Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ita amma ina ita gani take ta zubar da kimar tane ta tsaya tayi wannan makarantar.

Wannan dalilin yasa makarantar ta ɗauki nauyin nema mata admission a ABU zaria,haka iyan zazzau kuma ya ɗauki nauyin karatun ta.

Ni kuwa hakan ba ƙaramin faranta raina yayi ba yayinda Khairiyya kuwa baƙin ciki kamar ta haɗiyi zuciya.

Babu wanda yabi ta kanta dan babu wanda ya gayyace ta,harkar gaban mu kawai muke yi.

Bata ƙara jin haushi ba sai da taga na amshi wayar Jabeer munata ɗaukar hotuna,ji tayi kamar ta kashe kanta dan haushi.

Bana ta tata domin kuwa yanzu ni bata gaba na,sannan itama Rufaidan ban ga ta wani damu da ita ba,da dai tazo rabon kayayyaki ta bata amma tun daga nan bata kuma saurarar ta ba.

Jabeer kuwa yana gefe jingine da jikin motar shi yana kallon mu yana dariya,haka muke ta hotuna fuskar mu ɗauke da farin ciki.

Wata haɗaɗɗiyar mota ce ta fuskanto inda muke,tayi kyau sosai,mu da bata ita muke ba ta hotuna muke yi saboda zama da Rufaida na koyi yawan hoto.

Yaya Khaleel dake gefen me zaman banza ya ƙura mini ido,ran shi a ɓace ganin yadda nake dariya.

Kallon guy ɗin dake jikin mota yayi ganin mu yake kallo yana dariya ya kuma ɓata mishi rai.

Runtse idanu kawai yayi,ji yayi wani irin ɗaci a maƙogoron shi,yana yacan yana fama da aiki ne abinda ya hana shi zuwa da wuri kenan.

Yaya khaleed shima yana tsaye yana kallon mu yana murmushi,shima dai Yaya Abdus-samad dashi yake tuƙa motar murmushi kawai yayi.

Ganin ba zai iya jure hakan bane yasa ya buɗe motar a zuciye ya fice,muna tsaka da hotuna kawai naga mutum a tsaye a kaina.

Sai da muka tsorata domin irin kallon da yake yi mana,hannu na ya riƙo,da sauri nace"Yaya......".


"will you keep your mouth shut and follow me",ya faɗa cikin daka tsawa,kusan duka mutanen dake wajen suna hada-hadar su sai da suka juyo.

Raina ya fara ɓaci duk da yadda gaba na yake dukan uku-uku,Jabeer kuwa sarautar Allah ya zubawa ido.

Ganin da gaske tafiyar zai yi dani yasa yace"amm buddy phone ɗin",dan ya san yaya na saboda yadda muke ɗiban kama kuma jini dama ba wasa ba.

Yaya khaleel kuwa cak ya tsaya,cikin mamaki ya maimaita sunan"Buddy!",juyowa yayi yana kallo na.

Ɓacin rai,tashin hankali da zallar kishi duka na hango a cikin idanun shi,kamar na saki fitsari haka nake ji.

Hannu ya sa ya fizge wayar,cikin ran shi yana mamakin yaushe na koma haka?,Hajiya da Aunty da yake dasu muka zo babu wanda yayi magana a cikin su.

Wayar ya ɗaga ya buga da ƙasa,Jabeer cikin mamaki yace"what!my phone!",riƙo mishi riga Yaya Khaleel yayi yace"don't dare do that againa,Guy biya shi kuɗin shi",yana gama faɗin haka ya finciki hannu na mota ya buɗe ya saka ni sannan ya zagaya shiga ya fizgi motar da gudu.

Wa'inda suka ga abinda ya faru sosai suka dinga mamaki,Jabeer kuwa ya tsuguna ya ɗauki sim ɗin shi.

Yaya Abdus-samad yace"ur account number?",cikin jin haushi yace"ka faɗa mishi talauci na be kai nan.....",wani irin naushi Yaya Abdus-samad ya kai mishi.

Cikin sauri ya kauce,Yaya Abdus-samad ya nuna shi yace"ka san waye shi,kada ka kuma haka idan ba haka ba zamu wuce barrack sai muga ƙarfin arziƙin mahaifin naka,kuɗi kuma is an order dole ka bamu domin cika umarnin oga".

Jabeer ya tsorata sosai sannan sai yanzu ya fahimci da sojoji ma yake gardamar,ga kuma lokaci ɗaya yadda Yaya Abdus-samad ya koma mishi.

Jiki yana rawa ya bada account number ɗin,Yaya Al'ameen yayi mishi transfer,Yaya Abdus-samad ya shafa kan shi sannan yace"good boy",Jabeer kuwa ya gama tsorata cikin sauri yace"thank you sir",jinjina kai kawai yayi sannan suka juya suka tafi.

Dole haka suka bi motat gida,domin kuwa oga ya tafi da waccen motar,gudu kawai yake shararawa a titi.

Ni kuwa ina gefe a maƙure,gaba na yana faɗuwa,ina tunani yanzu idan kuma su Hajiya suka riga ni komawa gida fa.

Mema yasa suka zo ne?,ya Allah!"haka nake ta tunani har muka iso hanwa GRA,unguwar shiru sai kukan tsuntsaye da suke tashi.

Muna tafiya ina kallon gidajen har muka iso wani gida,sojoji ne birjik a bakin gidan suna hada hadar su.

Ganin isowar motar shi yasa suka sara mishi,ɗaya daga ciki ya buɗe mishi ƙofa ya fito.

Ni kuwa ina daga ciki ina zare idanu,kamar wacce tayi ƙarya,har lokacin fuskar shi a haɗe take.

Cikin zafin nama ya buɗe ƙofar ɓangare na,hannu yasa ya finciko ni,yadda kika san zan kifa.

Har cikin gidan ya nufa,ganin haka fa ido na ya fara raina,cikin tsori nace"Yaya please kayi haƙur....".

Kasa ƙarasawa nayi saboda kallon daya jefo mini,idanun shi ya kaɗa yayi ja,ni kusa na sadaƙar mutuwa kawai zan yi.

Yana buɗe ƙofar ya jefa ni ciki,faɗawa nayi na buge da gefen stairs,ƙara na saki ƴar kaɗan.

Cikin sauri na miƙe,kallon shi nake shima kuma ni yake kallo,jinin inda na buge ya fara zubowa saman ido na.

Jiki na rawa kawai yake yi,gaba ɗaya ji nake kamar zuciya ta zata buga,kallan shi nayi saitin zuciyar shi kuwa ina kallon yadda take bugawa.

Takowa ya fara yi zuwa kusa dani,cikin ɗaga murya yayi yace"waye shi",cikin kiɗimewa nace"waye kenan?".

Banyi zato ba naji saukar mari,dafe wajen nayi,sannan na fara ƙoƙarin matsawa ganin babu hankali a tare dashi.

Tsoro na kada yaje ya mini illa,hannu yasa ya fizgo ni,jikin stairs ya tura ni,baya na ya bugi,rasa me zanyi ma nayi.

Gaba ɗaya na san yau tawa ta ƙare,kuka na saki,me cin rai,kamar wanda kuma aka ce ya tsaya.

Saki na yayi sai kuma ya juya ya nufi stairs ya hau cikin sauri,ni kuwa ina jin na shaƙi iska me daɗi na nufi ƙofa.

Sai dai abin ban haushi a ɓame na same ta,jijjigawa nayi ina kuka,ganin taƙi buɗewa yasa na zame na zauna a wajen ina cigaba da kuka.

Jabeer ya ja mini masifa,yau kwanana ya ƙare kaina na haɗa da gwiwa ina kuka,haka na dawo kamar wata marainiya.

Ga mara ta dake tsikara mini kaɗan-kaɗan,hijab ɗina ma duk ya ɓace da jini,shafa goshi na nayi sai yanzu nake jin zafin wajen.

Fuskar shi ya dafa,har yanzu fa yana jin muryar shi inda yake kiran ta da *buddy*,kenan shi ta yaudara sai da fa yace mata kada ta kula kowa me yasa sai da ta kula wani.

Wanin ma namiji,why juwairiyya? why?"ya faɗa da ƙarfi,fuskar shi ya kalla cikin madubi.

Shiru yayi zuciyar shi tana bugawa,be san meye ma ya saka shi yin fushi ba?,hannun shi ya saka cikin sumar shi.

A hankali yake sauke numfashi tsayin lokaci sannan ya fice daga ɗakin cikin sauri,wani ɗakin ya shiga babu daɗewa ya fito hannun ahi riƙe da ƙaramin kit na first aid.

Lokacin daya sauko har naci kuka na na ƙoshi,tsugunowa yayi dai dai kusa dani,fuskata ya leƙa,idona a buɗe yake sai dai hawaye da yake kwaranyowa.

Dafa ni yayi a hankali,cike da razana na ɗago kai na,ganin shi kusa dani ya ƙara ruɗani,hannu na na haɗa alamun ban haƙuri ina sakin kuka.

Shima kamar zai yi kukan ya ɗora hannun shi saman hannun nawa,girgiza mini kai yayi sannan yace"kin san fa kina da hawan jini amma kike irin wannan tashin hankalin?".

Cikin kuka nace"Yaya"wanda har murya ta,ta riga da ta dashe,hannu ya ɗora saman leɓen shi.

Kit ɗin ya fara buɗewa sannan ya fara dressing ɗin ciwon dake saman goshi na,idanun mu na sarƙe dana juna.

Be ɗau lokaci ba ya gama miƙewa yaya yace"ki tashi ki biyo ni",koda na miƙe har jiri ya fara ɗiba ta.

A haka na daure na muka hau saman stairs ɗin,ɗaki ya buɗe mini na shiga,kallo na yayi fuskar shi ɗauke ɗa murmushi yace"kiyi wanka kinji".

Ɗaga kai nayi,murmushi yayi yana matsowa daf dani,kashe ido ɗaya yayi yace"ko na saka ki kiyi wankan tsarkin ne".

Zaro idanu nayi kafin na juya da sauri na riƙo hannu na,juyowa nayi na kalle shi fuskar shi ta nuna alamun damuwa sosai.

Cikin sanyin murya yace"pls Juwairiyya kada ki kuma bari Ummi ta raba mu",shiru nayi kaina yana ƙasa.

Sakin hannu na yayi a hankali sannan ya jingina da jikin ƙofar ɗakin,lumshe idanu yayi sannan yace"ba zaki iya ba ko".

Da sauri na kalle shi,idanun nashi yana lumshe,cigaba da cewa yayi"nima ban san me yasa nake jin hakan yayi mini nauyi ba".

"ki je ki shirya kan ki,wankan tsarki kuma ki shirya yin shi nan da kwana huɗu",daga haka ya juya ya fice.

Bayan shi nabi da kallo ina mamakin meya saka shi dogon wannan ra'ayin?,sannan me yake nufi da nan da kwana huɗu zan yi wankan tsarki.

Ganin bana da amsa yasa na juya na shige bathroom ɗin,abinda ya bani mamaki yadda naga mensturation ɗina.

Kamar na nutse a bayin tsabar kunya,haka nayi wankan ina mamakin ya akayi Yaya Khaleel ya san cewa al'ada na tazo?.

Koda na gama wankan sai da na fara leƙawa naga babu kowa sannan na fito,jikin madubin naje na tsaya ina shafa mai.

Koda na gama sai da na fara neman kayan da zan saka,ina tsaye jikin wardrobe ɗin ya shigo.

Kallo ɗaya yayi mini ya kauda kai gefe,jin wani abu yana tsarga mishi,yace"madam ai nan ba ɗakin ki bane dan haka babu kayan ki nan,kin ga inda naki kayan yake".

Kallon shi nayi,ya juyar da fuska sannan kuma yana nuna ƙofa,tahowa nayi a hankali ina so na ga inda yake nunawa.

Shi kuwa jin ɗumin mutum kusa dashi yasa ya juyo da sauri,runtse idanu yayi yace"pls ki saka hijab sai na kai ki".

Sai da ya faɗi haka sannan na kalli kaina,sai lokacin naji wata irin kunya ta dirar mini.

Yaushe na koma haka ne,ai wannan ma sai ya ɗauke ni bana da kamun kai,dan ma dai gidan mu ɗaya ya san yanayin tarbiyar gidan namu da kuma na mahaifiya ta.

Hijab na ɗauko na saka,kallo na yayi sannan yace"na rasa yaushe kika koma haka wankan tsarki kwata-kwata kin canza".

Ƙasa na kalla kawai domin dai naji kunya sosai,gaba yayi ni kuma na bishi a baya har zuwa ɗakin.

Ƙofar ya tura mini,ni kuma na shiga,ɗakin ya haɗu sosai komai kalar Lemon green ne.

Ga wani ƙamshi da yake tashi,bin ɗakin nayi da kallo,makeken italian bed ne a ciki wanda yaso yafi na wancan ɗakin girma.

Wardrobe kuwa ta cika bango ɗaya,sai gefe dressing mirrow wanda yake facing bed ɗin.

Couch kuma daga jikin window sai ɗayan ɓangaren bayi,daga ƙurya kuma change room ne.

Haƙiƙa tsarin ɗakin yayi mini kyau sosai,dan komai yayi kyau a ciki,wardrobe ɗin na buɗe kaya ne shaƙe a ciki.

Ɓangaren atamfofi da kuma lace daban haka ɓangaren kayan kanti da ƙanana daban.

Sai gefen jakunkuna da agogo da kuma undies wanda sune a sama,can ƙasa kuma set ɗin takalma ne kala-kala.

Inda yake tsaye yana kallo na na kalla nace"Yaya wannan duk kayan fa",murmushi yayi yace"kayan matar da zan aura ne,ke ɗakin ma gaba ɗaya nata ne".

Taɓe baki nayi nace"yayi kyau sosai nata ma yafi naka kyau",murmushi yayi wanda har sai da jerin ƙananan haƙoran shi suka fito yace"ai kin san son da nake mata yafi wanda nake yiwa kaina shi yasa dole na gyara mata ɗakin ta yafi nawa kyau".

"to dama anan zaka barta ba zaka tafi da ita borno ba",na tambaya ina ƙoƙarin kauchewa haɗa idon da yake so muyi.

Ɗaga gira yayi yace"eh a nan zan bar ta,kinga kema sai ki dawo nan gidan da zama kawai dan naga kina son zaman sabon gari".

Ɗagowa nayi cikin fushi nace"ni ba zan zauna a wajen matar ka ba,kuma ai na faɗa maka sai bayan nayi aure zaka yi".

Dariya yayi wacce ta ƙarawa fuskar shi haiba da kwarjini da kyau,yace"hakane fa sarautar mata,ni ban taɓa ganin inda ƙanwa ta tsarawa yayan ta lokacin auren shi ba sai kanki".

Hannu na nuna shi,raina a ɓace dan har ga Allah raina ya ɓace,yatsan ya riƙe yace"stop threaten me mana,kina tsorata ni da yawa,sorry kinji".

"muga hoton ta na buƙata",wayar shi ya ciro sannan ya miƙo mini,amsa nayi na kalla,fuskar ta yayi duhu kaɗan sai dai zan iya shaida abu biyu daga gare ta.

Tana da gashi sannan kuma tana da dimple,miƙa mishi wayar nayi sannan nace"wannan ai bata ma fini kyau ba,dan duk abinda take dashi ina dashi".

Kallo na yayi ya ɗaga gira ɗaya,yace"really!?",ɗaga kai nayi dan ban kawo wani tunanin ba.

Raina har wani zafi yake yi,ƙirji na yana bugawa ban san meya saka hakan ba,shi kuwa abin dariya yake bashi da mamaki yarinya ƙarama da kishi haka!?.

Be kuma cewa komai ba ya wuce ya ɗauko mini kaya daga wardrobe ɗin,miƙo mini yayi yace"gashi saka mu tafi".

Ban san na dalla mishi harara ba,sai da naga ya zare idanu yana faɗin"kai ni kike harara",kaina na saukar ƙasa.

Turo baki nayi nace"ni ba zan saka kayan ta ba",hannu ya saka saman haɓar shi yace"yanzu ya za'a yi kenan".

Haɗe fuska nayi ina wasa da zobe hannu na,damƙa mini kayan yayi yace"please ki saka mana,ai ta bar miki".

Wani kallo nayi mishi sannan nace"kace mata bana so domim kuwa ni ba matsiyaciya bace",ya fashe da dariya.

Hawaye ya zubo mini daga idanu,da sauri ya dakata sannan ya matso kusa dani ya fara lallashi na,a haka har ya samu na saka rigar.

Sosai tayi mini kyau,dan purple ce me adon stones farare sai kuma ɗan kwalin ta fari,dan haka shi na ɗaura saman kaina.

Wani ƙaramin mayafin na yafa a jiki na,maida kaina nayi ƙasa,shi kuwa Khaleel kallo na kawai yake yi fuskar shi ɗauke da murmushi.

Waya ya ciro ya fara ɗauka na hoto,murmushi nayi sosai nake so a yaba idan nayi kyau.

Daf dani ya matso,gyalen ya cire daga saman kaina ya sannan ya ɗauke mu tare,hoton yayi kyau sosai.

"kiyi sauri na maida ki gida",dama ban shigo da komai gidan ba hakan yasa kawai bin bayan shi nayi.

Mota ya ɗauko sannan na shiga muka tafi,a maimakon ya ɗauke hanyar zaria sai ya ɗauki hanyar kwangila,dai dai a Alnasiha muka tsaya.

Gari har ya fara rufawa saboda duhu yayi,jerawa muka yi idan ka ganmu sai ka tsaya kallan mu saboda wani kyau da muka yi.

Kai zaka ce wasu shahararrun masoya ne mu ɗin,Waiter na wajen ne suka fara mana barka da zuwa.

Kujera ya fara ja mini na zauna sannan shima ya ja ya zauna,katin me ɗauke da list ɗin abinda suke dashi ya turo mini.

Amsa nayi sannan nace"me zanyi da ita",murmushi yayi cikin raɗa yace"abinda zaki ci zaki zaɓa baƙauyiya".

Ban kuma cewa komai ba na fara duba jikin katin,sai da na gama sannan nace burger da kuma milk shake.

Kallo na yayi da sauri,har waiter ɗin ya tafi ya kira shi,cewa yayi"ka kawo mata chicken pulser da kuma orange juice,ka haɗo da coffee.

Amsawa waitern yayi sannan ya juya ya tafi yayin da ni kuma na ƙi yadda mu haɗa ido,haka har aka kawo abinda muka yi order ɗin.

Coffee ya ɗauka yayin da ya zuba mini idanu,ni kuma naƙi kallon shi haka kuma naƙi ci.


Sai da ya gama shan coffee ɗin sannan ya ɗauke fork da wuƙa,kallon shi kawai nake yi,plate ɗin yaja gaban shi.

Yanka yayi sannan ya dauƙo ya matso da ita dai dai baki na,so nake na juyar da kaina amma kallon da yake mini yasa na kasa.

Kamar mai yanga na buɗe bakin a hankali ya zuba mini,taunawa nayi sannan na lumshe idanu.

Murmushi muka yi a tare,hannu nasa na amshi cokalin nima na sa wuƙa na yanka na ɗauko da fork na miƙa mishi.

Haɗe rai yayi ya mini alama da ido akan ya ƙoshi,shagwaɓe fuska nayi hakan yasa yayi saurin buɗe baki nima na saka mishi.

Lumshe idanu yayi alamar yayk daɗi,murmushi muka kuma yiwa juna,a haka muka dinga ci idan ya bani na bashi.

Har ya kai ga na miƙa mishi ya ture cokalin yace"kin san fa bana cin abu me nauyi amma kika tilasta mini naci".

Tissue ya ciro ya goge mini baki,nima na ɗauka na goge mishi,wajen muka ji ya ɗauki tafi.

Abin mamaki duka mutanen wajen mu suke kallo,duk da waje ne da kowa ke harkar gaban shi amma ji yadda ake bin mu da kallo.

Har da masu ɗauka a waya,miƙewa muka yi yayin da mutanen wajen suka cigaba da ihu,sosai abin ya birge su.

Wani ɗan matashi ya matso ya miƙawa Yaya khaleel hannu suka gaisa,yace"haƙiƙa oga kun birge mu,wannan kamar a india dana shigo.na ɗauka ma film aka ɗauka sai da naga babu cameras a wajen sannan na fara mamakin dama a cikin hausawa akwai ma'aurata masu soyayya irin haka amma dai sabon aure ne ko".

Sai da Yaya Khaleel ya kalle ni ta gefen ido sannan yayi murmushi yana ɗagawa mishi kai alamar eh.

Wajen ya kuma ɗaukar ihu,saurayin yayi murmushi sannan yace"to oga idan ba zaka damu ba sunan ka dana madam".

Sai da yayi jim sannan yace"Khaleel da Juwairiyya",tafi wajen ya kuma ɗauka,saurayin zai kuma magana Yaya Khaleel yayi saurin jan hannu na.

Wajen cashier muka ƙarasa domin biya,murmushi tayi tace"ai an riga da an biya muku manager ma yace a bar shi domin kun birge shi".

Ta faɗa tana nuna mana inda managern yake tsaye,kallon wajen muka yi mutum ne me ɗan shekaru da dama hannu ya ɗago mana.

Yaya khaleel ma ya ɗaga mishi hannu,daga haka muka yi waje domin tafiya gida.

Ko a mota bance komai ba sai dai ban san meya saka nake iya kauda kunya ta akan Yaya Khaleel ba.

Zuciya ta sai da ta buga lokacin da muka doshi ƙofar doka,don kusan duka iyayen mu maza suna gari dan jiya duka suka dawo.

Ummi kuwa ta kasa tsaye ta kasa zaune babu abinda take tunani sai yarinyar ta duk da ance mata tare da yaya Khaleel muke.

Ɓangaren Momma ma hakane dan Khairiyya taje mata da kuka tana bata labarin abinda ya faru hakan yasa itama hankalin ta ya tashi.

Motar mu na shigowa ta hasko mini Ummi a tsaye a bakin part ɗin mu,gaba na ne ya faɗi.

Shi kuwa Yaya Khaleel kamar ma be damu ba fita kawai yayi ya zagaya ya buɗe mini ƙofa nima na fito.

Momma muka haɗa ido da ita dake tsaye itama a bakin nata sashen Khairiyya na gefen ta,kallon bakin get nayi Baba malam ne da Abba duka suma idanun su na kan mu.


#LIKE
#SHARE
#COMMENTS

*babyn Abdul maman meenal,farouk da elham*.


*ƳAR MUTAN ZAZZAU*


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


1 Comments On KAREENATEEY
avatar
hauwa-8-2

1 year ago

Reply

Mashaa Allah

Please Login or Register in order to submit comment