Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na ajiye sannan na shiga bathroom wanka nayi marar tana mintsina mini.






Ina fitowa ummi ta shigo, sannu da gida nayi mata abinda na lura dashi har lokacin bata wani damu da karatu na ba hakan yasa ko matsala ta bata wani dame ta ba.





A baya idan lokacin period d'ina ya matso ita zata kawo mini pad tare da diclopenac domin in case da yazo kawai na sha,amma wata na uku kenan ko complain na kai mata marata na ciwo Allah ya sauwake kawai take cewa.






K'arar waya ta ita ta dawo dani daga tunanin dana tafi,da sallama na d'aga,amsawa yayi sannan yace"ya jikin zaki iya zuwa?? ".





Kamar wacce akayiwa dole nace"eh",to kizo yanzu", Abinda ya fad'a kenan ya kashe wayar,ajiyar zuciya nayi sannan na mik'e,ummi ta tab'e baki ta fice.





Doguwar riga ta kanti cikin wacce Rufaida ta bani a lokacin da mukaje sabon gari na saka,hijab na dora fari k'arr, sannan na d'auki wayata.





Fitowa nayi, ruwa na d'eba a kofi na karanta fatiha k'afa bakwai sannan na sha domin in samu ya lafa mini.







Babbar wayata na d'auka sannan na fice,wani bak'in ciki ya tarun mini, wai yanzu ummi ko zan kwana a waje bata tab'a damuwa idanu kawai ta zuba mini.




Rufaida na kira nace mata dan Allah idan zata dawo ta siyo mini pad domin ita bata dawo ba saboda yanzu haka ta shiga mpd gudun kada karatun nata yayi rauni.







Da sallama na shiga,kamar koda yaushe Ya Abdus-samad yana zaune yana danna waya shi kuma yana zaune yana danna laptop.




Ina shigowa duka suka d'ago suka kalle ni,k'asa nayi kawai da kai na, sannan na gaishe dasu, yaya Abdus-samad ne kawai ya amsa banda oga daya zuban idanu.





Tsayuwar ta ishe ni na d'an yamutsa fuska,kula da hakan ne yasa yace na zauna,gefe naja na zauna.




Yaya Abdus-samad ya mik'e, ya fice yana amsa waya,kaina na k'asa ban san lokacin daya taso ba sai jin saukar numfashi da naji.






Cikin sauri na d'ago kai na,yana tsugunne a gaba na,gaba na ya tsanan ta bugu,"Me yake damun ki? ",dan ina kusa dashi ne yasa naji abinda yace amma na tabbatar da yaya Abdus-samad yana nan ba zai ji ba saboda yadda yayi maganar k'asa-k'asa.






Kaji shi da wata magana,wai meke damuna??,na fad'a cikin raina, cuno baki nayi nace"nima ban sani ba",murmushi yayi na gefen baki.





Ban yi aune ba kawai naji ya rik'o hannu na,tafin hannun ya bud'e,ban san me yake kallo ba sai naga ya saki dariya.





Sakin hannun yayi sannan yace"mik'e tsaye",kamar yadda ya umarta haka na mik'e,bedroom be dad'e ba ya fito hannun shi rik'e da ruwa.





Mik'o mini yayi sannan ya b'allo maganin shima ya mik'o mini, Amsa nayi ina yamutsa fuska nasha.





Hannu na ya kuma rik'ewa ya kai ni har bathroom amma be shiga ba,a bakin k'ofa ya tsaya sannan yace"shiga ki gyara kan ki".




Ya fad'a yana saka mini pack na paddery,cikin tsananin kunya Na amsa sannan na shige.





Tsayawa nayi ina bin bayin da kallo, ko'ina tsaf-tsaf,yaya khaleel akwai tsafta yau fa ya dawo amma har ya wanke bayin.






Kayan nawa na cire tabbas dana duba na b'ace, murmushi nayi ina fad'in "na shiga uku na yaya khaleel".





Wanka nayi sannan na wanke kayan na shanya a bayin duk da kunyar da nake ji,sai da na lek'o naga babu kowa sannan na fito.




Man shi na shafa kamar kwanaki kaya na gani gefen gadon shi hakan yasa na d'auka kawai na saka.





Riga ce bak'a sai gaban ta da akayi kwaliyya da stone zama kuma anyi tattara da wani yadi me santsi fari,sai skirt d'in ta fari irin me bud'ewa d'in nan ne.






Mayafin fari ne hakan yasa na bud'e shi na yafa tunda yana da girma, kallon turaren shi nayi wanda idan ya fesa nake jin kamshin shi .




D'auka nayi,na fara fesawa, kamar ance kalli madubi muka had'a ido dashi,yana tsaye a bakin k'ofa ya zuba mini idanu.





Jiki na y fara rawa, kamar muna fika na ajiye turaren,a hankali ya fara takowa zuwa inda nake.





Wayyo kamar nayi fitsari a wajen,bakina har rawa yake yi,k'asa na kalla idanu na suna kawo ruwa.





Hannu yasa a hab'a ta ya d'ago da fuska ta,juna muke kallo ni kam ba zan ce ga abinda nake gani ba sai dai ji nake har tsigar jiki na tashi take yi.




Hannu ya sa ya d'ago gyalen daga kafad'a ta ya d'ora saman gashi na wanda daman tunda muka fara kallon juna gyalen ya fad'i saman kafad'a ta.






Murmushi yayi zuciyar shi na canza bugu ganin yadda yarinyar tayi kyau sosai,hannun shi yasa ya zagaye ni dashi.






Dole na tsaya domin dai yanzu ta dole ya koyi tab'a ni, shi kuwa he can help him self out,na lura indai be tab'a ni ba baya jin dad'i.





Mun yi nisa cikin kallon juna kowa da abinda yake sak'awa cikin ran shi, muka ji k'ara tare da flash a haske mu.




Cikin sauri muka kalli k'ofar yaya khaleed ne a tsaye bayan shi kuna yaya Abdus-samad wanda suke kallon mu kamar sun samu tb.





Da sauri ya sake ni nima kuma da sauri na tsuguna a wajen,"yaya shigo mana",ya fad'a cikin basarwa.





Yaya Abdus-samad yace"ma shigo kuna nan kuna soyayya,ni wallahi ban so ka tona mu ba shiyasa da zan d'auki nawa na kashe flash d'in".





"Ai nima mantawa nayi da kashewa zanyi amma dai hoton yayi kyau sosai",yaya khaleed ya fad'a yana k'arasa shigowa ciki.





Da sauri na lallab'a na fice daga d'akin, wato ma hotunan ba d'aya ba kenan,ina daf da fita naji yace"dawo".





Tsayawa nayi sannan na juyo yana tsaye a k'ofar bedroom d'in shi ya saka hannayen shi duka a cikin aljihu.





A hankali na dawo na zauna,sai lokacin na lura da wayoyi na dake ajiye akan kujera,juyawa yayi ya koma ciki.






Hannu na saka na d'auki babbar, ina d'auka messages na shigowa,dubawa nayi pics d'in mu ne yaya khaleed ya turo mini.



Khaleed ya kalli d'an uwan shi yace"khaleel ka dawo cikin hayyacin ka, momma fa fushi take da kai".




Khaleel yace"to yaya kake so nayi yaya?,yarinyar nan fa anriga da an bani permission na cigaban karatun ta".




"Ni ba haka nake nufi ba, me zai hana ka d'an janye daga shige mata da kake yi,kayi kamar ka ban zantar da ita daga baya sai ka dawo ka cigaba da kula da itan idan har momma ta sauko", khaleed ya bashi amsa.





Kallon yaya khaleed yayi ya girgiza kai yace"yaya ba zan iya ba kada ka manta har tana kud'in transport yana kai na ne idan har na barta waye zai bata!?".





"To me zai hana ka kama mata accomodation kaga sai idan taso shine zata dawo gidan ko kuma idan anyi hutu".
.




Shiru yayi yana tunani,ganin hakan Yaya Abdus-samad da tun d'azu be ce komai ba yace"kaga babu ruwan ka dame ka tura mata babu wanda zai sani sannan ita kanta zata sami sauk'i na al'amuran gidan".





Ajiyar zuciya yayi sannan yace"shikenan zan ga yadda za'a yi zuwa next registration sai na nema matan kawai", daga nan yaya khaleed ya mik'e sannan yace"ni zan wuce sannan ya kamata kaje ka gaida momma ka kuma duba lafiyar khairiyya ",daga haka ya fice.




Ina zaune a falo yazo ya wuce ni,yana d'an tsokana ta ni kuma ina dariya dan bani da abinda zan ce.





Be dad'e da fita ba,yaya khaleel suka fito, sanye yake da yadi me taushi a jikin shi, kan shi babu hula, yayi kyau sosai.





Yana fitowa na mik'e, shima kallo na yayi sannan yace"ki tsaya ki gyara mini d'aki sannan ki nema mini abinda zan ci mara nauyi, hope yanzu dai marar ta dena ciwo".




Ta gefen ido na kalli yaya abdus-samad kamar bamu yake kallo ba hankalin shi na kan agogon da yake d'aurawa.




D'aga kai nayi nace"eh ya dena",jinjina kai yayi sannan ya juya ya fita yayinda cewing gum d'in shi ya bishi a baya.




Da kallo na bisu har suka fice,ajiyar zuciya nayi wanda yayi dai-dai da k'arar waya ta,d'agawa nayi ganin Rufaida.




"Haba juwairiyya kince na siyo miki abu gashi tun d'azu ina part d'in ku bakya nan, na tambayi ummi tace bata san inda kike ba haka ma Abdul'azeez shima yace ya dawo ya tarar bakya nan ne, wai ina kika shiga ne? ".





"Ina d'akin yaya khaleel, yanzu haka ma gyarawa zanyi",dariya tayi k'asa-k'asa, sannan tace"gani nan zuwa".





Bathroom na shiga kayana har sun fara bushewa,wanke shi nayi tas, sannan na dawo bed room na gama gyarawa kenan Rufaida ta shigo.





Tare muka gyara falon, sannan na koma bathroom na kwaso kaya na, kallo na tayi tace"wa'innan kayan fa? ".




Hararar ta nayi sannan nace"wallahi yanzu kin cika saka idanu",dariya tayi tace"Allah yasa muna da rai za'a yi",duka na kai mata.




Ta goce tana dariya, muna fitowa momma na k'arasowa, da mamaki take kallo na,da sauri nayi k'asa da kai na.




"Oh na shiga uku ni maryama naga ta kaina daga dawowar shi ai kya bari ya huta amm dan maya ta har kin zo inda yake.





Rufaida ta gaishe da ita, babu yabo ba fallasa ta amsa,nima gaishe da ita nayi, mari ta wanke ni dashi sannan ta kama kunne na.





Cikin gargad'i tace"wallahi idan baki fita harkar yaro na ba sai na wulak'anta rayuwar ki keda uwar taki da take d'aure miki gindi".




Cikin jin zafi hawaye suka zubo mini, cikin kuka nace"kiyi hak'uri momma",rank'washi na tayi saura kad'an fitsari ya zubo mini.





Harara ta balla mini sannan tace"sai ki fad'awa shi wanda kika shanye d'in cewa uwar shi tana son ganin shi, kuma wallahi ki kiyayeni,ni kuruwata tafi k'arfin ki, shegiya dangin mayu", haka ta yi gaba tana cigaba da zagi na.







*A gaskiya ina godiya sosai da irin k'aunar da kuke nuna mini,na san kud'i baya tab'a siyan masoya ina godew ubangiji bisa wannan kyautar da yayi mini na gode sosai da sosai, sannan ina k'ara baku hak'uri na rashin ganin k'areenateey kullum, kuyi hak'uri ku cigaba da bina dan har yanzu labarin bema soma ba, na gode sosai da sosai*.






#LIKE
#SHARE
#COMMENTS.




*_Babyn Abdul, maman farouk meenal da elham_*.





*YAR MUTAN ZAZZAU*.



♥ ❤
♥♥❤
*~K'AREENATEEY~*
(K'AWATA)

(It's all about friendship)

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*





*written *✍
-by-
*Deeja one love*




*JAKADIYAR GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION👸*



Wattpad 13deeja.


Daga wannan page d'in har zuwa k'arshe sadaukarwa ne gare ki *AISHATU BABAYO* saboda kaunar da kike wa *GOLDEN PEN WRITERS* ba muda abinda zamu biya ki dashi, dan haka *K'AREENATEEY* har zuwa k'arshe ya zama naki sis kiyi yadda kike so dashi, *JAKADIYA* ta baki wannan yan shafukan har zuwa karshe, muna godiya sosai da irin kaunar da kike mana.





_Allahumma inney a'uzubika minal hammi wal hazni wal ajazi wal kasli wal jubni wal bukhli wadala'id daini wagalabatir rijal_.





_An karɓo daga Abu Huraira Allah ya ƙara masa yarda yace"manzon Allah tsira da amincin Allah sun tabbata agare shi yace:ana amsawa ɗayan ku Addu'ar sa matuƙar beyi gaggawa ba har yace" na roƙi Allah amma be amsa mini ba_.





*TSOKACI*

da farko dai ya ƴan uwa na ku sani idan har kun roƙi Allah to matuƙar Addu'ar ku ta cika sharaɗi,to Allah zai amsa,kada kayi addu'a ka gindayawa ubangiji cewa yanzu kake so ya biya maka ita.




Akwai addu'ar da mutum yake yi amma ba'a bashi sai tsayin lokaci ba wai dan Allah beda shi ba a'a dan ya jarabta ka yaga zaka yi haƙuri,Annabin Allah Annabi musa yayi Addu'a amma sai bayan shekara Arba'in abinda ya roƙa ya tabbata.



*LOKUTAN DA ALLAH YAFI AMSAR ADDU'A*.

Bayan kiran kowacce sallah ta kamsi salawat,wato azahar la'asar magrib isha da kuma asuba,bayan kayi addu'ar da manzon Allah ya koyar.




Ƙarshen dare wato kashin ƙarshe na dare misalin ƙarfe uku kenan na dare shima Allah yana saukowa a daidai wannan lokacin kuma addu'a tana amsuwa.





Loƙacin da ruwan sama ke sauka,shima a lokacin Allah ya bude ƙofar rahamar shi da tuba.





A yayin naƙuda,dai dai lokacin da kan yaro ya kusa fitowa,shima wannan lokacin lokaci ne me tsada Allah yana amsar Addu'a.




Ranar Arfah,rana ce me tsada wanda Allah yake Amsar addu'a duk wacce kayi ta.




Yayain sujjada wannan shima lokacin Allah yana amsar addu'a sosai.





Lokacin da mutum ya kai azumi wato yayi ifɗar shima lokaci ne me tsada da duk abinda mutum ya roƙa Allah amsa.


Allah kasa mu dace ameen.




*_16_*




Khaleel ya kalli yana yin garin yace"guy mu wuce five stars hotel kawai,dan kan mu ƙarasa barrack ruwan nan zai sauko.





Direct suka wuce can kawai,no 443 suka kama,suna shiga ɗakin yaya Khaleel ya cire kayan shi ya wuce bathroom kawai.



Sai da ya fito wanka ya canza kaya zuwa nighties sannan ya ɗauki waya ya kira major Aliyu,ya sanar dashi cewa ruwa ya tare su.




Major Aliyu yace"babu komai Insha Allah da yau da gobe duka ɗaya ne a wajen Allah",haka suka yi sallama.






Yaya Abdus-samad shima wankan yayi sannan yazo ya kwanta,Yaya khaleel shi a Lokacin har ya fara barci.





Zuby ta buɗe idanu,cikin sauri ta miƙe ta zuba mishi idanu,dariya yake yi,jikin shi ɗaure da towel yana tsane sumar kan shi da ƙaramin towel ɗin.





Cike da mamaki tace"my soldier Khaleel",ta ƙarasa sunan tana murmushi,jin saukar mari ya dawo da ita hayyacin ta.



Dafe kunci tayi sannan ta kalle shi,fa'iz ne tsaye a kanta ranshi a ɓace yake jifan ta da mugun kallo.





Da mamaki take kallon shi,cikin fushi yace"Uban waye Khaleel kuma",kai ta saukar ƙasa.




"ba magana nake miki ba haka jiya kika dinga ambatar sunan,kada kice mini kin canza ni ne,wallahi sai na kashe shi".





Shaƙe mata wuya yayi,idanun ta ya kawo ruwa ganin kamar ba'a hayyacin shi yake ba yasa ta fara ihun neman taimako.




Khaleel yaja tsaki jin ihu yaƙi ƙarewa,tattara kayan su ya fara yi sannan yace"my guy ka taso mu wuce kawai wannan ƴan iskan zasu fasa mana kunne".





Ita kuwa duk abinda hannun ta ya kai ɗauka take tana ƙwala mishi,so take kawai ya sake ta amma abu yaci tira.




Securities suka ƙaraso bakin ƙofar,spare keys aka saka sannan aka buɗe,da ƙyar suka ƙwace ta.



Shi kuwa fa'iz babu abinda yake amabata banda sai na kashe ki sai na kashe shi,ke macuciya ce".




Zuby kuwa tunda taji ta shaƙi iska purse ɗin ta kawai ta ɗauka da sauri tayi waje tana shafa wuyan ta.





Cak ta tsaya ta zuba mishi idanu,yana tsaye ya harɗe hannuwan shi a ƙirjin shi,yana kallon ta da ɓacin rai a fuskar shi.





Duk da yadda tayi kewar shi amma bata so haɗuwar su ya kasance anan ba,gaban ta ya buga.




Dafe kanta tayi tace"na shiga uku ni zubaida",ɗagowa tayi gaba ɗaya ta tsargi kan ta ganin yadda yake kallon nata.






"hi" tace mishi tana washe baki,kallon ta yayi up and down kafin ya juya ya tafi,Abdus-samad yabi bayan shi kawai.





Ajiyar zuciya tayi kafin tayi saurin fita,kan ta fito har sun fice,motar tasu tabi da kallo tana mai wasi-wasi a zuciyar ta.






Cikin sanyin jiki ta nufi motar ta,ta shiga sannan ta tada motar itama ta rufa musu baya.




Koda suka isa direct office ɗin mahaifin ta suka wuce,sai da suka yi duk abinda zasu yi,daman file na zaman da sukayi a Abuja zai amsa yana amsa kuwa ya wuce.






Shima ɗin major gida ya wuce,yana parking itama tayi,da sauri tace"dad welcome back home yanzu dama nace bari na biya ta office ɗin ka ashe gwara da banje ba".





"zubaida ina kika kwana jiya,dan baki kwana a gidan nan ba",yarfe hannu tayi tace"daddy ba dai ka fara zargi na bane".





Girgiza kai yayi yana faɗin"a'a ni na isa kawai dai na tambaya ne amma tunda bakya so shikenan zo mu shiga ciki,yanzu muka rabu da lit.Ak ya dawo daga zaria jiya yace mini a five star hotel suka kwana".




Gabanta ya faɗi cikin sauri tace"bayan haka fa?",kallon ta yayi yace"meya faru",girgiza kai tayi tace"a'a babu komai kawai dai ƙawata itama acan ta kwana ne,ya faɗa maka wani abu kuma?".





"a'a be faɗa mini wani abu ba,ko wani abu ya faru ne",ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ta sauke"a'a kawai dai ƙawar tawa ke bani labarin wai taga wani soja wanda ya birge ta inaji shine".





Riƙo hannun ta yayi yace"may be to,amma kuma ai shi ya faɗa mini cewa da safe suka baro tun kan mutane su fara zirga-zirga".





Jan kujera tayi ta zauna tace"oh dad ka manta kawai ka sani ko ita ta ganshi,shi kuma be gan ta ba".




"oh yes "ya fada yana zama,haƙiƙa yana son yarinyar shi saboda mahaifiyar ta da Allah yayiwa rasuwa tun tana ƙarama.





Haka suka ci abinci cikin farin ciki da annashuwa,sama ya nufa inda ita kuma tayi ɗakin ta.





Kamar yadda ta zata zuly bata nan,ɗan ƙaramin tsaki taja sannan ta cire kayan ta,tayi bathroom.






Koda ta fito ta sami zuly a zaune wanda alamu ya nuna bata daɗe da shigowa ba,kallon juna suka yi sannan kowa ya saki tsaki.





Itama zulyn bayin ta shiga tayi wanka sannan ta fito,a tsaye ta sami zuby sanye da atamfa doguwar riga.





Kallon ta tayi sannan ta taɓe baki tace"da alamu Khaleel ya dawo",murmushi ya suɓuce mata gira ɗaya ta ɗaga mata.





Jinjina kai tayi tace"kina tattare da aiki wallaho",ita dai bata ce mata komai ba ta ɗauki gyalen ta ,ta fita.






Ƙaramin tsaki zuly taja tace"iska na wahalar dame kayan kara",daga haka ta cigaba da shirin ta.





Zuby kuwa mota ta shiga ta tada ta fice daga gidan,fuskar ta cike da annashuwa,a dai dai bakin get ta tsaya.




Yau fuskar a ɗaure take haka kuma sanin ko ƴar waye yasa yau basu hanata shiga ba,gashi dama bata zo da wargi ba.





Khaleel da tunda suka taho hanya yake jan tsaki,shi dai dama Yaya Abdus-samad be tanka mishi ba.





Suna isowa wanka kawai ya shiga yayi,farar singlet ke jikin shi sai wando three quater me ruwan kunun kanwa.







Laptop ɗin shi ya janyo sannan ya fara aikin shi,shi kuwa yaya Abdus-samad kitchen ya shiga domin sama musu abinda zasu ci.







Knocking yaji,cike da mamakin waye tunda ya san Al'ameen kaɗai ke zuwa kuma shi yana kaduna har yanzu be dawo ba.





Bada iznin shigowa yayi,kamar mutuniyar arziƙi haka ta shigo,shi kuwa mamaki kawai yake yi meya kawo wannan kuma?.







"ina kwana?"ta gaishe dashi,kallon ta yayi ƙasa da sama sannan yace"lafiya",daga haka ya cigaba da abinda yake yi.






Ni kuwa jiki Alhamdulillah,sai dai tunda suka tafi nake jina wata iri,kamar wacce wani ɓangare na jikin ta ya bar jikin nata.







Da yamman kuma Abba da momma suka zo harda yaya Khaleed,ni dai tunda na gaishe da momman bata ce mini ko ya jikin ba,khairiyya kuwa ko kallo na bata yi ba,da Rufaida suka ɗan taɓa fira,ni dai bata tasu nake yi ba.






Bayan sun tafi da daddare kuma Hajiya da Umma sai Baba malam suma suka zo,Hajiya kam ita bayan na gaishe da ita tace ya jiki,amma daga nan bata kuma magana ba,nima kuma haka.




Da zasu tafi suka wuce da Rufaida,haka na zauna na rasa tunanin da zanyi,kamar na kira shi sai kuma na fasa,wannan videon da Rufaida tayi mana shi kawai na dinga kalla har barci ya ɗauke ni.







Washe gari aka sallame ni hakan yayi mini daɗi sosai domin zaman ya ishe ni,Rufaida kuwa kullum tana waje na.





Sai da na ƙara kwana biyu sannan na koma makaranta,banda ƙawa hakan yasa babu wanda ya tunkare ni da maganar meya hana ni zuwa nima kuma ban damu ba.






Amma dai ya kama ta ace nayi ƙawa koda guda ɗaya ce gudun irin wannan,to wama zan zaɓa duka nice bana basu fuska,Ya Allah ga baiwar ka juwairiyya.





Yaya Abdus-samad ya fito hannun shi ɗauke da plate na abinci,ɗayan kuma tea,kallon ta yayi sannan ya kalli ɗan uwan nashi.






Aikin shi kawai yake yi yayin da ita kuma ta zuba mishi idanu,share tan da yayi be dame ta ba tunda ya bata damar kallon shi.






Miƙa mishi kofin hannun shi yayi,sannan shima ya zauna ya hau cin abincin,Khaleel yace"kaga na kira juwairiyya bata ɗaga ba".





"amma ka san may be yanzu tana aji ko?",girgiza kai yayi yace"hakane kuma fa,to yanzu ya zanyi ne?".




"ka bari sai anjima"ya bashi amsa yana murmushi,wai ya zai yi ne???abin dariya😂😂.





Kallon shi ya kuma yi,shi kuwa khaleel kallon da Abdus-samad yayi mishi,shi ya tunatar dashi meya faɗa.






Cikin waskewa ya janyo laptop ɗin shi ya cigaba da aikin da yake yi.







Zuby kuwa wani ƙolulun baƙin ciki ya tokare ta,wato a gaban ta yake ambatar wata ƴar iskar ma kenan.






Ihu tayi wanda sai da suka rufe kunnuwan su,cikin tsananin rainin wayo yace"su ashe da mutum a wajen,amma kuma ai nan be miki kama da asibitin mahaukata ba ko,ya kama ta ki fita sai ki nema a aiki can,idan kuma na sojoji kike buƙata we have guardroom".







Hawaye ya zubo mata,tama kasa magana,shi kuwa yaya Abdus-samad bece komai ba,baɓda cigaba da cin abincin shi.







"wacece juwairiyya or what??",ita kanta bata san lokacin da tambayar ta fito daga bakin fa ba.





"to momma sai ki shaƙe ni na faɗa miki,kin tashi kin fita ko sai na balla ki,gaba ɗaya yanzu kin raina ni,idan banda raini kinje kin gama iskancin ki da wani ƙaton banza yanzu kuma kin dawo kina so kiyi mini hauka,kin tashi kin fita ko kuwa?".






Miƙewa tayi cike da rashin kunya tace"Ai wallahi koma wacece bata isa ba,kuma ka sani abinda ya faru ba wai shike nufin abinda kake tunani muka aikata ba,sannan maganar na fitar maka daga gida,kai ka san gidan mu ba sak na tsaya dogon bayani ba,kuma wallahi ina nan dawowa",taja tsaki sannan ta fice.





Cigaba suka yi da harkar su,domin dai a banza ya ɗauke ta,gaba ɗaya ba tada saiti ma.






Tana tafe tana masifa ita kaɗai"wallahi koma wacece bata isaba,Khaleel nawa ne ni ɗaya babu wacce ta isa",haka take faɗa tana maimaitawa.






Oh really🤔zamu gani waye zai yi winning zubaida Aliyu ko kuwa juwairiyya mahmoud muktar???.



*sai kun cigaba da bina a cikin dai littafin ƙareenatey*



*kuyi haƙuri da wannan iya ƙoƙarin da zan iya muku kenan,na gode*.




#LIKE
#SHARE
#COMMENT


*Babyn abdul,maman meenal,farouk da kuma elham*





*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.


♥ ❤

♥♥❤
*~K'AREENATEEY~*
(K'AWATA)

(It's all about friendship)

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*





*written *✍
-by-
*Deeja one love*




*JAKADIYAR GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION👸*



Wattpad 13deeja.


Daga wannan page d'in har zuwa k'arshe sadaukarwa ne gare ki *AISHATU BABAYO* saboda kaunar da kike wa *GOLDEN PEN WRITERS* ba muda abinda zamu biya ki dashi, dan haka *K'AREENATEEY* har zuwa k'arshe ya zama naki sis kiyi yadda kike so dashi, *JAKADIYA* ta baki wannan yan shafukan har zuwa karshe, muna godiya sosai da irin kaunar da kike mana.





_Allahummaghfir lihayyina wa mayyitina,wa shahidina wa gha'ibina wa saghirina wa kabeerina wa zakarina wa unsana,Allahumma man ahyay tahu minna fa ahyihi alal islam,waman tawaffaitahu minna fatawaffahu alal iman,Allahumma la tahrimna ajarahu,wala taftinnah ba'adahu_.





An karɓo daga Anas Allah ya ƙara masa yarda yace:manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yace"duk wanda yake so a yalwata masa arziƙin sa,a kuma faɗaɗa masa takun sa to ya sadar da zumanci.




_Allah shine wanda ya shinfiɗa muku Ƙasa,ya gina muka sama ginawa,Sannan ya saukar muku da ruwa daga sama,sai ya fitar muku da ƴaƴan itatuwa arziƙi gare ku,kada ku sanyawa Allah kishiyoyi Alhalin kuna sani_

*suratul baƙara,aya ta 22*



Masu tambaya akan meye ma'anar sunan wannan littafin,to wannan sunan littafin yana nufin *ƙawata* ne kamar yadda nake rubutawa a baka biyu,amma ainihi larabci ne,zan muku cikakken bayani a feji na gaba.





💃💃💃 muna taya ki murnar dawowa daga tafiyar da kika yi,yar gatan golden pen,dafatan an dawo lafiya sannan kuma anyi mana tsaraba,*Aishatu babayo*.





*Ebraheem Aliyu da kuma Sardauna ina godiya sosai da sosai,a tashi a cigaba da typing muna nan muna jiran Habibullah*.


*zainab bala Abubakar da kuma Meera ta annabi ga naku page ɗin saboda ina jin daɗin comments ɗinku*.




Al-Baseeɗu



*_17_*



Tana shiga ɗaki ta faɗa gaɗo kawai ta fashe da kuka,zuly taja tsaki tana

1 Comments On KAREENATEEY
avatar
hauwa-8-2

1 year ago

Reply

Mashaa Allah

Please Login or Register in order to submit comment