sosai hakan yasa ma ina gama abinda zanyi na shirya domin tafiya sabon gari.





Rufaida tace"wallahi daba dan zan shiga makaranta ba da tare zamu tafi",murmushi nayi nace"babu komai zan tafi kawai".




Na fito dai-dai bakin get ɗin gidan mu ban yi aune ba naji saukar ruwan zafi,inalillahi nake faɗi da karfi kafin na zube ƙasa.






Khairiyya ta kama ƙugu hannun ta riƙe da ƙaramin bokiti,yaya Abdul-fatah ya shigo da sauri dan yana bakin ƙofa kuma zai iya juyo abinda ke faruwa.




Daka mata tsawa yayi,Momma dake jiran hakan tayi saurin ƙarasowa tana faɗin"dakata baka san meya faru ba amma zaka zo ka wani saka baki".





Ummi kuwa da ita ma ta fito janye ni tayi kawai ta matsar dani kusa da tank ɗin gidan mu,ruwa ta tara sannan ta dinga shara mini.




Hajiya itama tace"haba ya zaki dinga dakawa ɗa na tsawa haka",Momma tace"wai ke me ɗa ko?".



Abin mamaki babu wanda ya damu da abinda ya faru akai na sai faɗan ya koma tsakanin ƴaƴa.





Ita dai Ummi ja na kawai tayi muka koma part ɗin mu,towel ta miƙo mini,amsa nayi sannan na cire kayan da yake jiki na.




Allah ya taimake ni ma ban ƙone sosai ba,kusa da fanka na zaune sai lokacin na samu hawaye ya zubo mini.




Can kuwa sai da Baban malam ya tsawatar sannan suka dakata,kowa kuma yaja nashi ɗan suka yi part ɗin shi.




Khairiyya tayi shewa tace"wallahi naso tafi haka ƙonewa amma duk da haka ai jikin ta ya faɗa mata".




Momma ta janyo ta jikin ta tace"ai kin gama mini komai ke dai Allah yayi miki Albarka",Yaya Khaleed da shigowar shi kenan ya kuma ji abinda ya faru,ya girgiza kai yana musu fatan shiriya.



*kuyi haƙuri da wannan dan Allah*




#LIƘE
#SHARE
#COMMENTS


*babyn Abdul,maman Farouk,Elham da kuma Meenal*





*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.


♥ ❤

♥♥❤
*~K'AREENATEEY~*
(K'AWATA)

(It's all about friendship)





https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/



*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


*YAN UWA MUNA KARA KIRA DA MABIYA LITTAFAN GOLDEN PEN WRITTERS ASSOCIATION DA SU KIYAYE DA WANNAN MAI CUTAR TASU DA SUNAN YANA SAIDA LITTAFAN KUNGIYARMU,TO KARYA YAKE MACUCI NE KAWAI LITTAFANMU IS FREE 1 NE KAWAI NA KUDI,KUMA DA YACE YANA BA KUNGIYARMU KUDIN REGISTER DIN DA KUKE BIYA DOMIN MU TURA MASHI SABBIN LITTAFAN MU,TO WALLAHI DUK KARYA YAKE MANA MU BAMU DA MASANIYA AKAN WANNAN B'ARNAR DA YAKE MANA SAI DAGA BAYA MUKA JI,SANNAN KUMA INA SON KUSAN NUMBER DIN SHI SABODA YANA NAN YANA SHIGA GROUPS NA MATA DA SUNAN MACE SABODA HAKA KU KIYAYE GA NUMBER DIN SHI NAN (08107707692)*




*written *✍
-by-
*Deeja one love*




*JAKADIYAR GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION👸*



Wattpad 13deeja.


Daga wannan page d'in har zuwa k'arshe sadaukarwa ne gare ki *AISHATU BABAYO* saboda kaunar da kike wa *GOLDEN PEN WRITERS* ba muda abinda zamu biya ki dashi, dan haka *K'AREENATEEY* har zuwa k'arshe

1 Comments On KAREENATEEY
avatar
hauwa-8-2

1 year ago

Reply

Mashaa Allah

Please Login or Register in order to submit comment