Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hau sha.




Ummi tace"wallahi ka ganta nan,tun d'azu bata da lafiya ma gaba d'aya", matsowa yayi ya tab'a wuya na yace"Allah ya k'ara sauk'i", daga haka ya mik'e ya fita.






Kallon Abdul'azeez nayi da yake kallo na nayi murmushi nace"yi hak'uri sweet wallahi dariyar ce na kasa rik'ewa".




Harara ta yayi yace"eh ai dole kice haka wallahi sweet babu amana",dariya nayi nace"wallahi akwai".




"Babu wani nan, ni na lura ma nafi damuwa dake",ummi ta dakatar damu ta hanyar cewa"ya isa haka,Abdul'azeez wuce muje ka kai musu".




Babu musu ya wuce,ina zaune ina tunani idan fa har ya kai to duka ne da hukunci zai biyo baya.



Fitowa yayi d'auke da tray a hannu, kallon ahi tayi ganin be damu ba yasa tace"sweet wai ka san me yaya khaleel zai maka kuwa".




"Eh mana, duka ne ko punishment daga shi sai me? ",mik'ewa nayi nazo na amshi tray d'in sannan nace"bari naje ni".




"A'a kada ki damu sweet kema zai iya hukunta ki ai",tafiya nayi ba tare da nace mishi komai ba.



Sai da na kai b'angaren shi sannan na kwankwansa,daga ciki yace"come in".





Cikin natsuwa na tura na shiga,yana zaune kan lap din shi laptop ce yake tapping,kujerar dake facing d'in shi kuma yaya Abdus-samad ne.





Yanzu singlet ne a jikkn shi sai wando three quater,idanun shi sanye da medicated glass.




Idanu ya zuba mini har na k'arasa kusa dashi,center table d'in dake kusa dashi na d'ora abincin.





Idanun shi akan hannu na wanda nake zuba abincin cikin natsuwa da takatsantsan,sai da na gama sannan na mik'a mishi.




Be amsa ba haka be dena kallo na ba, kamar wanda aka yiwa dole yace"kena saka ki kawo mini? ".



K'asa nayi da kaina gabana yana fad'uwa,ba tare da damuwa ba ya cigaba da cewa"to shikenan sai kije ki turo shi".





"Kayi hak'uri dan Allah",na fad'a ina yin k'asa da kaina,zuba mini idanu yayi kafin ya mik'e ya matso kusa dani.




Runtse idanu nayi gabana yana cigaba da fad'uwa, hannun shi yasa ya shafo marin da aunty fauza tayi mini.




Shi d'azu kwata-kwata be lura da shatin dake fuskar ta ba,alamun hannu gashi nan yatsu ya fito har guda uku.





Cikin sark'ewar murya yace"waye ya mare ki? ",na bud'e baki zanyi magana wayar shi k'ara, be kula ba ya kuma tambaya ta.






Cikin rawar murya nace"d'azu ne na yiwa ummi laifi shine ta mare ni", kallon da yayi mini yasa nayi saurin yin k'asa da kai.





Ajiyar zuciya yayi kafin ya juya ya kalli yaya Abdus-samad yace"tashi muje wajen baban gida yana nema na".



Yaya Abdus-samad bece komai ba ya mik'e,kallo na yayi yace"ki tabbatar baki fita ba,zanje wajen baban gida na dawo".



Be jira me zance ba ya juya ya fita,yana fita naja numfashi sannan na nemi kujera na zauna.




Shi kuwa can gidan suka wuce, koda suka shiga sun sami Abba da baba duka suna can.




Sai da suka gaishe da iyayen nasu sannan suka zauna,baban gida yace"to habeebu da Abubakar abinda yasa na kira ku nan shine,khaleel yazo mini da maganar yana so 'yar uwar shi mama na ta cigaba da karatu, ya kuke gani? ".





Abba yace"wannan shirmen banza ne ba zai yiwu ba wannan dokace a gidan nan saboda yana so ba zai tab'a yiwuwa ba ace saboda shi mu bar wannan dokar tamu".




Murmushi baban gida yayi yace"wannan ba uzuri bane", Baba yace"to amma ai ya san da hakan baya yiwuwa ko".




"Amma me zai hana mu bar shi ya gwada mu gani",baban gida ya fad'a,shiru suka yi saboda ba zasu iya ja da yayan su ba.




Baban gida ya kuma cewa"yanzu dai ku bari mahmoud ya dawo shima muji me zai ce, sannan kuma za'a kira yarinyar muji ra'ayin ta".





Kallon shi ya mayar kan khaleel yace"tashi ku tafi za'a sake zama nan da wani lokaci,amma yaushe zaku koma wajen aikin naku ne? ".




"Nan da jibi ne idan Allah ya kaimu",ya fad'a yana k'ara yin k'asa da kai, umarnin tafiya ya basu yana sake yi musu addu'a.



Sannan yace"idan har kun kuma dawowa zamu sake zama", daga haka suka fice.








♥ ❤
♥♥❤
*~K'AREENATEEY~*
(K'AWATA)

(It's all about friendship)

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*





*written *✍
-by-
*Deeja one love*

~Dedicated~

To


*~Aisha yunus(eesher lurv)~*


Wattpad 13 deeja

*ADDU'AR NEMAN SAUK'I NA AL'AMURAN DUNIYA*

Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahla wa'anta taja'alul hazna iza shi'ita sahla


an karb'o daga abu huraira Allah ya yarda dashi yace:manzon Allah tsira da amincin Allah sun tabbata agare shi yace"duk wanda Allah yake son shi da alkhairi sai ya jarabce shi".




*YA ALMALEEKU*



*_5*_


Ni kuwa ganin sun fita ga zaman ya ishe ni yasa na mik'e na shiga bedroom d'in shi,dube-dube na fara kamar wacce tayi ajiya.





Tsautsayi yasa na ga wani d'an k'aramin box akan dressing mirror,yadda yake da kyau yasa na nufi wajen domin na d'auka.




Ina k'arasawa k'afata ta bugi gefen dressing mirror d'in duka kayan dake kai suk zubo,zaro idanu nayi ina bin kwalaben turare wajen guda takwas da suka zubo.




Banda wata k'aramar flower da kuma wani glass me shape d'in curve,gabana ya fara dukan uku-uku.





Kafin nayi wani motsi yayi sallama ya shigo,da sauri na kalle shi sannan na kalli b'arnar da nayi mishi.




Shi kuwa tsayawa yayi yana kallo na ganin yadda na zaro idanu yasa ya nufo waje na,a matuk'ar tsorace naja baya ina fad'in "dan Allah kayi hak'uri".







Zaro idanu yayi ganin b'arnar da nayi mishi, had'e fuska yayi ya nufo ni, wayyo ji nayi kamar k'asa ta tsage na shige, kad'an ya rage fitsari be zubo ba.





Hawaye ya fara zubo mini,hannun daya d'aga yasa kuka ya kufce mini me k'arfi,jin saukar hannun shi a fuska ta yana shafa inda aunty fauza ta mare ni yasa nayi saurin bud'e idanu na.




Har lokacin fusakar nan a had'e take,cikin d'aure fuska babu wasa yace"waye ya mare ki? ",girgiza kai nayi.




Tsawa ya daka mini yana fadin"idan har kika kuma yi mini magana da kai sai na karya ki, bude baki ki amsa mini".




Cikin rawar baki jiki na na rawa nace"aunty fauza da aunty sumayya sune suka dake ni",idanun shi dan danan yayi ja,jijiyar kan shi ta mik'e.




Kallo na yayi idanu jajir yace"kwashe kayan da kika lalata b4 nayi ball dake a wajen", a be rufe baki ba na tsuguna na hau kwashe wa.





Zama yayi gefen bed yana murza hannun shi,daya daga ciki kwalbar ce ta caki hannu na, runtse idanu nayi.



Ga azaba babu damar kuka domin na san a yadda yake inayin ihu sunana sorry,hannun na runtse sannan ta cigaba da kwashe wa.




Ina gamawa ya nuna mini hanyar waje, ai bana ji ya sauke hannu na fice,jikina gaba d'aya kad'awa yake yi.





Dai dai shiga bangaren mu, nayi karo da mutum,ihu na saka dama gashi a tsorace nake ga kuma dama ni can akwai tsoro.




Da sauri yace"sweet daga ina yanzu nake ta neman ki, sai yanzu ya sake ki Allah yasa be ji miki ciwo ba".




Kasa tsayuwa nayi saboda yadda kafafuna ke rawa, tsugunawa nayi kawai na fashe da kuka, ga rad'adin ciwo ga kuma tsorata da nayi.





Abdul'azeez kuwa tsayawa yayi yana kallo na,mun fi minti goma a haka sannan ya tsuguna kusa dani.




Hannun shi ya d'ora saman nawa yace"please sweet ya isa haka, ki tashi mu shiga daga ciki,shi yasa tun farko naso ki bari naje da kai na".




Ni dai bance komai ba, ganin ba zan mike bane yasa ya d'auke ni cak kawai, duk da abdul'zeez kanina amma kuma yanayin girman mu ba d'aya ba.




Yana shiga ummi dake zaune tana karatu ta d'ago ta bimu da kallo, cikin tashin hankali take fad'in"lafiyar ta kuwa".



Ni dai shiru nayi har lokacin gaba na be dena faduwa ba,"ummi babu komai kawai dai faduwa tayi".



"Shine dan ta fad'i sai ka wani dauko ta haka,ke kuma katuwa dake ki rasa wa zaki zauna kina langwab'ewa sai k'anin ki, kin ji kunya wallahi".



Daga haka ta wuce ta barmu, shi dai Abdul'azeez be damu ba nima kuma ban ce ya ajiye ni ba saboda har lokacin ban dawo dai-dai ba.




Kan bed d'in mu ya ajiye ni, zama yayi kan bed side cabinet, ni kuwa ina kwance har lokacin ina zubar da hawaye.




Zaro idanu yayi lokacin daya lura da jinin daya b'ata riga ta da rigar shi, cike da tsoro yace"sweet me yayi miki ne?, ko yayi raping d'in ki ne"ya karasa maganar cikin jan ta.




Girgiza kai nayi alamar a'a, ajiyar zuciya yayi yace"da sauki ai ma", daga haka ya shiga bathroom din mu.





Bai jima ba ya dawo dauke da karamin bowl da ruwa a ciki sai karamin towel,hannun ya kama nan fa akw yin ta domin kwalbar na ciki.





Janye hannu na nayi ina hararar shi,kara kama hannun yayi ta karfi ya cire, sannan ya fara wanke jinin wajen.



Sai da ya gama sannan ya dauko first aid box ya k'ara gyara ciwon ya d'iga spirit.



A hankali na koma na kwanta na runtse idanu domin zafin da nake ji, shi kuma ya fice daga nan.





Shi kuwa uban gayya tunda ta nufi hanyar fita ya kafe ta da idanu,lallai yaran nan basu da hankali.




Kamar ya bari sai da safe amma yadda zuciyar shi ke azalzalar shi dole ta sa ya mik'e ya fita.







Direct gidan su ya shiga gidan ya fara tsit kasancewar tara ta wuce, bagaren su ya nufa,kwankwasa kofar yayi.




Duka yan matan wa'inda kenan suka mike jin ko waye kallon-kallo suka fara,daka musu tsawar da yayi yasa suka bud'e jiki na rawa.





Nafisat dake gaba ya kalla, ita kanta sai da gaban ta ya fad'i ganin yanayin idanun shi,cikin daka tsawa yace"ina fauza da sumayya".





Jiki na rawa tace"suna bangaren inna suna tad'i",be jira karashen maganar ba ya wuce cikin sauri.




Duka suka sauke ajiyar zuciya suna hamdala tare da tausayawa yan uwan su.




Firar da ake cewa no gap ita ya samu suna yi su uku ne kowacce da saurayin ta,kasancewar da duhu ba gane su zai yi ba yasa ya kirasu duka.





Tun da suka ji muryar shi gaban su ya fad'i,wayar hannun shi ya kunna haske ya gauraye wajen.




Sumayya dake farko ya wanke ta da mari, sannan zainab dake bi mata sannan fauza,duka dafe kumatu suka yi suna sauke kai k'asa.





Zainab cikin rawar murya ta fara fad'in"yaya dan Allah kayi hak'uri", harara ya galla mata yace"get lost b4 I scatter you",ai yana rufe baki ta fece.




Sumayya kuwa da fauza gaban su sai faduwa yake yi, kallon samarin nasu yayi kawai kowanne ya bawa bujen shi iska.




Cikin fushi yace"oya frog jump har d'aki na kuma idan har na riga ku zuwa call your self sorry",suna kuka haka suka tsugunna suka fara.




Gashi gidan ba d'aya ba daga ma cikin gidan nisane dashi kan su fito get,balle su shiga gidan nasu, saukin ta ma da yake suna shiga bangaren mazan yana daga bayan get ne.





Kan su fito bangaren baba ma har ya fice,hak suna kuka suna yi har suka fito, a bakin get suka same shi kallo d'aya yayi musu ya cigaba da tafiya.




Wato dai muguntar shi yau a kansu zata k'are,haka suka cigaba har b'agaren mazan, da k'yar suka k'arasa d'akin shi.





Yana zaune gefe kuma abdus-samad ne yana tapping phone d'in shi,suna shigowa ya bisu da kallon mamaki.




"Su kuma wa'innan fa me suka yi",banza yayi dashi sanin halin shi yasa yaja bakin shi yayi shiru.





up and down ya saka su, da k'yar ma suka iya mik'ewa suka fara,fauza da tafi sumayya gajiya biyu kawai tayi ta tsaya.





"Au ba zaki cigaba ba kika tsaya kina kallo na? ",kuka ta saka tana bashi hak'uri,ganin haka ya mik'e ya nufo ta.





Belt dake hannun shi ya dinga zuba mata tana ihu, tun tana tsaye har ta zube a kasa a wajen.




Ganin kamar ba'a hayyacin shi yake ba yasa yaya abdus-samad mik'ewa ya tare shi, da k'yar ya iya amsar ta.






Kama hannun shi yayi ya zaunar dashi sai da yafi minti goma sannan yace"wallahi daga yau ko hararar ta kuka kuma yi sai na b'alla ku a gidan nan, wato ku har kunyi girman da zaku hukunta wani kenan".





"First and last duk ranar da d'ayan ku ta kuma d'aga hannu ta mare ta saina d'auke numfashin ta get out".




Cikin jan jiki suka fice suna kuka,a bakin bangaren suka zauna suna zubar da hawaye,sumayya cikin kuka tace"wallahi dana san irin wannan wahalar zan sha da ban kula ta ba".





Fauza tace"nifa har da duka,amma dole mu rama a kanta",da sauri sumayya ta kalle ta tace"babu saka hannu na a ciki".





Abba ne yazo wucewa ya hango su zaune,"kai waye a nan", jin muryar Abba yasa suka mik'e da k'yar suna fad'in "mune Abba ".





"me kuke yi anan ne? ",ya fada yana haska su, da sauri suka yi k'asa da kai,sun bude baki zasu yi magana ya fito abdus-samad na bayan shi.





Da sauri jiki na rawa suka wuce babu ko waiwaye,Abba ya bisu da kallo kafin ya dawo da kallon shi kan su.




Murmushi yaya khaleel yayi yace"barka Abba da wannan lokacin",jinjina kai yayi yace"meya same su",babu ko d'ar yace"abba laifi suka yi mini na hukunta su".




Abba yace"Khaleel ka dinga rage wannan zafin zuciyar taka wata rana fa zaka yi dana sani,kaga wannan tsaurara musun da kake yi zafa su fand'are maka wata rana".





K'asa yayi da kai yace"Abba ayi hak'uri ",Abba yace"Allah ya kyauta", ya wuce.








Suma daga nan suka wuce inda zasu je,fauza kam da sumayya duka babu wanda ya kuma yiwa juna magana har suka isa b'angaren matan inda suke kwana.





Kowacce sai da ta gasa jiki sannan ta kwanta tana jan Allah ya isa a ranta.




Ni kuwa ban ma san lokacin da barci ya d'auke ni ba,Ko da Abdul'azeez ya dawo yaga ina barci komawa kawai yayi.




Mafarkin da nayi ne yasa na farka cikin sauri,share zufar da take tsatstsafo mini nayi, idanun da yaya khaleel ya zubo mini ne nayi mafarki wai har jini yana zubowa.





Aikuwa tsorata na kuma yi ina faman rawar jiki,jikin hafeeza na shige ina zazzare idanu addu'a duk da ta zo baki na.





Na dad'e kafin barci ya zo mini,ai kuwa da asuba dana farka kaina har sarawa yake yi saboda ban sami damar yin barci ba.





Ina sallar asuba na kuma na kwanta, ko ummi data shigo taga ina barci tayi mamaki domin hakan ba hali na bane.



Kallon hafeeza tayi da take karatu tayi ajiyar zuciya sannan ta fita.




Cikin shirin sojoji suka fito,kasancewar baba malam na gari yasa suka fara shiga domin yi mishi sallama acan suka tarar da yaya khaleed.




Suna zaune abdulhafeez ya shigo yace duka baban gida yana neman su har da baba malam d'in da yaya khaleed.





Duka suka mike suka tafi domin zuwa can d'in, yaya abdulhafeez kuma ya wuce b'angaren mu.




Duka muma ya kira,da ni da ummi sai Abdul'azeez,haka muma muka nufi can gidan duk muna mamakin kiran kona lafiya ne.







Muna zuwa muka tarar da falon cike da mutane duk wani babba na gidan yana wajen.




Sai da muka mika gaisuwa sannan muka zauna, gaba na yana ta faduwa domin dai na san irin wannan zaman baya wuce maganar aure.





Baban gida yayi hamdala ya godewa Allah sannan yayi salati ga annabi,Abba ya bude taro da addu'a.




Baban gida ya dube mu duka yace"Abinda yasa na tara ku anan shine,maganar yaran mu da suka isa aure".




"Kamar yadda kuka sani tun farko yarinya bata wuce karatun secondary a gidan nan,muke aurar da ita,to har yanzu haka ne".





"Dan haka a yau zamu saka lokacin bikin yaran da suka isa aure,na farko akwai fatima ita da abdulhafeez,khairiyya da abdus-samad,rufaida da khaleed, sai sumayya da fauziyya ku har yanzu muna jiran isowar naku".





"Sai mama na wacce ita kuma a shekaranjiya muka yanke hukunci kamar yadda d'an uwan ta yazo mana da cewa yana so ta cigaba da karatu,sai kuma jiya khaleed yazo mini da maganar auren ta".





"Sai dai na bashi hak'uri kansancewar an riga shi magana akan ta,to kamar yadda khaleel na fad'a maka zan yi tunani akai, na riga da na yanke hukuncin mun barta zata cigaba da karatu kamar yadda ka buk'ata, sai dai ka sani akwai sharudd'a idan ka yarda shikenan".





"Na farko shine zaka d'auki nauyin karatun ta tunda kai ka bukata,na biyu kuma duk abinda ya faru a bayan karatun ta to hukuncin da muka yanke dole ka d'auke shi, sannan na uku shine duk laifin da tayi zaka dauka sannan tare zamu hukunta ku, ka yarda? ".





Ba tare da wani nuna damuwa ba yace"eh na yarda baba insha Allah babu abinda zai faru",baban gida yace"mama na kinji hukunci da kuma alfarmar da d'an uwan ki ya nema kin yarda kema".





D'aga kai nayi na kalle shi, wata uwar harara ya galla mini,ban san lokacin da jiki na ya d'au rawa ba,duk yadda naso na kalli yaya khaleed kasawa nayi.




Haka na saukar da kai na k'asa cikin girmamawa nace"eh baba na amince",baban gida yace"to alhamdulillahi Allah ya taimaka",kad'an daga wajen ne suka amsa.





Baba ya rufe taro da addu'a, ai tun kan a bar falon aka fara magan-ganu, kowa da kalar tashi.




Ni dai ina tsugunne sai da abdul'azeez yazo ya d'aga ni, hannu na ya rike kam ya jani muka fice.





Duk maganar dake tashi dan inaji cikin matan baba suna cewa"dama ai kowa yasan 'yayan ta sune yaran gata a gidan nan",wata ta kuma cewa"waya sani ko shima dai son ta yake yi,wannan hukuncin ai babu adalci a ciki".





Maman su yaya khaleel tace"hmm ni bani da abin cewa tunda shi ya gani yaji zai iya ba shikenan ba".





Ni dai bance komai ba haka shima abdul'azeez d'in,wucewa kawai muka yi.





Muna shiga get muka tarar dashi a tsaye ya d'aura hannayen shi duka biyun akan fuskar shi,gefen shi kuma yaya abdus-samad ne yana waya.





Kallo d'aya nayi mishi na kauda kai,kamar daga sama naji yace"ke zo nan",tsayawa nayi na kalli abdul'azeez, shi kuwa murmushi yayi mini sannan ya saki hannu na.



Kamar me tsoron taka k'asa ko kuma mai irga takun ta nake tafiya, daga gefe kad'an na tsaya.





A hankali ya sauke hannayen shi sannan ya bud'e idanun shi,yaya abdus-samad daya gama waya shima mu kawai ya zubawa idanu.






"Zamu tafi yau,ga wannan takardar post ume din ki ce jiya nayi miki registration",ya fad'a yana mik'o mini.




Hannu nasa na amsa,kudi ya kuma miko mini yace"gashi wannan na transport ne da abinda ba za'a rasa ba",na mik'a hannu domin amsa sai ga bataliyar 'yan gidan mu.




Salati hajiya ta fara tana fad'in "na gaya miki maryam sai kin tashi tsaye, wannan ai su yake yiwa aikin",baba malam ya tsawatar musu yana fad'in"ban san jin komai kowa ya wuce bangaren shi".





Ba dan sun so ba kowacce ta wuce,shi kuwa ko a jikin shi,maman su ta kalle shi tace"idan kun gama ina son magana da kai".





Da to kawai ya amsa,ni kuwa kud'in na rik'e ina wasa dashi,kaina a k'asa,d'agowa nayi saboda maganar da naji yana yi yace"amsa".





D'aya daga cikin wayar hannun shi ya mik'o mini yace"da sim da komai a ciki duk wani abu daya faru ki kira ki fad'a mini".





Amsa nayi ina godiya,bece komai ba kawai ya kalli yaya abdus-samad daya saki baki yana kallon mu yace"muje ko? ".





Yaya abdus-samad yace"momma fa tace kaje",cikin had'e rai yace"dalla malam muje na fika sani ai ni bana cikin shirmen gidan nan".





Ya k'arasa yana bud'e mota, juyowa yayi ya kalle ni yace"da wani abu ne? ",girgiza kai nayi, "to bar nan kafin na karya ki",cikin sauri na wuce.




Shi kuma ya shiga mota suka tafi,tab lallai halin wannan da ban ne, ji kamar wani mai aljanu yanzu zai yi dariya anjima ya d'aure.




Dai-dai bakin falon baba malam na hango yaya khaleed kallon da yake mini ne yasa jiki na yayi sanyi.



Bece komai ba ya juya ya shiga falon, jiki a sanyaye na wuce,ji nayi an janyo ni ganin momma yasa nayi saurin yin k'asa da kai.





Kallo ta bini dashi kan tace"ina kudin daya baki,jiki na rawa na d'auko na mik'a mata,amsa tayi tana fad'in"Allah ya taimake ki", daga haka ta wuce.




Ban damu ba dan na san wannan ba halin ta bane,kai duka ba halin gidan bane abin ne yazo a baibai gaba d'aya abinda be saba faruwa ba.





Ina shiga na sami ummi da baba malam a falo,sallama nayi suka amsa sannan na k'arasa na zauna.




Baba malam yace"dama kun yi hakan dashi ne mama na",d'aga kai nayi ummi ta jefo mini harara.




Shafa kaina yayi yace"da kin sani da baki amince ba domin hakan zai canza tsarin gidan nan, amma gaba duk abinda zaki yi ki fara tuntunb'ar mu kinji".




"Insha Allah baba ba zan kuma ba, ummi kiyi hak'uri",baba yace "kada ki damu mu bamu yi fushi dake ba, yanzu ina khaleel d'in? ".




"Sun tafi,yanzu shi da yaya abdus-samad,",to tashi kije kin ji Allah yayi miki albarka",tashi nayi na amsa da ameen.





Ina shiga d'akin mu,ummi ta biyo ni,"ke kina ganin kin yiwa kan ki adalci kenan, maganar da zaki janyo mini a gidan nan bata damun ki ko? ".





"Ummi dan Allah kiyi hak'uri ",Dallah rufe mini baki, tun wuri ki kira shi kice kin fasa karatun idan ba haka ba wallahi zaki had'u da fushi na".




Bata jira me zance ba ta fice ta barni, kuka na fashe dashi wanda yayi dai-dai da shigowa abdul'azeez fitar ummin yasa shi shigowa.





Ganin ina kuka yasa yayi saurin k'arasowa yana fad'in"sweet meye hakane dan Allah".




Cikin kuka nace"sweet ummi na fushi dani",hannu na ya rike yace"sweet kada ki damu hakan da kika yi shine dai-dai wallahi yaya khaleel be ta'a birgeni ba kalar na yau, ki kwantar da hankalin ki zamu shawo kan ummi".





Ajiye wayar nayi da phone d'in na shiga bathroom domin yin wanka, ina wankan ina tunanin halin da nake ciki.





Ina fitowa na sami wayar a hannun abdul'azeez yana juyawa yana mamaki, kallo na yayi yace"sweet anya kuwa?, kin san wayar nan ta kai dubu d'ari uku da wani abu".




Zaro idanu nayi nace"da gaske sweet ni gaskiya ba zan iya rik'e wannan wayar ba, tab".




"Ai dama wannan maganar bata taso ba,ana ganin ta yanzu kin shiga uku a gidan nan fad'a zaki kima had'awa,yanzu abinda za'ayi ina kud'in daya baki? ".





"Momma ta amsa",na bashi amsa,"to kin gani ko?,kada ki fad'awa ko ummi ne cewa ta amshi kud'in yanzu abinda za'ayi shine zan siyo miki k'arama sai ki cire sim d'in ki saka a wannan ki dinga amfani da ita wannan kuma ki ajiye tukunna mu ga ya za'a kaya? ".





Ni kai na nayi na'am da zancen domin ko yayyen mu ba duka suke rike da irin wannan waya me tsada ba balle ni wannan kam had'a husuma ne.





A take a wajen ya cire mini sim d'in ya saka mini a wayar shi kafin ya siyo k'aramar, wancan kuma ya fita da ita zuwa d'akin su domin ya b'oye.




Zama nayi ina tunani lallai Allah ya bawa k'ani na basira idan ba haka ba da ban san ya zanyi ba.




Ko ummi ta san da wannan wayar ai na shiga uku balle kuma sauran yan gidan.





Momma dake cika tana batsewa ta kalli khairiyya tace"kinga yaron nan alamu ya nuna ba zai zo ba kenan tafiyar shi yayi".




Khairiyya ta tab'e baki tace"momma ina zai zo bayan ya sallami gimbiyar tashi,har fa da wannan wayar me tsada daya siyo ranar nan ya bata".



Da sauri momma ta mik'e tana fad'in "what harda waya fa kika ce",khariyya ta amsa da"wallahi da gaske nake harda waya ya bata na ga lokacin".




"Aikuwa

1 Comments On KAREENATEEY
avatar
hauwa-8-2

1 year ago

Reply

Mashaa Allah

Please Login or Register in order to submit comment