Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yau mulkin ya tashi kenan.

A hankali na fara tafiya domin barin wajen,da idanu ya bini sai da na ɓace daga ganin shi sannan ya lumshe ido ya daɗe be ganta ba hakan sai yaga ta ƙara mishi girma.

Ɓangaren mu kawai na wuce domin kuwa zan sami sauƙin aikin a can,cous-cous nayi mishi saboda na san yana so sosai.

Koda na gama sai da na shiga bayi nayo wanka,samun kaina nayi da tsayawa na tsantsara kwaliyya sosai riga buba na saka ƴar kanti sannan na zauna na kafa ɗauri me steps.

Turare na ɗauko na feshe jiki na dashi sannan na ɗauko veil na yafa a kafaɗa,kallon kai na nayi a madubi oh ni Juwairiyya yanzu na zama me yawo da mayafi.

Ina ƙoƙarin maidawa Rufaida ta shigo,galala ta tsaya tana kallo na,tayi dariya tana tafa hannu sannan tace"sis kinga kuwa yadda kika haɗu kuwa gaskiya wankan yayi ina ma yaya Khaleel yana nan".

Ta gefen ido na kalle ta,riƙe haɓa tayi sannan tace"sai ina haka ko Jabeer na hanya ne?", na harare ta nace"ke dan Allah kin cika saka ido".

Sai da na ware hijab ɗin sannan nace"Yaya Khaleel zan kaiwa abinci",cikin sauri ta janyo ni tace"ke wallahi ki cire hijab ɗin nan".

Haka ina kallo ta hanani saka hijab dole na saka mayafi domin kuwa bana so muyi ta jayayya.

Jere abincin nayi cikin basket sannan na ɗauka nayi hanyar waje,a falo na sami Ummi zaune sai da na faɗa nata sannan na nufi hanyar waje.

Ina zuwa dai dai bakin ƙofar part ɗin muka haɗu da Khairiyya itama hannun ta riƙe da basket.

Kallon juna muka yi sannan kowa ya kauda kai,ina daga gefe na tsaya ganin yadda take harare harare sannan kuma kamar zata bangaje ni.

Ita ta ƙwanƙwasa ƙofa,Yaya Abdus-samad ya buɗe ƙofar dan haka cikin sauri ta wage baki tace"Yaya sannu da dawowa".

Fuskar shi ɗaure yace"yauwa",daga haka ya juya ya fice nayi murmushi ina ɗagowa muka haɗa ido.

Dogon tsaki taja sannan ta shige ni kuma na biyo ta a baya,ran Khairiyya kuwa a ɓace yake dan tana laɓe tana kallon shigowar shi hakan yasa ta faɗawa Momma ita kuma tayi girki tace a kawo mishi wai kada yaci nawa wanda aka barbaɗe da magani inji ta fa.

Gashi kuma Yaya Abdus-samad ya bada ita a gaba na,hakan ba ƙaramin baƙan ta ranta yayi ba.

Koda muka yi sallama babu kowa a falon dan Yaya Abdus-samad daya buɗe mana ƙofa waje yayi kawai.

Ajiye abincin tayi a falo,nima na ajiye nawa,bedroom ɗin shi ta nufa a bakin ƙofa suka yi clashing.

Fuska a haɗe yace mata"ke lafiya",zunɓuro baki tayi tace"kai zan kira yaya".

"ke da yake wawiya ce sai ki kama shigar mini cikin bedroom babu izini",ƙasa tayi da kai tana ƙunƙunai.

Ni dai ina zaune ina kallon ikon Allah,sai iyayi takw gashi iyayin baya amsar ta.

Ya daka mata tsawa yace"ke out wawiya kawai",juyawa tayi ta dawo ta zauna a ɗayar kujera wacce take facing wacce nake zaune.

Shi kuwa bema lura dani ba sai da ya gama abinda yake yi sannan ya fito jikin shi sanye da singlet da kuma baƙin jeans.

Zama yayi ya zuba mini ido,nima kallon shi nake ko ƙiftawa bana yi,Khairiyya kuwa dake cika tana batsewa tayi gyaran murya.

Ƙasa nayi da kaina shi kuma ya zare nashi idanun ya maida kan Khairiyya,fuska ya haɗe sannan yace"lafiya?".

Duk da yadda take jin tsoron shi sai da ta wulla mini harara sannan tace"yaya Momma tace na kawo maka abinci".

A taƙaice yace"ki ɗauka ki maida kice na ƙoshi",kallon shi ya mayar kaina,da idanu yayi mini nuni akan na zuba mishi.

Cikin natsuwa na sauko na fara zuba mishi abincin,Khairiyya ta taɓe baki tace"mutum dai ya cigaba da iyayi,ance ba'a jin yunwa amma ke kin maƙale to yace baya ci".

Kasa ƙarasawa tayi ganin ya ɗauka ya fara ci,buɗe baki tayi tana mamaki,shi kuwa kamar be san da zaman ta ba.

Lumshe idanu yayi alamar abincin yayi daɗi sosai,murmushi nayi shima yayi mini murmushi.

"ya makaranta?",ya tambaya,kaina a ƙasa nace"tana lafiya kuma karatu yana daɗi sosai",Allah ya taimaka,na amsa da ameen.

Muna fira jefi jefi har ya gama cin abincin,tattara kwanukan na fara yi,yace"baki tambayi ina tsarabar ki",murmushi nayi kawai bance komai ba.

Bedroom ya shiga be jima ba ya fito hannun shi riƙe da babbar leda sai kuma ƙarama.

Babbar ya miƙo mini yace"ga tsarabar ki nan",amsa nayi nace"na gode Yaya Allah ya ƙara arziƙi da buɗi yasa kafi haka".

Cike da jin daɗin abinda na faɗa yace"ameen wankan...",ta gefen ido na kalli inda Khairiyya take idanun fa ƙyam akan mu tana faman naɗa dan taje ta fesar.

Shi kuwa kamar be damu da zaman ta a wajen ba,ni kuwa juyawa nayi kawai na nufi hanyar waje kawai.

Da murmushi ya bini har na fice,ƙaramar ledar ya ajiyewa Khairiyya yace"ga naki nan".

Bata wani yi godiya ba saboda ita ta hannu na take kallo,bata gode wanda Allah ya bata ba na wani take hangowa hakan yasa amsa kawai tayi ta tattara kayan ta ta fice da sauri.

Ni kuwa sauri nake yi domin kuwa Rufaida ta kira akan nayi sauri tana jira na domin mu tafi wajen lalle.

Ta baya ta jani,cikin sauri na ɗago na kalle ta,dama na ayyana hakan a raina,ajiye basket ɗin hannun ta tayi sannan tace"wai ke me kike taƙama dashi ne?,ba zaki fita hanyar yaya Khaleel ba wai ke yaushe zaki dena kwaɗayi ne".

Ƙasa nayi da kai kawai,ta harare ni sannan tace"banza kwaɗayayya kawai,karya kowa bi kike kibi na gida kibi na waje,wai ke yaushe maza zasu ishe ki ne anya kuwa baki da ƙanjamau?".

Da sauri na kalle ta hawaye na zubo mini,taɓe baki tayi tace"dan Allah Juwairiyya kije duk inda aka yiwa yaya Khaleel asiri kije a kwance shi pls and pls koda kuwa da saka hannun tsohuwar magajiyar karuwan nan".

Yanzu kuwa ƙirji na ya fara canza bugawa,har na fara ganin jiri-jiri,bata wani damu da yanayin yadda nake ciki ba tace"koda yake a cikin gida ma za'a iya ƙulle ƙullen abinda ake so ayi tunda waya sani tsohon ko malami ne ko kuma akasin haka".

Ido na na runtse kawai ina dafe saitin zuciya na,dan wani nauyi naji zuciya ta tayi,ƙasa nayi ina faman janyo numfashi na.

Shewa tayi sannan ta saka hannu zata amshi jakar hannu na,riƙewa nayi gam,dariya tayi tace"oh wannan son abin duniyar ina zai kai ki,wato kina daf da wucewa ma amma kin kasa sakin kayan dalla bani".

Hannu ta saka ta fincike ledar,saukar mari taji wanda ya saka ta saki ledar kawai a ƙasa,kai ta ɗago ganin Yaya Abdus-samad yana kallon ta yana huci.

Jikin tane ya ɗauki rawa tuna kashedin da yayi mata a kan Juwairiyya,cikin sauri ya ƙarasa kusa dani ya riƙo ni yana ƙoƙarin ɗago ni.

Yaya Khaleeƙ dake kallin abinda yake faruwa ya koma gefen kujera ya jingina be san meya saka abinda ya faru yanzu mintsilin shi yake yi a rai abinda ya hana shi fita kuwa haushin sanyin raina yake yi.

Duk abinda ya faru a idanun shi ya faru,sai dai har yanzu yana so na koyi tsiwa da dauriya amma abu ya gagara.

Murmushi yayi daya tuna yadda Yaya Abdus-samad yazo ya taimake ta,tuna halin da take ciki yasa ya miƙe da sauri ya ɗauki key ya fice.

Yaya Abdus-samad kuwa kallon Khairiyya yayi yace"wallahi duk abinda ya same ta u will pay for it,kin watsa mata manja ban ɗauki mataki ba kin watsa mata ruwan zafi shima ban ɗauki mataki ba shine yanzu kuma kike so ki kashe ta ko".

Fitowar Yaya Khaleel yasa Yaya Abdus-samad yin shiru,Yaya Khaleel kuwa amsa ta kawai yayi ya buɗe mota ya saka ni.

Shima yaya Abdus-samad bin shi yayi da sauri,Khairiyya kuwa data saukar da kanta ƙasa kamar munafika tana ganin fitar su tayi shewa tace"Allah yasa daga can ki wuce kawai".


Oh ni deeje wai Khairiyya sai yauahe zaki gane gaskiya ne🤔.

Su kuwa asibiti na kuɗi suka wuce dani kawai,Alhamdulillahi kan su ƙarasa ma ai na far a dawowa hayyaci na.

Muna shiga aka bamu gado,sai da suka yi gwaje-gwaje sannan suka yi mini allurar barci,cikin lokaci ƙanƙani barci ya kwashe ni.

Likita ya kalle su yace"yallaɓai dama nafa faɗa muku a guji ɓacin ranta saboda jinin ta na hawa,abin mamaki kuma sai naga jinin nata yanzu ya ƙara hawa ya wuce ƙa'ida.

Yaya khaleel yace"to likita yanzu yaya za'ayi",likitan dake rubutu a jikin takarda yace"yanzu ga wannan takardar magun-gunan da zaku siya mata kenan sannan duk da haka a guji abinda zai ɓata mata rai sannan kuma zata dinga ziyarar nan ana yawan duba ta kuma a dena barin ta ita kaɗai".

Yaya Khaleel ya amshi takardar sannan ya miƙe yayin da Yaya Abdus-samad yabi bayan shi.

Wani medicine store suka je suka siyo magun-gunan sannan suka dawo wanda har lokacin ban farka ba.

Babu wanda suka faɗawa a gida saboda likitan ya riga ya faɗa musu cewa ba kwantar dani za'ayi ba.

Suna zaune Yaya Khaleel na gefen gadon hannun shi na sarƙe da nawa,kallon fuska ta yayi yace"my guy wai meya faru ne".

Yaya Abdus-samad yace"nima kawai na fito ne sai naga tana neman faɗuwa tare ma da Khairiyya muka kusa riƙo ta kuma fa normal take kawai Allah ne ya kawo".

Da mamaki Yaya Khaleel ya kalle shi yace"amma ka bani mamaki yanzu akwai abinda zaka ɓoye mini to a gabana komai ya faru,ban sani ba ko kana tunanin ba zan iya amsar mata ƴancin ta bane?".

Yaya Abdus-samad yace"ba haka bane bana so kullum matsala na faruwa tsakanin ka da Momma ne shiya saka,kuma maganar ƙwatar mata ƴanci ai ƴancin ta kenan hmtayi haƙuri".

Kallon shi kawai yayi ya kauda kai,shima kuma Yaya Abdus-samad be kuma magana ba.

Sai dana kwashi awa shida ina barci sannan na farka,yana gefe na a zaune,kallon ɗakin nayi daga gani a asibiti muke hawaye ya zubo mini.

Ya riƙo hannu na cikin kwantar da murya yace"kiyi haƙuri da komai na rayuwa kinji kuma ki ƙara jarumta mana".

Ɗaga mishi kai nayi yace"yauwa ƴan matan Al'ameen",murmushi ya suɓuce mini,shima yayi murmushi haka Yaya Abdus-samad.

"Yaya me yasa baku zo dashi ba?",na tambaya,yace"kina so ya zo ne?",ɗaga kai nayi dariya yayi kaɗan sannan yace"yanzu ki kwantar da hankalin ki,ki tashi kije kiyi sallar azahar da la'asar anjima kuma Al'ameen yana kan hanya".

Shi ya tainaka mini na miƙe na shiga bayi nayi alwala sannan nazo na tada sallar har na idar da sallar suna zaune.

Abinci ya ɗauko,ya matso kusa dani sannan ya ɗebo abincin ya miƙo shi dai-dai baki na.

Kallon shi nayi,haɗuwar idanun mu yasa wuta tayi tartsatsi ta gauraye jiki na,wani magnet je jana daga idanun shi.

Ban san lokacin dana buɗe baki na ya zuba mini ba,a hankaƙi nake taunawa yayin da shi kuma yabi leɓen nawa da kallo.

Lumshe idanu na nayi murmushi nayi mishi shima kuma yayi mini,haka ya dinga bani abincin hannun mu sarƙe da juna haka ma idanun mu.

A hankali yake murza hannu na wanda yake cikin nashi wanda hakan yasa har wani garɗin abincin nake ji.

Shi kusa Yaya Abdus samad video coverage yake yi mana da kashe mana poster dan kuwa mun burge shi ya san da cewa gaba akwai badaƙala idan bamu auri juna ba.

Har na cinye abincin ban sani ba sai da naji ya saka mini empty spoon a baki,kallon cokalin nayi sannan na kalli take away ɗin babu komai a ciki.

Murmushi yayi yace"kai wankan tsarki wannan cin abinci haka anya ba sai mun kaiwa mijin ki tallafi ba?".

Murmushi kawai nayi,tissue ya yaga ya goge mini baki,har lokacin ban bar kallon shi ba.

Da ido ya mini nuna da lafiya,nima na maida mishi da yayi kyau,murmushi yayi har haƙoran shi ya fito.

"ai ni dama ke kyau ne uwar gida",tafi kawai muka ji daga bayan mu,da sauri muka waiga,likitocin asibitin da ma'aikatan ne kai harda wasu marasa lafiyan na sasibitin wanda suka ɗan ji dama-dama.

Ashe wata nurse ce taga abinda yake faruwa taje ta faɗa musu shine suka zo kallo.

Likitan dake duba ni yace"ah lallau romeo da juliet ko ince layla da majnoon,wannan love haka gaskiya kun birge mu,wannan cikin kwana biyu ai sai jinin yayi ƙasa har tama warke sosai".

Yaya Khaleel yace"ƙanwa ta ce fa likita",kusa duka wajen sunyi mamaki,likitan kuwa kallon Yaya Abdus-samad yayi yace"kazo ka amsar muku sallama".

Duka suka watse suna mamakin irin wannan soyayya,ƴan matan wajen kuma suna burin auren miji kalar shi.

Likita ya kalli Yaya Abdus-samad yace"ka bani address na gidan ku,dan inso naje",yaya Abdus-samad yace"kada ka wahalar da kanka akan su domin kuwa an riga da an ɗaura auren su tun shekara ɗaya data wuce".

Ni kaina one love sai da nayi mamaki,haka shima likitan da mamaki ɗauke a fuskar shi,yaya Abdus samad kuwa murmushi kawai yayi.

*ina godiya da ƙaunar ku gare ni,naga covers na gode sosai na san da cewa inda masoya da yawa har da na bayan fage kuma ina godiya*.



#LIKE
#SHARE
#COMMENT


*babyn Abdul maman meenal,farouk da Elham*.


*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.


♥ ❤

♥♥❤
*~K'AREENATEEY~*
(K'AWATA)

(It's all about friendship)





https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/



*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


*YAN UWA MUNA KARA KIRA DA MABIYA LITTAFAN GOLDEN PEN WRITTERS ASSOCIATION DA SU KIYAYE DA WANNAN MAI CUTAR TASU DA SUNAN YANA SAIDA LITTAFAN KUNGIYARMU,TO KARYA YAKE MACUCI NE KAWAI LITTAFANMU IS FREE 1 NE KAWAI NA KUDI,KUMA DA YACE YANA BA KUNGIYARMU KUDIN REGISTER DIN DA KUKE BIYA DOMIN MU TURA MASHI SABBIN LITTAFAN MU,TO WALLAHI DUK KARYA YAKE MANA MU BAMU DA MASANIYA AKAN WANNAN B'ARNAR DA YAKE MANA SAI DAGA BAYA MUKA JI,SANNAN KUMA INA SON KUSAN NUMBER DIN SHI SABODA YANA NAN YANA SHIGA GROUPS NA MATA DA SUNAN MACE SABODA HAKA KU KIYAYE GA NUMBER DIN SHI NAN (08107707692)*




*written *✍
-by-
*Deeja one love*




*JAKADIYAR GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION👸*



Wattpad 13deeja.


Daga wannan page d'in har zuwa k'arshe sadaukarwa ne gare ki *AISHATU BABAYO* saboda kaunar da kike wa *GOLDEN PEN WRITERS* ba muda abinda zamu biya ki dashi, dan haka *K'AREENATEEY* har zuwa k'arshe ya zama naki sis kiyi yadda kike so dashi, *JAKADIYA* ta baki wannan yan shafukan har zuwa karshe, muna godiya sosai da irin kaunar da kike mana.


An karɓo daga Abu huraira Allah ya ƙara mishi yarda yace:Manzon Allah tsira da Amincin Allah sun tabbata agare shi yace" *duk wanda ya kashe kanshi da wuƙa,to wuƙar shi a hannun shi yana sokawa cikin shi a wutar jahannama yana mai dauwama a cikin ta har abada,wanda yasa guba ya kashe kan shi,to shi zai ta kwankwaɗar ta a cikin wutar jahannama yana mai dauwama a cikin ta har abada,wanda ya faɗo daga saman dutse ya kashe kan shi,to zai ta faɗowa daga saman dutse a cikin wutar jahannama har abada yana mai dauwama a cikin ta*.

*~_Bukhari da Muslim suka ruwaito_~*


_*26*_


Likitan ya dafa shi yace"shikenan Allah ya sanya Alkhairi ya basu zaman lafiya",Abdus-samad yace"Ameen",daga haka ya juya ya tafi.

Ya tarar damu muna zaune muna jiran shi har ya dawo,yana kawo takardar muka wuce muka tafi.

Ko a mota babu wanda yayi magana nima kuma waje kawai nake kallo,ina tunanin rayuwa ta.

Khairiyya cikin kuka tace"wallahi Momma ba zan miki ƙarya ba,a gaba na yaci abincin ta ya bar naki".

Momma ta zauna tana faɗin"aikuwa zai zo ya same ni",miƙewa tayi kuma da sauri ta nufi hanyar fita.

Dai dai muna shigowa gidan tana fitowa,gaba na ya fara faɗuwa addu'a kawai nake yi,be wani damu ba yadda na lura.

Ciki hanzari ya fito ya buɗe mini ƙofa na fito,ledar magun gunan ya miƙo mini sannan yace"Allah ya ƙara sauƙi kije ki huta zan shigo zuwa anjima",daga haka ya juya.

Kamar munafika haka na wuce kawai,ƙwala mini kira Momma tayi,ji nayi kamar fitsari ya zubo mini.

Shi kan shi ni yake kallo,ɓangaren Yaya Abdus-samad na kalla,kan shi a ƙasa kamar ma be san meke faruwa ba.

Ji nayi ƙafafu na yayi sanyi,haka na ƙarasa gaban ta,shima da sauri ya ƙaraso,kallo na tayi sama da ƙasa sannan tace"biyo ni ina son magana dake".

Binta nayi kawai a baya shi kuma ya biyo baya na domin ya san Momma zata iya yin abinda be dace ba.

Muna shiga tace"ga waje ki zauna",kallon shi nayi,alama yayi mini da ido alamar na zauna.

Zaunawa nayi kawai gaba na yana faɗuwa,itama zama tayi sannan ta kalle shi tace"kai fa ka zaunaana ka tsaya kana kallo na".

Zama yayi kawai,sai da ta ɗan tsaya tukunna sannan ta kalle ni tace"Juwairiyya kike ko,magana nake so nayi dake,kin san dai ba'a raba ɗa da mahaifi amma ku ta ƙarfi da yaji sai kun raba ni da ɗan dana haifa".

Miyau na haɗiye,sannan na kalle shi,shima ni yake kallo domin yaga yanayin fuskata,ganin ban nuna komai ba yasa ya mini nuni da ido akan nayi haƙuri.

Momma kuwa da tana kallon mu,wani ɓacin rai ya ƙara danno mata,cikin sauri tace"nan zaki kalla ba can ba,haba wai meye haka ni nayi wahala da yaro na amma kuma kune kuke cin arziƙin shi,kun mayar mini da ɗa kamar bawa".

"amma ban taɓa tunanin gori daga gare ki ba Aunty maryam,idan kin manta zan iya tuna miki da na cewa ni naci kashi naci fitsarin Khaleel a gidan nan,kada ki manta haifa ne kawai banyi na Khaleel ba",muryar Ummi ya ratsa dodon kunnen mu.

Duka maida kallo muka yi kan ta,cikin ɓacin rai wanda ban taɓa ganin tayi ba tace"Yanzu daya zama mutum kika san ya zama abin mora shine har kike mishi iyaka da abinda na haifa,amma kada ki manta babu wahalar shi da ban ci ba,amma tunda kin faɗi haka daga yau duk wani tallafi da yake mata ki sashi ya janye bama buƙata".

Zuwa tayi ta riƙo hannu na tace"ni da kaina zan iya biyawa ƴata kuɗin makaranta da duk abinda take buƙata,bana buƙatar taimakon kowa ni da Allah na dogara".

Ledar dake hannu na ta magani ta amsa buɗewa tayi ganin magani a ciki,bincika tayi ta ciro takardar perception ɗin sannan taje ta miƙawa Khaleel.

Tace"mun gode iya abinda kayi mata a haka ma,amma ka amsa bama buƙata zan je na siya mata".

Miƙewa yayi da sauri yace"Ummi pls wallahi ni ba haka bane a waje na Momma kawai ke faɗin abinda taso,Ummi kada ki yanke alaƙar dake tsakani na da Juwairiya alƙawari na ɗauka akan zan kula da ita".

Girgiza kai Ummi tayi sannan tace"Khaleel a yanzu mahaifiyar ka ta san amfanin ka,dan haka ka rabu da ita saboda samun zaman lafiya".

Miƙa mishi tayi sannan ta kalli Momma tace"Na gode Aunty Maryam duk abinda ke faruwa a gidan nan ina sane dashi kuma ina ji ina gani to naga baku san kawaici ba dan haka daga yau ki faɗawa ɗan ki ban amince da duk wani abu da zai fito daga hannun shi ba".

Jan hannu na tayi muka fice daga ɗakin,a waje muka sami Yaya Abdus-samad,a raina nace"wato Yaya shi yaje ya faɗa mata kenan".

Ni kaina yanzu na fara tsorata da yanayin ummin,bata saki hannu na ba sai da muka shiga falo.

Fuskar ta ɗaure tace"tattaro mini kayan daya baki",jiki na yana rawa na shiga ɗakin mu na kwaso.

Duka ta ɗauka ta fice,zama nayi kawai na buga tagumi ina tunanin anya kuwa Ummu na ce ko kuwa mafarki nake yi.


Yadda ta barsu haka tazo ta same su,zuba kayan tayi gaban Momma sannan ta juya,Yaya Khaleel yabi kayan da kallo.

Komai duka har kayan sakawa duka Ummi ta dawo dashi,zufar fuskar shi ya share sannan ya zame ya tsuguna a wajen.

Be san ya yake ji a cikin ran shi ba,ran shi ya bace sosai,mai da kallon shi yayi kan Momma itama kanta jikin ta yayi sanyi sosai.


Kallon shi tayi da alamu magana take so tayi mishi,girgiza mata kai kawai yayi kafin ya miƙe ya fice daga ɗakin.

To mema zata faɗa mishi?,itama dai kawai maganar take so tayi mishi,a haƙiƙanin gaskiya ta san ɗan nata yana son Juwairiyyar daga yanayin yadda take ganin su.

Yanzu kuma tayi sanadin da ta raba su,murna zata yi ko akasin haka,Khairiyya dake tsaye tana kallon komai.

Tana ganin fitar shi ta buga ihu ta fito tana murna,kayan ta ɗiba tana faɗin"Alhamdulillahi tsuntsu daga sama gasashshe".

Momma ta daka mata tsawa cikin fushi tace"dalla matsa ki bani waje",da mamaki Khairiyya take kallon ta.

Tsaki taja sannan ta wuce ta barta,ɗaki ta wuce ta ɗauko hijab ɗin ta saka sannan tazo ta fice.

Ita kuwa Khairiyya kwashe kayan tayi ta tafi ɗakin ta,tana murna,ta samu kayan kece raini sannan kuma yanzu ta wuce Juwairiyya.

Momma kuwa part ɗin mazan gidan ta nufa,amma duk ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin shi da take yi babu amsa.

Yaya Abdus-samad ya fito daga nashi ɗakin ganin ta a wajen yasa ya taɓe baki kafin yace"Momma bafa ya nan".

Sai da ta tsaya na ɗan lokaci sannan ta juya ta tafi dana sani take tayi,zuga ce kawai tayi aiki akan ta.

Wani sashe na zuciyar ta kuma yana raya mata cewa"ƙwatar wa ɗanki ƴan ci kika yi ai".

Shi kuwa Khaleel yana fita mota ya shiga ya bar gidan,sai da yaje wajen Alhudahuda collage sannan ya sami waje yayi parking.

Kifa kan shi yayi kan steering motar yana tunani,meya saka Ummi zata yanke wannan hukuncin ko babu komai ai shi yayan tane kuma sannan shi ya nemi alfarmar a barta ta cigaba da karatu sannan kuma ya ɗauki alƙawarin kula da duk wani nauyin ta".

Murza atm card ɗin daya bata yayi yana tunanin yanzu taya Ummi zata yanke wannan hukuncin?.

"to kai meye naka na damuwa,ko dai akwai wani abu da kake ji game da ita ne?",zuciyar shi ta tambaye shi.

Ya girgiza kai yana faɗin"ina

1 Comments On KAREENATEEY
avatar
hauwa-8-2

1 year ago

Reply

Mashaa Allah

Please Login or Register in order to submit comment