Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yayi yana tuno lips dinta a lokacin da take cuno shi gaba,bude ido yayi da sauri yana jan tsaki.



Kaya ya cire ya shiga wanka, abinda ya bashi mamaki yadda har lokacin bata shigo ba, jinjina kai yayi yana fadin"lallai kin rainani zan yi maganin ki".



Yana gama saka kaya ya kunna news yana kallo a bbc news english yana karkada kafa, babu abinda yake son ci irin girkin data dafa.




Tsaye nake bakin kofa ina wasi-wasi shin in shiga ne ko kuma in koma, can dai nayi shahada nayi sallama na shiga.




A zaune yana kallon news na same shi,jiki na har bari yake na karasa na ajiye a center table dake gaban shi, har na juya ya janyo hijab dina, kasancewar a tsorace nake yasa na tafi luuu na fada jikin shi,da sauri na mike ina kokarin gyara hijab dina, a zuciya ta ina istighfar.



Kallon shi nayi, kamar ba shi ba sai ma cigaba da yayi da kallon shi, cikin hanzari nake kokarin barin wajen, take mini kasan hijab yayi.



A hanakli hawaye ya zubo mini, domin matse mini wuya da yayi,tsugunawa kawai nayi a wajen ina share hawaye.




Fin minti goma sannan ya mike tsaye,ina ganin ya matsa daga wajen nayi saurin mikewa,hannu yasa ya finciko ni yace"ke wai wace irin dakikiya ce baki san ki zuba mini abincin bane ko kuwa so kike ni na zuba",ai kamar ya kara tsorata ni hannu na bari na fara zuba mishi.



Shikam waya ya fara dannawa ta kasa kuma yana satar kallo na, ji yadda tasa yake neman ya sake wani wankan kai wannan yarinya daga gani fitinanniya ce,tsaki yaja.



Cikin sauri na fara bashi hakuri,harara ya galla mini kan ya fara cin abincin,cokali daya kawai yakai, ya mike,ya zuba mini abincin a jiki,ihu nayi domin da zafi sosai,wanka mini mari yayi, kafin ya kama hannu na.




Bathroom din shi ya kai ni, fuska a daure yace"kiyi wanka", daga haka ya fice, hijab dina na cire sannan na fara wanka,na dade sosai sannan na gama.



Leko wa nayi,babu kowa a dakin, cikin sanda na fito,a gefen bed din shi naga wata doguwar riga, da sauri na dauka na saka, man shafar sa na shafa.




Ina gamawa yana shigowa, duk yadda yaso ya kauda kan shi kasawa yayi domin rigar ta amshi jiki na,cikin rawar jiki ya karaso inda nake.

Ni kuwa yadda naga ya taho na dauka laifi nayi, ai kuwa cikin sauri na tsuguna ina bashi hakuri.




Kasa cewa komai yayi kawai janyo ni yayi ya rungume yana mai da numfashi.....


















♥ ❤
♥♥❤
*~K'AREENATEEY~*
(K'AWATA)



*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*






*written *✍
-by-
*Deeja one love*

~Dedicated~

To


*~Aisha yunus(eesher lurv)~*


Wattpad 13deeja



*ADDU'AR HAWA ABIN HAWA*


_Subhanallazi sakhara lana haza wama kunna lahu muk'urineen wa'inna ila rabbina la munk'alibuun_.



*YA AR-RAHEEM

_*3*_



Jiki na ya dauki rawa, ganin bazan iya kwatar kai na bane yasa na fara hawaye, a sanyaye ya sake ni.




Idanun shi a lumshe yace"kije ki kawo mini abinci pls".


Har na juya zan fita ya riko hannuna ya kuma cewa"pls ki dafa mini da kan ki, kinji? ", daga kai nayi kawai na tafi.




Ko a hanya tunani nake me yake faruwa da yaya khaleel ne? Kamar bashi ba,ji nayi nayi karo da mutum da sauri na dago.




Aunty fauzah(yar wan baba na, amma a dayan gidan take),jiki na na rawa nace"yi hakuri aunty".



Kallon up and down tayi mini, sannan ta daga hannun alamar na tafi, har na juya ta janyo ni,hancin ta tasa a jiki na ta shinshina.



Cikin sauri ta kalle ni tace"daga ina kike?,da sauri nace"dakin yaya abdus-samad",jinjina kai tayi tace"ya naji kamshin turaren yaya khaleel a jikin ki? ".


Dan daburcewa nayi amma haka na daure na waske da cewa"mun dai hadu a hanya ne yace na kawo mishi abinci".



Kallon raini tayi mini tace"ki bar shi na riga da na dafa mishi, so baya bukatar naki",daga kai nayi nace"to aunty", daga haka na wuce.



Dai-dai palourn baba na gan shi, kamar yasan zan bullo ya zubawa hanyar idanu hakan yasa ina dago ido muka hade.



Murmushi muke jifan juna dashi,cikin farin ciki na karaso,da mamaki yace"daga ina haka? ".




"Wajen yaya khaleel mana, kasan idan ya dawo bana samun lokacin kai na", na fada idanu na cikin nashi.




Yanayin fuskar shi ya canza,dama nasan hakan zai faru domin baya so ka fadi wata magana akan dan uwan shi.


A sanyaye yace"kiyi hakuri kin san kani na,wata rana sai labari".



Dariya nayi ina rufe fuska, magana nayi niyar yi amma fitowar baba yasa na fasa.




Gaishe dashi nayi sannan na wuce,ina tafiya ina juyowa haka shima yaya khaleed ina tafiya yana kallo na har sai da na shiga bangaren mu.




Ajiyar zuciya nayi sannan na karasa kitchen,cous-cous na dafa jallop da yaji vegetables da hanta, sai kamshi yake tashi.




Pineapple juice na hada, sai zubo da yaji kayan kamshi sannan na hada komai a basket na fito.



Da ummi mu kayi karo, cikin sauri na kauche nace"sannu ummi", bata amsa ba sai kallo na da take yi.




Cikin sauri na kalli kayan kayan jiki na, tunawa nayi da yadda akayi na sa su,zaro idanu nayi.


Daure fuska tayi tace"a ina kika sami kayan nan? ",cike da tsoro na bata labari(dan bata yi mana tarbiyar yi mata karya ba)sai dai na boye mata watsa mini abincin da yayi na dai ce mata abincin zubewa yayi a jiki na.




Tace"to shikenan, nasan kina da kula dan haka dan allah ki kara kulawa", duk da ban fahimci inda maganar ta ya sa gaba ba na daga kai alamar to.



Cikin sauri na wuce, ita kuma ta bini da kallo har na fita, ta daga hannu tana addu'ar allah ya kare mata yaran ta.





Sauri nake domin ina so na kai mishi na dawo,da sallama na shiga cikin dakin, aunty fauzah na zuba abinci a plate shi kuma dan mulkin yana zaune ya dora kafa daya kan daya yana daddanawa waya.



Ina yin sallama suka d'ago a tare,harara aunty fauza ta galla mini,cikin daka tsawa tace"uban me ya dawo dake? ".




Cikin sark'ewar murya nace"ki..... Yi...... Kiyi..... Hak'u...... Ri..... Aunty abin...... Ci na......
Kawo..... Mishi".



Kallon rainin wayo tayi mini tace"amma me nace miki, bana ce kada ki sake ki dawo nan ba, wato ke bakya jin magana ko?, to koma kafin na tsinka miki mari".




Cikin rawar jiki na juya,a natse yace"kiyi sauri ki kawo mini yunwa nake ji",kallon shi muka yi a tare kamar bashi yayi maganar ba.



Duka mun san da wanda yake a cikin mu dan haka yasa ta mini wani kallo, wanda yasa da sauri na fara tafiya.




Taku biyu na yi naji an finciko ni, saura kadan abincin ya zube,cikin ido na ya kalla yace"ina wasa dake ne da zan yi magana kiyi banza dani?,wuce ki zuba mini abinci".



Da sauri na wuce shi kuma ya biyo baya na, zama yayi ni kuma na fara zuba mishi abincin, sai da na ajiye mishi komai sannan na koma gefe na tsaya domin nasan ina cewa zan fita zan kuma wani laifin ne.




Cikin fushi aunty fauzah tace"dan allah yaya khaleel meye hakane ya za'a yi nayi maka girki baka ci ba amma kaci na wannan kwailar".




Kamar ba zai tanka ba can kuma yace"ita kwailar ni na sata tayi mini, kefa nace kiyi mini ne? ",cikin hasala ta tattara kayan ta ta mike kallon zaki gane kurenki tayi mini sannan ta juya ta fice.



Ni dai kai na na kasa ina tunanin abinda zan fuskan ta dan nasan ba bari na zata yi ba, saukin ta ma kawai yaya khaleed zai tsawatar mata.



Kallon shi nayi, cin abincin shi ma akwai isa da iko, tauna yake kamar wanda baya sotabe baki nayi a raina nace"ina tausayawa matar ka da wannan mulkin".




Cikin k'asaita yace"dama ina so na tambaye ki, shin karatu kike so ki cigaba ko kuwa aure kike so kiyi? ".



Kaina a k'asa nace"ina so na cigaba da karatu sai dai ban da tabbabcin baba ko zai bari".



Da sauri yace"tambayar da nayi miki eh ko a'a",sai da nayi jimm sannan nace"eh,", daga haka be koma cewa komai ba.



Yana gama ci ya mike, kallo na yayi yace"had'a mini ruwan wanka,daga nan ki dauki wancan jakar ki kaiwa abdus-samad sai ki wuce bangaren mama na kice system dina yana kan bed din ta ta baki".




A natse na mike na shiga cikin bedroom din, da idanu ya bini har na shige, lumshe idanu yayi kawai domin gaba daya komai na jikin na idan ina tafiya sai ya motsa.





Kamar yadda ya buk'ata haka nayi, sannan na d'auki jakar na fice,k'ofar d'akin yaya abdus samad na k'wank'wasa.



Yana budewa farar rigace a jikin shi sai wandon su na sojoji, mik'a mishi jakar nayi, sannan nace"inji yaya khaleel".



"To shikenan,na gode ki gaida maman ki", daga haka ya rufe k'ofar.



A natse na nufi bangaren abba, ina shiga muka yi karo da yaya khaleed, murmushi yayi mini nima haka.



Yace"sai ina? ",nace"wallahi yaya khaleel ya aiko ni wajen mamie wai na amso mishi laptop d'in shi".




"Wai har yanzu bai rabun mini dake bane, domin ki samu ki huta",d'aga kai nayi nace"kada ka damu na saba in dai yana gari ai dama haka ne".




"Muje na raka ki",jerawa muka yi har ciki, a kunyace na gaishe da ita, ita kam murmushi tayi domin tana matuk'ar jin dad'in yadda nake yi.




Yaya khaleed ya rik'o laptop d'in muna tafe muna fira har bakin k'ofar d'akin,sai da muka d'an tsaya yace"hulwaty wallahi na k'osa abba yayi magana akan auren mu".



Jingina nayi nace"kada ka damu, insha allah lokaci kad'an zan zama mallakin ka".



Mik'o mini laptop d'in yayi yace"idan allah ya kaimu gobe baba k'arami yana dawowa zan tare shi da maganar dan naga so kike ki mini salalan tsiya".



Ina dariya na amsa na shige ciki, ina sallama ya fizgo ni ya matse, idanun shi sun kad'a sunyi jaa yace"bana hana ki tsayawa da yaya na ba".



Hawaye kawai ke zubo mini, tsugunnawa nayi k'asa jiki na yana rawa nace"kayi hak'uri yaya bazan kuma ba".


Hannu na dana dafe k'asa dashi yasa k'afa ya take, ihu nayi yasa hannu ya matse bakin, yanzu kam ko'ina na jiki na yana amsa wannan wahalar da nake sha.




Kukan ma babu hawaye, sai da ya gaji dan kan shi ya d'aga hannun, nuna ninyayi yace"ba naji yana magana akan auren ku ba".



"Anjima zan sami baban gida na gaya mishi karatu kike so nasan zai ce a tambaye ki".



"Idan kika sake kika ce aure kike so, kin ga wannan", karamar bindiga ya zaro, jiki na ya hau rawa, ban yi aune ba naji fitsari yana zubo mini.



Ya saita kaina da ita yace"sai na dauke numfashin ki gaba d'aya kina jina", kai na d'aga kamar k'adangaruwa.



"Tashi ki fice ki bani waje", kan ya rufe baki na bawa buje na iska, sai da na ganni a part d'in mu sannan na tsaya ina maida numfashi.





Wucewa nayi na shiga d'akin mu na kwanta,wai me yake damun yaya khaleel ne? Tambayar dana ke yiwa kai na kenan.



A sanyaye ranar nake har dare, sai da naje makaranta na dawo sannan na had'u da khairiyya, harara ta aika mini tace"wallahi kin cika mara mutunci dazu ma yaya yake cewa wai ina kike? ".




Murmushi nayi nace"kiyi hak'uri na manta ban biya miki ba",harara ta ta kuma yi tace"ba wani nan,yaya khaleel kike guduwar wa ai kowa ya sani".



Shiru nayi bani da abin ce mata domin kowa yasan hakan ne, ni kai na na yarda da hakan to amma ya zan yi.



***** ***** *****


Yaya khaleel ne zaune gaban baban gida kan shi a k'asa bayan ya gama koro mishi bayani.



Jinjina kai baban gida yayi yace"amma kasan hakan be tab'a faruwa ba ko,ace yarinya ta wuce secondary a gidan nan hakan bai tab'a faruwa ba".



K'ara kasa da kai ya kuma yi yace"baban gida shi yasa nazo wajen ka, domin ba zan iya tarar abba ko baba malam da wannan maganar ba, kuyi hak'uri ku bar ta ta cigaba da karatu tun da tana so, dan allah nasan idan ka amsa babu wanda zai k'i".





"To shin da kazo nan me kake so nayi?,tunda kasan hakan baya faruwa".



"Baban gida taimaka mini zaka yi,tun da har tana so,ya kamata ace kun duba dai ku gani".



"Ka bari zan yi shawara da yan uwa na, wannan ba abin da za'a yanke da wuri bane, ku tashi ku tafi".



Mikewa suka yi, shida abdus-samad, suka yi mishi sallama suka fice.



Kamar jiran fitowar su take, ta taho da sauri cikin yanga da iyayi.


"Sannu da fitowa yaya na, nazo ai aka ce kana wajen baban gida, shine nace bari na jira k....... ".




Kallon da ya aika mata ne yasa tayi shiru, dogon tsaki yaja yace"uban waye yace ki saka wannan kayan,bana hana ki bane ba kyajin magana ko? ".




Kallon kayan tayi,doguwar riga ce ta material,amma fa tabi jikin ta dan kamar zata yage idan tayi k'wakk'waran motsi.



"Wuce kije ki cire ki kawo mini kayan nan wajen",ya fad'a cikin daka tsawa,cikin sauri ta nufi bangaren su tana cuno baki.




Bata dad'e ba ta dawo da kayan a hannun ta, amsa yayi sannan suka tafi.



Dariya taji ta bayan ta, tana juyawa ta ga fauzah ce,had'e rai tayi, fauzah tace"na gaya miki ai yaya khaleel nawa ne, ni kadai dan haka ki dena wahalar da kan ki, sumayya".



Daga haka ta wuce ta tafi tana dariya,ita kuwa sumayya kuka ta fashe dashi sannan ta nufi hanyar dakin mahaifiyar ta.





Khaleel tun da yaje daki babu abinda yake tunani sai maganar da suka yi da baban gida,dafa shi abdus-samad yayi yace"dan uwa kana cikin damuwa ne".




"Wallahi abdul yau naje wa baban gida da maganar karatun juwairiyya shine nake tsoron kada yaki yarda".




Murmushi abdus-samad yayi yace "ni kuwa sai nake gani anya ba son yarinyar nan kake ba".



Da sauri ya mike yace..............











♥ ❤
♥♥❤
*~K'AREENATEEY~*
(K'AWATA)

(It's all about friendship)

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*





*written *✍
-by-
*Deeja one love*

~Dedicated~

To


*~Aisha yunus(eesher lurv)~*


Wattpad 13deeja


An karb'o daga abu huraira Allah ya yarda dashi yace:manzon Allah tsira da amincin Allah sun tabbata a gare shi yace: *duk tufar data wuce idon sahu to tana wuta*.



*_4_*



"Ni allah ya kyauta, na rasa wacce zan so, sai wannan yarinyar me take dashi wanda nake bukata, pls abdus-samad mu dena kalar wannan mana".




Da yake yaya abdus-samad mutum ne mai saukin hali be kuma cewa komai ba,yaya khaleel kuwa wayar shi ya dauka ya fita.




Washe gari da wuri na tashi domin yin ayyukan da na san zan yi, kasancewar ranar karshen mako yasa bayan na gama abinda nake yi na kwanta.




Barci nake yi cikin kwanciyar hankali kasancewar ba zan je makaranta ba,cikin barci naji ana tashi na,cikin nauyin idanu na bude su, suna rufewa.



Ganin khairiyya yasa nayi tsaki nace"haba khairiyya meye hakane? Kin wani tashe ni ina barci".



"Wallahi sis ba haka bane, yaya kahleel nima ya taso ni akan wai in kira ki,nazo na tarar kina barci naje na gaya mishi, saura kadan ya mare ni wai naje na taso ki, shine fa na taho".




Tsaki na ja nace"wallahi wannan matsala yake son zamowa a rayuwa ta ya ilahi!, yanzu yana ina".




"Dakin shi mana, wai ni wannan shirin da kuke yanzu na kasa ganewa kodai akwai wani abu ne a kasa? ".




Mikewa nayi ina hararar ta na fice, kamar yadda na zata falon babu kowa sai tashin karatun alqur'ani.




Cikin natsuwa tare da tsoro na isa bangaren su,sai da nayi sallama sannan na shiga.



Gaba na ya fadi ganin aunty fauzah a zaune ta dora kafa daya kan daya, gefen ta kuma sumayya ce tana faman danna waya, ko wacce fuska a daure.




Murmushi nayi bayan na kalli yadda gaban kowacce kayan kuloli ne.




Fitowa yayi daga bedroom d'in shi,k'ananan kaya ya saka sai kayan yayi mishi kyau soaai.





Da sauri nace"Ina kwana",Be amsa ba sai cewa da yayi"Ki nema mini abu mai sauk'i kiyi sauri ki dawo",Har na juya yace"amm pls kiyi da kan ki".






Ban jira komai ba na fice,fauzah ta dube shi tace"haba yaya khaleel ga abinci nayi maka,Wanne kake son ci".




Haramukull sumayya tayi kafin tace"yaya kaga fa na had'a maka break fast fa", Idan ke daba kya gidan kin tanka to ya tanka musu.




Ni kuwa ina shiga gida na wuce kitchen,gas na kunna sannan na dora ruwa,Kunnun gyada nayi mishi da egg rolls,sai coffee da milk shake,sannan nayi pepper soup na kayan ciki.



Da sauri na shirya kayan a basket sannan na fita,Nayi mamaki domin kuwa suna zaune a d'akin har lokacin.




Sai da nayi serving d'in shi sannan na koma gefe na zauna,hararar da suka yawan jefo ni da ita yasa nayi saurin kauda kai na.




Yana gamawa ya mik'e cikin bada umarni yace"ki tsaya ki gyara mini d'aki idan kin gama ki tafi da mukullin.






Amsawa nayi da to, sannan na kwashe kwanunkan, ina fita suka biyo ni.



Gaba na ya fad'i,cikin tsananin tsoro na fara basu hakuri,Aunty fauzah ta wanke ni da mari.




Ita kuwa aunty sumayya wuya na ta cakumo,sosai sika rufe ni da duka, kasancewar ba cikin gida bane, duk ihun da nake babu wanda ya jiyo ni.




Da kan su suka gaji suka kyale ni,haka na mik'e na nufi cikin gida,ina zuwa kitchen na ajiye kwanukan ummi ta shigo.



Da kallo ta bini kafin tace"ke kuma meya same ki? ",kai na a k'asa nace"ummi faduwa nayi".





"Dan Allah ki k'ara kula sosai, Allah ya kiyaye gaba",daga haka ta wuce.





Fitowa nayi na shiga d'akin mu,kallon kaina nayi a madubi, yadda suka maida fuska ta,kuka nake ina tausayin kaina.





Ni ban saba hayaniya ba haka ban tab'a fad'a ba, fatan shiriya nake musu domin dai ni ban d'auki dukan da suka yi mini a komai ba.





Sai da nayi wanka na canza kaya sannan naje na gyara mishi d'akin na shi,ina gamawa na rufe na taho da keys din.





Koda na dawo ciki har na fara rawar sanyi,daki na shiga na kwanta,ina rawar sanyi, blanket na saka na rufe jiki na.






Dandanan jiki na ya dauki zafi,ina kwance har magrib,babu wanda ya shigo,abdul azeez ne ya shigo da sallama a bakin shi.





Da k'yar na iya d'ago idanuna da suka yi mini nauyi na kalle shi, Zaro idanu yayi yace"sweet meya same ki? ",na kasa magana sai hawaye dake bin gefen kumatu na.




Fita yayi babu dad'ewa ya dawo hannun shi d'auke da magani,balla yayi sannan ya mik'o mini.



Babu musu na bud'e baki ya saka mini,ruwa ya d'auko ya sa mini na sha, sannan na kwanta shi kuma ya juya ya fita, Sai a lokacin na samu damar yin barci.





Bangaren khaleel kuwa koda ya dawo yaga yadda na gyara mishi d'aki sosai yaji dad'i,bayan isha'i yana zaune duk yadda zuciyar shi ke mintsilar shi amma baya son ya mik'e.





Abdus-samad yayi sallama ya shigo,amsawa yayi yana bin shi da idanu,sai da ya fara bud'e fridge ya d'auko robar ruwa sannan ya k'araso ya zauna.





Abdus-samad yace"ka san usman da mahmoud sun bud'e studio? ",da sauri ya mik'e yana fad'in "what!,a ina hakan ta faru? ".





"Wallahi wai a sabon gari, nima d'azu naji ameer da Aliyu suna firar, watan shi hud'u kenan".




Dandanan idanun shi ya kad'a yayi ja,a zuciye ya mik'e ya fice daga d'akin cikin hanzari,Yaya Abdus-samad ya bishi da sauri.





Bangaren hajiya ya nufa,yana shiga ya tarar dasu a zaune duka kowa da littattafai a hannun su, kasancewar sun san yayyin nasu suna nan.





Ganin yadda ya shigo yasa duka jikin su ya hau rawa, babu wanda zuciyar shi bata kad'a ba gudun kada ace laifin shi aka gano, sai dai d'aid'aiku da basu da laifi mai yawa.



da kallo yake bin su kamar wanda aka tilasta yace"wallahi ba naji ana maganar kun bud'e studio ba,Allah yasa naji cewa kuna buga wak'ok'in 'yan iska da sauran abinda bai dace ba domin zubar mana da sunan gida,dukkan ku zan hukunta gaba d'aya".




Daga haka ya juya ya fice Abdus-samad yana bin shi a baya,kallon-kallo aka fara domin dai be fad'i suna ba balle a tantance.


Kowa hamdala yake da ajiyar zuciya jin ba laifin shi aka gano ba.

Sai dai anbatar studio yasa kallon duka ya koma kan Usman, zazzare idanu suka fara yi suna harare-harare.




Halima data kasance yayar su tace"Wallahi Allah ya shirya ku dai, ace wai har yanzu kuna rashin jin magana kamar yara k'anana? ".



K'asa kawai suka yi da kai, suna k'unk'unai,zata sake magana hajiya ta katse ta dole tayi shiru.





Haka dai karatun ya tashi ana ta k'ananan magan-ganu.






B'angaren khaleel kuwa, yana fita ya tsaya kallon B'angaren mu yake yi kamar me son zuwa.




Duk da cikar falon hakan besa ya kasa gano babu ita ba, to meya faru da ita kenan.




Yaya Abdus-samad ya dafa shi yace"kaje kawai idan kana so",had'e fuska yayi yana juyawa.





Yaya Abdus-samad ya girgiza kai yana mamakin hali irin na d'an uwan shi,bin shi yayi a baya.




Yana daf da shiga b'angaren su ya had'u da yaya abdulkareem(baban d'an mama),hannu ya mik'a musu suka yi musabaha.





Yace"ashe kun dawo, yanzu baban gida yace na kira ka",ya fad'a yana mai kallon khaleel,d'aga kai yayi alamar yaji kawai ya wuce.





Da idanu suka bishi, kafin yaya abdulkareem ya kalli yaya Abdus-samad yace"kamar ran shi a b'ace yake".





"Anya kuwa kawai dai tension ne yayi mishi yawa"yana fad'in haka shima ya wuce ya tafi.









Ina zaune Abdul'azeez ya shigo,zama yayi yana fad'in"ah lallai sweet kin warke",murmushi nayi nace"kada ka damu d'an uwa na warke sosai".





Ummi data fito yanzu tayi dariya sosai take farin ciki idan taga muna kulawa da juna,hafeeza tace"ukhty kin san meya faru? ".




Girgiza kai nayi, dariya tayi tace"yau yaya khaleel yazo yayi warning akan su yaya usman, kinga yadda suke zare ida........ ".





Ummi tayi saurin dakatar da ita da fad'in"ke dakata bana hanaki d'aukar k'ananan magan-ganu ba,haba mama na".




K'aramin tsaki naja nace"shiya sani wallahi, ni hakan be dame ni ba",ummi tayi mini dakuwa tana fad'in"gidan ku....... ", sallamar sa ta katse ta.




Tun kan ya k'araso k'amshin turaren shi ya iso hanci na, da sauri na kwanta ina runtse idanu.




Abdul'azeez ya tab'e baki,jikin shi sanye da shirt fara da kuma blue jeans, kayan ya amshe shi sosai da sosai.




Abokin shi ko ince d'an uwanshi haka kuma cewing gum d'in shi na bayan shi,zama yayi suka gaisa da ummi.




Cikim sakin fuska da wasa,Abdul'azeez ya juyar da kai yana d'aukar littafin shi ya bar wajen.




Cikin sauri ummi tace"Abdul'azeez baka ga 'yan uwan ka bane",ba tare da shakka ba yace"na gan su ai ummi, mun riga da mun gaisa tun d'azu, barkan ku da dare yaya", daga haka ya juya ya bar wajen.





Ba khaleel ba har tana ni kai na naji shock,murmushi khaleel yayi yana fad'in "hakane k'ani na,amm zan tafi dan Allah ummi ki bashi abinci ya kawo mana",yana fad'in haka ya mik'e.




Dariyar da nake k'unshewa ce ta fito hakan yasa ya duka suka juyo suka kalle ni, ganin hakan yasa na fara k'ak'alo tari.




Da sauri ya d'auko ruwan dake center table ya mik'o mini yana mini sannu,da sauri na amsa na

1 Comments On KAREENATEEY
avatar
hauwa-8-2

1 year ago

Reply

Mashaa Allah

Please Login or Register in order to submit comment