Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

babu komai kawai dai ina ɗaukar ta kamar yadda Khairiyya take ne,sannan kuma ina tausaya mata".

Ko zuciyar shi ta kasa gasgata abinda bakin nashi ya faɗa balle ni one love da nake boot nake kwaso muku rahoto,bare kuma ku da kuka saki baki kuke sauraro na😜.

Zuciyar shi ke bugawa da ƙarfi,idanu ya lumshe sannan ya buɗe a hankali,kallon mutanen dake hada hada a wajen yayi.

Tada motar yayi ya nufi fita daga ƙofar dokar ma gaba ɗaya,ni dai fitowa kawai nayi daga motar dan ban shirya shiga sabon gari ba shi kuma naga alamun can ya nufa.

*Safe journey* inji turawa ni dai na koma wajen Juwairiyya.

Ummi ta zauna kusa dani,hannu na ta riƙe tace"kada ki mini mummunan fassara ki sani ke ɗin ƴata ce sannan duk abinda kika ga anayi miki ina kauda kai ina sane dake kuma ina son ki ba wai bana son ki ba,amma tunda na lura da ƴan gidan basu san kawaici ba to kuwa ba zan yi musu ba,daga yanzu bana so ki ƙara bari ku haɗu da Khaleel koda kuwa a kan hanya ne".

Idan har kun haɗu dole to daga gaisuwa bana so ki ƙara furta mishi komai kinji",ɗaga mata kai nayi.

Murmushi tayi tace"yauwa haka nake so Allah yayi miki Albarka",rungume ta nayi ina amsawa da Ameen.

Ban wani saka abin a rai na ba,buri na kawai tunda Ummi yanzu ta dawo mini kamar da shikenan.

Abdul'azeez yayi sallama ya shigo,miƙewa nayi cikin farin ciki na rungume shi.

Sai da ya kalli falon yaga ba kowa sannan yace"gaya mini meya faru?",hannu na miƙa mishi muka tafa sannan nace"Ummi ta sauko yanzu tana kula ni".

Ihu yayi sannan ya ɗaga ni sama yana juyi dani,Ummi data fito daga kitchen ta tsaya tana kallon ikon Allah.

"ke dai kam anyi babbar kwabo yanzu ƙanin ki ya ɗaga ki sama haka",Ummi ta faɗa tana dariya.

Harara na ɓalla mishi sannan nace"wallahi sweet ka raina ni,ba yayar ka bace ni",ɗaga hannu yayi yace"amma kuma ai ance ɗa shike magajin uba kuma dai girman na kwana nawa ne".

Da mamaki muke kallon shi,Ummi tayi mishi dakuwa tace"gidan ku,tsakanin ku fa shekara uku ne",dariya muka yi.

Shi kuwa haɗe rai yayi yace"ai duk da haka nine dai namiji na farko",jan hannun shi nayi nace"ni dai muje ka cire kaya kazo kaci abinci".

Ummi ta bimu da kallon sha'awa a yadda muka jera zaka ce shine babba saboda yana da tsayi sannan ƙara wani buɗewa yake yi.

Sai da ya cire kaya sannan muka zo.muka ci abinci,muna gamawa Ummi ta bamu takardar maganin ɗazu tace"kuje ku siyo amma kada ku daɗe",da to muka amsa sannan muka fice dan dama jiki na da hijab kusan haka nake wuni wani lokacin.

Muna tafe muna fira har muka je muka siyo muka dawo,a bakin get muka ga Yaya Khaleed da Rufaida a tsaye da alama magana suke yi.

Gaisuwa ce kawai ta haɗani da Yaya Khaleed amma daga nan ban kuma ce mishi komai ba.

Shima kuma be nemi wata magana daga gare ni ba,Rufaida ta harare ni tace"wallahi kin kyauta,sai yanzu nake ganin idanun ki".

Murmushi nayi sannan nace"Rufaida kiyi hakuri bana da lafiya ne",Allah ya sauwake tace mini.

Ban wani ja dogon magana ba,muka shige gida.

Rufaida tace"Yaya kaga lura da Juwairiyya ta canza kuwa",Yaya Khaleed yace"may be dai wani abu ya faru ne".

Muna shiga harabar gidan muka haɗu da Khairiyya,kallon juna muka yi ni da ita,kayan jikin ta na kalla.

Wata doguwar riga ce cikin kayan da Yaya Khaleel ya siyo mini,hannun ta kuwa waya ta ce.

Kauda kai nayi sannan na ja hannun Abdul'azeez nace"muje mana",yace"sweet kamar wayar ki na gani hannun Aunty Khairiyya".

Bashi labarin abinda ya faru nayi,sosai naga jikin shi yayi sanyi,ni kuwa ban damu ba sosai.

Barrack ya wuce direct,sai da ya kashe wayoyin shi duka sannan ya kwanta,duk abubuwan da suka faru a baya yake tunawa har zuwa yanzu.

A haka har barci yazo ya sace shi be sani ba.

Momma data kasa zaune ta kasa tsaye fatan ta ya kasance ɗan ta yana lafiya kawai.

Gashi sai faman kiran wayar shi take yi amma a kashe babu shiri ta fice,ɗakin Yaya Abdus-samad ta nufa sai dai abin haushin baya nan.

Ta rasa inda zata saka kanta,a haka Yaya Khaleed yazo ya same ta,"Momma lafiya kuwa kike?".

"ina fa lafiya Khaleel tun ɗazu nake kira yaƙi shiga gashi kwata kwata yaƙi ya dawo gidan ban san inda yaje ba".

"amma dai Momma Khaleel ai ba yaro bane ko",miƙewa tayi cikin fushi tace"rufe mini baki ka san a yaya ya fita ne,ranshi a ɓace yake fa".

"Momma to meya ɓata mishi rai",Yaya Khaleed ya tambaya,labarin abinda ya faru ta bashi sannan ta ƙara da cewa"tunda ya fita hrar yanzu shiru fa".

Yaya Khaleed kuwa ya rasa me zai cewa mahaifiyar tasu,"Allah ya kyauta kawai abinda ya faɗa kenan".

Sai wajen tara sannan ya farka,bayi ya shiga yayi wanka sannan ya ɗauro alwala,sallolin da ake bin shi yayi sannan ya fito.

Sai da ya ɗauko hanyar dawowa gida sannan ya kunna wayar shi,yana kunnawa saƙonni suka fara shigowa.

Kira kuma ya shigo,ganin daga Al'ameen ne yasa ya ɗaga,Al'ameen yace"Ya da kashe waya tun ɗazu na shigo nake neman ka amma shiru".

"amma naga ai ka san gidan mu ko",Yaya Khaleel ɗin ya faɗa,Al'ameen yace"ai gani a gidan naku muna tare ma da Abdus-samad",a taƙaice yace"gani nan zuwa".

Daga haka ya katse wayar,Al'ameen yayi dariya yace"K.A kenan",Yaya Abdus-samad kuwa murmushi kawai yayi.

Babu jimawa ya ƙaraso,suna zaune a harabar gidan kan kujerun roba,ganin motar shi yasa duka suka miƙe.

Cikin girmamawa suka sara mishi,Al'ameen yace"gani na zo na cika umarnin ka".

Tsaki yaja yace"dalla nan ba barrack bane,kuma ni daman nan gidan nake so kazo sai dai zamu shiga kaduna daku gobe amma ba zamu daɗe ba,ka kira major Muhammad sani ka faɗa mishi".

"sannan ka kuma kira lit.patrick odulowa ka faɗa mishi,domin ya san da zuwan mu,akwai special ganawa da zanu yi da officer ne".

Duka suka sara mishi suna faɗin"yes sir!",Murmushi yayi musu sannan yace"command oder",daga haka ya wuce.

Bayan shi suka bi,ɗakin shi ya buɗe ya shiga komai tsaf-tsaf kamar babu wani wanda yake kwana a ciki.

Bayi ya shiga yayi wanka sannan ya fito,gaban mirror ya tsaya ya zubawa madubin idanu.

Meke faruwa dani ne?,murmushi yayi sannan ya shafa cikin shi,yunwa yake ji dan rabon shi da abinci tun da safe.

Wayar shi ya ɗauko zai kira ta sai kuma ya tuna,nannauyar ajiyar zuciya yayi sannan ya jefar da wayar.

Dole hakan nan ya shirya cikin riga fari da kuma wando baƙi sumar kan shi tasha gyara sosai,sai ƙamshi yake zubawa.

Suna zaune a falo ya fito,da sauri suka miƙe,a taƙaice yace"muje wajen Momma muci abinci".

Basu ce komai ba,banda bin shi da suka yi,shi kuwa wani iri yake ji a jikin shi da kuma cikin zuciyar shi.

Momma na zaune tana tunanin shi,Khairiyya kuwa an sami waya sai danne danne ake yi danma da security a jiki.

Jira take safiya tayi kawai taje wajen ta ta buɗe mata,jin sallamar shi yasa tayi saurin ajiye wayar.

Be kalle ta ba haka be damu da yanayin da ta nuna ba,Momma kuwa cikin sauri na miƙe tana zuwa ta taro shi.

Ko a fuska be nuna mata komai ba,gaishe da ita yayi haka suma gaishe da itan suka yi.

"Momma abinci muka zo ci fa?",ya faɗa yana kallon Khariyya,cikin sauri ta miƙe,Momma ta kalle ta tace"yauwa yi musu setting ɗin table.

Ba dan taso ba ta miƙe,sai da ta shirya komai sannan suka tashi suka hau,babu laifi abincin yayi daɗi sosai wannan ya tabbatar mishi ba Khairiyya tayi girkin ba.

Sai faman iyayi take wanda babu wanda yama ɗago ya kalle ta,suna gama cin abincin suka miƙe.

Sai da suka zo fita sannan ya ƙwalawa Khairiyya kira,da sauri ta zo,"jeki kawo mini wayar da kuma system ɗin".

Ɗan tsayawa tayi jim kamar me tunani kafin ta tafi tana ƙunƙunai,kawo mishi tayi Al'ameen ya kalla wanda hakan yasa da sauri ya amsa.

Juyawa suka yi suka tafi,Khairiyya kuwa ta bisu da kallo sai da suka ɓace sannan taja tsaki tace"wai ina zan yarda miji na yana bin miji Juwairiyya a baya a matsayin yaro wallahi har abada,dama kai kake da muƙamin Yaya Khaleel ai dana more".

Khairiyya kin raina wanda Allah ya bashi kenan🙄.


************ *********** ***********

Ni kuwa a wannan lokacin ina ɗaki ina karatu,saboda ranar monday zan shiga makaranta.

Rufaida tayi sallama ta shigo,amsa mata nayi sannan na cigaba da karatu na,sai dai na lura jikin ta yayi sanyi.

Zama kawai tayi tana kallo na,ni kuma ban ɗago ba karatu kawai nake yi,hakan yasa ɗakin yayi shiru.

Sai yanzu na fahimci wani abu zama na a ɓangaren mu ba tare da shiga sabgar wani ba shine rufin asiri na.

Ummi tayi sallama ta shigo ɗakin,ganin yadda muke zaune yasa tace"au karatun kika cigaba ƴar uwar ki ta shigo ai kya tsaya ki saurare ta".

Kallon ummi kayi idanu na kamar zasu kawo ruwa,girgiza mini kai tayi tace"a'a bana son haka ni yaran Aunty Maryam nace kija baya da su ba wai Rufaida ba".

Zaunawa tayi kusa dani ta kama hannu na sannan tace"kin san kina da hawan jini idan baki da ƙawa wacce zaku yi fira da ita jinin fa ƙara sama zai yi".

Murmushi nayi nace"hakane Ummi amma ina tsoro tayi mini irin abinda Khairiyya tayi mini,Ummi yadda muke da Khairiyya be kamata tayi mini haka ba".

Rungumo ni Ummi tayi tace"kada ki damu,komai me wucewa ne,amma kiyi haƙuri a yadda rayuwa tazo miki".

Sai da ta lallashe ni sosai sannan ta miƙe ta tafi,kallon kallo muke da ita,murmushi muka yi a tare sannan tace"wai meya faru".

Labarin abinda ya faru tun daga farko na bata har zuwa ƙarshe,dariya ta kwashe dashi tace"wallahi Ummi ta birge ni haka ya kamata tayi sai dai be kamata da Yaya Khaleel ba".

Ban ce komai ba domin ma na kauda zancen sai nace mata"ya shirye-shiryen graduation?".


"baki ga na gama komai ba,yanzu abinda ya rage shine lallen ki da kuma gyaran kan ki".

"ni dai da kin ƙyale shi yaushe muka je aka yi mini har kuma akayi graduation ɗin",harara ta ɓalla mini tace"to malama an gama ma,domin gobe da asuba zata zo tayi miki".

Fira muka cigaba sannan Ummi ta turo Hafiza akan mu fito mu ci abinci,tare muka tashi muka fice.

Yaya Khaleel dake tsaye a ƙofar part ɗin mu,so yake ya shiga amma kuma ya kasa shigan.

Al'ameen yace"wai ba budurwa ta zaka kira mini ba?",hararar shi yayi yace"kai baka da bakin kiran ta",dariya Al'ameen yayi.

Abdul'azeez ne yazo wucewa sai da ya basu hannu suka yi musabaha sannan ya gaishe dasu.

Al'ameen yace"dan Allah idan ka shiga ka kira mini Juwairiyya",Abdul'azeez sai da yayi jim sannan yace"to".

Ƙirjin Yaya Khaleel ya fara bugawa da ƙarfi dan be sani ba ko Ummi zata barta ta fito, a zahirin gaskiya shi kan shi yana si ya ganta.

Ina zaune kan kujera muna waya da Jabeer akan gashi nan zai zo ya amshi assignment ɗin,ni kuma ina faɗa mishi ya bari gobe idan yazo graduation ɗin su Juwairiyya sai na bashi.

"Shikenan idan hakan kike so",daga haka kuma sai muka cigaba da fira,shigowar Abdul'azeez ma ina wayar.

Zama yayi sannan yace"sweet ana sallama dake a waje",sai da na ɗan dakata sannan na juyo na kalle shi kirji na yana bugawa.

Kallon Ummi nayi wacce take kallon wa'azi a tashar manara tv,itama ta juyo tana kallo na ne.

A iya tashi na babu wanda ya taɓa sallama dani wai da sunan yazo taɗi saboda bana basu ƙofar zuwan ma.

Gashi kuma waya nake da Jabeer balle nace ko shine,kuma ma idan shine ai be san gidan mu ba.

Ummi ta maida kallon ta kan Abdul'azeez tace"waye ke neman ta",ya bata amsa"wani abokin Yaya Khaleel ne".

Ummi fuskar ta sai da ya canza sannan tace"kaje kace mishi tana Sabon gari",miƙewa kuwa yayi ya tafi.

Tunani na faɗa kada dai Yaya Al'ameen ne yazo Ummi ta hana ni fita?,ko dama ɗazu da nace mishi ya kira shi kiran shin yayi da gaske?.

Sallama na yiwa Jabeer sannan na katse wayar,miƙewa nayi kawai na shige ɗaki,zama nayi bakin gado.

Kallon window nayi a hankali na miƙe har na isa bakin window ɗin,leƙawa nayi,kasancewar akwai haske yasa na hango su.


Sai dai sun juya baya dukkan su,suna facing ƙofar fitowa,Yaya Khaleel yana jingine jikin ginin gidan ya ƙurawa ƙofar ido.

Ban san meke tsargawa har cikin raina ba,Abdul'azeez ne ya fito sannan yace"kayi haƙuri ashe bata gidan tana Sabon gari".

Yadda Yaya khaleel ya runtse idanu hakan shi zai nuna maka beji daɗin abinda aka faɗa ba,da yake duk yana bayan su ne ba zasu lura da yanayin da yake ciki ba.

Murmushi yayi a iya sanin shi yaran Ummi basa faɗin abinda ba haka ba amma a yau sai gashi Ummin da kanta take sa su suyi ƙarya.

Idan mutum be saba abu ba da yayi zaka gane shi,hakan yasa koda Abdul'azeez yazo ya gane cewa abin ba haka bane.

Juyawa suka yi domin tafiya,ban san meya saka ya bani tausayi ba Alƙah sarki,ina kallo suka nufi hanyar fita.

Su Al'ameen na gaba hakan yasa suka riga shi fita,dai dai zai fita jikin shi ya bashi ana kallon shi.

Daga yanayin yadda zuciyar shi take bugawa da ƙarfi,tsayawa yayi sannan ya juyo.

Cikin sauri na koma da baya dan bana so ya ganni ya zama na abinda Ummi ta faɗa ƙarya ne a wajen shi.

Murmushi kawai yayi domin ya riga da ya ganni,sai dai ba sosai ba ficewa yayi ni kuma na koma kan gadon mu na kwanta.

Har lokacin bugun zuciya ta be dai daita ba,magani na na ɗauko na sha sannan na shiga bayi.

Wanka nayi sannan nazo na kwanta,tunani nake yi har barci ya ɗauke ni.

Shi kuwa ɗakin shi kawai suka wuce,be damu da yadda suke firar su ba,aikin daya ɗauko zai yi ma gagarar shi yayi hakan yasa kawai ya ajiye.

Kallon su yayi sannan ya kalli laptop ɗina da wayar,ganin hankalin su yana kan firar da suke yasa yayi saurin ɗauka ya shige bedroom.

Yaya Abdus-samad yayi murmushi kawai tabbas ƴan uwan nashi sun faɗa son juna ba tare da sun sani ba.

Wannan yasa yayiwa likitan nan ƙarya domin a yadda ya lura shima likitan so yake ya shigar da kan shi.

Yaya Khaleeƙ kuwa kan bed ya ajiye system ɗin sai da yayi wanka ya shirya cikin kayan barci sannan ya ɗauko system ɗin ya buɗe.

Sai dai fa da password,abin haushi,trying kawai yake yi amma ya kasa samun daidai.

Sunan ta dashi ya fara incorrect,ummi shima ba haka ba,to sunan wa'inda take so a yadda yake gani a zahiri Rufaida da Abdul'azeez amma ba haka bane.

Ajiyewa yayi kawai sai ya koma ya ɗauko wayar ta,ita ma nan ɗin password ne,wajen kashe ta ya dannan cikin ɓacin rai.

Hoton daya fito akai ne ya sa ya kalli wayar,pic ɗin shi ne wanda daga gani be san ma an ɗauke shi ba.

Zaune yake ya lumshe idanun shi,fuskar shi ta nuna damuwa da gajiya,a cikin falon shi ne,sanye yake kuma da khakhi.

Tunani yake a ina ta sami wannan hoton kenan,bin hoton yake da kallo sosai yayi kyau.

Ƙasan hoton ya kalla,emoji ne na flowar tsakiya an rubuta *YAYA NA*.,shafa kan sunan yayi yana murmushi.

Yaji daɗin sunan wato idan ta kira shi da Yaya na daɗin hakan yake ji,da sauri ya kuma wajen password yana rubuta yaya na kuwa ya buɗe.

Ajiyar zuciya yayi sannan ya buɗe ciki,babu wani tarkacen hotuna,nasu ne kawai ita da Rufaida sai Abdul'azeez da sauran ƙannen ta.

Sai nashi sai kuma na Ummi kuma duk da basu da yawa sosai,sai hotunan flowers wanda kusan su suka cika wayar.

Bincike kaɗan yayi sai kuma ya ajiye ya ɗauki system ɗin shima Yaya na ya gwada sai dai be buɗe ba.

Yaya khaleel ya rubuta sai kuma ya buɗe,hotan shi ne ƙato wanda ya cika screen ɗin gaba ɗaya.

Yana sanye da khaki ya saka hannun shi cikin sumar kan shi,ɗayan hannun kuma.ya saka cikin aljihu,fuskar shi yayi murmushi har haƙorin sa ya bayyana.

Daga ƙasa kuma hoton ta ne wanda take sanye da shadda ruwan purple doguwar riga ta ɗan tsuguna sai ta ɗan ɗago fuskar ta.

Ta rufe rabin fuskar ta da hannun ta alamun bata so hoton ta ba,shafa hoton yayi yana murmushi haƙiƙa tayi kyau sosai.

Shima nan videos ne da sauran pictures sai kuma file na karantun ta da sauran abubuwa.

Videon ɗazu na asibiti ya shiga a cikin wayar tata bayan ya ajiye laptop ɗin,shi ya dinga kallo abin yana birge shi har barci ya fara daukar shi sannan ya kashe wayar yayi addu'a ya kwanta.


*yau kuwa nayi muku typing da yawa saboda farin cikin ku,sannan wata ƙila anjima ku kuma samin wani amma kuyi haƙuri da jiya ina kuma godiya masu kirana a waya da maso turo mini da saƙo na gode sosai Allah ya bar ƙauna*.


#LIKE
#SHARE
#COMMENTS

*babyn Abdul maman meenal,Farouk da Elham*.

*ƳAR MUTAN ZAZZAU*


♥ ❤

♥♥❤
*~K'AREENATEEY~*
(K'AWATA)

(It's all about friendship)





https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/



*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


*YAN UWA MUNA KARA KIRA DA MABIYA LITTAFAN GOLDEN PEN WRITTERS ASSOCIATION DA SU KIYAYE DA WANNAN MAI CUTAR TASU DA SUNAN YANA SAIDA LITTAFAN KUNGIYARMU,TO KARYA YAKE MACUCI NE KAWAI LITTAFANMU IS FREE 1 NE KAWAI NA KUDI,KUMA DA YACE YANA BA KUNGIYARMU KUDIN REGISTER DIN DA KUKE BIYA DOMIN MU TURA MASHI SABBIN LITTAFAN MU,TO WALLAHI DUK KARYA YAKE MANA MU BAMU DA MASANIYA AKAN WANNAN B'ARNAR DA YAKE MANA SAI DAGA BAYA MUKA JI,SANNAN KUMA INA SON KUSAN NUMBER DIN SHI SABODA YANA NAN YANA SHIGA GROUPS NA MATA DA SUNAN MACE SABODA HAKA KU KIYAYE GA NUMBER DIN SHI NAN (08107707692)*




*written *✍
-by-
*Deeja one love*




*JAKADIYAR GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION👸*



Wattpad 13deeja.


Daga wannan page d'in har zuwa k'arshe sadaukarwa ne gare ki *AISHATU BABAYO* saboda kaunar da kike wa *GOLDEN PEN WRITERS* ba muda abinda zamu biya ki dashi, dan haka *K'AREENATEEY* har zuwa k'arshe ya zama naki sis kiyi yadda kike so dashi, *JAKADIYA* ta baki wannan yan shafukan har zuwa karshe, muna godiya sosai da irin kaunar da kike mana.



*_Manzon Allah tsira da amincin Allah sun tabbata agare shi yace"Allah yana cewa:ni ina a inda bawa na yake zato na,kuma ina a tare dashi idan ya ambace ni,idan ya ambace ni a ran shi to nima zan ambace shi a raina,idan kuma ya ambace ni a cikin taro,to nima zan ambace shi a cikin taron da yafi nashi alkhairi,idan kusance da ɗani ɗaya zan kusance shi da kamu guda,idan ya kusance ni da kamu guda zan kusance shi da gaba guda,idan yazo mini yana tafiya zan zo masa ina sassarfa_*

_~*bukhari da muslim suka ruwaito*~_.

*wallahi yanzu kam har kunyan baku haƙuri nake ji,amma dai duk da haka am sorry ku dai cigaba da haƙuri akan ce haƙuri cinikin annabi*.

*ba zan gaji da gode muku ba,Fatima zara,Aishatu babayo,Ebraheem Aliyu,Hajjaju,Farida atiku,Khadija z,fiddausi,sunan ku ba zai lissafu ba ina godiya sosai da sosai*.


*Wannan naku ne One love hausa novels da kuma ƙareenateey fans club saboda daɗin yadda kuke zuba comments hakan na bani sugar sosai*

Littafi ɗaya tamkar da dubu *Banfi ƙarfin ta ba* na *oum deedat* da kuma *Rudani* na sarauniya *beelat*,fans ku nema ku karanta kada ku bari a baku labari.




*_27_*


Da asuba me lalle tazo ta rangaɗa mini shi,ja tayi mini da ratsin baƙi kaɗan hakan yasa ya ɗau fata ta sosai.


Sai ƙarfe takwas sannan na wanke,Ummi haka ta dinga yabon shi wanda hakan shi ya ƙara tabbatar mini da Ummi yanzu ta canza.

Shaf-shaf na shirya cikin doguwar riga kalar ja ba me haske ba sosai,farin hijab na ɗora a sama.

Muna fitowa suma sauran mutanen suna fitowa wa'inda zasu je kenan,motar gida gaba ɗaya muƙa shiga.

A babban filin makarantar Ƴan ayaba wacce take sabƙn gari ake yi,mutane har suɓ fata taruwa.

Jana Rufaida tayi muka shiga cikin kasuwa,shagon wata bayerabiya me gyaran kai ta kaini.

Nan ta barni yayin da su kuma suka shiga cikin kasuwa,basu wani daɗe ba suka dawo kamar yadda matar itama bata daɗe ba ta gama dan bana son a gasa mini gashin dan haka wankewa kawai tayi ta dhafa mayuka ta taje.

Rankayawa muka yi muka koma harabar inda ake koyarwar ɗin wanda har an riga da an fara.

Anyi walima an tashi lafiya walima kuma ta ƙayatar da har me girma iyan zazzau ya halarta kuma ya bada tashi gudummawar.

Rufaida ta amshi kyautar mafi hazaƙa a cikin ɗalibai wanda haka ya faranta ran kowa.

Khairiyya taja tsaki,dafa yanzu da

1 Comments On KAREENATEEY
avatar
hauwa-8-2

1 year ago

Reply

Mashaa Allah

Please Login or Register in order to submit comment