Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sanyaye nace"da sauƙi",wata tambayar ya sake jefo mini yace"kin sha magani".





"eh na sha"nayi ƙarya,girgiza kai yayi sannan yace"baki sha ba",shiru nayi ,ya kuma cewa"yanzu kin koyi ƙarya ko?".





Ƙasa na saukar da kaina kamar yana gani na nace"kayi haƙuri yanzu zan sha",sai anjima kawai yace mini"sannan ya kashe wayar.







Nima sauke wayar nayi ina murmushi,ɗagowa nayi muka haɗa idanu da Hajjaju,da sauri na miƙe na fice.





Ruwa na ɗebo sannan nazo nasha magani na,na kwanta ina tunanin firar mu ta yau.





Wato dama Yaya Khaleel ya iya fira haka,chat ɗin na sake shiga ina biyowa ina dariya lallai ma yaya.





Shi kuwa yana gama wayar,Al'ameen yace"da alamu an baka saƙo ka bani".




Buɗe idanun shi yayi wanda suke nuna alamar gajiya yace"waye ya bani saƙon na baka?".





"waye kuwa banda budurwa ta",harara ya aika mishi yace"wacece budurwar taka?",kashe ido ɗaya yayi yace"juwairiyya".




Kallon da Yaya Khaleel yayi mishi yasa shi jan bakin shi ya tsuke,shi kuwa Yaya Khaleel wani shegen murmushi yayi.






Jiki na yanzu Alhamdulillahi lafiya ta fara samuwa,haka kuma jarabawa muna daf da gamawa.




Idan ka ganni har ƙiba na ƙara ga haske da nayi,to na sami kwanciyar hankali,Yaya Khaleel kuwa tun ranar dana tura mishi hoto da sunan zai bawa Yaya Al'ameen bamu kuma waya ba,sai dai duk sati ya kan turo mini da credit sannan kuma account ɗin daya bani ya kan turo mini kuɗi ta can.






Ɓangaren Zuby kuwa yanzu ta fara samun kan Yaya Khaleel duk da be gane ita bace,don tace mishi tana kaduna ne sannan kuma wani hoton ta tura mishi a matsayin nata suna kuma Raheela ta raɗawa kan ta.





Ta kan kira shi su gaisa,har shima wani lokacin ya kan kira ta,sannan sukan yi chat shima sosai.




A zahiri kuwa idan suka haɗu ko gaishe dashi tayi baya amsawa,hakan yasa ma bata wani damuwa tunda ta san suna maƙale a waya.






#LIKE
#SHARE
#COMMENT


*babyn Abdul,maman Meenal,Elham da kuma Farouk*








*ƳAR MUTAN ZAZZAU*


♥ ❤

♥♥❤
*~K'AREENATEEY~*
(K'AWATA)

(It's all about friendship)


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/



*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


*YAN UWA MUNA KARA KIRA DA MABIYA LITTAFAN GOLDEN PEN WRITTERS ASSOCIATION DA SU KIYAYE DA WANNAN MAI CUTAR TASU DA SUNAN YANA SAIDA LITTAFAN KUNGIYARMU,TO KARYA YAKE MACUCI NE KAWAI LITTAFANMU IS FREE 1 NE KAWAI NA KUDI,KUMA DA YACE YANA BA KUNGIYARMU KUDIN REGISTER DIN DA KUKE BIYA DOMIN MU TURA MASHI SABBIN LITTAFAN MU,TO WALLAHI DUK KARYA YAKE MANA MU BAMU DA MASANIYA AKAN WANNAN B'ARNAR DA YAKE MANA SAI DAGA BAYA MUKA JI,SANNAN KUMA INA SON KUSAN NUMBER DIN SHI SABODA YANA NAN YANA SHIGA GROUPS NA MATA DA SUNAN MACE SABODA HAKA KU KIYAYE GA NUMBER DIN SHI NAN (08107707692)*



*written *✍
-by-
*Deeja one love*




*JAKADIYAR GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION👸*



Wattpad 13deeja.


Daga wannan page d'in har zuwa k'arshe sadaukarwa ne gare ki *AISHATU BABAYO* saboda kaunar da kike wa *GOLDEN PEN WRITERS* ba muda abinda zamu biya ki dashi, dan haka *K'AREENATEEY* har zuwa k'arshe ya zama naki sis kiyi yadda kike so dashi, *JAKADIYA* ta baki wannan yan shafukan har zuwa karshe, muna godiya sosai da irin kaunar da kike mana.



Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yace"duk wanda ya zana sura a duniya,za'a matsa mishi a lahira daya busa mishi rai,kuma ba zai iya ba".







_Saboda Allah shine me jiɓintar lamuran masu imani,amma kuma tabbas kafirai basu da me jiɓintar lamuran su_



_Lallai Allah zai sanya wa'inda suka yi imani cikin Aljanna wacce ƙoramai suke gudana a ƙarƙashin ta,wa'inda suka kafurta kuma suna rayuwa kuma suna ci kamar yadda dabbobi suke ci sannan wuta ce makomar su_



*suratul muhammad aya ta 11 da 12*.


Manzon Allah tsira da amincin Allah sun tabbata agare shi yace"wanda ya riƙi mini koma bayan Allah haƙiƙa ya jafur ta.



Haƙiƙa ina roƙon Ubangiji ta'ala Allah ya baku lafiya *YAYA HAYAT* *OUM DEEDAT* *MAMAN ASHEFAT* *AUNTYNA AUNTY NABEELA*.




*Ƙafar yawo ki sani one lurhv na son ki irin kaɗan ɗin nan*.




Bloody kai daga jin sunan ka san wannan ta jiki ce,to ai sai dai nace mun zama jini da tsoka dan ba'a zama tare sai hali ra'ayi da halayya yazo ɗaya wannan kuma duk ƙauna ce ke kawo hakan,kin wuce nace ina sonki sai dai nace ina ƙaunar ki*.

*Ebraheem Aliyu a cigaba da yaɗa shirme(if you know you know),haƙiƙa na san Allah kawai ya haɗa mu kuma ina Alfahari da ɗan zaman da muka yi*.



*idan kana so kaga haƙorin one lurhv a waje tana dariya to tana karanta firar jika da kaka ne wato firar A'ishatu babayo da kuma Imam Rukayyat,ban taɓa ganin mu'amalar dake birge ni ba kamar tasu,kuna birge ni*.



*Hajjaju a cikin masoya na kin yi zarrah ba zan iya kiman ta son da kike yiwa Ƙareenateey ba*.



*zainab bala Abubakar ke da Meera ta annabi,maman zara da sanaz da group ɗin ki ina godiya sosai*

*_19_*


Haɗa kaya na nake yi Hajjaju na gefe tana ɓare gyaɗa,kallo na tayi tace"Dan Allah ki ƙara haƙuri kinji,haƙiƙa gidan yawa zaman cikin shi sai haƙuri,sannan ki ƙara kare mutuncin kanki kinji".




Jiki a sanyaye na amsa da toh,a ƙalla sati na bakwai kenan cikin na takwas rabo na da gidan mu,sai dai muyi waya da wasu daga ciki.





Yau zan koma gidan nan dai da ake cin zarafi na ake nuna halin ko in kula dani,a zalunce ni kuma a hanani kuka.




Haƙiƙa zama na a Sabon gari yafi mini da zama a gidan mu,saboda matsalolin da nake fuskan ta.




tun da na tabbatar da yau gida zan koma gaba ɗaya sai jiki na yayi sanyi,gaba na har faɗuwa yake yi ban san me zan je na tarar ba.





Hajjaju ta dafa ni,kallon ta nayi sannan nayi ajiyar zuciya na zage ƙatuwar jaka ta,Hajjaju tace"Juwairiyya ki dena damun kanki da yawan tunani",murmushi na ƙaƙalo nace"insha Allahu na dena kinji".




Miƙewa nayi sannan na ɗauki jaka ta na fita da ita,sai da na ajiye a tsakar gida sannan na warware hijab ɗina na saka.







Sallama muka yi da ita,ta miƙo mini baƙar leda wacce ke ƙunshe da kuka da kuɓewa da daddawa tace na kaiwa Ummi.




Amsa kawai nayi,ɗari biyar ta ciro ta miƙo mini tace"kiyi kuɗin mota kinji",nace"wallahi Hajjaju ki bar kuɗin ki ina da kuɗi na a hannu wanda zai kaini gida".







A hannu na ta damƙa mini tace"ja'ira amsa ni ki tafi kin tsaya wani iyayi",Baffa dake shigowa yayi dariya yana yin sallama.




Amsawa muka yi duka,fuskar dattijon ɗauke da fara'a yace"Kice bulaguro zaki yi,zaria tayi zafi kano zaki tafi ko?".




"a'a basu iya komai ba sai gurasa,ai ni ba zanje can ba",na faɗa ina dariya,hannu na ya riƙe yace"to kije funtua mana".




"A'a ba zanje garin fura da nono ba",to ina zaki je kenan?",ya tambaya,nima na bashi amsa da cewa"ina zazzau babban gari",dariya muka yi duka.




Addu'a ya fara jero mini,ina amsawa nida Hajjaju,bayan ya gama ya miƙo mini ledar dake hannun shi yace"gashi idan kinje gida kici sannan ki sanwa Mata ta".






Maƙe kafaɗa nayi nace"ba zan bata ba,itama idan tana so ta zo ta amsa,kada nayi dare bari na tafi",Ina faɗin haka na juya domin tafiya.




Haƙiƙa zan yi kewar kakannin nawa,ji nake kamar kada na koma gidan haka dai na fito bakin titi.





Motar da zata kaini kasuwar sabon gari na hau,wato keke napep ina tafiya gaba na yana faɗuwa.






Koda muka isa kasuwar sauka nayi sai da na ɗan taka zuwa gaban kotu sannan na sami motar cikin zaria.






Muna dosar ƙofar doka gaba na ya faɗi,Addu'a duk wacce take baki na ita nake yi haka har aka zo layin mu.



Sauka nayi cikin sanyin jiki,jakar tawa ma da ƙyar na iya ɗaukar ta,harabar gidan babu kowa haka har na ƙwankwasa aka zo aka buɗe mini.






Ina shiga harabar gidan mu ido na ya sauka ana Khairiyya,kallon kallo muka yiwa juna cikin sauri ta juya.






Ajiyar zuciya na sauke sannan na nufi hanyar part ɗin mu,dai dai part ɗin Umma, Rufaida ta fito da gudu tazo ta rungume ni.





Saki na kuma tayi sannan ta juya baya,murmushi nayi sannan nace"afuwan rabin raina,kiyi haƙuri kinji".





Juyowa tayi sannan tace"naji shikenan yanzu kawo jakar na kai miki,kuma da fatan kin zo mini da tsaraba",ta ƙarasa tana amsar jakar dake hannu na.






Muna tafe muna fira har muka shiga oart ɗin mu,ummi na zaune gaban ta Alqur'ani zagaye da ita kuma Abdumalik ne da Abdulhafeez sai hafeeza,da alamu musaffah suke.





Muna yin sallama suka taso da gudu suka rungume ni suna murna,da ɗai-ɗai na bisu na rungume ina jin kewar ƴan uwan nawa.





Zama muka yi,duk da yadda Ummi ke nuna mini amma yau sai da naga farin ciki a fuskar ta,sannu da gida nayi mata sannan na gaishe da ita.




Cike da kulawa ta amsa tana faman murnushi,sosai naji daɗin hakan ganin yau Ummi tana farin ciki da gani na bayan tsayin lokaci.





Tashi muka yi nida Rufaida,Hafeeza kuma na bin bayan mu,ɗakin mu muka shiga kan gadon mu na faɗa ina faman murmushi.





"wallahi nayi kewar gadon nan",na faɗa ina shafa saman shi,dariya suka yi sannan Rufaida tace"Dalla can ki tashi kizo ki bani tsaraba ta.




Hafeeza ta ɗago leda tana faɗin"Aunty Rufaida barta ta huta kawai,gashi nan kin gani",kallon ta nayi da sauri.



Ganin ledar dake hannun ta yasa nayi saurin dirowa daga saman gadon,fincikewa nayi nace"tab wannan kuma baki isaba",zuge jaka ta nayi,kwalin chocolate wato coconut rich da kuma fenza na miƙa musu.





Dariya duka suka yi sannan suka duka sannan suka hau buɗewa suna sha,ni dai cigaba da kwanciya kawai nayi.




Ummi tayi sallama ta shigo,"to ba sai ki tashi kiyi wanka kizo kici abinci ba",ta faɗa tana kallo na.




Miƙewa nayi sannan na shiga wanka,koda na fito shiryawa nayi cikin riga top fara da siket na jeans blue black.




Ina fitowa falo Ummi na fitowa daga kitchen,plate ɗin hannun ta ta miƙo mini,amsa nayi kawai.




Jallop ɗin taliya ce da sake ta man ja,sosai naci sannan na kora da zoɓo me sanyi,godiya nayi ga ubangiji na daya ciyar dani kuma ya shayar dani.





Rufaida da suka gama shan chocolates ta fito inda nake ta zauna tace"wallahi juwairiyya baki da kirki yanzu taliyar kika ci ko tayi babu".





"amma kina ji Ummi tace nazo naci abinci ko,ai da sai ki fito muci",bata kuma cewa komai ba.






Waya ta ta saka hannu ta ɗauka,shafawa tayi tace"Allah sarki nayi kewar ki",dariya kawai nayi kallo na tayi tace"yauwa bani labarin makaranta".





"Hmm sis mun ci wahala karatu babu sauƙi sai dai yanzu kuma mu bita da Addu'a kawai",daga nan muka shiga fira inda rabi ɗa kwata take bani labari akan yanayin zaman gidan da bana nan.




Wai komai ya dawo dai-dai,kenan nice matsalar gidan mu,sai dai wani labari data bani shine yaya Abdullahi daya cakawa wani wuƙa a ciki ya guda yanzu haka ba'a san inda yake ba.




Sai kuma Aliyu da ya fara waƙa,zaro idanu nayi nace"Wa me?",tace"waƙa da kika sani amma fa yaya Khaleel be sani ba".





Jinjina kai kawai nayi ina mamaki wai gidan malami kamar mahaifin mu Amma ake waƙa da kuma ƴan sara suka.




Koda yake da saka hannun baba malam a ciki ai shi yafi wajen yawon wa'azi amma ga gidan shi suna buƙatar wa'azin.





"Juwairiyya akwai jarabawa",wata zuciyar ta faɗa mini haka,girgiza kai nayi sannan nace"Allah ya kyauta gaba dan wannan kam ya gama faruwa,amma baba malam ya sani?,na jefa mata tambaya.





"Eh shida Baban gida har Baba ma,amma an hana a faɗawa Abba,da kuma su Yaya Khaleel".



Bance komai ba muka cigaba da firar mu,anan tayi magrib da isha'i,sai wajen tara sannan na raka ta.




Muna tafe muna fira,idan ka ganni nayi rama amma kuma nayi haske saboda kwanciyar hankali da nake samu.






Har part ɗin su na kai ta,sai da na shiga muka gaisa da Umma sannan na fito.




A waje muka haɗu da Yaya Khaleed gaisawa muka yi,"Ƴan matan makaranta an dawo ne?",eh Yaya na dawo ya muka same ku",na tambaye shi.





"lafiya lau ba dai jarabawa ce ta saka kika koma haka ba,kada dai kice mini ke raguwace?",girgiza kai nayi sannan nace"A'a kawai dai na yi ciwo ne sai kuma kewar ku".




Dariya yayi yace"kai Juwairiyya an iya daɗin baki yanzu ina sabo ina cikin zaria zaki wani ce kin yi kewar mu,da kinyi ai da kinzo kin gan mu yanzu dai kira mini yayar ki".




"wace ce yayar tawa?"na tambaya cike da mamaki,cikin tsokana yace"Rufaida mana",haba yaya nafa girme ta koka manta ne wajen wata biyar na bata".




"amma ni ai na baki shekara nawa",ya faɗa,shiru kawai nayi,dariya yayi yace"please jeki na gaji".





Cikin natsuwa na koma,har ta bararraje tana kwasar fira,hararar ta nayi nace"to ai sai ki fito yaya Khaleed yana jiran ki".





Ban jira cewar ta ba na fito,gaya mishi nayi gata nan zuwa sannan na wuce domin komawa ɓangaren mu.




Cak na tsaya ina kafawa part ɗin su idanu,haƙiƙa nayi kewar ganin shi,haka ma muryar shi kusan sati nawa kenan tun ranar dana tura mishi hoto be kuma kira na ba,haka credit ɗin da yake aiko mini duk sati shiru,may be yayi busy ne.






Ko dai yayi budurwa ne ya manta dani,a da ko babu komai zai kira ya tambaye ni karatu na,ya ilahi meke faruwa ne?.





Ganin tunani ba zai mini ba nayi saurin wucewa,ina komawa na tarar da Abdul'azeez ya dawo hakan yasa na zauna muka hau firar yasuhe gamo.





Khairiyya da kuka ta shiga part ɗin su,momma ta miƙe da sauri tana tambayar fmta lafiya?.





Cikin kuka tace"Momma me yasa a komai Juwairiyya take wuce ni,kin ganta yanzu ta dawo amma baki ga yadda ta daɗa kyau ba".





Ikon Allah 🤔sai kallo wannan hassada har ina???.





Momma cikin lallashi tace"Haba Khairiyya ki dena haɗa kan ki da wannan jikar magajiyar karuwan,ki sani kinfi ƙarfin ta nesa ba kusa ba,ai sama ta yiwa yaro nisa,sha kurumin ki akwai wani mai dana gani wajen bintu yarinyar hajiya zulfa shi zan siyo miki zai saka kiyi fresh kiyi haske".





Dariya tayi sannan tace"yauwa Momma na san cewa ke kaɗai kike sona wallahi",Momma tace"ke dai ki dena damuwa da ita yanzu tashi kije ki ci abinci".




Cikin farin ciki ta miƙe gani take ai yanzu tafi Juwairiyya kyau kawai.





Khairiyya kin raina kyawun da Allah yayi miki kenan???.




Kwance yake kan sofa ƙafar shi ɗaya kan ɗaya,riga da wando ne yadi a jikin shi kalar brown.





Hannun shi riƙe da wayar shi wacce ya kara ta a kunne yana amsa waya,haƙiƙa yanzu sun saba da Raheela sosai da sosai.





"yanzu dai kwantar da hankalin ki,mun kusa zuwa zaria zan shigo kaduna sai mu haɗu",ya ƙarasa maganar yana murmushi.





Zuby dake malelekuwa saman gadon ta na alfarma tana faman zabga murmushi wai kamar a mafarki yau ita ke waya da Khaleel har taji sautin murmushin shi.




Da sauri ta miƙe tace"Ayya gashi on monday zan koma school sai dai kawai ka bari ma haɗu wani lokacin".






"Anya kin san yadda nake so mu haɗu kuwa,amma babu yadda zamu yi yanzu kin san cewa na ƙosa na gan ki a fili".





"ayya wallahi hubby ina komawa zamu fara jarabawa,kaga kuwa dole na maida hankali sosai".




Tunda ta ambaci makaranta gaban shi ya faɗi,idan zai iya tunawa yau satin shi takwas babu kwana huɗu Rabon daya kira ta a waya,har tana credit ɗin da yake tƴra mata ya dena gaba ɗaya,balle transfer.




Dafe goshin shi yayi,cikin sauri yace"Juwairiyya",ya faɗa yana jan sunan,ita kuwa Zuby dake faman cewa hello jin yayi shiru yanzu kuma jin ya ambaci Juwairiyya yasa ƙirjin ta bugawa.






Da sauri tace"Hubby na wace ce Juwairiyya kuma?",cikin sanyin jiki yace"ƙanwa ta ce ina zuwa",daga haka ya katse wayar.





Zuby taja tsaki tana faɗin"wace ƴar iskar ce zata lalata mini shiri na,wai wacece Juwairiyyan nan ne?,lallai sai nayi bincike akan ta kuma sai na nuna mata cewa ba'a shiga gonar Zuby a zauna lafiya",ta faɗa tana huci.






*Gani dai na kqmawo muku Ƙareenateet sai dai ba zan gaji da baku haƙuri ba na rashin ganin shi kullum hakan yana faruwa ne aabida sauran uzururruka na rayuwa ku sani a koda yaushe kuna cikin zuciyar one lurhv*





#LIƘE
#SHARE
#COMMENT.




*babyn Abdul maman meenal farouk da Elham*.









*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.


♥ ❤

♥♥❤
*~K'AREENATEEY~*
(K'AWATA)

(It's all about friendship)





https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/



*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


*YAN UWA MUNA KARA KIRA DA MABIYA LITTAFAN GOLDEN PEN WRITTERS ASSOCIATION DA SU KIYAYE DA WANNAN MAI CUTAR TASU DA SUNAN YANA SAIDA LITTAFAN KUNGIYARMU,TO KARYA YAKE MACUCI NE KAWAI LITTAFANMU IS FREE 1 NE KAWAI NA KUDI,KUMA DA YACE YANA BA KUNGIYARMU KUDIN REGISTER DIN DA KUKE BIYA DOMIN MU TURA MASHI SABBIN LITTAFAN MU,TO WALLAHI DUK KARYA YAKE MANA MU BAMU DA MASANIYA AKAN WANNAN B'ARNAR DA YAKE MANA SAI DAGA BAYA MUKA JI,SANNAN KUMA INA SON KUSAN NUMBER DIN SHI SABODA YANA NAN YANA SHIGA GROUPS NA MATA DA SUNAN MACE SABODA HAKA KU KIYAYE GA NUMBER DIN SHI NAN (08107707692)*




*written *✍
-by-
*Deeja one love*




*JAKADIYAR GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION👸*



Wattpad 13deeja.


Daga wannan page d'in har zuwa k'arshe sadaukarwa ne gare ki *AISHATU BABAYO* saboda kaunar da kike wa *GOLDEN PEN WRITERS* ba muda abinda zamu biya ki dashi, dan haka *K'AREENATEEY* har zuwa k'arshe ya zama naki sis kiyi yadda kike so dashi, *JAKADIYA* ta baki wannan yan shafukan har zuwa karshe, muna godiya sosai da irin kaunar da kike mana.








*Tunatarwa*





Ɗan uwa idan zaka kwaikwayi gwanin ka,ka tabbatar wannan da zaka dinga kwaikwayon mutumin arziƙi ne domin manzon Allah tsira da amincin Allah sun tabbata agareshi yace"mutumin yana tare da wanda yake so a ranar ƙiyama".



Sannan idan kana son mutum toka so shi domin Allah dan wani hadisi daga manzon Allah tsira da Amincin Allah sun tabbata agare shi yace"A ranar ƙiyama Allah zai yi yekuwa yace"ina masoya wanda suke soyayya domin girma na a yau zan saka ku a inuwa daga cikin inuwa ta ranar da babu wata inuwa sai tawa".




Wani hadisin yace"mutum bakwai Allah zai sanya su a cikin inuwar shi ranar da babu wata inuwa sai tashi,saurayin daya shagala da bautar Allah,mutumin da mace ta kira shi ma'abociyar kyau domin suyi fasiƙanci yace mata ina tsoron Allah,da mutumin da zuciyar shi ke rataye da masallaci,da masoya biyu da suka yi soyayya domin Allah kuma suka rabu domin Allah,da mutumin da yayi sadaka har hagun shi bata san me daman shi ta bayar ba,da mutumin da ya tuna Allah a keɓaɓɓen waje idanun shi ya zubar da hawaye.


*_20_*.





Mun gama fira da Abdul'azeez har na shiga ɗaki domin yin wanka na shiryawa barci sai ga kiran shi.






Shiru nayi gaba na yana cigaba da bugawa,har sai da ta katse ya sake kira sannan na sami ƙarfin gwiwar ɗagawa.





Sallama yayi na amsa sannan na gaishe dashi,shiru yayi yana sauke numfashi,ni ma kuma bance komai ba.





Yace"ya karatun?",sai da na dai-dai ta kaina sannan nace"Alhamdulillah yanzu dai mun gama jarabawa ne".




"To Allah ya bada sa'a",nace"Ameen yaya Ina Yaya Abdus-samad?",ajiyar zuciya yayi yace"yana can cikin bariki yana aiki ne".





Sai da nayi jim sannan nace"ina Yaya Al'ameen fa",shiru yayi kamar ba zai tanka ba sai kuma yace"ya tafi gombe jiya,ko na haɗa ku conference ne".





Da sauri nace"eh,ina so mu gaisa",yaƙe yayi yace"to ina zuwa ban minti biyu",babu jimawa ya haɗa mu.




Bayan mun gaisa yace"Allah sarki budurwa ta,ashe haka kike so na?",Yaya khaleel yaja tsaki yace"minti biyar na baku ku gaisa".





Dariya Yaya Al'ameen yayi yace"shikenan babban yaya,angama nida budurwa ta muna godiya,juwairiyya",ya kira suna na.




Na amsa fuska ta ɗauke da murmushi,yace"To ya jarabawa,kun gama ko?",na bashi amsa da"eh".





"yauwa kiyi ki gama kinga dama yayan ki yace sai kin gama karatu zai bani ke,dan ni yanzu ke kawai nake jira".





Dariya nayi nace"kai Yaya Al'ameen ku da kuke da fararen mata ƴan fulani ga gashi ga kyau".




"kema kin san baƙaƙe sun fi kwaliti ganewa ne ba'a yi kuma ke ai ba zaki kira kan ki baƙa ba,kuma ai na san da fararen nace ke nake so".





Dariya na kuma yi nace"Allah ko kana bani dariya",Shima yace"ai haka nake so kiyi ta dariya dan ma bana kusa kuma Rambo ba zai bani number ɗin ki ba ai da video call zamu yi".





Nace"kamar ka san ina son video call sosai",Dariya shima yayi yace"wallahi ba zai bani number ɗin ki ba,wannan yayan naki gashi sai aiki yake sani amma zan daure na shigo zariar ayi mini sakwara kalar ta rana nan".





Nace"sakwara ai mai sauƙi ne in dai kazo",dariya muka yi duka sannan yace"yauwa wane kala kika fi so ne",na bashi amsa da"pink"taɓe baki yayi yace"kalar mata kenan ai".





"ai tana da birgewa ne",na bashi amsa,yace"yauwa yanzu ina saurayin ki",zaro idanu nayi nace"Yaya Al'ameen ka dena faɗan haka fa,kada ka haɗa ni da Yaya Khaleel".





"oh to ko dai dashi zamu yi ne?",ya tambaya murmushi nayi nace"haba dai ai yafi ƙarfi na wace ni kawai dai ya nuna baya so na da kowa".




"har ni?",ya tambaye ni,girgiza kai nayi nace"gashi ma shiya kira ka ya haɗa mu",kenan nima saurayin ki ne?",murmushi nayi.





"lokacin ku ya cika"mu kaji muryar Yaya Khaleel yana faɗin haka,Yaya Al'ameen yace"mun gode ma haka baby na kada ki damu ina nan zuwa zaria".




Yaya Khaleel yaja tsaki yace"naga uban da zai maka aikin ka kuma,sannan ka tabbatar jibi ka dawo",cike da tsokana yace"yes sir",daga haka ya katse wayar.





Shiru nayi ina sauraran me zai ce,katse wayar shima yayi,ajiyar zuciya nayi ina zama gefen gadon mu,kafin na tashi na shiga wanka.




Shi kuwa dafe kan shi yayi yana tunani,yadda take sakewa suyi fira da Al'ameen shi bata mishi haka me yasa haka???





Babu tsoro ba komai ta kan iya bashi amsa amma shi duk lokacin da zasu yi magana ya lura gaba ɗaya a tsorace take dashi.





Tunawa da yayi wai tana son video call,murmushi yayi sannan ya ɗauko wayar shi ya fara kiran ta.





Zuby ta zuba tagumi ranta a ɓace,wayar ta ƙara kallo tun ɗazu take kiran shi amma user,da wannan yake waya kenan??.




Ƙara trying lambar tayi amma duk da haka ana amfani da ita,cillar da wayar tayi ta hau kuka.



Zuly taja tsaki tana faɗin"wallahi har haushi kike bani",ɗagowa tayi ta kalle ta kafin tace"wallahi Zuly har naji bana ƙaunar ta,ina da kishi sosai".





Zuly ta taɓe baki tace"shi da ƴar uwar shi?",ɗaga kai tayi tace"tabbas duk da take ƴar uwar tashi amma wallahi bana ƙaunar ta".





Jan numfashi Zuƙy tayi sannan tace"hmm ki bi dai a hankali ga Fa'iz yana nan jiya ma ya kira ni yace bakya ɗaga wayar shi".





Cikin fushi tace"ba zan ɗaga ba ɗin,yabi ya dame ni an gaya mishi da da yanzu ɗaya ne?",ware hannaye Zuly tayi tace"oho muku",daga haka ta fice daga ɗakin.




Ina fitowa wanka wayar tayi ƙara,murmushi nayi ganin wanda yake kira,ɗagawa nayi ina mamakin meya faru bayan yanzu muka gama waya.





"kin gama shiryawar?",ɗaga kai nayi a hankali,sannan nace"eh na gama",yanzu sai me?",ya tambaya.





"barci",nima na bashi amsa a taƙaice,shiru yayi kafin yace"ok sweet dreams,kiyi mafarkin.......wanda kike so",ya ɗan waske",bance komai ba nayi murmushi kawai,shima murmushin yayi kafin ya kadhe wayar.





Humra kawai na shafa sai kayan barci dana saka sannan na kwanta,daga haka sai barci.





Ɓangaren shi ma hakane ta kasance,hoton ta ya buɗe wanda ta saka dpguwar riga baƙa,murmushin dake kan fuskar ta shi yafi ɗauke mishi hankali.





"smile always",ya faɗa yana shafa fuskar ta,Ɗora wayar yayi saman ƙirjin shi s haka har barci ya ɗauke shi.





Zuby kuwa sai da ta kora sannan ta iya barci yayin da ita kuma Zuly ta samu wannan damar wajen cikar burin ta.





Yau naje na duba result ɗin mu Alhamdulillahi naci komai wanda hakan ke alamta mini cewa zan wuce kenan.





Nayi murna sosai nida masoya na wato Abdul'azeez da kuma Rufaida,sai yaya Khaleed shima daya ganni ya mini congrats.




Domin taro aka haɗa a falon baban gida aka sanar,ranar naga zallar hassadar ƴan gidan mu,da yawa kasa cewa komai suka yi.




Umma dai ta daure ta mini murna haka ma Aunty amma Hajiya da Momma ƙiri-ƙiri suka maze.



To ni hakan be dame ni ba dan wacce ta haife ni ma bata mini murna ba balle wasu,ni bana ganin hakan a matsala.





Khairiyya kuwa da ƙyar ta riƙe kukan ta har muka fito,hannu na Rufaida ta janyo muka bita da sauri.





Ita kuwa sai sauri take a harabar gida muka

1 Comments On KAREENATEEY
avatar
hauwa-8-2

1 year ago

Reply

Mashaa Allah

Please Login or Register in order to submit comment